Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kara bata ran Hanne ganin duk shige da ficen da take da asarar dukiyarta da take duk a banza suke tafiya,Mamuda yanzu bama ta tasu yake,wannan ya kara hura wutar kiyayyar da Hanne take yiwa Aminar

Amma itako Amina tana ganin girman kishiyoyinta da 'ya'yansu sam batada mummunan manufa a ranta game da su

Shekara guda da ta zago da auren Amina da Mamuda ta haifi diyarta mace kyakkyawa mai kama da mahaifiyarta sak,tare da kishiyarta Amina ta haihu wato Suwaiba da ta haifi diyarta Malika
Safiyyya nada wata shida abubuwa suka fara sauyawa game da zaman Amina da mijin nata babu kwanciyar hankali, dama abokan zama duk ba shiri suke ba dan hatta Suwaiba Hanne ta fara zugeta akan Aminar,saidai ita Suwaiba tunanin da take baza ta ki Hanne da take 'yar uwarta ba tace zatayi shiri da bare da basu da alaka a tsakaninsu,gama halayyar Hannen da ta sani tuni inda ta fahimci shishshigin da take wa Aminar zata iya cewa akwai kullin da suke,ita ko Suwaiba macace mai gudun magana,wannan shine dalilan Suwaiba

Malam Basiru tun kafin aje ko ina ya fara dana Sanin aura wa Mamuda 'yarsa Amina don shi tunaninsa yana aurawa Mamuda 'yarsa shikenan sun samu hanyar samu gurin Mamudan,dukda a farko mamudan ya gwada hakan bayan bikinshi da Aminar abinci ake saukewa iyayen Aminar amma yanzu ko ko buhun gishiri basa samu

A yanzu haka Malam Basiru gani yake gwara Tijjani mijin Aliya akan Mamuda mijin Amina,saima da Aminar tazo gida bayan komawarta gidan mijinta bayan haihuwar ta da taje gida goyon ciki harta haihu yarinyar tayi wayau ,nan yana ganin Aminar yadda dukta rame daga komarwata gidan daga goyon cikin da tunda Aminar tazo Mamuda ke faman zarya gidan da naman kaji da lemuka amma daga komawarta duk ta rame nan iyayenta suka shiga tanbayar maike faruwa ba ta boye musu komaiba ta fada musu,tunda boyewar mai zatayi bayan ita dama Mamuda ba zabin ta bane,haka Malam Basiru da yasan shine silar auren 'yar tasa, nan ya fara rokon Aminar da mahaifiyarta yafiya
Saude tace"ai karshen kwadayinka ne dama yakai ka ya baroka gashinan tun kafin aje ko ina ga yadda ta dawo,kaje ka kai 'yarka cikin kishiyoyi kuma kowacce da 'ya'yanta bayan bata rasa ma rasa matar ba saboda son abin duniya ka manta ubangiji ke azurta bayinsa,amma idonka ya rufe tunaninka ai mijin Aminar shi zai a azurta mu ko ya azurta 'yarta mu,in banda zama babu kwanciyar hankali mai take yi"

Wannan abun da Mamuda yake yiwa 'yarsa ya yiwa Malam Basiru ciwo nan ya shiga neman Mamuda a kasuwa akan ya sakar masa 'yarsa amma Mamuda yace shi yana son matarsa ko ina zasu je bazai sake taba haka malam Basiru ya hakura
Aliya ma ta sake haihuwar diyarta mace Bilkisu sunan kakarsu Aliyar da ranar da Aliyar ta haihu aka saka
wa yarinyarta ta Bilkisu da aikowa da su Aliyar a lokacin da Aliyar ta haihu da kwana daya da rasuwar Bilki kakarsu Aliyar ta wajen uba wannan yasa Tijjani sakawa 'yarsa sunan kakar matar tasa Aliya
Wanda bayan haihuwar Aliyar Tijjani ganin sun fara tara 'ya'ya daga daya har suna biyu yanzu ga yanayin yanzu babu wani samun da suke a harkar ginin yasa ya yanke barin anan ya yanke shawarar zai dauki Aliya su koma Sokoto haka yadauketa zuwa sokoton da niyyar Tijjani da duk shekara zai kawo Aliya gida ta ga gida ba dan san ran mahaifan Aliyar da 'yan uwanta ba tabi mijin nata kuma gashi yace zai rika kawota gida wannan yasa shi jin dadi
Safiyya na da shekara biyar da haihuwa Amina ta sake haihuwar 'ya mace aka saka mata suna Hauwa'u wato ni da har nafi Safiya kama da mahaifiyarta mu Amina,a lokacin Saude mahaifiyar Amina ta haifi diyarta mace da ita Saude ta fidda rai da haihuwar ma a lokacin dan Haladu yayi shekara goma sha biyar sannan aka yi masa kanwar da taci suna Bilkisu aka sake maida sunan Kakarsu Aminar ga kanwarsu

Duk shekara sai su Malam Basiru sun zuba ido ko Aliya zata zo amma babu labarinta bana mijinta har tsawan shekara shida, duk wanda suka tanbaya a abokan Tijjani 'yan Sokoto idan sunje gida maiyasamu Tijjani har aka dauki wannan lokacin bai kawon Aliyar Kaduna ba amsarsu itace aisu Tijjani basu koma Kaduna ba wanda a wannan lokacin ne kuma Allah ya karbi ran Malam Basiru 'yan uwa da abokan arziki sunji mutuwarsa Amina da Mahaifiyar Saude da Haladu har sunfi kowa jin mutuwar Malam Basiru Bilkisu kuwa tana goye a lokacin batasan mahaifin nata ya rasu ba

Naji korafin page din danake muku nasan nima yana gajere amma kunsan yanayin rayuwa saboda karna rika barinku shiru yasa nake kokarin turo muku kullum ammah zan rika tsallaken rana indai kunaso sau uku a sati zan rika yi muku amma pages da yawa indai kun amince shikenan.
Nagode da yadda kuke nuna soyayyar littafin nan
[10/13, 8:18 PM] Sadiya Khalil MuhammadđŸ„°: A*JININMU 'DAYA*
By Sadiya Khalil❀

Book 2
5.

Shekaru na uku da haihuwa kanwar Mahaifiyarmu ta bace Bilkisu,da take sa'ar haihuwata sakamakon aiken da akayi mata siyo maggin miya shagon unguwa,neman duniya anyi mata amma ko alamun za'asake ganinta babu gidan Radio ba inda ba'a zagaba gurin cigiyarta amma babu duriyarta harma Inna Saude ta fidda rai gaba daya.

Batun Hakuri kuwa da Mahaifiyarmu take yi a gidanmu yana da yawa baga kishiyoyi kadai ba a'a har ga mijinta da 'ya'yansu dai dai kune cikin yayyenamu basu kama zugar da Hanne ke musu a kanmu da Mahaifiyarmu ba

Kwanaki sunzo sun wuce kamar kiftawar ido dukkanmu a yanzu haka mun soma girma dan Safiyya a yanzu tanada shekaru 11 ni kuma inada 5 Safiyya ta soma girma kuma ta taso da kyawunta Mahaifiyarmu takance ita da yayarta Aliya tafi kama,inda muka tanbayeta ina Umma Aliyar mu bamu santa ba anan ne take sanarmana labarinta haryau babu duriyarta da mijinta

Yau da wuri muka dawo makaranta muka shirya zuwa gidan kakarmu nida Yaya Safiya mu amso abincin da muka saba amsowa a kusan kowacce rana ta duniya
Tunda mu sam ko abinci bamu samu a gidan namu indai ba Ummanta mu tayi girki ba matan gidan hanamu sukeyi suce badan ita suke girkin ba,idan ta fadawa Baffanmu saiyace shi dai har da ita yake bada kayan abinci don haka ta kwatarwa kanta 'yanci ta rika amsar hakkinta gurin kishiyoyin nata,amma shi sam bazai yi mussu wata magana ba,kuma vazai bata wani abincin baba ta girka ,Ummantamu da tasan ko tayi maganar ba zata samu ba,wannan dalilin yasa duk ranar da ba itace da girki ba gidan Inna Saude zamu tafi mukarbo da ita din abincin saidawa takeyi a lokacin rayuwar tata abin tausayi muda muke a wannan babban gidan da zamu taimaka mata amma muke zuwa amsar taimako

"Umma ina kudin machine dinmu"
Fadina
Umma ta kalleni
"Kudin machine kuma Hauwa nan da unguwar Bellon saina baku kudin machine"
Safiyya ta harare in
"Umma kyaleta,batasan zuwa ne kawai"

Muna cikin hakanne yaya Jabir ne ya shigo bangaren namu,da shi da Yaya Usman da Yaya Malika muke shiri,akaf gidan namu da ya turo kofa da sallamarsa muka amsa masa ya na kokarin zama kujera muka gaishesa ya amsa mana da murmushi a fusakarsa ya 'dan kallemu

" ina zaku da ranar nan,naji ana cewa wata a cikinku bata da niyyar zuwa,kuma naga yau Alhamis babu makaranta"

Yaya Safiyya ta dan sosa kai
"Zamu je gidan Inna Saude ne,shine Hauwa tace saidai muje a machine"

Umma da take kallonmu ita Yaya Jabir ya kalla
"Umma mai zasu yo gidan Inna Saude da tsakar ranar nan,kuma a kafa ai akwai nisa, ko bata jin dadi ne?"

Nice nayi saurin yin magana kafin Umma tayi
"Yaya Jabir lafiyarta kalau abinci zamu je ansowa"

"Abinci kuma wanne irin abinci,kodai abinci zaku kai mata"fadin Yaya yana tsare ni da ido

Umma da Yaya Safiya da suke ta hararata ina kallonsu na cigaba da maganata a ganina boyewar mai za muyi

"Yaya ai indai ba girki Ummanmu ba bamu samun abinci,gwara ma girkin Mama Suwaiba takan bawa,Yaya Malika ta kawo mana a boye da idan Mama Hanne ta gani bata bari akawo mana"

Yaya Jabir da ransa ya baci ya kalli Umman tamu
"Yanzu Mama Amina,kuma kika yarda a rika yi miki hakan,ba zaki dauki mataki ba"

Umma tayi murmushi
"To Jabir mai zan iya yi,tunda bani na girka musu ba,mai gidan ma da nake ga zai iya tsawatar dasu yace bazai yi wata magana ba"

"To ai Baffa ba yi da laifi don yace hakan kece mai laifi,tunda yaga ba kisan ki kwatarwa kanki 'yanci ba fiyema da haka ce miki zaiyi, ke zaki kwatarwa kanki 'yanci,idan yaga kin yi jarumartar tararsu da maganar shine zai yi musu magana shima"

"To amma taya ya Jabir,kasan sunfi karfina sunfini manyan 'ya'ya ko ku sasa ku dokeni da 'ya'yana"Umma tayi maganar cikin raunin murya

Yaya Jabir ya zaro ido
" duka kuma Mama Amina wallahi indai ina gidan nan babu mai taba ki,ki cire tsoro kije ki tunkaresu da maganar,ke ranar girkin ki kike girka musu abincin da tarin 'ya'yansu kece suke kyashin baku abincin da bai kai ya kawo ba,haba kema said kace karamar yarinya"

Murmushi Umma tayi
"Ko 'daya Jabir ni dai banason neman rigima ne"

Nayi saurin sa baki da muke har lokacin muna jinsu
"Umma wallahi idan ba zaki yi magana ba zanje nayi"

Yaya Jabir ya kalleni yadda yaga nayi maganar ba alamu wasa hakan ya bashi dariya
"Kyaleta Hauwa'u zama tayi maganar ku je ku debo kwanuka kuje ku kai a zuba muku,idan Gwaggo Larai ta muku magana ku cemata nina ce azuba muku"

Haka akayi nice naje nakaiwa kula ta zobo mana abinci,Gwaggo Larai mai yi mana abinci,amma banda ranar girkin Ummanmu duk ranar girkin Ummanmu to ranar hutun Gwaggo Larai ne, haka ta zubo mana abinci mai rai da lafiya da aka dade da gamawa aka rurrufe a kuloli a ciki harda wanda za'a kaiwa makwabta gidajen da suke da karamin karfi a unguwar tamu

Koda na dawo Yaya Jabir yana nan sai da ya ga yawan abinci zai ishemu ya mike ya tafi
Gwaggo Larai da ina dawowa ,ta nufi bangarensu Mama Hanne ta sanar musu abinda ya faru Yaya Jabir yace a bamu abinci kuma ta zuba mana
Cikin bacin rai Mama Hanne ta nufo bangarenmu cikin bacin rai babu ko sallama ta kallemu da muke ta zuba uwar lomar abinci nida Yaya Safiya
"Da kyau tsofaffin mayu,kwayi loma mana tunda va'asa ba haduwa ba"

Umma ta doka wa Mama Hanne tsaki nayi mamakin tsakin daya fito bakin Ummantamu ganin bata saba yi wa wani tsaki maganar data fadawa Mama Hanne ta kara bani mamaki
"Kinga Hanne karki kara cewa 'ya'yana mayu don babu batun maita don sunci abincin gidan ubansu"

Mama Hanne da ita ma nasan tayi mamakin maganar Ummantamu ganin bata saba ba
"Idan na sake fada musu mai zai faru?"

"Zamu kwashi 'yan kallo,saboda yadda kike takama mijinki ya kawo abinci da za'a girka nima miji nane kuma wadannan ta nuna mu 'ya'yansane,don haka banga dalilin kiransu mayu ba,kuma abinci daga yau barar fashin kin zuba musu a gidan nan,tunda suma 'ya'yane"ta fadi haka tana tsare Mama Hanne da ido

Mama Hanne tayi dariya
"Yayi mai miji,miji da bai damu dake ba baidamu da 'ya'yanki ba harkike tunkawon mijinki ne"

Umma ta maida mata da martani
"To ai tunda zamansa nake,kuma 'ya'yana nasane to dole na kirasa mai miji na uban 'ya'yana, kuma ni miji na ya damu dani"

"Ina damuwar take ni bangani ko a jikinki ba bare a jikin 'ya'yanki" ta karasa zancen tana nuna mu

"Ai ni ba so nake ki ganta ba"
Fadin Umma ta na cigaba da
"Kuma ki fita ki barmin bangare, tun muna mu biyu
Ganin yadda Umma ranta ya baci yasa Mama Hanne saurin ficewa don tana tsoron su kwashi 'yan kallon da Ummantamu

Tun daga wannan lokacin muka samu saken cin abincin gidanmu amma sai dai wannan abun na kwaranyewa wata rana muna zaune a falo da Ummanmu tana koya mana karatun boko dukda bawai karatun bokon tayi mai zurfi ba ajinta biyar firamare aka yi mata aure amma yadda take da kokari sai kace takai matakin gama sakandire wannan yasa kullum da mundawo islamiyya take zama ta sake koya mana daga na islamiyyar har na bokon

Baffa ne ya shigo babu ko sallama da fadansa
" yanzu Amina abinda kikai kin kyauta kenan,ace tun daga ranar da nace miki akan abinci ki kwantarwa kanki 'yanci kika daina bawa Malika abinci a gidan nan sai dai ki tasa abincin gaba ke da 'ya'yanki ku ci"

Umman ta dago dakanta da idanunta jawur
"Amma Baban Sule ya kamata da aka fadama maganar ka zauna kayi nazari ba wai ka yanke min hukunci ba,ni ca nake sanda ba'a kasa abinci dani da 'ya'yana a gidan,duk ranar girki na ban fasa zuba wa diyayoyinsu ba ko su kansu"

"Nazarin me kuma zanyi bayan nasan fiye da haka zaki iya,akan wadannan 'ya'yan naki wallahi Amina kiji tsoron Allah,saboda kinga na baki dama shine kike kokarin ki zarce ko?"

"Bangane naji tsoron Allah ba da tsoron wa nake ji,kai duk cin zalinmu nida yara na da kake ci baka gani,sai kayi wa matanka suttura biki ko suna ni baka yiwa nawa ko tsinke ba,hatta karatu ma makaranta mai arha kasa su" Umma ta maida masa wannan martanin cikin bacin rai

"Lallai Amina wuyanki ya isa yanka ki dubi tsabar idona kice dani haka wato duk kokarin da nake akan 'ya'yanki bakya gani ko,to daga yau dinki ko sallah ce nadaina yiwa 'ya'yanki,makaranta kuma ta gwamnati zan sasu banda ma........."
Bai karasa maganar ba Kawu Haladu kanin Umma yayi sallama,mu da muke ta zaro ido muna kallon yadda Umma da Baffa keta fada a gabanmu,jin sallamar Kawu Haladu yasa mu saurin tashi muka karasa bakin kofar da Kawun namu yake muka rungumeshi da fara'arsa shima ya rungume mu sannan ya ruko Hannun mu zuwa cikin falon Baffanmu da yake har lokacin tsaye a gurin Kawu Haladu yana kokarin zama a kujerun falon
"Alhaji Ina yini"
Tsaki Baffan yaja ya five fuu da daga dakin namu yana banko kofa

Baffan na fita Kawu Haladu ya dubi Umma da muke zazzaune kusa dashi
"Yaya Amina ina yini"
Umman data dawo daga tunaninta jin maganar Haladu
"Bazan amsa ba" tayi maganar tana harararsa
"Kai Yaya Amina mai kuma nayi"

"Kaima kasani ni ban daukama talakawa na ganinku ba"

"Wallahi Yaya Amina kinsan yanayin sana'ar tawa yanzu ma wani yaro na bari a gurin"

"To Allah ya taimaka"

"Amin"
Mikewa Umma tayi ta shiga ciki

A lokacin muka gaishe muka gaishe da Kawun namu ya amsa yana tanbayarmu karatun mu
Muna cikin haka ne Umma ta dawo falon da abinci a plat da ruwa a kofi ta ajiyewa Kawu Haladu

"Sannu Yaya kamar ko kinsan banci komaiba,bayan abincin safe,ke din ma ban dauka zan samu gurinki na dan yau ko buga iskar motar da keken kadan akayi,kawai nace bari na zarto nan,na kawo miki cinikin ki sayi wani dan abin bukatar,saina jiyowa inna lafiyarsu Hauwa kwana biyu,basu jeba saima na sameku lafiya"

Umma tayi murmushi
"Yanzu har yau baka samu aikin ba,duk kudin da akayita caca,ai komai ya sauya muna samun abinci harma mu bada"

Sai sannan idon Umma ya sauka kanmu mu tsira musu ido muna saurarensu
"Ku tashi ku tafi wasanku,Yanzu nayi baki saina muku fada ku tashi"

Kawu Haladu ya katseta
"Yaya Amina,don sun zauna ai basu da laifi laifunsu su saka mana baki a maganarmu amma idan yaranmu busu ji matsalarmu ba waye zai ji mana"

Mu da muke kokarin tashi muka koma muka zauna,to dama ina zamu gaba daya 'yan gidanmu bamu yawon unguwa harta yayyenmu,imu imu muke wasan mu sai dai mu din a iya bangaren Umma muke wasan mu don dukanmu suke sauran idan mun shiga cikinsu,Umma ganin mun zauna ta bimu da harara

"Ai Yaya Amina kinsan aiki sai ka mika kudi to mu ina muke dana mikawar,kudin da aka kashe a karatu basa zama caca ai shi karatu indai kayi ka anfana koda ba kayi aiki ba zai canza ma rayuwa,dama yanzun nake shirin tanbayarmiki maike faruwa ne najiyo hayaniyar ku zan shigo falon kuma naga nagaida Alhaji Mamudan bai amsa ko dai akan abincin ne"fadin Kawu yana kallon Umma

"Hmm kai bari Haladu bama batun abincin yake fadan ba,tun ranar dana nuna musu basu isa ba suka soma bamu abincin nan ta bashi labari duk abinda ya farun
ta cigaba da
" yanzu akan abincin Malika da ban zuba mata ba,bata gidan lokacin ta kwana gidan Alhaji Audu shine ban masan da dawowarta ba,ashe tadawo a dazu,to yanzu matan suka zugosa ya shigo ya fara fada"shine ka taddasa yana wannan banbanmin yace makaranta ma ta gwamnati zai maida su Nana (sunan da take yawan kiran Yaya Safiyya dashi)kan hakan"

"Amma Yaya Amina, hakuri zaki rika yi komai yayi kansa amma hayaniya da mijinki ba mafita bace"

"Haladu, batun hakuri kam kaima kasan da cewar inayi" labarin duk abinda ya faru da itada mijinnata kafin shigowar Kawu Haladun ta basa

"Kai nidai Yaya Amina bansan halin mutumin nan ba,hakuri zaki tayi wata rana sai labari insha Allah komai zai wuce,kinga da kina sana'a da koda ya canza musu makarantar saiki maidasu wata ta kudin,to matsalar babu kudin da zaki ja jari,amma ki barsa ai duk makaranta makaranta ce"

"Hakane Haladu,wallahi a kullum yaran nan nake tunani banda haka ba zan iya cigaba da zama da Mamuda ba sabida iya biyayyar aure ina gwada yi masa amshi baya gani"

"Hmm Yaya Amina kenan,ai gidan mijinki shine rufin asirinki,duk tsiya gidanki yafi zaman gidanmu,kina gani da ran Baba ma yadda muke rayuwa bare yanzu babu shi,Inna sana'ar saida abinci take idan bake ma so kike ki rika yi ba,hakuri zaki cigaba dayi wata rana sai labari amma ki cigaba da addu'a don ina zargin shiga tsakaninku akayi da mijinki,dan da farko ba haka Alhaji Mamuda yake ba"

"Haka ne Haladu,amma wa make tunani zai shiga tsakaninmu,kishiyoyi na ko suwa?,banaso ka rika tunani irin wannan Allah ne mai yin komai babu wanda zai ma wani abu ba Allah ba,mutum sanadiyya yake zamowa,ni na mika lamurana ga Allah kaima inaso ka zamo hakan"

"Hakane Yaya Amina,amma kiga yadda Alhaji Mamudan yake nuna kaunarsa gareki kafin aurenku da bayan aurenku dama shine nake tunanin ko kishiyoyinki ne suka shiga tsakaninku amma tunda kin nuna ba haka bane shikenan"

"Bawai so ne bana yi ba Haladu,kaima kanka kasan dan Adam yakan boyema halayyarsa,sai daga baya inda tafiya tayi tafiya ka fahimci halayyoyinsa da yake voyema tunani na shima Mamudan haka yayi daga farko"

"Eh hakane Yaya amma dukda haka ki cigaba da addu'a a koda yaushe karki rika sake da ita domin ita takobi ce"

"Haka ne Haladu"

Kallo na Kawu Haladu yayi da tunda suka fara maganar ido na ke kansu dukda na fahimci akan Baffa suke maganarsu kuma ina saurarensun amma bazan iya wani tunani akan maganar ta su ba,tunda shekaru na baikai nan ba, yana dariya ya dubi Ummanmu
"Yaya kinga 'yar nan taki ta tsare mu da ido kamar tana fahimtarmu"

Itama Umma dariya tayi
"Lallai Haladu baka san wayan Hauwa ba,ai sarai tasan maganar Babanta ake tayi tunani inda maganarmu ta sosa sosai ne ba zata iya ba,amma jiya har cemin tayi idan ta girma zata siyamin irin kujerun dakin Mama Hanne dana Mama Suwaiba tunda Baffansu bai siyomin ba,na ce mata ai shima bashi ya siyo musu ba,tace min bata yarda ba tasan shine gashi nan iri daya ne dana dakinshi"

Dariya Kawu Haladu yayi
"Lallai Hauwa har kin zama kece babba ashe"

Dariya nayi

Yaya Safiyya da ta kai hannunta baya na ta makan duka

Umma da take kallon Yaya Safiya sanda take duka na
"Mai tayi miki Nana"

Yaya Safiya da idonta ya cicciko da hawaye
"Umma tun dazu fa ina kallonta tana murmushi taji ana fadar laifin Baffa a gabanta,yanzu shine zata yi mana dariya"

"To sata tayi kuka kamar me tunda,an fadi laifin Baffanku,kuma aiba wani abu akace game da shiba gaskiya aka fada abinda yake ko kar a fada,mai uba"

Yaya Safiyya ta girgiza kai kawai ta tashi daga inda muke wannan yasa nima na mike ma bita don nunyi sabon da ba zan iya ganin Yaya Safiya bata guri ni kuma na zauna ba
[10/13, 8:18 PM] Sadiya Khalil MuhammadđŸ„°: *JININMU 'DAYA*

By Sadiya Khalil

Book 2.
6.

Bayan watanni uku

Alokacin abubuwa da dama sun faru na farin ciki da kasinsa a lokacin ne Baffa ya aurar dasu Yaya Fati da Yaya Umma wato Salamatu,a Danbatta Yaya Umma tayi aure Dan uwansu Baffa ta aura, Yaya Fati kuma anan Kaduna dan kasuwa ta aura a lokacin kuma muka koma sabon gidanmu dake sabon Kawo babban gida yana da bangare akalla uku ,amma na tsakiyar da shine babban ciki a ciki gaba daya bangaren matan Baffanmu suke mu hadu a falo ne sai gefen falon matakalar bene bangaren Baffanmu daga gefe batun ko dai rayuwarmu a gidanmu gaskiya zan iya cewa sam babu dadi musamman yanzu da muka koma rayuwarmu dasu guri daya,indai har muka fito falo mu akaran kanmu wannan yayan namu ya doke mu wannan ya zagemu mune kawai ware a cikin gidanmu muda mahaifiyarmu hatta da Danbatta idan muka tafi nanma hakane babu wani so da suke nuna mana kamar sauran a raina nakance kodan mu bamu mahaifiyarmu ba su da alaka da Baffa ne don itace bare kadai a cikin matansa,amma dai ita ma bafulatanarce daga baya saina fahimci ba haka bane kawai dai ta ko ina Mama Hanne ta batawa Ummanmu suna ne da irin wannan rayuwar muka cigaba da tafiya batun makaranta kuwa tuni an sauya mana an maidamu ta gwamnati amma hakan bai sauya kwakwalwarmu ba muna ganewa sosai da haka har Yaya Safiyya ta kammala Secondary dinta sai ni da nike zuwa ko wacce rana ta duniya,Inna Saude da Kawu Haladu kuwa kullum naje gidan kamar na tasa su na dinga kuka ne gidan da suke ciki duk ya rushe amma Sam mai hayar yaki gyarawa yace basa biyanshi kudi,duk asabar da lahadi na kanje gidan Inna Saude na taya ta mikawa masu siyan wainar da tako ma yi da safe,Umma kuwa ita ba samun wani abu take ba gurin Baffa sai dai matan so su samu,haka zaka jisu a babban falo suna ta yiwa Baffa kidayar kudi da suke so yabasu su da 'ya'yansu amma banda mu tamu mahaifiyar duk ranar da kaji suna magana ta sake tayi masa zance kudi saitayi danasani ranar cin mutunci iri iri yake yi mata saboda har lokacin bai manta son kudin da Babansu Umma ya nuna ba lokacin aurenta ba,Kuka zaka ga muntasa ta muna yi,idan munce tazo mu bar masa gidan ta kance ba muda Inda yafi nan,sai muce garinsu ai yafiye mana nan,murmurshi take yi ta kallemu tace"kuma da zaku taimaka musu so zasuyi,rayuwarsu tafi tamu tausayi,takan ce ko a kauyenmu dangin mahaifina idan munje na kallesu na kalli ragowar na kanga kamar sunfi kowa babu,ku cigaba da hakuri ko vayan bani,batun sana'a Kawu Haladu da yaje garinsu Kuka kubeya dakakkun su barkono kanwa duk ya hadowa Ummanmu ta rika siyarwa ta soma a sa'a tana ciniki amma da matansa suka fahimci haka suka fadawa Baffa yazo ya hadamu duka ya fara mana fada "Ya za'ayi bamu rasa ci da sha da suttura ba,gama yadda yake da arziki mu rasa sana'ar da Umma zata rika yi sai saida su kuka, gaba daya ya kwashe kayan da Umman ke saidawa ya zuba a store dinmu na kayan abinci.

Yau kamar kullum da shiri na na makaranta na fito babban falo da na tadda Baffanmu zaune a kujera yana kidayawa Yaya Sule da Yaya Abdu da Yaya Bello kudi na hidindimun bikinsu da za'ayi a wannan watan

Gaishe su nayi sannan na kalli Baffa
" Baffa na fito kudin tara"
Yaya Sule ya duba agogon hannunsa ya kalleni
"Yanzu karfe nawa, 8:00 sai yanzu zaki tafi makaranta saboda shashanci...."
Baffa ya dakatar da Yaya Sule
"Au yanzu Hauwa'u yau ma makarar kikeso kiyi,karfe nawa Larai ke gama muku abinci"
Nayi kasa da kaina
"Baffa karfe shida da rabi"

Baffan ya sake kallo na
"Na lura karatun ne bakyaso ko gata ne yayi miki yawa akaiki a mota a dawo dake to yau a kafa zaki tafi haka ma batun dawowa karma kice zaki jira"
Jiki babu kwari na mike banma jira kudin tara ba saboda nasan tunda Yaya Sule ya hadani da Baffanmu biyar dinsa baya bani
"Na tafi"
Nace masu aiko cikinsu ba wanda yayi min koda magana
Har na fice

****
Ina tafiya ina tunanin rayuwar tsakanin gidanmu da makarantarmu akwai nisa bakadan ba,biyar kuma ba nida ita a jaka ta Horn da naji a baya na

Please Login or Register in order to submit comment