Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shaida ne.
Farida kam cikin zuciyar ta ayyana yadda za ta yi ƙuli-ƙulin Kubra da Naomi ta ke yi...

Kai tsaye sama su ka wuce. Sabreen na ta cewa ta yi a hankali saboda condition ɗin ta.

Su na isa office ɗin kuwa Naomi na fitowa daga office ɗin Najeeb.
Belt ɗin Najeeb da ta sa a jaka ta ciro, ta yi kan Naomi da sauri. Naomi ba ta ankara ba ta ji saukar belt a bayan ta. Dama ta gan su, ta kau da kai ne kawai, saboda yanzu ta gama convincing Najeeb akan ya aureta kuma ya ma ta alƙawarin zai auretan. Tunda za ta zama matar Najeeb mi zai sa ta wani tsaya ba wa Farida girma...

Farida ta sake warɓa ma ta belt ɗin tana masifa "shegiya mai kaman Aladu, ke ce sheɗaniyar da ki ka haɗa ni da miji na ko"

A na huɗu da ta kai ma ta dukan ne Naomi ta riƙe belt ɗin tana huci.

" 'yar iska ramawa za ki yi? Bismillah, rama" ta jawo gashin Naomi ta falla mata mari. Naomi ta challa ƙara tana kiran sweetheart.

"Kan Uban chan, mijina ne sweetheart ɗin ki" ta sake yowa kan ta. Naomi ta shige office ɗin Najeeb da gudu.

"Ayshah take it easy" abinda Sabreen ke ta faɗa kenan.

Farida ta cire gyalenta ta miƙawa Sabreen ta ce " yau yarinyar nan za ta san da wa ta ke ja, sai na chanja ma ta kamannin ta"...


Numfashin ta sai da ya kusa ɗaukewa saboda abin da idon ta ya ci karo da shi. Najeeb ne tsaye gaban Naomi yana goge ma ta hawaye da hankerchief ɗin sa.

"My Champ" kawai ta iya faɗa bakin ta na rawa.

Ya kalleta da idon sa da su ka rikiɗa su ka koma ja....



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣5️⃣3️⃣









"Mi ya sa ki ka dake ta"
Najeeb ya faɗa da ƙarfi.

Mamaki, tsoro, kishi, baƙin ciki su suka haɗu su ka hana Farida Magana.

"Sorry, sorry dear" ya faɗi yana bubbuga bayan Naomi.

Sabreen ma dai mamakin ne ya cikata. Da ƙyar ta iya cewa " Noory what's this?, what's happening here?"

"This should be the last time da za ku taɓa min ita, she's very special to me, duk abinda ya taɓani ya taɓa ta"

Maganar da yai ya sa hawayen da Farida ke tarewa su ka fara zubowa.

"Najeeb akan wannan Kafirar ka ke min walaƙanci tun shekaranjiya? Akan wannan fasiƙar?"

"Please ku bar min office ba na son hayaniya" ya faɗa tareda kwanto da kan Naomi jikin sa.

"Noory what's wrong with you?" Sabreen ta faɗa ganin yadda Najeeb ya bada hankalin sa kwacokam a wajen Naomi.

Zuciyar Farida kaman za ta bulluƙo tsabar yadda ta ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi. A hankali ta tako gaban su tana kallon cikin idon Najeeb.
Naomi ta sake narkewa jikin Najeeb tana kukan munafurci.

"Wallahi yau ka ce kana son Sabreen za ka dawo da ita rayuwar ka. Zan yi kuka, zan ji baƙin ciki, amma daga baya zan rarrashi kai na na amince ma ka. Amma wannan?"
Ta faɗa tana nuna Naomi.

"Ba zan taɓa amincewa ba har abada"


"Fine, dama ba amincewar ki na ke nema ba. Infact we are getting married soon"

Ta buɗe baki za ta yi magana amma sai hawaye. Ta juya da sauri ta fita, Sabreen ta bi bayan ta da gudu...



Ganin halin da ta ke ciki ya sa dole Sabreen ta raka ta gida. Kuka ta ke cikin motar kaman ranta zai fita. Da ƙyar Sabreen ta dinga rarrashin ta saboda abin cikin ta...

Kwanciya Farida ta ce za ta yi hakan ya sa Sabreen ta ma ta sallama tareda cewa za ta gayawa Mom abinda ya faru dan abin ya ɗaure ma ta kai...

Sabreen na tafiya Farida ta shiga haɗa kayan ta.


...........................



"Wato dai ba za ki gaya min mi ya dawo da ke gida ba ko"
Farida ta juyar da kai ta cigaba da hawaye.

"Ki tashi ki koma gidan ki kafin Baban ku ya dawo"

"Ummi kafira ce fa, wai kafira zai aura. Akan ta ba irin walaƙancin da bai min ba. Ni na haƙura, ya je ya auretan zai gani ai"

"Najeeb ɗin?"

"Ummi cikin ido na fa ya kalla ya ke faɗa min wai zai aureta. Ko na amince ko ban amince ba babu ruwan sa aurenta zai yi" ta fashe da kuka.

Ummi ba ta yi ƙoƙarin hanata kukan ba sai ma nazarin maganganun Faridan da ta fara yi wanda ta ke ganin ba lafiya ba. A yadda ta karanci Najeeb yana tsananin son Farida ba zai taɓa ma ta walaƙanci haka kawai ba musamman yadda ta ke da cikin nan.

Rarrashin Faridan ta shiga yi saboda cikin jikin ta...


Sabreen na zuwa ta sanar da Mom abinda ya faru. Mom ta ka sa gaskata hakan, ta ɗau waya ta shiga kiran Najeeb amma bai ɗauka ba. Mom ta ce ba ta ga ta zama ba dole su je har kamfanin ta ji bahasin wannan sabon salo na shi...

Da su ka je ba su same shi ba. Shi da Naomi sun fita. Mom ta je office ɗin Anas shima baya nan ya fita. Haka su ka dawo gida tana jira Daddy ya dawo ta sanar da shi komai...

Farida kashe wayarta ta yi lokacin da ta ga Anas ya dameta da kira. Bayan ta yi sallar Azahar ta samu ta kwanta saboda baccin da ba ta samu ta yi jiya ba.

Anas kuwa ya ga lokacin da Najeeb da Naomi su ka fita. Yana kiran Najeeb amma ya ƙi kula shi. Farida ya shiga kira amma ba ta ɗauka ba, ƙarshe ma aka kashe wayar. Hakan ya sa ya je ya shiga mota ya wuce gidan su. Da ya isa gidan Tasallah ke gaya ma sa Farida ta tafi gidan su kuma yanayin kayan da ta ɗauka kaman yaji ta yi.
Hankalin Anas ya kuma tashi yana tunanin mi ke faruwa tsakanin wannan masoya.
Gidan su Farida ya wuce direct. Da ya isa ya aika yaro akan ya kira ma sa Farida inji Anas. Yaron da ya shiga ya samu Ummi ya gaya ma ta. Ummi ta aiki Zainab ƙanwar Maijiddah akan ta cewa Anas Farida ba ta jima da bacci ba. Za ta kirashi idan ta tashi.

Anas dai ya tafi ne amma ya so ya ga Farida ya tambayi mi ke faruwa. Yana hanya saƙon Mom ya shigo akan idan ya tashi a waken aiki ya zo gida...



........................


Bayan la'asar ta farka. Kuma Alhamdulillah zuciyarta yai sanyi.

Sai da Ummi ta tabbatar ta ci abinci sosai sannan ta shiga ma ta nasiha tareda faɗa ma ta illar baro gidan ta da ta yi.

"Ummi to na koma na ma sa mine? Bayan ya samu 'yar ma su fitsari a tsaye yace yana so"

"Farida kenan, har yanzu da sauran ki. Wa ya gaya miki zaman aure zaman jin daɗi ne na dindindin. Ki koma gidan ki ki cigaba da yiwa mijin ki addu'a har Allah ya warware mu ku matsalar da ku ke ciki. Ni ina tunanin ba haka yarinyar nan ta bar shi ba. Amma addu'a ya fi ƙarfin ko wani sharri dan haka shi za ki riƙe"

Maganganun Ummi ya sa jikin Farida yai sanyi. Sai yanzu ne zuciyar ta ya fara wannan tunanin. Ƙila Naomi ta yiwa Najeeb wani abu ne...

Cikin ruwan zamzam da su ka zo da shi daga saudiyya Ummi ta ɗauko ta kawo ma ta. Sai a lokacin Faridan ma ta tuna su ma na su da su ka zo da shi bai ƙare ba. Ta amsa tana yiwa Ummi godiya.

"Kar ki saka damuwa a ranki dan Allah, ki riƙa tashi da dare kina yiwa mijin ki addu'a, sannan wannan ruwan zamzam ɗin ki dinga haɗa ma sa a ruwan shan sa, abinci dama shayin da zai sha. Ki riƙa tofe makwancin sa da kuma inda ya saba zama da Suratul Falaƙi da Naasi saboda suna maganin asiri da sheɗanu"...

Ƙarfe bakwai saura ta isa gida. Kunna wayarta da ta yi ta ci karo da saƙonni. Biyu daga Anas sai ɗaya daga Mom sai ɗaya daga Lukman inda ya ke ma ta godiya domin Sabreen ta amince da shi. Na ƙarshen ne ta ga Abdullahi dreba inda ya ke cewa "Hajiya dan Allah akwai maganar da na ke son gaya mi ki gameda Oga".

Ta turawa Lukman saƙon taya murna kafin ta kira Abdullahi. Da ke yana tareda Najeeb a mota sai bai ɗauka ba. Da aka sake kira sai ya ɗauka ya ce " ina tuƙi Hajiya, mun ma kusa isowa gida"

Farida ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ta kashe kiran.
Numbar Mom ta kira dan saƙon na ta cewa ta yi ta kira ta dan Allah.

"Ayshah ki na lafiya?"

"Lafiya Mom" ta amsa tana ƙoƙarin saita maganarta.

"Anas ya ce min kin koma gidan ku, dan Allah 'ya ta ki dawo, zan zo gidan na ku gobe"

"Mom na dawo ma, yanzu haka ina gidan"

"Allah ya miki albarka"
Farida ta amsa da amin...


Bai fi minti shabiyar ba sai ga Najeeb ya shigo gidan. Tana zaune a falo tana kallo ya shigo, a zahiri za ka ga kaman kallon ta ke amma ba kallon ta ke ba, hannunta akwai carbi tana jan Ya Hayyu Ya Qayyum.

Ba ta ma sa magana ba haka ya hau sama da gudu kaman zai tashi sama.
Tana ganin ya shiga ta kira Abdullahi akan ya shigo...

Duk yadda ta yi ya zauna a kan kujera ya ƙi. A ƙasa ya zauna su ka gaisa.

"Malam Abdullahi ina fata lafiya?"

" Hajiya dan Allah ki yi haƙuri da abinda zan gaya mi ki"

Farida ta ce ba komai.
Nan ya shiga gaya ma ta abinda ya lura tsakanin Najeeb da Naomi. Ya faɗa ma ta jiya da ya kai su hotel ne Najeeb ya fara ciwo amma da lafiyar sa ƙalau. Ya ƙara da cewa " Hajiya kar ki tsorata amma akwai asiri ajikin Alhaji. Wannan cegiyar arniyar ta yiwa Alhaji asiri"

Duk da gaban ta ya faɗi amma hakan bai sa ta ji tsoro ba, dan tunda Ummi ta ba ta shawarwari ta sa a ranta sai inda ƙarfinta ya ƙare akan yiwa Najeeb addu'a.

Ta yiwa Abdullahi godiya ta sallameshi...

Sai da ta leƙa ɗakin sa ta ga yana bacci kafin ta wuce na ta ɗakin. Ɗazu ta tsiyayi ruwan zamzam a hannunta ta tofa ƙula'uzai a ciki sannan ta yayyafa a gadon sa da duk kujerun sa...

Ƙarfe biyu da rabi ta tashi ta fara gabatar da sallah tana addu'a ba ta kwanta ba har asuba. Ƙarfe shida ta fito ta taya Tasallah haɗa ma sa breakfast duk da ma Tasallah ta ce tea kawai ya ke sha yanzu. Acikin tea ɗin ta tsiyaya ma sa ruwan zamzam kaɗan wanda shima ta tofeshi da addu'o'i...

Da za ta haura sama ta ce da Tasallah ta kai kuɗi gidan da ake musu kunu da ƙosan sadaka lokacin da Najeeb bai da lafiya su ma ta sadaka.
Ita kan ta Tasallah ta san akwai matsala a gidan dan masoyan da kullum su na manne da juna sai ga shi yanzu ko kallon kirki ba sa yiwa junan su.

Saboda bacci da ke idon tana shiga ɗaki bacci ta yi. Ba ta farka ba sai ƙarfe tara. Ta yi wanka ta shirya ta sauko. Kaman yadda Tasallah ta ce tea ɗin kawai ya sha ya fita.
Ta zauna a dining ta ci abinci sosai, ba wai dan daɗi ba sai dan ɗan da ke cikin ta.

Ƙarfe shaɗaya ta wuce gidan su Najeeb. Mom ta riƙa ba ta haƙuri tareda da nuna ma ta Najeeb yana cikin matsala dan jiya sa'insa su ka yi da Daddy akan ya ce zai auri Naomi.

Cikin kuka ta ce " he has never raised his voice to his father, amma jiya..." kuka ya kufce ma ta.

"Mom dan Allah ki dena kuka, addu'a za mu dinga ma sa har Allah ya kawo ma na ƙarshen wannan bala'i"...

Ta jima a gidan dan sai bayan Azahar ta tafi.
Anguwar su ta wuce amma ba ta kai gida ba ta tsaya a gidan su Saminu.
Saminu abokin Yakubu ne, amma tun secondary school ya lalace da shaye-shaye. Yanzu haka ba shi da aikin yi sai maula gidan 'yan siyasa, idan lokacin zaɓe ya zo sune 'yan bangan siyasa.
Duk da halin su da ya banbanta amma ba su dena mutunci da Yakubu ba. Lokaci zuwa lokaci yana zuwa wajen Yakubu ko kuma su haɗu a majalisa.

Da ta je gidan dai cewa aka yi Saminun baya nan amma an bata numbar shi.

Tana fitowa daga gidan ta kira numbar ringing ɗaya kuwa aka ɗauka.

"Kai ɗan dambulan 'wa ina ka shiga, na je shagon ka ban sameka ba" abinda Saminu ya fara faɗi kenan.

"Haba Saminu a bi a hankali mana"

Jin muryan mace ya sa Saminu ya fara washe baki yana faɗin sorry Hajiya.

"Suna na Farida ƙanwar Yakubu ɗan gidan Alhaji Musa Wase"

"Kai kai ashe Hajiya Farida ce. Ki gafarceni dan Allah na ɗauka wani banzan yaro ne"

Farida ta ce ba komai

"Ina son ka min wani aiki ne ka ɗan samu wani abokin ka sai ku zo. Za ku samu 'yan chanji na siyan kati"

Saminu ya sa ihu yana faɗin koma minene za su yi...


Farida ta yi murmushi ta ce "Naomi miji na ki ke so ko?. Fine, za ki same shi da kyau"...

...............................


Tana zaune tana duba kayyayakin da su ka siyo ɗazu ta ji wayarta na ringing. Da sauri ta ɗauka dan tunanin ta Najeeb ne ganin sunan Madam Farida ya sa ta yi tsaki. Ko me ta ke nema a wajena oho.
Kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka.

"Naomi Naomi, Naomi Masoyi. Naomi matar Najeeb ko?. Fatan kina lafiya? Ina son ganin ki ya za ayi ne?"

Naomi ta ja tsaki ta ce " ba za ki ganni ba. Na san plan ɗin ki bai wuce ki dake ni ba"

Farida ta yi dariya ta ce "Allah ko? To barin zo sai mu ga ko dukan na ki da gaske zan yi"...

Naomi ta kashe wayan tana tsaki. Baifi minti goma ba sai ga shi Mrs Comfort na kiran ta akan ta zo ta buɗe ƙofa ana ƙwanƙwasa ƙofa.
"Mama ina Abel, ya je ya buɗe mu su"

Mrs Comfort ta ɗaga murya tana faɗin " wai ba za ki fito ba. Abel baya nan fa"

Naomi ta yi tsaki sannan ta fito.

Mrs Comfort na zaune a kan keken guragu tana karanta bible Naomi ta zo ta buɗe ƙofa. Naomi ta zaro ido lokacin da ta ga Farida tsaye, bayanta kuma wassu samari biyu ne wanda da ka gan su ka san a buge su ke.
Ta ja da baya da sauri tana faɗin Mama.

Suna shigowa Farida ta ce "Saminu rufe min ƙofa dan Allah"

Naomi gefen Mrs Comfort ta tsaya jikin ta na rawa.

Farida ta kalli Falon na su da kyau sannan ta ce " Mrs Comfort ban san ko da sa hannun ki Naomi ta asirce min miji ba, har ta ke son auren shi"

Mrs Comfort ta zaro ido, Ita da ta tsani musulmai shi ne za ta bari 'yarta ta yi tarayya da musulmi. Ta dai lura da yawan kayyakin da Naomin ke zuwa da su kwana biyun nan, kuma ta yiwa Naomin magana amma ta ce saurayin ta ne ke siya ma ta.


"Ni ban san komai ba. Naomi wai mijinta ki ke so?"


"Madam Farida ki fita a gidan mu ko na kira police"

Farida ta kwashe da dariya ta ce " ina da numban comissioner of police zan baki sai ki gaya mi shi ƙorafin ki amma kafin nan..."

Ta kalli Saminu ta ma sa ishara da ido. Shi da ɗayan da su ka zo da ake cewa Maska su ka yi kan Naomi. Naomi ta yi hanyar ɗaki tana ihu amma ko takun kirki ba ta yi ba, Maska ya cafko ta.

Kujeran da ke wajen ɗan ƙaramin dining ɗin su Saminu ya ɗauko. Aka zaunar da Naomi ana ɗaureta bayan sun fara rufe bakin ta saboda kuka da ihu da ta ke yi.

"Tsirara za ku ma ta" Farida ta faɗa da ƙarfi.

Maska ya yaga vest ɗin da ke jikinta, mini skirt ɗin ma ya yage ta ya saura daga ita sai pant.

"Shi ma ku cire" Farida ta faɗa ba alamar wasa a fiskarta.

"Plz Madam Farida, i beg you. Naomi za ta bar mi ki mijin ki, plz dont kill her" Mrs Comfort ta faɗa tana kuka.

"Ni ba kisa zan yi ba, zan dai ɗanɗana ma ta kaɗan daga azabar da za ta ji duk ranan da ta sake neman mijina ne"

Ta kalli Saminu ta ce "bar ma ta pant ɗin, zai ma sa cirnakun su ci gindinta sosai"

Handglove ta cire ta miƙawa Saminu. Saminu ya ce " Hajiya barshi zan sa hannu kawai"

"A'a ka dai saka ɗin"

Ya karɓa handglove ɗin yana sawa. Daya gama Maska ya fito da wata leda wanda kwalbar Bama mayonnaise ne aciki cike da cirnaku baƙaƙe da jajaye.

Saminu ya ɗebo cirnakun nan ya sa hannu cikin pant ɗin ta ya zuba su. Har da cuccusawa cikin abun ta.
Da ya gama ya zuba sauran a cinyayyen gashinta, dama ta riga ta cire wig ɗin da ke kan ta. Sauran ya sa a bayanta....



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣5️⃣4️⃣





Naomi sai zazzare ido ta ke yi tana kici-kici akan kujera, idonta yai ja ga gumi da ke ta tsatstsafowa a jikinta. An ɗaure hannu da ƙafa ga bakin ma an kulle ba halin kuka.

Mrs Comfort ta turo kekenta zuwa wajen Farida da ke tsaye tana kallon Naomi.

"Plz Madam Farida, i beg you in the name of the Almighty God stop this. Naomi za ta bar mijin ki i promised you that"

Jin yadda Mrs Comfort ke roƙo tana hawaye ya sa ta ɗan ji tausayin ta.

Ta ciro Shentos insecticide a jaka ta miƙawa Saminu.
"Fesa ma ta su mutu, tunda uwarta ta roƙi alfarma"

Saminu ya ƙarɓa ya fara fesa wa Naomi a kanta da bayanta. Yana shirin feshe wajen abun ta, Farida ta ce "tsaya-tsaya Saminu. Cire ma ta pant ɗin za su faɗo"

"Hajiya ki bari na fesa a wajen za su fi mutuwa da wuri"

Farida ta girgiza kai. Saminu ya cirewa Naomi pant ɗin wanda ke cike da cirnaku wasu sun mutu wasu kuma suna ta mutsu-mutsu a jiki. Cikin minti ɗaya kusan duk cirnakun sun mutu saboda ƙarfin maganin. Wanda su ka tsira ma to sun nakasa sosai.

Farida ta kalli Mrs Comfort ta ce "ki jawa 'yar ki kunne, duk abinda ta yiwa mijina ta warware idan ba haka ba. Nan gaba ba'a cirnaku kaɗai zan tsaya ba, sai ta ƙwammace ba ta zo duniya ba"

Ta cilla ma ta wani tube na magani ta ce " idan ta wanke jikinta da kyau ta shafa wannan. Zai taimaka wajen rage raɗaɗi"
Ta kalli su Saminu ta ce su kunce ta. Ana kunce bakin Naomi ta ɓarke da kuka, ihu ta ke kamar wadda aka aikota saboda azaba. Ana gama kunceta ta fita da gudu sai banɗaki, tana zuwa taga ba ruwa a ciki ta fito ta wuce kitchen da gudu tana sosa gabanta da bayanta zuwa kanta duk lokaci guda. Suna ji ta buɗe randan ruwa ta fara kwararawa kan ta tana yi tana kuka...

Farida ta kalli Mrs Comfort ta ce "ki jawa 'yar ki kunne ko kuma jikinta ya gaya ma ta" daga haka su ka fice a gidan.

Gaba ɗaya ruwan randar ta ƙarar a jikinta still ba ta ji sauƙin komai ba. Sai ihu ta ke yi, Mrs comfort ta ɗau waya ta kira Abel ƙanin Naomi akan maza-maza ya zo gida.
Naomi ta zama tamkar mahaukaciya a cikin gidan, ta shiga nan ta fita chan, ta kasa zama ta kasa kwanciya sai kuka da soshe-soshe...


Ƙarfe shida na yamma Naomi na kwance tsiraran ta tana hawaye tana nishi sama-sama, gefenta ƙawarta Maureen ne ke ma ta fifita a gabanta. Maganin da Farida ta bayar aka shafa ma ta, ya ɗan taimaka wajen samun sauƙin raɗaɗin da ta ke ji. Ilahirin jikinta duk ya cika da tabon cizo.

"Na God go Punish that woman" Maureen ta faɗa tana tsaki

Mrs Comfort da ke gefe tana ganin 'yartata ta ce "ba laifin Madam Farida ba ne. Laifin Naomi ne, mi ya kaita soyayya da musulmi hakan ma married man"

"Mama ki dena faɗin haka. Ko ma mi Naomi ta yi ba ta chanchanci wannan punishment ɗin ba. This is pure cruelty"

Mrs Comfort ta girgiza kai tana tunanin idan Naomi ba ta ji sauƙi ba za su wuce asibiti kawai...


.............................

Hankali kwance Farida ta koma gida, zuciyarta saƙayau, ko ba komai Naomi za ta yi jinyar kwana biyu.
Ƙarfe shida saura sai ga Anas da Najdah sun zo ma ta.
Anas dai haƙuri ya ba ta kan wannan magana tareda nuna ma ta suna tareda ita ɗari bisa ɗari.
"Akwai wani Malami da na yiwa magana ya ce zai tayamu da addu'a. Insha Allah za mu ga ƙarshen wannan al'amari"

Farida ta ce " Ya Anas na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"

Najdah ta cire girman kai ta ce " Anty Farida, Big B yana son ki sosai, ba zai taɓa walaƙanta ki cikin hankalin sa ba, Please kar ki yi fushi da shi"

" Na gode Najdah, ku dai cigaba da tayamu da addu'a"

Najdah ta ce Insha Allah.


Sun ɗan jima kafin su ka tafi. Su na ma tunanin Najeeb zai dawo ya same su amma har su ka tafi bai dawo ba...

A ɓangaren Najeeb kuwa zuciyarsa tafarfasa ya ke lokacin da ya isa gidan su Naomi ya isketa kwance. Maureen ce ta kira shi ta sanar da shi komai.

Lokacin da Mrs Comfort ta ga Najeeb ya shigo gidan su hankalin sa a tashe ta fara tunanin kaman maganar Farida gaskiya ne. Idan ba haka ba Sir Najeeb ɗin da ta sani ɗan ƙwalisa mai ji da kan sa ba zai taɓa kallon Naomi ba balle ya damu da ita ko kuma ya so ta.

Tana gani ya ɗauki Naomi a hannun sa su ka fita tareda Maureen. Tana faɗin su tsaya amma ba wanda ya kulata cikin su...



Da su ka je asibiti gado aka ce ta kwanta sannan Likita ya duba ta daga sama har ƙasa. Da ya gama examining na ta ya nemi bahasin abinda ya faru har cirnaku su ka cize ta haka musamman a ta wajen abun ta. Maureen ta fara koro bayani akan ai wata Ogar Naomin ce ta sa ma ta cirnaku a jiki.

"Saboda me? Wannan ya kamata akai case ɗin nan gaban 'yan sanda" Likitan ya faɗa cikin faɗa.
Maureen ta ce yanzu ma daga asibitin police station za su wuce.

Magani ya rubuta mu su na sha da na shafawa sannan aka sallamesu bayan ya rubuta mu su report da za su kai police station.

Daga asibiti Najeeb ya ce Abdullahi ya kai su police station. Abdullahi dai mamaki ya cika shi dan bai gane wannan al'amari ba daga asibiti sai police station. Ya dai cika umurni ya wuce da su...

Ganin report ɗin da su ka kawo da kuma testimony da Naomi da Maureen su ka bayar ya sa aka haɗa su da police biyu dan su je su arresting wannan muguwar mata da aka kira da Madam Farida.
Cikin su Naomi ba wanda ya ambata cewa Madam Farida matar Najeeb ne. Shi kuma Najeeb yana zaune kaman wawa duk abinda Naomi ta faɗa to daidai ne...

Motar su na gaba motar police na baya har su ka isa gida. Abdullahi dai bai san mi ya ke faruwa ba.

Maureen sai kumfar baki ta ke tana faɗin "today she go know say our madness pass her own"
Naomi kam maƙalewa ta yi jikin Najeeb wanda ke ta ce ma ta sorry...


Bayan tafiyar su Anas, wanka Farida ta yi ta gabatar da sallar Isha. Tana ma kan sallayar tana addu'a Tasallah ta shigo ɗakin da gudu tana haki.

"Baaba Tasallah lafiya?" Farida ta faɗa ganin yadda ta tsorata.

"Folisawa a falo, Folisawa suna neman ki Hajiya"

"Police kuma"

Tasallah ta gyaɗa kai.

"To ki je ina zuwa"

Tasallah ta fita, still tana tsoro dan ganin Najeeb ne ya zo da su ya sa ta ƙara tsorata da lamarin.

Farida ta cire hijabin sallar ta ta je ta ɗauko ƙarami ta saka dama gown ɗin material ne a jikin ta.

Najeeb da su Naomi na zaune a falon su kuma police ɗin su na tsaye.
Ganin Naomi ya sa ta gane dalilin zuwan police.

"Suna na Sergeant Iliya. Mu na tambaya ko ke ce Madam Farida Salihu?"

Farida ta kalli Najeeb wanda ko wajen da ta ke tsaye bai kalla ba sannan ta kalli sergeant ɗin ta ce

Please Login or Register in order to submit comment