Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma kamun hannunta ya kai ga sauqa sai taji an riqe hannunta an buge gefe, cikin taqaici ta juyo za tayi ashar amma ganin waye ne sai ta haɗiye zagin tace "kai har ka isa ka hanani hukunta yarinya tamun laifi ina matar ubanka ni sa'arka ce da zaka riqe hannuna?

Kallon sama da qasa ya mata ya watsar da kashin ta kamun ya juya ga sweerie yace cikin Indianci "dama bance ku shirya bane ko reni ne? Wuce ki qira sweedy ku fito yanzun nan" ya faɗa yana zama a kan ɗaya daga lumstuma-lunstuman kujerun palourn Ammi.

Cikin taqaicin rashin ida nufinta ta juyo ta kalle sa tace "ina maka magana ka maida ni mahaukaciya amma ai kasan nima uwarka ce b...." Wani kallon da ya mata ne ya sanya ta haɗiye maganan dake bakin ta tana ja baya dan ta storita ganin yanda lokaci guda ya sanja fiska da irin kallon da yake mata.

Yatsa ya nuna mata kaman wanda bakinsa ke ciwo yace "watch ur tongue" iya abinda ya faɗa kenan ya fidda wayansa yana lastawa.

Cikin stiron masifa da ke cinta da ayyana irin abinda zata faɗa wa Abiy ta fice a sashin fuuuuu ta banko qofa.

Guntun tsaki yaja "mstwwww! Idiot human being bansan shima me ya gani a wajan ya burge sa ya auro ta ba" ya faɗa yana taɓe baki.

Sweerie da sweedy suka fito yace musu "ina key ɗin Ammi?

Sweedy ne ta miqa masa ya karɓa ya sasu gaba suka fice yaja sashin ya rufe ya jefa key ɗin a aljihun sa suka fice a gidan.

Suna fitowa a palourn a compound na gidan suka ci karo da Abiy da sweetie sun dawo hannunta da ledodi alaman siyayya ya mata.

Sweetie da gudu tayi wajan Darling ta rungume sa tana cewa "Darling ina ka baro Ammi" kallon ta yayi kawai ya kau da kai ya juya dan zuwa yanzu ya fahimci me Abiy ya faɗa musu ba sai ya tambaya ba.

Abiy ganin ko kallon sa be yi ba sai ya kai kallonsa kan su sweedy yace "Munawwara where are you going?

" Darling ne yace mu shirya ya kaimu mu gaishe da mummy" qarya ta sharara masa dan ita ma bata san ina zasu ba kawai ta faɗawa Abiy hakan ne.

"To ku dawo lafiya ku gaida mummynku" Abiy ya faɗa yana shigewa cikin gida.

Dukansu ɗuruwa suka yi seat na baya, har ya sawa mota key sai ya fasa tayarwa da Indianci yace "waye drivern ku?
Ba shiri sweetie da ke gwalalo ido ta fito dan tasan ko yaushe ita ce da zaman gaba, yanzun ma dan taga ransa a ɓace shiyasa ta storita ta shige baya.

Qwafa yayi yaja motan suka fice a gidan sai Tunfure.

A bakin gate yayi parking dan sharp-sharp yake so su gama su fito, cikin gidan suka shiga suka tarar mummy na saving Daddy da abinci.
Da gudu sweetie tayi wajan Daddy ta rungumesa, yana murmushi yace "manyan mata yaushe a gari?

Sweetie na dariya na farincikin ganin Daddyn ta washe baki tace "Daddy yau da sassafe".

Mummy na murmushi ta rungume su sweedy tana tambayansu wa ya kawo su?
Sweedy tace "Habibty Abiy ne ya kawo mu"

"Masha Allah Abiy ya kyauta sannunku da hanya"

Daddy sai biyewa sweetie yake, ta ɗau cokalinta suna cin abincin da aka saka masa tare.
Sweedy ma mummy ta saka mata ita kuwa sweerie tace ta qoshi dan ta gama cika cikinta a kitchen da ta taya Mama mai aiki girki.
DMD ma yace ya qoshi, sanin hali ya fi sanin kama dan haka mummy bata masta masa ba mutumin da kaman bai da halittan ƴaƴan hanji a cikin staɓar rashin son cin abinci kuma Allah ya taimake sa ulcer bata kama sa ba.

Sanda suka gama cin abincin suka ɗan huta dan sunyi awa a gidan kamun ya duba lokaci ganin yamma na yi ya dube su yace "maza ku tashi mu tafi".

Daddy ne ya kalle sa yace "har za ku koma gida son? Ni na ɗauka kwana za suyi kuma ai ko ba kwana ba ka barsu sai zuwa dare ko?

Kaman baison yin magana yace "Daddy ba gidan Abiy za mu tafi ba kar dare ta mana a hanya".

"To ina zaka kaisu son? Cewar mummy da idanuwanta ke kansa.

"Habibty Ashaka zan kai su kuma a yau nake so na dawo".

"Ashaka dai son? Shi Mustaphan ne yace ka kai su ko kuma me daga zuwan yara basu huta ba ka sanya su a hanya".

"Daddy gidan Abiy ne sai a hankali kasan abinda ya ajiye a gidan".

Mummy tace "duk da haka dai son bai kamata ba shi mahaifinku ne kuma gidansa naku ne ba matar da zata sanya hijabi tsakaninku da abinda yake mallakin ku, ka dinga haƙuri don dama mu mata sai a hankali".

Shiru yayi bai ce komai ba sai Daddy yace "shikkenan son na fahimce ka ku dawo lafiya amma ka kasance mai haquri da kuma biyayya ga iyaye kai ne babba abinda kayi shi suma qannenka za su gani su bi".

Sallama suka wa su Daddy ya sa qannensa a gaba suka fice, suna shiga motan yaja da mugun gudu dan so yake ya kaisu ya dawo da wuri ɗaga waya yayi ya qira layin Jay.



𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚'𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 - 250 𝟏𝐆𝐁 - 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 500
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎......



Jay na ficewa a gidan Hajja ya ciro waya yayi dialing layin abokinsa da yayi saving da "Farooq" qiran na bugu ɗaya aka ɗauka.

"Hello freind yau kayi mafarki nane?

Jay dariya yayi jin abinda abokin nasa ya faɗa sai yace "kaman kuwa ka sani, yanzu dai kana ina?

"Ina gida"

"So na shigo Ashaka ne mun kwatancen inda kake nazo dan nasan gida na bajoga"

"Okay ba kasan best way international school na nan cikin Ashaka ba?

"Yeah! Na sani"

"Okay in ka shigo makarantar ka qira ni"

Jay yace "okay freind" sannan ya kashe wayan ya juya kan motan sa yayi hanyan makarantan su Afrah.

Yana isa yayi dialing layin abokinsa ya faɗa masa ya iso ya kashe wayan, yana tsaye ba jinawa sai gashi ya iso yana murmushi ya miqa masa hannu suka tafa yace "freind ashe ka shigo Ashaka shiyasa ka qira ni, amma wa ya gaya maka ina Ashaka"

"Munyi magana da Waleed ne yake faɗamun kazo service Ashaka to banma san a nan makarantan kake ba ai da na baka aikin yi domin anan Auta ke karatu kuma bata ji"

Quarter's suka qarisa, Farooq ya buɗe qofan ɗakin sa, room and palour ne sai kitchen, ko ina a share fes-fes gwanin sha'awa, suka qarisa shiga yana cewa "dama anan Auta take karatu kenan? Amma wani class take?

Jay taɓe baki yayi yace "kaman dai a Jss 1 take ne ko SS 1 tsakanin biyun dai"

"Ai kuwa in SS 1 take to a ajina take dan yanzu presently ni ne form-mastern su, amma me sunan ta?

Hararansa Jay yayi yace "za kace baka san sunan Hajja Afrah take da shi ba ko kuwa sunan Daddy ne baka sani ba?

Farooq na dariya yace "sorry freind na tuna FATIMA NURA right? Amma ba mai sunan sai dai wata me suna FATIMA NURA MUHAMMAD".

"ɗan renin hankali ita ce to tunda baka san tana aiki da sunan Alhaji ba".

"Ai kuwa sai yanzu ma ta faɗo mun kasan ba cika kallon students nake ba yanzu ɗalibai renine da su in ka sake kaɗan su renaka wasu suce suna sonka wasu kuma su maka sharri a wajan qawayensu akan kace kana sonsu alhali ba haka bane".

Murmushi Jay yayi yace "kai dai faɗa gaskiya kasan dai na sani wannan AL'ADA ce ta malamai soyayya da ɗalibansu to kai faɗamun akwai wacce ta maka a students naka?

Farooq hararan Jay yayi yace "taɓɓ JAHILCI KO AL'ADAH? Kana Malami kayi soyayya da ɗalibar ka ba dai AL'ADA ba sai dai ko JAHILCI dan reni ne zalla gwanda ma in ɗalibai suka gama ka bi yarinya har gida in ta maka, thought akwai wacce suke zama da ita Afrah a class ina tunanin qawarta ce yarinyar nistuwan ta da hazaqanta na burge ni amma ba ina nufin wani abu ba dan duk ajin qwailaye ne irin nata ma yayi muni don ko Afrah ta fita cika ido".

Dariya Jay ya saka har da kama ciki yace "kaji ɗan iskan malami ba, wai qwailaye wato ido kake sawa ɗaliban ka?

Hararansa Farooq yayi yace "in nasa musu ido in kalli me? Ko ita ma wannan yarinyar ba wai sonta nake ba dan karkaji nayi magananta, ni ba ruwa na da soyayya da ɗaliba dan malamai masu irin haka ke ɓata ma saura suna, kaga malami yana bin ɗalibansa ba kunya balle storon Allah wani ma har yaje ya ɗirkawa yarinyar mutane ciki sannan a haka ya qira kansa a malami wanda aka bawa amanan ɗalibai, ai Allah shirya mana al'umma kawai amma wannan halin malaman namu da wasu ke masa kallon AL'ADA tamu ta malamai to bai haɗu ba dan bakomai ciki face cikakken JAHILCI, kuma abun haushin sai kaga sun manta da suma iyaye ne su dinga bin yaran wasu wanda suma in akawa nasu ba zasu ji daɗi ba, sai dare kaga malamai suna shigowa ɗaukan yaran hostel kaman wani College ko University dan tsabar lalacewan zamanin mu ta yau, to Allah kyauta ya shirya mu amma ni Umaru ba ruwana da harka da ɗalibai dan bana qaunar reni ma".

Jay cike da shaqiyanci ya ce "to in ba sonta kake ba me kake? Kaga in ta maka kawai faɗamun muje har gidan su in yaso sai ka rene ta kar ka damu da rashin girman ta, kawai ta girma a hannunka in kana zuba mata takin asali (sperm) tun yaushe zata girma kaman kazar gona, kai soyayyan aure zaka mata ba na lalacewa ba dan haka kai daban sauran malamai daban, Allah shirya mu duka".

"Kai dai ɗan iska ne Jay Allah kawo maka sauqi dan fa baka ga yarinyar ba ta haɗu kam amma ba komai a wajan ni kuma tsakani da Allah yacce na balaga na balagen nan ai duk wacce na samu kasan ba aikin wasa zan mata ba balle akai ga maganan reno, sai dai ko in kai zaka iya haqura kayi renon tunda ɗalibata ce sai ka fara kamun qafa".

Jay ya buɗe baki zai yi magana sai qiran da ya shigo wayansa ya kaste sa, ganin mai qiransa DMD sai ya ɗauka ya kara a kunne yana cewa "hello dude an tashi baccin ne?

Guntun tsaki DMD yaja yana driving, a taqaice yace "kana can har yanzu?

"Eh inanan amma bana gidan Hajja naje wajan freind".

Da yake DMD yasan wanda Jay ke qira freind sai ya kaste qiran ba tare da yace komai ba ya ci-gaba da driving da gudu, ba jimawa suka isa.
Gidan ba za'a ce masa babba har can ba amma duba da ba'a cikin gari yake ba to zai iya amsa sunan babba kuma stararre wanda a kaf anguwan babu irin sa.
Bai ko shiga gidan ba ya tsaya a bakin gate ya juyo ya kallesu yace "ku sauqa ku shiga kuma kar naji kar na gani fatan kuna ji na?

Duk amsa masa suka yi sannan suka sauqa, sanda yaga shigansu kamun nan yaja motan sa yayi gaba.
Layin Jay ya qira ya masa kwatancen inda suke, yana shiga makarantar ya tarar da su suna jiransa, dan sanin halin DMD basu bari ya iso ya qirasu ba suka fito jiransa.

DMD kallon Farooq yayi yace "yanzu kai a nan kake rayuwa? Service ɗin nan dole ne?

"DMD ba zaka gane bane".

Taɓe baki yayi ya shige cikin ɗakin ya ɗauro alwala ya dawo palourn ya same su suna hira sai ya shumfiɗa darduma ya ta da sallah.
Yana idarwa ya kallesu kaman wanda aka sa dole ko aka shaqe yace "kunyi sallan ne ko kun tsaya hiran mata?

Jay hararansa yayi cikin wasa yace "ba zancen mata ba cin mata muke ɗan renin hankali mutum sai kace mata-maza nikam anya dude lafiyan ka? Anyama kana jin feelings?

Ko kallo Jay bai ishe sa ba balle ya tanka ya juya yaci gaba da qirga countern sa.

Farooq dariya yayi har da kama ciki ya ce "kai fa Jay shahararren ɗan iska ne baka da magana sai na mata ai kam matarka ta shiga uku, yanzu angaya maka su mata-mazan basa jin feelings ne? Suma feelings gare su mai qarfi ma dan kaji kuma DMD irin su da kake ga suke shirun nan kaman abun bai damesu ba to sune oganni in suka kama mace sai sun sumar irinka kuma kuna good 5mints kun gama".

Wani kallon banza kallon bakasan me kake faɗa ba Jay yayi wa Farooq ya ce "amma tabbas in nace baka ci tuwo akaina ba to nayi qarya dan tsaban renin hankali ka dubeni jibgege da ni kana qiran 5mints ai wallahi yanda nake ji na ɗin nan in mace ta shiga hannuna sai an ɗinka ta, muga wannan kala muga wannan duk muyi ittaqillah mu haƙora ai in muka samu namu ta sunna da lada to sai mun qarar da arna dan kisa, kai dai kawai ayi shiru, ɗazu Afrah ke ban labarin wata qawarta inaga ma ita kake nufi Afrah yarinyar nan dan staɓar tana ji ta fara girma har da cemun wai na auri qawarta tana da hankali amma kuma na kawo kunne ta faɗamun wata magana, duk ɗauka na wata serious magana ta arziƙi za ta faɗa mun ashe yarinyar nan cewa za tayi qawar tata bata da ko nono, to sai ka tuno mun da Afrah nima kaman DMD nake da ra'ayi sai qosashshiyar mace kuma nunanniya wacce tasan ta amsa suna budurwa dan yarinya ba za ta ɗauki buqatar Jay ba".

"Hhhhh! Jay Allah kawo maka sauqi" faɗin Farooq yana miqewa.

DMD kallon Jay yayi ya aika masa da harara dan maganganun nasu sosai ya cika sa fam da haushi amma rashin son hayaniya yasa bai yi magana ba.




FAN'S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.


INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله


LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member's ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR'S ANNIVERSARY

Ameerah, jeddatulkair (oum abdusamad), Besty(Dr Seeyerth) wannan page ɗin naku ne kuyi yanda kuke so da shi.


JAHILCI KO AL'ADAH? FAN'S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku🤝



FAN'S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.


💋💋 امى بتولة💋




𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 27_28

Ɗage kafaɗa Jay yayi irin ko a jikina ɗin nan, yace "uban masu jin kai ai wallahi tun wuri ka rage wannan ji da kan ko kuwa kasha wahala a hannun 'yar mutane don na tabbata za'a wahalar da kai kamun a baka haɗin kai kuma kai kaja, sannan za ta qeraka staff ka shiga hankalin ka dan mata dai sun wuce duk tunaninka a seta maza duk mulkinka a waje a gida sune masu mulkin ƴan aljanna ba Allah dai ya qarawa mata albarka da ni'ima mu kuma ya qara mana qarfin kwasan ni'iman".

"Mtssswww! Kai fa Jay iskancinka bai da uban gida, yaro qarami sai son maganan banza" cewar DMD da ya ciro wayansa yana lastawa kaman ba shi yayi magana ba.

Wani wawan dariya Jay yayi kaman wanda akawa kyauta yace "dude kai cikakken ɗan renin hankali ne Wallahi nine yaro? Inaji shekara biyu zuwa uku ka bani to ba banbanci sannan kuma maganan banza dole nayi ta atou harka ce ta sharholiya kuma ta jin daɗi da samun nistuwa, ni wallahi zama haka ma ya ishe ni dole amun aure a wannan shekara dan bazan yarda na cika shekara talatin na stofe kaman kai bansan wancan hanyan ba, ni ko classic bazawara zan aura dan ban cika son gargada ba dama indai garin akwai ni'iman damuna sannan ko ina da damshi ga daɗi to an wuce wajan muje zuwa kawai kwasan albarkatun gari ba kakkautawa harka ta sharholiya, a shekara guda kuma za kaga yaro ya haifo yaro".

DMD dubansa ya kai kan stadadden agogon dake maqale a kakkauran hannun sa, ganin time sai ya miqe yana faɗin "in ka gama maganan yarantan taka sai ka taso mu wuce dan ba kwana a garin nan zan yi ba, in kuma baka gama ba sai ka dawo".

Hararansa Jay yayi ya miqe yana qwalawa Farooq qira, nan ya fito a shirye staff cikin qananun kayan da ya yi matuqar amsan sa.
Farooq (malam ba wasa) chocolate color ne amma ba mai duhu ba, yana da saje da gashin gemu, fiskan sa mai ɗauke da dogon hancin sa da idanuwansa ƴan dai-dai, yana da stayi amma ba sosai ba dan DMD ya fisa stayi sannan ba za'a ce masa stiriri ba kuma ba za'a ce masa mai jiki ba saɓanin DMD da Jay da jikinsu kenan kaman na mata waɗan da ake ce musu ƴan duma-duma abinda ya ɓoye jikin DMD kuwa stayin sa dan yana da stayi dai-dai burin ko wacce mace ga kuma faffaɗan qirji, shi Jay kuma stayin ba sosai ba sai jikin sa ya ɗan nuna.

Fita suka yi duka har inda suka Parker motocin su, Jay da Farooq suka shiga na Jay shi kuma gogan ya shiga nashi ya mata key.


Sweedy da sallama suka shiga palourn, Hajja da ke zaune tana kallon tashan kung-fu kaman tana jin Chinese, jin sallama sai ta juyo tana ganin su ta fara washe baki tana faɗin "maraba lale da kyawawan jikokin Hajja".
Sweetie ce ta qariso ta faɗa jikin Hajja tana magana da turanci "Hajja ta nayi kewanki".
Dundu Hajja ta mata tace "kindai san ke ƴar lukuta ce ba kamar sauran ba to ɗaga ni karki karyani da wannan yaren mutane da kuke satowa ba za ku iya naku ba"

Tura baki sweetie tayi dan ta stani ace tana da jiki, tashuwa tayi ta koma gefe tana magana da Indianci.

Gaishe da Hajja su sweedy suka yi ta amsa da fara'a dan Allah ya gani tanason yaran Mustaphan ta ba kaɗan ba barin ma dai yayansu babban jikanta.
"Halan ku da wa kuka zo? Naga ku kaɗai ku ka shigo.

Sweedy tayi shiru sanin tana faɗa Hajja za ta hau surutu amma sai ta ji muryan sweerie na faɗin "ai Hajja Darling ne ya kawo mu yanxu ma ya tafi wajan big bro ne zasu dawo tare" ajiyan zuciya sweedy tayi jin abinda sweerie ta faɗa tasan ko ba komai yanxu kam albarka zata saka masa.

Hajja jin haka sai ta washe baki tace "ban dai so qanin miji yafi miji kyau ba amma ba komai Allah kawo su lafiya ƴan albarka, shi kuma jabiru zai zo ya faɗa mun Maryam ce ko Nura suka ce ya fita da har zai ja mun jika wajan shirmen sa.
Da qyar ta lallaɓa sweetie ta haqura har ta sake suna dariyansu dan dama babbar abokiyar shirin ta kenan.
su sweedy suka tashi suka shige ciki ɗakin da yake nasu ƴammataye amma banda sweerie dan ita ɗakinsu da Afrah ne sai sweetie kuma wajan Hajja take tarewa muddin tazo ba tare da Ammi ba.
Samun Afreen suka yi tana kwance tana chat, ganin sweedy kaman daga sama ba shiri ta miqe ta rungumeta tana cewa "sweedy yaushe kuka zo? ke da wa? Ina Darling?
Sweedy hugging nata tayi tana murmushi dan daman tasani wannan wajibi ne sai ta tambayi Darling dan mutuwan sonsa take yi shi kuma Darling ko a jikin sa.
"Yau ɗin nan muka zo ko hutawa ba muyi ba aka kawo mu nan kuma aikin Darling ne amma ya tafi wajan big bro" sweedy na faɗa tana ɓata fiska dan gajiya.
Afreen tace "sorry my dear, sannunku da gajiya".

Sweerie ma ta gaida Afreen kana ta juya ta fice dan zuwa ɗakin su ita da Afrah su ma.

Da sallama ta shiga tana faɗin "qanwata Afrahty my love ina kike?

Afrah dake cikin banɗaki dan tashuwanta bacci kenan, jin muryan sweerie dan tasan ita kaɗai ke qiranta haka, barin wankan tayi ta ɗaura towel ta fito da gudu tana faɗin "oyoyooo sister sweerie".

Hugging juna suka yi suna dariya Afrah tace "ke kullum ba zaki ce Afrahty kaɗai ba sai kince qanwarki kuma shekara guda kawai fa kika ban, shiyasa inajin qiran nan nasan kece, ina mintin zuciyata? Ina yaya sweedy? Yaushe a gari? Wa ya kawo ku? Ina Darling?

Hararanta sweerie tayi tace "kede baki sauya ba kullum tambaya kaman ƴar jarida".

Dariya Afrah tayi tace "naji daɗin zuwanku dama ina missing na habibty na thank God gaku nan weekend zai yi daɗi, yanzu dai bani amsa ta".

Sweerie murmushi tayi tace "1 mintin zuciyarki na wajan Hajja, 2 yau ɗin nan muka zo, 3 yau muka diro Nigeria,4 Darling ne ya kawo mu amma daga Gombe daga Canada kam Abiy ne, 5 Darling yana tare da big bro".

Dariya Afrah ta sanya tace "kin bani duka kenan? Shikkenan sannunku da zuwa ba nayi wanka nazo na baki labarin Habibty ta" ta faɗa tana shigewa banɗaki ita kuma sweerie ta qarisa kan gado tana kwanciya.

"Hajja ina tambayanki ina Aunty masoyiya kinyi shiru ko? Faɗin sweetie tana tura baki.

"Sakalatun sakalalliya iyayen taɓara gaba ɗaya yarinya kin girma kin zama budurwa amma sakalci uwa sakakken mara, ni ina nasan kina da masokiya ne ko masogiya".

Tura bakin ta kuma yi tace "Hajja yaya Afrahty fa nake nufi".

"Au ai sai

Please Login or Register in order to submit comment