Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa office ne?
Lumshe ido yayi tare da jingina kansa a jikin kujeran yana faɗin "akwai zuwa office Ammi, sannan companyn da ke Jigawa ma suna buqatar gani na, ga kuma wanda ke Zamfara wai meeting kuma dole sai da ni, gaskiya ni sayar da companies da ke Nigeria duka zan yi banson headache da yawa ba son zuwa Nigerian nan nake ba".
Da mamaki Ammi da Dr Mufaddal ke binsa da kallo, Ammi ce ta fara magana "kuma sai aka yi rashin sa'a a Nigeria aka binne cibiyanka ba, citizen of Nigeria by birth ba ka da inda ya fi shi, duka ka shirya zuwa ka tabbatar ko bayan raina baka sai da qadaranka ko guda ba a Nigeria".
Dr Mufaddal ne ya numfasa ya ce "ka tabbatar ka halaccin meeting ɗin amma ka kula dan naji kaman Zamfara akwai issues a garin ga kidnapping ga sace-sace so ka kula".
Darling kaman zai yi kuka kawai ya miqe ya fice a Palourn.

Sweetie ce ta fara fitowa ta kalli kakan nasu ai da gudu ta koma ta tashi sweerie inda hayaniyan nasu ya tashi sweedy ita ma a baccin, jin sweetie na faɗin kakansu ya zo duk ba shiri suka wanke fiska suka fito palourn suna qiran sunan sa.

Dr Mufaddal jin muryan jikokinsa sai ya fara washe baki, ya buɗe hannu duk suka zo suka shige jikinsa suna faɗin "grandpa yaushe ka zo? Sannu da zuwa, ina staraba?
Yana murmushi duk ya amsa musu, sannan sweedy tabar jikinsa, sweetie da sweerie suka maqalqalesa, Ammi ce tayi magana su tashi amma sweetie yaqi sauqa a jikinsa, ita sweerie kuma ta sauqa ta zauna gefensa suka sanya shi a gaba suna masa hira.
Ammi miqewa tayi tabar palourn, wanka tayi ta shirya sannan ta dawo ta korasu suyi abincin rana su bar Papa ya huta.
Dr Mufaddal ɗakin da yake mallakin sa a nan palourn qasa ya shige ya wasta ruwa sannan ya kwanta dan ya huta.

Sai da suka gama ayyukan abinci sannan duk suka yi wanka Ammi ta sanya sweedy ta qira Papa, Afreen kuma ta qira Darling, Papa sun fito tare da sweedy amma Darling Afreen ta samu baya sashinsa, qiransa Ammi tayi ya tabbatar mata yana office sannan suka wuce dinning duka, Afreen ce tayi saving nasu kowa ya fara cin abincin cikin nistuwa ba tare da surutu ba.

Zaune yake a office nasa hankalinsa gaba ɗaya na kan aikin da yake yi a system nasa, knocking da aka yi ne ya sanya shi mai da idanuwansa kan ɗan computer da ke jone da CCTV camera da ke wajan office nasa, ganin wanda ke staye a qofan sai ya buɗe baki kaman baison magana ya ce "come in".
Mutumin ne ya buɗe ya shigo, sai da ya basa izinin zama kamun ya zauna, inaduwansa na kan system da yake aiki a kai ya ce "Yes", jin haka sai mutumin da ya shigo ya fara masa bayani a nuste, sai da ya kammala bayaninsa sannan a nuste cikin girmamawa ya ɗaura da cewa "Oga akwai buqatan shiganka Nigeria dan kayan da aka kama ba kaɗan ba".
Har mutumin ya gama magana ko mostawa bai yi ba balle ya kallesa, gaba-ɗaya idanuwansa na kan system nasa, sai da ya ɗau mintuna masu yawa sannan ya janye system ɗin zuwa gefe ya sanya hannu ya rage tied na wuyansa, kaman baison magana ya ce "ba mastala za ka iya tafiya" daga haka ya danna wani button akan table da ke gabansa, sai ga wata baturiya ta shigo, ba tare da yace mata komai ba ta wuce ta ɗauko masa magani a cikin wani haɗaɗɗen box ta miqa masa, sai da ya sha sannan ta mayar, mutumin ya fice itama ta fice, duba time yayi, ganin lokacin kaman zai yi kuka ya miqe ya shige haɗaɗɗiyar toilet nasa ya ɗauro alwala sannan ya fito ya shige wani daki da ya gaji da haɗuwa ya shumfiɗa sallaya ya gabatar da sallahnsa.
Da ya idar ya fito ya kuma jawo system ɗin ya cigaba da abinda yake yi.

Mutumin na fitowa daga office na DMD ya tsaya jin maganar abokin aikinsa "John daga ina?
Wanda aka qira da John ɗin ya ce "daga office na Oga, kasan wannan karon ansamu mastala".
"Wai ai naji maganan, kaya ba kaɗan ba, Oga sai ya kasa zama".
John na dariya ya ce "nima nayi tunanin hakan, amma bakasan abun mamaki ba, in kaga Oga kaman ba abinda ya faru, dan cemun yayi ba mastala, ni na rasa Oga wani irin human being ne ba'a gane yana farinciki ko akasin haka, kullum fiska ɗaya kuma ko ba shi yayi dogon magana ba indai aka masa sai ya sha magani".
"Hhhh! John ai lamarin Oga sai a hankali, mu wuce eatery antashi break lokacin sallah yayi" suka nufi lifter suna kan hiransu, duk abinda suke faɗa da turanci suke faɗa.

Sai da ya kammala komai sannan ya fito, sect.liliyan tana binsa riqe da wayoyinsa da jacket nasa har sai da ya shiga mota sannan ta juya, driver ya ja suka nufi gida.
Suna isa driver na gama parking ya fito bayan ya tattare wayoyinsa, da sallama ta shiga palourn amma ganin ba kowa sai hakan ya masa daɗi dan dama a gajiye yake, kawai sai ya haura sama sashinsa, ruwa ya wasta ya bi lafiyan gadonsa ya kwanta.

Sai dare kamun ya sauqo palourn qasa, inda ya tarar da Dr Mufaddal da su Sweedy duka, Afreen na ganinsa ta miqe tana masa sannu da shigowa, ba tare da yace qala ba kawai ya ɗaga mata kai tare da zama gefen Dr Mufaddal yana faɗin "landlord yaushe za ka koma?
Dr Mufaddal abun ma dariya ya basa, sai ya ce "korana kake yi kenan? Dan ma nazo ganinku ko".
Shiru Darling yayi bai kuma cewa komai ba illa wayansa da ya ciro yana laste-lastensa.
Sai can Ammi ta fito, suka yi dinner sannan ya tashi zai haura sama amma sai Dr Mufaddal ya dakatar da shi akan za suyi magana, su sweedy ya kora kowa ya je ya kwanta, dukansu haurawa sama suka yi inda suka kunna TV suna kallo, sweetie ce taqi binsu sama wai ita wajan Dr Mufaddal za ta kwanta, kallon da Darling ya aika mata da shi ne ya sanyata miqewa tana kuka ta haura sama itama, ganin haka sai ya taɓe baki kawai, Ammi da ke zaune tana jinsu murmushi ta yi tana faɗin "ka takurawa jinjirata, mutum da Angonsa za ka korasa ga shi ka sanya mun Auta na kuka, in na mutu zaka kula da sweetie kuwa Darling?
Shi dai shiru yayi bai ce komai ba, ganin haka sai Dr Mufaddal yayi gyaran murya tare da cewa "Maimoon je ki ɗauko min takardan da Mustapha ya baki".
Ammi shiru tayi kaman wacce ruwa ta cinye ta, dan mamaki ya kamata na yaushe Papa yasan da maganar wani takarda, amma sai ta fuske ta ce "Papa wani takarda kuma?
Kallonta kawai yayi ya murmusa nasu na manya ya ce "Maimoon banson magana biyu ke kinsani, ina takardan da Mustapha ya baki? Inkuma bai baki takarda ba me ya dawo da ke Canada da zama? Ko kin manta me kika ce a India lokacin da Mufaddal ya buqaci ki dawo Canada ku zauna".
Ammi qasa tayi da kanta ta kasa cewa komai, amma mamaki take wa ya sanar masa, tasan dai Abiy ba zai sanar masa ba kuma Mufaddal ma haka, sannan yaran ma ba zasu sanar masa ba, gaba-ɗaya kanta ya ɗaure, maganan Dr Mufaddal ne ya dawo da ita daga tunanin da take yi "Maimoon ba da ke nake magana ba?
Darling dai yana zaune shiru, yana danna wayansa bai ko ɗago ba balle ya ce musu uffan, Dr Mufaddal ne ya sake magana sai Ammi ta miqe ta haura sama, ɗakinta ta shiga ta buɗe drawern ta ta ɗauko takardan ta dawo da shi, cikin girmamawa ta miqawa Papa amma sai bai amsa ba ya mata nuni da ta zauna, zama ta yi sannan ya ce "inaso ki buɗe takardan nan da kanki ki karanta mun abinda aka rubuta, Ammi da yanayinta ya fara sauyawa kaman za tayi kuka ta ce "Papa kayi haquri amma bazan iya karantawa ba".
Darling ganin har idanuwan Ammi ya fara tara ƙwalla sai ransa ya ɓaci kallon kakansa yayi ya ce "wai duk me amfanin karantawan? Ba dai ya sake ta ba ya zaɓi matar sa akan ta shikenan ku qyale ta muma mu huta munaganinta hankalinmu a kwance".
Dr Mufaddal murmushi yayi tare da girgiza kai sai ya ce "Maimoon miqawa Mufaddal takardan", Darling amsa yayi yana kallon kakan nasa ya ce "me zan yi?
Dr Mufaddal na murmushi ya ce "kai ka karanta mana".
Darling cikin yanayin ko a jikinsa da abinda ke cikin takardan ya qarisa warwarewa, ganin abinda ya fara tozali da shi sai ya waro idanuwansa.
Tunda Dr Mufaddal ya ga haka sai ya murmusa, yayinda Ammi kuma tayi qasa da kanta jira take kawai Darling ya karanta domin tun ranar da Abiy ya miqa mata ta sanya a handbag nata to ko ta kansa bata bi ba balle ta duba domin bata son ganin abinda ke ciki zuciyanta zai karye da yawa.
"Mufaddal ka karanta kai muke sauraro" ya stinci muryan kakan nasa na faɗin haka.



MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA.




INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله


LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member's ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR'S ANNIVERSARY

FAN'S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.


💋💋 امى بتولة💋


𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 45_46



Darling fara karanta abinda ke rubuce a takardan yayi kaman haka "𝗠𝘆 𝗠𝗮𝗶𝗺𝗼𝗼𝗻 𝗶𝗻𝗮 𝘀𝗼𝗻𝗸𝗶 𝗶𝗻𝗮 𝗾𝗮𝘂𝗻𝗮𝗿𝗸𝗶 𝗵𝗮𝗿 𝗮𝗯𝗮𝗱𝗮, 𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗶𝗻𝗮 𝗯𝗮𝗻𝘀𝗮𝗻 𝗱𝗮𝗹𝗶𝗹𝗶𝗻 𝘆𝗮𝘄𝗮𝗻 𝘀𝗮𝗺𝘂𝗻 𝗱𝗮𝗺𝘂𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝗺𝘂𝗸𝗲 𝘆𝗶 𝗯𝗮 𝗮𝗺𝗺𝗮 𝗸𝗶 𝘆𝗮𝗳𝗲𝗻𝗶, 𝗻𝗮𝗰𝗲 𝗸𝗶 𝘁𝗮𝗳𝗶 𝗯𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗯𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗼𝗻𝗸𝗶 𝗯𝗮𝗻𝗲 𝗮'𝗮, 𝗻𝗮𝗰𝗲 𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗻𝗲 𝗱𝗮𝗻 𝗸𝗶 𝘀𝗮𝗺𝘂 𝗸𝗶 𝗵𝘂𝘁𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗸𝗲𝗺𝗮 𝗻𝗮𝘀𝗮𝗻 𝗸𝗶𝗻𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗱𝗮𝗺𝘂𝘄𝗮𝗻 𝗿𝗮𝘀𝗵𝗶𝗻 𝘆𝗮𝗿𝗮𝗻 𝗻𝗮𝗻 𝗮 𝗸𝘂𝘀𝗮 𝗱𝗮 𝗸𝗲, 𝗸𝗶 𝘆𝗮𝗳𝗲𝗻𝗶 𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗮𝗯𝘂𝗯𝘂𝘄𝗮𝗻 𝗱𝗮 𝗻𝗮𝗸𝗲 𝗮𝗶𝗸𝗮𝘁𝗮 𝗺𝗶𝗸𝗶, 𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝗲 𝗺𝘂𝘁𝘂 𝗸𝗮 𝗿𝗮𝗯𝗮 𝗶𝗻𝗮 𝗾𝗮𝘂𝗻𝗮𝗿𝗸𝗶 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗿𝗮𝗻𝗺𝘂 𝗱𝘂𝗸𝗮"
𝗗𝗔𝗚𝗔 𝗡𝗔𝗞𝗜 𝗠𝗔𝗜 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗜 𝗠𝗨𝗦𝗧𝗔𝗣𝗔𝗛𝗡 𝗠𝗔𝗜𝗠𝗢𝗢𝗡 (𝗔𝗕𝗨 𝗠𝗨𝗙𝗔𝗗𝗗𝗔𝗟).
𝗦𝗮𝗶 𝘇𝗮𝗻𝗲𝗻 𝗵𝗲𝗮𝗿𝘁 𝗱𝗮 𝗮𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗻 𝗜 𝗟𝗢𝗩𝗘 𝗬𝗢𝗨, 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲 𝗱𝘂𝗸𝗮 𝗿𝘂𝗯𝘂𝘁𝘂𝗻 𝗱𝗮 𝗶𝗻𝗱𝗶𝗮𝗻𝗰 𝗮𝗸𝗮 𝘆𝗶 𝘀𝗮.

Ammi kaman za ta fire, a take ta nemi duka damuwan da ke damunta ta rasa sai wani farinciki take ji mara adadi, amsan takardan tayi ta qara karantawa, hawayen farinciki da kewan Abiy ya zubo mata ta share sannan ta naɗe takardan.
Duk abinda take yi Papa da Darling suna kallonta, shi Darling ji yake kaman ya rusa ihu dan taqaicin Abiy ganin ya gama wulaqanta masa Amminsa sannan yazo yana faɗin wani abin daban, sai dai ba zaka fahimci hakan daga fiskan Darling ba domin wayansa ya jawo ya ci gaba da dannawa, Dr Mufaddal dai murmushi yayi dan ya sani tabbas yarinyansa soyayyan gaskiya take yiwa Mustapha da wuya ace wai rabuwan ne suka yi, sai kuma ya maida kallonsa kan Darling, ganin abinda yake yi sai ya murmusa kawai bai ce uffan ba, ya dubi Ammi ya fara magana "ina fatan kinji kuma kingani saqon mijin naki ba rabuwa da ke yayi ba?
Ammi na murmushi ta ce "eh Papa".
"Okay! To Yana da kyau duk lokacin da abu zai haɗaki da mutum ki tabbatar kinyiwa mutum uzuri domin kinga yanzu da ace yayi fushi da ke to zaki tabbata cikin stinuwan Mala'iku ne domin ba rabuwa yayi da ke ba kina da auren sa a kanki amma kikaqi sauraransa balle kiji me zai ce miki, kuma kikaqi duba takardan balle kisan hukuncin da kika yanke dai-dai ne ko akasin hakan, kiyi haquri ako da yaushe shi ne abinda zan faɗa miki domin ke kinsan wani irin aure kuka yi kuma kinsan irin soyayyan da Mustapha yake miki, daga qarshe kuma inaso ki tattara ki koma gidanki daga zaran mijin naki ya buqaci haka, sannan ki kiyaye gaba fatan kina saurare na?
Ammi cikin farinciki ta ce "Insha Allah Papa".
"Yauwá! Allah muku albarka ya raya zuri'a ya albarkace su, sannan maganan yara sai kisan yanda za kiyi, domin ita Muhseena wataqila ma tare zamu koma maganan makarantan su, sai Munawwara da ita Muheebbah duk yanda kuka yanke sai kuyi, don bana goyon bayan a barsu su kaɗai a gida ba kowa tunda shi Mufaddal ba aure yayi ba".
Ammi dai komai Papa yace amsawa take yi dan farincinkinta ba misali, sosai tayi kewan Abiy dan a yanzu ba abinda take buqata kaman ta kallesa.
Dr Mufaddal idonsa ya mayar kan Darling da ke danna waya ya ce "my man ka rage zuciyanka akan mahaifinka domin shi ne wanda yayi sanadin zuwanka duniya ba ka da madadinsa, in kuma kanason fushin Allah da rashin albarkan iyaye ta tabbata a kanka sai ka ci-gaba", Ammi ce ta tari bakin Papa ta hanyar cewa "indai dan ni kake wannan cin ran to ka daina Darling komai ya wuce, komi na duniya mai wucewa ne, sannan tare da kai zamu koma Nigeria wannan karon kuje Maiduguri wajan dangi".
Darling dai a fiska ba zaka gane me yake ciki ba amma a zuciyansa ji yake kaman ya tashi ya tafi kar ya kuma dawowa, ga abun haushin wai har Borno kuma za suje ba iya Gombe ba, Lumshe ido kawai yayi ya ce "Allah kaimu".
Nan Dr Mufaddal ya qara yi ma Ammi faɗa sosai sannan ya ce "gobe in Allah ya yarda zan koma".
Da "Allah ya kaimu" Ammi ta amsa, nan duk suka miqe Ammi tayi sama, Darling ma ya wuce sashinsa, sannan Dr Mufaddal ya wuce ɗakinsa dan ya sanya haqarqarinsa ya huta.
Amma tararwa tayi duk bacci ya ɗauki yaran sun bar TV a kunne, sai da ta kashe komai sannan ta tashesu suka tafi ɗakunan su, sweetie kuma ta ɗauketa ta kaita nata ɗakin itama ta mata addu'a sannan ta fito ta ja mata qofa ta nufi nata ɗakin cikin nishaɗi yau za tayi kwanan farinciki.

Darling yan haurawa sashinsa ya jawo system nasa ya ci-gaba da aikinsa dan bayajin bacci ma, Burinsa ya kammala ayyukan kamun ace za su tafi Nigeria, sai dai gefe ɗaya na zuciyansa tunanin Abiy yake yi na irin yanda ya mayar da Ammi dan yaga tana sonsa.

Washegari da sassafe Dr Mufaddal ya shirya dan ya dage Darling ne zai kai sa airport ba driver ba, ba yanda ya iya yana gama shirin zuwa office suka kama hanyan airport Dr Mufaddal nakan masa faɗa cikin sigan rarrashi har suka isa, ya shiga jirgi zuwa India shi kuma Darling ya juyo driver yayi office da shi.

Abiy yana tashuwa da sassafe ya fara shirye-shiryen zuwa wajan masoyiyar sa, Aunty Amarya dai tana ganin ikon Allah sai dai sanin halin sa bai cika son yawan tambaya ba sai tayi shiru, sai da zai tafi ya ce mata "sweetheart na tafi Canada zan kai week sai na dawo", Aunty Amarya da kallon taqaici da haushi take binsa, cike da kishi ta ce "me za kaje yi a Canada? Ina ka sake ta to me zaka je yi? In yaran ka kakeson kallo ba sai ka sanya shi ya kawo su ba tunda kai ka haifesa ba shi ya haifeka ba" surutu take yi ido rufe wanda kanaji kasan kishi ki azalzalanta.
Abiy kallonta kawai yayi bai ce komai ba, dan yana rasa dalili shi bayason ɗagawa mace murya amma duk da haka Maimuna da yake so yakan iya ɗaga mata murya, ba tare da ya damu da yanayin magananta ba ya ce "wanda ya faɗa miki na saki Maimoon to ki koma ki qara tambayansa, sai na dawo" yana gama magana ya fice.
Aunty Amarya bin bayan Abiy tayi tana surfa masifa, qarshe ganin driver ya fita da shi sai itama ta koma ta ɗau waya ta qira Hajj, "assalamualaikum Hajja anwuni lafiya?
"Lafiya Alhamdulillahi Rabi'atu ya gidan? Ya mijinku?
"Ba lafiya ba Hajja, gashinan ya kama hanya wai zai tafi Canada kuma bayan ta sake ta, nace in yaran yakeson gani ai sai ya ce a kawo su".
"Rabi'atu wa aka saka? Ba dai kicemun Mustapha ya saki Maimunatu ba, INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN! Wai yaran nan ina kukeson duniya ta kai ku ne? Mutum ya auri mace da wahala amma cikin sauqi ya rabu da ita, to dan ubansa zai dawo da ita dan wannan cin amana ba da Fatuma ba".
Auntu Amarya jin ba abinda take so Hajja ke faɗi ba sai ta kaste waya tana faɗin "mstwwww! Duk bakinsu ɗaya wallahi Maiduguri zan je, ba ta isa ta dawo ba" tana gama magana ta shige ɗaki ta hau shirya kaya a akwati.

Abiy driver ya kaisa har airport jirgi ya ɗaga da su sai Canada republic, taxi ya hau har qofan gidan yaron nasa sannan ya sallami taxi ɗin, da sallama ya shiga palourn inda ya tarar shiru ba kowa kaman basa gidan, sama ya haura nan ya samu yaran suna aikin karatun Alkur'ani wanda ganin Abiy ya sanya su miqewa da gudu kowa ya je yayi hugging nasa har Afreen suna masa sannu da zuwa, amsawa yayi yana tambayan su ina Amminsu? Hanyan ɗakinta suka nuna mishi alaman tana ciki, cikin zumuɗi da son ganin matar tasa ya lallaɓi sweetie da daraba ya zille ya nufi palourn da zai sada shi da ɗakin Ammi.
Fitowanta wanka kenan ta gama shafe jikinta da turaruka masu daɗin qamshi, kayan da suke matuqar amsanta ta fitar ta sanya, Pakistan dress tana staye gaban madubi taji anbuɗe qofan ɗakin nata, duk ɗaukanta yaran ne sai bata juya ba ta cigaba da rolling nata tana faɗin "wai sweetie ban hanaki shiga ɗaki ba sallama ba..." Maganan bakinta ne ya kaste jin ta jikin mutum wanda ta tabbatar ba kowa bane face Abiy, shi kuwa cikin farin ciki ya rungumeta ta baya yanajin kaman yau ya fara raɓarta, Ammi farinciki ne da wani irin nishaɗi ya lulluɓeta amma sai ta waske ta ja aji taqi yin mosti balle ta ce qala, sai qoqarin tashuwa da take yi amma Abiy bai bata wannan daman ba.
Duk yanda ta so mostawa Abiy ya hanata wannan qoqarin ita kuma ga shi tabbas tayi kewansa dan bata qi su qare rayuwansu a haka ba, cikin danne abinda take ji ta ce "sake ni kar yara su shigo su ganmu haka".
Abiy murmushi yayi dan yasan aji ake ja masa, kuma yasan me zai yi a wuce wajan amma sai ya nemi jan maganan dan so yake yau ta taɓa rigiman nata, muryanta ya kwaikwaya ya ce "babu ɗan albarkan yaron da zai shigo duk sun san Amminsu na kewan Abiynsu, sannan kuma nima ba sake ki zan yi ba dan da shiri na nazo wannan karon ya kamata a samawa Muheebbah qani tunda ta haura shekara biyar ɗin, kuma dama starin na shekara biyar-biyar ake yi".
Ammi qara ɓata rai tayi jin abinda ya ce "hmmn! Wato ma planning nake yi kenan? Good inma shi ne ai magana ta wuce yanzu ba komai tsakanina da kai sake ni".
"Aiko ni da ke muke da abu babba ma stakaninmu, yanzu dai fatan an buɗe takardan an ga me na rubuta kuma an yafe mini an karɓi tubana?
"Uhmñ! Na buɗe kuma naga saki uku, so na jima da yafe maka jeka wajan matar ka inma yaranka kazo ɗauka ka ɗaukesu Allah tsare hanya".
Murmushi Abiy yayi jin rigiman nata da gaske take yi, sai kawai ya haɗe bakinsu cike da son nuna mata irin kewanta da yayi da kuma soyayyanta da neman afuwanta haka yake sarrafa ta, wanda a take Ammi ta amshi tuban nasa ta kuma yaba soyayyan sannan itama ta miqa nata qoqon neman yafiyan ta hanya maida masa martani mai nuni da tayi matuqar kewan sa.
Cike da soyayya da qauna suka sarrafa juna wanda na tabbata ko wasu matasan ma'auratan ba lallai su shumfiɗa irin wannan soyayya ba (shi yasa ake son in za kayi aure kayi dan Allah, domin in kayi dan wani abu daga lokacin da abun ya gushe to fa ba zaman lafiya balle soyayya sai a ta ɗaukan alhaqin juna).
Bayan komai ya lafa sun yi wanka tare, Abiy na zaune kan Ammi a qafansa nan ya dinga qara bata haquri da lallashi, wanda Ammi ba ɓata lokaci ta ce "na yafe maka, komai ya wuce ina fatan hakan kar ya sake faruwa, kuma za ka yafemun Nima?
"Ai na jima da yafe miki Maimoon, Allah miki albarka ya barmu tare, sannan ina so ki sani har abada kibar tunanin rabuwa tsakaninmu, domin ban taɓa son wata mace kaman ke ba kuma bana tunanin akwai wacce zan so nan gaba kaman ke, abubuwan da suke faruwa tsakaninmu kuma in Allah ya yarda zan ɗau mataki kinji.."
Kaste Abiy tayi ta hanyar cewa "komai ya wuce ka daina dawo da shi, sannan in dai ni ce Maimoon za ka ɗau mataki dan ni to na yafe duniya da lahira kar kayi wani abun dan in kayi ma ba zan yafe ba".
Abiy na murmushi cike da son matar tasa ya ce "shikkenan angama ranki ya daɗe nustuwar Mustapha".
Ammi ma murmusawan tayi ta ce "to ranka ya daɗe yallaɓoi ina neman wata alfarma".
"Maimoon faɗi ko ma menene Insha Allah zan yi miki da yardan Allah in har bai fi qarfina ba".
"Yallaɓoi dan Allah maganan Mufaddal, ka daina biye masa kaga dai yaro ne kuma komai zai wuce in ya girma, dan Allah kai mahaifinsa ne ka yafe masa, sannan maganan komawa Nigeria ina neman alfarman zama a Canada tare da yaran nan tunda ya sanya su a makaranta inyaso sai mu dinga zuwa Nigerian in sun samu hutu".
Dogon ajiyan zuciya Abiy ya sauqe domin Allah ya gani baya jin akwai abinda yake qauna a duniya sama da yaran nasa amma kuma dan qara samun nistuwansu da faranta musu zai yarje da hakan, cikin murmushi mai nuni da gamsuwa da batun ta ya ce "kaman yanda na ce koma menene zan amince miki kuma zan miki, to na amince inyaso zan dinga zuwa akai-akai fatan zaki kula mana da su? Kuma ko ba'a yi hutu ba wani lokacin kema ki dinga leqowa tunda kinsan wani zubin muna busy sosai kuma ba zan jure har fin sati ba tare da na ganki ba".
Cikin jin daɗi Ammi ta amince tare da qara rungume mijin nata, nan suka ci-gaba da farantawa junansu.

Aunty Amarya shiryawa tayi ta kama hanyan Maiduguri, inda tana isa ta sami mahaifiyarta ta sanar mata, amma da yake mahaifiyar nata ba ruwanta sai ta tsawatar mata akan ta koma gidan mijinta, Aunty Amarya dai hakan bai gamsar da ita ba, sai ta samu fanne, itama fannen cewa ta yi "amma tabbas Rabi'atu baki da hankali, ki godewa Allah Mustapha ya aureki shi ne

Please Login or Register in order to submit comment