Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa"amma Yaya harda Safiyya za'azo ko?"
Yace "Bansaniba kin kagara tazo kenan ko,a fara Isar mutane gida kamar gidan kallan Kwallo don hayaniya" Dariya tayi tace"ai haka yafi ni ni kadaice gidan bayamin da'di"
"Shiyasa kike damin mutane ba" Ahmad da yashigo falon shima ya nemi guri ya zauna suka cigaba da firarsu.

LIMAT SADIY 🖊️*🔗JININMU 'DAYA🔗*

By Sadiya Ibrahim Khalil🖊️
Hikima writers asso......

17
"Yakumbo gaskiya kamata yayi kiya hakuri da tafiya mu tafi tare daganan gurin bikin murmushi" Kallon Husna Yakumbo tayi da ita ke maganar kana tace" kyayi kya gama yarinya sauranma sunyi sun gama"Husna ta mike tana 'bata rai" daya daga cikin matasan falon yacewa Husna "Haba Amminmu dawo ki zauna,meye abin fushi,
Tace "amma Yaya Bello daga fadar gaskiy.." Yace "kinga kyaleta"
Yakumbo data mike tayi hanyar barin falon,dan ta fahimci bata mata lokacin yaran sukesan yi
Su AbdurRa'uf da Dady da Momy har bakin mota suka raka Yakumbo Husna ta biyosu da jakar Yakumbo tasa a gidan baya addu'a sukayi musu Allah ya saukesu lafiya suna zolayar Yakumbo"cewa ta kagara taje taga Baffa shiyasa ta damesu da saita koma 'Danbatta yau" Murmushi tayi tace"to meye a ciki tunda Ahmad yafara nuna baya auren dani tun kafin ku juyan baya harda Babban mutum da Bellotu gwara naje nima na rike mai gidana kar matanku su yimin kwace nan gaba "AbdurRa'uf yace" wato Yakumbo hardani duk yadda nake auren nan dake"Bello dake kokarin tada mota yace" Yakumbo cefa ai duk ciki indai akan Baffa ne zata iya dena aure da kowa su Dady murmushi sukeyi su dai da haka motar su tabar gidan ran kowannensu babu dadi
ABDURRA'UF JABIR MAHMUD DANBATTA
Haifaffen garin Kaduna inda aiki yakai mahaifinsa AMBASSADOR JABIR MAHMUD DANBATTA a matsayin jakadan Nigeria a India da Matarsa daya Asma'u da akayi musu auren zumunci,inda a yanzu suke da zama a New Delhi babban birnin India AbdurRa'uf yayi karatunsa a fannin likitanci ya karanci Medicine a UNIVERSITY OF MEDICAL SCIENCE NEW DELHI yanzu ya zama kwararren likita a asibitin CHAUDHARY BRAHM PRAKASH AYURVED HOSPITAL,asibiti ne babba da yake zaman kansa,AbdurRa'uf shine 'da 'daya tilo gurin Asma'u ta haifi na farko ya rasu daganan ta haifesa ta yi masa kanne wajen hudu duk duk suna rasuwa a karshe haihuwar ta tsaya mata,Safiyya a garesu kuma 'yar riko ce"Shureim Khan Salim Abokin Ra'uf ne a India tare suke a makaranta hakama a gurin aiki Shureim haifaffen dan India ne shi
AHMAD USMAN DANBATTA daya kasance Aboki kuma 'dan uwa na jini ga AbdurRa'uf tundaga yarinta har zuwa girma kasancewar halayyarsu da ta zamo daya itace takara assasa abotar dukda da tazarar shekaru daya tsakaninsu bai hana su abota ba tundaga primary har zuwa secondary da suna shekarar karshe a makaranta Jabir yasamu Ambassador
USMAN MAHMUD DANBATTA mahaifin Ahmad Kani ne ga Jabir mahaifin AbdurRa'uf uwa daya uba daya yana zaune a cikin garin Kano da aiki ya maidosa Commissioner of Police ICP yana zaune a Zaria Road da Matarsa daya Hannatu da aka musu auren gida na zumunci kanwar Asma'u ce ita Mahaifiyar AbdurRa'uf Ahmad kannensa uku shine babba sai Husna da Ammar,da Abida
Ahmad a UK yayi degree dinsa ya samu koyarwa yanzu a haka a Jami'ar Northwest

Dady ya dubi Ra'uf da suke su biyu zaune a falon Dady Usman din yace "Ra'uf hidimar nanfa tana yawa banda hidimar kayan lefe ace kuma duk yawan ahalinmu sai ka yi musu kayan anko haba ka riqa rage wani nauyin mana ,da Malika ta shaidamin ba karamin bacin rai raina yayi ba" murmushi yayi yace"Dady indai inadashi banyi muku ba wazan yiwa komai na mallaka naku ne"Eh duk da hakan Ra'uf dawainiyar tana yawa yakamata ka rage,"yace"A'a Dady idan ban mukuba babu wadanda zan yiwa" yace "to shikenan Allah ya kara budi na alkhairi ,yanzu yaushe zaka tafi Kadunan,karfa kasa Hajiya tayo takakka shalelenta yaki tahowa inda take"murmushi yayi yace" Dady kyale Hajiyar nan taku jiya fa nazo saina huta kozan tafi"Yace"duk da hakan ka daure ka tafi akan lokaci,"Yace "to", ya kuma canza Maganar da wata yace"yawwa Dady yaushe za'a kawomin motar tawa inaso nafara sanin gari kafin na tafi Kaduna ko zuwa Juma'a ne idan su Ammin sun isa can"
Yace"kai dai kace kanaso kajewa su Hajiya da sabuwar Mota kar Hajiya tace ta daina auren ko"yace"ai Dady dama na dade da sakinta tayimin tsufa"Dariya maganar taba Dady yace "to shikenan itama ta dade da sakinka saki uku," yace "anya kuwa Dady ba gashi ba ta damu naje Kaduna ba,nine dai na saketa",yace "kundaifi kusa ninakema shiga yanzu ,munyi magana da kamfanin motocin ,yau nake saran na tura Mukhtar ya taho da ita"
Yace kai "amma Dady nayi murna sosai Allah ya kara tsawan rai" yace masa "Amin" Dady yana jin Dadin addu'ar da ABDUL-RA'UF yake masa

______________
"Rufaida zanyi tafiya ta nabarki, da wannan kwalliyartaki da sai kifi awa kina yi", Abdurrafi ne mai cewa haka cikin nuna 'kosawa.



"Yaya gani nan nafito" Rufaida dake 'ko'karin karasa sakkowa daga matakalar bene tace hakan, riga da siket ne a jikinta, saikuma hijabin jikin nata har 'kasa kalar kayan, masu kalar ruwan kasa.bawani kwalliya tayi ba maiyawa dan ita sam batasan yawan kwalliya"

" Abdurrafi" da ya maida dubensa ga ummin tasu da take kujerun falon zaune yacewa, "ummi danasan kwalliyar Rufaida kenan da tuni natafi nabarta, har yau taka sa sanin samir , yanzu zataga ya kira waya yacemin an aikesa, tafi kowa sanin da'dewar littafin nan gurin Samir" ummi ce takallesa da harararsa da cewa "yanzu dama ba hidimar biki bace zata kaika sai maganar wani littafi, har kake azalzalal Rufaida ko?"

Yace "A'a ummi ba haka bane" kafin Ummi Hauwa'u tace wani abu Abdul -Rafi yayi saurin sake cewa "mudai ummi muntafi", Ummi tace "to Allah ya tsareku, karku manta da sa'kona, akuma gaida momy"


Tukin da yake ya tsaida gami da ajiye wayarsa yakalli Rufaida yafara magana, "Rufaida kinjifa samir saboda rainun wayau bama ya gida sunfita dasu momy", dariya ita abin ma yabawa Rufaida, takalli Abdurrafi, tace "yaya fa'danka da yaya Samir wake shiga", yace "wannan karon dagaske nake mun 'bata da samir kinsan ko dad'ewar littafin nan kuwa, bara muje aiken ummin saura kuma kimana kauyanci, haba yaya a shoprite din zanyi kauyanci, kamanta muna zuwa da Abba ne" yace"Au hakane"da haka suka cigaba da hira har suka isa shoprite 'din

A harabar shoprite, suka a jiye motar suka fito a tare suka shiga ciki


Jin karon da Rufaida tayi da wani abu ne da taji har 'karar abinda ke hannunsa a 'kasa yasata saurin d'ago kai,Ra'uf ne tsaye, Abinda tayar ta du'ka tami 'kamasa da hannu biyu tare da basa ha'kuri, murmuushi AbdulRa'uf yayi yace ba matsala, ya juya ya cigaba da abinda yake itama Rufaida bayan Abdurrafi tabi

LIMATU B🖊IndaININMU 'DAYA*🔗
By Sadiya Ibrahim Khalil🖊️
Hikima writers asso.....

18

___________
"Gaskiya Ahmad nayi gamo fa",Abdurra'uf ya fa'da matashin da zasu iya shekaru d'aya da Ra'uf 'din sannan ga kuma kama da sukeyi. Ya dawo kusa dashi ya zauna saman kujera dake cikin 'dakin gado wanda ada yake 'kokarin ficewa daga dakin, magana matashin ya fara yaya Ra'uf dame kuma kayi gamo,murmushi Abdurra'uf yayi kafin yasoma magana dacewa "yau ne nayi gamo da yarinya mai tarbiyya", Dariya Ahmad yayi kafin yace,haba yaya Ra'uf kasan hajiya bazata yarda ba nima kasan da yadda ta amince da samiha dai, ga uwa uba kai ga karima da takeso ka aureta, murmushi Ra'uf yayi kafin yace kai ni kyaleni da rigimar wannan matar tuni fa karima tafa'damin ita dama tanada saurayi dan kada hajiya taga laifnta ne yasa bata fa'da ba, kuma ai muddin muka biyemata har abada bazamu auri za'bin muba. Labarin ha'duwarsa da Rufaida ya shiga basa, kafin yace kurum matsala 'daya bansaniba ko tana da aure, a'a yaya kada kabari wannan tunanin kabari yadameka insha Allah ma bata da aure da haka Ahmad yamike yana fa'din yaya bara naje wajen Sagiru kan maganar dinku nan mu shima mikewar yayi yace bara naje gurin momy naje maganar da sukayi da Aunty Malika tare suka fito inda suka samu Momy Hannatu suka a falo itada Ammar da yake tayata duba wasu kaya datake zaune 'kasan carpet sallamar da suka yi yasata dago ka ta kallesu da murmushi fuskarta ta amsa musu sallamar kafin tace 'yan biyun Ammi ina zuwa haka, Ra'uf ne ya zauna gefenta yace momy kinga dai mai fitar nan ya nuna Ahmad.



Ahmad yace momy cigiyar matar auran da ya samu zanje nemo masa

"Momy tace kai fa Ahmad kafiye wasa".

Allah momy gaske nake guri Ahmad din yasamu ya cigaba da bata labari.

Sai da ya gaji yayi shiru.

Momy kuwa tayasa takeyi dan har taji yarinya r tashiga ranta da irin ko'dawar da Ahmad ke sake yimata.

Sai da yagama yafice yana fa'din momy zan gangara bakin layi gurin sagiru maganar dinkunan mu.

"To a dawo lafiya"momy ta fa'da"

Inda Ra'uf shima yacemasa "a dawo lafiya"
Ahmad yace"Amin ,ko zamu tafi tare ne"
Yace"a'a gadai Ammar ya raka ka"
Ammar ya mike yabi bayan Ahmad da yake kokarin barin falo
Momy ce ta dubi Ra'uf bayan fitarsu Ahmad tacema sa da gaske ne abinda Ahmad yafa'da kuwa
yace mata "eh momy sai dai a tayamu addu'a,tunda har yau bansan gidansu yarinyar ba,banida tabbacinma ba matar aure bace danda wani saurayi nagansu tare a shopping din"

"Tace masa" Insha Allah hakan bazai kasance zan cigaba dama addu"ar Allah ya kara haduku ya kuma sa ita Alkhairi ce gareka damu ma"
yayi kokarin kar'bewa da "Amin" yanajin dadin addu'ar Momy Hannatu har ransa
Bayan shirun wucewar wasu sakunkuna ta sake kallonsa tace masa "Ra'uf yaushe zaka tafi kaduna ne kasan ko yau dady yamin maganar Hajiya ta kirasa a waya ta masa korafin 'kin tahowar ka"

Momy gobe nake son tafiya da naje gurin budurwar Ahmad yace narakasa gobe ya kaimata ku'din kunshi da kitso da zasuje gobe, dana dawo daga can saina shirya natafi
Tace"to shikkenan Allah yakaimu lafiya",kana tace "aw namanta malika tace an kammala d'inkuna tabawa karima jiya da taje gidan ta ta kaiwa kowa nasa, har da takalman, Ta fa'damin ka kunna wayarka tanaso kuyi waya yau"
Yace "Ok momy insha Allah namanta ma tun jiya nakasheta danaga Hajiya tana ta kirana nataho Kaduna"

Momy ta amsa masa da cewa" 'kila tama tanadi ne na zuwan ka"

Ya amsa da cewa "tanadin magana ba"
Dariya ka'dan momy tayi tace "baruwa na kunfi kusa"

"Yace wane ni kune 'ya'ya ni a kare nake,Yawwa momy Ammi tafa'damiki ranar juma'a zasu zo itada Safiyya"

"Eh tafa'damin amma tace a Kaduna zasu sauka, tunda muma ranar zamu tafi"
Yace"Momy banaso Safiyya tazo bikin nan ko daya,kina sane da irin cin fuskar da take sha a gidan nan musamman a gurin Hajiya"
Murmushi Momy Hannatu tayi tace"karka damu Ra'uf,ai naji Husna tace gidan Malika zasu sauka"yace Momy "itama Aunty Malikan kinsan halinta sarai" tace"eh duk da haka amma kasan ba zata mataba"yace"Hakane" 'dazu na sayoma yaran dogayen rigunan da sukamin magana suna boot nace mukhtar yabarsu tunda acan za ayi anfani da su, Hajiya ma dasu umma danaku ammi ta fa'damin ta ha'do kayan zata taho dasu"

Momy da ta kallesa da cewa "Ra'uf baka gajiya da hidima, eh tafa'damin tace kaman to sune sanda zaka taho, Allah ya'kara bu'di ya ha'daku da masu yimuku"
Yace "Amin momy, ina husna ne momy"

Ta amsa masa da cewa" kamanta taje gidan Ummi dagacen kasan zasu wuce Kadunar tare".
Yace"Eh hakane,nima gobe idan basu tafi ba zan shiga gidan Ummin tunda naji AHMAD yace unguwa daya suke da matar da zai aura"tace "Eh haka ne"
Da haka suka cigaba da hirarsu har Dady ya shigo falon da sallamarsa yana tsokanar Ra'uf da cewa babban mutum 'dan mama babban yaya, yaushe zaka je gurin mama da hajiya 'din ne inda yakarasa maganar yana zama kasan carpet din ya jingina kansa da kujera.


"Dady sannu da zuwa,gobe nake shirin tafiya tunda an kawomin motar"

Yace"Yawwa Ra'uf Wato karkaje Abba yama dariya ko?"

Momy Hannatu anan tasa baki tace"Eh mana ina nima zanbari aima 'dana dariya a gansa da tsohon abun hawa kuma ace daga kasar waje yake ai gwara aimasa komai sabo"

Murmushi dady yayi yace "guntun gatarinka yafi sari kabani Allah Ra'uf ka daka ta mace bazaka tara komai ba ta fiso komai ita a yimata na gwaninta"
Tace"Naji dai tunda kaine ka dauki alkawarin siya masa kuma ka siyamasa shikenan"
Dady yace wa "Ra'uf kajita ko bata damu da a ina nasamu kudin siyama ba"dariya shidai Ra'uf yayi
Tace " ai saboda nasan a albashinka ka siya masa"
Dady shi dai da haka ya mike yana cewa bari na karasa na watso ruwa naga la'asar tayi na fito mu wuce masallaci"
Ra'uf yace "to a fito lafiya" ya amsa da Amin yana mai shigewa ciki

Rufaida da suka shigo gidan tayo gaba da sakon Ummi ta shigo da sallamarta sai da tayi sau biyu Amma Rafi'a batasan tanayi ba sai da yi magana da karfi tace ke
"Rafi'a ina ummi?" Rufaida ta fa'da ta na dungura kan Rafi'a 'din da da take dan na waya tana game, Sai a sannan Rafi'a ta juyo

Ta na cewa " Yaya ta na kitchen sannun Ku da zuwa"

"Bazan amsa ba" ta fa'da tana cire hijabin kanta gami da zama gefenta tun 'dazu na ke tamiki sallama kika'ki amsawa," tace"yaya ban jiki ba," Dama baza ki jiba ai waya ta dauke miki hankali ta fada fa'da tana mi'kewa


"Ummi sannu da aiki"Rufaida ta ambata, Datake 'ko'karin shigewa cikin kitchen 'din, Ummi ce tajuyo tareda cewa badai har kun dawo ba?

"Eh ummi su momy 'din duk basa gida"

Murmushi ummi tayi kafin tace wani abu

Rafi'a tashigo kitchen 'din ummi ta mi'kawa wayar ta tana cewa "ummi ga wayarki momy tana kira.

Sai da suka kammala wayar, ummi ta dubi Rufaida "tana cewa momy tace zakuje 'kunshi, Samir zai zo 'daukanki"gobe da safe


_________________________
Abdurra'uf yaushe zaka shirya ne? yanzu fa tara ta yi, Bana son tafiya ace baza'a tsireta da wuri ba", Momy ta fa'dawa, Ra'uf da yake kokarin zura takalmi ya fito daga dakinsa yana cewa momy " yanzu zan fito muje gidansu yarinyar nida Ahmad dana dawo sai na zo natafi", To shikkenan inji momy, Naga Ahmad 'din yafita kasamesa Ku wuce, Da "to "ya amsa ya fice



"Amarya samiha bata laifi kota kashe 'Dan masu gida", Ra'uf kewa kyakkyawar budurwar kirari dariya kawai tayi tasamu kujera ta zauna dake cikin falon tana fa'din "yaya Ra'uf ai sai dai idan banyi ba" ta 'karasa maganar tana mai gaishesu



"Yanzu yaron nan har goma tayi bazai taho su tafi ba yafison sai rana tayi ace za' a tafi guri vaza'a tashi tafiya da wuri ba",dady ne keta sababin fa'dan da ya shigo falon yanzu, momy tace "nima sai da na masa maganar ko da zasu fita", waya dady ya ciro a aljihunsa ya dan na yasa a kunne

Jin karar wayar tasa ne yasashi 'dauka cikin gaggawa "dady ganinan zuwa" inji Ra'uf ya katse wayan, yana mai kallon Ahmad yace "dady yana kira na nazo mu tafi",zan biya gidan Ummi daganan zan kira Mukhtar yazo ya daukeni ,"Ga ku'din kunshi nan "ya zaro ku'di masu yawa ya ajiyewa Rufaida a centre table 'din falon godiya Samiha tayi da addu'ar Allah yakaisu lafiya Ahmad ya fito rakasa

Dady ne ya kalli momy bayan ya cire wayar daga kunnensa, yana cewa "yanzu da banyi masa waya ba bai da niyyar tahowa, Amma yacemin yanzu gashi nan zuwa".


Ahmad da yaraka Ra'uf gate din gidan yace dashi"Sai munyi waya idan kun isa kaje kasha fa'dan Hajiya, Ra'uf yace "ni so nake ma naje naji fa'dan da zan sha gurin Hajiyar da kake fada".


"Gaskiya Rufaida kin 'batamin lokaci sosai, Gashi kin barni da Abdur- Rafi sai fa'da ya kemin kamar wanda nama laifi", matashin saurayin dake tu'ka mota ya anbata,

"Haba yaya Samir kasan ba laifi na bane, Kasan yau Abbi zai dawo gida shine dalilin da yasa sai da na taya ummi aiki ta 'karasa maganar dacewa fa'danka da yaya Abdur-Rafi babu mai shiga ta fa'd tana murmushi"


"Au haka ma za kice to nagode " samir ya fa'da yana cigaba da tu'kinsa

Motar Ra'uf da tafito daga layin gidan nasu Samir ya 'dagawa Mukhtar hannu.

Ibrahim Khalil Family🖊️🖊️️*🔗JININMU DAYA*🔗
By Sadiya Ibrahim Khalil
Hikima writers assoc....
19
Jin sallamar tasu Rufaida ne yasa su Samima da yaran su Aunty Samira biyu dake cikin falon rugowa gurin Rufaida suka rungumeta, "oyoyo yaya Rufaida", Momy dake daya daga kujerun falon tace, samima kar fa yarda yayar taku,ku kuma Auntynku"

Hannunsu takama ta shiga cikin falon da murmushi fuskarta ta mikamusu Biscuit guda uku suka amsa suna godiya suka shige cikin gidan

Momy ta kalli Rufaida tana cewa "maraba da zuwa Umminku da nasake kiranta harda cewa da wuri zaki zo"

Momyn tace "sai yanzu zaki taho kunshin rana tafara yi da bansa Samir ya 'dauko ki ba zaki zo ba "


Murmushi Rufaida tayi tace" haba Momy zanzo Yaya Samir ne baizo da wuri ba dan har nace da baizo ba a napep zantaho ma ,kuma na taya Ummi girki yau Abba zai dawo gida"tace"Bansaniba da nabari sai yammar sai a daukoki tunda naji suna sai yamma karfe hudu za'aje kunshin saboda yanzu mai gyaran jiki tazo,kinsan halin Yayannaku shiriritarsa ya tsaya yi "murmushi Rufaida tayi ta gaida Momy Momyn tace"Samihan tana falon baki Ahmad yazo", kije Ku gaisa



"Lallai Rufaida dama kina nan" Ahmad yace bayan ta shigo suna gaisawa,


"A'a yaya Ahmad bama ha'duwa ne"


Samiha, Ahmad ya kalla "yace haka ne"?


Kai ta 'daga masa Samihan dan itama fushi take da Rufaida take ranar Laraba da sukayi bikinsu guduwa tayi tabi su ABDUL-RAFI gida

Ahmad yace " kin fitar da ita"


Sun 'dan ta'ba hira kafin , Rufaida ta fice daga falon bakin ta koma ciki dakinsu Rufaida ta shiga tasamu Yaya Saudat a ciki da ake mata gyaran jikin amare da ita suka cigaba da hirarsu sai mai gyara da take sa baki a wata hirar ,Shigowar Samiha yasa mai gyara fara yiwa Samihan ta aje musu rafar kudin da Ra'uf ya bata tace"Yaya Saudat gashinan ayi lissafin abinda ba'asiya ba ko sunyi kadan sai aba Driver ko Yaya Musa ya karo"Saudat takalli kudin tace"yanzu duk Ahmad ne yabada wa'dannan kuda'den masu yawa ,ke Samiha ba kya tausayin Ahmad ko "tace" A'a yayan sane ya bayar ,amma shima idan ya bayar ai dolene tunda shi ya tattago yin auren,komai sai kice a riqa tausayawa haka ma kike cewa Yaya Mujahid kenan,bakisan maza ba anuna ana tausayinsuba kusan duk basu da halarci"Murmushi Saudat tayi kawai tace"ke matsalarki kenan a fadamiki goma ki fadi dubu"Rufaida tace"wallahi Yaya Saudat haka take"Samiha ta harari Rufaida tace to aiku gaskiya ne bakwaso a fada"abunda yakamata a siyo ba asiyo ba suka fara rubutawa da yamma suka tafi gurin kunshi da suke saran tafiya Sakoto da asuba saboda daurin auren da za'ayi a can ranar Lahadi da zasuje ana i gobe biki da ranar Laraba sukayi hidimar bikinsu da kawayensu abokan karatunsu maza da mata da angwayen babu wanda yaje dan sai bayan bikin da sai ankai amaren angwayen zasu hada Dinner kowa da shi da Family dinsa banda ma ahalin matan nasu sai tsinta tsinta Saudat cema za'ayi dana ta 'yan uwan kasancewar ita auren zumunci auren gida za'ayi musu ita da Mujahid din nata

ABDURRA'UF ya 'dan duba gefen titi da suke tafiya ganin mota a tsaye gefen hanya yace"
Mukhtar dan duba Kaga kamar mota na gani a tsaye?ya kamata ka fita kaji lafiya,ni a gajiye nake na dade rabona da tafiya a mota mai nisa"Murmushi Mukhtar yayi ya maida dubensa wajen da Ra'uf yanzu na masa yace "eh nima naganta, Sai dai kuma kana ganin ba matsala Idan mukayi haka, Duba da yadda rayuwar ta zama a yanzu"

"Eh babu komai insha Allah sai Alkhairi tunda niyyar taimako mukayi,Allah zai dubi zuciyarmu"

Abba Aliyu wato mahaifin Rufaida ne a motar yana kokarin kiran wayarsu Abdul-Ahad da Abba Bukar ya sanarmusu fashewar da tayar motarsa tayi yanzu ko za'asamu mai gyara daga Zaria suzo a tafi da motar da yake ta kiran wayar baya samu Network ya hana ta shiga ,gefensa da ABDUR-RASHID ne da ya biyo ta Kaduna ya dauko ABDUL-RASHID daga gidan ZAINAB Inda mukhtar ya karasa da sallama a bakin sa , Da murmushi ya amsa masa sai da suka gaisa ya kuma mi'kawa ABDUL-RASHID hannu sukayi musabiha, inda mukhtar ke tanbayar ABDUL-RASHID sunansa,ABDUL-RASHID ke shaidamasa sunansa Abdul-Rashid.

Kafin mukhtar yace ma Abba Aliyu "yalla'bai mai ke faruwa ne naga kun tsaya a gefen titi ko wani kuke jira

yace masa" a'a ko 'daya tayar mota tace ta fashe muna baro cikin garin kaduna yanzu gashi banida wanda na sani mai gyara a cikin Kadunan,kuma banida safayar taya nakira Number din wanda nasani taki shiga "

Mukhtar ne yace"Allah ya kara kiyayewa bara nazo"
"ya amsa da amin, to nagode"

"Mai ya faru ne mukhtar" inji Ra'uf

Mukhtar yace"tayarsu suce ta fashe"

"Subhanallah ka kira mai gyara bai kamata a barsu a tafi ba, ga abinci ka mikamusu" Abdur-Ra'uf ya fa'di haka tare da mi'kawa Mukhtar abincin dake leda mai 'dan girma

Sai da mai gyaran yazo yayi gyaran suka 'karasa kaduna inda Abba ALIYU ke ta Sanya Albarka a garesu tare da addu'oi ma banbanta



"Maraba da zuwa mutanan kasar waje" Hajiya take fa'da da murmushi da ya nuna har a saman fuskarta


Mama ce da Yakumbo suka 'karaso falon suna nuna murnar ganinsa

Inda shi ko Ra'uf yayi 'dai 'dai a kujerar falon yana maida gajiya dan agajiye yake tibis yasha wahalar tafiyar


Yakumbo ta ce "wato Hannatu ta ri'ke ka sai yau kataho ko?" ta fa'da tare da 'kara sakin murmushi fuskarta

Hajiya tayi saurin karfe zancen da cewa "ahaf ai nasan za'a rina taya zan yarda da maganar ki suwaiba ace har yaron nan yayi sati biyu kice baije gurin hansatu ba, Ai nasan da cewa nice bakwa 'kaunata"

Mama ce mai cewa haba "maman jabiru ai kinsan da yaje gurin hafsatu ba ta yadda za'ayi ki'ki sani tun jiya da su Lamido suka fara isowa"

"Suwaiba babu ruwanki tun da kinfi kowa sanin abunda yaran nan nawa suke yi min duk akan 'ya'yen Hassatu yanzu zaki zomin da wata gulma"

Kafin ta 'kara cewa wani abu gaba 'dayansu suka bar falon

Suwaiba ta dubi Yakumbo tana bata ha'kuri "Hansatu kiya hakuri kema kinsan halin yayarki muyi ta yimata addu'a Allah ya shiryeta"


"Insha Allah ,amma Halayyar Yaya Hanne, Maman Hamidu badai zance komaiba tunda kince Allah amma abu tunda jajayen sahu ake har zuwa yanzu bata canza ba" inji Yakumbo wadda ita gani take abinda 'ya'yen nata ke ma yayarta ta basa yimata sai dai ita bata gani, Kullum gani take ita ake yiwa batun yanzu ba tuntuni yayarta ta ke ganin haka , kuma ita ina taga Ra'uf 'din da idanunta banda zuwan da tayi ranar da zaizo 'kasar da guntun hawaye ta 'karasa shigewa wani 'daki


Shiko Ra'uf kai tsaye 'dakinsa ya shige yanajin shigowar wasu mata falon da suka tarar da banbamin da Hajiyar keyi da cewa "Ai ni dai na kwari kaina da na ha'da zuriya da Hansatu duk an mallakemin 'ya'ya ba jabirun ba ba usman 'din ba Zuga Hajiyar suka shiga yi 'daya a ciki nacewa "Hajiya ai tunda kika bari 'ya'yanki suka auri 'ya'yan Hansatu ai sai dai kiyi ta addu'a
Dan kuwa----"

Da wannan Ra'uf ya shige cikin daga cikin dakinsa da yake cikin falon ,bai karasa jin maganarsu ba,da baya ma kaunar jinta wato har a gabansa ma maganar mahaifansa za'ayi saboda a nuna isa da fifiko akansa shida mahaifan nasa ,dafe kansa yayi da ya ke matu'kar sara masa, Bai ko tsaya watsa ruwa ba ya fada gado yana danna wayarsa, Sai da yaga kiran momy ya katse yabi kiran suka shiga fira yana bata labarin abubuwan da suka faru bayan zuwan sa Nasiha ta dinga yi masa data sanyaya zuciyar Ra'uf sosai

Jin bu'de 'kofar tare da yin sallama yasashi saurin tashi zaune ganin mai sallamar da yake jinta tamkar Ammi da Momy a zuciyarsa,Ga ma kuma kamannin da takeyi dasu,Ba wata bace illah Yakumbo,Sakkowa yayi daga gadon fuska dauke da Fara,a yana kar'bar 'katon farantin hannunta yana cewa"Kai Yakumbo irin wannan kayan sai su ya dake ki jawomana cinya"

Dariya Yakumbo tayi tace "Su dai bello sayi badai kaiba"

Ra'uf yayi murmushi yace "To ni 'din gunma indiya zamu tafi har ki warke"

"Allah ya 'kara kiyayewa" inji YAKUMBO, Ra'uf ya amsa da "Amin dai yakumbo"

Abincin ta shiga zuba masa Inda take sanar masa ita tayi girkin Dan shi ka'dai kawai


Ra'uf

Please Login or Register in order to submit comment