Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta kai Maijiddah kirki ba inji Faridan.

Ɓangaren Maijiddah kuwa da ta je ta samu jikokin Hajiya Yelwa suna karyawa dan haka sai da ta jira su ka gama sannan ta mu su kitson, da ke ba wannan ne karan farko da ta ke mu su kitso ba, su na yi su na hira. Yawanci in sun zo hutu wajen Hajiya Yelwa to ita ke mu su kitso.

Ta tsantsara mu su kitso mai kyau harda adon beads. Dama ga yaran 'yan gayu da su. A Lagos su ke da zama ko hausan kirki ba sa ji. Maryam da su ke kira da Baby saboda sunan Hajiya Yelwa da ta ci 'yar shekara bakwai ce, sai ƙaramar Alizah 'yar shekara huɗu.


Maijiddah ta na zaune a ɗakin Hajiya Yelwa tana jiran ta, ta riga ta gama yiwa yaran kitso tun ɗazu amma Hajiyar ba ta nan, ta ce kuma ta jira ta har ta dawo.
Tana zaune kan carpet tana danna ƙaramar wayarta ƙirar Tecno wanda ya ji jiki ya tsufa. Tun wanda Yaya Faruƙ ya siya ma ta ne lokacin da ta yi sauka shekara huɗu da su ka wuce.
Ba ta ankara ba ta ji shigowar Alizah ɗakin da gudu. Ɗago idon da za ta yi ta ga ƙatuwar kyanwa ta yo kanta, ƙwalla ƙara ta yi ta hau gadon Hajiya Yelwa da sauri, ai kuwa kyanwar ma kawai sai ta hau gadon da alama kyanwar gudun Alizah ta ke. Maijiddah ba shiri ta dira a gadon ta nufi ƙofa da gudu. Ɗaga labulen da zai yi yai karo da ita, da ke guntuwa ce kanta ya tsaya ma sa iya ƙirjinsa. Ƙoƙarin tureshi ta ke ta wuce dai dai nan kyanwar ta shuri ƙafarta ta fice daga ɗakin. Laushin jikin kyanwar da ya taɓa ƙafarta ya sa Maijiddah ta yi suman tsaye a wajen.
Alizah ta fara cewa " Daddy, please catch the cat for me"

Bai saurari yarinyar ba, ya ɗauki Maijiddah cak yai kan gadon Hajiya Yelwa da ita. Miƙar da ita yai sosai sannan ya cire ma ta hijabi dan ta samu iska ya shigeta sosai, Ƙaramin fridge da ke ɗakin ya buɗe ya ɗau goran ruwa mai sanyi. Ya zuba ruwan a hannunsa ya shafa ma ta a goshinta da wuyanta amma still ba ta farfaɗoba. Ya sake yin haka a karo na biyu wanda yana shafa wuyanta da ruwan sanyin ta jaa dogon numfashi ta buɗe ido, ta fara ƙoƙarin tashi dan ta zauna, ya sa hannu ya tallafa ma ta tareda faɗin "relax"
Sai alokacin ta fara wuri-wuri da ido saboda ganin ba hijabi ajikinta ɗankwalin kanta ma ya zame.
"Duk a dalilin kyanwa ki ke son hallaka kan ki. Miye abin gudu a jikin kyanwa?"

Ba ta bashi amsa ba sai ma ta sunne kanta cikin cinyoyinta. Ƙananun ƙitson kalaba (braids) da ta yi su ka zubo.

Ganin yadda gashin ke da tsantsi ya sa shi taɓawa dan ya tabbatar gashin kanta ne ba na aro ba (wig). Yana son mace mai gashi, haka nan ya tsani mace ta ƙara gashi abinda har yau matarsa Aneesah ba ta dena sawa ba kenan tun yana faɗan har ya gaji.
Tabbas gashin ta ne ya faɗi a ransa. Ga shi baƙi ga tsawo ga tsantsi.

Shigowar Hajiya Yelwa ya sa yai saurin cire hannunsa.

"Alhamdulillah!, ka ga yadda na tsorata da Alizah ta ce wai Hauwa'u ta mutu"

Yai saurin miƙewa ya ce " ai Hajiya ba dan ina wajen ba ƙila mutuwar za ta yi. Kin ga yadda ta firgita kuwa, sumewa fa ta yi"

"Ai Hauwa'u kam sai dai Allah shi albarka kawai. Tukunna ma waya fito da kuliyar ne?"

Alizah ta ɓuya bayan Daddynta dan ta san ita ce ta tafka aika-aikar nan. Tun kafin Maijiddah ta zo Hajiya Yelwa ta sa aka rufe kuliyar kuma ta mu su kashedin kar su yadda su buɗe ta.

Hajiya ta kama hannun Maijiddah ta ce " dan Allah ki yi haƙuri kin san sha'anin yara. Fatan ba ki ji ciwo ba?"

Maijiddah ta girgiza kai sannan ta lalumo hijabinta ta saka.

Yana tsaye ƙikam yana jira ta ɗago yaga fiskarta da kyau, ɗazu cikin ruɗu ya ke bai tsaya ya kalleta sosai ba. Sai da ya ƙare ma ta kallo sannan ya ce "Hajiya an gama haɗa kayan ne?"

"Angama Yaya, na ce da Faty ma ta kai su cikin mota"

"Barinje in gani kar su yi mantuwa"

Har ya kai bakin ƙofa sannan ya sake juyowa ya kalleta, har a lokacin bata gama nitsuwa ba jikinta na ɗan kakkarwa, yai murmushi sannan ya fita...

Hajiya Yelwa sai da ta tabbatar Maijiddah ta nitsu sannan ta sa autarta Faty ta raka ta har bakin gate duk da kuwa Fatyn ta tabbatar da an sake kulle kuliyar.

Hannunta riƙe da ledar da Hajiya Yelwa ta bata su ka fito da Faty.

Yana gindin mota ya ga fitowar su dan haka yai saurin ɗaga wa Faty hannu alamar ta zo.

"Kinga barinje Yaya na kira na" Faty ta gayawa Maijiddah.

" Lah ba komai, sai anjima" Maijiddah ta faɗi ta yi hanyar gate ɗinsu. Ba ta yi wasu taku mai yawa ba Faty ta ƙwala ma ta kira.
Da ta juyo ta ma ta hannu alamar ta zo. Tsayawa ta yi ta rasa mi za ta yi. Ga Daddyn su Alizah ya ƙura ma ta ido.

"Ki zo inji Yaya" Faty ta faɗi da ɗan ƙarfi. Ba yadda za ta yi haka ta fara taku a hankali har ta kai wajen motar, gefen Faty ta tsaya tana kallon ƙasa a hankali ta furta " ina kwana"
"Ki shiga ya kai ki a mota" Faty ta faɗi tana ɗan murmushi ƙasa-ƙasa.

A hankali ta ce " Lah Faty sai ka ce ba ki san gidan mu ba, ƙasan layi ne ba nisa"

"Wato dai ladar ne ba kya so na samu" Ya katse ta

"A'a Yaya, Allah ba nisa. Na gode"

" ki shiga mota ko na sa akawo kyanwar ɗazu"

Ai cikin firgici ta kama handle ɗin ƙofa tana kokawa da shi. Faty ta fara ma ta dariya.
Shi ma murmushin yai sannan ya danne key ɗin hannunsa ƙofar ta buɗu...


Sai da su ka fita daga cikin gidan ya ɗan kalleta ya ga ta takure gefe ya ce " ki na tsoron kar na sayar da ke ne?"

Ta girgiza kai

"Ko nima ina da kamannin kyanwa ne"

"A'a"

"To ya kika takure, kin ƙi ki sake jiki haka nan ba ɗan hira"

Shiru ta yi dan ba ta san mi za ta ce ba. " ashe ke ce me yiwa Hajiyata kitso. Kin san yadda ta ke yabonki kuwa. Ga ki 'yar ƙarama da ke, anya kin kai shashida kuwa?" Yai tambayar ne dan samun damar gabatar da ƙudirinsa, yanayin tsayinta da ƙaramin fiskarta ya ke ganin kamar ba za ta kai 18yrs ba shi kuma a gaskiya ba zai iya auren under 18 ba.

"Na wuce mana" ta faɗa a hankali

"Faɗamin gaskiya, shekarun ki nawa?. Idan ki ka min ƙarya ma zan gane"

"20"

"Ishirin! Kai yarinya ba ki kai ba"

"Yaya kawai ƙaramin jiki ne dani fah, amma anyi auren ƙannena har biyu yanzu ma an kusa wasu biyun" sai da ta yi maganar sai kuma taji haushin maganar da ta yi.

Cikin zuciyar sa ya ke jimami sai dai bai bayyana ba ya ce " ke mi ya hanaki auren? Karatu ki ke?"

Shiru ta yi ta juyar da kanta wajen glashi tana kallon waje.

Bai sake tambayarta ba yana dai sake karantar yanayinta. Sai da su ka iso ƙofar gidan su sannan ya miƙa ma ta wayarsa ya ce " sa min numbar ki anan"

Kwarjininsa da girmansa shi ya hana ta mishi musu. Ta ƙarɓa wayar ta saka nambobin ta.

Miƙa ma ta kuɗi yai ta ƙi ƙarɓa.

"Kuɗin ƙitson da ki ka yiwa su Baby ne"

"Hajiya ta bani ai"

"Hajiya daban ni daban. Ki ƙarɓa ko na sa a kawo kyanwar gidanmu na ɗaure mi ki ita a ƙafa"

Ta ƙarɓi kuɗin ta ce " na gode Allah ya saka da alkhairi" ya amsa da amin. Sai da za ta fita ya ce " a samu a addu'a, Insha Allah anjima zamu hau hanya"

"Allah ya kaiku lafiya ya tsare mu ku hanya"

"Amin"

...........................

Su Faridah ba su dawo ba sai yamma lis, da su ka dawonma hidimar gida ya sa ba su zanta da mutuniyarta ba. Sai da ƙarfe goma ta gota na dare bayan ta gama goge doguwar rigar da za ta saka gobe sannan Maijiddah ta fara ma ta bayani.

"Anty Farida barin nuna mi ki wani abu"

Ta miƙa ma ta wayarta. Farida ta amsa wayar tana faɗin " wannan tsohuwar wayar ta ki ma ya kamata ki chanja ta"

*Alhamdulillah! ni da yara na mun sauka lafiya. Na gode da addu'arki gare ni*
*AbdulWahab Bello Hassan*

"Weeeeeehuhu. Waye wannan dan Allah? ki ce addu'ar mu ta kusa karɓuwa"

"Kayya Anty, ɗan Hajiya Yelwa ne fa"

"Sai aka yi me. Abeg gist me, ya akayi ya samu numbar ki?"

Maijiddah ta labarta ma ta duk abinda ya faru.

"Ai Insha Allah mun sameshi 'yar uwa ki dai cigaba da tashin dare da kikeyi. Allah ya kusa amsar addu'ar mu. Tukunna ke da me ki ka ma sa reply?"

"Ban ma sa ba"

" amma anyi 'yar ƙauye anan"

"To Anty mi zan rubuta?"

"Mtsssw, give me the phone jooor"...


.........................


Doguwar riga ta atamfa ta saka kalar atamfar ja ce da ratsin fari dan haka ta saka ƙaramin gyale fari. 'Yar powder ta murza sannan ta goga jan janbaki kaɗan wanda ya ke ƙara haska fiskanta.

A karo na biyu Yakubu ya aiko ta fito shi zai tafi.

"Jiddah wannan yayan na kun ko"

Maijiddah dai sai dariya ta ke ma ta...

Su na tafiya Yakubu na ta yiwa Farida faɗa akan indai haka za ta dinga makarar da su to zai dena tafiya da ita kowa yai hanyar sa. "Haba Ɗan Musa, sai kace wanda mu ke aikin asibiti. Ban isa na fito ban karya ba, Allah na gani"

"Lallai kuwa, Sir Najeeb zai samu dalilin koran ki cikin sauƙi kenan"

"Ba Sir Najeeb ba Allah ya sa Sir Salihu ne"...


Office ɗin Anas ta fara zuwa dan ta gaishe shi ta samu cleaner tana shara.
Ta juya za ta fita sai ga Anas ɗin ma ya shigo.

"A'a ƙanwar mu ce da wurwuri haka, ashe da dai ba za kuyi faɗan latti da Ogan ki ba"

"Ina kwana Ya Anas"

"Lafiya Aisha Farida"

Bayan sun gaisa sannan ta wuce na ta office ɗin.
Nan ma ɗin ana kan gogewa ne hakan ya tabbatar ma ta Ogan na ta bai ƙaraso ba, ta zauna tana danna wayarta...

Cikin takunsa na ƙasaita wanda ke ƙara ma sa kyau da kwarjini ya shigo kamfanin na sa. Duk inda ya wuce gaishe shi ake yi sai dai fuskarsar nan mur ta ke balle ma asa ran zai amsa gaisuwar. Dama idan da sabo to sun saba. Sir Najeeb ba ya amsa gaisuwa.

Yana shiga lifter ya danna 3rd floor wanda nan ne za ta sada shi da office ɗin sa.

Ya ma manta batun yau sabuwar sakatariyar sa za ta fara aiki dan haka kai tsaye ya shiga office ɗin, sai dai tundaga bakin ƙofa muryarta ya fara dokan kunnensa.

"No it cant be her" ya faɗi lokacin da ya tako cikin office ɗin. Sai dai itan ɗin ce dai ya gani, ba ta san ya shigo ba saboda hankalinta na kan wayar da ta ke yi.
Ƙanshin turarensa da ya cikata ne ya sa ta ɗago da idon ta.

"And who are you?" Ya faɗi yana ƙare ma ta kallo.

" The new secretary" ta amsa ma sa

" This is bullshit" abinda ya iya faɗi kenan ya nufi hanyar office ɗin sa.

Tunaninta baƙon Oga ne dan haka ta yi saurin tsaida shi. Cikin bayanin da Anas ya ma ta. Bai kamata wani ya shiga office ɗin Oga ba tareda izininta ba.

" Mr Arab you cant enter the office, my boss is not around" ta faɗi da ƙarfi.


Tsayawa yai da buɗe ƙofar Office ɗin ya juyo ya kalleta, lokacin ta baro wajen kujeran ta ta nufo shi.

" you can seat and wait for him there" ta nuna ma sa kujeran da baƙi za su zauna Idan sun zo.

Ƙura ma ta ido yai, itama idon ta na cikin na sa. Hazel eyes na shi ta ke kallo wanda ya sa ta ji wani kasala nan da nan ta yi saurin ɗauke na ta idon. Ta yi gyaran murya sannan ta ce
" please go and wait for him"

Girgiza kai yai ya sa hannu zai buɗe ƙofar Farida ta yi saurin buge hannun sa ta shiga gaban sa ta stretching hannayenta tana tare ƙofar da su. "Dan Uban ka, dan kana balarabe sai ka ce ba za ka bi doka ba, to ba ka isa ba"
Idonsa ne su ka firfito lokacin da ya ji abinda ta faɗi.

Ta kalleshi ta ce " you will not enter this office. Anta La adkul.....a'a ba haka bane, Anta La Tadkulul Bab.... mtsww, yau ga ranan zuwa Islamiyya nan, ni Aisha ɗan Larabcin ma ta gagareni"

Hannu ya sa a aljihu ya zaro waya ya kira wata number, ana ɗaga kiran ya ce da kakkausar murya "Come to my office now"

Mamaki ne ya mamaye fiskan Farida lokacin da taji abinda ya ce sai dai ta dake a wajen ba ta matsa ba.

Suna tsaye a haka Anas ya shigo. Ganin yadda Farida ta yi kane-kane a bakin ƙofar office ɗin Najeeb ya sa shi fashewa da dariya.

"Tell this crazy girl to get out of my way" Najeeb ya faɗi cikin tsawa.

Anas ya dubi Farida wanda jin abinda Najeeb ya ce ya sa jikinta yai sanyi, ta sauke hannayenta amma ba ta matsa a bakin ƙofar ba.
Ya ce " Aisha ya ki ka hana Ogan na ki shiga office? ko salon na ki aikin kenan?"

"Ya Anas ni ban san shi bane ai. Akace sunan Oga na Najeeb Jibo, kuma na ga wannan balarabe ne. Suna *Jibo* kan ba na fulani ba ne?"

Anas ya fashe da dariya ya ce " kuma da gaskiyan ki fa. Sai dai wannan bafulatanin ruwa biyu gareshi, ruwan fulani kuma ruwan larabawa"

"Ya Anas ina dai ba ya jin Hausa?"

"Hausa kai, hausa kamar Jakar Kano ma"

"Shikenan ni Aishatu, daga fara aiki har na tafka katoɓara"

"Fatan dai ba ki zage shi ba?"

A sanyaye ta ce " sai dai gobe kar a ƙara"...

"Barin ji mi Ogan zai ce" Anas ya faɗi tareda shigewa office ɗin Najeeb. Dama tuni Najeeb ya shige ya barsu su.


Yana zaune kan kujerar sa ya na kallon ƙofa lokacin da Anas ya shigo.

" lokacin da na ce ka nemo min secretary, ban ce ka nemo mahaukaciya ba. She's fired, find another one" abinda ya faɗi kenan lokacin da Anas ya ƙaraso wajen sa

Maimakon Anas ya bashi amsa sai ya sa dariya har da riƙe ciki.

"This not funny, da na yi aiki da wannan gara na dawo da Joseph"

Har lokacin Anas bai bar dariya ba, sai da yai mai isar sa sannan ya zauna ya kalli Najeeb da ya cika yai fam.

"First of all Aisha ba mahaukaciya ba ce, secondly, a iya sanina da Najeeb na san girman kan sa ba zai taɓa bari ya dawo da Joseph ba. Thirdly idan ka kori Aisha, kai za ka ɗau nauyin neman wata ko wani da kan ka. Aisha ƙanwar Architect Yakubu Musa Wase ne, and as far as i know Yakubu is like a brother to me dan haka ƙanwarsa ƙanwata ce"

"Wow! Ban san ka fara kalen dangi ba ai"

"Ni ma kuma ban san ka fara tsoron mata ba"

"What do you mean?" Najeeb ya faɗa a fusace

"Na san ka gane Aisha ita ce yarinyar da ta tada hayaniya a restaurant ranan. Shi ya sa ka ke tsoron aiki da ita"

"Tsoro?" Ya furzar da iska daga bakin shi sannan ya ce " i'll give her a chance, idan ba ta iya aiki ba zan koreta. And i dont care who's sister she is"

"Ko kai fa mutumina" Anas ya faɗi tareda tashi tsaye. Har ya fara tafiya ya juyo ya ce " Dan Allah, ya ka ji da ta hanaka shiga office ɗin ka?"
Najeeb ya jefe shi da biro, Anas ya goce yana dariya...

Yana fita ya samu Farida tana zaune hankalinta kwance kamar ba laifin da ta yi.

" ƙanwata na roƙa miki shi, dan haka ba wata matsala amma ki bishi a hankali"

"Na gode Ya Anas"...
Ta so jin maganarsu, amma bangon office ɗin sa soundproof ne ba abinda ta ji shiyasa ta haƙura da laɓen da ta yi ta je ta zauna...
Fitan Anas ke da wuya telephone ɗin office ɗinta ya fara ƙara. Ta san shine, dan ta nan Anas ya ce za ta fi comminicating da Ogan ta.
Ba tareda wani tsoro ko fargaba ba ta amsa kiran.

"In my office now" abinda ta ji ya faɗa kenan da kakkausan murya..........



*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......


*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



*Free page*

0️⃣0️⃣6️⃣


Ta fi Minti biyar a tsaye bai ce ma ta komai ba, aiki ya ke yi ma a system na shi.

"Sir kai ka kirani kuma ka shanya ni kamar kayan wanki, idan ba abinda zan yi zan koma dan bana iya juran tsayuwa"

Ɗago ido yai yana kallonta. Lallai ma yarinyar nan, shi a tunaninsa da ta shigo office ɗin sa za ta bashi haƙuri sai ta yi ƙum da bakinta ko gaishe shi ba tayiba.

"Let me make this clear to you..."

"Sir Najeeb ka yi Hausa kawai zan fi ganewa, turancinkan nan ban faye ganeta ba. Lanƙwashe harshe ka ke kamar bature"

Bai ji mamakin maganarta ba duba da yadda ya san halinta.

" i will say this only once Miss Salihu. I do not tolerate laziness. This is an office, you should learn to behave yourself according to this company's rules. Is that clear?"

Kallon sa kawai ta ke yi ba ko kiftawa

"Miss Salihu is that clear!" Ya daka ma ta tsawa.

"Yes...yes Sir"

"Good, now get out of my office"...


Tafi minti goma ta rasa yadda za ta arranging files ɗin da ya bata, kamar da gayya aka hargitsa files su ka zama haka. Tana cikin yi kira ya shigo, ta yi tsaki kafin ta ɗauka.

"In my office now"

Doguwar tsaki ta ja sannan ta tashi ta wuce office ɗin sa.

Ce ma ta yai yana da meeting ƙarfe shabiyu. Baƙin ciki ya zo ma ta har wuya. Maimakon ya gaya ma ta da ya kira sai da ya bari ta sha wahala ta zo har office ɗin sa.

"Why are you still standing, get out?"

"Sir, na san kai Oga na ne kuma zan ba ka girman ka amma kuma wallahi ba zan ɗau walaƙanci ba. Sir daga zuwa na na yi jelen tsakanin office ɗinka ya fi sau goma. Haba dan Allah, indai saƙon magana ne idan ka kirani sai ka gaya min ba wai sai na zo har nan ba. Wannan ai salon mutum ya samu ciwon baya ne"

Ganin ya miƙe ya sa tai shiru. Har gabanta ya tako ya tsaya. " Miss Salihu, i know you are a lousy crazy girl but that should stop outside this company. Here, you are just a secretary, so work like one" yana gama faɗin haka ya fice daga office ɗin ya bar Farida baki buɗe.

"Allah ya isa na, mugu kawai. Daga ranan farko a addabi mutum da aiki kaman Jaki" ta yi tsaki sannan ta fice daga office ɗin...


...........................

Ƙarfe sha biyu saura minti biyu ya fito daga office biye da shi kuma sakatariyar sa Farida, tana ɗauke da wasu files a hannunta. Lifter su ka shiga saboda a second floor za a yi meeting ɗin. Ƙanshinsa ne duk ya bi ya cikata, ta rasa wannan ƙanshin na shi, its so inviting, so cool.

Kiiiinnnnn. lifter ta tsaya su ka fito yana gaba tana bin bayan sa har su ka shiga hall ɗin.
Kowa ya hallara a wajen dama shi ake jira. Dokar Najeeb ne lateness is a punishable offence.

Ta samu kujera kusa da mace ɗaya da ke wajen ta zauna bayan ta ajiye files a gaban Najeeb.

Duk yawancin bayanan su ba ganewa ta ke yi ba, ko dan maganar ta fi karkata zuwa ga ayyukan gine-gine da kamfanin ke yi ne...
Ƙarfe ɗaya saura minti biyar aka rufe meeting,su ka fito.

Yanzu ma bayanshi ta bi su ka haura. Sai dai ta yi laushi sosai tana ajiye files akan table ta kwantar da kanta.

Rufe ƙofar da yai ya sa ta ɗago idon ta. Ya cire suit ɗin sa, farar shirt ɗin ne kawai ajikinsa yana warware hannun rigar da alama dai alwala yai. Su na haɗa ido ya ƙara haɗa rai...

Sai da ya tafi ta fara ƙoƙarin neman banɗaki dan ta yi tsarki ta yi alwala. Office ɗin ta dai babu, ƙoƙarin fita ta ke matar ɗazu ta shigo office ɗinta.

"Assalamu Alaikum sister"


"Wa'alaikissalam, 'yar uwa sannu da zuwa"

"Suna na Munibat AbdulHamid, i'm an Engineer. Office ɗina na second floor"

"Masha Allahu. Suna na Aisha Farida, sabuwar sakatariyar Sir Najeeb"

"Na ce dama ko zamu sauka mu je sallah. Akwai masallaci a ƙasa"

"Wallahi na gode, kamar kin san abinda ke raina kenan , dama banɗaki na ke nema"...

Fita su ka yi Sister Munibat ta nuna ma ta inda banɗakin mata ya ke, sannan su ka sauko su ka wuce masallaci. Anan Farida ta ga wa su ma'aikata matan duk wanda tacewa ita sakatariyar Sir Najeeb ce sai su ce "Hmmm, Allah ya sa ki iya dan Sir Najeeb Sai a hankali"

Ita kam ba ta ce komai ba dan tun kafin su faɗi haka ta ji a wajen Yakubu da Anas.
Daga masallaci canteen ɗin kamfanin su ka wuce, su na shiga Farida ta hango Yakubu da wasu su na cin abinci dan haka ta yi saurin ƙarasawa wajen table ɗin su.

"Yaya Yakubu ka siya min abinci yunwa na ke ji"
Yakubu ya harareta ya ce " idan ba ki da kuɗin siya ki je ki karɓi ruwa, ruwa is free for all the workers here"

"Haba dan Allah, na ce ma Yayan ma ba za siya mun ba"

"Yayan ai ba na Allah Annabi bane. Na cin hanci ne"

Engr Mathew da ke gefe ya ce " sister ki zauna za'a siya miki abinci. You are our beautiful sister ai"

Farida ta je ta jawo kujera ta zauna. Yakubu ya ce "Matt, wannan yarinyar ci ta ke kamar gara ga ta da shegen son bati. Idan za ka bi shawarata ka barta ta siya da kanta idan ba haka ba kullum kai za ta maƙalewa"

"No problem, this beauty deserve to be serve like a Queen"

Farida ta yiwa Yakubu gwalo...

Su na cin abinci Najeeb da Anas su ka shigo, nan wajen yai tsit. Kai tsaye wani gefe su ka je su ka zauna inda wajene da aka tanada ɗan gefe da sauran mutane. Kujerun wajen da table ɗin ya fi sauran ƙayatuwa. Wajen cin abincin Sir Najeeb kenan, da ke Anas shi ne na hannun daman sa sai ya zamana tare su ke zama su ci a wajen.

Jin wajen yai shiru ba kamar yadda ta fara shigowa ba ya sa Farida cewa " ni kam mutuwa ce ta wuce ne? Na ga kowa yai shiru sai ƙaran sokala da fork kawai"

Yakubu ya taƙaleta ya mata nuni da ido. Sir Najeeb da Anas ta hango su na cin abinci.
Ta gane saboda Sir Najeeb ne kowa ya nitsu a wajen. Sakamakon da da ake cin abincin ana hira yanzu kam kowa abincin ya ke ci baki gum.

"Ya Anas...Ya Anas" muryarta ya karaɗe wajen.

Anas da ya ke kurɓan juice ya ajiye glass ɗin ya juyo da sauri. "A'a 'yar uwa ke ce, ya aiki"

"Lafiya yayana. Yaya wai ni an saka dokan hana magana ne anan? na ga anyi shiru"

Anas ya ce " ni ma ban sani ba amma ki tambayi Ogan ki"

Farida ta maida kallonta wajen Najeeb da ya cika ya kumbura kamar zai fashe. Ta ce " Sir Najeeb ka hana magana a nan ne??" Tambayar ta fi kama da gatse ko shaƙiyanci kuma da gangan ta yi hakan. Tashi Najeeb yai ya bar wajen. Yana fita daga canteen ɗin aka sa ihu. Wasu sai a lokacin su ka san miye aikin Farida, ta burge kowa, sai dai dayawa sun ji tausayinta dan a tunaninsu ƙarshen aikinta ya zo kenan. Harta Anas sai da yai dariya, shi kam sai da ya cinye

Please Login or Register in order to submit comment