Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Muheebbahn Abiy sweetien Ammi, ina so kar wanda ya ɗau qiran yayanku ko da ya qira ku karku ɗauka inaso mu masa surprise shi da Ammi".

Cikin gamsuwa da batun Abiy sweetie ta rungumesa ta masa peck a kumatu itama sweedy rungumesa tayi ta masa peck ɗin dan sun yarda da Abiyn su.

Sweerie ke sauqowa a benen da zai sada ka da ɓangaren su tana magana cikin harshen turanci "sweedy me kika bawa rigimanmiyan Ammi tayi shir... Maganan bakinta ne ya maqale ganin Abiy zaune a palourn, da mugun gudu ta gangaro ko takalmin hill's da ta saka bata damu da shi ba tana isowa ta faɗa jikin Abiy tana cewa "Abiy surprise! sannu da zuwa".

Rungume ta Abiy yayi ya mata peck a goshinta yace "Munawwaran Abiy ya school?

"School lafiya ba daɗi Abiy dan ma an bamu hutu".

"Yauwá good dai-dai kenan kunga sai mu tafi Nigeria tare wajan Ammi".

Waro ido tayi tace "Abiy! Darling fa ya hanamu yace kar ya kama qafanmu a Nigeria har sai sun dawo tare da Ammi in ba haka ba zai saɓa mana".

"Wasa yake muku sweerie, yanzu zamu tafi gobe da wuri in Allah ya yarda amma kar ku faɗa masa muma mu masa surprise".

Ɗaga kafaɗa tayi tace "shikkenan Abiy Allah ya kaimu amma tunda kazo Abiy ka kaimu yawo".

Murmushi Abiy yayi yace "duk kuje ku shirya ba na wasta ruwa mu tafi".

Sweerie tace "ni dai a shirye nake Auta da sweedy ne zasu shirya".

Abeeyh sama ya haura, ɗakin da yake mallakin sa a gidan ya shiga ya wasta ruwa ya sanja kaya.
Qananun kaya yasa inka gansa ba zaka ce ya haifi DMD ba dan kaman matashi haka ya koma kayan ya amshe sa kuma Abiy ba dai kyau ba dan kusan a wajan sa yaran suka ɗauko rabin kyawun su.

Suka fita Abiy ya kaisu Park ne restaurant ne etc yawo suka dinga yi sune basu dawo gida ba sai bayan isha'i, suna dawowa kowa ta shiga ɗakinta sweetie kuma tabi Abiy dan ta dage a wajansa zata kwana.
Sallolin su suka yi kamun kowa yabi lafiyar gado ya kwanta tunda Abiy yace musu gobe da wuri jirginsu zai tashi.



𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚'𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 - 250 𝟏𝐆𝐁 - 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 500
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎......




⭐⭐

"Wai me yasa ba zaka ci abinci ba son? Ko bai maka ba ne na dafo maka da kaina" cewar mummy da idanuwanta ke kan DMD.

Shafa kansa yayi mai cike da baqin gashinsa mai stayi yace "habibty na qoshi ne fa".

"Ka qoshi me kaci?

"Uhmn ɗazu munje gidan Abiy to na ci a can".

Mummy kallonsa take da mamaki domin kuwa qaryan ma bai amshe sa ba tunda kowa yasan ba shiri yake da matar Abiy ba balle yaci abincin ta, kallon Jay tayi tace "jabeer kunje gidan Abiyn naku?

Jay sosa qeya yayi yana kallon DMD dake lumshe masa ido alaman yace eh, hararan sa yayi kamun yace wa mummy "eh Habibty munje".

"Shikkenan to" mummy ta faɗa a taqaice suka ci gaba da cin abincin wanda a qarshe shikam miqewa yayi ya haura sama.

Bayan Jay ya gama cin abinci ya tashi yana sunne kai dan yasan mummy ta san qarya suka mata, ya haura saman shi ɗin ma. Yana shiga ɗakin ya tarar da DMD na ta aikin jan tsaki sai ya kalle sa yace "ka sa ni yiwa habibty qarya kai kuma kazo nan kana aikin tsaki kaman tsaka kai da waye?

Hararansa yayi yace "ni inba dalili ba har banson zuwa Nigeria kuma kai ma har da kai a masu hanani, surutu kaman parrot, ni da rabuwa da ciwon kai nasan sai nabar qasar nan".

Jay ya taɓe baki yace "tunda ance maka bansan hanyan Canada ba dole kace haka, yanzu dai me kake wa staki?

"Layin sweedy nake ta qira baya shiga duka layukansu a gidan baya shiga na driver na kuma ba'a ɗauka, so bansan ko lafiya ba".

"To ka bari zuwa safiya mugani amma nasan Insha Allahu lafiya lau ne".

DMD tashuwa yayi ya fita a ɗakin ya tafi nasa dan shi baya iya kwana da wani a ɗaki ɗaya balle gado ɗaya in ba sweetie ba.
Yana shiga yayi shirin kwanciya ya kwanta dan so yake ya tashi da wuri ya samu yayi nafila anjuma.


Abiy da sassafe ya sako su a gaba suka dawo Nigeria inda qarfe sha biyu ya same su a cikin garin Gombe.
Da sallama ya shigo palourn riqe da hannun sweetie, Aunty Amarya na murmushi ta fito sashin ta tana musu sannu ta ɗaga sweetie tana cewa "my baby girl nayi kewanku".

Sweetie dai taqi sake fiska dan damuwan ta taga Ammi.

Sweedy suka yi hugging Aunty Amarya ta musu peck a goshi tana cewa "babies nawa nayi kewanku"
Duk murmushi suka sakar mata taja hannun su har sashin ta, tasa mai aiki ta kawo musu komai suka ci tare da Abiy suka gama.

Sweetie ta kallesa tace "Abiy ina Ammi fa?
Murmushi ya mata yace "ku kwantar da hankalinku Ammi na Ashaka gidan Hajja jibi zata dawo okay".

Sweedy da sweerie miqewa suka yi zasu fice a sashin sai Aunty Amarya ta kallesu cike da kirsa tace "babies na ba zamu zauna anan kamun Ammi ta dawo ba?

Kamun su buɗe baki yin magana Abba ya rigasu yana washe baki yace "a'a ki qyale su suje can su huta, Muhseenan Abiy kuje sashin Amminku ku huta ko".

Qarisa ficewa suka yi ba tare da sunce komai ba, sweetie ta kalli Aunty Amarya ta harare ta sannan ta kalli Abiy tana tura baki tace "ni dai Abiy da kai zan zauna har sai Ammi ta dawo"

Abiy ba yanda ya iya da rigiman sweetie dan sun sakalta ta daga shi har Amminta da yayyunta dan haka dolen sa ya mata murmushi yace "sosai ma Muheebbahn Abiy gaki ga Abiyn ki har Ammi ta dawo my ƴar lukutan yarinya ta"

Tura baki tayi tace "Abiy bana so".

Aunty Amarya dake zaune ta cika tayi fam ji take kaman ta rufe ta da duka amma sai murmushin yaqe take musu a ranta kuwa ayyana abinda za tawa Muheebbah in Abiy ya fita take "sweetie a wajan Aunty zaki zauna ma ba Abiy ba".

"A'a ni dai wajan Abiy na tunda banga Darling ba halan shima yana tare da Ammi" ta faɗa tana shagwaɓe fuska.

"Karki damu Muheebbahn Abiy kina wajan Abiyn ki ko!
Sai sweetie ta gyaɗa kai alamun "eh".

Aunty Amarya murmushin yaqe kawai take amma ji take kaman ta kamata ta cinye ta ɗanya dan tasan yarinyar da shegen sakalci yanzu ko ina Abiy zai je zata ce zata bi sa in dai ta bari yayi nesa da ita to sai in zai shiga banɗaki, shiyasa bata son suzo kuma ta gwammace yayyun ta suzo akan ita tazo gwanda ma in da Ammi ta zo.

DMD sakamakon nafilfilun da yayi tun da ya dawo sallahn asuba ya kwanta shine bai tashi ba sai wajen qarfe sha-ɗaya 11, yana ganin time da mugun sauri ya sauqa a kan gadon sannan ya shige bayi wasta ruwa yayi ya fito ya shirya sama-sama ya leqa ɗakin Jay bai gansa ba sai ya sauqo palour nan ma bai tarar da kowa ba, hanyan ɗakin mummy yayi yana isa yayi sallama aka masa izinin shiga ya shiga ya tarar da ita tana gyara ɗakin nata sai ya stugunna ya gaishe ta yana cewa "habibty kawo na gyara miki".

Murmushi tayi tace "aikam son ni sheda ce yanda kake gyarawa Ammi ɗaki yayi kyau ɗin na amma dai na hutar da kai zauna abinka na gama ma".

Zama yayi a bakin gado yace "habibty Jay fa ban gansa ba kuma na qira layinsa bai shiga ba".

"Yanzu dama bai faɗa maka ba, ɗazu Afreen ta dawo kuma sun tafi Ashaka dan kana bacci ne ma dama Daddyn ku yace aje da kai dan tun ba yau ba yake binsu suje".

Taɓe baki yayi yace "Alhamdulillahi ina bacci ma suka tafi dan ba inda za ni, yanda halin stohuwar nan yake haka halin Abiy yake ina zuwa za tabi ta isheni da surutu tana zagin baiwar Allah bata ji ba bata gani ba".

"Allah shirya ka son, mahaifiyar mu ce ke masifa ko?

Shiru yayi bai ce komi ba ya miqe yana cewa "habibty ban karya ba" ya qarisa ficewa.

Tashuwa mummy tayi ta biyo bayansa ta same har ya shiga kitchen da mamaki take kallon sa tace "son ba dai girkin za kayi da kanka ba?

"Eh Habibty yanzu zan gama inaso na fita da wuri naje masallaci akan lokaci na bada abun sadaka a tayamu da addu'a".

"Oh to shikkenan, amma je ka zauna zan dafa maka me kake so?

"Habibty Allah ki huta indomie ne yanzu-yanzu zan gama nazo muci sai na tafi".

Mummy tayi-tayi amma yaqi bari ta dafa masa, haka ta haqura ta koma palourn ta zauna tana jiransa.
Indomie ya dafa sai ya soya qwai ya juye duka a plate ya kashe gas ɗin ya fito, a kujera ya samu mummy na zaune, sai ya jawo center table ya ajiye plate ɗin yaje fridge ya ɗauko wa mummy abun sha ya ɗauko nasa.
Mummy tana 1 spoon ta kalle sa tace "son wai kai ka dafa?
Yana murmushi yace "eh habibty ai har rice na iya dafawa"

"Eh lallai in-law tamu ta huta wannan iya girki kace in kana amarci na ɗan 1 month da ake kai abinci ka hutar da mu zaka dinga muku, indomie har da hanta da kifi ga cabbage ni Maryam ina na taɓa gani gwanda in Afreen ta dafa nakan ga tasa hanta wani lokacin amma bansan ana sa wannan duka ba"

Murmushi yayi yace "habibty ki staya santi zan cinye ne yanzun nan".

Suka gama ci ya tattare komai ya kai kitchen ya dawo palourn suka ɗan taɓa hira kamun ya mata sallama zai je gidan Abiy, mummy ta masa a dawo lafiya.

Yana fita yasa driver ya kai shi gidan Abiy, suna isa ya sallami drivern ya dawo dan dama so yake yazo ya ɗau motan sa dama da na Jay suke yawo kuma ya tafi Ashaka.

Ba tare da yayi knocking ba ya tura qofan palourn ya shiga dan Sallaman ma a ciki-ciki yayi shi.
Hanyan da zai sada shi da sashin sa ya nufa sai kaman ance juyo ya kalli qofan sashin Ammi a buɗe, da mamaki yake kallo yasan dai Ammi ke da key sai Abiy kuma shigowansa bai ga motan Abiy ba dan shiyasa ma ya shigo da qarfin guiwansa don baison abinda zai sa ya haɗa hanya da Abiy gudun kar a samu mastala.

Sharewa yayi ya wuce sashin sa ya bari akan ko Abiy ya sa a gyara sashin ne tunda dama ko bata nan ana mata shara.

Yana shiga ya kullo qofan sa, kallo ya qarewa sashin nasa ganin duk qura alaman anjuma ba'a shigo ba.
Kwaɓe fiska yayi yace "yanzu da Ammi na nan nasan da an gyaramun tunda ita kam na bata key na kuma na hana kowa shigowa in ba ita ba, da ace ma Ammi nanan me zai kawo ni wannan trouble Nigerian rashin Ammi ya kawo ni, Allah ya bayyana ta mu koma".
Duba time yayi ganin har 12 yayi sai ya ɗauko mooper da abun shara sama-sama ya gyara palourn nasa ya wuce cikin ɗakin sa ya share ya gyara shima da kyau ya shiga banɗaki ya wanke tass, shine bai gama aikin ba har qarfe ɗaya da rabi 1:30 sannan ya cire kayan jikin sa ya ɗaura towel ya shige toilet.
Yana gama wanka ya fito ya je gaban dressing mirror ya shafa mayukan sa ya shafawa kansa ya taje ya taje gemun sa duba lokaci yayi yaga qarfe biyu saura sai ya wuce ya ɗauko manyan kaya wata dakakkiyar jamfa milk color ya saka ya ɗau hula ya kafa.
Masha Allah! Manyan kaya ba qaramin kyau suke masa ba wanda shima kanshi ya sani kawai yanayin rayuwan outside ne da kuma shima bai dame sa ba yafi son qananan kaya.
Ya gama shirin sa da komai qarfe biyu ciff 2:00pm ya feshe jikin sa da turarukan sa iri da kala wanda sanyin qamshin su da daɗin su har hawa kai suke ga kuma sanya nistuwa ga mai shaqan su.

Sweerie na zaune a palourn Ammi sai taga kaman giftawan mutum yayi hanyan sashin yayansu, kamun ta fito kuma ba taga kowa ba taje jikin qofan ta murɗa handle nan ma taji a kulle sai ta juya tana cewa may be idon ta ne kawai.

Aunty Amarya da fitowanta kenan a sashinta tun da taji an buɗe gate kuma ta ga shi ya shigo sai tayi sauri ta fito amma sai ta tarar sweerie ce kawai a palourn, qwafa tayi fuska a haɗe tace "Munawwara tashi kije kitchen ki taya mai aiki girki, ko so kuke mu aurar da ku a dawo mana da ku baku iya komai ba mun sakalta ku?

Sweerie kallon Aunty Amarya tayi kawai ta miqe ba tare da ta mata musu ba tayi hanyan kitchen dan dama ita girki bai dame ta ba ko a can Canada suna girkinsu Ammi ta hana masu aiki yin girki, sai share-share da sauran ayyukan.
Aunty Amarya cije leɓe tayi dan taso ace ta tanka mata ta koya mata hankali amma abun haushi yake bata ko tayi abu basa tanka mata balle ta samu daman ce wa sun mata reni dan yaran staff halin uwar su gare su na haquri da kawar da kai ba ruwan su, juyawa tayi cikin jin haushi ta koma ciki.
Sweerie sun gama girkin tare da mama mai musu aiki sai ta fara jidowa tana kawo wa dinning, ta ɗauko kulan qarshe me cike da ferfesun naman zabuwa(Abiy baya cin kaza) tana fitowa a kitchen kaman daga sama aka jefo sa ta kalli mutum a stakiyan palourn ya nufi waje sai kawai ta sake kulan hannun ta tace "Darling!!

Ɓangaren DMD fitowa yayi ya kulle sashin sa ya nufi hanyar fita har ya kusa qofan palourn ya jiyo qaran faɗuwan abu sai kuma yaji muryan sweerie na faɗin "Darling!
Juyowa yayi mamaki fal ransa yace "sweerie, ke kuma a Nigeria ke da wa?

Qarasowa tayi tace "Darling kayi kyau, Abiy ne yaje ya ɗauko mu sweedy na ciki sweetie kuma sun fita da Abiy ta bisa masallaci".

Maimaita kalman "Abiy ne ya ɗauko mu" yayi sannan ya kalle ta ransa a matuqar ɓace yace "yaushe kuka zo?

"Ɗazu da safe muka zo, Darling wai kuna tare da Ammi ina take? Ko ka baro ta acan ne?

Kallon ta yayi kawai bai ce komai ba sai ya duba agogon hannun sa yaga ya kusa yin latti, cikin sauri yace "before na dawo ku tabbatar kun shirya" yana faɗa ya fice.

Ko ta kan kulan da ta yasar bata bi ba ta juya ta shige sashin Ammi tana qwala wa sweedy qira "sweedy! sweedy! sweedy!"

Fitowa tayi a ɗakin su tana cewa "irin wannan qira lafiya?

"Sweedy yanzu na ga Darling zai tafi masallaci".
Da mamaki take kallon ta tace "Darling dai sweerie ba Abiy yace mana suna tare da Ammi ba?"


FAN'S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.


INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚


𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله


LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member's ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR'S ANNIVERSARY


Ƙawalliya Dija k'aya ga naki page ɗin (Fulanin Royal Star) marubuciyar KAINUWA DASHEN ALLAH.

JAHILCI KO AL'ADAH? FAN'S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku🤝



FAN'S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.


💋💋 امى بتولة💋




𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 25_26




"Allah shi ne kuma nima naji mamaki na tambaye sa Ammi fa sai yace bari ya dawo daga masallaci zai yi latti".

"To Allah dawo da shi lafiya dan na mastu na kalli Ammi".

"Amma fa inaga shi kaɗai yazo dan yace mun mu shirya kamun ya dawo wataqilan zai kai mu wajan Ammin ne".

Yana ficewa a gidan ya ɗauki motan sa qirar Toyota mai tinted glasses ya mata key sai babban masallacin juma'a na qofan Sarkin Gombe.

Yana zuwa Allah ya taimake shi ba'a fara salla ba nan ya samu ya lallaɓa har wajan liman da ya idar da khuɗuba suka gaisa cikin mutuntawa ya faɗa masa buqatan sa, nan limamin yace masa mahaifin sa ya jima da masa magana kuma suna kan addu'a, godiya yawa limamin sannan ya bada kuɗi a sayi abun sadaka 2million ya basa check dan dama tun a gida ya rubuta check ɗin.

Suna gama magana da liman ya koma wajan zaman sa ya zauna jiran a tada Salla yana danna counter (carbin qirge) zuciyansa cike da tunanin dama Abiy ya damu da ɓatan Ammi ne da har ya bada ayi addu'a? Inda gefe ɗaya kuma yaje cike da taqaicin zuwan su sweetie Nigeria.
Ajiyan zuciya ya sauqe jin ana qiran sallah sai ya miqe shima ana idar da Qiran kamun a tada iqama ya jero addu'oeen sa ya shafa aka tada sallah.

***
Manzon Allah SAW yace "ku kasance masu miqa addu'oeen ku ga mahaliccin ku Allah maɗaukakin Sarki a ko wanni lokaci sannan mafi soyuwar lokaci ita ce yayin da liman yake tada iqama na sallahn asuba da kuma ranar juma'a domin kuwa a ranar juma'a akwai wani lokaci wanda ke ɗauke da sa'a wanda duk wanda Allah ya nufa yayi addu'ansa a wannan lokacin ta sa'ar to ba hijabi tsakanin karɓuwan addu'an sa ga Allah".

To sai malamai ke cewa wanne lokaci ne wanda Annabi stira da amincin Allah su tabbata a garesa ya ambata? Wasu daga cikin malamai ke cewa sa'ar na nan lokacin sallar asuba ta ranan juma'a, wasu kuma suce tana nan a lokacin da liman ke qiran sallah kamun kuɗuban farko wasu kuma suce kuɗuba na biyu wasu kuma suce yayin ta da iqaman sallahn juma'a.

Mu qwata wunin juma'ar mu da zikiri da ambaton Allah da kuma yawaita salati ga shugaban Annabawan Allah Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ♥️

WALLAHU A'ALAM.
***

Suna idar da Sallah, aka ɗaura aurarraki aka yi addu'a sannan liman ya roqi jama'a da a taya su da addu'a akan ɓatan wata baiwar Allah, nan aka kuma addu'a aka shafa.

Yana fitowa yayi ta aikin raba sadaka, dama halinsa ne kyauta duk ranan juma'a kuma yana sadakan kuɗi wani bin har da abun ci.
Yayi wa masu Dabino da Alewa juye kowa ya raba sadaka sannan ya shiga motan sa ya ja ya nufi anguwansu GRA.


Mama mai aiki tana fitowa kitchen tayi mummunan gani, dan a wajan ta wannan mummunan gani ne dan tulin jarabar da yau zata kwasa akan wannan aika-aikan, kulan ferfesun Abiy a yashe a qasa.
Cikin hanzari take qoqarin tattare wa kamun aunty amarya ta fito ta gani ta fara mata tijara, amma sai aka yi rashin sa'a tana cikin share wajan Aunty Amarya ta fito.
Kallon mama mai aiki tayi sama da qasa tace "me wannan ya zube?

Cikin in e na tace "ha...ha... Hajiya ayi haquri nima wa...wall....wallahi bansan da.. da wannan aiki ba sai yanzu na gani".

Malalacin kallo ta wasta mata sama da qasa dan ko ba'a faɗa ba tasan ferfesun Abiy aka zubar kuma daga maganan mama mai aiki ta gane Munawwara ce ta zubar, dan haka rai a ɓace tana huci ta nufi sashin Ammi.
Ba sallama ta tura qofa ta shiga tana haqi tana huci kaman za taci babu, tana qwala wa sweerie qira "Keeeee! Keeeee! Munawwara".

DMD da ya iso gidan ya buɗe qofan palourn kenan ya shigo sai yaga bayanta ta shige sashin Ammin sa kuma ta banko qofa, rai a ɓace ya buɗe qofan sashin ya shiga amma sai ya tsaya a bakin qofa yana qare mata kallo jin irin qiran da take wa sweerie kaman ita ta raɗa mata sunan, tsayawa yayi ganin iya gudun ruwanta.

Bata san da shigowan sa palourn ba ta ci-gaba da cewa "Munawwara! Munawwara! Keee Munawwara ba ke nake qira ba?

Cikin sauri Munawwara ta fito a ɗakin, sanye take cikin dogon riga wanda bai kama jikinta sosai ba bai kuma mata ruwa sosai ba, idanuwan ta akan Darling dake staye bakin qofa suka sauqa amma sai ya mata alama da kar ta nuna ta gansa.

Cikin qufula Aunty Amarya tace "ke dan uwarki ba ke nake qira ba kika yi banza da ni? Ina wasa da ke ne zaki zubar da abincin miji na dan nace kije ki taya ta girki wato gaki fistararriya ko? Tunda ba Uwarki ce ta sanya ki ba dole kimun ta'adi tunda buri kuke ubanku ya sake ni ya zauna da uwarku kawai kuna taya ta kishi ko?

"Kiyi haquri Aunty ba da sanina bane ya faɗi a hannuna kiyi haquri" Munawwara ta faɗa idanuwanta cike da ƙwalla sakamakon masifan Aunty Amarya, dan su basu saba da masifa ba balle stawa, Ammi bata musu Abiy ma haka Darling ma haka.

Tsabar masifa Aunty Amarya har qanqance ido take kaman zata rufe sweerie da duka, cewa tayi "Har zaki ce bada saninki ba dan uwarki" ɗaga hannu tayi zata sharara mata mari

Please Login or Register in order to submit comment