Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa kaduna tun barinku kasar nan amma inajin labarin bata shekara biyu bata zo taga uwarta ba saboda ni bata daukeni uwa ba duk irin halaccin dana yimusu daga ita har hafsatun wadda a kaf zuriyarmu babu wadda nayima abinda nayima hafsatu a matsayinta na yar uwata mafi kusanci a gareni amma yau ga irin abinda kajanyo ma kanka ka janyo ma zuriyar ka haba *Abdur ra'uf* .jin ta tsagaita maganar tatane yasa shi mikewa yana fadin haba Hajiya duk mai ne ne anfanin fadin haka inji AbdulRra'uf din da yamike yana kokarin daukar wayarsa ya cigaba dacewa tun a lokacin da abun yafaru yakamata aman ta da maganar.hajiyar ce ta kara dacewa naki mantawa da maganar idan kai bakasan ciwan kan zuriyar ka ba aini nasani nasan tozarcin da akamana nidai hada ji'bi da zuriyar hansatu bai kareni da komai ba wato ma kawai nabar maganar . saurin ficewa daga dakin yayi danshi dayasan kalaman na hajiyar yana da cikin mizanin muni nada ga gareshi da baiyi jimirin zama a 'dakin nashiba shidai sam kalaman hajiyar sun masa matukar munin da bazai sake son jinsu ba wadda shidai sam hajiyar bata kasance macen da zai duba amatsayin uwa ga mahaifinsa ba domin da hakan yakasance yasan tabbas bazata zamanto
Mai sake kokarin jefa zuciyarsa tasa bisa ga kangin damuwa ba duba da irin kiyayyar da aka nuna masa a bangaren gidansu Rufaida wanda shi yasan ko da bai san dalili ba Ahalin nasane silar rugujewar farin cikin nasa a karo nafarko yarasa yarasa masoyiyarsa mai matukar son farin cikinsa wadda tarbiyyarta ce silar son cigaba da zama da ita na tsawon har abada yana cikin tunanin ne yakarasa bude kofar wani daki yashiga da sallamarsa. Gefen sallayar da yasamu dattijuwar matar fara yazauna yana fadin ammi sannu tasbahar hannunta ta ajiye akasa tana mai amsa masa sallamartasa dafadin yawwa *RA'UF* kafin tadora dacewa sarkin a zama har naga kashirya tun a subar fari tafada tana mai kau da kanta daga kallonsa *RA'UF* 'din ne ya kalleta yana fadin tuba nake *Ammi* tun 'dazu nagama shirya komai wannan rigammiyar tsohuwar ce ta tsaidani nagama shirina ta tsaidani *Ammi* ce ta dubesa tace kaidai kasani yawwa *Ammi Ra'uf* ya anbata dama har yau Hajiya na nan da fadan ta mara karewa idan ta fara Dariya abin yabawa *Ammi* tace sai hakuri zama da hajiya. Ina fata dai ka kammala shirya kayan naka eh ammi danladi ma har yasa su a mota.




Ko a jikin motar da hajiya tafito yi musu rakiya ita da sauran mutanan gidan fadan ta hau yi tana fadin idan kakoma kasar fararen motar ka mutu babu aure kannen ka kuma baza su fasa aure ba kamar yadda dai Ahmad yayi kafin tajuya ga Ammi tana fadin ke kuma banaso kodai da rana daya kisake zuwa daga ke har dan nawa dakika shanyeshi kubari sai mutuwata kuzo.ita dai Ammin ba tace ko mai ba sai kanta dake kallon kasa Baffa Alhaji da sai yanzu yasa baki da take gefen hajiyar ne yace haba hannatu kedai sam bakya iya hakuri ne da harkar duniya komai bazaki mikasa ga Allah ba sai kin nemi wani abu da zaki fada akanshi maine laifin yaran nan jabiru bata tsaya jin karshen maganar ba ta bar gurin Mama Suwaiba tace to babban mutum Allah yaki yaye hanya amin umma Ra'uf ya fada yana murmushi dukda yadda zuciyarsa bata masa dadi amma yanajin dadin sunan nan da Mama ke kiransa dashi anan motar ta tasu ta tashi duk zuciyoyi babu wani dadi ba daga shiba har ga zuciyar Ammi da take mahaifiyarsa suna barin gidan Malika suka nufa daganan suka nufa dako zama busu yiba Safiyya ta fito da Jakarta da take ja Aunty Malika da yaranta suka fito musu rakiya harabar gidansu.
***
Wayarsa yake dannawa da yake kwance a falon gidan Bello dake Abuja sai dai wayar kawai take dannawa amma tunaninsa naga Rufaida fuskar Rufaida ita yake gani a idanunsa,shi kansa yasan bakaramin so yakewa Rufaida ba
Bai saurari lemukan da Bello ya shigo musu da suba ya mike yabar musu falon ya shige ya cigaba da tunaninsa yanasan kiran Rufaida saidai idan ya tuno wayarsu da Ahmad a dazu da yake shaidamasa aure za'a yiwa Rufaida zata auri cousin dinta saiyaga babu anfanin kiran idan yakirama bazai anfanesa ba kiran dalilin da yasa ya hakura yayi kwanciyarsa da addu'o'in kwanciya barci a bakinsa.
[8/24, 7:48 PM] Sadiya Ibrahim Khaleel: *JININMU 'DAYA*

By Sadiya Khalil😘


*Afuwan masoyan littafin jininmu 'daya kuyi hakuri bisa tsaikonsa ya Allah ka bamu ikon rubuta abinda zai anfanemu duniya da lahira*

*Note ABDULAHAD shine ya koma ABDULWAHID*
36

Sai karfe goma saura Rufaida ta kunna wayarta da tagama shirinta na tafiya gidan Gwaggo da Abba Bukar ya umarci ta cigaba da zama har ayi bikin a gidan dan yasan fitinar Hajiya Jamila shi kuma mutum ne mai ra'ayin rikau zai wuya yayi magana ya canzata,jiran Abdulmalik take yazo ya su tafi sai goma saura ya shigo gidan ya dauki kayanta yasa a boot suka nufi gidan Gwaggo
A kofar gidan Gwaggon AbdulMalik ya tsaida motarsa da gidan yake ginin blo da blo da a kofar gidan sukaci karo da Malam suna fira da wasu dattawa AbdulMalik ne yayi gaba da kayan Rufaida ta tsaya suna gaisawa Malam shida dattawan cikin wasa da dariya
Sallama yayi ya shiga gidan Gwaggo da zaune kujera tana dukar dakanta tana tsintar wake jin muryar AbdulMalik yasata dagowa cikin fara'a ta amsa masa tana yi masa maraba
"Amsawa yayi ya aje Jakar ya aje ma Rufaida kofar daki
Tsintar waken Gwaggon ta'aje ta mike yayi hanyar daya daga cikin dakunan gidan da suke a Jere tana kokarin shigewa dakin tace
"Shigo daga ciki mana"
Abdulmalik yace"a'a Gwaggo daukomin tabarma na zauna daga nan ga darbejiya nasha iska naji garin yau antashi da zafi zafi"dakin ta ka rasa shiga ta fito cikin sauri dauke da tabarma a hannunta
"Nayi zaton ai kun rikemin jikartawa nayo muku takakka" Gwaggo take fa'dawa AbdulMalik haka da take kokarin yi masa shinfidar tabarmar
"Haba wane mu Gwaggo ai Rufaida mallakinkuce keda Malam" AbdulMalik yayi zancen yana aje jakar Rufaida a tsakar gidan ya karasa kan shimfidar da ta masa ya zauna
Gwaggo tace "kwarai kuwa fa'di ka kara,ina Rufaidan ne banga ta shigo ba" tayi maganar tana karasa wajen tulun ruwa
"Tana can waje Malam ya tsareta da surutu"
"Ai ko rabinka baiba India a surutu me nasan" tayi maganar tana karasowa inda AbdulMalik din yake da kwanon silba da cikosa da ruwa takawowa AbdulMalik tanemi guri gefe ta zauna kusa da shi
Baikai ga sake yin magana ba suka ji sallamar Rufaida
Amsa mata sukayi inda AbdulMalik ya kalleta
"Sai yanzu tsohon ya barki ki shigo kenan kinaso ki kwacewa Gwaggo shi ko"
Rufaida tace
"Ai yayi min tsufa"
"Naji dai Ku varmin kayana na ni inasan shi duk tsufanshi" Cewar Gwaggo
"Ai Gwaggo dankema kinsan tsohuwar ce"Rufaida tayi maganar tana dariya
" sa'arma duk zaku tsufan kuma indai da rayuwa.
Abdul malik ya 'dauki ruwan ya'dan kurba ya aje
Ya canza maganar yana cewa"wannan ruwa haka Gwaggo sanyinsa kamar na fridge"
Gwaggo ta murmusa
"Kai AbduMalik banda sharri fa ina zaka hada sanyin tulun ruwa dana fridge kai dai tsokanarka kace"
Dariya yayi yace "au Gwaggo bamu gaisa ba"
A tare shida Rufaida suka gaisheda Gwaggon
Inda AbdulMalik ya cigaba da cewa
"ina dumamen tuwon ne yau naji biki min tayi ba"
"Gashi can a murhu a sako ma ko"
"Anya Gwaggo tuwon nan zai samu shiga naci girkin Mama Kubra ya cikamin ciki kuma sauri nake yau munada lecture karna makara
Rufaida da bata ce komaiba tunda suka fara maganar batasa baki ta mike daga zaman da tayi ta shige dakin Gwaggo Gwaggo ta bita da kallo ta juyo ta maida dubenta ga Abdulmalik
Shima maida kallonsa yayi ga Rufaida da take kokarin daga labulan dakin
Ya maida kallon ga Gwaggon cikin yanayin tausayawa Rufaidan ya dan sassauta murya
"Gwaggo ya kamata ku daure ku aura ma Rufaida zabin ranta gudun karta shiga wani hali,duba da ko Yaya Wahid kunsan ta aura bawai da'dinsa zata ji ba saboda Umma kuna sane da duk abinda ke faruwa
Murmushin Gwaggo tayi
"AbdulMalik kai kanka kasan da inada iko da Bukar da Aliyu in fadamusu suji da sun amince da zabin nata amma kememe sunyi kunnen uwar shegu da maganata suka nuna ban isa dasu ba,ka kyalesu duk abinda suka jawo ma 'yarsu suya shafa"
"Hakane Gwaggo amma ina gudun abubuwan da zasu iya zuwa ki dawo kina sane da halin Umma amma kiyi tunani, ni bari na tashi daganan makaranta zan wuce idan nadawo zan biyo" AbdulMalik yayi maganar yana mikewa tsaye.
Itama mikewa Gwaggo tayi don ta rakasa"
"To Allah ya taimaka aidama nasan tunda 'yar uwarku tana gidannan zamu rika ganinku tunda albarkacin kaza kadangare kansha ruwan kasko"
"Au haka kikace Gwaggo nasan da Malam yana nan bazai ce haka ba"
"Aiko har gwara ni dashi ma"
Takarasa maganar tana kokarin karasa rakashi zauren gidan
Har zai fita yace"to Gwaggo tunda tsohon yaji tsoron shigowa bari na samesa a wajen, ita kuma Rufaida tunda ta gudu daki nakawota gida shikenan"
Dariya Gwaggo tayi tace
"Ai ni Mijina ba matsoraci bane bayaso ya tsorata ka da maganganunsa masu karsashi ka kasa juresu ka gudu dukda yanzu ma da vai shigo ba gashi harka gudu kana tsoron gamuwarku,Rufaida kuma kunfi kusa duk abinda zaka ce mata"
"Gwaggo kenan bari dai na tafi saina shigo anjima zan mayarmiki da martaninki"yayi dariya yana karasa ficewa waje
Addu'a ta bisa da ita ta dawo cikin gidan datayi kacibis da Rufaida
" Lah Gwaggo ina Yaya AbdulMalik 'din na fito da niyar muyi sallama ashe harya tafi"cewar Rufaida
"Dake zai zauna zaman jira ana firar arzi'ki kin tashi fu kin shige daki kamar wadda aka tsikara"Gwaggo ta karasa maganar tana cire kofin saman tabarmar ta ajesa gefe ta fara nanna'de tabarmar
" Gwaggo shiga nayi amsa waya fa Yaya Abdul ne ya kirani"
"Oho miki dai kina kokarin sa damuwa a ranki bayan addu'a ce mafita,ki kuma dauki abinda Allah ya kaddara a rayuwarki yafi duk wannan tarin damuwar"
"Hakane Gwaggo kuma insha Allah zanyi yadda kikace dama ba wai kin Yaya Wahid nake ba"
"Yawwa jikalli ta ki dinga mi'ka lamuranki ga Allah"
Da wannan maganar Gwaggo ta shige daki da tabarma rike a hannunta
Rufaida ta nufi kitchen dan marmarin cin tuwon Gwaggo take.

*TEAM OF RUFAIDA*
*TEAM OF ABDULWAHID*
*TEAM OF RA'UF*
Muje zuwa anya kuwa....me zai faru a next page ya kuke tunanin Hajiya Jamila zatayi idan taji labarin saka ranar wannan auren
πŸšΆπŸ½β€β™€οΈπŸšΆπŸ½β€β™€οΈπŸšΆπŸ½β€β™€οΈπŸšΆπŸ½β€β™€οΈ


More comment's more typing
[8/24, 10:52 PM] Sadiya Ibrahim Khaleel: *JININMU 'DAYA*

BY SADIYA KHALIL



37.

"Ina Rufaidan ne yaran nan sai jiranta yake ta shanyasa banda da dare ne ai sai ya bushe"
Gwaggo tace
"Kwalliya ai take masa karya 'dauketa budurwar kauye yace ya fa....
Gwaggo da bata karasa maganar ba Rufaida ta karasa fitowa daga 'dakin da cikin shigar atamfa riga da siket da hijabinta iya gwiwa da hasken lantarki ya sa Gwaggon hangota daga inda suke zaune itada Malam suna fira
Inda suke ta 'karaso tana cewa
" kai Gwaggo mai naji kina cewa,Yaya Wahid 'din zan tsaya yi ma kwalliya,kamar bako"
Gwaggo tace
"Bama dole ba yarinya kar yace ya fasa, kuma ni da ku'di aka ha'dani bazan iya nemo wancen dan kasar turawan yaron ba "
Ba tare da Rufaida ta sake furta komai ba tabar wajen su Gwaggon da ko saita dawo bata tsaya ce musu ba dan an ta'bo mata abinda take kokarin mantasa a babin rayuwarta dukda tasan da kamar wuya kaunar Ra'uf daga jininta yake ba daga zuci ba,tasan zata iya auran wani amma kuma bazata iya manta Ra'uf ba dan ya zama kamar 'dan uwa a gareta take ji a ranta
Tana jiyo maganar Malam da yake cewa
"Haba Zainabu ke maiyasa kika fiye kato 'barar zance kamar yarinya tunda batun yaron nan ya riga da ya wuce"
Ba tare da taji mai Gwaggon zata ce ba ta karasa zauren gidan da haske ya gauraye sa sallama ta masa da ta samesa tsaye cikin shigar wando da riga na yadi tazarce kayan isassu ya har'de hannunsa saman 'kirjinsa da ya soma yanke tsammanin fitowar Rufaida dukda bawai lokaci ne ya kure ba sai dai sanin wancen dalilin da yake tunanin zai iya hanata fitowa sai kuma yaga akasin tunaninsa aje wancen tunaninsa yayi ,ya amsa mata sallamar da tayi ya kuma kasa dauke kansa gareta harta karasa shigowa cikin zauren nesa dashi sosai ta tsaya
Murmusawa Wahid yayi kafin yace "barka da fitowa Matata Insha Allah"
Cikin zaro ido Rufaida ta 'dan kallesa lokaci guda da ta maida kanta 'kasa
"Eh mana bikisan ansa ranar bikin mu ba"
Cewar AbdulWahid da yaga kallon da Rufaida tayi masa alamun kamar bata yarda ba.
"Ina yini" Rufaida tayi maganar tana son a bar waccen firar haka
"Lafiya Kalau,amma ya kika canza mana fira,amma dai na kyaleki ko tanbayi Gwaggo idan kin koma ciki"
"To" kawai tace kafin Wahid ya maida dubensa ga Rufaida sosai
"Rufaida ina sanki tun kafin nayi girman da zan fahimci menene so da kauna nayi tunanin so ne irin na 'yan uwa na jini sai a karshe na fahimci bawai hakan bane,tun tuni naso furta miki sai dai fargabata Umma ya zata dauki lamarinki zata amince dake kuwa,ganin shurun zai soma cutar dani yasani sanar da Abba da ya amshi zancen hannu biyu harma yace naje na nemi soyayyarki indai kin amince shikenan shima ya amince,a lokacin da nazo sanar miki a waccen ranar na tarar wani ashe ya rigani furtawa nayi kukan zuci a wannan ranar karshe dai na hakura na barwa Allah lamura na,saidai bawai bana kishinki ba a lokacin amma hakanan a waccen ranar na yava da zabinki tundaga kallo daya dana masa tabbas nasan idan kika kasance matarsa da inada yakini da kin kasance cikin farin ciki saboda naga alamun kaunarsa a fuskarsa fiye da yadda ni nake kaunarki saboda in 'din mai raunin zuci tamkar wata macen i,hakanan naji a raina,sai dai kuma bansan yadda gobe zatayi ba,wanda zan iya hakurta ma raina ke indai yadawo zai aureki saboda inasan farin cikin kanwata matuka ko ya kikace ya karasa zancen yana sake duben Rufaida
Murmushi tayi masa tana son Wahid fiye da son da take tunanin tana masa a baya kasancewarsa dan uwan nata halayoyinsa masu kyaune bayida son kansa sa'banin sauran ahalinta,shi mutum ne mai tsage gaskiya a duk wani hukuncin da zai yanke tuni batun yau ba,tasan tana san shi amma zulliminta 'daya ummansa wannan mataki zata dauka akanta matukar ta aurar mata 'da
Jin shirun ya soma yawa yasa AbdulWahid magana
"Ya kikayi shiru kin barni na gama zuba zance"
Maganarsa ta maidota daga tunanin da take yi
"To Yaya Wahid mai zance"
Murmushi ya dan sake yi
"Au baki san mai zaki ceba,to yardarki nake bukata kin amince dani"
Yakarasa maganar yana nuna kansa
Bata da wani zabin daya wuce ta amince don tasan da yardarta ko babu aure dai sai an'daura ita da AbdulWahid indai suna raye tunda iyaye sun shiga lamarin auren,bare itama dai bazata ce bata sansa ba dama dai zulliminta guda mahaifiyarsu wahid Hajiya Jamila hakan yasa ta 'daga masa kai
Yayi murmushin jin da'di
"ina godiya kanwata Allah ya bani ikon riqeqi da amana"
A iya fatar bakinta tace Amin ba tare da ta furta ba
Ya sake cigaba da magana
"Nasan yanzu dai zulliminki Umma ko ki kwantar da hankalinki yanzu Umma ta zubda makaman ya'kinta tabarwa Aunty Amarya da Mama Kubra"
Murmushi ta 'danyi ka'dan dan tasan AbdulWahid ya fa'di maganar dan yaji da'din bakinsa zatace banda haka inasu Mama Kubra suke da wani kata'bus a gidan da umarninta ake bi a gidan matukar Abba Bukar yasakai yabar gidan kuma a jiya fa tagama jin maganganun da tayi masa akanta,haka itama ta tabbatar da ta shiga dakinta gaida ita ,shima dai kokarin sa take gani da yau yazo gunta bayan mahaifiyarsa vatasanta bataso ya aureta akan wani shirmen zancen da take da tabbacin baida wata makama dan kawai kanin mijinka yayi aure saika dauki kiyayya ka dorawa matarsa ita ba kishiyar kiva bakomai ba.
"Kodai nayi laifi ne kinki sakin jiki muyi fira yau"
Maganarsa ta katse tunaninta
"Ko 'daya"
Agogon hannunsa ya duba ya 'dago da kansa ya dubeta
"To shikenan bari zanje gida ni naga lokaci ya fara ja tara tayi harma ta gota kuma gobe nakeson komawa abuja,zan kiraki zuwa anjima"
"To Allah ya kiyaye hanya" tayi maganar tana 'dago kanta daga kallon kasan da ta ke.
Cikin jin dadin addu'arta ya amsa da "Amin"
Da haka sukayi sallama ya tafi Rufaida jiki ba kwari ta koma cikin gidan
Da sallama ta shiga cikin gidan inda ta bar su Gwaggo anan ta same su.
Amsa mata suka yi
Gwaggo tana cewa "wannan zancen haka daga zuwa kodai korarsa kikai ne"
"Kai Gwaggo kona koresa ai kinsan bazai tafi ba,tunda gidansu ne"ta karasa maganar tana kokarin cire takalminta ta shige daki
Ganin hakan yasa malam gyaran murya
" Rufaida zonan"
Rufaida da taji maganar malam yasata maida takalminta ta karaso wajen da suke ta zauna
"Malam gani"
Sake gyaran murya yayi ya soma magana
"Rufaida dalilin kiran dana miki shine na sanar miki sa ranar bikinki da iyayenki sukayi sun yanke hukunci nanda wata guda za'ayi,dan Allah kar asami matsala daga gareki ki mika lamuranki ga Allah,Allah yasa hakan yafi zama alkhairi"
Gwaggo ta dan dubi Malam ta soma magana
"Malam yaushe akasa ranar bikin kuma banida wani labari a matsayinka na uba ga Hauwa'u hatta nima bansani ba,maisu Aliyu da Bukar yaran nan suka maida kansu ne,ace komai isu isu zasu rika yi
Malam ya murmusa yace
"na samu labarin gurin Ashiru to ni nafadamusu suyi komai saboda kinsan dazu na shiga Kaduna"
Rufaida da haka ta mike ta shige daki ta zauna gefen gado ta soma tunanuka mabanbanta a ranta ace har ayi maganar aurenta Malam mahaifin Umminta ba'a fadamasa ba hatta Gwaggo itama da take tasu basu fadamata koda a waya bane takanji labarin matsaloli a cikin Family amma bata ta'ba cin karo da irin nasu matsalolin ba a cikin wadanda takeji ba banda su Gwaggo ta haifi 'ya to da danginsu babu mai saurararsu da komai to yanzu ma gashi sunada 'yar ana kokarin yi musu yadda akaso da 'ya'yenta dukda suke jikokinsu ace hidimarsu ta soma tashi ba'a sakasu a ciki ba suda suke matsayin kakanninsu amma da rashin mutunci ne dangin Abbannasu da Umminsu sunfi kowa yi musu ,dan ba suda banbanci abinda yayi Abbansu shi yayi Ummin nasu duk dangi guda suke dan bata mantawa da Gwaggo da mahaifin Abbansu uwa daya uba daya suke sai dai ita Umminsu mujiya ce a cikin dangin nasu kodan ita ka'dai ce gurin iyayen nata abu saiya taso a danginsu aki fadamata sai Gwaggo taji ta fadamata idan kuwa taje a dinga jifanta da bakaken maganganu tun da suka fara tasowa suke fahimtar haka, suma yau su Gwaggo gashi a aurenta an nuna musu iko.
Ganin tunanin ba zai fishsheta ba yasata daukar wayarta ta 'dan nemo littafi ta karanta kota ji sauki a ranta

*TEAM OF RUFAIDA*
*TEAM OF ABDULRA'UF*
TEAM OF ABDULWAHID

Ko ya zata kasance dai muje zuwa😊😊😊..ku biyo niπŸšΆπŸ½β€β™€οΈπŸšΆπŸ½β€β™€οΈ


More comment's more typing
*JININMU 'DAYA*

BY SADIYA AL-KHALIL

38.

ABDULWAHID
"Hajiya Jamila ta zauna gefen gadon da ta samu Wahid kai ta cije le'benta na katsa
AbdulWahid da tunda ta shigo dakin bayan ya amsa mata sallama yake kallonta saboda yasan babban abu ne zaisa Ummantasu shigowa dakinsa da yake kwana,maganarta ta maidoshi daga wancen tunanin da take
" Nasa Abdussalam yayi min kiranka 'dazu yace yazo baka nan"
Cike da nuna girmamawa yace
"Eh Umma naje gidan su Gwaggo Zainabu ne"
"Gurin Rufaida ko"
Hajiya Jamilar ta yi maganar ta kuma cigaba da cewa
"Wahid maiyasa kakeson abinda raina zai baci"
Da sauri ya 'dago ya kalli mahaifiyar tasa
Kai ta daga masa ta cigaba da magana
"Kwarai kuwa Wahid da bakaso da baka yi gigin kwatanta koda son Rufaida ba bare har kaso aurenta,kana sane da buku dace da juna ba ta kowacce fuska,wannan tunanin da nake yana kara batamin rai idan naji ita kakeso ka aura bayan kai masa nine akan komai,tun farko har zuwa yanzu,ga uwa uba kasan halin munafurcin Hauwa'u da mai goye mata bayan Gwaggo Zainabu shiyasa banasan ka aureta saboda....
"Haba Umma maganar duk ta mecece hakan ,dukdan akan nace inasan Rufaida"
AbdulWahid yayi maganar yana kokarin katse maganganun da mahaifiyar tashi keyi.
"Murmushin alamun cin nasara da take ganin ta farayi tayi daga visa ni tace
" to naji zan daina amma sai kamin alkawarin zaka janye maganar aurenka da Rufaida,ka amince ka auri Rukayya yarinyar nan tana sanka gata mai hankali ga iya zama da mutane,kuma kana sane da irin soyayyar da Yaya Sha'awa(wato mahaifiyar Rukayyan keyi ma tana sanka kamar 'dan cikinta
Shiru yayi yana tunanin maganganunta da duk ba gaskiya a cikinsu kafin ya ce
"To Umma zanyi tunani"
Da fara'a akan fuskarta da jin maganar da yayi tace
"Yawwa Wahid Allah yayima albarka amma dai kayi tunani mai kyau" da haka ta mike ta tura masa daki
Bayan fitarta ya kwanta yana tunani ,tabbas yasan yanasan Rufaida bayaji zai iya rabuwa da ita,kuma idan ya rabu da ita yasan babu lalle a wannan zamanin ya samu tanada halayya mai kyawun gaske, yasan kawai dan kiyayyar da Ummansa ke musu yasa take alakanta su da munanan zantuka,gaskiya bayaji a ransa zaibi maganar mahaifiyarsa ,saboda nufin Alkhairi ya keson yi,toma idan bai aureta ba Rukayya da takeso ya aura shifa basanta yake ba da aure,batayi masa ba a irin matan da yakeson aura,bata da kunya ga raina mutane to ma shi mai zai kaisa yayi sure a dangin mahaifiyarsa da duk halayyoyinsu daya yawancinsu musamman ma Aunty Sha'awa mahaifiyar Rukayya da ta takasu rashin mutuncin,yana sane da kallon wulakancin da Aunty Sha'awa keyi musu idan sukaje Nasarawa Ummansu tace suje gidanta kasancewar mai kudi take aure ,wanda saida mahaifinsu yayi kudi ta dawo tana kaunarsu,shine yanzu akeso a makala masa Rukayya saboda sunga shima ya dago da arzikinsa,dukda Ummansu batasan wulakancin da Aunty Sha"awa ta riqa musu ba idan sunje gidanta saboda basa fadamata amma su suna sane busu manta ba ,da wannan tunanin ya kwanta ba tare da ya kira Rufaida ba da ya fadamata zai kirata idan ya koma gidan da yana dawowa Umman tasu ta shigo ta tare sa da wannan maganganun.

KANO
Abba Aliyu da ya fada'da fara'arsa da shigowarsa cikin falon ya tarar da iyalansa guri guda zaune suna fira shima fasa fitar da ya fito da niyyar yi yana kokarin zama
"Abba sannu da fitowa" yaran suka hada baki gurin fadar hakan.
Da yawwa ya amsa ya zauna kujera yana sauraron firarrakin nasu da kusan duk na yayarsu ne da sai yanzu ya tuna bai fadamusu bikin ta saura sati uku ba da shima jiya Abba Bukar ya kira yake shaida masa dukda baiji dadin abinda Abba Bukar yayi akan 'yar tasa ba ace babu ko shawartarsa a ce za'ayi aure asa biki sati hudu saikace bazawara dukda dai ana hakan amma bawai yanzu ba saboda idan ya shirya shi Uban 'dan to shi bai shirya ba,ga dadin bacin rai shida 'yarsa ba'atashi fadamasa bikin ba sai saura sati uku,saidai inda hankalinsa ya kwanta Abba Bukar din yace shi zai mata komai,shine zuciyarsa ta daina ganin laifin Abba Bukar din,sai dai yanzu zulluminsa guda yadda Hauwa'u zata dauki lamarin da har yau zullumin sanarmata bikin yake,dukda yasan bata kyauta musu ba amma yanzu yana ganin sunfita rashin kyautawa koda ita Rufaida 'yar rikoce gare ta abinda sukayi busu kyauta ba asa ranar 'yarta ba'anemi shawarar ta ba aka zartar da hukunci,sallamar Ummi Hauwa'u ta maidosa daga wancen tunanin nasa,amsa mata sukayi shida yaran suna yi mata sannu da zuwa Rafi'a ta fado jikinta tana yi mata oyoyo
Sauran yaran suna dariya suna cewa
"Kamar Ummin ta shekara a wani gurin"
Hauwa ta hararesu ta riqe hannun Rafi'a suka karaso cikin falon
"Ai tafi ku sona ne kuda ko murna bangani kan fuskarku ba"
Rumaisa tace
"Wallahi Ummi munfi sonki kinga yadda mukai kewarki tanbayi Abba kiji hirarki data Yaya kawai muke tunda kika fita ya jikin Ra'is din namu"
Ummi Hauwa'u ta murmusa tana zaunakujerar da mijin nata ke kai sannan tace yana gurin yayanku yaji sauki"
"To Allah ya kara sauki" cewar AbdulRashid.
"Amin ya rabb
Kallonta ta maida ga Abba Aliyu ta dan dubesa ganin fuskarsa babu walwala ba kamar yadda suka barsa ba,gashi bayasa baki a firar tasu.
"Abban Abdul anya lafiyarka kalau kuwa"
Sai da yaji muryarta sannan ya fahimci ashe harta zauna kusa da shi baisani ba yanacan yana tunani murmushi ya ka kalo
"Me kika gani,bayan nine na

Please Login or Register in order to submit comment