Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fa bandama shirme irin naka ina zaka hada Ruqayya da Rufaida kodai kai wawane sai haka tuntuni nake nunama banbancin dake tsakaninsu"AbdulMalik yace"haba Umma ni haryau bana ganin banbancinsu a zahirin gaskiya ma Rufaida tafi Ruqayya dangantaka da gidannan ta kowacce fuska gaskiya"Hajiya Jamila data fusata tace" to yima Ruqayya gori cewa tazo gidanku cin arziki arzikin da duka yaushe ubannaka yayi kuma kasani komai zakace idan ni kahanani fa'dar banbancin dake tsakaninsu to bazaka hana duniya fada ba,abinda bakowanne biladama zai iya ba saiga wancen matsiyacin yayi da kuma waccen...."AbdulMalik ganin Ummantasu bazata tsaida wannan cin zarafinba yasashi harda saurinsa dan yasan indai zai biyemata tone tone zatayi abinda yasan yana daga cikin kaddarorinsu to akanme za'a dinga jagwalgwala magana dashi haryau yake tantama ga waccen labarin kanzon kuregene da saboda suma suji waccen tsanar kamar yadda ita kiri kiri take nunawa ga wancen rayukan masu matukar muhimmanci a rayuwarsu tabasu labarin da babu kamshin gaskiya a ciki dukda dai mahaifiyarsu ce tabasu,to shi koda ma hakanne shi baiga abin da zaisa yaki 'yan uwansa ba danshi yama jahilci labarin tunfarko kodama gaske ne,Rufaida da take kokarin shigowa falon ta fadawa Hajiya Jamila ta gama abinda tasata mai zata kara dorawa a kunnenta ta fara jiyo maganganun Hajiya Jamila da yaranta data fahimci akanta ake maganar bata karasa jin maganar b takoma kitchen din gudun kada AbdulMalik yazo yasameta anan da haka yasata komawa kitchen din dukda bawai tsaiwar ta gulma bace a'a kowa 'dauka zaiyi itace tana kuma tsoron Hajiya Jamila taji Abdulmalik ya mata magana ta zata ra'be take musu shikenan kuma abin ya zama abin magana a gidan tarasa wannan wanne labari ne kuma wanne tarihi ne dayake shafar rayuwarta har yakawo tsanar da Hajiya Jamila a duk cikin zuriyarsu sai tace tafi nuna musu dukda ita 'din ba zuriyarsu bace kai tsaye a'a aure yakawota zuriyar tasu amma tasan abune babba karon farko ta fahimci shine ya raba wancen ran mai muhimmancin gaske a zuciyarta shine yajawo tafiya mai nisan gaske a tsakaninsu da haryau babu waiwaye,tanbayar zuciyarta take yaushe zatasan labarin waccen rayuwar ta baya da tasan tabbas itace rusa waccen rayuwartata kuma take cigaba da shafar rayuwartata dumin da taji a kuncinta yasata sa hannu ta duba abinda tasan tabbas shine dama ta gani wato hawaye ,tuno waccen rayuwartata dama wadda takeyi yanzu shine abunda a kullum yaake kokarin da gula lissafe lissafen rayuwarta dama tunaninta kai tsaye zama tace Sallamar da taji AbdulMalik yayi kitchen din yasata saurin daidaita nutsuwarta ta goge hawayenta kafin ya karasa shigowa amsa masa sallamar tayi yayi murmushi ya karasa inda take tsaye tana kokarin cemasa "Yaya sannu da zuwa"Ya amsa da" yawwa Rufaida"kafin ya'dan ha'de rai yace "Rufaida"ta amsa da " na'am Yaya"cikin muryar raunana ta amsa masa"ya sake murmushi karo na biyu ganin yadda ta ru'de dagajin kiran sunanta yana mamaki haryau Rufaida bata canza ba daga yadda take,dukda gata da 'da harma ya kusa shekara uku ita kanta a shekaru zata kai 22 a yanzu haka koma da uku amma haryau yarintarta ta rashin son hayaniya da shiga abinda bai dameta da hakurinta yana nan yadai fahimci wannan halayyar a jininta suke"magana AbdulMalik ya cigaba dayi da cewa"yanzu Rufaida Fisabilillah dukda matsayin da kike dashi a gurin mu kinada wata bukatar ta wani abu kudi ko abinci ko abinsha ace bazaki tanbayemu kai tsaye ba muyi miki ba sai kin cemin zakimin transfer haba Rufaida duk abinda muka miki aike din tamuce bama bukatar ki bamu abin hannunki,muddin muna dashi idan bamudashi mumasu tsaya miki ne da karfinmu,bare ina tunanin dubu 2 zuwa uku ko ma fiye da haka ko Abdussalam kika tanbaya ko Hassan ko Hussain ba zata gagare suba haba Rufaida tuntuni kinsan kina bukatar wani karamin abu wato caza danni dai a a karamin abu na dauketa dan inada ita kamar abin banza a dakina tunda nasan zata kai 4 ko 6 duk wayoyin da nayi da caza dinsu a dakina ace bazaki ce na baki ba ko Umma da kike gudun taji kinsan ba zata hana na bayar da abuba tunda kinsan bata hana kabayar da abu bare ma kinada lambar Iowa a gidannan name tunani haba mana ki zama wayayya ta wasu fannonin mana"Rufaida da sai yanzu take ganin laifinta ne dan ita kanta amsar dalilin da zata fadawa Samiha Idan ta sake kiranta jin dalilin kiran nata bata samuntan bazatama iya fadar wancen dalilin ba dan baikai matsayin ka fadawa wani ba tunda akwai hanyoyi da dama na magance waccen matsalar,sai dai ita dalilin kin maganar gani take kamar zata matsawa mutanan gidanne kaita cewa ayima ayima ko abani abani ita bata saba dashiba mijintama da yarasu bata yimasa,bare tayi anan da surikartata bata raina abin magana ,Rufaida tace"Yaya kaya hakuri na daina"yace "Yawwa shikenan ina Yasir din ne ga alewa nan na siyomasa" Rufaida tace" yana can gurin karamar Auntysa Ummu kursum yana mata wasa"AbdulMalik yace "ok to ga naki sakon nan" ya bu'de ledar ya dauki wata ledar ya aje mai dan girman yana cewa bari nakaiwa Yasir nashi"Rufaida tace" Allah ya kara bu'di"AbdulMalik yace "Amin"kafin yace "au na manta ina Inna Lamin" wato mai tayasu aiki Rufaida tace "taje gidan Gwaggo Lariya" AbdulMalik da ya gane Gwaggo Lariyar kanwar kakarsu ce mace yace"lafiya dai ko"Rufaida ta visa da cewa "lafiya lau abincinta ne ba'a kai mata ba har 'yan makaranta suka tafi"yace mata "Ok ", da yasan halin Ummansu Hajiya Jamila sarai ko 'ya'ya zasu fasa gidan indai Inna Lami na gidan aiken duniya ita zata yiwa kaikace Inna Lamin sa'ar tace a haifema Inna lami ta haifi Hajiya Jamilar amma nuna ikon Hajiya Jamila kamar kanwar kanwartama ta maida Inna lamin sai kace ita ta bawa kanta daular da take ciki ba Allah ba itama Inna Lamin sai Allah ya bata Iran yaso hakan da haka yake cigaba da tunanin halayyar mahaifiyartasa datayi sanadiyyar kawosa duniya ,yana kokarin ficewa yaga Rukayya tsaye a bakin kofar kitchen din da Hajiya Jamila tace ta biyo AbdulMalik taji neman maiyakewa Rufaidan ha'de rai AbdulMalik yayi daya ganta cikin rawar jiki na nuna alamun rashin gaskiya tace masa" dama Umma ce tace na samo mata ruwa a kitchen"tsaki AbdulMalik yayi yace" tanbayar ki nayi abinda yakawoki koko yaya?" Rukayya kai ta girgiza alamun a'a wucewa AbdulMalik yayi Inda yana kallon Ruqayya ganin ya tafi yasata bin hanyar komawa falon danko kitchen ma bata waiwaya kai kawai AbdulMalik ya girgiza yana tunanin halin mahaifiyarsa mara kyau wato bata yarda da su ke'be shida Rufaida ',year uwarsa suyi fira ba sai ta sa anjiyo mata,ita batasan shi baya gudun fadan gaskiya ba koma gaban waye ba shifa aransa cewa yake baza'a masa abinda akayiwa yayansuba ya yarda yanzu za'ayi kaca kaca dashi danshi bazaiyi biyayya gurin abinda zak cutu ba kuma za'a cutar da abinda yakeso ba shiyasa yake da kudure kudure aransa da yasan bamai yunkurin hanasa tunda kudurin vamai cutarwa bane da haka ya karasa sashensu da sai ya kammala abinda take zai fito kaiwa Yasir alewarsa

Ganin Ruqayya na waigegen bayan shigowarta falon dako sallama babu dan duk adabirce take yasa Hajiya Jamila tanbayarta"ke lafiya "Ruqayya da saida ta zauna a kujera tace" Umma ai Yaya AbdulMalik ne ya kamani ina musu la'be"Hajiya Jamila tace"to saime ince dai ba dukanki yaiba ko?"Ruqayya tace"a'a bai dokina ba,Gaskiya UMMA Yaya AbdulMalik baida mutunci matarsa zatasha wuyar zama dashi kafin tasan halinsa kai kodama tasani idan ta sake ta kuskure masa zatasha bala'i da masifa kings ko yadda yayi min yanzu" labari ta bawa Hajiya Jamila"Hajiya Jamila tayi murmushi tace"to kuma dake zamu aura masa"Rukayya ta zaro ido tace wa waini Umma ko wata dai?indai dan ta nice na yafe akai kasuwa dama dai waccen da yake nuna alamun yanaso Rufaida kika barsa ya aua kodan tasha wuyar sama dan in inbama itan da yakeso ba dawa yake zama yayi magana ta da'din rai mai tsawo sai dai ko Abba dan koke indai yaji kinsa abinda bai masa ba a hirar tuni yake tashi"Hajiya Jamila da ranta ya soma 'baci da maganar Rukayya tace mata "keni rufemin baki tunda kince bazaki aure sa ba saiki bar maganar ,sai shigo da yarinyar da kuke da banbanci maiyawa tsakaninku" Rukayya ta 'dan yatsina fuska tace haka nefa"amma 'kasan ranta addu'a take Allah yasa AbdulMalik ya aureta kodan tasha wuyarsa dan ita gani take ma tafi Hajiya Jamila tsanar Rufaida da kishi da ita tunda ta auri masoyin da taso take karaso har yau wato AbdulAhad shiyasa duk wannan tsanar da take nunawa Rufaida bata shafi Yasir ba dan har wayarta basa take yayi game da take ganin Yasir din kamar AbdulAhad dan ita kanta Rukayya batayi tunanin tanasan AbdulAhad har hakaba sai bayan rasuwarsa ta fahimci haka dukda dai kiyayyar da yake nunamata a fili amma tunaninta data samu ta auresa zai daina anata ganin kenan Hajiya Jamila ta katse shirun da cewa "ni waima na tanbayeki Rukayya wa Rufaida tace ya hanata saka caji nifa shiyasa kin ganni nan banasan zaman ire-iren Aliyu da Hauwa'u a gidan nan indai neman gurin zama ne sun iyashi an musu lecture dinshi" Ruqayya da maganar Rufaida ta fara isarta dan ita duk abinda bataso batasan aita surutunsa kai ko ma dason abin take batasan a dinga damunta da maganar baki ta ta'be tace"Umma bara na 'dauko wayata"daganan tasamu damar tserewa tabar Hajiya Jamila a falon da tunda gari ya waye ko tsinke bata daukaba bare ta wanke ba dukda ranar girkintane ga bayinan tasamu Rufaida da Inna Lami,da sanda ba Rufaida bata gidan wannan bautar ta Inna Lamice sai taga dama sukeyi tare idan taga an kuskure mata ta fara fada kaikace cinye mutum zatayi 'danye

Rufaida jin shigowar Inna Lami ta kofar kitchen wadda take ta baya bata falon yasa Rufaida yi mata sannu da zuwa, Inna Lamin ta amsa da dan murmushi fuskarta tace "yawwa Rufaida kinsha wiki Rufaida yakamata kije ki huta ai tunda na dawo" Rufaida tace "haba Inna keda kikasha tafiya ai gwara kibarmin aikin tunda saura karashe shima don baki fadaminba zan tanbayo Umman Yaya AbdulMalik ya shigo kitchen din" Inna Lami tace Allah sarki amma dai kibari na karasa tunda kinga ni aiki name"murmushi jin maganar Inna Lami tayi tana tausayin Inna lami ta fara tsufa amma tana wannan wahalar ta yiyu rashi garesu shine ya janyo hakan kuma sai gashi ta ha'du da muguwar uwargijiya Hajiya Jamila tunda dai kusan aikin gidan da take kusan natane kuma Hajiya Jamilar ce ta samo ta,Rufaida da bayarda ta iya ganin yadda Inna Lamin take ta roqonta da take ji ba dadi ace babba na rokarta da haka yasa Rufaida bar rmata ragowar aikin kayan da AbdulMalik a siyomata ta dauka ta yi hanyar dakinta.


SADIYA IBRAHIM KHALI✍🏽*JININMU 'DAYA*
HalimatusSadiya Ibrahim Khali
(Sadiya Khalii)
Page9
Dady da ransa yakai makura gurin 'baci ya soma magana cikin bacin rai yace"Ra'uf abinda kakefa ya fara isata kace bazakayi aure yanzu ba na hakura na qyaleka yanzu kiri kiri ka nuna bazakaje gurin danginka ba Nigeria so kake kayafe zuwanta gaba daya shekarunka nawa da daina zuwa haba Ra'uf yanzu kai sai wani yayi ma fadan abinda yakamata kayi yanzu"

Ra'uf yana mamakin fadan Dady akan abinda baikai yakawoba dan kawai yace bazaije Nigeria ba,toma shiko mai zaiyo a Nigeria a yanzu haka yake jin kansa kasar da aka saka masa ciwan da yake damunsa har yau da yasan duk sanda zaije wannan mikin sashen rayuwartasa zasu kara tuno masa abinda yake da tabbacin ku'di martaba duk ahalinsa suna da shi mai kuma yayi saura da har zasu rasa Samar masa farin cikinsa dan shi a yanzu ma koda zaije Nigeria ba wai don waccen rayukan zaijeba sai dai dan rayukan da duk sanda ya kwanta yake tuno su

"Ra'uf ya takaita tunanukansa yace "a'a Dady kaima kasan yanayin aiki ne yake hanani zuwa Nigeria" Dady da ya'dan sassauta murya yace "ai kai ne agogon sarkin aiki dama,Ra'uf ko ka'ki koka so bakada kamar mahaifarka ko ta iyayenka amma Yaro ace kiri kiri kaki kasarka duka duka zuwannaka Indian duka yaushe"

Ra'uf ya dan kara gyara muryarsa ya nutsu gurin fa'dar cewa"a'a Dady kaima kasan banda yanayin aiki babu abinda zaisa nace bazanjeba"tsaki Dady yaja yace"nikaga kakiyayeni da wannan dadin bakin naka kamar mace,tunda bazaka ba shikenan zanje da Safiyya kawai"shiru Ra'uf yayi yana tunanin halin da Safiyya zata shiga idan aka tafi da ita dan bawai sabawa tayi dasu ba sabodahantarar Safiyyan da suke yi shiyasa babu sabo tsakaninsu wannan shine abinda yasa ma bayasan zuwan Safiyya kwata kwata cikin zuriyar tasu",ya ce "amma Dady a kano za'a bar Safiyyan ko?" Dady da ya gane wancen tunanin nasa sai kawai ya share yace"kamar ya na barta a kano,ita bazataje cikin dangintaba a yanzu haka tanada kamarsu ne fadamin?"Ra'uf yace"a'a Dady"Ra',uf ya sauya maganar da cewa yanzu ranar yaushe zaku tafi?"Dady yace"sai zuwa wani satin nake tunani"Ra'uf yace"to Allah ya kaimu lafiya zan bada sako akaiwa Momy Hannatu"murmushi Dady yayi"yace toni tawa Momyn fa"murmushi shima Ra'uf yayi yace"ni fa tawa Momyn kawai zanyiwa kowa yayi wa momynsa"dariya Dady yayi yace"shikenan tunda abin 'yar hakane"Dady yace "yawwa Ra'uf kunyi waya da Malika kuwa ta fadamin akwai sa'kon da zaka bani na tahomata dashi" Ra'uf yace"Eh Dady ita Safiyya zanbawa sakon ta bata" yace to shikenan dadai haka suka cigaba da firar duk dai akan tafiyar har zuwa wani lokaci"

Dan Allah kuya hakuri kuyi maleji✍🏽

SADIYA KHALI✍🏽*JININMU 'DAYA*

By Sadiy Khali

10
WAIWAYE

Ajin da ya hargitse da surutu kasancewar babu malami 'daliban wasu duk suna saman benci kowa surutu yake maza da mata ko ina an hada group group Rufaida da Samiha da suka hada rukuni na musamman su da suke a gaban layi jin Sallamar Class masters su yasa kowacce daliba rugawa cikin kiftawar ido bencinansu dan sunsan halin Sir Nura wato class mastern su amsa masa sallamar sukayi ya shigo shida wani bakuwar fuska da zai kusa tsarar Sir Nuran ne kallo 'daya Sir Nuran yayi musu ya fahimci basuda gaskiya gashi nan sai kokawa suke gurin gyara zamansu a benci kuma sunayowa birandar ajujuwan sukafara jiyo surutu kuma yasan daliban ajin nasa ne dan yasan duk sunfi rashin ji saidai a ajin bazaice dukansu ba amma dai ana masa kuka da ajin koma malamai,Sir Nura ya 'dan hade rai yana amsa gaisuwar da daliban ke musu shida sabon malamin bayan sungama ya kalli duk daliban ajin kafin ya nunamusu mutumin da suke tare yace"Wannan sunansa AbdurRahman shi 'dalibine a jami'ar BUK yazo Teaching practice yana shekararsa ta Uku a matakin karatu Yana karantar Biology Education yanzu haka...."yana cikin maganar ya jiyo sautin muryar wasu daga cikin daliban tsayawa yayi da maganar yanasan jiyo muryar su waye Rufaida da 'kafa take ta'bo 'yan bayan layin nasu da sune suke surutun alamun suyi shiru amma babu wacce ta fahimta Sir Nura da yagane Su waye masu surutun da busu sam ma yayi shiru ba Sir Nuran hankalinsu nacen wajen hirarsu ya kira sunayensu "Hauwa'u Umar ,Nasiba Abubakar,Ku fito waje Ku fadamin mai kuke fa'de" Cikin rawar jikin suka fito su biyun suna ayyano hukuncin da Sir Nura zaimusu dan baida mutunci ko 'daya a gaban allo suka tsaya suna kukkushe fuska,Tsawa Sir Nura ya dakamasu yace"wato saboda kun raina malamanku ina magana kunayi ko? Kuma bako ma saikun nunamasa halayyarku, to kufadamana muda sauran 'yan aji mai kuke cewa"hakuri suka shiga basa shi kuma ya kafe akan sai sun fadamasa mai yake cewa"nan Nasiba tace Sir cewa nayi sabon malamin da aka kawomana Yana kama da Yayan Rufaida Aliyu Bukar shine Hauwa'u Umar tace itama taga kamar"tsaki yaja Sir Nura bayan ya gama ji yace"Nasiba wato rashin mutuncin naki haryakai ina aji na kawo sabon malami kintafi can yimin hirar kamarshi da wani kin dauke hankalin masu San gane inda maganartawa ta dosa,yanzu haka ma ba haka kikace ba?"Nasiba tace wallahi Sir haka nace,kuma Hauwa'u kawai na fadawa yan aji da sunajin diramar da ake wasu Allah ya kara sukewa Nasibar dan dama duk tafi 'yan ajin rashin kunya da raina malamai da kyar ma idan hakan tace ba fara sawa malamin sunan banzan da dalibai suke sawa malamansu ba to yau ta hadu da Sir Nura dan sunsan yau Allah ne kadai zai kawo silar kwatar Nasiba daga hannun Sir Nura dan bashida mutunci bazai rangwantamata ba Sir Nura yace "su fita waje su tsaya harya fito sukarbi hukuncinsu"karasa maganar yayi da cewa shine zai riqa daukarsu Biology da ayanxu basuda malamin ya tafi karo karatu Sir Nura ne ya fito daga ajin yabar AbdurRahman yana musu tanbayoyi don yaji daga ina zaifara kasancewar dalinan SS3suke sune masu fita a shekarar Sir Nura yana fitowa daga ajin Sir ya kali su Nasiba yace" sakarkaru kawai da bususan darajar malamansu ba bako ma yazo saikun nuna halinku na rashin mutunci tun ba'aje ko ina Ba"nuna Hauwa'u Umar yayi yace" wato kema ina ganinki mai mutunci ashe kinbi sahun wannan sakaryar kawartaki"Nasiba da ranta ya fara 'baci kan kawai tace Sir AbdurRahman yana kama da Yayan Rufaida za'abi a fara cin mutuncinta ita sai yau ta kara tabbatar da rashin mutuncinsa yakai haka ita dai ana cemata"Acid and Base baida mutunci,sunan da aka sa masa kenan saboda tsabar rashin mutuncinsa a makarantar juyar dakai Nasiba tayi tana harare harare ya dakawa Nasiba tsawa da cewa "juyo ki kalleni mara kunyar banza wadda bata da tarbiyya cikakka" AbdurRahman da ya fito daga ajin yace masa Dan Allah ka kyalesu haka daganan Sir Nura ya kyalesu yayi gaba AbduRahman ya dubi Nasiba yace "yanzu abinda kuke baidace ba malami yana magana kuna magana bazasu bari yakai sakon da yakesan isarwa ba yanzu girmankune ace anfito daku waje ana ci muku mutunci bayan kuma duk kune kuke jawa kanku baza kuyi abinda malamanku suka ce kuyi ba" Nasiba tace"Wallahi Sir ba karya muke ba kuna kama da yayan Rufaida A Bukar"AbdurRahman ya girgiza kai ganin su bama tunaninsu sunyi laifi ba yace" waye muke kamar ne " Nasiba tace"wallahi Sir wani yayan 'yar ajinmuce muce Rufaida A Bukar "AbdurRahman yace"a'ina yake fa"Hauwa'u cikin zumudi tace Rijiyar Zaki farko mun dauka ma zakace mana kai 'dan uwansa ne"AbdurRahman yace"Allah sarki a'a kawai kama ce kinsan Khalid Bashar Majiya?"suka cemasa"A'a Sir akwai dai wata 'yar ajinmu a unguwar da yake take kai 'dan sane?"AbdurRahman murmushi kawai yayi batare da ya basu amsa ba ya 'Dora da cewa "amma zanso na ganshi mai kama dani 'din na gani ko haka ne"su Hauwa'u ganin karsu kuresa yasa busuce ya amsa musu ba dole dan daganin AbdurRahman 'dan manyen mutane ne kuma ga sunan mai kudin da aka sanshi sosai tunda manyan kamfanunuwa garesa ya kuma ce ko sun sanshi da gani yanada alaka da Khalid Bashar Majiyan sunmafi tunanin 'dan sane suka ce"wallahi Sir kuna kama daga nesa ma kai kace shine nan makarantar ma ya gama"yace " ok" yasa kai yabi Sir Nura dan shi bai fiye san surutu ba kuma ganin Sir Nura su shiyake jira Sir Nura ya dubi AbdurRahman da suke tafiya yace masa" ai yarannan idan zaka kwana nasiha basaji ko 'daya sunfiso aci nutuncinsu"murmushi AbdurRahman yayi yace"wallahi Sir ni dasuka ce ina kama da wanine ya 'dauremin kai"Dariya Sir Nura yayi yace"lallai AbdurRahman bakasan halin yarannan ba karya cikinsu ba'a magana"suka bada hira yana basu labarin halayyar dalibai ,suko su Nasiba suna shigowa ajin aka fara kus kus ana maganarsu Nasiba ta haye saman bencinsu Rufaida Hauwa'u takoma bencinsu ta zauna Nasiba tace kewai Rufaida bakiga kamar wannan gayen da yayanki ba "Rufaida tace " keni fa bangani ba"Hauwa'u da take baya tace"ke Nasiba ki kyaleta mana kema kinsan Rufaida batasan abin arziki ba,amma yanzu waye zaiga wancen malamin meyema sunanshi kuma ace basa kama da AbdurRafi",Samiha da maganar take cinta ,dan tasan bazasuyi da Rufaida ba, Samiha tace"ke Hauwa jiddah Allah nima nagani ,shiru dai kawai nayi"Rufaida dai tana jin kaya kaya dinsu batace komai ba dukda itamadai taga 'yar kamarsu amma bawai kama suke maiyawa ba amma tasan inta tayasu har atashi ana abu daya fitowar break shine ya watsa group 'din da suka ha'da Samiha ganin anfito Break tace "malama ki fito mufita mai take gaskiya"Rufaida ta dan tabe baki tace" gaskiya yau bazan fita Break ba,ke maii nayi ne na take gaskiya"Samiha tace "hakanan kiri -kiri kince mana sabon malamin nan baya kama da Yaya AbdurRafi bayan nasan karya kike"Rufaida tace" ai nasan halinku da cewa nayi suna kamar da tuni group din nan bai waste ba yanzu kuwa gashi bakowa amma aini ma naga kamar"Samiha tayi tsaki tayiwa Rufaida tace mata kuma"yar rain in hankali kawai,Samiha ta 'Dora da cewa"keni ban shakamiki labari ba"Rufaida ta maida hankalinta ga Samiha tace"shakamin naji kawata"Samiha tace"keni nafasa ma"Rufaida tace "haba Hassanata shakamin dan Allah naji" Samiha tace"ke wani gaye muka ha'du dashi jiya ke kinganshi kuwa kyakkyawa kalar namijin da nakeson aure dogo kyakkyawa"tsaki Rufaida tayi tana dokin jin labari amma Samihan ta tsaya shirmen banza tace"ni fadamin a'ina kuka ha'du yimin bayani naji kinki yimin bayani yadda zan gane "Samiha tace " aike bakya cin ribar zance dama sai kin nuna kin gaji"Rufaida tace"naji dai nidai fa'damin" Samiha tace"na fito Momy ta aikeni gidan su Fahat Hassan na nan ajin"Rufaida tace"Eh naji dai na gane jeki zancenki"Samiha tace"gidan Aunty Ummi na bayani gidanmu a kofar gidan muka ha'du ya tsaidani da kamar bazan tsayaba sai naga baikamata na masa hakaba tunda naga Hanif din Aunty Ummi a hannunsa ,shine na tsaya,muka gaisa,Har yake shaidamin yana sona ganin bankulasa ba shine ya bini gidansu Fahat yacemin Auny Ummi cousin dinsa ce Baban Aunty Ummi da mamarshi wa da 'kanwa ne ,yace yana ganina a unguwar idan yazo yace har a gidan Auny Ummi ya taba ganina ni dake,danshi tunaninsa mu 'yan biyu ne ni dake amma zai shiga mota ya tayar zai fitamu shiyasa bamu gaisa ba dan alokacin mun shiga gidannevgaskiya gayen nan yayi a kasar waje UK yayi karatunsa yace min zaizo gidanmu yau idan ya shigo unguwar da wuri dan yace bays rabo da unguwar"Rufaida tayi murmushi tace "kai amma kawata na tayaki murna Allah ya tabbatar da akkhairi,saidai kibi a hankali karki cika nuna kinasansa ,kuma karki sakankance dashi sosai,ki rika abu da wayewarki" Samiha tace "haka ne " year uwata amma duk ina kikasan wannan sirrikan soyayyar keda bakyayi?i"Rufaida tace"a gurin su Nasiba kinmanta natafi yajin aiki bencinki"Nasiba Shehu Abubakar India batun soyayyah ne ko a ajin azo gurinta yanzu haka ma bikinta za'ayi"Samiha tayi dariya danta tuna sun ta'ba wani fa'da da Rufaida tabar mata bencin Hauwa'u Umar ta koma Samiha tace "kai Rufaida aji tsoron Allah bakya mantuwa kinsan da yanzu ne bazanyi fa'da kan yoghurt ba" Rufaida tace"naga alama fa nidai na baki shawara kibi a hankali ki tsare mutuncinki a gurinshi karki cika nunamasa sosai"Samiha tace"to shikenan kawata,Amma nifa koshi zan aura tare za'ayi bikinmu nidake banaso nayi aure nabark"Dariya maganar taba Rufaida ma tace"banda abin Samiha ai da Allah nima yakawomin kusan hadawa ma za'ayi,yanzu dai Da yaya Saudat za'a ha'daku tsaki Samiha tayi tace "kewai Yaya Saudat zan zauna jira inama saurayin nata ya ta'ba zuwa gidan mu kurum daga haduwa a bikinsu Yaya Samina tace lallai shi take so,ke kin ganshi kuwa kato dashi da gani ma ya fara tsufa" Rufaida tace"kai Samiha banda sharri fa?"Samiha tace"Allah da gaske nake dandai bakije Sokoto bikinba da kinganshi kato tsawo da kiba"Rufaida tace"koma dai ya yake ita tanasan kayanta bare ma dai nasan bahaka bane"Samiha tace"au shigarwa Yaya Saudat yau kike kuma"murmushi Rufaida tayi tace"Eh mana"da haka dai suka kara taba hira har aka dawo break da sabon malaminsu ya shigo Sir AbdurRahman ganin sabon zuwane yasa duk ajin akayi shiru sai yayi tanbaya idan sun sani su bashi amsa don basa so daga zuwan AbdurRahman ya fara fahimtar halinsu gasu Nasiba sun gwangwadamusu cewa shi 'dan babban gidane shiyasa suka fara ganin girmanshi dan Khalid Bashar Majiya ba laifi kam yayi suna a cikin garin Kano.

SADIYA KHALI✍🏽*JININMU DAYA*
By Sadiya Ibrahim Khaliy(Sadiya Khaliy)

11

Rufaida Aliyu Bukar Hafaffiyar garin Zariya ce da aiki ya

Please Login or Register in order to submit comment