Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

in ba Allah ya shiryamin kai ba Darling, Allah kai mu in aka basu hutun inma Abiynku bai zo ba zan dawo na ɗauke su mu koma amma ba zaka turamun yara su kaɗai a jirgi ba inason yarana".
Murmushin da ya qara masa kyau yayi ya ce "Allah bar mana ke Amminmu" dai-dai sun iso airport nan Ammi ta sauqa ta samu jirgin ya kusa tashuwa fasinjoji na shiga, ta gama bin step's na jirgin har ta kusa shigewa ta juyo tana masa murmushi ta ce "ka kulamun da yarana Darling".
Hannu ya ɗaga mata yana faɗin "Ammi Karki manta da Jigawa".
Murmushi kawai tayi ta qarisa shigewa dan tasan dalilinsa na jaddada mata bai wuce baya son zuwa Nigerian ba, wajan zamanta ta wuce tana mai karanto addu'an shiriya ga yaran nata a zuciyarta.

Ganin jirgin nasu ya tashi sai ya koma cikin motan, driver ya ja suka wuce katafaren Companyn sa.

Ammi tunda ta zauna a cikin jirgin zuciyarta ke stinkewa, amma bata jin za ta iya haqura ta koma domin tabbas tayi kewan mijin nata, addu'oe ta cigaba da karantowa har jirgin nasu ya ɗaga zuwa Nigeria (ƙasar mu ta gado😂).
A Jigawa jirgin nasu yayi landing, tana sauqa ta wuce Companyn yaron nata dake garin, qiransa tayi ta sheda masa ta isa a Jigawa ta staya za ta duba kamun ta wuce, DMD kaman zai yi kuka haka ya dinga yiwa Ammi magana meyasa bata wuce Gombe.
"Please Ammi ki bari driver ya kai ki".
"Kaga Darling ƙyaleni in naso driver ya kaini in naso kuma nayi driving da kaina nan da Gombe wani nisa ne?
"Ammi amma kinsan Nigeria ba Canada ba, hanyoyin nasu kaɗai ma ya ishe ki ciwon kai ba sai kin haɗa da driving ba".
"To ubana! Ni dai ka kulamun da yarana" tana gama faɗa kitt ta kashe wayan ta yi duk abubuwan da ya dace a Companyn sannan ta fito da niyan tafiya amma Managern ya bata haquri ta huta tukunna.
A cikin motocin Companyn Managern yaɗau guda ya bawa Ammi driver akan ya kai ta Gombe, amma sai da yaja masa kunne ya kula sosai da tuƙinsa, sannan suka yi bankwana da Ammi driver ya kamo hanyan tahowa Gombe.
Hankali kwance suke tafiya, inda ta sanya drivern ya tsaya suka yi sallah a Bauchi sannan suka nufo Gombe, har sun fara shiga qauyukan Gombe dan sun kusa isa Kwami, gaban Ammi ne ya tsananta da faɗuwa dan haka sai ta ciro wayanta a haka dan qiran sweedy taji ko suna lafiya, gani tayi babu network dan haka sai ta aje wayan tana ambaton Allah da fatan Allah yasa lafiya.
Kaman daga sama ba zato ba tsammani driver yaji ya yi karo da wani abu kaman an aje akan kwaltan wanda hakan ya sanya shi kasa sarrafa stering motan, ƙwace masa motan yayi hakan ya sanya suka fara gangarawa gefe wanda da qyar drivern ya samu ya tsayar da motan, Ammi da ke bayan motan salati kawai take aikin yi, kamun ta dawo daga duniyan firgicin hastarin da suka kusa yi, kawai ta hangi mutane a gaban motan tasu da makamai, cikin storo ta jawo wayanta ta shiga WhatsApp, ita batama san layin wa ta shiga ba kawai rubutu take jikinta na rawa, tsawan da aka daka mata ne ya sanyata yin saurin kashe wayan ta tura a jakanta ta jefar a qasan motan wajan qasan seat.
Ƙattin maza ne baƙaƙe munana wanda kana ganinsu kasan babu ko ɗigon Imani a tattare da su, bindigu ne a hannun kowannen su kusan su rai bakwai 7, bindiga suka sanya a goshin driver wanda ya sanya shi dole ya fito, Ammi ma fitowan ta yi dalilin stawan da suka daka mata cikin yarensu da batasan me suke nufi ba.
Ammi da hausarta da ba sosai ba ta buɗe baki za ta yi magana amma kamun ta ma fara maganan wani a cikinsu ya buga mata kan bindiga, ai sai kawai Ammi ta faɗi ta sume, wanda drivern ganin haka sai ya fashe da kuka, amma mutanen nan ba imani balle tausayi haka suka dinga jan Ammi.
Jan Ammi suke ba tare da damuwa da gurjewan da take yi da buga kanta ba, kanta ne ya bugu da wani kututturen duste wanda ba shiri ya dawo da ita daga duniyan suman da tayi.
Tafiya mai nisa suka yi, nan kuwa mamaki ya kama Ammi duk da ba ta hayyacinta sosai, wasu mutanen suka tarar tare da waɗansu, munana ƙarfafan maza sun kai goma 10 tare da wasu mutane da suka kai Shida 6 wanda da alama suma kamosu aka yi kaman yanda aka kamo su Ammi.
Mutane biyar a gaba biyar a baya, uku a gefe da gefe suka sanya su Ammi a stakiya suka naushi jeji, tafiya suke iya tafiya ba tare da sun staya ba ko Hutu balle batun shan ruwa.
Abinda su Ammi suka fahimta mutanen basa jin hausa ko kaɗan kuma english ɗin ma sai caping suka iya basu iya brokin ba balle ordinary english.
Tafiya suke sai wata cikin waɗanda mutanen suka ɗauko ta gurgura caping ɗin ta ce "ina jin fitsari".
Mutanen cikin faɗa da masifa suka yi yare, ganin matan na ƙoƙarin tsayawa suka sanya bindiga suka harbeta nan ta faɗi gawa, suka stalleke suka tusa su Ammi gaba aka cigaba da tafiya.
Wannan lamari ya storata sauran mutane huɗu da su Ammi su biyu, wani a cikinsu da alama tare yake da wacce aka harbe sai kuka ya sanya yana ambaton Allah.
Ammi ce tayi qarfin halin basa haquri da hausanta da bai nuna ba, sannan ta ce suyi ƙoƙari susan yadda za su yi su gudu, duk kallon bakisan me kike yi ba suka wurgawa Ammi domin Waɗannan mutane marassa imani masu fuskan kafuran da ko da kuɗi aka ce ka gudu ba zaka iya ba domin bindigun hannayensu da zubin halittansu kaɗai ya ishe ka shiga storo da tashin hankali.
Tafiya suke har yamma ta yi, Ammi abinka da ba sabonba har qafafuwanta sun kumbura kana ganinta kasan bata hayyacinta, ba abinda suke sai ambaton Allah ya kawo musu ɗauki domin su ba su ma san ko kidnapping nasu mutanen suka yi ko wani nufin daban.
Su Ammi su huɗu mata sai maza biyu, drivern Ammi da kuma ɗan uwan wacce aka harbe, mutanen nan ko alaman gajiya babu a tattare da su ko kaɗan tafiyan da suke yi bai dame su ba, su Ammi ne dai tafiyan ta jikkata su, musamman Ammi kana ganinta kasan duk tafi sauran kalan hutu bata saba da wahala ba.
Ammi kanta ciwo yake ga qirjinta na haka, jiri take gani qafafuwanta sun sunduma ga bugun da suka mata ɗazu ga kuma buguwan da tayi da suke janta, jinin da ya zuba a jikin Ammi shi ya haddasa mata wannan jiri da ciwon kai domin sosai tayi raunuka kuma ta zubar da jini, bibbiyu ta fara gani wanda kamun tayi wani yunquri tuni ta faɗa a jikin wani murɗeɗen qato a cikin waɗanda suka ɗauko su.
Wanda ta faɗa jikinsa cikin faɗa yasa qasan bindiga ya bugeta da shi wanda ya yi sanadin qarisawanta qasa babu numfashi.
Sauran duk stayuwa suka yi suna yare cikin fushi da stawa-stawa kaman za su kaure da faɗa a junansu, cikin yaren nasu wanda da alama shi ne babba stakaninsu ya ce "cap me de legit, oh she wan for her bodi woto-woto?(me ya faru ko bugu take buƙata?)
"Oga Pwade faɗuwa tayi a jikina kuma kaman bata numfashi".
Wanda aka qira da Oga Pwaden ne ta masto ya sanya jibgegen qafansa yayi ball da Ammi amma ko mostawa bata yi ba dan kaman ta sandare ma da alama bata numfashi, qara naushinta yayi jin shiru sai ya stugunna ya sanya hannunsa a hancinta ya ji shiru ba numfashi, haka wuyanta da zuciyanta, jin shiru sai ya miqe yana masifa "kunsan dalilin ɗauko su, abinda za suyi baya buqatan kasancewan su da yunwa ko ciwo me yasa baku tambayi ne take so ba yanzu ga shi kunmana asaran mutum biyu kuma mata ga shi wannan kana ganinta kasan za ta fi burge Oga-kwata-kwata".
"Sorry Oga pwade, to Ojonjo ya ɗauke ta mu tafi mana" sauran suka haɗa baki wajan faɗan hakan.
"Ku baku da hankali ne? Inmuka tafi da deathbody(gawa) muyi me da ita inba Oga-kwata-kwata ya kashemu ba, mu bar gawan mu tafi amma mu kula da sauran kar asaran tayi yawa ga shi ba mutane da yawa muka samo ba".
"To Oga Pwade" suka haɗa baki suka faɗa, duk sai da suka naushi Ammi sannan suka tsallake gawanta suka tusa qeyar sauran a gaba suka cigaba da tafiya.
Tunda drivern Ammi ya ga haka sai shima ya kama salati yana kuka, dan duk stiya gwanda ace da ranta akan yanda suka mata ga shi ta mutu, baiwar Allah da gatanta amma dabbobin daji ne za su ci gawanta, kuka ya dinga yi wanda mutanen da suka ɗauko su sun zaci wani abu ne nan suka ciro biscuits suka raba musu, ai da gudu duk suka amsa kowa na korawa a cikinsa hannu baka hannu qwarya.
Ammi yanda suka barta a yashe kaman gawa ko mosti bata yi har can stakiyan dare wajajan qarfe biyun dare sai ga hadari da walkiya ba jimawa aka fara ruwa kaman da bakin qwarya, ruwa ake me qarfi kuma duka a jikin Ammi yake sauqa, kaman wacce aka stikara haka taja dogon numfashi tare da buɗe idanuwanta, jikinta ba inda baya mata ciwo ga kanta da ke sara mata kuma yana mata kaman jiri-jira, abu ta gani a hannunta kaman kwali, ba tare da ta tsaya duba menene ba ta sa a bakin zaninta ta tashi tanajin jirin haka ta sanja hanya ta kwasa a guje dan tabbas ta tuno abinda ya sa ta ganta a tsakiyan daji.
Gudu Ammi take yi ba ko waiwaye dan ji take kaman zasu biyota, ba tare da ta damu da kumburan qafan nata ba ko raunukan jikinta haka take kwasan gudu tana taka qayoyi jefa qafa kawai take yi bata san inda take nufa ba, jirin ne ya ci-gaba da damunta tana kan gudun amma abun fin qarfinta yayi tana gudu tana layi kaman wacce ta sha wani abu, ba zato ba tsammani lokaci guda ta taka wani mugun qaya da kuma kwalba, garin waywaye taci karo da wani ɗan bishiya tayi baya ta buga kanta akan wani qaton kututturen bishiya mai stini, shikkenan Ammi a gurin ta kuma mugun faɗuwa ba ta ko mosti dan ta bugu, qafafuwanta na jini kanta na jini.


Belloji ɗa ɗaya tilo ga Arɗo wanda Allah bai bashi haihuwa ba sai yayansa da ya haifa ya basa kyauta kuma ba jimawa Allah yawa iyayen belloji rasuwa, nan Arɗo ya riqesa gam-gam tunda shi baya haihuwa kuma ɗan yayansa sannan yayan nasa ya basa kyauta tun da ran sa, belloji na da shanyensa da mahaifinsa ya bar masa, Arɗo ma yana da nasa, sai belloji ya haɗa yana zuwar musu kiwo, tun yana yaro har ya girma.
Su bororaye ne na usul masu kiwon shanu, da ikon Allah dai suka ya da zango a wannan jejin har suka gina gidajensu na kara suka hayayyafa, amma sunqi shiga cikin mutane balle batun yin wani karatun zamani, sai ta muhammadiya kawai itama ba wai har can ba kawai na yin salla ɗan fatiha, Nasi da Falaqi.

"Hai belloji kam wei hai me shisheyi a shikin uwar ɗaka ba jaki hito hai ki tai kiwo ba, ko hai sho kike shaniyata ya mace da yunwa ce? Arɗo ke magana cikin harshen shi da fillanci ya cinye.
Yaron da ya qira da belloji ne ya fito daga wani ɗan madaidaicin bukka sanye da wando wanda suke ɗinkawa sama ya ɗame qasa ya buɗu da riga burgujeje da takalminsa wanda akewa laqabi da "tashi ka bi shanu".
Belloji ɗan mastashin saurayi da ba zai haura shekara 17 ba siririne fari yana da ɗan tsayi sannan kyakkyawa ne dai-dai gwargwado, sandarsa ya ɗauka ya saqala a bayan wuyansa yana faɗin "yanju jan tai kiwon fa Arɗo, aradun Allah shaniyaki ya qi yin shauri aradu buge hegiya jan yi, na tai hai na dawo" ya faɗa yana ficewa a gidan.
Arɗo cikin fillanci ya zagi bellojin yana faɗin "cegiya belloji hai ki dawo da shanuwai na lahiya".

Belloji yana fita ya kaɗa kan shanaye fin ɗari biyu suka yi jeji, yana tafiya yana ɗan waqar sa da fillanci.
Tafiya suka yi sosai shanaye na kiwo yanda ya kamata domin yanayin garin anfara ruwa ciyayi sun fito yanda dabbobi za su ci su qoshi, qasan wani bishiya belloji ya samu ya zauna yana ɓare gyaɗansa da ya taho da shi yana ci dabbobi na cin ciyayinsu su ma.
Har yamma ta yi sannan belloji ya fara kaɗo kan shanayen, wasu biyu ne suka yi kwana nan ya bisu yana taro kansu, da qyar ya samu ya haɗe su ya gangara da su rafi suka sha ruwa sannan suka nufi hanyan dawowa gida, belloji yana tafiya dai ya hangi bishiyan gwandan jeji yayi 'ya'ya sun nuna, rasta wajan yayi yana faɗin "cege Arɗo jai washe matauni (haƙora), wanga gwandan da ta nune hai ka she kana taɓa hi kai fahe na shan jaqi jai yi".
Kamun belloji ya qarisa wajan yayi tuntuɓe da abu, da yake kansa na sama miqawa kawai yayi zuwa bishiyan bai lura da me yayi tuntuɓe ba sai da ya gama ciki aljihunansa da gwandan jejin ya juyo kawai ya ga mutum jina-jina a kwance a qasa kaman gawa, cikin rashin storo ya masto kusa da ita yana faɗin "hai belloji ta shiga shaba'in Aradun Allah, wannan mutum ko aljan? Aradu ji cegen da cau dole na ɗauke sa hai muje na nunawa Arɗo me cau na shan Arɗo bata taɓa ganin mai cau ba aradun Allah".
Belloji ɗago ta yayi ya saɓa a kafaɗa, qarshe akan shanu ya ɗaurata suka koma gida.
Suna shigowa gida ya bar shanayen a garekensu sannan ya ɗago matar da ta ɗauko yayo gidan Arɗo da ita yana shiga ya ce "Arɗo jo kiga aljana na shamo Aradun Allah yau, ai ni naga aljana mai cau Aradu".
Matar Arɗo ce ta fito cikin fillanci tana faɗin "ke belloji ina kinka shamo wanga mutum?
Belloji ya buɗe baki zai yi magana sai ga Arɗo ya shigo "belloji kin higa uku kin lalashe, ina kika shamo aljana mai kyau? Cewar Arɗo yana qarisowa cikin gidan.
Matar Arɗo ce ta ce "haba Arɗo kur kuyi irin ta belloji mana, wanga ba aljani bane mutum she Aradu".
Arɗo ne ya ce "Allah sarki bawan Allah dubi jikinshi hai duk shiwo, kai Maman belloji kawo tabarma".
Matar Arɗo taburman ta ɗauko aka shumfiɗe Ammi, ruwan zafi ta ɗaura bayan ya ɗumu ciwokan fiskan Ammi da qafanta aka goge aka manna mata wani ganye da Arɗo yasa belloji ya daka.
Anan rugan tasu Arɗo ya aika aka qira wani mai magani, amma har aka kwana biyu ba alaman sauqi dan ga duk alama matar dogon suma ta yi, inka kalleta ma ba lallai ka gane da ranta ba.
Daga qarshe Arɗo ya aika rugan hamman aka masa magana da Baffai saboda dama kowa yasan Baffai a harkan magani dan ya gaji mahaifinsa ne mijin Baabaa Mero, anci sa'a Baffai ya amsa zai zo, inda ba ɓata lokaci ya je ganin matar sai ta basa tausayi kuma ya dage zai taimaka dan shi ma ya samu lada ba sai anbiya sa komai ba, kuma cikin ikon Allah ya mata magani ta warke.

CIGABAN LABARI.

Baabaa Mero ke rafka salati tana faɗin "ai nikam tunda Allah yasa Isa da Indo suka haifoki shikkenan sun haifomin jaraba, jarababbun iyaye koɗaɗɗu suna ganin na stofe sun turoki ki qarisa ni, da basa sonki suka haifeki ni Meramu naga rayuwa, Allah na tuba badan-badan ba ai sai nace da basu ma haiho ki ba, yarinya kullum abu guda jaraba akan bokon 'yan wuta, to Aradu aure za'a miki a haka kije can ki fama in aka miki gori baki da ko nunu kece kika ja, shawaragiya shiyasa kullum ba ki da auki kaman hastin-bana".
Innai tura baki tayi ta ce "ni fa ba iya zuwa zan yi ba baabaata".
"Don yayan ubanki Musa ni baabaar ubanki ce ba taki ba, ja'irar yarinya kawai, Aradu in baki shirya ba kinfito yau sai nayi qasa-qasa da ke a garin nan, ko ma kija na ɗauke ki mu tafi masallaci naje can na bada sadakarki, ai ni Meramu aiki kuma ya qara samu na tunda jarababben hamman naku ya tattara komastansa wai ya tafi shima tasa karatun can wata uwa duniya ai ni aka bari da dogon baki akanki dan dama shi kaɗai kike storo kaman azara'ilunki,to bari kiji ubanki Isa zan sanya a nemomin salula duk randa kika buga min tijara nima na kamosa a salula na sanar masa yana miki adashe a littafi duk randa ya dawo ya ɓarzamin ke 'yar buhun uba".
Innai tura qaramin bakinta tayi tana qunquni ita qafanta na ciwo ba inda za taje, qarshe kuka ta sanya tana shura qafa "ni bazanje ba yau kuma ni na gaji da bokonma kuma Allah ba zan yi aure ba yiiiiiiiiiii yiiiiiiiiiii Wayyooo! Uwataa".
Baabaa Mero wangale baki tayi tana ganin ikon Allah dan taqaici ta ma rasa me za ta yi wa jikartata ta huta, sai kawai ta rarumi daron kwano da yake gefenta tayi kan innai, ita kuwa ganin haka sai ta ruga a guje ta shige ɗakin ta turo ƙofa tana ihu ta rarumi kayan makaranta ta sanya ta fito ko mai bata shafa ba balle kwalli a ido, Baabaa ganin ta fito a shirye taɓe baki tayi ta ce dan uban mutum inyaga dama ya tafi tunɓur nidai abarmin gida a tafi koyo yaren 'yan wuta, Allah yasa wancan qawar taki fatuma ta miki dariya".
Innai tura baki tayi ta qi ko cin komai ta fice, gidansu taje ta iske Baffai ya fita, kaman za tayi kuka haka ta gaishe da mama Lami ta gaishe da Innarsu duk da ba amsawa take ba, Allah yaso ta Mama Lami ta bata Naira ɗari sannan ta fito ta samu Rabe na jiranta kawai ta ɗale mashine suka ɗau hanyan makaranta.


Kunce kunyi kewan Baabaa Mero 😁 to naga ruwan sharhinku ga Baabaa Mero.

MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA.




INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله


LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member's ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR'S ANNIVERSARY

FAN'S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.


💋💋 امى بتولة💋


*Wannan page naku ne masu daraja 'yan Amana Uwar batoorl na yinku*

Deejerh nata'ala

Surayyatou nah




𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 49_50


Hajja ce ta tura qofan ɗakin Afrah ta shiga tana faɗin "wai Fatuma yau ba za ki je..." Maganan ta kasa qarisawa kawai ta sanya salati "La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, ni jikar mutum huɗu me zan gani? Fatu baccin asara kuke yi tun ɗazu dama baki shirya ba kin biyewa Munawwaratu ita da ba uwar inda za ta leqa ko qofa ta-kashi, to tashi kamun na qira Nura yanzunnan" ta faɗa tare da zubawa Afrah bugu a cinya.
Afrah kaman za tayi kuka ta tashi dan ita sam duk ta mance yau Wednesday ne suna da school, sauqa tayi a gadon tana qunquni "ni wallahi na manta yau akwai makaranta kuma yanzu lokaci ya tafi ko naje nasan duka na za'a yi, ni ba inda zanje" ta faɗa tana shigewa toilet.
Taɓe baki Hajja tayi sannan ta juya ta fice a ɗakin tana cewa "sai kinje dan uban wani ne ya sanya ki yin bacci ko stabar samun waje wai karuwa da sallahn walha, to za ki fito ki tafi kuma yanzunnan zan qira Nura na sani shi ne dai-dai da ke 'yar fatarin uba ta renani ina takwararta", Hajja ɗakinta ta shige ta samu sweetie na game na maciji a Nokianta, zama tayi tana faɗin "ƙawar Hajja kamomin layin baffanki Nura dan in bai stawatar wa wannan sakalalliyan ba nasan ba inda za taje yaran zamani duk idanuwanku a tsai-staye kun fistare qafafuwanku bakwajin maganan kowa sai na iyayenku dan carɓin rashin ta idonku kun cike shi cass, mu a zamaninmu ai ko kakar kishiyar maƙociyar goggon mai anguwan garin su pendon uwar ubanka ce ta maka magana tsaff muke biyayya amma ku yaran yanzu sai addu'an shiriya domin wasu yaranma ko na iyayensun basa ji, to Alhamdulillahi tunda kunajin nasu Allah ya muku albarka ya shirye ku".
Sweetie jin lissafin kalen dangi da Hajja ta surfa ai sai ta dinga tiqa dariya kaman za tayi kuka har sai da Hajja ta dundeta kamun ta tsagaita ta qira mata layin Daddy, yana shiga ya kashe ya qira ta miqawa Hajja ta cigaba da dariyanta.
"Nura ka qira yarinyarka yanzunnan ta shirya ta tafi makaranta ko na mata rashin kirki" faɗin Hajja cikin faɗa ko gaisuwan da Daddy ke mata bata amsa ba.
Daddy haquri ya bawa Hajja sannan ya gaisheta ta amsa suka yi sallama ta kashe wayan tana faɗin "Muheebbah kekuma taho mu karya".
Sweetie tana dariya ta shirya tsaff suka fito da Hajja suka zauna dinning da aka gama jera kayan kari, ba jimawa sai ga sweedy ta fito, ta gaishe da Hajja itama ta zauna suna Indianci da sweetie.
Afrah wasta ruwa tayi ta fito ta shirya sama-sama ta juya zata fita qira ya shigo wayanta, tana ji tasan Daddy ne kaman za tayi kuka ta ɗauka dan bata isa taqi ɗauka ba.
"Hello! Daddy good morning".
Daddy a ɗaya ɓangaren jinjina kai kawai yayi yana addu'an shiriya ga yaran nasu ya ce "Afrah morning daga ina? Har yanzu kina zaune baki tafi ba kina sane da exam's za kuyi nan da kwanaki ko, ki fita idona Afrah maza-maza ki shirya ki tafi kar na saɓa miki".
Kaman za tayi kuka ta ce "kayi haquri Daddy na gama shiryawa yanzu zan tafi".
"Good a dawo lafiya kuma a mayar da hankali ayi karatu".
Sallama tayi da Daddy ta kalli sweerie da ke shiryawa ta ce "sistor na tafi makaranta jaraba kai da hutawa sai ka mutu, kai ni Allah bani miji nayi aure na huta kuma Allah yasa ya ce bazan cigaba ba dan sai nafi murna, kuma Allah ko su Aunty Afreen ba suyi aure ba yin abuna zan yi tunda dai ban hanasu ba bari Allah ya bani miji kugani har Hajja sai tasha mamaki" ta faɗa tana ficewa a ɗakin.
Sweerie dariya ta dinga yi har ta kammala shirin

Please Login or Register in order to submit comment