Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa ni matsawa gefe Yaya Jabir ya leko da kansa ganin shine yasa ni sauri karasawa inda yake
Yaya Jabir ya kalleni
"Hauwa yana ganki a kasa yau ina drivern?"

"Na makara,shine Baffa yace na tafi a kasa"

Yaya Jabir ya girgiza kai ya bude mota
"Kinga shigo na kaiki,banda abin Baffa ai yanzu ne ma yafi kamata a kaiki a mota"

Daga haka na shige motar Yaya Jabir na zauna gidan gaba,da duk cikin motocin Baffanmu ne ya fito da daya daga ciki
Sai da muka fara tafiya Yaya Jabir ya soma magana

"Ya yau kika makara ne Hauwah vayan ba halinki bane makara makaranta"

Murmushi nayi
"Wallahi Yaya Jabir Exam zamu fara na jima ina karatu daga sallar asuba saina koma na kwanta"

"To Allah ya taimaka"
"Amin" na furta muka cigaba da tafiya

Yaya Jabir ya sake kallona
"Bari na yima wancen abokin nawa magana" daga haka ya gangara da motarsa gefen titi kusa da inda wani saurayi yake tsaye da alama shine abokin nasa kansa ya zura ta motar

"Ibrahim lafiya dai ko?"

"Abokin nasa mai suna Ibrahim naga ya waigo ya dubi Yaya Jabir da alama yasanshi ganin ya karaso inda muke ya leko cikin motar yana fadin"
"Oga Jabir dama kana gari"
Yaya Jabir yayi murmushi
"Gani ma"

Sai a sannan na gaishe da abokin Yaya Jabir din nayi ba tare dana dago kai na ba Ibrahim din ya amsa da fara'arsa

Yaya Jabir ya dora da magana
"Ina zaka nufa ne naga alama kamar abin hawa kake jira"

"Eh wallahi zanje Mallam Madori Road ne"

"Ah to shigo mana na kaika

"A'a bana shigo ba naga bakai kadai bane kuma da alama yar makaranta zaka kai"

"Badamuwa duk hanya daya ne GGSS Dutsima Road kaga zaina karasa dakai ai can Road din,bari ta koma.baya kai saika shigo gaban"

Ni Yaya Jabir ya kalla
"Ki fito ki koma baya ya shigo"

Babu musu na fito daga motar sai sannan na kalli Ibrahim din yana kokarin shiga motar daganin alamu Ibrahim akwai son gayu

Muna fara tafiya makaryaya " jiyo muryar Jabir yana cewa da Ibrahim din
"Dama talakawa na ganinku Ibrahim"

Ibrahim yace
"Kaji ka ai mune talakawan naku"

Yaya Jabir yace
"Hmm,haka dai kace,ina motar taka yau?"

Ibrahim yace
"Tana gurin gyara"

Ibrahim ya juyo inda nake yana fadin
"Yan makaranta ya kike makara makaranta ki daina kin jiko ko karatu bai wuce ki ba za'a doke ki"
Murmushi nayi kawai nace nasa
"Insha Allah na daina"

Daganan ya juya gurin Yaya Jabir
"Danbatta ya bansan wannan ba wai itama kanwar kace"

Yaya Jabir yace
"Eh mana,yanzu bakasan Hauwah ba a gidanmu"

Ibrahim yace
"Nasan sunan amma bamu taba haduwa da ita ba idan nazo gidanku ba"

Yaya Jabir yace
"Diyar Mama Amina ce amaryar Baffa"

Ibrahim yace
"Ah shiyasa duk tafi ku kyau ashe mamarsu ta biyo"
Mamaki ya cikani jin maganar Ibrahim ashe har Ummanmu ya sani amma ni ban taba ganinshi ba,wata zuciyar tace.kila sanda yake zuwa gidan namu muna makaranta maganar da naji Yaya Jabir nayi ta katsemin tunani na

"Wato mu munana kenan?"

Na juyo dariyar Ibrahim ya dora da
"Bare ma ni ban ki yaban kyawunku ba,kuma ai kyawawane Fulani,amma dai Hauwah ta daraku"

"To ai nace dai naji dama na fiso ta fimu kyawu ai?" Fadin yaya Jabir

Da haka suka cigaba da firarsu da take nuni da Ibrahim abokin Yaya Jabir ne sosai.*JININMU 'DAYA*

BY Sadiya Khalil
Book 2
7.

Yau kam saura kwana uku bikinsu Yaya Sule hakan yasa 'yan Danbatta suka fara zuwa a yau din yawanci duk gwaggoninmune daga diyoyin kannen babansu Baffa sai diyoyin kannen su Innarsu Baffanmu dasu da yaransu.hakan yasa yau duk bamu da wani kuzari tunda muka ji zuwansu muke a daki ni guga ma na debo na fara yi Yaya Safiya tana shirya mana a sib ko niyyar zuwa gaishesu ba mayi.Umma ce ta shigo dakin mu da sallamarta a same mu ina cikin gugar kallonmu tayi
"Ban gane ba Nana,nufinku ba zakuje gaishe da Gwaggonin naku ba,kuka debo guga kome"

"A'a Umma zamu" fadin Yaya Safiya da take kokarin mikewa

Dutsen da ke jikin socket na jingine na kalli UMMA
"Kai Umma yanzu sai munje wani gaishesu,tunda kinje ba shikenan ba"

"Shikenan din wa ni badan ku zani ba dan kuma mahaifinku,da nake auranshi amma ku ai danginku ne dolenku ne"

Na zunburi baki nace

"Amma Umma bafa da san....

"Umma cikin fada ta katse maganar dana keson fada
" Zaki tashi ko ba zaki tashi ba,bafa nasan gaddardami banfi ki sanin komai ba"
Badan na soba na mike ina kunburo baki muka fice Umma tabiyo bayanmu.

A falo muka tarar da Yaya Jabir zaune a kujera
"Umma ta kallesa da fara'arta
"Yaushe ka shigo ne Jabir"

"Wallahi Mama yanzu na shigo da naga kayan kallo kunne nayi tunanin baki dade da barin gurin ba" fadin Yaya Jabir

Umma ta dube mu
"Eh Jabir ciki na shiga ciki kiran kannenka suje yiwa gwaggoninku da zuwa su gaisa"

Yaya Jabir ya dubemu
"To shine,harda batan rai,don ance kuje,kamar wadanda za'a kama

"Nace
" amma Yaya"

"Amma me ku wuce ku tafi"

"Umma tace
" kaga ni sai gardama nima suke ta yimin"

"Daga gaisuwar kuyi ku taso inma busu amsaba kundaije sai duk abinda za'a fada akanku indai kunsan ba haka bane damuwar mai zaku yi,tunda kunsan halinsu kuma Mama saita zuge suma indai baku jeba"
Badan munso ba muka bude kofar falo muka fice
Muka jiyo Umma na cewa

"Yawwa fada musu dai yara sai bakar gardama"

A babban falo muka tadda bakin duk kannen iyayen Baffa ne da 'ya'yansu suma dana su 'ya'yan ayari guda sai Gwaggo Hadiza itama da tata gayyar sun bararraje sa falo wasu suna cin abinci wasu kuma suna ta zuba fira cikin fillanci dasu Mama Hanne sallamarmu ta tsaida firarsu Gwaggo Hadiza da idanta ke kanmu har muka tsugunna muna gaishesu da musu sannu da zuwa amma ko kusa Gwaggo Hadiza bata amsaba sai kallonmu da take tayi can muka jiyo muryarta
"Sai yanzu Uwarku taga damar barinku kuzo gaidamu,marasa mutuncin banza da wofi"
Kanmu muka dago jin kalamin Gwaggo Hadiza
Mama Hanne tayi caraf tasa baki tace
"Ai kunga halin nasu yanzu da nake fada muku,musamman ke Hadiza kin gaza yadda,ai yanzu ke yarda, Amina yadda ta dauki kanta kamar diyar Dangote tasa diyoyinta suka dauki kansu"

Gwaggo Hadiza da Gwaggo Harira suka hada baki gurin cewa
"Aiko bata basu tarbiyya ba,ita Aminar 'yar matsiyata ubanta harya mutu da talaucinsa"

Mama Hanne ta cigaba da magana jin sun dauki zugarta
"Ai Amina makirar macace hatta diyoyinta ta koya masu halinta"


Gwaggo Hafsatu da ita ma kanwar Baffa CE abokan wasa suke da Baffa,hakama kanwar Mama Hanne ce tasa baki a maganar
"Kunga ku tashi ku tafi"
Jiki ba kwari muka mike sakaka muka bar gurin dama munsan fiye da haka zamu tarar
Gwaggo Hafsatun muka jiyo tana cewa
"Haba Yaya Hanne mai yasa zaki rika irin haka,ko kaffara babu kece makirar"

"Ke Hafsatu nice makirar wallahi saikinyi danasanin ce mani makira" muka jiyo muryar Mama Hanne cikin fada
Daganan muka bude murfin motar bangaranmu muka shiga

Da sallama muka shige falon namu,firar da Umma da Yaya Jabir suke muka katse masu amsa mana suka yi muka zauna kujerar mai biyu mai kallan ta Yaya Jabir

Yaya Jabir ya kallemu
" badai har kun dawo ba,mai ya bata ranku naga fuskarku haka"

Murmushin yake muka yi

Yaya Jabir yayi gyaran murya
"Hakuri zaku cigaba da yi watarana kowa sai yayi alfahari daku an kuma so ku"

Guntun hawayen idona na goge nace
"Yaya Jabir hakan bamai yiyuwa bane nake tunani,kaga fa irin kiyayyar da suke nuna mana koda yaushe aita aibata mana uwa"

Umma ta kalleni ta soma magana da sai yanzu tasaka baki a maaganarmu tunda shigowarmu
"Hauwa'u to meye na damuwar don an aibata ni, duk abinda za'a fada a kaina indai kunsan ba haka bane kudai na damuwa,wata rana bazasu fadamin ba,wata rana sai labari"

Na kalli Umma nace
"Amma Umma..."

Sallamarsu Yaya Malika ta katse maganar da nake son karasawa duk muka maida dubenmu gare su da gudu na karasa na rungume wasu daga cikin yayyena diyoyin Gwaggo Hafsatu suma suka rungume ni da haka muka karaso ciki da Umman mu cikin nuna kulawa take musu Sannu da zuwa

Har kasa suka duka suka gaishe da Ummanmu,har raina inasan su Yaya Ma'u da Yaya Hannatu da suka fita daban su da mahaifiyarsu akaf cikin dangin Baffanmu suna nuna soyayyarsu gare mu muddin munje Danbatta kosun zo Kaduna dasu a cikin Danbattan suke zaune shiyasa muka saba sosai. da Yaya Ma'u tsarar Yaya Safiya ce Yaya Hannatu kuma ta girme min da shekara a akalla hudu saboda rashin tazara mai yawa tsakaninsu da Yaya Ma'u don Yaya Ma'u baifi shekara 1 da rabi ta bawa Yaya Hannatu ba,hakan yasa suka taso kamar tagwaye ga kamar da suke da juna.

Umma ta katse min tunani na naji tana cewa
"Dama har daku a kazo hala dai su Hauwa'u busu ganku ba yanzu suka dawo daga gaishe dasu Mamartaku"

Su Yaya Ma'u da suka zazzauna a kujeru Yaya Ma'u tace
"Eh wallahi Mama,muna ciki mu,yanzu da naga su Safiya busu shigo ba,nacewa Malika hala busu san da zuwanmu ba,da sun shigo"

"Eh gaskiya basu sani ba,to ya hanya yasu Baffanku da sauran mutan gida"
Fadin Umma

"Yaya Ma'u tace
" wallahi duk suna lafiya,su Baffa jibi ranar daurin aure zasu iso"


"Allah ya kaimu lafiya"
Fadin Umma daganan ta kalli Yaya Jabir suka cigaba da firarsu

Yaya Ma'u ta dube ni
"Hauwa'u hala duk murnar ce kika tsare mu da ido"

Nayi murmushi
"Wallahi kuwa Yaya Ma'u kamar ko kin sani, ya hanya"

"Alhamdulillah" Fadin Yaya Ma'u tana murmushi
Daganan muka mike zuwa dakinmu muka zauna zaman baja kolin fira

Zuwa can Yaya Hannatu ta kalli Yaya Malika tace
"Yaya Malika wallahi kwadayi nake ji muje bakin titi ko biscuit na siyo"

"Yaya Malika tace
" aifa kinzo uwar kwadayi,wannan yaya Usman ya bani da kwadayi"

Dukkanmu dariya muka yi.Yaya Usman shine saurayin Yaya Hannatu suna matukar son junansu

Da zunbula zunbulan hijabanmu muka fito harabar gidanmu muna fira cikin nishadi abakin gate muka ci karo da Yaya Jabir ya kallemu ya dauke kai

"Ina zaku je ne?"

Nice nayi saurin cewa
"Mama Suwaiba ce ta aikemu shago"

Kai ya daga muka yi saurin ficewa don nasan indai ba sharara karyar muka yi ba ba zai barmu mu fitan ba muna fita muka sa dariya savoda karyar da na yiwa Yaya Jabir haka.muna kokarin karasawa wani shago da yake jikin wani dan karamin gida mai kyau Yaya Safiya tayi saurin cewa ga wani shagon nesa da wancen muje
"Yaya Malika ta tsaya jin maganar Yaya Safiya ta kalleta tace
" don me zaki ce muje mai nisa gana kusa,ko basu saida biscuit "
Yaya Safiya ta girgiza kai tace
"A'a kawai dai"
"Kawai me" Yaya Malika ta fadi haka tana cigaba da tafiya muma da muka tsaya muka bi Yaya Malika
da sallama muka karasa shagon ba mu samu mutane a shagon ba mai shagon ne kawai kai ya dago yana amsa mana sallamar da murmushi a fuskarsa daganinsa zaka tabbatar bafulatani ne sosai gaishe sa muka yi ya amsa yana bin kowaccenmu da kallo yana jiran jin mai zamu siya

"Yaya Hannatu tace
" Dan Allah zamu samu Waper ne anan"

Murmushi yayi yace
"A'a Cabin muke saida wa"

Yaya Hannatu tace
"Yanzu duk girman shagonnan babu wafer?"
Yaya Safiya ta kalli Yaya Hannatu tasa dariya tace
"Anyi maganin mai kwadayi"

Saurayin ya kalli Yaya Malika yace
"Ya kike mata dariya idan ma fiye da wafer ne zata samu anan"yayi maganar yana sake kallen Yaya Ma'u

Murmushi Yaya Malika tayi
" amma da kace babu"

"Eh mana naji kuna tanbaya kamar kun raina shagon shiyasa" ya fadi haka yana karasawa jikin kantocin shagon ya debo mana buskunan kala kala ya zuba a leda ba tare da ya tanbayemu nawa kudinba

"Yaya Ma'u ganin ya miko wa Yaya Hannatu ledar ta kallesa
" ya zaka bamu kaya haka baka tanbaye mu kudinba,baka tanbayi kalolin da muke soba"

"A'a bama saina tanbaya ba na dade da sanin abinda ya cancanceku"
" Saurayin yayi maganar yana sakarwa Yaya Safiya murmushi da kanta yake kasa tunda muka zo shagon ina kula da ita

"To nawa ne kudin"
Fadin Yaya Ma'u tana kokarin bude jakar hannunta ta debo kudi

"A'a kubarshi"

Godiya muka yi.muna kokarin barin shagon muka jiyo muryarsa yana cewa
"Zan zo yau saura kiki fitowa kamar jiya"

Yaya Safiya da na fahimci da ita yake tunda muka zo shagon muke kallon yadda yake kallonta nan nayi tunanin ashe shine Hashim din da yazo jiya Yaya Safiya taki fita

Saida muka fara tafiya Yaya Malika ta tsaya muma muka ja muka tsaya ta soma magana
"Ku Daka ta wai wancen saurayin dawa yake nidai nasan ba dani yake ba"

"Yaya Ma'u tace
" bare kuma mu,baki"

Nima nace
" bare kuma ni sai dai koda Yaya Safiya yake,ina kallon irin kallon da yake mata"

Duka muka sa dariya
Yaya Malika tace
"Nima na gani Safiya,she shine na karfen,shiyasa da zaki mana bukulin samun wannan buskunan kyauta"

Yaya Safiya tace
"Kai Malika nidai ba haka bane"

Yaya Ma'u tace
"Nufinki bahaka ba saurayin naki bane kome"

Yaya Safiya ta daga kai tace
Na kalleta nace
"Kai Yaya Safiya kiji tsoron Allah jiya fa an aiko kiranki akace inji Hashim kuma baki fita ba"

Yaya Safiya ta harare ni
"Da tsoron ki nake ji,mara kunya kawai"

Zanyi magana Yaya Ma'u tace
" kyaleta Hauwa'u mun san komai ai yanzu"dukkanmu muka saka dariya muka cigaba da tafiyarmu

A falon bangaren Ummanmu muka baje buskunan Umma da take zaune tana kallo ta kalli buskunan
"Usman ne ya siyo muku wannan kayan ko masu yawa"

"Yaya Ma'u ta kalli Umma tace
" ai dama shine Umma da munji dadi tunda budurwar shi ce mai kwadayin dama,wannan saurayin Safiya ne ya bamu,shagonsa muka je siyayya,wallahi Umma yana da kirki surikin naki"

Umma tayi murmushi tace
"Tunda zai baku ba,ayi dai a hankali da samari don basu da tabbasa karku zurfafa soyayyar kowanne saurayin Allah ya tabbatar da Alkhairi"


Muka amshe da Amin
Daganan Umma ta mike tabar mana falon
Yaya Safiya kanta a kasa tunda aka fara magana ganin Umma ta bar falon tace
"Allah ya shiryi magulmata,harku gwangwadawa Umma"

Yaya Ma'u tace
"Ba wata gulma indai ba yaudararsa kikeson yi ba gwara mu fada tun wuri kowa ya sani,tunda za'a dashi"

Yaya Safiya tace
"Kai Ma'u dan baku buskunan har kun yadda dashi"

"Kwarai kuwa ai damai bayarwa muke yi,kuma dagani ma yana da kirki"

Haka dai muka cigaba da firarmu cikin farin ciki.


Umma ce ta leko dakin da muke duk mun kwankwanta har dasu Yaya Ma'u da a dakinmu zasu kwana ni ta kira na fito na sameta a dakinta nace
"Umma gani" bayan na zauna kusa da ita

Ta dubeni ta soma magana
"Hauwa kinsan Ibrahim abokin Jabir"

Na daga kai nace
"Eh kwanaki mun hadu da Yaya Jabir zai kaini makaranta"

Tace "yawwa to shine ya samu Jabir da maganar yana sanki tun kwanakin da kuka hadu, kuma bada wasa yake ba yace wa Jabir ya fadamiki,amma Jabir din yayi shiru yanasan ya sake fahimtar da gaske Ibrahim.din yake ko kuwa,ganin kullum Jabir ya hadu da Ibrahim sai ya masa maganar ki ya sanar miki abinda me ransa hakanne yasa Jabir ya yanke shawarar zai fadamin ni kuma na amince sai dai ko ke din,amma dai Ibrahim mutumin kirkine ina fatan zaki amince dashi"

Nayi murmushi da kaina ke kasa harga Allah nima bazance ban amince da Ibrahim ba saboda koba komai abokin Yaya Jabir ne kuma Yaya Jabir mutumin kirki ne inada yakinin abokinsama zai kasance haka.kuma ma yadda na dauki Yaya Jabir ba zai kawo abu na iya bijerewa ba saboda inada yakinin yana kaunarmu fiye da yadda nake tunani yakan dauki matsalarmu kamar tasa.ga uwa uba ma gaskiya ba macen da zata ga Ibrahim indai yace yana santa ba taki amincewa ba"

Hakan yasa nace wa Umma na amince daganan na tashi na koma dakinmu na kwanta ina farin cikin da ya kasa boyuwa a zuci har saida fuskata ta muna

Ranar Lahadi aka daura auran su Yaya Sule duk diyoyin Alhaji Audu dan uwan Baffanmu ubangidan Baffanmu duk suka aura Yaya Abdu kuma jikar Alhaji Audu ya aura diyar Gwaggo Hajara,Gwaggo Hajarar da Baffa yaso aura a baya anyi bikin cikin tsari dukkansu su Yaya Bello da Yaya Abdu a waje Baffa yayi musu gini Yaya sule ne yace a gida yake son zama wani part aka ware masa shida matarsa.A wannan bikin kuma Yaya Sumusi babban dan Gwaggo Hafsatu yaga Yaya Safiya ya nuna yanasan aurenta harma ya fadawa Baffa re da ya nemi amincewar Yaya Safiya baffa yace babu matsala ya bashi.don shi a tunaninsa Yakumbo Hasiya babu abinda diyoyinta ko jikokinta zasu nema a gurinsa indai yanada shi bai masu ba kasancewar Yakumbo Hasiyar kanwar Malam Jauro mahaifin Baffanmu ga shi kuma Yakumbo Fati surikan Baffa ce mahaifiyar Mama Hanne hakan yasa baiyi tunanin halin da Yaya Safiya zata kasanceba idan ta auri Yaya Sunusin kasancewar kiyayyar da danginsa ke muna mana,kuma Yatya Safiya a lokacin ta amince da Hashim don ta fahimci mutumin kirki .Aiko koda Baffa ya fadawa Umma maganar Yaya Sunusi nan ta sanar masa Yaya Safiya tana da saurayi Hashim Baffa yace saidai Yaya Safiya ta basa hakuri tunda gana gida da Umma takara magana yace abinda ya shirya kenan gwara tun wuri tasa Yaya Safiya ta bawa Hashim hakuri.Mama Hanne da taji labarin Yaya Sunusi nasan Yaya Safiya ba karamin murna tayi ba don indai auran ya tabbatar Kaduna zatace Yaya Sunusi ya dawo ya sauna shida Yaya Safiya ko banza Yaya Safiya ta zama boyi boyinta wannan kenan Yaya Safiya har kuka tayi da aka sanar mata labarin tasan shikenan zata zama abar tausayi tunda har taga Mama Hanne bata hana ba tasan kuwa da cewa akwai abinda suka shirya,ga kuma uwa uba tana matukar son Hashim Wanda Hashim din ya kasance haifaffan Adamawa aikin gidan Radio ya kawo Kawunsa Kaduna ya taho da dashi. koda ta sanarma Hashim din ta bangarensa nuna mata yayi bakomai duk abinda Allah ya tsara shine dai-dai hakan kuma baisa ya daina zuwa gurin Yaya Safiya ba.niko nida Ibrahim muna soyayyarmu cikin girmama juna duk iyayenmu sun sani,don murna sosai yayi don yasan baban Ibrahim sosai shima dan kasuwa ne hakan ya Kara karfafa soyayyarmu jira ake kawai na kammala sakandire a mana aure da lokacin nake aji 3 a sakandiren batun hidima kuwa Ibrahim yana yi mana hakan yasa ba muda wasu matsaloli masu yawa a yanzu sai dai Umma san itada Baffa babu wani mutunci tsakaninta dashi komai ta masa gaban Iowa hantararta yake da fada mata bakaken maganganu Mama Hanne kuma ta dora da NATA kota zuba Baffa amma hakan baisa Umma indai ba Baffa ya kaita makura ba tayi magana ba Allah ya zubawa Umma.hakuri a kullum.na tuno Umma nakan jinjinaa hakurinta ba duka mace za'a samu da shi ba.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment