Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ta ke yi a school. A haka har ta ƙare secondary school ɗin ta. Jamb ɗin ta na farko ba ta ci ba dan haka ta fara zuwa koyon computer a shagon ƙanin Umminta Ahmad. Ta koyi abubuwa da dama dan Alhamdulillah Allah ya bata ƙwaƙwalwa. Da ta sake Jamb ta tafi Federal polytechnic da ke Bauchi saboda UJ da ba ta samu ba. Business Administration ta karanta a ND da ta zo HND ta koma Marketing. Aisha Farida 'yar kasuwa ce tuƙuru. Dan tana makaranta ba ta zauna haka ba ita ce saida turare, takalma da jakukkuna. Ga shi duk hutu idan ta je Jos za ta saro gwanjuna ma su kyau ta zo tana sayarwa students. Wannan ya sa 'yan ajin su ke kiranta Aisha mai gwanjo.
Yanzu shekarar ta ashirin da uku, tana service a Yola. Tun a camp su ka haɗu da Yasir Sa'ad ɗa ga senator Sa'ad Babagana. A UK Yasir yai karatu. Da farko su na fita daga camp zai relocating zuwa Abuja Inda iyayen sa su ke sai dai soyayyar Farida da ya shigeshi farat ɗaya ya sa ya fasa. Hakan ya sa a Inda aka turata primary assignment ɗin ta shi ma ya je. Duk iya watannin da su ka yi tare Farida ba ta bashi dama ba. Tausayin sa ta ke ji ta girme shi da shekara ɗaya ita kuma tana ganin tsayawa soyayya da shi ɓata lokaci ne. Ga uwa uba kiran da Hajiyar sa ta mata akan ko da wasa kar ta amince da soyayyar Yasir saboda karatu zai yi hakanan akwai alƙawarin aure tsakanin sa da wata. Ita dai Farida ba dan tsoro ta ke baya-baya da shi ba ko kuma ta ƙi son sa ba sai dai bazata bawa kanta ciwon kai a kan Yasir ba. "Yaushe ma ka girma?" Abinda ta ke yawan gaya ma sa kenan.


*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣0️⃣2️⃣


Da dare baƙuwar number ya kirata, da ta ɗauka sai ga muryan Rayyan.
"Ɗankwassi! a ina ka samu number ta?"
"My Farida kenan, abinda ka ke so ai duk wuya duk rintsi sai ka samu"
"Chan ta matse ma ka" ta faɗi tareda kashe wayar.
Ya sake kira ba ta ɗauka ba. A hankali a hankali Rayyan ya cigaba da kiran Farida, tun tana ƙin ɗauka har ta koma idan ta ɗauka za ta surfa ma sa masifa, shi kam da gaske ya ke dan haka bai damuba duk abinda za ta ce ma sa shanyewa ya ke. Cikin sati uku sai da ya san yadda ya ja hankalin Farida har tana ɗan kulashi ta dena ma sa faɗa idan ya kira.
Ranan da su ka yi passing out ɗin su sai ga shi a Yola. Ta ji mamaki hakanan kuma ya ɗan samu matsayi a zuciyarta. Saboda Yasir ya haƙura da ita ya sa ta introducing Rayyan a matsayin saurayin ta. Yasir kamar ya haɗiyi ran sa saboda baƙin ciki haka su ka rabu da shi baran- baran. Ko sallama babu.

Rayyan Abdullahi ɗan Kano ne kuma ma'aikaci a Zenith bank. Ya je Bauchi ta'aziyar 'yar yayarsa da ta rasu su ka haɗu da Farida. Sosai ya ke jin Farida a ransa, tsiwarta da masifarta yana burgeshi matuƙa. Ya ɗau ɗamaran koyawa Farida son sa musamman da ya gane ba ta da wani tsayayyen saurayi. To ina za ta yi saurayi bayan masifarta kaɗai ya isa ya sa samarin su dinga gudun ta.


..................................

Isowar sa kenan cikin gidan a gajiye. Kai tsaye ɗakin sa ya wuce dan ya san Daddy ba ya nan balle ya je ya gaida shi. Ya na shiga ya danna SHS zuwa Main kitchen "lemon tea in 10minutes" ya faɗi tareda zama ya fara cire socks na shi daga nan ya cire gaba ɗaya kayan jikin sa sannan ya shiga toilet.

Adama ta zo haurawa ɗauke da tea ɗin Najeeb ta haɗu da Afrah da ke shirin haurawa saman. Ta duƙar da kai ta gaisheta, Afrah ta amsa a gatsine.
"A Ya Najeeb za ki kai wa?"
Adama ta amsa da "eh"
"Kawo zan kai masa" ta ƙarɓi tray ɗin daga hannun Adaman.
Ta cigaba da hawa stairs ɗin tana tafiya ƙarar takalminta na ba da sautin ƙas- ƙas- ƙas...

Tana jin ƙaran ruwa a banɗaki lokacin da ta ajiye ma sa tea ɗin a ɗakin, kamar za ta fita sai kuma ta samu kujera ta zauna tana jiran sa. Kusan minti biyar sai ga shi ya fito ɗaure da towel. Ya na faman goge gashin sa da ɗan ƙaramin towel ya ganta ta ƙura ma sa ido.
"What the fuck! Mi ki ke yi a ɗaki na" Ya daka ma ta tsawa

Daburcewa ta yi ta fara kame-kame.
"Get out" ya daka ma ta tsawa ba shiri ta fita da gudu dan ta san halin sa sarai.

Sai da ya shirya cikin farar riga da wando baƙi three quater sannan ya buɗe laptop ɗin sa ya na duba wani aiki da Joseph sabon sakatarin sa ya turo ma sa. Yana dubawa yana sipping tea ɗin sa a hankali. Ba laifi Joseph yai ƙoƙari, da alama ya san aikin sa dan tunda ya fara ma sa aiki bai samu kuskure ɗaya cikin ayyukan da ya ke sa shi ba, sai dai da saura tunda dududu sati biyu da Joseph ɗin ya fara ma sa aiki kenan.


..........................

A hankali soyayyar Rayyan da Aisha Farida ta fara nisa, domin har ya je Jos ya gaida Ummi...

"Farida ba magana na ke mi ki ba"

"Ummi dan Allah ki haƙura da wannan zancen, zan dai dinga zuwa mu su akai-akai yanzu tunda na gama bautar ƙasa"

"Kin sani sarai har yau Alhaji Musa ni yake ɗaurawa laifi akan na raba ki da dangin Baban ki. Sun fi ni iko da ke Farida"

"Ni kan Ummi ki yi haƙuri, ba zan je ba, albarkacin Inna na ke zuwa mu su dama, kuma ta rasu shikenan"

"Ki yi yadda ki ke so Farida" Ummi ta faɗi tareda barin ɗakin.

Ita ta rasa dalilin da zai sa sai yanzu Baffa Musa zai takura wai ta koma wajen sa da zama. Ita yaushe ma za ta juri zafin Kano balle uwa uba rashin kunyar yaran sa. Dama dalilin Inna ke kaita Kano kuma tunda ba ta nan kowa ya riƙe kan sa. Da wannan tunani ta janyo purse ɗin ta tana irga kuɗin da ke ciki a karo na biyar kenan tun safiyar yau.

Sosai Ummi ta nuna ɓacin ranta akan ƙin zuwa Kano da ta yi, ko gaisuwarta yau da safe ba ta amsa ba.

"Nanna dan Allah ki cewa Ummi ta bar ni na yi zamana anan. Wallahi ba jin daɗin zaman Kano na ke yi ba"

Nanna da ke shan kunu da ƙosai ta ce " kin dai san da daɗewa Ummin ki tai alƙawarin za ki koma Kano da zaran kin gama makarantar ki. Alhaji Musa da kan shi ya kirata jiya ya ke cewa ya ji shiru. Ke idan ba ke bama ba saurayin ki ɗan Kano bane, idan ki ka je chan sai ku saita kan ku, kinga ba sai an sha wahala ba daga nan sai dai mu je bikin ki chan Kanon"


Ta turo baki tana faɗin "Allah dama kun gaji dani. Ni dai ba zan je Kano ba"

"Ah to, sai ki kira Baffan na ki ki gaya ma sa ai"

Farida ta zumbura ba ki ta fice a ɗakin....


Cikin kwana biyar ta gama shirin ta tsaf, ba wai tana son zuwa Kano bane, sai dai tunda abinda Ummi ke so kenan dole ta yi shi. Ranan asabat ta wuce Kanon tsabar haushi ko kiran Baffa Musan ba ta yi ba balle ta sanar ma sa da zuwan ta.
A ƙofar gida ta haɗu da su Kamal yaran Baffan su na wasa, da gudu su ka zo su ka tareta sannan su ka tayata ɗaukan kayan ta.

Da sallama ta shigo tana ƙarewa cikin gidan kallo wanda ya sha sabon fenti da alama dai saboda bikin Hajara da Salima da za a yi ne.
Baaba Sabuwa ta fara gani wanda ihun yara ya sa ta fito daga kitchen. Duk cikin matan Baffa Musa ita Farida ke ɗan gani da mutunci saboda itace uwargida kuma ba laifi tana da kirki.

"Oyoyo mutanen Jos. Sannu da zuwa"

Gyalenta ta saƙala ajikin igiyar shanya tana faɗin "fatan mun sameku lafiya"
"Lafiya lau, ya su Ummin na ku?"
Daga kitchen ta ke amsa ma ta da lafiya. Sai faman buɗe tukwane ta ke yi tana neman abin da za ta sa a baka.

"Baaba Sabuwa ni kam har yanzu ba ku bar baƙar al'adar ku ba, ace abincin rana sai ƙarfe uku"

"Lah yanzu na ke son ɗaurawa ai"

Farida ta dubi wayar ta tana faɗin " a ƙarfe ɗayan!"...



Sai da dare Baffa ya sa aka kirata. A falon shi ta sameshi yana cin abincin dare. Bayan ya ma ta ya hanya sannan ya fara bayani " Aminah ta ce ba ki fara aiki ba dan haka zan sa Yakubu ya nema mi ki aiki a kamfanin da ya ke aiki ko za a dace kema ki samu. Kafin nan kuma ki cewa yaron da ke neman ki ya turo saboda mu san da gaske ya ke yi. Kin dai ga yanzu shirin auren ƙannen ki a ke yi, zuwa ƙarshen shekara ke ma ayi na ki"

"Ni dama na san dalilin cewa in dawo Kano kenan, ni Baffa ban san mi na tare ma ka ba. Kanata wani ƙannena-ƙannena, na ga su suka ƙi karatu su ka ce aure za su yi. Ni dana zaɓi karatu na yi kuma na gama ai sai a bar ni na ɗan sha iska kafin a fara maganar aure na"

Ya ma ta daƙuwa ya ce "Uban ki Farida, na ce kin ci ƙaniyar ki. Wato har yanzu ba ki bar rashin kunyar ki ba ko" .

"To Baffa ina zaman zamana a Jos, ka takura Ummi wai ta turoni Kano. Duk abinda na yi ai kai ka ji za ka iya..."

Marfin kwanon silver ya wurga ma ta ta kauce ba shiri. " ki kiyaye ni Farida wallahi zan mummunan saɓa mi ki. Tashi ki bani ware! Ja'ira kawai"

Sum-sum ta tashi ta fice a falon dan ta san ƙarshe zai iya marin ta ko ma ya daketa. Dan Baffa Musa akwai saurin hannu.


..........................

Ba ƙaramin kyau yai ba cikin shirin sa na riga da wando baƙi sai kuma blazer kalar navy blue. Ɗauke da briefcase ɗin sa ya sauko daga stairs ɗin cikin takunsa na girma da ƙasaita.
Ƙai tsaye wajen dining ya je inda iyalen gidan ke cin abinci. Ya sunkuya yaiwa wata budurwa peck a kumatu yana faɗin " good morning baby"

"Morning Big B" ta amsa tana ma sa murmushi

Itama Afrah da ke gefe ta ce " Good morning Yaya"
"Morning" ya faɗa a taƙaice.

Tea ɗin da ke gaban Baby ya ɗan ƙurɓa ya ce " sai na dawo ko"

Wata haɗaɗɗiyar mata da ke zaune opposite da Baby wanda tun saukowar shi idon ta ke kan sa ta ce "have breakfast with us, please"
A dararance ya kalleta ya ce "na gode Justice Nabilah"
Har ya bar falon ba ta dena kallon sa ba, zuciyar ta na ƙuna. Sai yaushe ne ɗan ta zai kira ta da sunan uwa? Sai yaushe alaƙar su zai dawo dai-dai kamar kowace uwa da ɗan ta? Shekaru sun ja amma har yau babu wata chanji tsakanin su.

Baby ta ce"Sorry Mom"
Justice Nabilah ta girgiza kai ta ce " kar ki damu Najdah" ta ƙaƙaro murmushin dole dan jaddada maganar da ta yi.
Ita dai Najdah jikin ta ne yai sanyi, har yau ta kasa gano dalilin ƙiyayyar Yaya Najeeb da Mom, wanda tun tasowar ta haka ta same su.
Tambayar duniyar nan ta yiwa Big B da Mom amma duka babu wanda ya bata gamsashshiyar amsa. Harta Daddy bai san dalilin wannan gabar ba. Tun yana faɗa akan wannan ƙiyayyar ta su har ya haƙura ya zuba mu su ido...

Tunda ya fita daga gidan kai tsaye wajen motar sa ya wuce. Wanda tuni aka fito ma sa da ita daga parking lot. Sau ɗari zai ɗau driver sau ɗari zai koresu. Shi ya sa yanzu kusan wata uku kenan rabon da ya sake ɗaukan driver. Shi ya ke tuƙa kan sa, ran da yake son yin aiki a cikin mota kafin ya ƙarasa office to zai sa drivern Daddy ya kai shi office.



*Najeeb Adam Jibo*

matashin da ya ke ji da kyau,kuɗi,ilimi da kuma gata. Ɗa namiji guda ga tsohon Ambassador kuma Professor Adam Jibo da Justice Nabilah Al-Jabir.

Adam Usman Jibo ɗan asalin ƙaramar hukumar Kumo ne da ke jahar Gombe, sai dai kasancewar tun rasuwan mahaifinshi ya dawo wajen ƙanin Baban sa da ke Kano da zama ya saka zamansa ya koma Kano. Alhaji Mustafah Jibo babban ɗan kasuwa ne da ya ke da arziƙo tun a wancan lokacin.

lokacin da Adam ke da shekara bakwai a duniya mahaifin sa ya rasu, dan haka zaman sa da shi da ƙannen sa mata biyu su ka dawo hannun Alhaji Mustafah , lokacin Mustafah da matar sa shekarar su takwas da aure amma basu taɓa haihuwa ba. Sun riƙe Adam da ƙannen sa Ruƙayya da Fatima tamkar 'ya'yan da su ka haifa. Sai da su ka shekara goma sha biyar da aure ba haihuwa sannan Hajiya Mama wanda haka su Adam ke kiranta ta dage akan lallai Alhaji Mustafah ya ƙara aure ko za a dace.

Wata ƙanwar maƙocinsa kuma amininsa ya aura. Budurwace dan a lokacin da aka yi auren su shekararta shashida. Cikin ikon Allah watan Halima goma ta haifi ɗan ta namiji ya ci suna Sulaiman. Murna wajen Alhaji Mustafah ba a magana. Bayan Sulaiman ta haifi Abubakar sai da ta shekara huɗu kafin ta haifi Aisha wanda lokacin haihuwanta ta wahala sosai, tun lokacin haihuwar kuma ta ke jinya bayan sati uku ta rasu. Mutuwar da ta girgiza iyalen Alhaji Mustafah gaba ɗaya.

Hajiya Mama ba ta haifa ba amma ta ɗauki duka yaran tamkar ita ta haifesu, wanda ko kaɗan ba za ka taɓa ganin abu ɗaya da zai nuna ma ka ba ita ɗin ta haife su ba. Ba ma kamar Aisha wanda ita ta shayar da ita. Haka yaran su ka taso ba su da wata uwa da ta wuce Hajiya Mama. Kuma har lokacin da Alhaji da Hajiya Maman ba wanda ya banbanta tsakanin yaran marigayi Usman Jibo da kuma ainihin yaran Alhajin. Sai dai a hankali su ka fahimci Aisha ba ta magana, kurmiya ce. Anyita magani amma shiru, tana ji amma ba ta iya magana. Wannan lalura ta sa da Alhaji da Hajiya Mama su ka maida hankalin su wajen kula da Aisha sosai.


Da Adam ya gama primary school na shi Alhaji Mustafah ya kaishi Lagos karatu. Bayan kammala secondary school na shi a kings college da ke Lagos ya wuce Harvard yai degree ɗin sa a fannin International relation,daga nan ya wuce London Business school yai wani degree ɗin a fannin Business sannan yai masters na shi da Phd a Yale University. Ya fara koyarwa a Yale kafin Nigeria ta tura shi Canada a matsayin Ambassador daga nan aka maida shi USA daga USA sai Belgium daga nan sai South korea wanda daga south korea ɗin ne yai retire ya dawo Nigeria inda yai zaman shekara ɗaya yana hutawa, gomnati ta mi shi chaaa akan ya shigo siyasa a dama da shi sai dai shi ya fi son koyarwa saboda ya amfanar da mutane ilimin da ya tara. An awarding na shi professor kuma yana visitin lecturer a jami'o'i da dama a ƙasar, musamman ABU, BUK, UJ, UI da sauran su.

Adam Jibo ya haɗu da Nabilah Aljabir ne a Yale University lokacin yana masters na shi. 'Ya ce ga wani hamshaƙin mai kuɗi Aljabir Al Mukhtarr ɗan asalin ƙasar Bahrain. Soyayya ce mai ƙarfi ta shiga tsakanin su tun haɗuwar su a library. Ba ƙaramin sa'insa aka samu ba kafin aka amince da auren su musamman da ya ke tana balarabiya shi yana bafulatanin Nigeria. Sai dai Nabilah ita kaɗai ce 'ya mace a wajen mahaifinta kuma mahaifinta na son ta sosai.

Bayan auren su da shekara ɗaya ta haifi Najma wanda sunyi niyyar sawa yaransu sunayen da su ka fara da harafin N da A da J. Harafin N saboda Nabilah, harafin A da J kuma na Adam Jibo. Bayan shekara uku ta haifi Najeeb wanda daga shi sai da shekaru su ka ja kafin Najdah ta zo duniya, kusan shekara sha uku Najeeb ya bata. Dawowar su Nigeria Nabilah ta yi Pre Law school na wata shida kasancewar a ƙasar waje ta yi karatu kafin ta yi regular Law school. Ta yi aiki a kotuna da dama kafin daga bisani ta kai matsayin Justice.
Najma ɓangaren likitanci ta karanta tana aiki a National hospital Abuja a matsayin gyneacologist. Tana auren wani hamshaƙin mai kuɗi ɗan kasuwa kuma likita Dr Mujahid, yanzu haka yaran su uku.

Tun kafin Adam Jibo ya dawo Nigeria dama ya riga ya gina wani ƙaton gida a Kano. Anan iyalen sa ke sauka idan sun zo hutu Nigeria. Ƙannen sa sun yi aure suma da nasu iyalin Fatima na aure a Kano yayinda Ruƙayya ke aure a Katsina. Suma ƙannen sa 'ya'yan Alhaji Mustafah sun yi aure da iyalen su. Sulaiman yana Kano yayinda Abubakar ke Abuja. Duk wata su kan haɗu ayi meeting a gidan tsohuwa wato Hajiya Mama. Alhaji Mustafah ya jima da rasuwa tun kafin rasuwan Aisha. Hajiya Mama tana nan a gidan Alhajin sai fama da jikoki. A gefen gidan Alhajin duka Sulaiman da Abubakar su ka yi gininsu. Shi Adam ne gidan sa yai nisa da su. Sai dai shima indai yana gari to kullum sai ya je ya gaida Hajiya Mama wannan ya zamo ma sa al'ada. Hajiya Mama ita ya sani a matsayin uwa. Goggon su ta jima da rasuwa bayan rasuwar Mahaifin su ta sake wani auren a Ashaka inda wajen haihuwa ta rasu. Haƙiƙa Hajiya Mama uwa ce ta gari. Ba ta haifi nata ba amma ta riƙe yaran mijinta tsakani da Allah wanda har yau suna darajata. Inda ace ta ha'ince su da tuni sun watsar da kashinta musamman bayan da Alhaji Mustafah ya rasu.


Duka karatun Najeeb a ƙasar waje ya yi su. To dama a ƙasar wajen aka haife shi. Yai degree na shi na farko a MIT (Messacheusettes Institute of Technology ) inda ya karanchi Engineering and Technology daga nan ya sake wani degree ɗin a ɓangaren Architecture. A London yai Masters na shi kafin ya tafi Korea yai Phd na shi.
Ya fara aiki a Korea da wani construction company kafin ya ajiye aikin ya je yai wani course a India, lokacin Mahaifinsa Professor Adam Jibo ya dawo Nigeria da zama. Bayan ya ƙare course ɗin ne ya dawo Nigeria ya buɗe Kamfanin sa mai suna *Najeeb constructions* shekaru bakwai da su ka wuce kenan.

Ya taso cikin kuɗi kuma ya nemi kuɗi ya samu. A shekarun sa talatin da huɗu, ba abinda ke gaban sa da ya wuce kamfanin sa. Zai iyayin komai saboda samun ɗaukakar kamfanin sa.

Anas shi ne babban aminin sa, jinin su ya haɗu sosai duk da kuwa Najeeb ya girmeshi da shekara uku, amintar su ta sa lokacin da ya buɗe kafanin sa ya jawo shi gefen sa su ka haɗu su ka ɗaukaka kamfanin saboda shima Architect ne. Bayan Daddy da Najdah wanda ya ke kira Baby to Anas shi ne mutum mafi kusa gareshi idan ka ɗauke Hajiya Mama. Sun jima da baran-baran da yayarsa Najma a kan ƙin Mahaifiyar su daya ke yi wanda har yau babu wanda ya san dalili abu kusan shekaru ishirin kenan.


*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣0️⃣3️⃣



Kamar kowani lokaci idan ta zo Kano ɗakin Inna ta ke kwana, wannan karan ma hakan ce ta faru, sai dai yanzu Maijiddah da Zainab ke kwana a ɗakin bayan rasuwar Inna. Daga zuwan Farida ta kori Zainab a ɗakin tace ba za su kwana su uku ba. Zainab ta fice daga ɗakin tana ƙuƙuni.

Maijiddah 'yar Baaba Sabuwa ce, kuma duk cikin yaran gidan tafi su hankali, kasancewa anyi auren ƙannenta biyu gashi za'ayi wasu biyun ya sa ake goranta mata rashin miji, kullum a takure take, dududu shekarar ta ishirin amma yadda ake mata gori a gidan ka ɗauka ta shekara talatin ne ba tayi aureba. Wai har 'yar Zainab da ke shekara shahuɗu tanada samari ita ba ta da kowa. Duk masu zuwa wajenta ba sa jimawa su ke guduwa. Islamiyya kaɗai ta ke zuwa yanzu, sai kuma takan taɓa ɗinki a keken Baabarta sannan tana sana'ar kitso. Dan wani lokaci har gida ake zuwa a kirata ta je ta yi kitso, domin gaskiya Allah ya bata baiwar iya kitso.

Shekarar ta uku da gama secondary, dokar Baffa Musa ce, sai dai mace ta yi karatun gaba da secondary a gidan mijinta amma ba a gidan shi ba, shi ya sa Maijiddah ba ta yi wani hoɓɓasa domin ta cigaba da karatu ba, saidai cikin ran ta tana ƙwaɗayin hakan. Ba wai muni gareta ba tana da kyau dai-dai gwargwado sai dai gaskiya guntuwa ce. Dan harta Zainab da bata gama tsayinta ba, ta fita tsayi.
Maijiddah tafi ganin gajartar da Allah ya mata a dalilan da ya sa ta rasa manema...

Suna sallar Asuba Maijiddah ta gaida Farida sannan ta fara gyara ɗakin su har lokacin Farida na yin azkar. Da ta gama ta fita dan ta fara hidiman cikin gida. Lokacin da Farida ta fito daga ɗaki Maijiddah kaɗai ta samu a tsakar gida tana shara. Cikin isa ta riƙe ƙugu tace " Jiddah ina batun dokokin dana sa a gidan nan wancan zuwana Kano?"

"Anty Farida kin san yau Lahdi ne ba a tashi da wuri"

Murya sama-sama ta fara magana. " Tab! wato dan bana gidan shine aka watsar da dokokina ko. To ku sani Wallahi duk wanda ya san yau ranan aikinsa ne bai fito ba ganinan zuwa har ɗakin uwarsa in dakeshi kuma ba abinda zai faru. Zan irga uku ɗaya....biyu...." sai ga yaran suna fitowa daga ɗakunan su da gudu. Da ke sun manta tsarin da ta musu, kowa sai ya fito dan kar ya zama ranar sa ce kuma bai fito ba ta bishi ɗaki ta zane. Ba yau Farida ta fara zane yaran gidan ba, yanzu haka yadda su ke tsoronta ko su Yaya Yakubu iya kaci.

Maijiddah ta ɗan yi murmushi lokacin da ta ga ƙannen nata na fitowa da gudu.



...............................


Ba tareda ya ɗago ya kalli Joseph ba ya ce " three days" Joseph ya haɗiyi yawu moƙot saboda ba shi da ta cewa, amma taya kwana uku zai ishesa ya je Enugu burial na Maman sa ya dawo a kwana uku, bayan Enugun ma chan cikin wani ƙauye mai nisa su ke.

"Anything else?" Muryar Najeeb ta dawo da shi daga tunanin da ya ke. Joseph ya girgiza kai da sauri ya ce "no sir". Da hannu Najeeb ya ma sa nuni da yai waje. Joseph ya bar office ɗin da sauri...



Tare su ka fita da Anas, sunje sun duba wani site da kamfanin su ke ginawa. A hanyar su ta dawowa Anas ya nuna yunwa ya ke ji dan haka dole su ka tsaya a wani restaurant da ke kusa.

Fiskar san nan tamau ta ke kamar bai taɓa dariya ba a tarihin rayuwar sa. A haka su ka shiga wajen cin abincin, shi idan ba dan Anas ba ba abinda zai sa ya tsaya a irin wannan waje. The restaurant is not even classy.

Sai da su ka zauna waiter ya zo dan ya ƙarɓi order ɗin su. Da sanin Najeeb ya faɗi wani kalar girki wanda baya cikin menu ɗin su. Saurayin ya ɗan tausasa murya ya ce "sorry sir, we dont have that in our menu"

Najeeb ya smirking ya ce " then, water will be fine"

Har zai tafi Anas ya tsayar da shi ya ce ya kawo wa Najeeb irin abinda ya ordering.

"Seriously!" Najeeb ya faɗi yana ɗan girgiza kai.

"Mutumina kai fa ba engine ba ne, tun safe fa ba abinda ka ci. Gara ni naci ɗumame na ƙoshi kafin na fito, amma kai

Please Login or Register in order to submit comment