Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama inason fada miki"
Da haka ta kashe data tana kokarin bin kiran wani wani ya sake shigowa
"Assalamu Alaikum matata"
Jin muryarsa ya sata murmushi
"Wa'alaikumus salam mai gida ya aiki"
"Alhamdulillah,yanzu kofur Bala ya tawo amsar abinci ki hado da Plat da yawa yau Kabir yace da abincin ki zaiyi launch,dafatan kingama aikin lafiya kuma baigaji dake ba"
"Murmushi tayi jin maganar mijin nata
"To sai yazo nagama komai"
"Yawwa farin ciki na da fatan kin Zubawa su Umma tun dazu"
Tayi saurin ce masa
"Eh ya mijina"
Yace ok take care bye ina aiki yanzu"
Tace masa"agama lafiya take care to u my regard to Yaya Kabir
Da ganan ta katse wayar ta mike ta nufi kitchen ta hada abincin a basket ta dawo falon inda tasa mesu nan ta barsu
"Sannu da hutawa Umma" Rufaida tace tana zama kujerar dake gefen tasu ta aje basket din kusa da ita batayi tunanin zasu amsa musu ba ita ma ta share su jin alamar kararrawar kofar falon na motsi ya sata zura hijabin da ta fito dashi a hannu ta dauki basket din sukw gaisa da kofur bala ta mika masa basket din ta dawo ciki ta zauna inda ta tashi tanaji suna yi mata habaici amma bata saurare su ba ta cigaba da kallonta
Ruqayya ce cikin tsawa ta fara magana tana kallon Rufaida
"Ke yar masu samu tafi iyawa ina ne matsugunnunmu,ko bamu da shi"
Rufaida ta kai muryarta kasa dan yanzu taga rashin kyautawar nuna musu masaukinsu amma dai bata ga fuska ba zata iya cewa tace
"Kiyi hakuri Ruqayya na manta wallahi da kin shiga ciki kin wuce wani corridor to daki na farko shine naku"
Tsaki Ruqayya taja ta mike ta shige ciki Rufaida ma mikewa tayi ta shige ciki,tanason tanbayar Umma ko sun ci abinci amma tana tsoron abinda zaije ya dawo"
Bayan wata 8
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da Rufaida da yanzu take da ciki Na Wata 6 , tsananin hakuri take duk a wannan lokacin da surikartata da kanwar mijinta zaman su da ita kullum dai cin mutunci ne gareta duk yadda take kyautata musu,dan har lokacin basu tafi ba,Ruqayya ce kawai taje gida yin jarabawar jamb tana gamawa kuma ta dawo
shikansa Wahid yana kallon abinda akewa matar tasa sau tari sai dai bai isa yace wani abu ba,ba tun hidima iya yi yana yi musu dan albashin na watan da mahaifiyartasa suka zo yana dauka dinkunan sawa yayi wa mahaifiyar tasa dasu,Ruqayya ko duk yadda ta kai da shishshige masa baya koda saurararta don shi soyayya ba ta damesa ba koda ma auren nata zaiyi matar da ya aura ma da yake sonta baiyi soyayya da ita ba ta azo a gani saboda rashin lokaci bare kuma yayi da Ruqayya,Rukayya kuwa tana kara jin son Wahid har ranta ganin yana da halin mai kyau zaman da suke yanzu take kara fahimtarsa, shiyasa take kokarin shige masa ko zai sota dukda tanada samari amma halayyar Wahid tana burgeta musamman yanzu da take ganin zaman su da matar shi tana nuna kulawarsa ga matar tasa,sau tari tana mamakin hakurin Rufaida dan ko ta tarar suna fira da Wahid din da ita suna zaune bata koda saurararsu zata koma ciki abinta wanda gaskiya da ita ce baza ta iya ba,ita ko Rufaida rashin zabi shike sawa ta koma ciki don tanada kishi da idan ta zauna ba zata hakura da abinda zata ga Ruqayya zata riqa ce masa ba a gabanta alhalin bata ga anfanin maganar ba idan tace ba zata hakuran ba don namiji ba'a shaidarsa ko kusa,ba zata ce nata bazai so wata ba bayan ita idan tayi hakan ba ta yiwa kanta adalci ba,yanzu ga cikin jikinta shiyasa ma bata son zama a cikin su saboda karsuyi abinda zai jawo mata bacin rai.

ABDULRA'UF
Sai a page na gaba zamu waiwaya bangaransa Insha Allah.

SadiyaKhalil.

Dan Allah Ku rika yin share,wani groups din.*JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil❤️

43
Wannan page naku ne
Amina Muhammad baso
Safiyya Galadanci
Aisha Umar Ibrahim
Nagode da gudunmawarku gareni bisa son cigabana kuyi yadda kuke so da shafin nan Allah ya bar zumunci🖤

ABDULRA'UF

"Ra'uf meke damunka" Shureim yayi maganar da yake zaune a kujerar dake kallon ta Ra'uf a office din Ra'uf din
Kansa ya dago ya kalli Shureim da murmushinsa yace
"Mai ka gani?"
Shureim ya girgiza kansa kawai yace "komai ma Ra'uf ,kana tunanin zaka shiga wata damuwa na kasa fahimta,nasan komai damuwarka ta soyayya ce,Ahmad ya fadamin komai,Ra'uf dan Allah ka cire damuwarka,tunda Ahmad ya sanarmin ita ta riga da tayi aurema yarinyar,ka cire ta a zuciyarka please ka samu wata ka aura ga kanwata nan Ruwaydah kaje ka nemi aurenta indai kana santa"
Murmushi Ra'uf yayi ya maida dubensa kaco kam ga Shureim ya soma cewa
"Shureim ba soyayyar Rufaida ce damuwa ta ba illah iyaka sanin dalilin hanani aurenta shine damuwata,amma ni aure a yanzu haka baya gaba na,sai dai bazan ki Ruwaydah ba amma ba tsari aure yanzu a tsarina sai nan gaba
Tausayi Ra'uf ya bawa Shureim saboda shima yanajin zafin soyayya yanzu haka saboda yanasan Inteesar sosai saidai ya kasa furta mata saboda yana tsoron karta ki amincewa da soyayyarsa,ga soyayyarta da ke nuqurqusar zuciyarsa a kullum,dole ya tausayawa Ra'uf danshi sunyi soyayya ma suna da shirin aure aka rabasu ya dai daure ya kauda tunaninsa yace
" Eh aboki na nasan da ciwo ravuwa da masoyi amma hakuri zakayi ka cigaba dayi kuma Allah yasa rabuwar tafi zama alkhairi sannan ka cigaba da addu'ar neman zabin Allah a rayuwarka"
Ra'uf ya jidadin nasihar abokin nasa Shureim abokine nagari,shiyasa yake alfahari da abokin nasa da murmushi ya kalli Shureim yace
"Nagode aboki na"
"Haba babu komai aboki na damuwarka ta wace da zan iya fidda ma damuwarka da nayi wallahi amma zan cigaba da tayaka addu'a,tun sanda na fahimci baka da walwala a kwanakin nan kuma naji baka kara yimin maganar budurwarka ta kasarku ba,shine yasa nayi tunanin ko akwai abinda ya faru da soyayyarku shine yasa nakasa hakura har saida na tanbayi Ahmad ko yasan meke damunka ya fadamin shine yasanar dani komai,nasan zafin so Ra'uf nima kullum ina cikinsa zullumi na kar na fadawa Inteesar ta kasa amincewa dani" Shureim ya karasa maganar da rarraunar murya
Dafa sa Ra'uf yayi yace
"Haba abokina karka damu zata amince dakai yau zanje gidansu Inteesar na sanar mata da soyayyar da kake yi mata nasan zata amince"
Shureim ya murmusa yace
"Kai abokina ina godiya sosai"
"Haba aboki na karka damu komai nayi ma kacancanta da ayi ma ne"
Cewar Ra'uf
Da haka suka sauya fira ta aiyukansu har zuwa wani lokaci

Komai ya sauyawa Ra'uf soyayyar Rufaida koda yaushe ita ke nuqurqusar zuciyarsa sai dai ganin bazai sameta ba yasa shi maida lamuransa kacokam ga ayyukansa yasa kwazo fiye da nada akan aikin nasa,A yanzu haka sunsha hidimar bikin abokinsa Shureim da matarsa Inteesar,da Ra'uf din ne silar auren shi ya shigar da Shureim gurin Inteesar,dan abaya da Ra'uf yaje gurinta kafin ya sanar da ita son da Shureim.ke mata tayi tunanin Ra'uf din ke sonta kamar yadda take sonsa sai taji zance yasha banban ganin bazata iya nunawa Ra'uf batason Shureim ba shi take so,don Ra'uf a matsayin yayanta ta daukesa saboda kawarta Safiyya yasata hakura dan Shureim tasan baida wata makusa,don fannin kyau da kudi Shureim yafi Ra'uf sosai

Bangaren Samiha kuwa suna london abinsu acan ta haifi 'yarta mace ,wanda taso kafin haihuwar su dawo gida saidai yanayin karatunsa bai kammala ba a lokacin,shi kuma bayason ta taho kaduna ita kadai ba tare da shiba dom yasan ba wata kulawa 'yan uwansa zasu bata ba tunda yasan a kaduna zata zauna,haka Ahmad din ya nuna bayason wani yazo,ranan suna yarinyar taci sunan Rufaida wanda Samiha ta bukaci Ahmad ya samata yako biye mata yasa mata,don ya fahimci bada wasa Samiha ta dauki Rufaida a zuciyarta ba hakama ya fahimta a bangaren Rufaidan ma haka ne,haka ya jinjina wannan soyayyar tasu sosai a ransa babu wani kusanci na kusa kona nesa tsakaninsu amma suke wannan zumuncin har takai ga sa wa 'ya sunan kawa lalle abun babba ne,koda Ahmad ya fadawa Ra'uf sunan Rufaida yarsa taci ba karamin dadi ya jiba don yakasa mantawa da Rufaida a zuciyarsa har zuwa lokacin ya kuma kasa kula wata ta zama makwafinta a zuciyarsa,takakka yayi ya tafi London daga Delhi shida Sophie da Husna da Husnan ta soma karatunta a Delhi,dukda da yace bazai samu zuwa ba amma jin sunan da Ahmad yasa wa 'yarsa ya sashi tafiya da kayan jaririya masu yawan gaske suka tafi da duk yawan wanda Ammi da Dady suka hada mata saida yakara wasu saboda murnan abinda yayi na saka sunan Rufaida da Ahmad yayi ji yake kamar don shi yasa sunan ga murnar karuwar da suka samu don Ahmad ya wuce amini a garesa, Ammi da ita a lokacin ta ma manta da sunan Rufaida yasa mata fahimci murnar Ra'uf ba,sai tunaninta ya bata saboda Ahmad ya haifi yarinya yake murna don kowa yasan yadda suke da Ahmad din shi yasa babu wanda yakawo komai,bayan shi kuwa murna biyu yake yi

RUFAIDA
Haka take cigaba da rayuwa da uwar mijinta da Rukayya abun babu dadi,kuma har lokacin Abba Bukar baisan wannan zancen ba,taje Kano tayi Kwana biyu da dakyar Wahid ya barta taje ganin tanada ciki a lokacin shi da kansa Wahid din ya kaita Kanon da shima zaije wata seminar kanon ,bakaramin murna daganinta suka yi ba,ganinta dauke da ciki da kuma ganin babu alamun damuwa a tare da ita don har kiba cikin yasata yasa hankalin Ummi Hauwa'u kwanciya , saida ta zaga gidajen kawayenta ta kuma je gidan Momy maryam tayi kwana daya sannan suka juyo
Murnar sawa Rufaida takwara sosai Wahid yayi da Ahmad yake sanar musu bayan dawowarsu Kano da kwana biyu bakaramin kudi Wahid ya tura ba a siyawa baby kayan sawa Rufaida kuwa ranar kwana tayi da farin ciki ta kuma karawa Samiha matsayi a zuciyarta sosai,hakama a bangaren su Ummi Hauwa'u da Momy Maryam sun sallama irin kaunar dake tsakanin Samiha da Rufaida sai da jikin Rufaida yayi wata takwas Abba Bukar yaji labarin zaman da Hajiya Jamila da Rukayya keyi a gidan Wahid da AbdulMalik ya sanar masa da yaje wani aiki abujar yaje gidan,dukda Abba Bukar bayason dawo da Hajiya Jamila don bakaramin dadin zamansa da sauran matansa yake ba tare da Hajiya Jamila ba dama itace damuwarsa,badan yaso ba ya maido da ita ya kuma maida Rukayya nasarawa,saboda yana bukatar zaman lafiyar su Wahid da Rufaida

SadiyaIbrahimKhalil❤️
*JININMU 'DAYA*
BY Sadiya Khalil

44

*Duk abinda ka rubuta baya gogewa a littafinka koda kai ka goge shi a zahiri*


RUFAIDA
Bugun wayarta da take ji yasata katse aikin da take na shirya kayanta a drower da take da tsohon cikinta a lokacin ta mika hannu gefen gado ta dauki wayar ganin Samiha ce akan layin yasata saurin dauka da Sallamarta tasa wayar a handsfree ta cigaba da aikin da take ta soma da cewa Samihab
"Mai jego ina 'diya ta,takwarata"
Samiha da take riqe da Rufaida karama a hannu ta kurawa Rufaidan ido tanaji kamar Rufaida Aminiyarta take kallo ido ta lumshe ta bude kafin ta soma magana
"Wato babu wata gaisuwa tsakaninmu ko,bare tanbayar lafiya ta sai tanbayar 'yarki ko?saboda takwararki ce,shiyasa Ahmad yace karna sakawa 'yata sunanki,saboda yasan yadani zakiyi soyayyar da mukewa junanmu ta koma ke Rufaida zaki riqa yiwa"
Dariya maganar Samiha ta bata don bata tunanin akwai mahalukin da zai canza soyayyar dake tsakaninta da Rufaida
"Au dariya ma kike"Samiha ta fada da ta jiyo dariyar a cikin wayarta
Rufaida tace"yi hakuri yar uwata amma wallahi soyayyar da nake miki a jinina take,soyayyar da zanwa Rufaida duk saboda ke zan mata,badan kinmin takwara ba
Samiha tace "to naji nima wasa nake miki,ai idan kikaso Rufaida tamkar ni kikaso ne,fatana na rayu da ita domin koda muna nesa da juna dana kalleta na tuno dake"
"Hmm to naji 'yar uwata ina godiya da kaunar da kikemin fatana na wanzu gurin yi miki,koda bakya raye zan kula da duk abinda kika mallaka fiye da yadda zan kula da nawa"
Rufaida tayi wannan maganar
Samiha tace" haba 'yar uwata babu godiya tsakaninmu,ya Yaya Ahmad da baby na Allah dai yasa ki haifi namiji Rufy tayi miji"
Dariya maganar taba Rufaida tace
"To shikenan,Yana lafiya yana gurin aiki amma nasan yana hanyar dawowa ma baby kuma yana gaisheki,amma ni baby na ba zata auri kaninta ba gaskiya ki bari dai shi sai ki haifar masa mata nan gaba"
Murmushi Samiha tayi tace
"Aiko ni babyn cikinki na yiwa mata tun kafin yazo duniya,don haka babu fashi, indai namiji kika haifa shine mijin Rufaida,kuma tsiran nasu ba zai kasance mai yawa ba"
Rufaida tace
"To shikenan wai ma dakata ina Yaya Ahmad din ne"
Samiha tace
"Hmm ya tafi raka Yaya Ra'uf da su Husna wani store,kinsan su Ra'uf din sunzo daga Delhi,dafa baiyi niyyar zuwa ba yanaji ansa wa baby sunanki yazo,wallahi banyi tunanin har yanzu kina zuciyar Ra'uf ba sai da yace zaizo da kuma ganin kayan da ya siyowa Baby gaskiya ya kashe kudi,Ahmad yace tunda yaki fidda mata tunda kuka rabu yanzu sai ya auri Rufaida karama"
Rufaida tayi murmushi kamar tana ganinta tace
"Allah sarki,nifa na dauka yayi auren ma,amma ai bazan ba 'yata tsoho ba"
Samiha tace
"Da yayi aida na sanar miki har yau baiyi ba tunda ya rasa ki ya fidda tsarin aure a ransa tunda idan an masa maganar auren sai yace ba yanzu ba,shi kwata kwata ba tsarin aure yanzu a tare da shi,da Ahmad yace masa ko dai saboda ya rasa ki ne shine yace ko daya yasan dai ya soki amma dai yanzu tunda kinyi aure shikenan,shi dama halayyarki ta rudesa yasa har yaji yanasan yayi aure a baya auren ma kuma ya aureki,tunda kuma iyayenku ke da shi suka nuna basaso ya hakura"
Rufaida da maganganun Samiha suke shigar mata zuciya sosai jin Samihan ta dakata da maganarta yasa tace"Kinga aiki nake yanzu zan kiraki anjima"
Ba tare da taji mai Samiha zata kara cewa ba ta katse wayar da suke,don baza ta iya jure a rinqa yi mata maganar tsohon saurayinta ba ana tuno mata baya ne da har yau takasa mantawa da ita bakin cikin rayuwarta har yau ya kasa gushewa bawai son Ra'uf take har lokacin ba don yanzu soyayyar ta ta Wahid ce ba ta saka kowa a zuciyarta da sunan so idan ba mijinta ba, sai dai takasa manta yadda suka rabu da iyayen Ra'uf da nata,don tanada yakinin da kalmar karuwa da wasu daga cikin dangin Umminsu ke kiran Ummin nasu dashi a kayi anfani gurin ruguza wancen maganar auren nata,aka hadata da Wahid saukinta guda mijinta na kaunarta,matsalarta a gurin wasu daga cikin 'yan uwansu take da kuma surikarta sa'arta guda ce tayi nisa dasu sai dai duk ranar da suka zo habaici kam ta bani da shi samun daukinta kadai su tafi gida
Samiha da take ta magana a wayar jin bata ba ta amsa ba yasa ta duba taga ta katse kiran murmushi tayi ta aje wayar itama tana nazarin dalilin saurin CE mata zasuyi waya anjimar da tayi bakomai bane illa maganar Ra'uf da tayi mata tunda akayi haka ta fahimci Rufaida batasan a yi mata maganar Ra'uf din kwata,koda yake tasan halin Rufaida tun suna 'yam mata bata damu da maganar namiji ba,kota Yaya Abdul ne da Yaya Samir ma ba'ayi take ba su da suke matsayin 'yan uwanta,bare kuma ta saurayi gashi kuma yanzu tana da aure don haka itama Samiha ta dauki alwashin bazata kuma yiwa Rufaida maganar Ra'uf ba idan ba ita ta sako, bare kuma tasan za'a yara kafin tayi maganarsa

Wahid da yake tsaye jikin kofar dakin Rufaida da hankalinta nakan wayar da take da Samiha batasan ma ya shigo ba yana kallon yadda yanayin matarsa ya koma bayan ta kammala wayar murmushi yayi ya karaso inda take ya karbe kayan da take kokarin sakawa cikin drower ya riqe hannunta ya zauna gefenta kallon mamaki ta bisa dashi don batasan ya dawo ba, fuskarta ya kalla yace
"Waye ya batamin ran mata ta"
Sai a yanzu ta iya magana tayi saurin cewa
"Babu kowa,mai ka gani"
Ya danyi murmushi tukun yace
"Ban yadda ba Samiha ta bata ranki saboda tayi miki maganar Ra'uf ko saboda kinason ki manta shi a yanzu haka"
Ido ta zaro tace
"Yaya waye ya fadama munyi maganar Ra'uf da Samiha?"
Ya danyi murmushi yace
"Nina jiyewa kunnena babu wanda ya fadamin,na dade tsaye anan,ina jin duk wayarku da Samiha,Rufaida a kullum ina godiya ga Allah dana samu mace ta gari kamarki"
"Hmm Yaya kenan maiyasa kace haka"
Rufaida tayi wannan maganar"
Ya dan kalleta yace
"Saboda kin hakura da zabina da Allah yayi miki wato ni baki kasance mai bibiyar tsohon saurayin da kaunarsa nasan ita ta fara linkaya a ruhinki,gashi sai kikayi rashin sa'ar mijinki bai iya soyayya ba,bare lokaci guda ya fitar miki da son Ra'uf a ranki,amma ke din sai kika bada gudunmawar hakan,kinga dole nace nasamu mace ta gari"
Murmushi tayi tace
"Shikenan ya isa haka mu manta da baya mu tunkari gaba"
Yayi saurin ce mata
"Hakane mata ta,yanzu mai kika tanadarmin yaufa yunwa nakeji sosai,Kabir ya cinye abincin da kika kawomin office"
Ta dan yi masa hararar wasa tace
"Duka fa abincin na zubo muku dana girka azo muje dai kitchen kayi girkinka dai,wai shi Yaya Kabir Luba bata iya girki bane?"
Yace"Am sorry my wife ki girkamin ko indomie ne,kinsan dai Kabir bayan abincin matarsa bayason cin na kowa saike,Kabir yace abincinki dadinsa daya dana matar Uncle dinsa da take porthacourt,yace gani yake idan yaci abincinki kamar nata yaci"
Murmushi Rufaida tayi tace
"Kasan dai halin Yaya Kabir kila ma ba haka bane,nidai muje na tayaka kazo nima ka karasa shiryamin kayana"
Wahid ya kalleta bayan ta mike yace
"Nufinki dai abokina karya garesa ko,ba ruwa na keda luba wallahi,dama yace min yau zata zo, kinga saina fadamata"
Zama tayi kokarin yi tare da cewa
"OK jeka ka fadamata ni kuma naki tayaka girkin"
Wahid da yake kokarin fita yace
"Sorry,my wife,wasa nake miki"
Da haka ta mike tabi bayansa zuwa kitchen

*Bayan wata biyu*

A wannan lokacin abubuwa da dama sun faru na farin ciki da akasinsa abun farin cikin harda haihuwar Rufaida ta haifi yaronta kyakkyawa da yaci suna Yasir da yake kama da mahaifansa,Samiha da aka tura mata hoton yaron ba karamin farin ciki tayi ba,kamar ita aka yiwa haihuwar ta kuma turo masa da kaya masu kyau da tsada ba karamin soyayya ake nunawa yaron ba,a gidansu ta haifesa Kano da taje goyon ciki har saida akayi arba'in ta dawo wannan zuwan bakaramin farin ciki Ummi Hauwa'u tayi ba na zuwan 'yarta ta koba komai ta rage jin bacin ran irin auren da akayiwa Rufaidan,ta kuma dora so akan Yasir,da itama Ummi Hauwa'u ta kara wata haihuwar ta haifi 'yarta mace mai suna Amina suna ce mata Rahima a lokacin akayi bikin Nasiba shehu kawa ga Rufaida da duk ta hadu da class mate dinsu da hakan ya tuna musu da rayuwar makaranta Samiha ce kadai bata samu zuwa ba kasancewar Ahmad yace sai ya kammala karatunsa zasu dawo tare,duk yadda taso zuwa haka ta hakura Abdul-Rahman ma yazo bikin dukda baya kasar yana Cyprus saida yazo daurin auren Aisha kasancewar ita ce ta hannun damarsa,haka nan ya dinga tsokanar Rufaida Yasir ya fi ta kyau,Hajiya Jamila badan taso ba tazo ganin da saboda matsawar da Abba Bukar yayi tazo ba tare da ta kawo ko tsinke ba,tana ganin Yasir kuma taji kiyayyarsa ta shiga ranta,da habaice habaice da bakaken maganganu ta baro Kano,wata 1 tayi cur a Kano daganan ta koma Abuja da Luba taje gidan ta gyara mata shi itama a lokacin ta haifi dan ta Yusuf a kwantagora da nanne garinsu Kabir din aiki shima ya maidoshi Abujar da yake matsayin Kwararren likita

Share plz kuma kuyi manage
*JININMU 'DAYA*
By Sadiya Ibrahim Khalil
(Sadiya Khalil)

45.
Ayi manage please ba yawa


*Bayan shekara biyu*

Wahid ya dago jajayen idanunsa ya kalli Hajiya Jamila da take zaune saman kujera Wahid yana gefenta kan carpet zaune ya soma magana cikin raunin murya
"Mama nifa bana qi auren Ruqayya bane,illa ni dai kawai,bata daga cikin tsarin matan da na keso na aura"
Hajiya Jamila cikin zafin zuciya ta kalli Wahid ta soma magana
"Na fahimceka Wahid,'yar karuwa wadda banbancinku yafi gaban kwatance har ta fiye ma Ruqayya,to wannan karon muddin baka auri Ruqayya ba sai dai ka saki waccen yarinyar don ba zan bari irin karuwa ta cigaba da haifamin jikoki ba,dan shi kansa wancen 'dan ban yarda naka ne ba ne"
Da sauri ya kalli mahaifiyar tasa yace
"Haba Umma mai yasa zaki ce haka,dan Allah Umma mu daina tuna baya mu tunkari gaba kawai...
Abba bukar da ya dade a tsaye a kofar dakin da yakejin duk abinda suke tattaunawa wanda babu wanda yaji motsinsa a cikinsu yace
"Barta ta tuna duk abinda ke ranta Wahid"
Muryar Abba Bukar din ce ta katse karashen maganar da yakeson yi
Abba Bukar din ya dora da cewa
"Jamila tunda har Wahid yace bazai auri Ruqayya ba da bakinsa to nima,bazan amince ba kai koda ma ya amince din,saboda koda ban hada iri da Rufaida ba wallahi ta fiye min ke da yan uwanki"
Wata shewa Hajiya Jamila tayi kafin tace
"Bari na tuna ma idan ka manta ni din da kake fadar hakan akaina ko makaho ya shinshina yasan cewa nafi wancan dan iskan kanin naka,wanda saboda abun kunya saurayin 'yar da iyayensa suka fasa,sai danni nawa 'dan ya taimaka musu zakayi min maganar banza,me ake da zuriya irin taku
Abba Bukar ya tunkaro Hajiya Jamila cikin zafin zuciya zai kai mata duka da take zaune kujera ba tare da tayi koda motsi ba Wahid ya mike ya rike hannun mahaifinnasa yana cewa
"Abba kayi hakuri"
Abba Bukar da idonsa ya soma ja yace
"Wahid yanzu ni Jamila ta ke fadawa wadannan maganganun,ita ta manta abunda ya faru da tata 'yar uwar ranar da ranar aurenta mijin ya fasa ta manta kuma abunda dan uwanta ya aikata da..."
Hajiya Jamila sai yanzu ta mike daga kujerar da take ta katse maganar Abba Bukar da cewa
"Bukar wallahi karka kusa,ka fadi wata magana akaina idan ba haka wallahi saikayi dana sani mara iyaka"
Cikin bacin rai ya kalli Hajiya Jamila yace
Wanne dana sani zanyi daya wuce ke wanda zakiyi"
Murmushi Hajiya Jamila tayi kafin tace
"Aini banida wani danasani,kune kukayi shi,tuntuni bama yanzu ba saboda kuskuren shigowar karuwa kazama cikin.....
Wahid ne ya yayi kokarin jan Abba Bukar ganin Ummantasu bazata fasa maganar da take,suka fito daga daki saida suka fito wahid ya dubi Abba Bukar yace
"Abba dan Allah kayi hakuri,da abinda Umma tayi yanzu"
Abba Bukar dafa kafadar Wahid yayi yace
"To ya zanyi Wahid kullum cikin hakuri nake yi,dawowar dana yi mata na dauka abun zaiyi sauki amma abun yafi nada ma,saboda don kawai na hadaka aure Rufaida"
Wahid cikin ba ya dubi ABBA Bukar yace
"amma Abba menene laifin Rufaida,bata aikata musu komai ba,haka ma ummansu Abba"
Abba Bukar yace
"To dama mai zata aikata musu Wahid kasan shi makiyi ba ya jira kayi masa laifi yake ba,yanzu ka wuce ku tafi karkuyi dare a hanya"
Jiki ba kwari su Wahid suka fito harabar gidan shida Abba Bukar gurin motarsu da Rufaida da sauran matan gidan suke jikin motar sun fito rakiyarsu
Haka suka shiga Wahid ya tada motar Rufaida ta shiga tare da Yasir da yayi girma ya fito a kyakkyawan Hausa Fulani da ya debi kamanni mahaifinsa sak
Har suka fara tafiya a motar babu wanda cikin Rufaida da Wahid sukayi wa juna magana saidai takan ji firarsu jefi jefi da Yasir don bataji akwai abinda zata iya cewa dashi shi din ma haka ne saboda bayason ta fahimci abinda ya faru shida mahaifiyar tasa a yanayin maganarsa ita dinma bata damu da hakan ba ta bude gidan gaba ta shiga jikinta babu kwari don tasan tabbas akwai abinda ya faru,a shigarsa sa dakin mahaifiyartasa,da niyyarsa tayi mata sallama sai kuma ga wadancen maganganun sun biyo baya

****
Marhabin da manyan baki wallahi sam ban tsammaci zuwanku ba"Rufaida ta furta hakan tana kokarin matsawa daga kofar falon da ta bude
Luba da ta shigo da Yusuf data riqewa hannu tace
"Ai dama haka zaki ce,uwar cika alkawari"
Ta karasa maganar tana hararar Rufaida
Rufaida tace
"Ayi min afuwa matar likita bokan turai kinsan Yasir baiji dadi ba yau kwana 2,yanzu dai ku zauna na kawo muku ruwa"
Luba ta zauna kujera tana cewa
"Var ruwan nan daga gida muke yanzu Abban Yusuf ya saukemu ya wuce asibiti"
Rufaida da take kokarin zama kusa da kujerar dasu Luba kekai tace
"Kai Yaya Kabir yana kokari, su likitoci kullum aiki kamar agogo ace har

Please Login or Register in order to submit comment