Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

To cigaba da bani labari na kagu naji koda sunanta ne"
Ya cigaba da cewa
"Maigadin ne yayi wajensu da har sun fara fitowa daga motar ita magana naga yayi wa wadda nagani din kamar ba zata zoba naga wata mata ta mata magana,sai gata ta biyo bayan maigadin,maigadin daya rigata karasowa yace min cikin girmamawa " yallabai gatanan"yana barin gurin ta karaso tayi min sallama muka gaisa"nace mata Suna na AbdulMalik da wata kanwata dama naga suna kama shine na mata magana"tace min
"Ok nagode,amma yanzu ina sauri ne wani lokacin saika hadaDariya kanwarta ka ko a waya ne nace to ai bani da number dinta"shine ta samin ta fadamin sunanta Safiyya amma fa yarinyar batajin Hausa?"
Dariya Rufaida tayi tace"sai kaita mata turanci"
"Au van dake,anjima zan hadaku a waya"
"To Allah ya kaimu lfy"
Daganan suka cigaba da firarsu zuwan Hajiya Jamila falon shiya tsaida firarsu,Rufaida ta mike taja hannun Yasir suka zasu bar gurin da ta fara ganin hararar da Hajiya Jamila ke aika mata tun kafin aje ko ina,don tunda abin da ya faru dasu da Rukayya komai ya kara sauyawa don habaici zagi bakar magana shan su take gurinta,da yanzu yau kawai ya rage mata tabar gidan zuwa gobe
AbdulMalik ya tsaida Rufaida da cewa
"Ina zaki ne,muna fira"
"Firar me kukeyi kuma,nifa AbdulMalik vangane maka ba fa"Hajiya Jamila tayi maganar rai bace tana kokarin zama
Jin haka yasa Rufaida saurin barin gurin tana ji AbdulMalik na cewa
"Kamar ya Umma vaki gane minba"
Daganan dakin Hajiya Kubra suka shiga aka bude faifan fira


Sadiya Khalil🥰
[9/26, 9:37 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA*



By Sadiya Khalil

50.
Masoyan wannan littafin ina godiya gareku,Allah ya hadamu da alkhairan dake kunshe cikin wannan littafin.

RUFAIDA POV
"Wallahi ina murna yau matuka Samiha
Rufaida da take kwance kan gado da waya a hannunta take furta hakan
Wayar da take a handsfree Samiha tace
" to fa murnar me kike yi"
Tsaki Rufaida tayi
"Kiji 'yar rainin wayau kin manta gobe zan koma gida"

"Na shafa'a 'yar uwa sorry,ke dawa zaki tafi ne?"
"Ba muyi maganar da Abba Bukar ba bai shigo gida ba"
"Ok to ko Yaya Samir na masa waya ya biyo tanan daga sokoto yazo ku tafi tare"
"A'a ki barshi nafi tunanin Abba zaisa Yaya AbdulMalik ya kaini gida"
"To badamuwa Allah ya jikan Yaya Wahid yasa can ta fiye masa nan,Rufaida!na rokeki ki cire duk kan damuwar mutuwar nan a ranki duk da nasan dole ki damu tsawan lokaci amma ki tuna da cewa ubangijin da haliccesa yafi ki sanshi shiya karbi kayansa,haka dukkanmu lokaci muke jira shida ya tafi vaiyi gaggawa ba mu da muke raye amu yi jinkiri ba"
Jikinta duk yayi sanyi ta fadi
"Hakane Samiha,Allah ya sa muyi kyakkyawar cikawa"

"Amin kawata, sannan sai maganar aure don Allah idan kin samu miji kin tabbatar da nagartar halayyarsa ki auresa ki zauna gidan mijinki kiyi hakuri bana so rayuwarki ta cigaba da kasancewa kamar ta yanzu inaso ki samu cigaba ko yaya ne"fadin Samiha

" Hakane kawata nagode da nasiharki"Rufaida da hawaye ya taru idonta ta fadi haka hakika ita tasan taronsu da Samiha na da ban ne,Samiha ta dace a kirata kawa ta gari,batun yau tasan da hakan ba a'a tuntuni kafin su kai ga aure bayan sunyi saboda kaunar da take mata tasa wa 'yar cikinta sunanta ba tare da tasa na mahaifiya ko 'yan uwa gare ta ba,lallai duk inda kawa ta gari takai Samiha takai harma ta zarce,maganar da Samiha keyi ta katse tunaninta

"Godiya ni dake Rufaida ai babu ita,yinta sabo ne fa,idan baki sani ba"

Jin maganar Samiha ta karshe yasa murmushi subuce mata tare da cewa
"To shikenan kawata,ina takwarata"

Batare da taji amsar Samiha ba ta jiyo sallama a falo
"Kawata zan sake kiranki anjima" daganan ta katse wayar ta ajiyeta saman drower din gadon ta yafa mayafi ta fito falon tana amsa sallamar Umar ta gani 'dan wajen Hajiya Kubra ya rissina tar da cewa
"Yaya Barka da dare"

Murmushi tayi
"YawwaUmar"

Umar yace
"Abba ke kiranki yana bangarensa"
Tace masa
"To muji kawai"tare suka kira har bangaren Abba Bukar din sallama suka yi ya amsa musu tare da yi musu izinin su shigo a falon suka same sa zaune a kujera hankalinsa nakan wa'azin da ake a Tv zama suka yi a kasan carpet

Umar ya dago kansa ya kalli Abba bukar
"Abba ga yaya Rufaidan nan na kira ta"

Sai sannan ya dago kansa daga kallon wayar da yake yace
"Yawwa Umar"

Umar din yana jin haka ya mike ya basu guri

Ganin fitar Umar Abba bukar ya kalli Rufaida ya soma da fadin
"Rufaida duk kan mai rai mamaci ne nasan kinyi rashin miji nagari kamar AbdulWahid,sai dai hakuri,da kuma fatan Allah ya sake baki kamarshi ko wanda ya fishi,sannan jiya munyi waya da Kabir akan wani satin zai sa mota ta kawo kayanku kaf na Abujar,kuma ke nasan gobe zaki koma gida,don haka kayanki dana dakinki za'a kawo miki su,ha'de da tumunin takabarki da gadon Yasir duk AbdulMalik zai kawo muku,Abdul saiya cigaba da kularmuku da dukiyar ku tunda yayi girman da zai iya rike dukiya a hannunsa"

Rufaida kanta a kasa har sai da taji Abba ya gama maganarsa ta dago tace
"To Abba,Allah ya bar zumunci ya jikan wadanda suka rasu"
Cikin jin dadi Abba Bukar yake cewa
"Amin Rufaida,yawwa batun tafiyarki AbdulMalik yace baya jin dadi,Hassan ko Hussaini sune zasu kaiki Kanon"

"To Abba Allah ya kaimu lafiya,shi kuma Allah ya basa lafiya"

"Amin Rufaida,kije ki hada kayanki,kar dare ya cika yi"Abba Yayi maganar yana jin dadin yadda Rufaida take bata da fitina balle hayaniya,komai nata mai sanyi ne,shiyasa shima bai ki wa AbdulWahid auren Rufaida ba da ya nuna yana santa saboda yasan ita Alkhairi ce ga rayuwar 'dan nasa,maganar ta ta katse tunaninsa

" to Abba sai da safe"

"To to mu kwana lafiya"
Daganan ta fice tana tura masa kofar karo suka so yi da AbdulMalik da yake kokarin shiga falon shi kuma yayi saurin ja da baya yana dadin
"Subhanallah"
Daganan ya fara kokarin mur'da hannun kofar falon

Rufaida ta kallesa ganin abinda yake kokarin yi tayi saurin fadin
"Yaya Barka da dare"

Ya 'dan juyo da kallonsa gare ta
"Yawwa Rufaida ya Yasir,ya bangansa ba"
Murmushi tayi tace
"Tara tayi ai ya kwanta"
Ok kawai ya iya furtawa

Ganin yanayinsa kamar bayasan firar tayi kokarin barin gurin
AbdulMalik ya bita da kallo a ransa yana ayyana,anya zai iya barwa Zahraddin abinda yake so tuntuni tausayi da soyayarta suka wanzu a ruhinsa wato Rufaida,wata zuciya tana ayyana masa taya ma zai iya bari abokinsa ya auri Rufaida da shine tunanin Zahraddin da ya kirasa dazu ya fada masa, munufarsa akan Rufaida, saidai yana tunanin Zahraddin abokin sane tun yarinta sunyi rayuwa ta tausayawa juna hawayen idonsa da suka fara ta ruwa idanunsa ya goge yana ayyana yanzu indai ya amince shikenan,ya rasa farin cikinsa,fasa shiga gurin Abba Bukar din yayi ya nufi bangarensu

Washe gari

Rufaida ta karaso falon cikin shigar leshi ta riga da siket da hijabinta milk colour dogo har kasa da ya haska farar fatarta kyawunta na Hausa fulani ya bayyana sosai hannunta cikin na Yasir da shima ta shirya sa cikin shadda ruwan kasa mai haske sosai
"Badai har kun fito sai tafiya Ba,wannan sammako haka"
Hajiya Kubra da murmushi fuskarta take fadin haka
Hajiya Jamila ta saki dariya ta saka baki
"Ke ko Kubra tayi sammako mana tanaso taje ta tarar da karuwar uwarta"

Jin maganar Hajiya Jamilar ta dago ta kalleta ta goge hawayenta tanaji yau bazata hakura a cigaba da fadar aibu akan mahaifiyartaba ai uwa uwace ko ya take kuwa, ta dan yi murmushi mai ciwo ta soma fadin
"Umma kenan kalmar karuwanci da kike fada Ummin tayi ,mantawa kikayi kece uwar dakinta a can wajen karuwancin"

"Hajiya Jamila jin karashen zancen Rufaida yasa ta mike a fusace tana fadin
" Allah ya rabani da karuwanci,ni zaki hada da wannan kalmar shaidaniyar yarinya"tana fadin haka tayo kan Rufaidan zata doketa da sauri Hajiya Kubra tasha gabanta
"Laifin mai ta yi miki zaki doketa,kina tunanin ko jikar kice zaki riqa fadar wani abu kan mahaifiyarta tun bata tanka wa ai kinsan wata rana dole ta mayar miki da martani,bare ma yarinyar nan ta kawar dakai fiye da tunani"fadin Hajiya Kubra

" ki matsa min a hanya na ko muyi fatarta ni da ke,yar da na haifa zata hadani da kalmar karuwa,karuwa fa!,bama karuwa ba nufinta nice uwar karuwan" fadin Hajiya Jamila ta karasa zancen tana nuna kanta

Dariya Aunty Amarya tayi da shewar ta kuma ja tsaki
"Dan Allah matsa ki bata gurin Maman Umar,naga karyar haukan matar nan,tazo ta tabata idan ban 'balla banza na zubar ba,banda ke din banza ce ai maganar Rufaida ba karya a cikinta,indai bake ce uwar karuwan ba ina kika san Ummi Hauwa'un tayi karuwancin,indai ba an taba yawata duniyar ba kema"fadin ta tana sake cigaba da wata dariyar

Kan Aunty Amaryar Hajiya Jamila tayo a fusa ce tana fadin
" Amina ni kika samu damar fadawa magana"daganan ta soma kokarin rike hannunta zasuyi danbe

Shekeke Aunty Amarya tayi tana kallonta ta janye hannunta daga na Hajiya Jamilar
"Kinga malama karki sake hannunki ya taba nawa ma bare harkiyi kokawa dani,don mijinki da kika raina shine dai-dai dake bani Amina ba,don ni ko maganar banza kika fadamin sai kinyi dana sani wallahi,ke kanki kin san niba ajinji bace,dana san haka kike karya da banyi gigin hada gida da keba wallahi,fitinanniya duk halarcin da mijinki ya yi miki ya debo 'yan uwanki ya rike bai ishe ki ki zauna dashi lafiya ba sai kin masa kinwa 'yan uwansa"

Hajiya Jamila jikinta duk yayi lakwas don tasan duk da Aunty Amarya ba girma gareta ba sarai zata iya doketa tayar da ita abanza don ita dama ba karfin gare ta ba,kuma ko magana sai Aunty Amarya ta caba mata wadda bata yi tunani ba,don ita dama wanda ta raina take wa wulakancinta

Su Hajiya Kubra da suke tsaye circirko Aunty Amarya da take jiran taji Hajiya Jamila ta fada mata wata maganar ganinta tayi shiru kamar gunki, yasa su kokarin fita raka Rufaida harabar gidanku inda zata shiga mota da Rufaida yanzu take jin zuciyarta wasai kamar ta cire dutse a zuciyarta ta,don koba komai yau ta maida martani inda ya dace ace ta dade da mayarwa.

AbdulMalik da yake tsaye bayan kujerun falon da tunda aka fara maganganun yake tsaye yana jinsu shi wata maganar ma dariya ta rika basa ya gimtse dariyarsa ya karaso inda suka bar Hajiya Jamila tsaye kamar gunki ya dafa ta yana fadin
"Kiyi hakuri Umma ki zauna"
Hannunsa ta cire daga kafadarta
"Ka gama dariyarka kenan?"

Ya dan zaro ido da mamaki kan fuskarsa shi baisan Ummantasu tasan yana gurin ba
"Umma dariyar me?"

"Ta gidanku ko nace ta ubanka,da ya gama bata ni gurin matansa,nufinka banga sanda kazo nan bane Malik kenan kanaji ana cin mutunci na,maimakon kazo ka shigarmin saika tsaya yimin dariya,saboda baka dauke ni uwaba ko?"

Kai girgiza yana cewa
"Ko 'daya Umma ai ita uwa uwace,amma dai ni kinsan bana goyon bayan rashin gaskiya tunda ke kika jasu tunda basu saki a maganarsu ba kika shiga,shigarma da kika yi ba Alkhairi kika fada a maganar ki ba,sannan Aunty Amarya ba karya ta fadaba abinda kike wa Abba ta fada kuma a gaban kowa ma yi masa kike,kuma ba ruwan Abba bashi ke fadamusu ba gani suke kinayi"

"To Ubana tsare ni kamin fada,wallahi Malik bansan wanne irin da na haifa ba da baya kishi na....." Jin ta fara sababi yasa shi saurin barin falon ya fice harabar gidan da ya tarar Rufaida har ta shige gidan baya Yasir a gaba ,Hassan da da Hussain ne zai kaita suka tafi wata unguwa da Abba Bukar,yana wajen Boot din motar yana kokarin rufewa alamun ya gama zuba kayan Rufaida dana Yasir sai tafiya
AbdulMalik ya riko hannun Hassan da yake kokarin bude kofar mota ya masa ra'da Hassan ya dago fuskarsa ya kalli Rufaida yana fadin
"Kace ta kusa zama Auntynmu" AbdulMalik ya maka masa a baya duka yace"kaifa matsalarka ba'a sirri dakai
Su Hajiya Kubra suka yi dariya

sirrin mai za'ayi dani kuwa bayan abin alkhairi ne ya samu,Aunty kinsan mene ya faru"fadin Hassan

Aunty Amarya ta girgiza kai

Hassan yace na hannun damar Yaya Malik ne Yaya Zahraddeen,yaga Rufaida yace ya 'kyasa idan ba ita ba sai rijiya"
Gaba 'daya suka sa dariya banda Hajiya Kubra da Hussain ya sameta da maganar shifa yanason ya auri Rufaida kuma ita ma ta basa goyon vayan hakan saboda yarinyar akwai nutsuwa da sanin yakamata ga rashin hayaniya kuma uwa uba 'yar uwarsa suce ,to kuma yanzu ga wannan ta fara kunno kai duk da tasan baza'aki na gida aba na dawa ba inba daurowa tayi ba,zata fada Hussain yaje mata da soyayyarsa gare ta ko zai dace,ko a ina ma Zahraddin din yaga Rufaida oho Hajiya Kubra tayi wannan tunanin

Rufaida da take jin abunda suke fadi ta danyi murmushi kasan ranta tana tuna kamannin Zahraddin kyakkyawane ba laifi,gashi da son barkwanci,sai dai bataji a yanzu zata iya sa wani a zuciyarta guri kusa saboda tayi babban rashi da haryau bata gama jinyar zuciyarta ba ta rasa miji nagari a rayuwarta,saidai tunowa da Nasihar da Samiha ta mata jiya yasa ta kauda wannan tunanin sai dai zatayi addu'ar Allah ya yi mata zabin Alkhairi a rayuwarta jin Hassan ya tada motar da bata ji shigowarsa ba yasa ta dawowa daga tunanin da ta tafi da addu'a su Hajiya Kubra,Aunty Amarya, AbdulMalik suka bisu dashi suna daga musu hannu har ya fara tafiya ya karasa wajen bakin gate maigadi ya bude musu gate din motarsu ta fita ya bisu da addu'a
[9/29, 7:00 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA*

By Sadiya Khalil
51
RUFAIDA POV
Jin Hassan ya taka burki yasa Rufaida 'dago kai ta kalli gefen titin da takai kallonta gasu Hassan da ya faka motarsa da Yasir keta barcinsa tunda sukaf fara tafiya shi dama Yasir baida wuyar barci ta soma da fadin
"Yaya Hassan ya naga ka tsaida motar,a gefen titi lafiya kuwa?"

"Eh inaji dai kamar tayar mu ce tayi faci,amma bari na fita nagani Ku zauna basai kunfito ba"yana gama fadin haka bude murfin motar ya fito

Rufaida na cewa
" to Allah ya tabbatar da lafiya,ya kuma kara tsare mu"

"Amin ya rabb"

Yana fadin haka ya shiga duba tayoyin motar tasa bai jima yana dubawa ba ya leko da fuskarsa cikin motar daga gefen titin yana fadin
"Kamar ko na duba dazu,tayar ce tayi faci ko"

"Subhanallah,To yanzu ya za'ayi gashi mun baro zariya"

"Zan kira wani mai yi mana gyaran mota sai ya hawo machine ya zo Inda muke da kayan gyaran,dama ban tsaya duba motar ba muka taho"yana fadin haka ya zura hannunsa a aljihu ya fito da wayarsa ya shiga dannawa ya lalubi lambar mai gyaran ya kira sa yayi masa bayani ya sake shigo da kansa cikin motar yace
"Ya ce min yana zuwa"

"To Allah yasa yazo da wuri"
fadin ta
"Amin"
Sunyi kamar Rabin awa agurin suna jiran mai gyaran amma babu ko alamunsa
Ta dan leqo daga cikin motar da Hassan yake waje har lokacin a gurin tana cewa
"Yaya Hassan anya zaizo kuwa?"

Nima abinda nake tunani kenan,bari na sake tabasa"yana fadin haka ya dauko wayarsa ya soma danna lambarsa

"A'a Yaya kawai dai a kira wani Yaya Hassan,yaci ace tun dazu fa yazo"

Dariya yayi ka'dan da cewa
"Kin ka gara dai,kije kika su Ummi ko?"

Murmushi tayi
"A'a kawai dai"
jin Horn din da ake abayansu yasa Hassan maida abinda yayi niyyar fada cikin bakinsa ya juyo ya kalli motar Prado baka"
Ganin ana kokarin fitowa daga motar yasa Hassan fasa karasawar da yayi,Dady Jabir ne ya fito daga motar a mazaunin driver da fara'arsa ya karaso Inda Hassan yake tsaye yayi masa sallama ya mika masa hannu,
Hassan da murmushinsa da baikai zuci ba ya amsa sallamar Dady Jabir ya mika.masa hannu sukayi musabiha ,daganan Hassan ya dan rissina cikin nuna girmamawa Hassan ya gaida Jabir din ganinsa matsayin babban mutum,kuma ya girmemasa Dady Jabir,don zai iya sa'an Abba Bukar duk a cikin tunanin Hassan

"Yadai 'dan samari maike faruwa, yanzu 'diyata ta hangoku ta cikin glass din mota" fadin Dady Jabir

Hassan da maganar ta katse tunaninsa ya dan sake sakin fuska jin maganar da Dady Jabirun yayi yace
"Eh dama Yallabai motar muce tayi,faci amma mun kira mai gyaran yace mana yana kan hanya,to mun jima muna jiranshi har yau bai kara soba"

"To Allah ya kiyaye gaba,amma wanne gari kuke shirin zuwa?"

"Eh kano zan kai kanwata ne"

"To Allah ya kara kiyayewa"

"Amin"

Har Dady Jabir ya juya baya ya soma tafiya ya 'dan dawo da baya yace
"Naji kamar kacemin kanwarka zaka kai"

"Eh yalla'bai"

"To kenan kai rako zaka yi kenan ma?"

"Eh to yalla'bai zan iya cewa hakane"

"To indai kana ganin babu damuwa,zamu tafi tare,in yaso kai kaje daukarta idan zata dawo"

Rufaida da take jiyo maganganunsu Dady Jabir da Hassan da mutumin da yayi mata kwarjini, wanda daga kallo guda idan kayi masa zaka tabbatar kudi da hutu sun ratsashi,haka ma a siffar sa zakasan bafulatani amma jin yace bata san shi ba yace su shiga motarsa ya kaisu Kano yasa jikinta yin sanyi,don yanzu dan adam ba abin yarda ba ne dukda akwai na garih amma sunyi karamci ta tsaya jin mai Yaya Hassan din zaice masa sai kuma taji Hassan din fadin

"Yalla'bai ayi haka kuwa,karmu dora ma nauyi mai garan ya kusa zuwa ai"

Murmushi yayi kana yace
"A'a kaidai kace baka yarda dani ba ko?,nima yarinyata zan kai Kanon gidan kanina,ka ganta can a motar"ya karasa zancen yana nuna masa cikin motar da Safiyya ke zaune ta bude kofar bangaren mai zaman banza da take itama tana hangosu da ga cikin motar

" a'a yalla'bai babu alamar rashin yarda a tare dakai ai"

Murmushin jin dadin kalmar da Hassan ya fadamasa Dady Jabir yayi,dukda yasan kasan zuciyar Hassan din sam baiyi kama da furucinsa na zahiri da yayi ba,amma bai nuna masa rashin yarda kiri kiri ba,Aljihun gaban rigarsa Dady Jabir ya dauko ya mikawa Hassan
"Kaga wannan kati nane, ka ajiyesa a hannunka,har mu isa Kanon,idan kaga wata matsala,ka kira gurin aikina kasanar musu"

Katin Hassan yasa hannu ya karba ya fara dubawa saida ya gama karantawa ya dubi Dady Jabir din
"Yalla'bai ashe kai jakadanmu ne 'yan Nigeria a India"

Ya murmusa yace
"kwarai kuwa yanzu to zaka barni na tafi da kanwarka,dan naga kamar a baya kana shakku a kaina"

"Ko 'daya yalla'bai bahakabane,bari nayi mata magana"

Bai jira amsar da zai basa ba Hassan ya karasa jikin motarsa ya shiga da sallama Rufaida da taga ma jin mai suke cewa ta amsa masa gamida cewa
"Yaya Hassan kana gani babu matsala mu bisa"
Ya juyo da Kansa yana kallonta
"Eh babu wata matsala a katin da yabani akwai address dinsa da komai,kuma bai kamata muyi masa mummunan zato ba daga yi masa kallon farko kinsan duk yadda rayuwa takai da lalacewa akwai na Allah"

Tace masa"Eh hakane"

"Yawwa kinga muyi addu'a kawai,tunda kinga mai gyaran baida niyyar zuwa ni kuma bansan wani mai gyaran ba bayan shi,ki fito kinga mu yake jira"Hassan na fadin haka ya soma kokarin kinkimar Yasir yayo waje dashi

Jikin motar Dady Jabir yayi da shi kai tsaye Rufaida ta fito ta bi bayansu,a bakin motar suka sami Dady Jabir din tsaye yana jiransu idanunsa ne suka kai kan yasir da yake kafadar Hassan,ba tare da yaji gaisuwar da Rufaida ke masa ba yace
" ashe ma harda yaro bari na yiwa yarinyarta wa magana ta koma baya sai a kwantar da shi a gaba kaga idan ya farka sai na samu abokin fira"yayi maganar da murnushi bayyane a fuskarsa,cikin motar ya leka yayi wa Safiyya magana,sai gata ta fito daga motar cikin kayanta Pakistan riga da wando sai mayafin kayan
Hassan da idanun Safiyya suka sauka akansa tace wa
"Morning"
Hassan yayi dan murmushi yana kallon Safiyyan yace
"Morning 2"
Daganan Safiyyan ta bude baya ta shiga
Hassan yayi kokarin kwantar da Yasir a gidan gaban
"Suna da kaya ne" Dady Jabir yayi maganar yana kallon Hassan,
Hassan yace
"Eh yalla'bai"

"To muje a daukosu"
Dady Jabir da suke kokarin brain gurin ya dan kallo Rufaida da kallo guda ya mata ya fahimci yarinyar da alamar nutsuwa tare da ita kuma yaji lokaci guda ta shiga ransa yace
"Shiga motar mana,Safiyya bude mata ta shiga"

Rufaida ganin an bude mata murfin motar ta shiga da anbatan Bissimillah hadi da yin sallama
Safiyya da take can gidan baya ta amsa mata sallamar
"Rufaida ta dan waiga ta kalleta tace
"Sannu ,Ina kwana"
Safiyya tace
Yawwa sannu kin tashi lafiya"
"Alhamdulillah"fadin Rufaida
Daganan Safiyya ta maida hankalinta ga danna wayarta itama Rufaida ta juya tana kallan su Yaya Hassan suna dauko kayanta,saida suka gama Dady Jabir ya shigo motar,Hassan ya leqo da kansa jikin glass din da Rufaida take yana fadin
" ki kula da kanki da Yasir,please da kun isa kimin waya"

"Insha Yaya Hassan yanzu waye zai kaika gida da motar,zan kira Yaya Malik sai aja motar mu tafi da ita,Allah ya kiyaye hanya ya tsareku"

"To shikenan,Amin Yaya Hassan, nagode"
Safiyya ta dan murmusa da take jiyo abinda suke cewa ta cigaba da danna wayarsa

Daganan ya juya ga Dady Jabir ya yi masa godiya da addu'a ,sai da yaga tashin motarsu sannan ya fara danna wayarsa yasa kunne Rufaida tana hangoshi ta glass din motar da sanyin Ac motar ya fara ratsata tace
"Ina kwana Abba"
yana murmushi jin Abban data kirasa yace
"Lafiya kalau,yayi maganar yana cigaba da tukinsa

Sunana Safiyya,kefa Mene ne sunanki"
Taji muryar Safiyya na fadar haka
"Rufaida" ta fadi haka tana kokarin zage zib din jakarta da take kara alamun kira taji Safiyya ta canza yare zuwa indiyanci da batasan mai take cewa ba
Rufaida ta daga wayar ganin mai kiran tayi saurin dagawa tasa handfree da sallama ta dora da cewa"Yaya ina kwana"
"Lafiya kalau,kun taho ne?"
"Eh Yaya Abdul muna hanya"
"Dama Ummi tace na kiraki naji tayi miki alala"
"Eh a yimin kasan na dade dama banci shi ba"
Tsaki Abdul yayi yana fadin
"Yanzu fa za'a fara yi mana alala a gida tunda zaki dawo"
"Kai Yaya nifa kadai akewa ko nayi abu na"
"A ina,ni kinga ina Yasir yake"
"Ya kwanta barci"
"To ki kula da kanki,munyi waya da Yaya Hassan yanzu yayi min bayani"
"Insha Allah,Allah ya tsare Ku ya kawoku lafiya daganan ya katse wayar Rufaida ta sauke wayar tana murmushi
Yasir ne ya tashi barci ya fara waigen Maminsa ganin ya hangota yace
Yasa shi kokarin haurawa inda take,Dady Jabir ya kallesa yace
"Aboki ina zaka?"
Yasir yace
"Gurin Mami"
Daganan ya haura ya fara waige waige yana cewa
"Mami ina Dady Hassan"
"Ya koma gida"
"Safiyya da idanunta suka sauka kan Yasir tace
" wannan kyakkyawan Boy din fa Masha Allah na waye,ko kaninki ne"
Murmushi Rufaida tayi kawai
"Safiyya tayi dariya tace
" yaron kine kenan,kyakkyawa dashi Masha Allah "
Ta mika hannu ta dauki Yasir zuwa inda take ta fara ce masa"
"Ya sunan ka?"
"Yasir"
Sunan Abbanka fa jin yayi shiru yasa Safiyya ita ma kyalesa saboda karar wayar ta da taji ta mika hannu ta dauki wayar tasa a kunne
Ta fara magana cikin yaran Hausa.
[9/30, 7:57 PM] Sadiya Ibrahim Khalil🤍: *JININMU 'DAYA*

By Sadiya Khalil🖤

52.
Hudu na yamma suka iso Kano Dady Jabir ya kallo Rufaida yana fadin
" a wacce unguwa kuke ne"
Rufaida da ta soma jin barci taji maganar Dady Jabir din tayi saurin fadin
"Muna Rijiyar zaki"
"Dady Jabir yace
" kash gashi mu a nan Zaria road gidan kanin nawa yake, bari mu fara zuwa kuyi sallah,mu huta sai mu kaiki,tunda unguwarku tana gaba da nan"

Rufaida cikin nuna girmamawa tace
"A'a Abba dama ka bari saina kira a kaini gida"

Yace
"A'a ki bari dai muje muga gidansu abokina"

Safiyya da take danna wayarta tace
"Wallahi kuwa Abba,Dady kaga idan muka ga gidan kafin mu tafi saina je,inason yaron dama ta bamu shi"

Dady yayi dariya
"To gaki gata in tayarda ta baki babansa ba"
Rufaida murmushi takeyi , da take jin maganar da suke tattaunawa

A kofar gate din gidan yayi parking yayi Horn maigadin gidan ya bude musu gate din gidan suka shigar da motarsu da 'yan sandan da shigarka cikin gidan zaka tarar dasu zai tabbatarmaka gidan babban dan sanda ne Rufaida da ido take bin ko ina na gidan da kallo
Har suka karasa parking space sukayi parking da suke hango mutanan gidan sun fito tarbarsu ta glass din motar

Suna fitowa Husna ta rugo ta rungume Safiyya da murnarta
Ammar da Abida suka rungume Dady Jabir suna masa oyoyo
Daganan suka koma suka rungume Safiyya suna murnar ganinta
Momy Hannatu da take gefensu Husnan tace
"Yaya Jabir sannu da zuwa"
Ya amsa da fadin
"yawwa Hannatu"
Rufaida da take tsaye tana kallonsu gwanin sha'awa
Dady Jabir ya maida duba inda su Rufaidan suke tsaye
"Gafa baki nan kunyi,tare muke, kinga wadancen sunyi gaba sun barmu tsaye" yayi maganar yana nuna su Husna da su Abida da su kayi cikin gidan

"Momy

Please Login or Register in order to submit comment