Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auren"
Hajiya Jamila tayi murmushi tare da cewa
"Lariya ke nan kina tunanin kan auran nan nawa ne ban kashe ba,da naji shiru na dauka asirin nawa ya fara aiki amma ashe lamfa lamfa aka yi min"
"Gaskiya kuwa dan nima abin ya bani mamaki danaji kai kayan shiyasa na fara shakku akan saninki dan nasan vazaki yarda ba,dan koni ma vazan yarda inaji ina gani surajo ya auri Rufaida ba bare kuma ke"
Gwaggo Lariya tayi maganar dan ta sake tunzura Hajiya Jamila
Hajiya Jamila tace
"Wallahi kuwa Lariya munafuntata sukayi,yanzu nama rasa mafita dan a dazu so nai nakashe banza"
Gwaggo Lariya ta jinjina kai daga bisa ni tace
"Yanzu dai tunda har yau ba'a daura auran ba yanzu zan hadaki da wata aminiyata tana da shige shigen malamai,nima tana yi min tayin naje nace mata bani da kudin biyen malamai"
Hajiya Jamila cikin murna da doki tace
"Yaushe zamu je gidan nata,kinga gobe zan tafi Nasarawa da sassafe"
Gwaggo Lariya ta nisa tace
"Ki bari anjima baban Surajo idan ya dawo saina tanbayesa muje gidan nata"
Da haka suka cigaba da fira kafin wayar Gwaggo Lariya tayi kara wayar dake gefenta tasa hannu ta 'dauka ganin mai kiran nata Gwaggo Hajiya yayarta yasata saurin 'dagawa da sallamarta Gwaggo Hajiyar ta amsa saida suka gaisa Gwaggo Hajiyar take cewa"
"Ki kira mijinki ki fa'da masa zaki gidan Yaya Ashiru,anjima zamu hadu gurin daurin auren nan Rufaida da Wahid,kuma za'a kai lefe
Gwaggo Lariya tayi saurin cewa
" Yaya Hajiya ina ce sai wani satin aka ce"
"Eh da hakane amma matar Bukar 'dazu tazo 'dazu tayi wa mutane Hauka a gidan Yaya Zainabu,ta kusa kashe 'yar mutane aini bansan munafunki da ya kai mata zancen ba"
Gwaggo Lariya ta shiga zaro ido jin zancen Gwaggo Hajiyar harda kiranta munafuka to da tasan itace ta fadi hakan fiye da munafuka fadamata Gwaggo Hajiyar zata yi,da haka dai sukayi sallama da cewar sai tazo
Daidaita nutsuwarta tayi bayan katse wayar dan kada Hajiya Jamila ta fahimta da take can daddana wayarta jin Gwaggo Lariya ta gama wayar yasa Hajiya Jamila dago kanta ta kalleta da cewa
"Naji kamar unguwa zaki fita"
Gwaggo Lariya da sauri tace
"Eh wallahi zanje gidan Yaya Hajiya,zamu tafi wata unguwa,amma ba zamu Dade ba zamu dawo yanzu yaro zanyi kira yaje wajen aikin su Baban Surajo ya fada masa",dan tasan muddin ta kuskura bata jeba zarginta za'ayi harda hadin bakinta Hajiya Jamila ta san zancen tunda itama kiri kiri take nuna kiyayyar su Rufaidan,da haka ta mike ta fita daga dakin zuwa wani ba jimawa ta fito kasancewar batada karamin da yanzu haka cikin adonta na kure adaka ta fito ta dawo dakin da tabar Hajiya Jamila data sameta tana waya wayarta ta dauka tana cewa Hajiya Jamila saita dawo ta fice Hajiya Jamila data bita da kallo a ranta tana ayyana tabbas babban abu ake tunda taga Gwaggo Lariya ta caba wannan adon baki ta tabe ta cigaba da wayar da take saida ta gama ta lalubi lambar AbdulWahid amma a kasheta ta sameta dan haka yasa ta hakura da kiran dan tuntuni take kira suna sanarmata akashe wayar take.

******
ABDULWAHID
Da farin cikinsa ya kasa boyuwa da albishirin da mahaifinsa ya tare sa dashi dan tun yana Abujar yaso sanar masa to sai ga matsalar Network baya samunsa a waya koda ya daga wayar ta katse ga wadannan kwanakin aiyuka sunsha kan AbdulWahid din kwana biyu

Saida aka shiryawa Rufaida gidanta sosai da kayanta masu tsada da Abba Bukar duk shi yayi komai sannan AbdulWahid ya dauki matarsa Rufaida suka tafi tare da wasu daga cikin "yan uwan Rufaidan su Aunty Samina da har kwanakin suna Zaria da zasu ganin gidan Rufaidan Ummi Hauwa'u da ba yadda ta iya ta hakura da irin auren da aka yi wa 'yarta da Gwaggo ta dinga yi mata ban baki kafin ta hakura
*****
Gwaggo lariya ta maida dubenta ga Hajiya Jamila
" Jamila kiyi hakuri an riga da an 'daura auren,Rufaida da Wahid sai dai mu sauya shiri,fitar da nayi 'dazu najiyo labari gurin Yaya Hajiya"
Wani kallo Hajiya Jamila ta yiwa lariya kafin tace
"Lariya wannan wanne irin magana kike min ta rainin hankali aure kuma aka daura kuma kicemin baki sani ba aiko a garin mahauta muke bazan yadda ba kikasan maganar kai lefe bare ta aure, ai a dazu na fahimci fitar tafiya kai lefe kikayi ashe ni zaki munafunta nufinki ban fahimci wayar da kikai bane"Hajiya Jamila ba tare da ta jira abinda Gwaggo Lariya ke fada ba ta zari hijabinta da makullanta ta fice tana kokarin ficewa daga gidan gaba daya da har zaure Gwaggo Lariya ta karaso tana bawa Hajiya Jamila baki amma taki koda sauraronta motarta da take kofar gidan ta shiga ta yiwa key tabar gidan ta nufi gidan wata aminiyarta da zata yi kwana daya a gidan daganan ta nufi gidansu nasarawa a ranta tana jinjina halin dangin miji

" Yanzu Yaya inaji ina gani 'dana ya auri wannan yarinyar ba yadda na isa nayi,kina gani ko waya raban da AbdulWahid ya kira ni yau ake kwanan sati don karna masa maganar Auren nan,ga uwa uba ubansa ya koreni daga gidansa"
Cewar Hajiya Jamila da take zaune a babban falon gidan shema'u take wannan maganar
Murmushi Aunty Shema'un tayi kana ta dubi Hajiya Jamila ta soma magana
"Ki kwantar da hankalinki Jamila ai idan sunsan wata basu san wata ba,dama nagama yanke shawarar ku tafi Abujar yau keda Rukayya ku zauna acan tunda shi Bukar baida mutunci idan yaji kina can zaice ki koma dakinki dan ba saurara mata zaki ba idan kuka je,tunda gashi Bukar din ya zuga gaba 'daya 'ya'yanki bama Wahid ba tunda kika zo nan waye cikinsu ya kira ki sai munafukan kishiyoyinki da ba kaunar zamanki suke a gidan ba bayan duk arzikin Bukar din dake akasha wahala gurin samu su da suka zo zuwan daga baya"
Murmushin jin dadin wannan shawarar da 'yar uwarta ta Hajiya Jamila ta mike tana cewa
"Ai Yaya yau ba sai gobe ba zamu tafi" da haka ta shige ciki tana murmushi




****
ABDULRA'UF
" Ra'uf anya kana da cikakken hankali kuwa"Ra'uf yayi saurin dago kansa daga kwanciyar da yayi saman kujerun falonsu jin maganar da Ammi tayi masa ya soma magana da cewa
"Ammi maina aikata kuma?"
"Kafi kowa sanin koma maikayi ace daga wannan lamarin yanzu ka daina hatta da zuwa aiki baka yi kadaina walwala bayan Ahmad ya sanarma ita hartayi aurenta ta manta dakai amma kai tana makale a ranka ,tunda muka dawo baka leqa gurin aiki ba"
Mikewa yayi daga kwanciyar da yayi ya maida kallonsa ga Ammin nasu yace
"Ammi sam yadda kike tunani ba haka bane,wannan maganar ba ita bace ta hanani zuwa aiki ba,kinsan hali na daban manta da itaba bazan hakura ta auri wani ba,kawai dai nasan inajinta a cikin jinin jikina har yanzu"
Ammi ta dan tabe baki kana tace
"Ai saikai tayi, Shureim ya kirani a waya na lallabeka ka koma gurin aiki dai"
Murmushi yayi yace
"Ammi kenan,eh gobe dama zan koma,dama hutun dana daukane bai kareba"
Murmushi tayi jin abinda Ra'uf ya anbata ta maida duk natsuwarta garesa tare da soma magana
" mai zai hana kaje kanemi Auren Inteesar Khan Dawud abokiyar karatun Sophie ina lura da yadda take nuna ma soyayya tun tuni,kaje gurinta a tsaida magana nasan su ba zasu yi mana haka ba"
Ido ya zaro Ra'uf tare da jin wata faduwar gaba lokaci guda taziyarcesa ,inteesar din zai nemi aurenta yarinyar da abokinsa Shureim yake fadamasa irin son da yake mata yadai kasa furta mata ne
"Ya kayi shiru Ra'uf ko ba kai maraba da shawarata ba"Ammi tayi maganar tana kokarin katse shirun Ra'uf kallon Ammi yayi yace
" Ammi shureim ne ke san Inteesar yanzu koda zanje gurinta saidai naje saboda na shigar da soyayyarta gareta"
Tsaki Ammin tayi jin gaba daya dan nata har yau hankalinsa baya ga duk zancen da zata yi masa ya karkata ne kawai ga Rufaida,banda haka ina zaice Shureim yana san Inteesar mikewa tayi ta bashi guri rai a bace
Da kallo Ra'uf ya bita dukda baya san bacin ran mahaifiyarsa amma dai gaskiya bazai amince da shawarar taba na ya auri Inteesar yarinyar da abokinsa ke so dukda ita bata sani ba amma shi ai ya sani idan yayi masa hakan bai kyauta ba ko 'daya, ga uwa uba shifa a tsarinsa bazai iya auren macen da ba 'yar kasarsa ba.

"Ya ko aminci da maganar da kikaje masa da ita"Dady ya tari Ammi da wannan maganar da take kokarin karasa zama gefen gado Da dady yake zaune akai shima
" ai dama na fadama bazai amince ba,kaima kasan halin yaron nan da gaddama,tunda ya nuna waccen yarinyar yakeso kuma bai same ta ba zai wuya a yanzu ya amince da wata macen"Ammi ta karasa maganar da alamun bacin rai a fuskarta
Dady ya girgiza kai tare da cewa
"Wallahi Asma'u ina san farin cikin yaron nan,sai dai a karo na farko nima ba zan amince ya auri yarinyar nan ba,ko ni kaina bama ga Yaya Sule da Yaya Abdu kadai ba suka hana auren ba harda ni kaina mutanan da sukai kokarin lalata mana suna sukai silar rabamu da farin cikinmu rabuwar da sai dai mu kira ta da ta har abada" daga nan Dady Jabir ya fashe da kuka kai kace karamin yaro ne"
Ammi ganin mijinta na kuka yasa hankalinta ya tashi da cewa
"Haba Abban Safiyya me yayi zafi haka kai ba karamin Yaro ba bakomai ba,addua zaku cigaba dayi tuno da abinda ya wuce ba shine mafita ba"
Da wannan kalaman ta cigaba da lallashinsa har ya hakura

*****
Yaya yayaa Safiyya take kwalawa Ra'uf kira da baccin ya fara daukarsa
Ra'uf da yaji maganar Safiyya kamar a mafarki ya vu'de idanunsa ya mike zaune ya dora idanunsa akanta ya dan harareta da cewa
"Sophie Khan ya akai ne,kike kokarin fasamin dodon kunne"
Zama tayi kusa dashi tare da cewa
"Yaya yanzu Intee ta kira ni sunje Us ita da yayanta ankafe suna taga sunanmu nida Husna"
Murmushin Ra'uf yayi tare da cewa
"Kai amma ina miki murna sister,kin fadawa Husnan?"
Safiyya tayi saurin cewa"A'a Yaya,zuwa nayi ka kira ta a wayarka a fada mata"
Ra'uf yace
"Ke ina kudin wayar taki?"
Safiyya tayi saurin cewa
"Yaya ai ba kudi a wayata kamanta ne"
Hararar wasa yayiwa Safiyya da cewa
"Dady jiya ya sa miki kudi ina kika kaisu"
Marairaicewa Safiyya tayi
"Na kira kawaye na tun jiyan"
Tsaki Ra'uf yayi ya mikamata wayar dan sarai ya gano kudin nata ne batasan kashewa na cikin wayar.
Lambar Husna ta kamo ta kira ta shaida mata samun makarantar da sukayi ba karamin murna Husna tayi ba ita ma,daga nan suka cigaba da firarsu saida Ra'uf ya gaji da surutun da Safiyya ke masa a kunne ya anshe wayarsa ya kashe

Sadiya Khalil🖤*JININM U 'DAYA*
By Sadiya Khalil❤️

42.

Ina yiwa masoya wannan littafin fatan alkhairi a kowanne lokaci ina kuma anfani da wannan damar gurin yiwa 'yar uwata Aisha Umar Ibrahim fatan alkhairi na gama littafinta mai suna ZAN JIRATA lafiya Allah ya hadamu da alkhairan cikin littafin ya kawar damu da akasinsa ya shiryar damu bisa tafarkin tsira ya bamu ikon rubuta abinda zai anfanardamu ko bayan bama raye.Amin

42.
ABDULWAHID

Cikin kwarewa yake aikinsa da kwanciyar hankali auren Rufaida,bakaramin farin ciki yake da shi ba,tana nuna kulawarta gare sa,aikin da yake ya ajiye gefe,ya dauki wayarsa da take ringing wanda tunaninsa Rufaida ce,ganin tunda ya tafi aiki busu yi waya ba yadda suka saba,sai tunaninsa ya basa ko itace da taga bai kira ta ba ko ta kirasa,duba screen din wayarsa da yayi ya kaudar masa da tunanin sa ganin sunan da yasa wa Ummansu akan screen din itace mai kiran nasa wata irin faduwar gaba yaji ta ziyarce shi tunda yaga kiran Ummansa yasan sai ta yi masa fada sosai don yasa koda bakin aurensa a ranta sai ta masa don rab. an da ya kira ta yau kwana 7,a bakin Abbansu yaji duk abinda ya faru ganin tana kokarin katsewa yasa shi saurin dagawa
"Assalamu Alaikum,Umma ina yini,ya su Aunty"
Yayi maganar a jere a kuma tsoro ce
"Kazo ka shiga damu barrack din ku munzo yanzu nida Ruqayya"ba tare da ta vashi waccen amsar ba ta tare sa da wannan maganar da haka ta katse wayarta
AbdulWahid da baida wani zabi da ya wuce yaje tararsu da haka ya mike daga office dinsa ya fito ya fito yaje tarar mahaifiyar tasa ba tare da ya tuna da kiran Rufaida a waya ba ya Shiga motarsa ya fito daga headquarter dinsu

RUFAIDA

Jin bugun kofar falon nata yasa ta mikewa daga kwanciyar da ta tayi a kujera da barci ya fara daukarta jin an cigaba da bugawa yasa ta mikewa ganin waye cikin tsakar ranar nan yazo gidanta sai da ta leka kofar ganin mijinta tsaye jikin kofar ya sata kokarin bude kofar da murmushi akan fuskarta,ido biyu tayi dasu Hajiya Jamila da suke bayansa da hanzari tayi kokarin basu guri tana cewa
" Sannunku da zuwa Umma"
Wani banzan kallo suka jefeta da shi,suka karasa shigowa falon wanda da ido suke bin ko ina na kusurwar falon da suke kokarin ganin makusar falon nata
Da wani murmushin ta sake cewa
"Sannunku da zuwa Umma ku zauna mana kunsha hanya bari na kawo muku ruwa" daga nan ta shige ciki
Basu ce da ita komai ba ganin ta wuce yasa suka bita da wani banzan kallo daganan suka zauna a kujerun falon suna ya mutsa baki dukda kayatuwar falon kuwa
AbdulWahid katon akwatunsu ya shigo musu da shi da shima ya najin sannu da zuwan da ta musu basu amsa ba,har karo biyu sharewa yayi ya shige da akwatun nasu ciki dan yana ganin akwatun ya fahimci bada tafiya suka zoba da zama suka zo kofar wani corridor na gefen wani daki ya aje kayan ya shige cikin kitchen din da yake tsammanin Rufaidan na ciki jikin kofar kitchen din yayi tsaye yaki karasa shiga ciki da murmushi kan fuskarsa yake kallonta tana kokarin jera lemuka da ruwa akan faranti mai girma ta juyo zata fito idanunta ya sauka cikin nasa murmushi tayi masa inda take ya karaso ya mika mata hannu ganin haka yasa ta gane manufarsa mika masa plat din tayi ya amsa ya rike dubensa tayi kana ta soma magana
"Haba Yaya yanzu su Umma zasu zo koka sanarmin gashi sunsha hanya,kuma nasan suna jin yunwa yanzu fa sai sun jira na dora"
Murmushi yayi jin kalamanta gaba daya baza kace bata murna da zuwansu ba dukda kuwa yasan hakan ne don koshi da Umma take mahaifiyarsa Rukayya kuma take matsayin kanwarsa baya murna da zuwansu bare kuma ita dan yasan babu alkhairi a zuwan nasu tunanin da yake ya aje gefe kafin yace
"Kanwata sai yanzu suka sanarmin da zuwan nasu tuba nake" ya karasa maganar da murmushi
"Hm" kawai tace tana kara mika hannu ta amsa tray din
"A'a ki kyale zan kai musu ki dauke musu kayan nasu ki kai musu inda kikaga ya kamata su sauka suna corridor" daga nan suka fito daga kitchen din tare

Da sallama ya dawo falon da sallamar ta katse musu firar da suke ganinsa dauke da tray da yake kokarin aje musu akan centre table yasa Hajiya Jamila saurin kallonsa tare da kokarin cewa
"Wahid me zan gani haka,kaine dan aikin gidan kardai daga auren harka zama mijin tace"
Kai ya sosa da kokarin cewa
"A'a Umma wanne irin mijin tace taimaka mata nayi fa"
"Taimako a haka ake taimakon,dalilin gujema auren nan da nayi kenan,haka kurum kaje ka kwaso irin karuwai,ba dole su mallake ka ba,gashi harsun rabani da kai,ko waya yaushe rabon da ka kira ni" cewar Hajiya Jamila
Rukayya tayi saurin cewa
"Wallahi kuwa Umma"
Hararar Rukayya yayi yace
"Ke kuma dake ake magana ya kalli mahaifiyartasa yace mata,
"amma ni Umma wannan va mallakewa bace,kowa yasan akwai taimako tsakanin mata da miji sannan,vatun kalmar karuwanci da kike jifansu dashi ,ina jin tsoron mahaifiyata ranar lahira ta tsaya gaban ubangiji ace tazo da wannan shaidar,biki gani ba ba ayi a gabanki ba,to me zaki cewa ubangiji a wannan,sannan ni Umma wallahi ba ruwan Rufaida da kin wayata dake dangataka da ita daban da taki ma haka,ba ruwanta da mahaifiyata,idan ba itama biyayya zata yi miki ba"
Hajiya Jamila cikin fusata ta dubesa tare da cewa
"To ubana jeramin magana,don ance matarka tana kokarin mallekeka zaka rika jeramin magana" ganin yadda mahaifiyata sa ta fusa ta daga 'yar maganar sa yasa shi sassauta murya gurin cewa
"Umma kiyi hakuri" sai a sannan ya gaishe da Umman tasa,kamar ba zata amsa ba tadai daure ta amsa,Rukayya da dakyar ta iya gaishesa don bakara min haushin abinda yayi mata lokacin ta ji ba amsa mata yayi ya mike yabar falon yana kokarin shiga ciki kiran Rufaida jin har lokacin bata fito ba wanda ta tsaya sake gyara dakin da su Umman zasu sauka ne a hanya yaci karo da Rufaidan zata fito falon bayan gamawarta murmushi ya sakar mata don baya so ta fahimci wani abun ita ma murmushin itama tayi don bata so ya fahimci taji duk maganar da sukeyi a kokarin ta na dawowa falon da tayi jin suna magana ya sata kasa karasawa kuma takasa barin gurin kuma maganarma duk dai akanta maganarsa ta katse tunaninta
"Dama nazo na sanar miki zan koma vakin aiki,ki fito kuyi fira karki varsu su kadai,sai ma naganki zaki fito din"
Ba tare da tace komai ba suka rankayo falon tare
Rufaida da suna isowa ta durqusa har kasa tana gaishesu da sake musu sannu da zuwa harda Rukayya ta gaisar da Rufaida bata tunanin Ruqayyan zata iya gaida ita kamar ba zasu amsa ba Hajiya Jamila ta daure tace mata
"Lafiya"
Daganan ta mike ta nufi Centre table din ta tsiyaya kowacce ruwa da lemo tace musu
"Ga ruwa kafin a dora abinci" babu wadda tace mata koda to a cikinsu ita ma batayi tunanin hakan ba daganan ta mike ta basu guri,AbdulWahid dake tsaye jikin TV yana kokarin canza tasha yana jin duk abinda yake faruwa bai sake saurararsu ba yayi hanyar barin falon
Yana kallonsu dukansu har Rufaida da ta yiwa kanta matsugunni a wata daga cikin kujerun falon yace musu
"Zan koma bakin aiki saina dawo"
"Adawo lafiya"
Hajiya Jamila ta iya furtawa,Ruqayya ko kallonsa bata yi ba bare tayi masa addu'a
Rufaida ta biyo bayansa yi masa rakiya da su Hajiya Jamila suka biyota da wata muguwar harara,musamman Ruqayya dan gani take da tuni ita ce a cikin daularnan fa wannan yarinyar tayi mata shigar sauri a zuciyar AbdulWahid dalilin da yasa take jin wani matsanancin kishi akan Rufaida, har jikin motarsa ta rakasa
Wahid da yake kokarin shiga motarsa ya juyo yana Kallonta cikin nuna tausayawa zamansu da mahaifiyar tasa tun kafin aje ko ina yace
"My wife kiyi hakuri nasan kemai hakuri ce anma ki cigava dayi karki gaji nasan kinsan halin UMMA bana tunanin zaki sha wuyar zama da ita,dama kafin sanin halin mutum shine wahalar kafin nan dai da Abba ya sauko ta koma dakinta"
Murmushi tayi masa ta kallesa
"Haba Yaya ai mamarka kamar Ammi ce koda ba muda alaka ni dakai"
Ya tari zancenta da cewa
"Eh dukda hakan,kinsan zama da uwar wani sai hakuri musamman Umma"
"Haba Yaya karka ce haka uwa uwa ce mu cigava da yi mata addu'a Allah ya ganar da ita Rufaida take fadin haka
" Hakane my wife,bari na koma aikin,sai na dawo"yayi maganar yana yi mata kallo mai cike da soyayya
Kai ta sunkuyar kasa ganin kallon da yake mata
Murmushi yayi yace
"Badai kunya na baki ba dan na kalli mata ta kallon soyayya,wallahi Rufaida ina sanki kinada halayya mai kyau,da yake karamin sanki koda yaushe,gaki kyakkyawa" yayi maganar yana dariya ya shige mota yana kokarin tayarwa yace
"Ya ba kice komai ba"
Ta kallesa race
" to Yaya mai zance?"
Yace mata
"kice wani abu nake so"
Tace
"To ka kulamin da kanka banda kula 'yammata"
Ya dan harareta yace
"Idan na kifa"
"Hmm"kawai tace
Yace
" kinga uwar kishi ni bani da lokacin kula mace,amma ga babbar wadda zaki kishi da ita nan tazo har gidanki Ruqayya,kibi a hankali dama inason fada miki"
"To Yaya insha Allah,ka koma naga lokaci na kurewa"tace masa
" to My Special na tafi
Yana kokarin tada motarsa tayi kokarin yi masa addu'a
"Adawo lafiya Allah ya tsare minkai"
Amin ya fadi hakan da murmushi yayi kokarin barin harabar part din nasu.
Saida taga wucewarsa tabar wajen ta koma ciki tana murmushi tana san mijinta saboda halayyarsa abar so ce ya iya nuna kulawarsa ga mace,dukda tasan tanasan Ra'uf amma yanzu ta manta dashi,dama addu'arta a kullum Zabin Allah sai gashi yayi mata zabi da Wahid ta kuma rungumi mijinta don dama uwarsa ta jiwa tsoro ba auransa ba amma tunda tanasan zama dashi dole tayi hakuri da mahaifiyarsa domin ance maso uwa taso danta haka ma maso da sai take ga taso uwarsa zaifi,dan da uwar bata haifesa ba ita da bata auresa ba
Da sallama ta shiga falon da babu wacce ta amsa mata bata damu da hakan ba ta dubi centre table din yadda ta tsiyaya musu lemukan haka ta tarar dasu
Murmushi tayi tace
"Umma naga buku sha komai ba anan"
"Haka karuwar uwarki ta koya miki bawa baki abinci kenan,amma ta ko yamiki mallake miji ko,to ni bazan jure haka ba saboda akwai banbanci tsakaninmu mu daku,gadon tsiya kawai"
Hajiya Jamila tayi maganganun tana sake gyara zamanta
Ruqayya shewa ta buga ta ya mutsa fuska tace
"Kinga zo ki mikomin ruwan nina sha"
Bata ko tankawa Ruqayyan ba ta shige ciki ta barsu,dan Ruqayya bata kai matsayin da zata sata aiki ba ta yi mata saitayi niyyar dukda durqusawa wada ba gajiya bane saboda a girme ta girmi Ruqayyan amma ita Rukayya da izgilanci tayi mata maganar kuma ita bataga laifin taba takawo musu ruwa ta tsiyaya musu,daukarce zata gagaresu,to ko ita 'yar aikice aikinta iya nan zai kare

Ruqayyan da kallon mamaki tabi Rufaida don tana da yakinin Rufaida ta fara cin ganye ne.
Girki Rufaida ta dora jallop din shinkafa da taji kayan lambu,da suke a fridge,sai kuma lemon abarba data hada,bata yi tsammanin Rukayya zata iya shigowa tayata ba yasa ita ma bata maida kai a hakan ba dan danan ta gama ta zubawa mijinta nasa daban da zai aiko a ansar masa yadda yake yi tun bayan aurensu daganan ta kawo musu nasu ta aje musu a dining ta karaso cikin falon ta sanar musu da ga abincinsu data samesu kowacce ta hakimce a kujera duk sun kwarkwanta suna kallo abinsu sanyin Ac na ratsasu
"Umma ga abincinku can a dining kona kawo muku nan" ta furta babu wacce ta kalleta saima dogon tsaki da suka ja mata
Ganin haka yasa ta barin inda suke ta ta shige dakinta tayi wanka ta shirya cikin atamfarta kalar lemon green da brown daganan tayi sallah falon dake dakinta ta dawo ta kunna TV ta fara kallo ta dauki wayarta ta kunna data suka fara chat da Nasiba Shehu Garba class mate din ta sosai suke chat suna labarin makaranta,bayan Nasiba ta gama cakakin bata fadamusu bikinta ba sai abakin Samiha suka ji can Nasiba tace
"Ke ban baki labari ba Sir Nura ashe Saliha Nasir budurwarsa ce har ankai kudin nagani ina so"
Emoji na mamaki Rufaida ta tura mata kafin tace
"Ke wai da gaske kike kawata,Saliha dai dana sani"
"Kwarai kuwa,Saliha Nasir mutuniya da suke dabi da Sir nura"
"To Allah ya sanya Alkhairi,idan sa ranar bikin yayi dai dai da zuwana gida zanje bikin ai Saliha nida ita da amana"
Rufaida ta rubuta ta tura mata
Nasiba ta turo mata Voice note ta bude taji Nasibar nace wa
"Kai da mun jidadi to Allah yasa,baki cemin ina Sir AbdulRahman ba"
Voice note din ta mayar mata ita ma da cewa
"Ya na ina badai har ansa ranar aurenku keda shi ba"
Zuwa can Nasiba ta dawo mata da amsa
"A'a ko 'daya,amma dai ansakamin rana a Adamawa zanyi aure, wata makwabciyarmu to dan Yayanta zan aura,da yazo gidanta muka hadu,shima anan Abujar yake aiki a central Bank"
Rufaida ta sake tura mata da voice note din
"Wow kice gidan kudi burinki ya cika"
"Murmushi Nasiba ta turo mata na emoji ta kara yi mata voice
"Rufaida kenan kudin da ba baka za" a rikayi kana yawo dasu ba,kedai kawai addu'ar samun miji nagari da kwanciyar hankali bayan auren,danta kudin miji ba kwanciyar hankali aina banza ne gwara ma ace talaka ka aura indai zai mutuntaka"
Voice Rufaida ta sake tura mata
"Haka ne kawata,Allah ya baku zaman lafiya ya tabbatar da Alkhairinsa"
Ganin wayarta na kara alamun kira yana shigowa Wahid ne mai kiran tana kokarin dagawa ta katse
" yasa tayi saurin cewa Nasiba zamuyi chat anjima" Nasiba ta rubuto mata
"OK akwai labari

Please Login or Register in order to submit comment