Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na san bayan tea ba abinda ka sa a baki"

"Did i complain?"

"Idan kai ba za kula da kan ka ba, i'll help you do that"

Kafin a kawo abincin wayar Anas ta yi ringing ganin mai kiran ya sa ya ce da Najeeb yana zuwa. Fita yai daga wajen don ya samu daman magana sosai.

Wata budurwa da saurayi su ka shigo wajen cin abincin . Hankalin Najeeb na kan wayar sa dan haka bai lura da su ba, sai dai table ɗin da ke kusa da na su su ka zauna, da ke budurwar ce ta bashi baya dan haka bai ga fiskarta ba sai dai ya ga na saurayin lokacin da ya ɗago zai ɗau ruwan da waiter ya ajiye mishi.

Surutun da budurwar ke yi ya sa ya ƙara tsanar wajen saboda hayaniya da ta cika shi. Tukunnama, ta ya mace za ta dinga surutu haka in a public place kamar wannan. Tun da su ka shigo siririn muryanta ya gauraye wajen. Kafin saurayin da su ka shigo tare yai magana ɗaya budurwar ta yi ɗari. A haka Anas ya shigo ya same shi, su na fara cin abincin Najeeb yai tsaki ya aje fork da sokali sannan ya ɗau tissue ya goge bakin sa.

"Abincin bai ma ka ba ko?" Anas ya tambaya yana kallon sa. Najeeb ya ɗau ruwa ya kora batareda ya bawa Anas amsa ba. Tsakani da Allah ba wai abincinne bai ma sa ba, ba kuma yunwanne ba ya ji ba. Sai dai surutun wannan budurwane ya cika ma sa kunne. A rayuwarsa ya tsani hayaniya balle kuma yawar magana.
Kamar Anas ya gane damuwarsa ya ce a hankali "wannan yarinya ba dai surutu ba. Kamar radio"

Najeeb ya cigaba da danna wayarsa ba tareda ya ce komai ba...


..........


"Ka san Allah, idan na yi wata ɗaya a garinkun nan toyewa zan yi. Irin wannan zafi haka!. Da wayona Ray ban taɓa fin sati uku a Kano ba, ina ma zan iya"

Farida ta faɗi tana kora ruwa amaƙoshinta saboda tunda su ka zauna ta ke ta zuba surutu.

Rayyan ya ce "gashi ɗan Kano za ki aura ba"

"Ai ka ji inda matsalar ta ke, ina ga fa sai dai kai ka dinga zuwa Jos, dan ba zan tare a Kano ba. Tukunna Ray, wai a garin nan ka taso cikin wannan zafin?"

Rayyan ya langwaɓe kai dan wannan tambayar kusan karo na uku kenan da za ta yi shi a ɗan zaman su a wajen nan.

" My Farida mu ci abincin nan, zai yi sanyi fa"


A hankali ta fara tauna jollof rice ɗin wanda ko loma uku ba ta kai ba ta ajiye cokali. Ta yiwa wani waiter hannu akan ya zo.

Rayyan ya ma ta kallon mi ke faruwa amma ta kauda kan ta ta yi kamar ba ta gani ba.

"Waye ya girka abincin nan?" Tambayar da ta yiwa waiter kenan.

"Any problem ma'am?" Ya tambaya with politeness.

Farida ta kalli abincin ta kalle shi sannan ta ce "abincin ku shine problem ɗin ai. Na san wadda ta girka abincin nan ko tantama babu Bayarabiya ce. Idan ba haka ba taya za'a yi jollof rice a restaurant kuma a cika ma sa yaji. An gaya mu ku kowa ne ke son yaji? ko kuma dai so ku ke mutum ya ci ya koma gida yana gudawa. Da a garin da ba zafi ne sai ace ya yi dai-dai amma wannan Kanon na ku da shegen zafi kuma ku dafa abinci mai yaji kuna ba wa mutane. Mi ku ke nufi?"

Waiter ɗin bai gama fahimtar maganar Farida ba, saboda ba wani hausan kirki ya iya ba. Shekaran sa na uku kenan a Kano. Ya dai gane kalmar 'Yaji' dan haka ya ce " ma'am with due respect, i dont think the food is pepperish"

Farida ta hangame baki " Yo ƙarya na ke yi kenan?"

"Sorry ma'am"

Rayyan ya girgiza kai ransa a ɗan ɓace ya ce " Farida dan Allah ki barshi haka, bari a kawo mi ki fried rice"

"A'a Ray, sai ya taɓa abincin nan ya ji dan ya tabbatar da magana ta"

Wani matashi wanda tun shigowar su Farida ya ke ankare da yadda ta cika wajen da surutu ya taso ganin dramar da ake yi.

"Haba Madam. Tun ɗazu ki ke damun mutane da surutu fa, kar ki manta nan public place ne"

Kallon sama da ƙasa ta ma sa sannan ta ce " Malam sa'ido,gulma da munafurci. Kunnen ka bai jiyo surutun da ke fitowa daga TV ba sai nawa. Tsabar ha'inci ka bar matarka da cin garau-garau , ka zo ka tisa tumbinka a gaba kana cin fried rice da chicken, Allah wadai"

Kunyar da Rayyan ya ji ko wanda aka yiwa maganar bai ji ta ba. A ƙalla mutumin nan zai kai shekara Arba'in, amma Farida ba ta ga girman sa ba ta ke yaɓa ma sa magana.

Mutumin ya zuba ido yana kallon ta kawai tsabar mamaki.

"Kalleni da kyau Malam na fi ƙarfin ka, inma kana ƙungiyar mafiya ne to jinina fau-fau ya fi ƙarfin ka"


Mutumin ya kalli Rayyan ya ce "ɗan uwa gaskiya kana ƙoƙari. This girl is fire" sannan ya koma table ɗin sa.

Ta ce "Ba fire ba Volcano. Mtsww"

Ta kalli waiter ta ce "taste this food before i loose my temper"

Da sauri ya ɗau sokali ya ɗeba abincin ya taɓa. Irin masifan da ta yiwa mutumin nan wai ta ce ba ta loosing temper ba to idan ta yi ya za ta zama kenan.

Tabbas abincin ya ɗan fito da taste ɗin yaji amma bai kai har yadda Farida ta kururuta ba.

"Sorry ma'am, i apologise on behalf of our kitchen...."


Lokaci guda Najeeb ya miƙe tsaye hakan ya bashi damar ganin fiskar budurwar wanda alokacin ke yiwa waiter bayanin abinda zai kawo ma ta a madadin jollof rice mai yaji da su ka kawo. A yadda ta ke masifa ya ɗauka zai ganta gabjejiya sai ya ganta 'yar mitsila bai fi mutum ya mangajeta ba amma sai shegen baki. Kallo ɗaya ya ma ta ya ɗauke idon sa ya fice daga restaurant ɗin.
A mota ya jira Anas wanda shi kam sai da ya ci yai naƙ sannan ya fito.

"Mutumina ka san yarinyar nan ta bi waiter har kitchen ɗin su. Na ji tausayin saurayinta wallahi, haka yai wani lafau da shi abin tausayi"

Najeeb ya ce " its his fault ai, ta ya zai dating lousy girl kamar wannan"

"Yarinyar tana da kyau ba laifi, sai dai surutu kam Tabarakallah ko gidan radio iya ka ci" ...


Rayyan da Farida kuwa ba su suka bar restaurant ɗin ba sai da Farida ta sauke masifar ta ta huce. Shi Rayyan abincin ma kasa ci yai, ita kuwa aka kawo ma ta fried rice ta naɗa harda take away ta yi.



....................


"Gaskiya Yaks idan na ce ma ka akwai vacancy a ƙasa na yi ƙarya, sai dai ka bani lokaci nan zuwa next week zan bincika, idan ma ba ta samu anan ba zan iya nema ma ta a wani wajen. Ai ƙanwar mu ba za ta rasa aiki ba Insha Allah"

Yakubu yai ma sa godiya sannan ya fice daga office ɗin.
Anas kenan, yana da sauƙin kai ba kaman Oga kwata-kwata ba, wanda mulki da girman kai ya hanashi sakewa da mutane. A shekarun sa na uku da fara aiki a Najeeb constructions sun saba da Anas sosai, tamkar yayansa haka ya ɗauke shi...


Anas na tattara wa su files kiran Najeeb ya shigo wayar sa, dama files ɗin wajen Najeeb zai kai su dan haka ya amsa wayan da sauri dan ya san abokin na sa da gajen haƙuri.

"Mr Man yanzu na ke shirin kawo ma ka files ɗin"

Cikin huci Najeeb ya ce " Anas ka san that stupid boy bai zo ba, and numbar sa ba ta shiga. Find a replacement, ba zan iya da shi ba"

"Calm down Yallaɓai, barin zo office ɗin sai mu yi maganar...

Duk yadda Anas ya so Najeeb ya ƙarawa Joseph lokaci hakan bai yiwu ba, ƙarshe dai cewa yai ya nemo ma sa wani ko wata.

"Gaskiya you need to change abokina, this guy is good, and kai ma tsakani da Allah ka san kwana ukun da ka bashi ya yi ma sa kaɗan"

"I dont bloody care. Zaman shi a chan ba zai dawo da wanda ya mutu ba neither will it profit him in anyway. So why will he risk his job for that"

"It's his mother's burial, kuma kasan al'adun su da namu ba ɗaya bane"


"And so freeking what?. Just ka nemo wani kawai"

Anas ya kalli abokin na sa cike da takaici ya ce " ba kowa ke da mummunan ra'ayi irin taka ba Najeeb, just because ba ka ɗauki mahaifiyar ka a bakin komai ba doesnt mean kowa ma haka ya ke. Joseph yana son mahaifiyar sa, shiya sa ya tsaya yaiwa mahaifiyar sa proper burial kaman yadda al'adar su ta tanada. I hope you understand that"

"Oh please Anas! Not this talk again"


"Ka na so, ba ka so, gaskiya ce dole na faɗa ma ka duk min ɗacin ta kuwa"


"Find another secretary for me Arch Anas Ali Almustafah"

Kallon-kallo su ka yiwa junan su kafin Anas ya fice daga office ɗin.


*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣0️⃣4️⃣




Ranan Tuesday sai ga Joseph ya zo office, ya sani sarai Najeeb zai yi fushi da shi amma bai ɗauka abin zai kai ga kora ba. Infact, irin koran walaƙancin da Najeeb ya ma sa sai da yai dana sanin fara aiki da Najeeb. Tun farkon zuwan sa kamfanin ya samu labarin halin maigidan na sa a wajen sauran ma'aikata, sai dai bai ɗauka abin na sa ya kai yadda ake faɗi ba sai da ya gani muraratan.


Anas dai ba yadda ya iya ne amma ran sa ya sosu da abinda Najeeb yai wa Joseph.

"Sir, he gave me 3 days, only 3days. I left Kano on tuesday morning, i reached my village on wednesday. My mother was buried on saturday and i make sure i squeezed myself and came back to Kano on Monday night. But he wont listen"

Joseph ya faɗi yana goge hawaye. Shi takaicin sa ma bai wuci yadda Najeeb ya nuna halin ko in kula da mutuwar mahaifiyar sa ba.

Anas ya kalle shi ya ce "please dont take it personal, Najeeb doesnt even respect his own mother. I'm sorry about your loss Joseph, i lost my mother when i was only 7yrs so i know how you feel"

Kalaman Anas su suka kwantarwa Joseph hankali har ya ƙarɓi check ɗin da Anas ya bashi sannan ya tafi...


.....................


Ido Yakubu ya zaro lokacin da Anas ya gaya ma sa akwai vacancy na ɓangaren secretary ɗin Najeeb.

Indai kana aiki da Najeeb Constructions to dole ne ka san halin Najeeb balle kuma jiya-jiya Najeeb ya gama koran Joseph wanda harda kira ma sa security su fita da shi, ba dan Anas ya sa baki ba Allah kaɗai ya san halin da Joseph zai shiga.

"Kana tsoron kar a walaƙanta ƙanwarka ko?" Anas ya jefa ma sa tambaya

"Na ma ka alkawari zan yi ƙoƙari na ga ƙanwarka ba ta walaƙanta ba, za tai aiki da Najeeb na lokaci kaɗan ne ana samun wani vacancy ɗin zan chanja ma ta aiki"

Yakubu ya sauke ajiyar zuciya ya ce " Aikin Farida da Sir Najeeb ba mai yiwuwa bane, idan Farida ba ta ƙona shi ba to shi zai murɗe ma ta wuya ya kasheta. Ka san Farida kuwa? Ai Najeeb da Farida su ka haɗu anan kamfanin inaga ƙonewa kawai zai yi dan wuta da wuta ne"


Dariya Anas yai ya ce " har akwai yarinyar da za ta iya karawa da Najeeb? Gaskiya zan so ganin wannan Faridan"

"Hmm, na san halin Sir Najeeb na kuma san 'yar uwata Farida, amma wallahi duk inda Sir Najeeb ya kai da jin kai da miskilanci to Farida ta taka shi. Maganar ta zama Sakatariyar sa ma bai taso ba. Farida Farida Hmm..."

"Wallahi ni kuma da ka yi bayanin nan sai na ga sun dace gara a samu wacce za ta iya taka ma sa birki ko zamu huta da halin san nan"

"Allah akwai matsala idan Farida ta yi aiki da Sir Najeeb, yaƙi za'ayi fa a kamfanin nan"

"Kar ka damu mutumina, ka turo ta kawai na ma ta interview"



...........................


Ɓangaren turaruka ya nufa a Mall ɗin saboda favourite perfume na shi ya kusa ƙarewa. Kamar daga sama ya fara jin muryan ta, kamar ranan da ya fara ji yau ma masifa ta ke yi. Zuciyar sa ce ta raya ma sa ba ita bace amma kunnensa ya ƙaryata hakan, domin kuwa muryar sak da wadda ya ji ranan a restaurant. Yana so ya maida hankalinsa kan abinda ya ke dubawa amma kuma idanuwan sa na ƙwaɗayin gaskata abinda ya ke ji, shin yarinyar ranan ce? ko kuwa wata ce mai irin muryarta.
Kasa daurewa yai sai daya juya ya maida dubansa ga inda ya ke jiyo muryan. Ita ɗince dai, 'yar mitsilar yarinya mai shegen surutun nan. Ya kai duban sa ga wanda ta ke wa masifan ya ga ba saurayin ranan bane wani ne daban, haka kawai ya ji tsanar yarinyar dama ma su irin halinta kam ina za su iya kama kai.

He couldn't believe it, garin kallonta sai ga shi har turaren da ya ɗauka yana shirin faɗuwa daga hannunsa. Yai saurin taro turaren tareda sake murmushi saboda wautar da yai, garin gulma. Abin haushin ma ba wai ya san yarinyar bane amma kuma gashi halayyarta ya dameshi. Ya saurin kauda kan sa lokacin da su ka zo za su wuce shi, tana tafiya tana surutu, kafaɗarta ya ɗan gogi bayansa kaɗan, yai saurin juyowa ya bi bayanta da kallo amma she's too busy talking to even notice what happened.

"Lousy girl" ya faɗi a fili sannan ya ɗau turaren ya bar wajen...


"Ni wallahi da na san ɗan abinda za mu saya kenan da ban biyoka ba Yaya Faruƙ. Duk abinda mu ka ɗauka ka ce yai tsada. Dama ai abu mai kyau shi ake siya da tsada"

"Wallahi mijin ki ya shiga uku Farida, ke fa ki ka ce mu zo nan ba ni ba. In ba dan ke ba mi zai sa na zo siyayya a nan"

"Amma Yaya ai ba ka cemin ba ka da kuɗi ba ko!"

"Allah ya shiryeki dai"

Har su ka bar Mall ɗin ba ta dena complain ba, dama wasu kaya ne Yaya Faruƙ zai siya na bikin ƙannen sa. Ƙarshe dai daga Mall ɗin kasuwa su ka wuce...


......................


Ana zaune ana duba kayan da su Faridan su ka siyo Maijiddah ta shigo tsakar gidan da sallama, dawowarta kenan daga yiwa Hajiya Yelwa kitso. Kai tsaye ɗaki ta nufa bayan ta gaishe su.
"Ke Jiddah zo nan" Farida ta kirata.
Ba mu su ta dawo ta tsugunna gefen Faridan ta ce "gani Anty"

"Kina gani kowa yana duba kaya yana sa albarka ke za ki tsallake ki shige ciki"

"Lah Anty zan cire hijabi ne na wanke hannuna sai na fito"

Zainab ta ce " ba wani, baƙin ciki ta ke ba nata kayan bane"

Farida ta wurga mata wani awarwaro wanda ya doki hancinta maimakon bakinta da Faridan ta yi niyya.

"Zan ci Ubanki agidan nan, sa'arki ce da zaki dinga yaɓa ma ta magana son ran ki. Na ce sa'arki ce!" Ta daka ma ta tsawa.

Anty Hanne wanda ita ce ta biyu a matan Baffa Musa kuma Umman Zainab ta ce " Yo ba gaskiya ta faɗa ba. Anyi auren ƙannenta biyu yanzu za a sake wasu biyun. Ai abin kunya ne ace ko mashinshini ba ta da shi"

"Da kyau, dama Zainab ai daga nono ta sha. To barin gaya mu ku, tafi ƙarfin tayi baƙin ciki da bikin ƙannenta saboda duk cikin su ba wanda yake auren mijinta. Na ta mijin na nan zuwa, za ku ganshi handsome gentleman da shi"

Hajara ta ce " waya ga handsome mijin shortie" gaba ɗaya sai aka sa dariya banda 'yan ɗakin su Maijiddan wanda su ke tausayinta. Maijiddah ta fashe da kuka ta tashi za ta bar wajen Farida ta riƙe hannunta ta ce " ba inda za ki je. Ki tsaya ki kalli kowacce ido cikin ido ki maida mata martani daidai da ita"

"Anty Farida gaskiya su ka faɗa, na yi kwantai"

"Ji mim shirme, inba dan ke da su ɗin duk 'yan ƙauye bane dan kina 20yrs ba ki yi aure ba shine kin yi kwantai. Tukunnama ke za ki aurar da kan ki ne? Ko mijin ya zo kin ce bakya so"

Ta kalli Hajara da ke dariya ta ce " ke kuma fantsararriya, za ai aurenki at 16yrs ba abinda ki ke hangowa sai kwanciyar aure saboda abinda ki ka sani kenan. Gaya min me ki ka iya? Wacce sana'ar ki ka iya? Jakar banza kawai, yanzu haka wankar tsarki mai kyau ba ki iyaba, tun tasowar ki ke daƙiƙiya ce, shiyasa ko jarrabawar WAEC ma ki ka ce ba za ki rubuta ba. Har mijin da za ki aura abin alfahari ne, ina shi ma wani tunkuzan ne kamar ki, ba ilimin Arabi bare boko"

"A hakan dai auren za ta yi, ta fi wasu da maneman ma ba ta da su" Anty Hanne ta faɗi tana hararan Farida

"Wallahi Jiddah ta fi ƙarfin ta auri miji kaman Haladu, mi za tai da irin su Haladu ai shi kam sai jaka irin Hajara. Mijin Jiddah ɗan gayu kuma mai ilimi ne Insha Allah"

Tuni wajen ya kaure da hayaniya, Baaba Sabuwa dama tuni ta shige ɗaki saboda takaici, ita ɗin kanta ba daɗin ganin Maijiddah ta ke agidan ba. Anyi auren ƙanwarta Murja duk da kuwa tsakaninta da Murjan shekara ɗaya ne to yanzu ga Salima ma za ayi na ta amma ita shiru. Tana jin hayaniyar su amma ko leƙowa ba ta yi ba.
Farida kam duk ta inda aka ɓullo kare Maijiddah ta ke ta hanata tafiya kuma ta hanata kuka. Ƙarshe dai sai gajiya su ka yi su ka barta dan indai wajen ɗasa magana ne to Farida ta kere su...

Da dare da za su kwanta Farida ta sa Maijiddah a gaba da masifa.

"Ke sai ana magana ki fara kuka, ba dole su raina ki ba. Ai su na magana ki na magana, wanda ya gaji ya bari. Tukunna ma ke idan za ki fita sai ki dinga saka dogin hijabai kamar matan Malam, a haka kam ai ko mutum zai tsaida ke a hanya ma zai ɗauka ke matar aure ce ya fasa"

" Lah na saba ne ai"

"A wannan zafin, to kul, kisa ɗan dai-dai amma banda dogin nan, idan ba haka ba zan sa almakashi na rage mi ki tsayin su"

"Kai Anty"

"I'm serious"
Maijiddah ta sa dariya...

Washe gari da sassafe Farida ta shirya za ta bi Yakubu wajen aiki saboda interview da ya ce za a ma ta yau. Sai da za ta fito daga ɗaki taga Maijiddah na shiryawa itama da alama fitan za tai,

" 'Yan mata ina zuwa da sassafe haka"

" Hajiya Yelwa ce ta kirani wai dan Allah na zo na yiwa jikokinta kitso yau za su tafi"

"Ba za dai ki gyara ba ko"

"Mi na yi Anty?"

"Jiya mi na gaya mi ki?"

"Kayya Anty"

Farida ta je ta binciko ma ta wani hijabi cikin kayanta wanda bai da tsayi ta miƙa ma ta. "Sa ka wannan"

"Anty da kin barshi, skirt ɗin da na sa fa ya ɗan kama ni"

"Saka!"

Ba mu su ta amsa hijabin ta saka, da ke ita ɗin guntuwa ce ya kusa kai ma ta gwiwa.

Haka su ka jero su ka fito, ɗakin Baaba Sabuwa kawai su ka shiga su ka gaisheta sannan su ka fita...




..............................


A office ɗin su Yakubu ta zauna wanda shi da colleage ɗin sa Engr Mathew su ke sharing. Tun a office ɗin ta dinga sa Mathew dariya da surutunta. Ƙarfe tara da rabi Yakubu ya dawo office ɗin ya ce Farida ta biyoshi. Kai tsaye office ɗin Anas su ka je. Da sallama su ka shiga office ɗin lokacin Anas na duba wasu takardu. Ɗagowar da zai yi ya ga yarinyar ranan, ta ke murmushi ya suɓuce ma sa cikin ransa yana ayyana abubuwa dayawa.

"Bismillah zauna" ya faɗi yana nuna ma ta kujera.

Yakubu ya ce " sir ni zan wuce office"

" Ok Yaks"
Sai da Yakubu ya fita sannan ya kalli Farida ya ce " Aisha Farida Salihu right?"

"No" ta faɗi tana kallon cikin idon sa.

"No kuma, ba sunan ki kenan ba" ya faɗi da mamaki

"To yallaɓai ka ga takarduna ka ga sunan da ke jiki kuma sai ka sake tambaya"

"Hmmm. Well na ga takardun ki kuma ba laifi i'm impressed. Sai dai aikin da za ki yi babban aiki ne kuma aiki ne da sai kin yi haƙuri sosai"

"Rayuwar duniya kanta sai da hakuri, balle aiki a ƙarƙashin wani" ta amsa tana kallon laptop ɗin da ke gaban Anas

"Da alama dai Yaks bai yi ƙarya ba gameda yarinyar nan, tabbas za a sha kallo tsakaninta da Najeeb" abinda Anas ya faɗi a zuciyarsa kenan. A fili kuma ya ce

"Malama Aisha, kasancewa muna buƙatan Secretary da sauri so gobe za ki fara aiki. Kafin nan zamuje ki ga office ɗin ki sannan zan nuna mi ki yadda za ki dinga gudanar da ayyukan ki"

"Abin da sauri-sauri haka?" Ta tambaya

"Ko ba za ki iya ba ne?"

"Kana ganin Ogan ka zai iya korana ne? Dan ance mini abu ƙiris mutum zai yi ya koreshi"

" I see, ashe kinada labarin wanda za ki yi aiki a ƙarƙashinsa. Kin san ba ya ɗaukan raini, Malama Aisha"

Farida ta ɗan yi murmushi ta ce "ni kuma banda mutunci ba, ga rashin haƙuri kamar zawo"

Anas yai murmushi sannan ya miƙe ya ce " welcome to Najeeb constructions miss Aisha Farida"

"Thank you" ta faɗi tareda miƙewa itama...

Ta yi mamakin ganin girman wajen da aka nuna ma ta a matsayin office ɗinta, cikin ranta tana ayyana irin shagalin da za ta yi a wannan waje, ga ƙaramar fridge ga AC, kai aiki cikin jin daɗi haka.

"Ehmm, Ogan ki bai ƙaraso ba tukunna so zuwa gobe idan kin fito za ki ganshi. Ba sai an nuna mi ki shi ba kina ganin sa za ki ganeshi" maganar Anas ya dawo da ita daga tunanin da takeyi.

"Ba matsala Sir Anas"

Anas ya ce " Kira ni da Anas ɗin kawai ai ke ƙanwar mu ce"

"Rufa min asiri, rashin kunyata ba ta kai nan ba. Kai fa sa'an Yaya Faruƙ ɗin mu ne"

"To kirani da Yaya kawai kinga dama ba ni da ƙanwa mace"

"Na gode Ya Anas"...

Ba su shiga office ɗin Najeeb ba haka su ka fito. Ya ƙara ma ta wasu bayanai gameda aikin, sannan ya ba ta takardar shaidar ɗaukanta aiki. Sai da ta biya office ɗin Yakubu sannan ta wuce gida.


Anas kuwa Farida na fita daga office ɗin sa ya ɗau waya ya kira Najeeb. A take ya sanar ma sa an samu sakatariya kuma gobe za ta fara aiki.

"she better be good" abinda Najeeb ya faɗa kenan.

Anas ya ce " ai mutumina sai ka ganta kawai. Wannan karan kai da chanja Secretary sai dai in ita ce ta ajiye aikin"...

Sai da Najeeb ya tsaya har Hajiya Mama ta gama ganin likita sannan ya maida ta gida. Da zai tafi kamar kullum sai da ta tsokale shi

"A dawo lafiya tuzuru"

"Ke fa tsohuwar nan kinada matsala" ya faɗi yana ɗan hararanta

"Matsala ta ɗaya ce, kai aure ka ajiye iyali kamar kowa. Ko sai ka gama tsohewa kafin kai auren"

"Ke zan aura ai, zan ɗau ragowar Alhaji Mustafah"

"Allah ya jiƙan rai, ai shi bai fi rabin shekarunka ba ya ajiyeni a gidan sa"

"Tsohuwa na tafi, kar ki riƙeni da surutu"

"Allah ya bada sa'a tuzuru"

Girgiza kai kawai yai sannan ya fice daga falon. Idan da sabo ya saba da tsokalar kakar ta sa, wanda da ita ya ke sakewa yai walwala kamar mahaifiyar sa. Kulawar da bai nunawa mahaifiyar sa ba a Hajiya Mama ya ke ba wa...




*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣0️⃣5️⃣



Daga Najeeb constructions kai tsaye gida Farida ta wuce, ba ta samu Maijiddah a gida ba dan haka kaya ta chanja su ka wuce kasuwa da ƙanwar Maijiddan, amarya Salima. Da ke ita ɗin tafi Hajara mutunci shiyasa ta su ta ɗan zo ɗaya da Farida, duk da ba

Please Login or Register in order to submit comment