Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

doing here?"

"Son, Kakan ka ya rasu da safiyar yau" ta faɗi cikin muryan kuka


"Allah ya ma sa rahama"

"Zan wuce Bahrain gobe. Za ka je?"

"i'm busy" ya faɗa a taƙaice

"Saboda ni ko saboda Sabreen ne ba za ka je ba"

"Enough Justice Nabilah. Ki fita min a ɗaki"

"Najeeb please" Mom ta faɗa kamar za ta yi kuka.

"Ke ko Sabreen, ba ku da wani matsayi da zai sa na yi abu ko kar na yi abu"

Hawaye ne ya gangarowa Mom ta yi saurin sharewa ta ce " sai yaushe za ka yafe mi ni"

"When you are ready to tell the truth"

"Najeeb!" Ta faɗa da ƙarfi.

"Oh, Justice ki na tsoron gaskiyan ne?"

Shiru Mom ta yi tana ƙoƙarin maida hawaye.

Sai da ya ga ta fice ɗakin sannan ya sauke numfashi, zama yai a bakin gadon lokaci guda jikin sa ya fara maƙyarƙyata, abinda ya gani shekaru ashirin da ɗaya da su ka wuce ya fara dawo ma sa. Duk yadda yai ya manta da komai ya ka sa. He was only thirteen amma yana iya tuna komai harta fiskar wanɗanda su ka ɗau gawan a ranan...


...............


Washe gari da wuri Farida ta je office ta ajiyewa Najeeb takarda a table ɗin sa. Bai fi minti shabiyar da isowarta ba sai ga shi ya zo. Tana gaishe shi ma amma ko kallon ta bai yi ba. Sai da ta bashi minti biyar sannan ta bi bayan shi. Takardar ne a hannunsa lokacin da ta shigo.

"Sir na san na yi laifi amma ka yi haƙuri dan Allah"

Ya na so ya ma ta faɗa, ya na so ya nuna ma ta ko shi waye, amma ba zai iya ba saboda ransa da ke a ɓace saboda kuma...

Cillar da takardar ba da haƙurin da ta rubuto yai sannan ya ce " get back to work"

Ta yi mamaki da bai yi masifa ba ita kam hutarerenta ai. Har za ta fita sai kuma ta lura da yanayin sa kaman ba shi da lafiya ko kuma akwai abinda ke daminsa dan tsakanin jiya da yau ya chanja ma ta gaba ɗaya.

"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?"

"Get out Miss Salihu"

Simi-simi ta fita kar ma ta tunzura shi ya ce zai hukuntata.

Ya fara duba wasu takardu amma hankalinsa ya kau, tunanin kyakyawar fiskarta ya ke da murmushinta mai shiga zuciya. Ya missing ɗin ta sosai, *Aysherh* ya furta a hankali.

Ya na mamaki da Aysherh Farida ba ta da sanyi da haƙuri irin na Aysherh. Halin su ya sha banban duk da kuwa sunan su ɗaya....



***

Aisha Mustafah Jibo ta taso cikin soyayya da kulawar iyaye da 'yan uwanta. Kasancewarta kurmiya bai rage ma ta komai ba na jin daɗi a wajen iyayenta. Gata kam tana samu tun daga kan Alhaji da yayyanta ga uwa uba uwar da ta shayar da ita wato Hajiya Mama.

Karatu mai zurfi Alhaji Mustafah ke so Aisha ta samu saboda ya zamo ma ta gata ko ba sa raye, wannan ya sa ya turata ƙasar waje karatu wajen yayanta Adam. Komai cikin sauƙi Adam ya nema ma ta tundaga dreba zuwa ma su kula da ita a gida saboda shi da Nabilah ba zama su ke ba. Sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin Aisha da yaran Adam musamman Najeeb wanda ke da shekara tara a lokacin. Kamar wata babbar yayarsu su ka ɗauketa hakanan itama ta kan zama yarinya acikinsu duk da ita ɗin ma ba wai ta girme su da yawa bane dan shekararta goma shabakwai.
Yaran da sun dawo daga makaranta su na maƙale da ita, za ka gansu da biro da takarda suna hira da Aisha ko kuma suna wasa. A hankali har su ka iya maganan kurame ya zamo idan za su yi magana ba sa buƙatar su rubuta sai dai su yi yaren kurame.
Shekaru biyu kenan da komawar Aisha wajen Adam. Duk hutun ƙarshen shekara ta ke zuwa gida amma su Alhaji da Hajiya Mama su na kawo ma ta ziyara lokaci zuwa lokaci. A wannan ƙarshen shekaran da ta je ta tarar Alhaji ba lafiya. Nan ta tubure akan ba za ta koma America ba sai dai ta zauna kusa da Baban ta.

Adam daga Belgium ya taho dubiyan Alhaji saboda a lokacin an maida shi chan. Zuwan sa kuwa ya tarar jikin Alhaji yai tsanani. Shi da su Sulaiman su ka fara yunƙurin yadda za a yi su turashi ganin likita a ƙasar waje sai dai shi Alhajin ya ce ba inda zai je. Ana gobe Adam zai koma Alhaji ya nemi alfarma a wajen sa duk da alfarmar ta zo ma sa bazata amma Alhaji ya fi ƙarfin haka a wajensa dan haka ba tareda ya ja ba ya amince. A yammacin ranan aka ɗaura auren Adam Usman Jibo da 'yar uwar sa Aisha Mustafah Jibo. Washegari ya koma saboda jikin Alhajin ya fara sauƙi dan an sallamoshi daga asibiti.
Kwana uku da tafiyar Adam, Alhaji ya rasu mutuwar da ta girgiza 'ya'ya da 'yan uwansa musamman Aisha.

Sai da aka yi da gaske kafin Aisha ta yarda ta koma karatu duk da kuwa ta san da auren Adam a kanta dan Alhaji ya gaya ma ta kafin ya rasu.

Larabawa da shegen baƙin kishi, tunda Adam yai wa Nabilah bayanin aurensa da Aisha sai ta tuɓure ma sa ta ce ita ba ta san zan ce ba. Sosai abin ya jawo rikici tsakanin su.
A da ba ta shiga harkan Aishan dan ba ta da lokacin ta amma tunda ta zamo matar Adam sai abin ya chanja, kullum cikin tsangwamarta ta ke. Ta kori dreba da mai kula da ita da Adam ya ɗauka ma ta, ta hana yaranta kulata amma Najeeb bai daina ba sai ma ƙara jin son Aishar da ya yi.
Lokaci guda Aisha ta chanja kullum sai ta yi kuka a ɓoye saboda indai Najeeb ya ganta cikin ɓacin rai to sai ya yi ta tambayar ta dalili haka shima ranan ba za a gane ma sa ba.
Allah-Allah Aisha ta dinga yi ta gama makaranta ta bar mu su gidan ta koma Nigeria.
Shi Adam a nashi ɓangaren duk lokacin da ya zo yana ƙoƙarin ganin komai ya tafi dai-dai sai dai ita Aisha ba ta nuna ma sa tana cikin matsala haka nan Nabilah ma tana nuna komai na tafiya dai-dai.
Ganin ba abinda ya ke shiga tsakanin su ya sa Nabilah ta ɗan saki ranta kaɗan, sai dai shi a nashi ɓangaren ganin Aisha na karatu ya sa ya bari har sai ta gama tukunna ya tare da ita.

Wani hutu, Nabilah ta ɗau Najeeb da Najma ta wuce da su Bahrain wajen iyayen ta. Sai aka bar Aisha a gida.
Aisha tun tana tsoro har ta dena, kwana uku da tafiyar su Adam ya zo ya ɗauketa ya wuce da ita Belgium.
Ya kira Nabilah ne sai Najeeb ya ɗauka ya ke shaida ma sa ai sun bar Aisha ita kaɗai a gida kuma itama ta gama jarrabawarta.

A Brussels babban birnin ƙasar Belgium su ka sauka. Ba su tsaya ko'ina ba sai gidan shi. Haƙuri ya dinga ba ta na barinta da aka yi ita kaɗai.
Da dare ya zo dubata a ɗakin da ya sauketa sai ya samu tana kuka. Hankalinsa a tashe ya ce " Aisha mi ya same ki?"

Ya ɗauko biro da takarda ya ma ta rubutu. Ya miƙa ma ta biron akan ta rubuta ma sa amsa. Ta amshi biron ta rubuta " ina so na je wajen Mama"

" ba kya son zama da ni ne? Kin tsane ni ko? Saboda ba na zama ina kula da ke" ta yi saurin girgiza kai bayan ta karanta.

Jawota jikinsa yai ya rungumeta sosai ya na ɗan bubbuga bayan ta a hankali har bacci ya saceta...

Wannan sati ukun da ta yi a Belgium cikin gata da kulawa ta yi su. Adam yana tare da ita koyaushe, harta office mafiyawancin lokuta da ita ya ke zuwa. Har 'yar ƙiba ta yi saboda kwanciyar hankali.

Da hutun ta ya ƙare ya maida ita lokacin su Nabilah sun dawo. Ita da ta dawo ba ta ga Aisha ba, ta ɗauka Nigeria ta wuce sai da ta ga Adam ya dawo da ita hankalinta ya tashi. Ta san yadda ta gansu akwai abinda ya shiga tsakanin su nan da nan ta nuna sai dai Adam ya rabu da ita ba za ta iya zama da kishiya ba ko kuma ya rabu da Aisha.

Rikici sosai su ka yi har ya ma fi na farkon lokacin da ya ce ma ta ya auri Aisha.
Ƙarshe ta ce za ta shigar da shi ƙara a raba auren tunda ba zai saketa ba. Ta chanja gida ta ɗau yaranta amma Najeeb ya gudo ya koma wajen Aisha.

Abu sai ƙara rikicewa ya ke, wata rana da ta zo ɗaukan Najeeb sai ta lura da ciki ajikin Aisha, wannan ya sa hankalinta ya kuma tashi. Ƙarshe ta shigar da Adam ƙara, ganin ya ba da haƙurin ta ƙi haƙura ya sa ya ma ta saki ɗaya dan mutum mai matsayi irin na sa ace yana hayaniya da matarsa a kotu ba dacewa bane...

Ma su aiki biyu Adam ya ɗaukawa Aisha dan su dinga kula da ita lokacin cikinta ya girma.

Lokacin da cikin ta ya shiga wata na takwas Hajiya Mama ta ce za ta zo ta zauna da ita, ta shirya zuwa sai aka ma ta rasuwa Babban yayan su ya rasu sai ta ɗaga tafiyar zuwa wa ta sati....



***

"Sir Najeeb, Sir Najeeb"

Muryan Farida ya dawo da shi daga dogon tunanin da ya ke.

"Sir ka na da meeting ƙarfe tara"

"Ok" kawai ya faɗi ya miƙe tsaye.

Yanayinsa kaɗai ya nuna ma ta akwai abinda ke damun Najeeb, kuma koma minene to yana da girma.



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣1️⃣4️⃣


Tana zaune a office Faruƙ ya kirata wai gashi a kamfanin su. Kwatancen office ɗin ta ta ma sa sannan ta ajiye wayar tana cigaba da aiki. Minti biyar kacal sai ga Yakubu da Faruƙ sun shigo.

"Farida haka yaron nan ya zama luƙeƙe. Kin san da farko ban ganeshi ba"

"Kai ma ka faɗa ai, wannan sai ya goyeni yai yawo da ni duk faɗin garin nan bai gaji ba"

"Haba Anty, ɗan ni ɗin nan" Faruƙ ya faɗi yana dariya

Yakubu ya fita ya basu wuri, dama wajen Anas zai je ya haɗu da Faruƙ ɗin.

'Yan uwan biyu su ka zauna su na taɗi, su na yi su na dariya.


Wayar Farida ya ƙarɓa ya na duba hotuna. Ko ba a gaya ma sa ba ganin hotunan selfie da Farida ta yi da wani saurayi ya tabbatar ma sa shine Rayyan.

"Sis, wannan shi ne sirikin na mu ?"

"Kai ba na son gulma"

"Wallahi ba ku da ce ba, wannan ai kin fi ƙarfinsa. Hmm ina tausaya ma sa wallahi, aka yi auren nan mijin ta ce zai koma dan ba zai iya da masifar ki ba"

"Buuuuyagi" wafce wayan ta yi tana faɗin " ka ji min rainin hankali, wato dai ni ka ke zagi ko" ta maki kafaɗar sa ta ce " Faruƙ yaushe ka raina ni haka?"
Yarfe hannu ta farayi shi kuma ya fara dariya. " jikin ka kamar wani katako, wai yaushe ka girma ne haka? Faruƙ"

"Serious Anty Farida ba ki dace da shi ba, kin ga lokacin Lukman..."


"Faruƙ!" Ta faɗa da ƙarfi.

Ya haɗa hannu ya ce "afuwan Anty na ta kai na"

Haɗe fiska ta yi ta tsume.
Faruƙ ya sa hannu ya fara tattaɓa kumatun ta yana tsokanarta kaman yadda yake yi lokacin suna yara.
"Anty kumatu, Anty Kumatuttu"

Ba ta san lokacin da dariya ya kuɓuce ma ta ba.
"Yaron nan ka mugun raina ni wallahi"

Yai dariya ya ce " na tuna da, lokacin idan na ce mi ki Anty Kumatu har maƙota sai anji faɗar mu"

Ta fara dariya sosai harda kama ciki.

Faruƙ ya cigaba " lokacin tunda na gano bakya son sunan sai na samu abun tsokala. Kin tuna lokacin da ki ka kwaɗa min tukunya har goshi na ya fashe?"

"Ai ranan Ummi ta zane ni kamar ba gobe" ta faɗa cikin dariya. Suna cikin dariyan kakkausan muryan Najeeb ya doki kunnen ta.

"Miss Salihu"

"Sir" ta faɗi tana miƙewa tsaye.

"To my office"

Ya jima tsaye yana kallon su tun daga lokacin da Faruƙ ya ke shafa mata kumatu. Zuciyar sa ta yi baƙi haka nan idon sa ya kaɗa yai ja, a take ƙwaƙwalwarsa ta tariyo ma sa sunan da ya gani ranan *My Ray*
Ta ya za ta kawo saurayinta har office tana iskancin da ta ga dama. Enough is enough dole ya taka ma ta birki. Abinda zuciyarsa ta tsayar kenan dai-dai lokacin da Faridan ta shigo.

"Ga ni Sir" ta faɗi a hankali

Da ƙarfi ya fara masifa "Miss Salihu yaushe ki ka maida office wajen soyayya da iskanci?. Listen young Lady, idan ba ki san yadda za ki kama kan ki ba go and get married. Ki dena mayar min da office wajen karuwanci. And i..."

"Sir Najeeb ba fa ni na kar zomon ba balle a bani ratayar sa. Daga ƙani na ya kawo min ziyara sai ka maidashi wani zancen banza wai karuwanci. Ba Karuwanci ba a'a Kwartonci"

Kalmar *ƙani na* da ya ji shi ya sanya duk wani masifar da ke cinsa ta washe, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kamar kiftawar ido, muryar sa da yanayin sa su ka chanja. Cikin sanyin murya ya ce "Miss Salihu, da ƙanin ki da saurayin ki, nan ba wajen ziyara ba ne"

Haushin sa da ta ji kaman ta makeshi takeji sai dai yanzu ba ta son samun matsala da shi dan ankusa biyan albashi, ƙaramin aikinsa ne ya cire mata wani kaso a ciki.

"Zan iya tafiya?"

Yai ma ta nuni da hannu. Sai da ta fita ya sauke numfashi. Cikin zuciyarsa yana cewa to ma miye ruwansa idan ma saurayinta ne?.


Tana zama ta yi tsaki " shi komai masifa, yai wa mutum kyakykyawar fahimta ba zai yi ba"

"Sis Ogan kin nan ya burgeni fa. Saurayi da shi amma ya mallaki babban kamfani kamar wannan, gaskiya na jinjina mi shi"

"Ko za ka je ya baka aiki ne. Nan za ka san wannan saurayin zuciyar dutse gareshi"

"Oh really"

"Hmm ai ni ma ba dan bana barin hau ta hauni ba da tuni an jima da fatattaka ni"

"Kai Masha Allah, wa su kam Allah ya basu duniya, ga shi handsome, ga kuɗi, ga class..."

"Zan make bakin ka Faruƙu"

Dariya yai ya ce " Jiya na yi mafarkin kin auri wani millionaire. Wai gamu a wani haɗaɗɗen mansion, wai nan ne gidan ki"

"To Sayyadi Sheikh Umar Faruƙ, ma su mafarkin waliyyai"

"Da gaske fa Anty Kumatu"

Ta ɗau wani littafi za ta buga ma sa ya kauce yana dariya...



...................


Wannan karan ba ta yi garajen barin wajen aiki ba dan ta san yana ɗaya daga cikin babban dalilin da ya sa Najeeb ya rage albashinta a watan farko da ta fara aiki. Ranan Laraba ta tambayeshi leave ɗin kwana biyu ya ce ya bata kwana ɗaya. As usual sai da ta yi ƙorafi amma bai kulata ba.
Wannan karan bayan Walima ba abinda za'ayi. Baffa yai iya ƙoƙarinsa wajen yiwa Maijiddah kaya, duk da bikinta ya zo ma sa cikin matsi.
Ranan Alhamis aka je yi ma ta jere, su Farida ne 'yan gaba-gaba wajen ganin komai ya tafi dai-dai. Gidan yana da kyau sosai, tana da ɗakuna biyu na ta sannan an ware ma ta kitchen daban sai dai store ne za su haɗa da Aneesa...

Gidan ya cika saboda gobe ne walima jibi Asabat kuma a ɗaura aure. Farida tun da su ka dawo daga wajen jere ba ta samu zama ba, shiga ta yi cikin ma su haɗa kayan waliman gobe ana aiki da ita.
Cikin ma su aikin cupcake ta ke ana yi ana hira. Chan wata 'yar uwar su wanda ita kan ta Faridan ba ta san takamaimai ta ina su ka haɗu ba ta ce " Ikon Allah, kaman ba yau aka yi hidiman bikin Farida ba, na tuna cake ɗin da aka yi ranan mai daɗi, su Talatun Haruna ne su ka yi cake ɗin nan ko?"

Farida ta fusata da wannan zance. Ta miƙe tsaye " Inna Tabawa ki ke ko wane. Wallahi ki riƙe girman ki, na ga take-taken ki tun awajen jere. Ba zan miki da daɗi ba"

"Daga magana. Ni na ce kiyi sosayya da ɗan shege" Taas Farida ta wanke ta da mari ai kuwa matan kowa ya tashi wasu su ka ja Farida gefe wasu kuma su ka tsaya da Inna Tabawa da ta ke ta zage-zage...

Kai tsaye falon Baffa Ummi ta shige da ita bayan an kawota wajen Ummin.

"Mi ye haka Aishah?, zafin kan ki har ya kai ki mari mace kamar Tabawa"

"Ummi so ta ke ta ci mutuncina cikin jama'a. Tun a wajen jere ta ke ta min habaici ina shareta. So ta ke wanda ma ba su san abinda ya faru ba su sani"

" shikenan?" Ummi ta faɗi ranta a ɓace

Farida ta kalli mahaifiyarta da mamaki ta ce "Ummi maganan Lukman fa"

" da ta yi maganan akwai abinda ya ragu ko ya ƙaru a jikin ki ne?"

Farida ta girgiza kai.

"To ni banga abin ɗaga hankali ba anan. Ƙaddarar ki ce ta zo da haka. Kuma Alhamdulillah Allah ya chanja mi ki da mafi alkhairi sai ki yi ta gode ma sa, ki share 'yan gulma da gulmar su"

"Amma Ummi..."

"Kul. Ba na son jin wani magana, ki je ki nemi abinci ki ci ki samu ki huta"...


Ɗakin su Yakubu ta shiga ta ke cin abincin, ba wai daɗin abincin ta ke ji ba sai dai saboda Ummi ce ta takura sai ta ci. Gaba ɗaya zuciyarta na ma ta ɗaci. Duk yadda ta so ta basar da abin ta ka sa, kawai sai hawaye. Ta ya za ta manta da wannan rana a rayuwarta, ranan da ya kamata ace ya zamo ranan farin ciki amma kuma komai ya zo ya dagule, ya zamo ranan shine rana mafi baƙin ciki a tarihin rayuwarta. Sai da ta yi kuka mai isarta kafin ta share hawaye ta tattara kwanukan ta fita...

...................


Anyi Walima lafiya, sai dai duk yadda Farida ta ci burin ganin anyi komai da ita abinda ya faru daren jiya ya kashe ma ta jiki. Da farko ma shiri ta yi kawai za ta wuce office amma amarya Jiddah ta hanata.
"Dan Allah Anty Farida kar ki tafi, ki taimakeni ki tsaya ayi komai da ke. Ke ce support ɗina Anty"

"Na san kin ji abinda ya faru jiya, ba na son tsayawa anan wata ta gayamin maganan banza mu kwashi 'yan kallo. I dont want to ruin your day"

"Anty dan Allah ki mance da komai, Allah ina buƙatar ki kusa da ni fiye da kowane lokaci"

Da ƙyar Farida ta haƙura ta tsaya. An ci kuma an sha sannan an kira Malami ya yi wa'azi.

Washe gari Asabat ƙarfe shaɗaya aka ɗaura auren *Hauwa Maijiddah Musa Wase da AbdulWahab Bello Hassan Kachako*

Ɗaurin auren da ya samu halarcin manya-manya mutane, ta ɓangaren Alhaji Bello Kachako da shi kan sa AbdulWahab ɗin.
Da dare aka kai amarya gidan ta wanda kwana biyu kawai za ta yi su wuce Lagos...


Gidan Amarya Maijiddah kam bayan kowa ya tafi aka bar amarya da halayenta.
Tun safiyar yau ta ke gudawa saboda tsoro da fargaba.
Akwai mafiya yawancin mutane da idan su na cikin damuwa ko tashin hankali ko tsananin farin ciki ko baƙin ciki za ka ga yanzu-yanzu cikin su zai hautsine su fara ziryan banɗaki.
Maijiddah was nervous tun wayewar garin yau, abu ne da ta jima tana roƙo sai gashi ya tabbata, wai ga ta amarya. Ta sha Flagyl kam har ba adadi duk dan ta samu sauƙin wannan abun amma kaman tunda Maghriba ta do so abin ya fara ƙaruwa. Yanzu haka kafin Farida ta tafi sai da ta tabbatar ta sha magani amma yanzu da ta ke ita kaɗai sai ta ke jin cikin ta na ƙugi yana kuma murɗawa.

Tana cikin wannan yanayi wanda ta kira da ƙarshen kunya aka shigo ɗakin. Buɗe ƙofar ɗakin yai daidai da kukan da cikinta yai "ƙululululu"

A hankali ya tako wajen da ta ke ya ajiye ledar hannun sa akan drawer sannan ya tsugunna gaban ta ya sa hannu ya ɗaga gyalenta sama yana mai yin Bismillah.
Jikinta rawa ya ke, sai zufa ta ke haɗawa. Na farko saboda tsoro na biyu kuma saboda yanayin da ta ke ciki.

"Alhamdulillah, finally Gimbiya Allah ya nuna ma na wannan rana"

Duk maganan da ya ke yi sama-sama ta ke jin sa. Kamar ta saki ihu ta ke ji saboda kunya da haushin kan ta. Ta ya za ayi daren farkon su ace ta ɓarke da gudawa, wannan abin kunyan har ina.

Hannunta ya kamo yana wasa da yatsunta bayan ya zauna kusa da ita.
"Bari mu yi sallah sai mu ci abinci, na san baki ci wani abin kirki ba yau"

A karo na ba adadi cikinta ya sake yin ƙugi, wannan karan kam AbdulWahab ya ji.

"Sorry princess yunwa ko?"

Idan ta cigaba da shiru za ta cutu haka nan da kunya ace ta gaya ma sa matsalarta sai dai ya za ta yi.

"Ki shiga ki yi alwala ni inada alwalata" ya katse tunanin ta

Ai da sauri ta miƙe ta shige banɗakin. Duk yadda ta so ta daure ta yi alwala amma hakan bai yiwuba dole dai sai da ta je ta zauna a toilet. Ƙarshen kunya sai ga shi ƙaran gudawan na fitowa da ƙarfi wanda tabbas ta san AbdulWahab da ke ɗakin ya ji.
Ta gama amma kunya ya sa ta kasa tashi ta yi flushing, ta jima tana zaune daga baya ta yi ta maza ta tashi ta flushing na shi sannan ta yi alwala. Sai dai ka sa fitowa ta yi daga banɗakin dan ba ta san da wanni ido za ta kalli AbdulWahab ba.

Jin shiru kuma ta ƙi fitowa ya ce " gimbiya ko na zo na fitar da ke ne?"

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito. Daga bakin ƙofa ta tsaya kanta a ƙasa ta ce a hankali " I'm sorry, cikina ne ya ruɗe Yaya"

Tasowa yai har wajen da ta ke tsaye ya kamo hannunta ya ce " There's nothing to be sorry about my dear, mun riga mun zama ɗaya ai"

Sai da ya zaunar da ita sannan ya ce "kinsha magani?" Ta ɗaga ma sa kai.

"Barin haɗo mi ki tea sai ki fara sha"
Fita yai daga ɗakin wanda cikin minti shabiyar da ya ɗauka sai da Maijiddah ta sake zagayawa banɗaki.

Lokacin da ya dawo ya sameta a ɗan kwance gefen gado. He know she's nervous shiyasa ta ke experiencing wannan abun. Ya tuna akwai wani abokinsa mai irin wannan, ko exam za su yi sai ya ɓarke da gudawa, a ranan da za su fara exam na Waec shekaru da dama da su ka wuce sai da Hussaini ya makara saboda ruɗewa da cikinsa yai.


A yadda ya ganta she's already weak, idan yai yunƙurin yi ma ta wani abu that will label him a cruel man.
Taimaka ta yai ta tashi ta sha tea ya haɗa ma ta da kaza.
"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zan miki, ki ci ki samu ƙarfin jikin ki"

Shi da kan shi ya fara ba ta naman a baki har ta ƙoshi. Ya ce ta shiga ta yi wanka ta ce na yi.

"Kinga yanzu jikinki ya tsatstsafo da gumi saboda tea da ki ka sha. Ki je ki watsa ruwa"

Gaba ɗaya kunya sai ya sake rufeta. Ta tashi ta shiga ta sake wanka da ta fito ba ta same shi ba ya tattara wajen. Ta yi saurin buɗe closet ta nemo kayan bacci riga da wando ta sa, sannan ta ɗaura hijab akai.

Da ya dawo a zaune a bakin gado ya sameta.
"Hauwerh cire hijabin nan akwai zafi"

Ba mu su ta cire hijabin ta sunkuyar da kai tana wasa da bakin pyjamas ɗin ta.

"Ya cikin na ki?"

"Da sauƙi"

"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru kin ji"

Ta gyaɗa kai.

"Now breath in and breath out"

Ba ta gane ba har sai da ya nuna ma ta yadda za ta yi da kan sa sannan ta yi yadda ya ce. Sai da ta yi kusan sau goma kafin ya ce ta kwanta.

Kafin ya shimfiɗa sallaya yai sallar nafila tuni bacci ya sace amaryar sa. Da ya idar sai ya gyara ma ta kwanciya sannan ya kwanta bayanta ya musu addu'a ya kashe wutan

Please Login or Register in order to submit comment