Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

game ace har Rumaisa sai anbata....da wannan fadan da Abbansu yakewa mahaifiyarsu tabar dakin.
Kai tsaye kasa ta sauka ta amsa wayar gurin Rumaisa da yaya Abdul ke musu karatun hadisi amma Rumaisan hankalinta nakan waya saida ta mangareta ta amsa wayar danma bataso ta hadata da yaya Abdul din zama tayi nan ta turawa Abba Aliyu text ta amince anan ta cigaba da zama anan karatun da ita a zuciyarta tanajin sha'awar rayuwar gidansu dukda mahaifiyarsu ita kadai gurin iyayenta baisa sun lalatamata tarbiya ba sunbata tarbiya da suma yanzu Ummintasu ce jagaba gurin basu saida

Abba Aliyu da yakaranta text message din ya kalli Ummi Hauwa'u data fito bandakin da taje hadawa Abba Aliyu ruwan wanka yace
" kinga message (sakon)Rufaida tace ta amince"
Itama murmushi tayi tace
"Dama nasan da saninta tayi maganar munyi waya da Zainab a jiya da safe tace saurayin Rufaidan sun gaisa da yaxo daukarsu jiya da suka kwana gidanta"
"Eh dukda hakan kinsan dai zuciya Hauwah zata iya sauyamata tunani mudai yanzu fatanmu Allah ya tabbatar musu da Alkhairi ya kawar da dukkan sharruka"
"Amin ya Allah"cewar Ummi Hauwa'u

Jin karar wayar Ummin nasu yasa su gaba dayansu maida dubensu ga wayar da take kusada Rufaida ganin me kiran Yaya Abdul-Ahad be yasata rigasu dauka Yaya Abdul ya dubeta yace mata
Wai waye ne mai kiran"
Tace masa
"Yaya Ahad ne"
Ko kallan wayar bai sake yi ba ya cigaba da abinda take
Da haka ta daga wayar da Sallamarta shima daya bangaren Ahad jin muryar Rufaida a wayar yasashi amsamata sallamar da murmushi kamar tana ganinsa ta dora da gaishesa ya amsa ya dora da cewa Rufaida 'yan Candy kunyi Candy bamuzo walima ba bai karasa maganar ba Rufaida taji muryar Hajiya Jamila har kunnenta kasancewar yana zaune cikin 'yan uwansa a babban falo suna fira kamar ko yaushe
" Cikin fada Hajiya Jamila tace masa
"Ahad tanbayar Candy zakayi ko cewa tabawa Hauwa'u wayar kayimata maganar zuwanku gobe, kar a sake kwatanta waccen zuwan fa"
Ahad aje wayar yayi saurin yi Wanda atunaninsa ya katse kiran ya aje yace"Umma ki bari mana anajinki fa"
Hajiya Jamila tace "ni rufemin baki sakarai ajini mana karyanayi inba tsabar iskanci tasan da zuwanku tasakai tabar gidan itada mijinta,ni mutane naban mamaki da sun samu wata dama saisu fara manta Alkhairi duk abinda mahaifinku yayi musu sun manta shi"
Murmushi Rufaida tayi mai ciwo ta kuma kasa cire wayar a kunnents ita ta rasa menene laifinsu me suka aikatawa dangin su suke musu horon aibanta Umminsu tuni batun yau ba bayan itama mahaifiyar tasu 'yar dangi ce ita iya saninta Gwaggo kakarsu data haifi Ummnsu zaune take da kowa lafiya hakama Ummintasu amma haryau takasa fahimtar maiyasa ake cin fuskarsu ake aibatasu ake waresu kowa musamman cin fuskar da zarafin da akewa mahaifiyarsu dasu kansu Hajiya Jamila tafi yin hakan sai a lokacin tayi danasanin 'daga wayar
Jin muryar Ahad ta cikin wayar yadawo da ita daga tunaninta
"Umma sau nawa zan fadamiki fitarce ta dole har yasa muka je gidan basanan,kuma ai sun dawo kafin mutaho"
"Dallah rufemin baki mai kake nufi karesu zakayi took ubanka baka isa ka karesu gurinsa ba akan wannan maganar bare kuma ni da bana kalar dangi ka...." bata karasa jin maganarba ta katse wayar ta ajeta a gefe ta zuba ta gumi hannu biyu ta kuma kife kanta jikin hannuwan nata ita gani take babu wanda yakaisu matsala da 'yan uwansu a ranta tausayin mahaifiyar ta takeji ita kadai ce gurin iyayenta ita kadai tasa ba rayuwa batada abokan shawara sai iyayenta batada yayye ko kanne 'yan uwa kaikace mujiya CE a cikinsu idan ta shiga ko ina Hajiya Jamila ta zauna bata take cikin yan uwa suma da take basanta suke ba saisu yarda tarasa mai Ummintasu ta tserewa Hajiya Jamila gashi tunda mahaifinta ya daina jiran abashi ya daina ci da sha da sutura karkashin wani shikenan tsana da tsangwama garesu ta karu kukane ya kwacewa Rufaida
Ummi Hauwa'u data karaso falon ta karasa gurin da Rufaidan ke zaune ta dafata
"Ke Rufaida lafiya maike damunki ne"
Gaba daya 'yan uwanta suka tsaida abinda suke suka dawo gareta
Abdul yace
"Ummi daina wahalar da kanki gurin tanbayarta Yaya Ahad ne yakira waya to kila mamarsu yabawa wayar ta fadawa Rufaidan maganganu marasa dadi shine take kukan,har yau takasa dauriya akan abinda banga ranar daina shi ba kishin facala matar wa da kani to ita na mamar Yaya Ahad mai zafi ne Gwaggo tasha fadamana haka"
Murmushi Ummi Hauwa'u ta ta dago fuskarta tana goge mata hawaye
"Haba Rufaida komai fa lokaci ne wataran zai wuce gaba 'daya yanzu ina waccen rayuwartamu ta baya take da mukayi ba gata ta zama labari ba"
Gyada kai Rufaida tayi ta mike tabar falon Ummi Hauwa'u da ido tabi Rufaida ta dau wayar tabi kiran Ahad
Ahad dayake zaune kan gadonsa ya zuba tagumi yana tunanin halayyar mahaifiyarsa da baisan randa zata sauya ba yanzu yasamu ya baro mata falon ganin batada niyyar daina maganar karar wayarsa da yaji ya maida kallonsa ga wayar
Ringing biyu ana uku ya dauka cikin zullumi maizai faru a idan ya daga dan ya fahimci Rufaida taji duk irin cin mutuncin da mahaifiyarsu ta musu dukda yasan su wacece Ummi Hauwa'u ba tada maida kai ga al'amuran mutane kome zaka mata bata ko nunawa a fuskama bare kaji a furucinta suma kuma 'ya'yan nata irin halin nata gare su yadda ya zata ko hakan yaji gun Ummi Hauwa'u yaji tace
"Assalamu Alaikum Babban Yaya"
Murmushi yayi a nashi bangaren ya amsa Sallamarta ya gaisheta cikin girmamawa
Sun dan taba hira daga bisani tabawa yaran waya duk suka gaisa
Ahad bai gigin cewa Ummi ina Rufaida ba ganin cewa dama sun gaisa da haka ya katse wayar bayan Ummi Hauwa'u ta amsa wayar ya sanarmata zuwansa a washe garin da haka sukayi sallama tana cewa ya gaida mutan gidan nasu.

SADIYA KHALIL🖊️*JININMU 'DAYA*
*NA SADIYA IBRAHIM KHALIL*

*SHAFI NA ASHIRIN DA BAKWAI 27*

*MASU GANIN BANA TYPING KUYI HAKURI KUNSAN TYPING AKWAI CIN RAI WANI SA'ILIN MUSAMMAN KUMA TYPING NA LITTAFI MASOYA LITTAFIN JININMU 'DAYA RUFAIDA NAGAIDAKU ITADA DANTA YASIR DAFATAN BAKU MANTA SHIBA*😊🤔
*******
Yaya Abdul Abdul-Rashid ya kalla da suke Dining suna karin safe su duka yace mass"Yaya ban haka wani kyakkyawan labari ba munje wani boutique nida su Uncle Haris da Aunty naga wani kamarkai"
Abdul yace"nine ma mantawa kayi"yayi maganar yana hararar Abdul-Rashid
"Allah Yaya nima nida Rafi'a munga wani a mota a flyover kamar kai har Rafi'a ta masa magana"Rufaida tayi maganar da fara'arta
"Wallahi kuwa nima Yaya Rufaida har magana mukayi" Abdul-Rashid ya karasa maganar yana tari maganar da yake yanacin abinci ya kawo masa tarin
Kallonsu Abba Aliyu yayi ya soma magana
"Gashinan kaika shaqe ,bakwa tashi yin magana sai kuna cin abinci,duk fadan da ake muku bakwaji"
"Hakuri suka basa suka cigaba da cin abincinsu.
Ummi Hauwa'u kuwa ko magana batayi ba saboda sun bata haushi
Karar wayar Abba Aliyu yasa Abba Aliyu daukarta da take saman Dining ya duba mai kiran da murmushi ya dauki kiran da Alhaji Hashim ne mai kiran sai da suke gama wayar Abba Aliyu ya dubi Ummi Hauwa'u yace
" Alhaji Hashim ne maganar yaron nan saurayin Rufaida ya kira yanzu yana kofar gida
Abdul ne ya cire hannunsa a abincin ya kalli agogon hannunsa 11 saura Abba Aliyu ya kalli Abdul "din ya soma magana
" yanaga ka cire hannunka a abinci badai harka koshi ba"
Yatsina fuska Abdul yayi
"Abba na koshi ,lokacin cin abincina ya wuce indai Rufaida ce zatayi batason gamawa da wuri"
Ummi Hauwa'u tayi murmushi kana tace
"To za'adawo da duty hardakai"
"Haba Ummi 23 shekaru nake dasuba yanzu ai na girmi girki da sauran aikin gida sai kace wani dan daudu"
"nikaga tashi tunda ka gama kaje ka shigo da bakin nan kakaisu falon baki ke kuma Rufaida kije ki shirya Hauwa ki hadamusu abin tabawa a baki"Abba Aliyu yayi maganar yana mikewa yayi Upstairs
Abdul ya fito falon yin abinda Abbansu ya umarceshi.
****
Ra'uf ya dubi Mukhtar da suke tsaye jikin motarsu a kofar gidan su Rufaida
" Mukhtar kodai Ba kofar gidansu Rufaida tace kasauketa ba jiya daka kawota gida,naga nakira Ahmad run dazu kuma inada yakinin ya kira"
"A'a nan ne mujiradai mugani" Mukhtar yayi maganar yana sake kallon kofar gate din

Abdul da yakarasa fitowa daga gate din gidan Mukhtar da Ra'uf suka maida kallonsa garesa Ra'uf da kallo daya yayiwa Abdul yaga kamar da yake da Rufaida ganin yana kokarin wucesu yasa Mukhtar saurin yi masa Sallama
"Assalamu Alaikum Bawan Allah"
Abdul ya juyo da tunda ya fito ya hangosu yadai wuce ne saboda shi kwata kwata busy kwantamasa rai ba dukda yadda ya gansu tsaye jikin mota mai tsada karasowa yayi inda suke da idonsa kyar ya sauka ga Ra'uf da gabansa yaji ya fadi daganin Ra'uf din addu'a yayi ya daure yace musu
"Wa'alaikumus salam"
Hannu Mukhtar ya mika ma Abdul shima ya mika masa cikin murmushin yake sukayi musabihar Ra"uf shima cikin murmushi ya mika masa hannun suka gaisa
"Kune bakin da Abba yace na shugo daku ko"
Abdul yayi maganar
"Eh mune"
Cewar Mukhtar
"OK to bari na bude muku gate din ku shigo daga cikin"
Abdul yayi maganar yana kokarin barin wajen
Suma motar suka shiga Mukhtar ya tayar suka dannan hancin motarsu cikin gidan da Abdul ya wangame musu gate din gidan ya birge Ra'uf sosai duk da bawani mai girma bane amma ginin gidan anyi sa cikin tsari maganar Abdul ta katsewa Ra'uf tunaninsa inda yace musu
"Bissimillah ku karaso mana"
Bayansa sukabi ya karasar dasu falon baki suka shiga falon
"Bissimillah Ku zauna,bari nakarasa ciki nakira muku ita"
Abdul yayi maganar yana kokarin barin falon
Zama sukayi suna mai ce masa "to"

Da sallama Abdul ya karasa falon ya zauna kujera ya kishingi'da
Ummi Hauwa'u ta dubesa bayan ta amsa masa sallamar "badai harka kaisuba"
"Eh Ummi na kaisu,ina Rufaidan"
"Tana ciki ,yanzu zata fito"
Sallamar da Rufaida tayi yasa Ummi Hauwa'u amsawa tana cewa da Abdul kaga ta fito ma
Gurinsu ta karaso cikin shigar atamfa riga da siket da hijabinta har kasa kalar atamfar.
"Ummi saina dawo" Rufaida tayi maganar tana kallon mahaifiyarta
"To adawo lafiya ki kula da kanki"
"To insha Allah Ummi" Rufaida ta karasa maganar tana kokarin barin falon taji muryar Abdul
"Wato ni bazaki cemin Yaya saina dawo ba bakomai kyasami mai shigo mini da bakon naki ai"
"Kai Yaya" Rufaida ta karaso maganar tana barin falon da murmushinta
Shima Abdul murnushi yayi ya maida kallonsa ga Ummin nasu
"Ina ganin wani a waje tayiyuma shine saurayin Rufaidan kinsan mai naji ina kallonsa gabana ne ya fadi"
Ummi ta dubesa sosai
"Subhanallah Allah yasa dai shigowarsq rayuwarmu da Allah kawosa Alkhairi ne Amma kayi addu'a ko dan Allah kudaina wasa da addu'a"
"Amin Ummi Eh Ummi saida manayi na amsa musu sallamarsu",
" yawwa Abdul Allah ya kareku daga sharrin duk wata halitta ya shige muku gaba"
"Amin ,Ummi saidai wallahi Ummi nifa baikwantamin a raiba ma koda nagansa"
"Banasan haka Abdul addu'a zaka riqa ma kanwarka idan shi Alkhairine gareta Allah ya tabbatar da Alkhairi ya kauda fitintinu"
"Amin Ummi,karfe nawa su Yaya Ahad zasu zo ne"
"Nafi tunanin sun kusa karasowa ma dan wajen 12 zasu karaso ina tunanin don damukai waya bayan fitarka sun cemin saura kadan su shigo Kanon"
"Allah ya kawosu lafiya"
"Amin yawwa bari kaga katunamin ma bari naba Abdul-Rashid ya siyomin kabeji wanda Abbanku ya siyo Rumaisa tacemin ya kare Kunada lecture ne yau idan zama fita sai ka ajesa a bakin titi"
"Wallahi Ummi kin tunamin ma,munada ita 11 na safe zamu shiga yanzu gashi har tayi Abdul ya karasa maganar yana kallon agogon bangon falon.
" ato saikayi ka shirya"
"Yanzu fa Ummi"Abdul ya karasa maganar yana mikewa"
"Kayomin kiran Rumaisa da AbdulRashid ita takaiwa bakon Rufaida ruwa da lemon shi kuma Abdul-Rashid nafadamasa sakon da zan aikesa"
"To Ummi Abdul ya amsa mata yana nufar Upstairs.
Murmushi Ummi Hauwa'u tabisa dashi kawai.

*SADIYA KHALIL*🖊️*JININMU 'DAYA*
*NA SADIYA IBRAHIM KHALIL*

*SHAFI NA ISHIRIN DA TAKWAS 28*

*NOTE:ABDUL-RAFI SHINE ABDUL WATO YAYAN RUFAIDA.FANS INA GODIYA SOSAI*

"Assalamu Alaikum" sallamarsu Rufaida ita ta katse firar Ra'uf da Mukhtar
"Wa'alaikumus salam" suka amsa mata bakinsu a hade wajen amsawar
Jin amsawar yasata kokarin bude kofar ta tura ta shiga
Sansanyin kamshin turaren Rufaida yasa Ra'uf dago kai ya kalli fuskar Rufaida matukar kyau tayi masa a yau din kasa Rufaida tayi da kanta ganin idon Ra'uf nakanta harta tako kusa dasu bata dagoba.
Cikin girmamawa Rufaidan ta risina ta gaishesu suka amsa Ra'uf da take amsawa yanajin wani dadi a ransa najin muryar Rufaidan.
Mukhtar da ya mike yanaso ya basu guri
Yace"Matar oga Insha Allah ya gajiyar jiya"
Cikin kunshe fuska da alamun kunyar maganar Mukhtar tace masa
"Alhamdulillah ,yataku gajiyar"
"Tabi lafiya" cewar Mukhtar
"Yallabai bari in jiraka a waje" Mukhtar yayi maganar yana bude kofar falon ya fice said a Ra'uf yaji turo kofarsa ya maida kallonsa gareta
"Da alama dai gimbiyar nan tawa soja zata tafi"
Murmushi tayi kokarin zama kujerar dake kusa dashi.
Gaishesa ta sakeyi ya amsa mata cikin nuna kulawa
Shiru ya ratsa tsakin kafin Ra'uf yayi murmushi ya dubeta ya fara magana
"To ya gajiyarku nasan baki saba tafiya daga wannan state (jaha)zuwa wannan ba"
"Murmushi itama tayi
" Eh hakane amma dai ina zuwa Zaria da Kaduna lokaci guda"
Dariya ta basa
"Kinsan fa Kaduna da Zariya ai duk jaha dayane kuma basuda nisa,kunada 'yan uwa a zariya"
"Eh hakane,Mamata da Babana duk 'yan Zariya ne Nina acan aka haifeni,aiki ya maido iyayenmu Kano"
Kai Ra'uf ya gyada alamun gamsuwa da maganarta
"Ashe jahar mu daya nima dai kamar yadda na fadamiki ni dan Kaduna ne amma asalinmu 'yan Kano ne"
"Murmushi Rufaida tayi batare da tace komaiba shima baice ba dan baida tacewar shima saboda busu gama sabawa da juna ba,can ya nisa ya soma magana
" Gimbiya Rufee biki sanarmin wani abu da ya danganceki ba,vayan ni tuntuni nayi kokarin gavatarmiki da kaina"
Wani murmushi ta sake yi da Ra'uf yake hangosa kan fuskarta kuma yake ganin yana kara mata kyau kafin ta nisa ta soma magana jin sallamar Rumaisa yasa ta barin abinda zata fada sukayi kokarin amsa mata sallamar turo kofar Rumaisa tayi ta shigo da plat babba da lemuka da ruwa a ciki teburin tsakiyar dakin takaraso cikin nutsuwa ta a jiye ta tsiyaya masa lemo da ruwan a Kofi sannan ta dago.
Rissinawa tayi ta gaisheda Ra'uf ya dago ya kalli Rumaisa da alokacin take da shekaru 14 ya amsa mata da murmushi kan fuskarsa itamadai Ra'uf yana ganinta ya fahimci sunada alakar jini da Rufaidan ganin tana kokarin fita yasa Ra'uf saurin cewa
"Haba kanwata ya zaki fita hakanan bayan ko sunanki baki fadamin ba"
Murmushi Rumaisa ta juyo ta zauna kusa da Rufaida.
"Yi hakuri Yayanmu sunana Rumaisa"
"OK ni kuma sunana Ra'uf nasan da wuya yayarki ta fadamiki sunana ba ya fadi hakan yana kallon Rufaida.
Murmushi Rumaisa tayi kawa
" yace kina tsoron duka ko shiyasa bazaki bani amsa ba ko,to yanzu ya karatu"
"Alhamdulillah"
"Ya biki je ba yau"
"Anyi mana hutu bamu koma ba"
"Au namanta,Allah ya taimaka"
Daganan Rumaisa ta mike zata bar falon Ra'uf yayi kokarin tsaidata ta hanyar cewa ga wannan kya kashe indan an koma hutu yayi maganar yana zaro kudi a aljihunsa. Murmushi Rumaisa tayi ta kalli kudin masu yawa
"Tace Yaya kabarsu nagode tayi maganar tana sakai ta tura kofar falon ta fice dan karma ya roketa ta amsa"
Murmushi yayi ya aje kudin kan Centre table yana tunanin lalle bayan wannan ahalin akwai uwa tagari a bayansu da shima burinsa ya samu 'ya garesu wato Rufaida da yake da tabbacin ita dinma ta zarta kanwar tata Rumaisa
"Murmushin ya sakeyi ya dago ya kalli Rufaida
" kin hanata karbar kudina ko,nagode"
"Wallahi baruwana"Rufaida ta karasa maganar tana satar kallon fuskarsa
"Banyarda bayan ina kallonki kina harararta karta amsa"yayi maganar cikin wasa
" Ni din bani bace"
"To naji bake bace,yanzu mu cigaba da hirarmu,ki fadamin ina jiranki"
Nisawa tayi tace"
Sunana Rufaida Aliyu Bukar ,mu shida ne gurin iyayenmu nice ta biyu akwai Yaya Abdul-Rafi ne babba da muke cemasa Abdul saini daganan Abdul-Rashid,Rumaisa,Rafi'a,Ra'is shine karamin aikine ya maidomu Kano kamar yadda na fadama a baya mu 'yan zariya ne"
"Kai ya gyada da alamun gamsuwa da maganar ya gane Abdul din shine ya musu jagora suka shigo gidan amma yafi tunanin akwai tazara sosai a tsakaninsu
"na fahimceki inadai fatan nine kawai a zuciyarki babu wani,shine dai biki fadamin ba kawai
Murmushi tayi ta maida kanta kasa don batasan me zatace masa ba
Shima murmushin yayi don yanada yakinin bazata amsa masa tanbayarsa ba ruwan da Rumaisa ta zuba masa ya dauka ya fara sha
****
Abba Aliyu da ya karaso wajen aje motoci da yake azamar tafiya makaranta idansa ya sauka kan Mukhtar da yake cikin mota ya bude kofar motar mutumin da bazai iya manta fuskarsa ba saboda yayi silar taimakonsu a hanyarsu ta dawowa daga Kaduna ya mafi tunanin ko shine saurayin da yakeson 'yar tasa da murmushi Abba Aliyu ya karasa wajen da Mukhtar yake Sallama ya gabatar masa yana mika masa hannu Mukhtar ya dago ya kallesa da kallo daya Mukhtar ya shaidasa shima ya amsa masa sallamar da murmushi kan fuskarsa shima ya mikamasa hannu suka gaisa,saida suka gama gaisawar Abba Aliyu ya kallesa da murmushi saman fuskarsa
" Ashe zan iya ganeka,ya bayan rabuwa,ka tafi wancen karan bansan sunankaba"
"Wallahi kuwa yallabai bayan rabuwa Alhamdulillah,Sunana Mukhtar yallabai"
"Murmushi ya sake Abba Aliyun
" Kaine maisan diyartawa ko gaskiya nayi murna kashigo daga ciki mana Abdul baima iso bane"
Mukhtar yace
"Yallabai bani bane yana can falon bakin na barosa ni driven gidansu ne shine ma a waccen ranar yace na fito naji matsalar motarku harma yasa na kira mai gyaran"
Abba Aliyu cikin jin dadi
"Amma naji dadi sosai Allah ya tabbatar da Alkhairi bari na kira mai dakina a waya akawoma ko ruwa ne"
"To yallabai Allah ya kara girma nagode" cewar Mukhtar da ya yaba da kirkin Abba Aliyu
Waya Abba Aliyu yasa kunne ya fadawa Ummi Hauwa'u.
Yana gama wayar ya kalli Mukhtar
"Zan fita yanzu za'akawo ma yanzu"
"To yallavai a dawo lafiya"
"Amin,yawwa ya batun karatu fa kayi ne"
"Eh yallabai iya secondary na tsaya"
"OK bari na baka lambata saika kirani idan ina gida kawomin takaddunka"
Mukhtar godiya ya dinga yi ma Abba Aliyu murmushi yayi yana cewa babu komai yiwa kaine daganan ya shiga motarsa ya bar gidan
*******
"Sarauniyar mata biki fadamin ina iya karatunki ya tsaya ba"Ra'uf yayi maganar yana kallon Rufaida
" iya secondary a wannan shekarar muka yi Candy"tayi maganar tana maida kallonta kan TV
"Ki shiyo mana ki kalleni a yanzu fa nine TVnki"
"Murmushi tayi kawai
Shima murmushin yayi don yasan bazata ce masa komai ba.
Daganan ya maida kallonsa ga wayarsa ya danna Lambar Mukhtar ya kirasa ringing biyu ana uku ya dauka sakon da zai fadamasa ya fada masa ya katse wayar ba jimawa Mukhtar ya shigo da ledoji a hannunsa Ra'uf yace ya aje mata
Baijira me zatace ba yace
" ki kulamin da kanki zan kiraki anjima" daganan ya mike yabar kudin da ya bawa Rumaisa yace wadannan kuma natane bai jira me zatace ba yabi bayan Mukhtar don yanada yakinin bazata amsa ba indai bai saurin fita ba"
Jiki bakwari Rufaida ta mike ta kwashi kayan tana tunanin toda wacce wayar zai kirata tabar falon ta jawo ta rufe

******
A gurin aje motocin Ra'uf idanunsa suka sauka kan Ahad da da shigowarsu Ahad din gidan kenan yaji lokaci guda gabansa ya fadi sunan Allah ya fada a ransa yana tunanin to waye shi Ahad din yasan dai wannan ba Abdul bane tayiyu cousin's din sune.
Shima Ahad da ya dago kansa ya kalli Ra'uf yana mamakin shi waye a gidan baisan saba,tayiyu dai makwaftansu ne,ko abokin aikin Abba,da alamu dai akwai Wanda yasani agidan, hannu Ahad ya bawa Ra'uf hannu suka gaisa.
Daganan Ra'uf ya shige motarsu Mukhtar ya tayar sukayi hanyar gate suka fice da Abdul-Rashid ya bude musu suka fice
Ahad yabi motar da kallo harta fice kafin ya dawo suka yi hanyar cikin falon gidan.

VOTE☑️
SHARE☑️
COMMENT☑️
LIKE☑️


SADIYA KHALIL🖊️*JININMU 'DAYA*
NA SADIYA IBRAHIM KHALIL

SHAFI NA ASHIRIN DA TARA 29

A gurin aje motocin Ra'uf idanunsa suka sauka kan Ahad da da shigowarsu Ahad din gidan kenan yaji lokaci guda gabansa ya fadi sunan Allah ya fada a ransa yana tunanin to waye shi Ahad din yasan dai wannan ba Abdul bane tayiyu cousin's din sune.
Shima Ahad da ya dago kansa ya kalli Ra'uf yana mamakin shi waye a gidan baisan saba,tayiyu dai makwaftansu ne,ko abokin aikin Abba,da alamu dai akwai Wanda yasani agidan, hannu Ahad ya bawa Ra'uf hannu suka gaisa.
Daganan Ra'uf ya shige motarsu Mukhtar ya tayar sukayi hanyar gate suka fice da Abdul-Rashid ya bude musu suka fice
Ahad yabi motar da kallo harta fice kafin ya dawo suka yi hanyar cikin falon gidan.

"Kai kayan nan sunyi yawa aje Abbanku sai ya dawo an nuna masa idan ya amince a taba shikenan" Ummi Hauwa'u ce tayi wannan furucin
"To Ummi nima haka dai nagani ki dubi yawan kudin da za'aba Rumaisa fa"cewar Rumaisa
" kinga tashi ki kaisu dakinku ki ajiyesu dai Ummi Hauwa'u tayi firicin"
Rufaida na mikewa da kayan a hannunta taji sallamar su Yaya Ahad amsawa tayi kawai ba tare da ta juyo ba tayi hanyar upstairs(saman bene)da murna sosai a ranta ita batasan har sun karaso ba busuyi maganar da Umminsu ba yanzu"
Ahad da kallo yabi Rufaida har ya zauna Ummi ta washe baki tana musu sannu da zuwa suma su AbdulMalik duk zama sukayi suna amsawa Ummin da "yawwa"
Bayan sun gaisa da Ummi Hauwa'u
Su Rufaida suka shigo falon itada su Rumaisa da murmushi fuskarsu
"Sannunku da zuwa Yaya"
"Yawwa 'yan matan Ummi Hauwa'u"
Murmushi sukayi suka gaishesu
"AbdulMalik ya kalli Rumaisa yace
Momy wannan Rumaisan nan gaba saitafi Rufaida girma gata kuma Copy din Rufaidah"
Ummi Hauwa'u tayi murmushi kawai
Nan su Rufaida suka shiga kitchen suna jigilar kawo musu abinci
Saida suka gama cin abinci suka bude babin hira kafin lokacin sallah yayi suka tafi masallaci suda Abdul-Rashid
Suma su Rufaida sama suka koma da Wasila kanwarsu Ahad din suyi sallah
Koda su Ahad suka dawo gidan Ummi Hauwa'u suka tarar a falon tana sake gyara falon
Zama sukayi suna mata sannu da gida
"Abdus-salam yadai ko har yau baka watstsake da gajiyar tafiyar ba"cewar Ummi Hauwa'u tayi maganar tana murmushi
Abdussalam dariya yayi yace" wallahi Ummi akwai gajiya"
"To kaje ka kwanta dakinsu Abdul-Rashid mana"
Hassan yace" kyalesa Ummi ba kwanciyar da zaiyi ba wani gajiya da yayi"
Abdussalam baki ya Dan turo jin maganar Hassan din
Ummi Hauwa'u "tayi murmushi tace"kai Abdussalam jeka kwanta kayi kwanciyarka ka kyalesu yayan naka"
Tashi AbdusSalam yayi yayi hanyar Upstairs
Sukuma suka cigaba da firarsu
Da Ahad ya kasa hakuri ya tanbayi Ummi Hauwa'u Ra'uf yace"Ummi Hauwa'u dazu muka ci karo da wasu a harabar gidannan zasu fita bansan su ba ,hala makwabtanku ne"
Ummi Hauwa'u tayi murmushi
"A'a sirikinkune saurayin Rufaida ne"
Maganar sosai ta bugi zuciyar Ahad domin shi har cikin ransa tun Rufaida na karama yake sonta amma sai yau da yazowa Rufaida soyayyarsa sai gashi wani ya rigasa tabbas yasan yayi zurfin ciki
A hankali ya dawo da tunaninsa gudun kar Ummi Hauwa'u ta fahimci wani abu ya kirkiri murmushi yace
"Kai amma Ummi Hauwa'u nayi mata murna,Allah ya tabbatar da Alkhairi"
"Ummi Hauwa'u tace"Amin saura ku saika daure kafito da mata a hadaku tare ,tunda dai kayi karatu ka kuma samu aiki kaga babu abinda yayi saura yanzu"
Murmushi kawai yayi
"Ummi a tayamu da addu'a dai kawai"
"Ummi Hauwa'u tace"munayi saidai mu cigaba dayi Allah ya kawo ta gari"
"Amin suka amsa gaba daya falon
Suna zaune har Abba Aliyi ya dawo suka gaisa suka cigaba da fira
Har Abdul ya dawo suka tafi yawo dan ba aranar zasu koma Zariya ba

********
"Kai Hauwa'u kayan nan sunyi yawwa fa ko ma anfani ne da wayar kawai zatayi anfani"Abba Aliyu yake maganar da Ummi Hauwa'u ta kawo masa kayan dakinsa
"Nima haka nace saidai tunda ba suttura bace ai ba wani abu idan zatai anfani dasu"inji Ummi Hauwa'u
"Kiyi kawai abinda na...wayarsa da tayi kara yasa shi tsaida maganarsa ya dauki wayar ganin mai kiran Abba Bukar ne ya sashi murmushi ya kara wayar a kunne.
Saida suka gama gaisawa ya mikawa Ummi Hauwa'u wayar suka gaisa ta sake mika masa wayar suka cigaba da firarsu shid yayan nasa ta kwashi kayan ta bar dakin saboda ya samu damar waya da yayan nasa sosai
Wayar kawai taba Rufaida da take kwalinta Iphone ce fara da dama Rufaidan ta hangota a ledojin da Ra'uf ya kawo mata cikin zumudi ta ansa Ummi Hauwa'u na barin dakin ta cirota a kwalinta ta kunnata data sameta a saite take harda Sim
****
Ganin kiran Abba Aliyu a wayarta da Ummi Hauwa'u tayi da shigarta dakin kenan ta mike tayi dakin Abba Aliyu
Sintiri ta sami Abba Aliyu yanayi a dakinsa jin sallamarta yasa shi juyowa ya kalleta ya amsa mata

Please Login or Register in order to submit comment