Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma ya sauqe kuma yana qoqarin shiga junior secondary shima, Maimuna ta kusa sauqewa kuma itama tana qoqarin shiga junior secondary, Hajja bata sake haihuwa ba shi kuma Alhaji dukiya sai gaba-gaba yake dan zuwa lokacin filayen sa a cikin Gombe ba zasu irgu ba kuma tun bayan barowansu Maiduguri basu koma ba har yanzu da Nura ke neman shekara 11.
Nura ya kasance yaro ne mai sanyin hali da jin magana ga gudun zuciya, haka Maimuna akwai gudun zuciya ga ta shiru-shiru, saɓanin Mustapha da yake yaro mai hazaƙa fa qoqari amma yana da zuciya ga kuma kafiya, ba shi da reni amma ba ya storo kuma ba maganan kowa yake ji ba.
Maimuna na gama primary Alhaji ya ɗauko ta ya kawo cikin Gombe makarantar kwana ta fara secondary, Hajja ganin haka sai ta saduda ta yarda zata zauna cikin Gomben ita ma ganin za'a rabata da yaranta duka.


FAN'S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.


INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله


LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member's ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR'S ANNIVERSARY


JAHILCI KO AL'ADAH? FAN'S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku🤝



FAN'S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.


💋💋 امى بتولة💋


Not edited ayi haquri da mistake's.

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 33_34



Hajja na dawowa cikin Gombe Alhaji ya sauyawa Maimuna makaranta daga na kwana zuwa na aje a dawo, Nura ma ya dawo gida amma shi Mustapha yaqi yace a makarantar zai zauna.

Rayuwa na tafiya abubuwa da yawa sun faru masu daɗi da marar daɗi inda a cikin wannan halin Allah yawa matar Alhaji-baba rasuwa inda saqon na riskar Alhaji ya tarkata iyalansa duka suka nufi Maiduguri cikin motan su na kansu dan yanzu Alhaji ba abinda bai mallaka ba,sun isa lafiya sai da suka share wata guda har da ɗori kamun suka juyo kasancewar hutun yaran ya qare inda a hanyar su ta shigowa Gombe suka yi hastari kuma duka sunyi rauni, kwanansu biyu 2 a asibiti Allah yawa Maimuna rasuwa, wannan rashin ya jijjiga gaba-ɗaya iyalan Alhaji barinma Mustapha da ke staninin qaunar ƴar uwar sa kuma shaquwa mai qarfi ne tsakaninsu duk da kasancewar basu zauna mai stayi a waje guda ba.

Mustapha na kammala secondary Alhaji ya basa zaɓin inda yake son cigaba da karatun sa, shi kuma sai ya zaɓi India.
Alhaji ganin zuwa lokacin ya girma tunda ya kai shekaru sha biyar 14 sai ya amince ita kuma Hajja ba abinda tace sai addu'an Allah bada sa'a kuma ya kula, Nura dai ya zaɓi qarisa karatun sa a Maiduguri kuma Alhaji da Hajja sun amince da hakan sannan sunji daɗin hakan inda ya tafi Maiduguri yana karatun sa yana zaune a family house kuma hakan ba qaramin daɗi yawa baba-alhaji ba duk da zuwa yanzu ya stufa kucuf.
Mustapha anshirya masa komai ya tafi India yana karatun sa hankali kwance, Hajja zama ba yaranta abun bai mata daɗi ba amma kuma ba yanda ta iya a yanzu kuma tasan bata isa tace zata koma Ashaka ba haka ta haqura.

Sai da aka shekara biyar kamun Mustapha yazo gida inda ya tarar yayan sa ya jima da dawowa gida dan ya kammala degree da master's nasa akan kasuwanci((business), Hajja tawa Mustapha faɗa sosai akan rashin zuwansa amma ya bata Haquri abinka da uwa da ɗa tuni ta haqura, nan suka ɗugunzuma suka tafi Maiduguri, suna zuwa baba-alhaji yace sam sai sun zaɓi mata a cikin yaran dangi sunyi aure kowa ya koma da mata barinma dai Mustapha dake garin mutanan da basu damu da AL'ADUN musulunci na rufe jiki ba, tunda ya kai shekara ishirin to ya kai riqe mata, Nura tunkan a iso kansa ya bayyana cewar yana son yarinyar Gwaggon sa mai suna Maryam dan tunkan ya koma suke soyayya, wannan abu ba qaramin daɗi yawa baba-alhaji da iyayen su Nura ba nan kuwa aka tsayar da komai tunda abu na gida ne kowa yasan AL'ADUN yaren nasu da yanda suke gudanar da biki sai aka aje nan da wata huɗu kamun Maryam ta kammala secondary.
An kaɗa an rawa da Mustapha amma yaqi yace shi dai a masa uzuri tunda saura masa shekara guda to sai ya kammala zai dawo ya dubi mata inyaso sai ayi auren, saboda qaunar da Hajja kewa yaron nata nan ta tayasa roqon baba-alhaji da mijin nata wanda da qyar baba-alhaji ya amince sannan ya jaddada masa kada ya wuce shekara 1 dan ba yanda za'a yi ya ɓata mata sunan zuria'a.

Sai da suka yi mako biyu sannan suka shirya suka dawo Gombe, Nura cike yake da kewar sahibar sa Maryam wacce yake qira da Habibty, amma kasancewan wayayyen zamani muke sai ya saya mata waya wanda zasu dinga gaisawa.
Mustapha tunda suka dawo yayan sa Nura ke masa magiya akan baya so ayi bikin sa bayanan, ganin yayan sa ya damu kuma shima daman yafi qaunar yaga bikin wan nasa sai kawai ya tura saqo makaranta zai qara 2 months aka hutun su, to abinka da harka ta kuɗi nan take makarantar suka yarda tare da bashi daman yin komai na attending class a online.
Akwana a tashi asaran ma rai yau auren Nura da Maryam saura sati biyu, baba-alhaji ya buqaci da su koma cikin dangi ayi auren acan in aangama sai su dawo, suka tattara suka tafi Maiduguri.
Angudanar da shagulgula da AL'ADUN yaren nasu na kanuri kama daga events na Amarya da kuma Ango su Wushe-wushe da dai sauran su, an ɗaura auren NURA MUHAMMAD NURA & MARYAM TIJJANI ɗaurin auren da ɗumbin jama'a suka halarta kama daga abokanayen Nura har da na Mustapha da kuma manyan masu kuɗi jama'un Alhaji, aka kai Amarya ɗakinta wanda yake nasu aduk sanda suka zo garin Maiduguri.
Bayan mako guda ankammala komai Amarya tayi bankwana da mutan Maiduguri suka kamo hanya da su Hajja duka, anan gidan Alhaji dake anguwan federal-lowcost Nura ya zauna da Amaryar sa Maryam a sashin da dama Alhaji ya gina wa ko wannensu sashin sa a cikin gidan.
Bayan sati 1 da dawowan su Mustapha ya shirya ya koma India yaci gaba da karatun sa, mutan Gombe kuma rayuwa suke cikin farin ciki da girmama juna.

Bayan komawan Mustapha India garin Hyderabad, Telangana ana makarantar da yake take.
Watarana ya fito class da abokanan sa yana tafiya ba tare da ya kula ba sai ya buge wata baiwar Allah, juyowa yayi da niyan bata haquri amma kamun ya buɗe baki guard's nata suka riqe sa suna surutu cikin Indianci wanda duk abinda suke faɗa yana fahimta, idanuwan sa ya ɗago dan ganin wacce ya buge "fatabarakhallahu ahsanul kaliq" shine abinda bakin sa ya furta ganin yarinya kyakkyawar gaske wacce kana ganinta kaga ba-indiya kuma ƴar mai kuɗi.
Fara ce sol, mai dogon hanci da kuma stayin gashi ga qaramin bakin ta, kayan dake jikinta kaɗai ka gani kasan ita musulma ce ba hindu ba, sanye take da riga da wando indian dress mayafin da yake babba ta rolling nasa yanda ba bar shape nata ko gashinta a waje ba, shigarta komai na mutunci ne sai dai abinda baza'a rasa ba abinka da AL'ADAR qasar da take.
Mustapha bai ce komai ba sannan guard's nata basu sake sa ba, buɗe baki yarinyar ƴar kimanin shekaru 15 tayi tace "ku sake sa bada saninsa bane" cikin harshen Indianci.
Guard's ɗin sake sa suka yi suna nuna sa da yasta alaman jan kunne, shi dai har lokacin bai ce komai ba dan Mustapha akwai zuciya, yarinyar ce ta dube sa da murmushi fiskanta tayi magana da English "kayi haquri da abinda suka maaka".

Sai lokacin Mustapha ya samu daman magana, cikin harshen Indianci yace mata "bakomai".

Cike da mamaki ta dube sa tace "Wow! So kai ba-indiye ne?

Girgiza kai yayi yace "Nigerian" ya miqa mata hannu alaman su gaisa.

Kallon sa tayi a karo na biyu da mamaki ganin shi ɗan Nigeria kuma yana bata hannu bayan ita ba muharrmar sa ba, a zuciyar ta tace "wannan dabi'an qasar tamu JAHILCI NE KO AL'ADAH oho musu duk wanda yazo sai ya ɗau banzan AL'ADAN su.
Maganan da yayi ne ya kaste mata maganan zuci da take yi.

"am i not welcome?"

Murmushi ta masa tace "you're welcome, amma addini na ya hana gaisawa da namiji".

Wani abu ne ya dirar masa a zuciya tare da mamaki dan tabbas ta burgesa ya buɗe baki zai yi magana sai qira ya shigo wayanta, ɗauka tayi ta kara a kunne tayi magana cikin Indianci wanda kana ji kasan da mahaifiyarta take magana, tana gama wayan ba tare da ta bi takan Mustapha ba ta juya ta tafi guard's nata na take mata baya.

Tundaga wannan rana har aka kwashe wata ɗaya, biyu har uku bai qara ganin giftawanta ba, kuma gashi soyayyan ta ta riga ya masa mugun kamu dan yarinyar ta shiga ransa shi ko takan AL'ADAN su na dole sai ka auri ƴar dangi kuma Kanuriya ba bi ba son baiwar Allahn nan yake bilhaqqi, ana haka kwastan ranan ya fita yawo da abokanan sa sunje wani Cafe suna zaune kowa yayi ordern abinda za'a basa, waitern ne ya tambaye sa mai yake so? Buɗe baki yayi ya faɗa sai dai da mamakin sa muryan ta ya jiyo a gefe itama tana faɗin "biryani" juyawa yayi yaganta tare da qawayen ta amma duka cikin su ita ce mai shigen mutunci dan yau ma irin shigan ranan tayi.

Yana zaune yana cin biryanin sa ganin suna qoqarin barin wajan sai ya miqe ya qarisa wajan su yana musu sallama, ita kaɗai ta amsa dan sauran kallonsa suke da mamaki, murmushi tayi tace "You again? Sorry that day i gone without saying byee, my Ammaah called me that's why".

Murmushi Mustapha yayi yana mamakin meeyasa take son masa turanci bayan ya nuna mata yana jin Indianci, roqon ta yayi ta basa numbern ta, ba tare da tayi musu ba ta basa dan tun kallon sa da tayi ya burgeta, domin Mustapha ya ɗauko kyawun Alhaji da na Hajja duka.

Cikin watanni huɗu masu kyau soyayya mai mugun qarfi ya qullu stakanin Mustapha da Maimoon, mastalan da suka fara samu tun farko daga mahaifiyar ta Hindu ce, dan Maimoon yarinya ce ga shugaban makarantar da Mustapha ke karatu, University of Hyderabad, Telangana.
Dr.Mufaddal shine sunan mahaifinta, babban mai kuɗi ne da India gaba-ɗaya keji da shi ba iya Hyderabad ba, matar sa ɗaya Hindu da yarinyar su Maimoon wacce suke wa soyayya ta duniya gaba-ɗaya kasancewan ita kaɗai suka haifa, su musulmai ne duk da asalinsu ƴan India ne amma ilimin addini ya sanya ba suyi wasti da abinda addini ya umurta ayi ba.
Mahaifiyar Maimoon ta dage nan duniya yarinyar ta ba zata auri ɗan Nigeria ba, dan ita a AL'ADAN su basa auren baqin fata, hukuncin mahaifiyar ta shi mahaifinta yabi yace ba zata auri ɗan Nigeria ba, wannan hukunci na iyayen nata ba qaramin tashin hankali ya haddasa mata ita da Mustapha ba dan har sai da ta kwanta ciwo, kusan wata guda tana asibiti akan soyayyan Mustapha wanda mahaifinta Dr.Mufaddal ganin yana qoqarin rasa yarinyar sa akan abinda bai taka kara ya karya ba nan yace ya amince, da amincewar mahaifinta ko kwana biyu bata qara yi a asibiti ba ta warke nan yasa ta aiko masa Mustapha, cike da ladabi ya amsa qiran Mahaifin Maimoon nan ya faɗa masa ya basa yarinyar sa inyayi ya turo iyayensa ayi baiko(saka rana), cike da farin ciki ya tashi ya tafi.

Yayan sa Nura ya fara qira ya sanar masa da komai cike da ɗimbin damuwan jin irin son da yarinyar kewa Mustapha ya ce "kana da hankali kuwa? Zaka sa yarinya ta faɗa sonka bayan kasan irin AL'ADAN mu, kaima ka sani ko mutuwa za kayi ba iya baba-alhaji ba ko Alhaji da Hajja ba zasu yarda ba, daga ni ba mai goyon bayan ka akan wannan lamari da ka kawo".

"Yaya gaskiya nikam bazan iya da wani AL'ADA ba, wacce nake so ita zan aura inma menene sai su bari daga baya insunga bata da hali mai kyau sai su saka ni auren Kanuriyan, wannan yarinya yaya da ka ganta ba kaman sauran ƴammatan indiyawa bane ba ruwanta da wani AL'ADUN indiyawa da ya saɓawa addini, ranan na taɓa gwada ta amma har muka kusa samun damuwa tayi ta surutu wai wannan abinda nake yi JAHILCI KO AL'ADAH za'a qira sa".

Nura a ɗaya ɓangaren yace "shikkenan fatan alkhaeri Allah kawo komai da sauqi ya kuma tabbatar da alkhaeryh".

Bayan kwana biyu ya qira Hajja ya sanar mata, nan ɗin ma wani faɗan ya tarar.
"Hajiya wallahi yarinyar na so na kuma mahaifanta sun amince, ai ko dan amincewar su ya kamata ku amince min tunda dai AL'ADUN su sunfi naku stauri kasancewar su indiyawa" faɗin Mustapha da ke kare da waya a kunne.

"Mustapha ba indiyawa suke ba koma menene ni ba ruwana kuma karka bari maganar nan yaje kunnen mahaifinku balle akai ga kunnen baba-alhaji, kana gani dai kuma kana sane sai da nasa baki kamun ya barka kai ma ba'a yi aurenka ka koma da mata ba, kuma ko tafiyanka wannan qasar sai da aka sha daru da shi, to karka yarda magana ya kai kunnen sa ni bansani ba kuma karka sako ni ciki, nasan duk abinda kake qullawa ɗan uwanka yana sane to kuje ku fama" Hajja na gama magana ta kashe waya kittt.

Dafe kai Mustapha yayi gaba ɗaya ya rasa yaya zai yi kansa ya qulle, qira ne ya kuma shigowa wayansa ya duba ganin ita ce sai yaqi ɗauka.
Abubuwa sun taru sun masa yawa ga kuma final-year exam's nasu dake kusantowa wanda bai wuce watanni biyu ya rage musu ba kuma sunayi ba jimawa makaranta zata sallamesu kowa ya kama hanyar sa.

Wasa-wasa har aka yi sati guda baya ɗaukan qiran Maimoon, abubuwa ne suka kacame masa dan ko ya ɗau qiranta baisan me zai ce mata ba.
Yana zaune a wani ɓangare na cikin makarantar kwastam yaji an rungume sa, juyowa yayi amma bai sha mamakin ganin ita ɗin ce ba, nan ta dinga masa kuka akan me yake shareta? Ba tare da ya ɓoye mata komai ba ya faɗa mata halin da ake ciki, nan suka rarrashi juna suka yi hira ya rakata har gida ya wuce gidan da yake.

Bayan Papanta ya dawo ba tare da ta ɓoye masa komai ba ta faɗa masa abinda iyayen Mustapha suka ce, Dr. Mufaddal nan ya lallaɓata ganin tana kuka.
Ko da mahaifiyar ta taji abinda ke faruwa nan tayi hamdala tace "shikkenan kowa ya huta, ita ta auri ba-indiye ɗan uwanta shima yaje can ya auri ƴar Nigeria ƴar uwar sa".
Papanta ya qirata ya bata haquri saboda abinda mahaifiyarta ta faɗa, su haqura Allah bai yi zasu auri juna ba. Nan fa hankali ya tashi dan ko makaranta taqi zuwa qarshe ma ba tare da kowa ya sani ba har guard's nata ta fice ta tafi gidan kakarta mahaifiyar mamanta dake cikin Bangalore.
Dr. Mufaddal suka neme ta suka rasa, har ya kori wasu daga cikin masu staronta dan aganinshi basu da hankali tunda zata fita ba tare da sun sani ba, ya nemi Mustapha ko tana wajan sa shima yace baisan bata gida ba, nan fa hankalin su ya tashi dan duk basu kawo wa ransu tana Bangalore ba.



FAN'S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.


INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

Wannan shafi gaba ɗayansa sadaukarwa ne gare ku iyayenmu mata❤️ Allah saka muku da aljanna, Allah ji qanku ya muku rahama, Allah qara ma ko wacce mace haqurin zama da mijinta ya kuma bata dama da ikon masa biyayya, Allah ya albarkaci zuri'a duniya da lahira.

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 35_36



Ko da taje nan ta faɗawa kakarta duk abinda ake ciki na abunda mahaifiyarta take faɗa.
Faɗa kakarta ta dinga yi kaman zata ari baki.
Sai da tayi sati biyu a gidan kakanta, ba tare da tayi waya da iyayen ta ko Mustapha ba dan wayan nata kashe shi tayi ta baro sa a gidan su, saboda tasan in tana waya da Mustapha za'a san inda take ta wajan shi.
Shiryawa suka yi suka kama hanyar Hyderabad da kakarta, ko da suka isaa kakarta ta dinga aikin surfawa yarinyarta masifa tunda tasan ba laifin Papa bane Ammaan ta ke hanawa, nan tasa Papa ya aika qiran Mustaphan saboda shi da kansa take so yaje Nigeria akan maganan auren.
Qiran Mustapha tayi bayan ya gama mata faɗa akan tafiyanta ya ɗaga masa hankali sai ta bashi haquri nan ta faɗa masa Papa na nemansa, suka yi waya suka yi sallama.

Mustapha yazo ya samu Papa nan ya tambaye sa halin da ke ciki ba tare da ɓoye-ɓoye ba ya faɗawa Dr. Mufaddal komai akan abinda iyayen sa suka faɗa, nan yace ya basa address na gidan nasu zai je, amma sai kakar Maimoon tace ya bari in Mustaphan ya gama exam's su tafi tare har da ita, sannan ta kuma yiwa iyayen Maimoon faɗa "shi aure da kuke gani nufi ne na Allah, in Allah yaso kuma rabo ya ranste sai ku mutu ayi, ko ayi ba yanda kuka iya kunya ta kasheku daga baya".
Sallaman Mustapha Papa yayi, sannan ya sanya aka maida kakar Maimoon (Aliyah) Bangalore.

Bayan wata biyu su Mustapha sun gama exam's, nan aka dinga shirin graduation nasu wanda kowa iyayensa zasu halarta, mutanen Nigeria sun samu isowa suma, Nura, Hajja, Maryam(matar Nura) sai Alhaji.
Tunda suka zo Hajja ke qara jaddada masa jan kunne akan kar ya kuskura yayi wannan magana balle mahaifin sa yaji, Nura da yasan duk abinda ake ciki har da maganar da yayi da Papa nan shima yake kaffa-kaffa yake addu'an Allah kawo wa ɗan uwansa komai da sauqi.

Ranar graduation akayi hidindimu, kama daga yaye ɗalibai da wasanni da al'adun makarantu yayin sallaman ɗaliban su.
Mustapha da familyn sa suna zaune a qayataccen wajen zaman da yake nasu shi da iyayensa, Alhaji ke magana "yanzu tunda an kammala komai yau gobe zamu wuce kai kuma yaushe zaka biyo mu?

Qasa yayi da kai yace "Alhaji sai nan da wata guda zamu gama kammala komai".

"To Allah ya kaimu, ka tabbatar ka gama komai akan lokaci ka dawo tunda kana sane da batun baba-alhaji kuma so ake a hada bikin naka da na ƴan uwanka acan Bornon..."
Maganan da Alhaji yake yi ya dakatar ganin wata yarinya da tazo ta tsaya gefen Mustapha.

Ba iya Mustapha ba, hatta Nura da Hajja sai da suka sha jinin jikinsu domin kana ganin yarinyar kasan ita Mustapha ke so, Maryam matar Nura tayi qasa da muryanta tace "mijin habibty wannan baiwar Allahn tamun kyau Allah sa budurwan Mustapha ce".
Nura dai ya kasa bata amsa dan dukan su idanuwan su na kan Alhaji da jin abinda zai faɗa.
Maimoon da ta tsaya gefen Mustapha ganin dukansu su kalleta su kalli babban mutumin da ta bashi matsayin mahaifin Mustapha, sai kawai ta stugunna tana gaida Alhaji, shi kuma ya amsa cike da mamaki yanawa Mustapha kallon neman qarin bayani.
Gaishe da Hajja tayi ta amsa ba yabo ba fallasa, Nura ma suka gaisa fuska a sake, Maryam ma suka gaisa tana mata murmushi dan ita Maryam har zuciyarta Maimoon ta burge ta.
Mustapha yasha jinin jikinsa sosai dan kallon da Alhaji yake masa kaɗai yasan akwai yinta, miqewa yayi ya bar wajan sai Maimoon ta biyo bayansa, su Alhaji kuma binsu da ido suka yi duka.

Kallonsa tayi ta fara magana cikin indiyanci "iyayenka dama sunzo baka gayamun ba?

"Kiyi haquri, yanzu kije gida za muyi magana daga baya".

Kallon sa tayi sai ta juya tayi tafiyanta, shi kuma ya koma wajan zaman nasu.
Alhaji kallonsa yayi yace "ina sauraranka".

"Alhaji me ya faru? Faɗin Mustapha da ya waske kaman baisan abinda Alhaji ke nufi ba.

"Mustapha mun fara wasan reni da kai? Inajinka wacece ita?
Hajja kau da kai tayi, Nura kuma yayi qasa da kai ya ciro wayan sa yana dannawa, Alhaji duk yana kallon su kuma ya fahimci sun san komai da ke tafiya "Mustapha ina sauraranka".

"Alhaji ba komai dama...dama...".

Cikin qufula Alhaji yace "Mustapha dama me? Ko ba zaka iya magana bane?

"Alhaji wacce zan aura ce, kuma dama babanta ya....."

Cikin ɓacin rai Alhaji ya dakatar da shi "Mustapha dama abinda kake qullawa anan qasan kenan? Dan na baka damar zuwa nan karatu ko? To bari kaji tun wuri ka aje maganan nan a gefe kana komawa kaje borno ka zaɓi mata a haɗa aurenku ayi da ƴan uwanka, karka bari ma baba-alhaji yaji zancen nan".
Juyawa yayi yana qarewa Nura da Hajja kallo, ƙwafa yayi yace "duk abinda Mustapha yake qullawa da saninku da kuma goyon bayanku da ɗaurin gindi da kuka masa, kai Nura ka fita idona ka kama kanka, Hajiya karki bari labari yaje kunnen baba-alhaji da ba zaku kwashe ta daɗi ba kema kin sani" yana gama magana ya miqe yabar wajan.

Sai sannan Hajja ta samu daman yin magana "kaga abinda nake gudu ko? Ni na sani kome zaku aikata za'a ce nice na ɗaure muku wajan zama barin ma dai kai Mustapha amma babu komai".

"Hajiya kiyi haquri ki bimu da addu'an alkairi" faɗin Nura da ke cike da tausayin ɗan uwansa.

"Nura in banyi haquri ba ya zanyi da ku? 'ya'ya ne Allah ya bani duk kuma sun tafi sai ku biyu kawai kuka tsaya Allah ya nufa, to ai haquri

Please Login or Register in order to submit comment