Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, ubanku yazo ya ɗauke ku ya maida ku gidan sa dan wannan kukan mutuwan ba'a gidan Fatuma ba".

"Eh ɗinnn an...an..anyi kuuu kann.. ai dan ke maaa..maaaan..kii bata duniya shiyasaaaa.. Wayyo Allah na Ammi na!" Sweetie ta faɗa cikin kuka.

"Eh lallai kukan munafurci kike yi muhibba, yau dan staɓar carbin fistaranki a cike yake ni zaki cewa Uwata ta mutu? Yau dama uwar waye ba zata mutu ba, Uwar kowa ma sai ta mutu dan haka zaku barmin gida na bana uwaku ba, yarinya qarama sai cikakken rashin kunya, waye baisan haquri ba inbanda rashin hankali da ke damunki".

Sweedy da ke zaune gefe damuwa ya taru ya mata yawa ga kukan sweetie da yake ci mata zuciya ga kuma labarin Ammi shiru sannan Darling tunda ya kawo su bai waiwayo su ba.
Afreen da ta shigo palourn yanzu wajan sweedy ta nufa tana faɗin "lafiya da tagumi? Cikin harshen turanci.

Sweedy kaman mai shirin kuka tace "komai ma ba lafiya ba ni banma san ya zanyi ba wallahi gaba ɗaya duniyan tamun zafi, gashi layina na Nigeria na nemeshi na rasa Darling bai zo ba bai neme mu ba".

Hajja da take ta aikin hararan sweedy tace "ai dole duniya ta miki zafi tunda a bakin kura kuke, shi yayan naku ai stakar dokan daji ya aje ku dole kice bai waiwayo ku ba, ooh ni fatuma na shiga aljanna na kasa fita wai yau ace jikoki na neman maida ni zabiya ko stigai rana tsaka abinda banyi tun tale-tale ba sai yau rana tsaka, gaba ɗaya jikoki sunbi sun buwaye ni".

Sweedy ko kallon Hajja bata yi ba balle ta mata magana dan ita bata cika hayaniya ba, indai stiwa kake so to ka samu sweerie ko sweetie dan halin DMD da sweedy ba banbanci basuson yawan magana.
Afreen da idanuwanta ke kan sweedy tace "yanzu ki amshi wayata ki qira Darling inyaso sai ya rarrashi sweetie da kansa, zuwa gobe sai mu nemo miki layi".

Murmushi Kawai sweedy tayi bata ce komai ba ta amshi wayan tayi dialing layin Darling, ganin sunan da Afreen tayi saving sai abun ya sanya ta murmusa sosai har fararen haqoranta suka bayyana tace "Wow! Sunan yayi daɗi ina aure haka zan dinga qiran mijina da shi Insha Allahu".
Ta qira yakai sau 3 bai ɗauka ba sai kawai ta tura message ta rungume wayan a qirjinta idanuwanta akan su sweetie.


DMD dake zaune gaban Daddy kansa a qasa yana sauraran faɗan da Daddy ke masa sai jin qira ya shigo wayan sa yayi, bai kalli wayanba balle ya duba har akayi qira uku duk suka kaste, Daddy yace "son ba qiranka ake yi bane?

Ya buɗe baki zai yi magana sai yaji shigowan message, ɗaukan wayan yayi ya duba ganin abinda aka tura sai kawai ya lumshe ido ya aje wayan yayi shiru.

Daddy ganin haka sai yaci gaba da maganan sa "son shi fa mahaifinka ne, baka da kaman shi ko madadin sa a duniyar ka, ka daina gaba da mahaifinka akan abinda bai taka kara ya karya ba dan nasan baka mari Rabi'atu ba".

DMD dai kansa a qasa baice uffan ba har Daddy ya gama, godiya kawai ya masa ya tashi ya fice a palourn yana ciro wayan sa dan qiran qannensa.

Mummy da kallo tabi sa har ya fita kamun ta sauqe ajiyan zuciya tace "gaskiya lamarin Mufaddal sai addu'a, Rabi'atu bata kyauta ba haka shima Abiy bai kyauta ba duk da yaron sa ne amma kuma Mufaddal bai yi dai-dai ba akan ɗauke yiwa mahaifinsa magana, Ammi shiru ba labarin ta shi Abiy da kuke tare ai sai ku dage ku rabu lafiya da shi".

"Ai ni rasa abun faɗa nake habibty addu'a na kawai Allah dawo da Maimuna lafiya dan har da rashin ta ya qara ta'azzara wasu abubuwan a halayyar sa duk da dama dai Mufaddal bauɗaɗɗen mutum ne" cewar Daddy yana ciro wayan sa dake qara a aljihu.

Sweedy na zaune riqe da waya shiru tana tunani kawai ta ji qaran shigowan qira har sai da ta razana, ganin Darling ne mai qira sai ta ɗauka ta kara a kunne "Hello".

Cikin Yaren Indianci ya mata magana a ɗaya ɓangaren "Sweedy ya aka yi?

"Darling, sweetie kuka sweerie kuka ni na rasa ya zanyi sunqi bari na naji da abu guda ɗaya ga layina na Nigeria ya ɓata".

Ajiyan zuciya ya sauqe yace "kuyi haquri Ammi ta kusa dawowa in Allah ya yarda, sa wayan a handsfree".

Sawa tayi a handsfree kaman yanda ya umurce ta cikin yaren hindi.

"Sweetyn Ammi kukan me kuke?

Sweetie da ke aikin ajiyan zuciya jin muryan Darling da sauri ta fara magana da Indianci cikin dashashshiyar muryanta "Darling, Abiy yace Ammi na gida amma munje gida ba Ammi sai yace kuna tare a gidan Hajja, mun ganka ka kuma kawo mu gidan Hajja yau kwanmu 4 ba Ammi bamu ganta ba kuma Hajja tace Ammin mu ta ɓace".

Dafe kai kawai DMD yayi jin irin surutun da take korowa bata ko jan numfashi ga kuma ciwon kai dake kan addaban sa "sweetie kina ji ba, to kuyi haquri ba yau Monday ba to Ammi zata dawo ranan Thursday kinji ki dena kuka kiyi shiru okay".

Sweetie tura baki tayi kaman tana gaban sa tace "Darling kai kuma yaushe za kazo to nayi missing naka kuma Abiy ma yaqi zuwa".

Busar da iska yayi kamun cikin gajiya da magana yace "zanzo Wednesday" kittt ya kashe wayan, yana qarisawa wajan da ya Parker motansa ya fice yayi wajan Jay dake asibiti.
Yana isa direct office na Jay ya nufa, qwanqwasa qofa yayi nan aka basa daman shiga, ya tura qofan ta shiga ko kallon Jay bai yi ba ya nufi wani qofa ya tura ya shiga, Wow! Kai ka ce ɗakin wata Amarya ne dan kuwa kujeru ne set guda ga kuma fridge ga kuma wani madaidaicin gado a gefe.
Jay buɗe qofan yayi ya shigo, ganin DMD akan dogon kujera mai ɗaukan mutum uku sai ya qarisa ya zauna akan 1seater yana faɗin "dude lafiya kuwa?

"Normal" abunda ya faɗa kenan a taqaice yana mai lumshe ido.

Murmushi Jay yayi sanin stokana zai yi, sai yace "dude ko dai abun ta mosta ne?

Wani banzan kallo DMD ya wasta masa sannan ya kuma maida idon sa ya kulle.

"Dude in abun ne in nemo magani ko kuma na qira maka ɗaya daga Nurses namu" ya faɗa yana danne dariyan sa dan yasan tabbas ya nemo magana.

Tashuwa zaune DMD yayi rai a ɓace kaman wanda aka stare da bindiga dai yayi maganan ya ce "Jay kasan bana son maganan banza ko? In abinda kake yi kenan ance maka ni kai ne da ko wacce qazamar zata taɓa? Mind ur word's, u know i hate this, mutum ko da yaushe ba shi da magana sai na mata to za su kashe ka, in kuma batun magani ne kai ka sani na fika sanin maganin mastalata dan kai ne babban ciwo na, mutum kullum surutu ka dinga saka mun headache, ina barin Nigeria ciwo na ya warke" faɗin Darling yana komawa ya kwanta.

Jay dariya yayi dan ko kaɗan kalaman DMD basu damesa ba "dude nima dai saurayine gal a leda kaman kai....." Knocking da ake wa qofan office nasa shi ya sanya shi miqewa ya fice dan dama akwai patient nasa da ya tura yin scanning su dawo.

DMD gyara kwanciyan sa yayi ya lumshe ido dan bacci yake buqata ko kansa zai yi masa dai-dai.


Ayi Haquri da ƙarancin page ɗin nan.

FAN'S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.

A yi sharing dan girman Allah.

INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚


𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله


LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member's ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR'S ANNIVERSARY


JAHILCI KO AL'ADAH? FAN'S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku🤝



FAN'S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.


💋💋 امى بتولة💋




𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 31_32


Jay ne ya shigo ɗakin ya nufi inda yake kwance yana qiran sunan sa "Dude! Dude! Dude..."
Kasancewan bashi da nauyin bacci tun shigowan Jay qaran qofan ya tayar da shi, idanuwan sa a kulle yace "Jay meyasa ka cika rashin ji ne? Ka qira mutum sau ɗaya bai yi ba sai ka qarar min da suna" yana gama faɗa ya miqe ya zauna yana laluɓo wayansa.

Jay taɓe baki yayi yace "daɗin abun ba sunanka na qira ba, koma dai mene tashi mu tafi gida".

DMD bai ce komai ba ya miqe ya shiga toilet ɗin dake ɗakin, can ya fito yana gyara hannun rigansa da ya nannaɗe.
Bai ko kalli Jay ba ya shumfiɗa darduma ya tada Salla, sai da ya idar ya naɗe darduman sannan ya kalli Jay yace "let's go" yana gama magana ya fice a ɗakin.

Jay miqewa yayi ya bi bayansa bayan ya kulle qofan office nasa.
Kowannen su motansa ya shiga suka yi gidan Daddy.

Ɗaya na bin ɗaya haka duka taho har suka iso gida gate man ya buɗe musu gate suka shigo kowa yayi parking suka nufi cikin palourn da sallama.
Mummy da ke zaune tana waya wanda daga ji kasan akan business nata ne, tana gama magana ta kaste tana amsa sallaman yaran nata fiskanta ɗauke da murmushi "wa'alaikumussalam sannunku da dawowa mazajen Hajja".

Jay ne ya fara magana "habibty gaskiya nidai ba zan iya da fitinan stohuwar nan ba, nabar wa dude kyauta".

DMD hararan sa yayi sannan ya buɗe baki kaman baison magana yace "Habibty yunwa" da Indianci yayi maganan.

Mummy na murmushi tace "yanzu son ai ko sayar da ni kayi niyan yi sai dai ka saida ni har ka amshi ƴan canjinka, dan ban fahimci ko kalma ɗaya a maganan ka ba, wannan yaren sai ku ai tunda Amminku taqi koyamin".

DMD murmushi yayi jin abinda mummy tace, sai ya tuno rigimansu da Ammi watarana akan indiancin
** Ammi ce tayi magana cikin harshen Indianci "habibty wai Hajja na magana mune muka hana yaranmu yin aure sun girma suna gaban mu".
Mummy idanu ta zubawa Ammi kawai bata ce komai ba.
Ammi ta kuma magana cikin harshen turanci "wai baki ji me nace ba habibty?
Sai sannan mummy tayi magana da turancin itama "ta ina zanji abinda kika ce Ammin su, bayan kinqi koyamun kuma dai so kike muyi gulmanmu amma kinqi koyamun yaren da za muyi gulman gashi ke kuma bakya jin yaren mu duka".
Ammi murmushin ta mai stada tayi tace "karki damu yaronki zai koya miki tunda shi yana jin yaren ku yana jin Indiancin" cewar Ammi da turanci.**

Muryan mummy ne ya kaste masa tunani "Son me kake tunani tun ɗaxu ina magana shiru? Mummy ta faɗa tana kallon DMD da ya faɗa duniyar tunanin mahaifiyar sa.

Lumshe ido yayi ya buɗe su a hankali yace "ba komai habibty".

Mummy ba dan ta yarda ba tace "shikkenan, kai kuma jabeer maza-maza kaje ka ɗauko min yarinya tunda gobe Wednesday hutun ya qare akwai school".

Jay langwaɓe kai yayi kaman mace yace "Habibty zan ɗauko ta dole na, amma nima ki dinga cemun yaronki, kowa daga son sai daughter sai yarinya na, nine kawai ake qira da sunana jabeer".

Hararan sa mummy tayi ta wuce dinning tana faɗin "son zo kaci abinci shi kuma in ya gama kishi da yaran nawa sai yazo ya ci shima".

DMD kallon sa yayi tare da yin murmushin gefen leɓe "ka daina kishi da mu".

Jay taɓe baki yayi yace "ayi kishi da kai akan me? Ni wuce muje muci abinci".

"Kaci abinci a ina bayan baka yi sallah ba".

Jay hararansa yayi yace "in kai ke amsan sallahn in tawa tazo ka dawomun da ita, kana sharar baccinka nayi sallah kace banyi ba".

Dukansu miqewa suka yi suka nufi dinning ɗin, mummy tayi saving nasu duk suka yi shiru suna cin abinci.
Bayan sun kammala suka miqe suka haura sama kowa yayi ɗakinsa dan ya wasta ruwa.

DMD yana shiga ɗakin sa ya cire kayan jikinsa sannan ya ɗaura towel ya shige toilet, can ba jimawa ya fito ɗaure da towel ɗin a qugunsa daga leman ruwan dake jikin sa kasan wanka yayi.
DMD namiji ne iya namiji wanda kana ganinsa kaga ingarman namiji domin ya tara duk wani abu da mace ke buqata a wajan mijin aure, Allah ya hore masa kyau ga kuɗi sannan mutum ne mara hayaniya, yana da tsayi amma ba stayi mai muni ba sannan yana da jiki wanda tsayin sa ya ɓoye jikin sai komai ya tafi dai-dai, qirjinsa mai cike da haiba a cike yake da kwantattun gashi wanda kai kace gashin kan jariri ne ba kaman na wasu mazan kaman quda-quda ba, yana da haske sannan yana da yalwan gashin kai da na gemu waɗanda suka sha gyara, gashin kansa kuwa kai kace mace ce, yana da hanci mai stayi dai-dai da kuma bakin sa wanda bai da girma sosai mai tafiya da yanayin sa na rashin son yawan magana, DMD kyakkyawa ne ajin qarshe kana ganinsa kaga wanda ya haɗa jini da larabawa ko kuma indiyawa.
Ba tare da ya staya shafa mai ko kuma sanya kaya ba ya nufi kan gadon da towel dake qugunsa, kishingiɗa yayi kansa akan fillow dake jingine da kan gado, ya sanya hannayen sa duka biyu ya tallafo ƙeyarsa yana tunanin rayuwan da suke ciki da kuma qaddaran da ya sauqa kan mahaifiyar su.
Lumshe idanuwan sa da suka koma jajaye yayi a hankali ya furta "Ammi nayi kewanki sosai, ki dawo gare mu Ammi mu koma Canada muyi rayuwanmu kaman baya hankali kwance, I soo much miss you Ammi".



𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚'𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 - 250 𝟏𝐆𝐁 - 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 500
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎......



WAIWAYE ADON TAFIYA!
Cikakken tarihin DMD!
Asalin labarin...

Alhaji Muhammad Nura mai fata shine asalin sunan kakan su DMD, haifaffen garin Maiduguri ne a local government na Wuba anguwan Askira, Alhaji Muhammadu ya kasance yaro ɗaya tal da Allah ya bawa iyayen sa Malam Nura mai fata da kuma mahaifiyar sa Zainabu wacce ake qira da Yah-gana, ya taso cikin soyayya da qaunan iyaye wanda suka kasance daga cikin yaren bare-bari waɗanda aka fi sani da Kanuri.
Iyayen Alhaji Muhammadu auren dangi suka yi wanda hakan yake AL'ADAH a gare su, mutum ba zai yi aure ba sai ƴar dangin su kuma ta kasance Kanuriya gaba da baya haka ma mace sai mijin ya kasance Kanuri, Alhaji muhammadu tun da ya mallaki hankalin kansa ya nuna yana son wata yarinya a wani yanki Magumeri itama Kanuriya ce amma ba a familyn su take ba, iyayensa sun yarje masa neman ta amma da suka je wajan kakannin sa sai suka nuna basu amince ba an masa mata kuma ƴar gidan yayan maman sa. kasancewan sa yaro mai biyayya da jin magana ba musu ya amince kuma ya rabu da wacce yake so inda ba jimawa aka masa aure da FATIMA da ta kasance yarinyar kawun sa.
Bayan auren su bai wuce da shekara guda ba mahaifin sa da mahaifiyar sa suka yi hastari inda ko shurawa basu yi ba suka ce ga garinku nan (Allah musu rahama).
Kakan sa ya nemi da ya koma cikin Maiduguri ya zauna da Fatima wacce suke qira da Hajja a family house amma sai ya nuna ba haka ba shi yana son zuwa qaro ilimi, kakansa yayi-yayi ya zauna tunda anan Maidugurin ma suna da wadatattun makarantu amma yaqi dan haka sai suka bisu da fatan alkairi sannan ya tabbatar suna zuwa duba dangi, nan Alhaji muhammadu ya kamo hanyar Gombe tare da matar sa Hajja wacce har zuwa wannan lokaci bata taɓa ko ɓatan wata ba.
Sun shigo Gombe cike da sa'a inda basu staya ako wanni yanki na Gombe ba sai Ashaka, kasancewan yana da rufin asiri dan mahaifansa suna da qadarori kuma kamun ya taho ya buqaci wasu daga qadaran gadon sa kuma kakan sa baba-alhaji bai hana sa ba ya basa tunda garin mutane zai je ga kuma iyali.
Gida ya saya musu na rufin asiri, inda yake shiga cikin Gombe dan duba makarantar kaman yanda yayi niya, ya samu wani babban sangaya a nan cikin Gombe yana qara karatun sa in yayi kwana biyu a cikin Gombe ya dawo Ashaka yayi kwana biyu zuwa uku, a cikin wannan halin Allah yasa ya fara sana'ar fata inda Allah ya sawa abun albarka kuma ya karɓe sa, har dai ya siya fili a cikin Gombe.
Bayan dawowarsa Ashaka ya huta suna zaune tare da matarsa Hajja sai ya dube ta yace "Yah-gana na saya mana fili a Gombe saura ginawa in Allah ya yarda kinga sai mu koma can da zama abunmu, ke kin huta kewa na nima na huta kewanki da kuma jigile a hanya".
Hajja sai tace masa "a gaskiya nikam Alhaji nafi son zaman nan garin sai dai in ka sayawa yaranka amma dai ni zaman nan yafi min".

Ganin Hajja ta dage sai Alhaji muhammadu ya qyaleta ya cigaba da kaiwa da komowa tsakanin cikin Gombe da Ashaka, wanda ana cikin haka a shekarar su ta farko da zuwa garin Gombe kenan Allah ya azurta Hajja da samun juna biyu, wannan ciki ba qaramin farantawa Alhaji muhammadu rai ya yi ba, sosai yake kulawa da Hajja da abunda ke cikinta.
Tunda cikinta ya girma ta shiga watan haihuwan ta sai Alhaji ya kuma tunkaran ta da maganan komawa cikin Gombe amma nan ma taqi ganin haka sai yabar maganan gaba ɗaya shima ya daina yawaita zuwa Gombe dan ko harkan fata yanzu yana da yaran gida daga Gombe har nan Ashaka da sauran local government na Gombe har ma da wajen Gombe.
Ranar da naquda ya tashi wa Hajja ya ɗauke ta suka tafi asibiti, da zuwansu da haihuwanta duka bai fi minti biyar ba ta santalo yarinyar ta mace mai matuqar kyau dan tana kama da Alhaji kuma shi kyakkyawan gaske ne duk kyawun Hajja bata kama qafan sa ba, suka dawo gida da farinciki nan ƴan barka ke shigowa kowa ya shigo sai ya yabi kyau na yarinyar, ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Alhaji wato Zainabu amma sai suka ɓoye sunan suna qiranta Yaanah, bayan suna da kwanaki dan har sun fita arba'in nan ciwo ya kama yarinya, ciwon ciki ba ji ba gani duk kyawun yarinya cikin kwanaki ta koma abun tausayi kuma a cikin wannan halin wani cikin ya qara bayyana a jikin Hajja nan dai abubuwa suka taru suka musu yawa sai gaba ɗaya ya ajiye shiga Gombe komai kawai ana masa yana daga gida yana kula da iyalan sa.
Yarinya taji sauqi inda zuwa yanzu take da kusan wata 7 cikin jikin Hajj na wata 6, kwastan suka wayi gari yarinya babu rai wannan rashin yarinya ya damu Hajja inda har ya janyo ta rasa cikin jikin ta, Alhaji yayi jimami na rashin cikin da kuma yarinyan amma ya miqawa Allah lamarin sa dan Allah ne mai bayarwa kuma shine mai karɓa.

Sai da Hajja ta shekara da yin ɓari sannan ta kuma samun wani cikin ta haifi yaranta ƴan biyu duka mata aka sawa ɗaya sunan Zainab ɗayan kuma sunan mahaifiyar Hajja wato Hajara, har yara suka kai shekara 2 Hajja bata kuma haihuwa ba inda ta masta ma Alhaji akan suje Maiduguri ba tare da ya mata musu ba ya miqa amanan ayyukan sa a hannun yaran gidan sa, suka wuce Maiduguri da ƴan biyun su inda suka isa lafiya kowa yayi farincikin ganin su stoho Alhaji-baba yayi ta sa musu albarka sannan yace su kula da bakin mutane akan yaran su, satin su biyu da zuwa zazzaɓi ya bugi ƴan biyu wanda ko lokaci bai ɗauka ba a ranan da Magrib zainabu tace ga garinku, an barta zuwa safe a mata sutura amma kamun gari ya waye itama Hajara tace ga garinku, Hajja tayi kuka har kaman zata bi yaranta dan sosai take qaunar ƴan biyun ta.

Sai da suka kwashe wata guda a Maiduguri kamun suka juyo garin Gombe, suna dawowa basu yi sati ba ciki ya bayyana jikin Hajja nan ta dinga addu'a da amfani da magungunan da baba-alhaji ya bata, wata tara ciff ta haifo yaronta namiji mai kama da ita inda ranan suna yaci sunan kakansa Nura, Alhaji sosai yake son wannan yaron nasa yana da shekara 2 ya ɗauke sa ya kaisa cikin Gombe yana karatun Alqur'ani a sangaya kuma yana zuwa boko, Hajja har da kukanta an rabata da yaronta qarami amma ko takan magananta Alhaji bai bi ba tunda ba zata zauna a cikin Gombe ba to shikuma yaransa za suyi karatu.
Ciki ne ya qara bayyana a jikin Hajja inda bayan wata tara ciff ta kuma haifo yara biyu mace da namiji, ranan suna mace aka sa mata maimuna takwarar matan baba-alhaji namijin kuma aka sa masa Mustapha, yara suna cika shekara biyu Alhaji ya ɗau Mustaphan ya kai cikin Gombe ya sanya shi a makarantar da yayan su Nura yake wanda shi Nura a lokacin shekarun sa huɗu 4.
Hajja haka ta zauna daga ita sai maimuna a Ashaka duk da Maimuna ma ba zaman gida take ba Alhaji ya sata a makaranta a nan cikin Ashaka.

Nura na da shekara goma ya sauqe Qur'ani mai girma kuma lokacin yana qoqarin shiga secondary, Mustapha ma a lokacin yana da shekaru 8

Please Login or Register in order to submit comment