Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi baƙo. Tun tafiyar ka su ke tare"

Najeeb bai kawo komai a ransa ba ya buɗe office ya shiga. Ta glass ɗin da ya raba office ɗin sa dana Farida ya hango Farida da Lukman su na zaune. Zahiri ba wai su na wani abu ba ne. Magana ce su ke yi amma fiskan Farida ɗauke da murmushi.
Sheɗan ne ya tunzura shi a wannan lokaci. Har zai buɗe office ɗin ya shiga sai kuma ya juya ya fita, Kan sa ke wani irin ciwo. Idon sa ya yi ja zir.
Yana fitowa ransa a ɓace zai tafi Naomi ta kira shi.

"Sir"

Ya juyo a fusace ya kalleta. Naomi ta fara ƙyafƙyafta ido, ta taso ta zo gaban shi har lokacin bai iya janye idon sa daga na ta ba. "dear ka yi haƙuri. Ka kwantar da hankalin ka, ina tareda kai"...


*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣5️⃣1️⃣






Naomi ta sa hannu ta fara shafa ƙirjin Najeeb. Bai motsa ba bai kuma hana ta ba. Ganin bai yi masifa ba yasa wanni daɗi ya ziyarci zuciyar Naomi. Ta kwantar da kai jikinsa tana cigaba da shafa shi. Najeeb dai yana tsaye kaman gunki bai iya aiwatar da komai ba.

"Sweetheart ka yi haƙuri ka ji"
Najeeb ya tsinci kan sa da gyaɗa ma ta kai...


Farida ta ji farin ciki sosai da amincewar Lukman. Tanada yaƙinin Sabreen za ta amince da shi musamman idan Najeeb ne ya ma ta maganar.

"Barin kira mijina yanzu na san ya kusa dawowa"
Ta ɗau waya ta fara kiran numban Najeeb. Sau uku tana kira sau uku wayan na tsinkewa ba tareda an ɗauka ba.
Duk da gabanta ya faɗi da hakan amma ba ta nuna ba.

Ta yi murmushi ta ce "ƙila wayar ba ta kusa da shi ne, bari mu ɗan hira shi"

Lukman ya miƙe tsaye ya ce "Aishah zan wuce, kawai duk yadda ku ka yi da shi sai ki sanar da ni"

"Insha Allahu wannan karan za a dace"

A zuciyar sa ya amsa da amin amma a fili murmushi kawai yai.

Har ga Allah tausayin shi ta ke ji. Lukman ya haɗu ta ko'ina musamman ma da ya kasance mutum ne da ya ke da tarin ilimi a ɓangaren addini, hakanan yana da kyawawan halaye...

Ta cigaba da kiran Najeeb amma shiru. Hakan ya sa ta kira Abdullahi. Bugu ɗaya ya ɗauka. Ta tambayeshi ko har yanzu Najeeb bai gama abunda ya ke bane. Abdullahi ya ce yanzu ma muna hanyar gida ne.
"Gida kuma?" Farida ta faɗa cikin rashin fahimta.
"Hajiya ai daga kamfanin ne ya ce mu wuce gida" ya amsa ba tareda ya fahimci mi ke faruwa ba.
Farida ta kashe kiran ta cigaba da kiran Najeeb amma still bai ɗauka ba.

Jakarta ta ɗauka ta fito.
"Ma, za ki fita ne?" Naomi ta faɗa tana murmushi.
Farida ba ta kulata ba ta cigaba da tafiya, har ta kai ƙofa sai kuma ta juyo ta ce "Naomi miji na ya zo ne?"

Naomi ta yi saurin cewa "No ma"
Farida ta fita cike da tunani a ranta...

............................

Tunda ya fito daga cikin Kamfanin ya ke jin shi kaman marar lafiya. Yana ganin kiran Farida amma ya ka sa ɗauka. Daga an kira wayan idan ya duba ya ga My Queen sai ya maida ta ya ajiye.
Ko wanka bai yi ba da ya shiga ɗaki ya kwanta a kan gado. Jin jikinsa ya ke kamar ba shi ba, kamar akwai abinda aka cire ma sa a jiki.
Yana kwance a haka har Farida ta shigo. Ganin sa kwance da kayan office a jiki ya sa ta san ba lafiya ba. Duƙawa ta yi ta cire ma sa takalman sa kafin ta ƙarasa dai-dai kan sa tana faɗin " miji na lafiya? Are you Ok?"
Bai ce komai ba sai ma juya ma ta baya da yai.
Tunanin ta ko ciwon kan sa ne ya tashi. Dan tunda aka sallameshi daga asibiti yake fama da ciwon kai amma ya fi tashi ma sa idan ran sa ya ɓaci ko kuma he's stressed. Likita ya ce a hankali ciwon kan zai tafi gaba ɗaya, amma kuma ya dinga samun isashshen bacci, sannan duk lokacin da ya jima yana aiki to ya tabbatar ya ware lokacin da zai kwanta dan ya huta. Hakanan ya guji duk wani abu da zai ɓata ma sa rai.


"My Champ dan Allah mi ya sameka? Wa ya ɓata maka rai?"

" ba na son surutu" ya faɗa a hankali

"Shikenan tunda ba za ka gayamin miya faru ba, amma dan Allah ka tashi ka rage kayan jikin ka za ka fi jin daɗin baccin"

Mirginawa yai ɗaya ɓangaren ba tareda ya amsa ma ta ba.
Ganin dai ba tashi zai yi ba ya sa ta tashi ta fita tunanin ta idan ya huce zai gaya ma ta koma minene.

Ɗakin ta ta wuce ta je ta yi wanka ta chanja kaya. Sai da ta kira Ummi su ka gaisa kafin ta wuce kitchen dan ta taya Tasallah aiki...

Su na jera abinci a dining ya fito ya sha wanka. Baƙin riga da wando ya sa sai ya ɗaura farin blazer a kai.

"My Champ fita za ka yi ne?"

"My Champ...My Champ" ta cigaba da kira har lokacin da ƙofar ta rufu. Baki tasake tana bin ƙofar da kallo. Ya kalleta sun ma haɗa ido kuma ya ji maganar da ta yi amma ya shareta.
Mi ke faruwa, abinda ta tambayi kan ta kenan.

Tun tana jiran shi nan da awa biyu har ta koma cewa nan da ƙarfe takwas na dare zai dawo amma shiru. Ta kira duka nambobinshi amma a kashe.

Tana kwance a kan kujera da ke falon ta ji takun sa. Ta yi firgigit ta tashi dan dama ba wai ta jima da bacci ba ne, baccin ma rabi da rabi ta yi.

"My Champ, My Champ" da sauri ya dinga taka stairs ɗin har ya ƙule ma ta.
Agogon falon ta duba ta ga ƙarfe goma har da rabi. Tunda su ka dawo gidan su bai taɓa wuce ƙarfe tara a waje ba...
Tashi ta yi ta bishi dan ba ta ga ta zama ba. Yana banɗaki lokacin da ta shigo. Itama banɗakin ta je za ta shiga dan ta taya shi wanka ko za su shirya daga nan amma ta ji banɗakin a rufe. Mamaki ya kamata dan indai wanin su ya shiga banɗaki yo baya rufewa tunda su biyu ne a gidan Tasallah ɗakinta na ƙasa.

Ta zauna a bakin gado tana jiran fitowar sa. Tana zaune ya fito, ya shirya yai ɗan shafe-shafe da feshe-feshen sa ya zo ya kwanta.
Mamakin yadda yai kamar babu mutum a ɗakin ya sa Farida ka sa magana. Ganin ya ja bargo ya kwanta ya sa ta lalubo sauran maganan da ke bakin ta ta ce "My Champion dan Allah ka yi haƙuri, idan ma wani laifin na maka ka yi haƙuri ka yafemin. Dan Allah miji na ka min magana. Ka gaya min laifina" tana maganan ne kaman za ta yi kuka

"Idan ba za ki iya kwantawa shiru ba, to ki koma ɗakin ki"

Kan ta ya ɗaure. Najeeb ba zai taɓa gaya ma ta haka ba, ko lokacin da ba sa shiri ma duk shirmen ta ba ya cewa ta bar ɗakin.

"Miji na dan Allah, hankalina ba zai kwanta ba idan ban san laifin da na yi ma ka ba"

tsaki yai ya tashi ya ɗau pillow ya koma kan kujera ya kwanta.

Haushi ya cikata. Idan ma laifin ta mishi bai ci ya ma ta wannan walaƙancin ba. Ta ja tsaki itama ta kwanta, a zahiri ranta na raya mata kar ta kuma bashi haƙuri zai zo da kan sa ya bata amma kuma chan cikin ranta tana tsoron wannan chanji bagtatan da Najeeb yai ma ta. Ta dinga tariyo abubuwan da su ka faru ko za ta tuna wani furuci ko wani abu da ta ma sa da zai iya ɓata ma ta rai amma ba ta gano komai ba. They are just fine, tun jiya har safiyan yau, infact san da zai fita a office ma sai da ya kissing ɗin ta sannan ya kissing cikin ta amma komai ya wargaje ne tun daga tafiyan sa. To ko a inda ya je ne aka ɓata ma sa rai? To ai koma wani ya ɓata ma sa rai bai kamata ya sauke fushin a kanta ba musamman saboda condition ɗin da ta ke ciki.
Da ire-iren waɗannan tunani ne bacci ya sace Farida.

Da asuba ma gum ya ma ta ba magana. Bayan ya dawo daga masallaci ta gaishe shi amma bai amsa ba. Haka kawai jikinta yai laushi ta fashe ma sa da kuka. To her uttermost shock maimakon ya rikice ya fara ba ta haƙuri sai ya shige banɗaki ya barta zaune tana kuka.

Innalillahi kawai ta ke ta maimaitawa a fili.
Najeeb ne zai ga tana kuka ya share, yai kaman bai ganta ba, gaskiya da matsala.

Ta zauna har ya fito ya fara shirin fita office still ignoring her. Tsoro da fargaba su ka cika ma ta zuciya.
Ba ta san ma ya za ta fassara wannan yanayi ba. Wannan yanayi mai kama da mafarki ko almara.
Wai Najeeb ɗin ta ke ma ta wannan walaƙancin. Yadda ta ke zaune tana kallon sa haka ya ƙarisa shiryawa ya fita daga ɗakin. Tunda su ka shirya ya dena fita da sassafiya haka, tunda tare su ke fita office ɗin, amma sai ga shi bayan ma yai fitar sassafiya bai ma damu ya san ko wani hali ta ke ciki ba balle ya ji ko za ta fita office ko ba za ta je ba.

Farida ta jima zaune a kan sallaya ta rasa ma abinyi Allah kawai ta ke kira a ranta. Dan wannan sauyi ya fi ƙarfinta, nan gaba kaɗan za ta iya shiga wani hali...


Shi kuwa Najeeb yana shiga mota ya ce Abdullahi ya kai shi gidan su Naomi. Tun jiya Abdullahi ya shiga ruɗu, ya kai Najeeb kamfani inda ya ɗau Naomi su ka fita, wani haɗaɗɗen restaurant su ka je daga nan ya kai su wata babbar shopping Mall inda su ka fito da kaya niƙi-niƙi. Gidan su Naomin ya kai su ta shiga ta ajiye kaya sannan ta sake shiryawa cikin wassu matsatstsun kaya ta fito.
Sunan hotel ɗin da Naomin ta faɗa ne ya sa shi sake maimaita sunan da ɗan ƙarfi alamun mamaki.
Najeeb ya ce ya kai su inda ta ce. Lokacin kusan shida na yamma ta wuce, har ma wassu wajen ana kiraye-kirayen sallan magriba. Sun kusa isa hotel ɗin Daddy ya kira Najeeb akan ya zo yanzu-yanzu.
Najeeb ya cire kuɗi ya bawa Naomi akan ta je ta jirashi. Idan ya dawo daga wajen Daddy zai zo.
Bai bar wajen Daddy ba sai ƙarfe tara na dare. Har sun kama hanyar hotel ɗin Naomi ta kirashi akan ta koma gida an kirata mamanta ba lafiya. Wannan ya sa su ka dawo gida...

Naomi ta shiga mota tana zuba murmushi. Cikin kayan da su ka siyo jiya ta sa wani shegen gown ɗan guntu da shi. Har gashin wig da ke kamta ta chanja shi. Ta kamo hannun Najeeb tana kaiwa kan nonuwanta tana shashshafa su. Najeeb bai hana ta ba bai kuma yi yunƙurin yin wani abu ba. Kallon ta ya ke yi zuciyar sa na raya ma sa abubuwa dayawa. Naomi ta kai baki za ta kissing Najeeb Abdullahi ya ce " Alhaji yau Hajiya ba za ta aiki ba ne?"

Naomi ta koma baya tana hararan ƙeyar Abdullahi ita shaɗaf ta manta da wani driver. Abinda ya cika ma ta zuciya shine yadda za ta ji idan Najeeb ya shigeta. Yau kan ko ma wani irin uzuri ne ba za ta yadda ba sai ta san yadda za su je hotel su je su yi abubuwa...

Farida kam wani zazzaɓine mai zafi ya rufeta.
Kusan ƙarfe shaɗaya sai ga Sabreen ta kirata.

"Mi ya sa za ki min haka? Ba na son shiga rayuwar kowa Ayshah"

Ta sani ƙila Lukman ya kira ta ne dan jiya ta bashi numbar Sabreen ɗin.

Ta danne duk wani baƙin ciki da ke ranta ta shiga ba ta labarin Lukman a taƙaice. Ta ƙare da cewa " Sabreen kince kina son gyara rayuwar ki. Shiyasa na miki kwaɗayin ki kasance tareda mutumin da zai taimaka miki wajen cimma burin ki. Lukman mutum ne da zan iya bugan ƙirji na ce shi ɗin namiji ne na gari wanda ya san kima da darajar mace. Wanda ya ke da ilimi ya ke kuma ƙoƙarin amfani da wannan ilimin da Allah ya bashi. Amma idan kina ganin na miki shishshigi a rayuwar ki to kiyi haƙuri"

Shiru Sabreen ta yi na kusan rabin minti kafin ta ce za ta yi tunani a kai. Farida ta kashe wayar tana fatan Sabreen ta amince da Lukman. Bayan wayan su da Sabreen shiryawa ta yi dan ta je gida. Ko idan ta ga Ummi hankalin ta zai kwanta har ta iya tambayarta shawara bisa yadda za ta ɓullowa wannan baƙon lamari da ta tsinci kan ta a ciki...



*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


0️⃣5️⃣2️⃣








Aure Rahama ne, musamman idan ka samu kwanciyar hankalin mijin ka. Ummi har wani ƙiba ta ƙara ga haske da ta yi, annurin fiskar ta ya ninka na da.

Kunun Aya da Ummin ta yi ta kawowa Farida. Farida ta ƙarɓa ta tsiyaya a kofi. Ta riƙe ƙofin amma ba ta kai baki ba. Zuciyarta ne ya tafi ga abinda ke faruwa da ita tsakanin jiya da yau.

"Farida lafiya?" Ummi ta tambaya ganin 'yarta ta yi nisa cikin tunanin da ta ke.

"Dan Allah Hajiyata ina da tambaya"

"Minene?"

"Shin dama akwai lokacin da Namiji zai juya ma ka baya ne bayan kuna zaune lafiya?"

"Kin yiwa mijin ki laifi ko?"

"Ummi ba abinda na ma sa fa, idan ma akwai to ni duk iya tunani na ban gano ba. Ummi na bashi haƙuri amma ko kallo ban isheshi ba"

Ummi ta yi shiru tana nazartar Farida wanda damuwa ya bayyana ƙarara a fiskarta.


"Yanzu haka cikin yawar maganar ki ki ka gaya mi shi abinda ya ɓata ma sa rai"


"Najeeb bai taɓa fushi dan na gaya ma sa magana. Ba halinsa ba ne"

"Yanzu dai idan kin koma ki tsugunna har ƙasa ki bashi haƙuri. Ko ma minene Insha Allah za ki ga ya sauko"

So ta ke ta yiwa Ummi bayanin yadda Najeeb ya iya ganinta tana kuka amma ya wuce bai nuna ya damu ba. Amma kuma kar hakan ya sa Ummi ta shiga damuwa.
Ta daure ta ce "Insha Allah zan yi hakan"

"Dan Allah ki riƙe addu'a sosai. Domin addu'a da haƙuri su ke riƙe aure"

Farida ta ce "na ji Hajjaju na"

Ƙoƙarin sake fuska ta yi dan kar Ummi ta sa damuwa a ranta...

................................

Shigar su ɗakin hotel ɗin Naomi ta shiga cire kayan jikin ta. Najeeb na tsaye bai iya yin komai ba. Sai da ta gama fidda komai na jikinta sannan ta fara jujjuya jikinta tana faɗin " ya ka ga sexy body. Ko'ina a cike ya ke fam domin ka"

Idon sa yai ja zir yana fidda numfashi da sauri-sauri. Idon ta ke sa shi samun nitsuwa, idon ta ke sa ya ji sanyi a ransa. Amma yanzu da ta ma sa tsirara sai ya ke jin wani ƙunci da baƙin ciki, kan sa ne ya hau sarawa ya dafe goshin sa yana jin kan kaman zai tsage biyu.

"Sweetheart mi ya faru? What's wrong? Are you sick?" Naomi ta faɗa tana ƙoƙarin riƙe shi. Gaba ɗaya rikicewa yai yana jin kamar idan ya sake goshin sa kan shi fashewa zai yi.

Ganin yadda ya ke yi ya sa Naomi ta tsorata, ta shiga maida kayan ta...


...............

Tun kan su isa asibiti Abdullahi dreba ya turawa Farida text akan Najeeb ba lafiya su na hanyar asibiti.

Ta fito daga wanka kenan ta ji ƙaran shigowar saƙo. Da sauri ta je ta ɗau wayar saboda tunanin ta Najeeb ne ya ma ta reply ɗin texts ɗin da ta tura ma sa ɗazu.
Tana ganin Abdullahi hankalinta ya tashi. Ta buɗe saƙon da sauri.

*Oga ba lafiya muna hanyar asibiti*

Innalillahi ta faɗa tana kiran numbar Abdullahi...


Su na zuwa asibitin aka shiga da shi emergency saboda kafin su isa asibitin ya riga ya suma.

Naomi jikinta ɓari ya ke yi. Tsoro biyu ne a ranta, na farko kar asirin da ta ma sa ya zama ya karye na biyu kuma kar Najeeb ya mutu domin za ta shiga hali na ƙunci ga zargin ta da mutane za su yi...

A birkice Farida ta shigo asibitin. Ganin Abdullahi da Naomi su na tsaye cirko-cirko ya sa zuciyar ta ya karaya.

"Malam Abdullahi mi ya samu miji na? Ina ya ke?"

"Hajiya dan Allah ki kwantar da hankalin ki. Insha Allahu ba abinda zai sami Oga"

"Ina ya ke?" Ta faɗa da ƙarfi.

Kafin Abdullahi yai magana aka buɗe ƙofan ɗakin da ya ke. Da sauri ta ƙarasa gaban likita tana tambayar lafiyar Najeeb.

"Hajiya yana bacci yanzu. Sai dai dan Allah ku dinga kiyaye ɓacin ransa, yanzu haka jinin sa ne ya hau sosai"

"Can i see him?" Ta faɗa da raunatacciyar murya.

Likita ya ce e amma ta bari za a chanja ma sa ɗaki yanzu.

Su na tsaye aka fito da shi akan gadon marasa lafiya, aka turashi zuwa ɗakin da aka ba shi.
Farida da Abdullahi su ka bi nurses ɗin har ɗakin da aka maida shi, yayinda Naomi ta juya da baya ta tafi. Ta ji kaf abinda likita ya ce, amma zuciyarta ta rasa gane ko mi ya sa ran Najeeb ya ɓaci har ta kai ga haka. Normal su ka je hotel ɗin, infact da murmushi a fiskar sa lokacin da su ka shiga ɗakin. Tana cikin keke tana tariyo duk abinda ya faru tun safiyar yau. Ba wani abinda zai ɓata ma sa rai sai dai.... karaf ta tuna dai-dai lokacin da Najeeb ya fara chanja fuska. Tabbas tsiraicin ta da ya gani ne. Idan har saboda ba su yi aure ba ne ya ke jin ba zai iya kusantar ta ba to tabbas za ta gaya mi shi su yi aure nan ba da jimawa ba...


Awa uku kafin Najeeb ya tashi, lokacin duk 'yan gidan su sun zo har da Sabreen. Kowa tambayar abinda ya faru ya ke amma Farida ba ta da bakin magana tunda itama ba ta sani ba. Tunaninta ko saboda ita ne ya shiga wannan hali. "My Champ laifin mi na ma ka ne?" Ta faɗa a zuciyarta.

Daddy ya tambayi Abdullahi ko daga ina su ke. Ya san matuƙar ya faɗi gaskiya to iyayen Najeeb za su shiga tashin hankali musamman ma Farida da ciki gareta.
Ya chanja maganar da cewa sun je wani site ne yai magana da ma'aikatan da ke wajen to da su na dawowa shi ne ya fara riƙe kan sa yana nishi sama-sama.

Daddy ya ce " Allah shi kyauta, amma daga yanzu duk wannan aikin fita supervision ɗin ya isa haka. Anas ko wani daban zai dinga zuwa"

Lokacin da ya farfaɗo garau ya ke jin sa sai dai rashin ganin Naomi a wajen ya sa ya ji ba daɗi. Yana son tambaya amma Mom da Farida sun ƙi bashi dama kowa nan da nan ya ke da shi. Ya haƙura ya zuba mu su ido.
Chan dare aka sallamesu saboda ya ce ba zai kwana ba, shi lafiyarsa lau...

Su na cikin mota amma ba wanda yai wa ɗan uwansa magana. Farida ta kamo hannun sa ta kai kan cikin ta tana faɗin "baby ya missing ɗin ka sosai"
Zare hannunsa da yai daga kan cikinta ya sa ta zaro ido. Tana binsa da kallon mamaki, juyar da kan sa yai yana kallon titi.
Hawayen baƙin ciki su ka fara zubo ma ta.
"Wai mi ke faruwa ne?" Ko lokacin da bai gane ta ba a asibiti farkon farfaɗowan sa ai ba ya ma ta wannan walaƙanci balle yanzu da su ke tsaka da soyayya. Wai har cikin da ke jikinta ma bai damu da shi ba.

Ba ta kuma yunƙurin yin wani abu ba har su ka isa gida. Ido kawai ta ke binsa da shi duk abubuwan da ya ke yi.
Tana ganin ya zauna a bakin gado yana shirin kwanciya ta zo gaban sa. Tsugunnawa ta yi ta riƙe gwiwowin sa duka biyu.

"Na roƙe ka da girman Allah Ubangiji Mai Rahama. Ka yafe min mijina, na yadda na yi ma ka laifi a rashin sani amma ka yafe min. Horon rashin magana da halin ko in kula ya min tsauri. Mijina abin so na, abin muradi na. Kai kaɗai ka mallake zuciyar Aisha Farida. Ba ni da tamkar ka kuma ba zan taɓa samun tamkar ka ba, ka yi haƙuri dan Allah ka gaya min mi na maka ka kuma yafe min. Idan ka cigaba da haka ciwon zuciya zai kasheni...." kuka ya kufce ma ta.

Duban ta ya ke yadda ta ke ta sheshsheƙar kuka, maimakon ya ji tausayin ta sai ma ran sa ya ɓaci.
Da kakkausar murya ya ce " you liar, ba ki da wani bayan ni? Oh really! Shi ne daga fita na ki ka kira tsohon saurayin ki ya ɗebe mi ki kewa kafin na dawo ko?"

Shiru ta yi tana rarraba ido dan ba ta gane maganar sa ba.
"Tsohon saurayina kuma? My Champ...."


"Oh please! Ba na son jin komai ki je ki yi duk abinda ki ke so"

"Wai Lukman ka ke magana? Haba My Champ, haba. Tsakanina da Lukman ya zama tarihi"

Miƙewa yai ya ɗau pillow zai fita ta riƙe ƙafar sa.

"Dan Allah ka tsaya na ma ka bayani. Wallahi ba abinda ka ke tunani ba ne"

Turata gefe yai ya fice abinsa.
Farida ta fashe da wani sabon kukan. Ba abin da ya fi damunta irin wai duk hukuncin nan akan zargi ne. Ta ya zai zargeta, wani irin so za ta nuna ma sa ta tabbatar babu wani namiji a rayuwarta da ya wuce shi. Tafi minti talatin tana kuka kafin ta tashi ta shige banɗaki ta ɗauro alwala.

Bayan ta yi sallah ta zauna a sallayar tana kuka tana gayawa Allah buƙatunta. Ta jima tana addu'a kafin ta naɗe sallayar ta je ta kwanta. Ba abinda ke ranta irin cin uban Naomi da za ta yi gobe, tunda ita ce 'yar burauban da ta haɗa ta da mijinta, ta ma ta ƙaryan mijinta bai zo ba ranan. Ashe ya zo har ya ganta da Lukman.
Ta jima tana saƙa da warwara kafin bacci yai gaba da ita.


.........................


Washegari tun da sassafe ta kira Sabreen akan dan Allah ta shirya za ta mata wani taimako. Sabreen ta amsa da ba matsala.

Karyawan kirki Farida ba ta iya yi ba. Zuciyarta ke tafarfasa yana zafi. Ba ta san sadda ma Najeeb ya fita ba tana tsammanin ƙila lokacin da ta koma na ta ɗakin ne...

Kamar jiya ma dai Najeeb cewa yai ya kai shi gidan su Naomi. Jin haka ya sa Abdullahi ɗaura aniyar dole ya sanar da Farida, domin gaskiya akwai lauje cikin naɗi a wannan al'amarin.

Naomi ta yi farin cikin ganin Najeeb garau ba kamar jiya da ya ke rai a hannun Allah ba. A cikin motan hannunsu sarƙe cikin na juna har su ka isa kamfani...

Suna isowa sai ga Anas shima motar sa ta yi parking. Da sauri ya fito ganin Najeeb da Naomi sun fito mota ɗaya.

"Najeeb... Najeeb" Anas ya kira shi da ƙarfi da ke sun riga shi fitowa a mota.

Najeeb ya juyo ya kalli Anas. Kallon tuhuma Anas ke wa Najeeb ɗin har ya iso.

"Good morning Sir" Naomi ta gaishe da Anas tana murmushi.

Ko amsawa bai yi ba ya ce ta basu waje. Naomi ta yi gaba tana tafiya tana yauƙi.

Anas ya kalli Najeeb ya ce "mi ke faruwa Najeeb? Mi ya sa za ku taho tare kai da sakatariyar ka? Ina Farida?"

" Dude ka ci sa'ido. Ina Baby? Fatan ka na kula min da ita sosai"

"I'm serious Najeeb. Mi ke faruwa?"

Najeeb ya ɗan buga kafaɗar sa ya ce " kar ka cika ni da surutu we have board meeting today"

Girgiza kai Najeeb ya fara yi yana neman yaƙi da abinda zuciyar sa ke raya ma sa. Najeeb ba zai taɓa haka ba, ba halin sa ba ne, No.
Ya jima tsaye kafin ya bi bayan Najeeb wanda tuni ya shige ciki...


Ƙarfe tara da rabi Farida da Sabreen su ka iso Kamfani. Tun a mota Sabreen ke tambayar Farida me ke faruwa amma ta ka sa gaya ma ta. Cewa kawai ta yi za ta ba da wani

Please Login or Register in order to submit comment