Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har kike kawo wani maganan? Wannan auren su Mustaphan fa kaman an bisa da baki wallahi kana mastawa a lamarin ka baqonci lahira, yanzu ina baba-alhaji? Ina Alhaji surkinki? Ina Asma'u? Ko yarinyan da Asma'u ta haifa bata zauna ba dan haka ya isa kisan wannan auren nasu Allah ne ya haɗa, amma kuma tunda kince sakinta yayi ba mastala kya iya samun Alhaji babba amma dai ni fanne naga ayar Allah ba ruwana da lamarin Mustapha da ƴar qasar can".
Aunty Amarya kaman za ta haɗiye zuciya haka ta yi kwana biyu a daddafe ta dawo bayan ta gama ɗaura aniya da sabon shirin shiryawa Ammi manakisa wanda sai ya rabasu na gasken-gaske.
Ɓangaren Hajja kuwa Daddy (Nura) ya qira ta dinga masa faɗa akan ya tabbatar Mustapha ya dawo da maimuna inba haka ba zata saɓa musu, shi dai Daddy haquri ya dinga bawa Hajja sannan suka yi sallama ya qira layukan Abiy baya tafiya sai ya bari akan zai qira daga baya.

Yau aiki ya sha ba kaɗan ba dan da qyar ya samu kayakinsa da aka riqe su suka fito, companyn Jigawa kuma ya seta komai dan shi ne dama dalilin aikin da ya hanasa bacci da wuri jiya, sai dai duk da haka akwai buqatan ya je dan duba sauran abubuwan ga kuma maganan meeting da ake jiran approval nasa, sai can yamma kamun ya fito ya dawo gida.
Da sallama ya shigo palourn wanda tun daga bakin qofa ya gama kallon farincikin da ke kwance a fiskan Ammi kuma yasan tabbas Abiy ne ya zo, ba tare da ya ce qala ba ya qarisa shigowa yana faɗin "sannu da gida Ammi" yana gama faɗa ya wuce haurawa sama.
Ammi dai amsawa tayi tana murmushi ta masa sannu.
Abiy ne ya sauqo ɗauke da sweetie tana ta aikin shagwaɓa, domin su ma yaran karan kansu sunsan yau Ammi na fatinciki kuma suma zuwan Abiy ya sanya su farinciki domin kewan mahaifin nasu suke.

Wasta ruwa yayi sannan ya jawo wayansa yana laluɓo Numbern Jay yau kusan kwana biyu bai qira sa ba, "hello dude yau ka tuna da ni ne? Cewar Jay da yayi picking call ɗin.
"Mtsw! Za ka fara surutun naka ko?
"Hhh ba dole nayi surutu ba Allah ya stagomin baki, ai kaikam sai tsagun bakinka ya manne tunda baka buɗewa kayi magana da kyau, salatin ma a zuciya ake yi, yanzu dai ya su Ammi? Ya kuma labarin Abiy? Ina su sweetie ina Afreen?
DMD dafe kai yayi yana faɗin "ko me kayi ba laifinka ba nine na qiraka, amma kaji wallahi ko ɗaya ba zan amsa ba, ka gaida gida" kitt ya kashe wayan yana jan guntun tsaki.
Jay na kan qiransa amma ko kallon wayan bai yi ba, ya shige toilet.
Ɓangaren Jay kuwa dariya ya dinga yi yana faɗin "Allah ka shiryi dude ka gwadamun ranan da zai sauya, ai wannan mace me zama da kai ta shiga uku".

Sai da Ammi ta tura aka qirasa kamun ya fito, sama-sama ya gaishe da Abiy sannan ya zauna Ammi tayi saving nasa ta cika cikinsa.
Washegari DMD bai je office ba, Managern sa ya qira ya tura masa abubuwan da ya kamata, dan so yake ya huta aikin da yayi kwana biyu ko ishashshen bacci ba ya yi, inda ɓangaren Abiy da Ammi kuwa soyayyan su suke yi kaman sabbin aure, a ranan kuma Abiy ya sa duka suka shirya har Darling suka tafi shopping, kaya niqi-niqi kowa ya jida, aka wa sweedy sayayyan tafiya school Afreen ma aka mata na dawowa Nigeria, Abiy ma ya jida kayaki, shi dai DMD ba abinda ya ɗauka illa iyaka wani headband na mata da ya gani ya masa kyau, Abiy ne ya biya kuɗin komai suka kuma wucewa suka yi sayayyan kayan ƙwamulashe, yawo suka yi sosai sannan suka dawo gida, kowa ya jida nasa yayi ɗakinsa da shi, Darling a Waldrop ya jefa headband ɗin ba tare da yasan ma me zai yi da shi ba.
Washegari da sassafe sweedy ta kama hanyan India bayan Abiy da Ammi sun mata faɗa ta kula sosai, Afreen kuma sai da aka kwashe sati guda kamun suka juyo tare da Abiy da ke cike da kewan matar sa.

Abiy na dawowa Aunty Amarya cikin kirsa ta lallaɓasa ta basa haquri akan ba tayi dai-dai ba kuma ba zata qara ba, abinka da mata da miji nan suka shirya suna soyewansu, da farko sai yayi kwana biyar ko sati a Nigeria sai ya je Canada yayi kwana biyar ya dawo, ana rayuwa ana tafiya haka har dai Aunty Amarya ta fara kasa hali, sai yayi sati bai je Canada ba kuma in yaje baya wuce kwana biyu zai dawo, qarshenta kwana ɗaya yake yi ya dawo, daga baya kuma zai fi sati biyu bai je ba kuma a ranan da yaje a ranan zai dawo, ita dai Ammi duk haka bai dameta ba, ga yaranta na makaranta tana kallonsu suna kallonta hankalinta yafi kwanciya, a cikin wannan halin DMD yayi approval na meeting nasa a Zamfara inda yana shigowa ya gabatar da komai ya juya ya koma ko sauran companies ɗin bai leqa ba balle Gombe, Abiy da sai da ya raba hali domin faɗa ya dinga yiwa Ammi kaman ita ce ta yi hakan, qarshe sai da ya kwashe wata bai je Canada ba, Ammi kuwa duk tabi ta damu a wannan lokacin ne kuma yara suka samu Hutu har da sweedy da ta kwashe shekara a makaranta ta dawo dan haka sai Ammi ta sako su gaba har DMD duka diro Nigeria.
Aunty Amarya a fiska kuma a gaban Abiy nunawa take duk duniya ba wanda take so irin yaransa kuma bata kishi da Ammi, amma a bayan fage rashin kunya takewa Ammi ta ke kuma zuba mata munafurci, sai da suka kwashe sati biyu da zuwa sannan suka je Ashaka, Hajja farincikin rasa inda zata sanya kanta ta yi ganin jikokin nata, nan ta dinga zubawa Abiy faɗa kaman za ta ari-baki " Maimoon kiyi haquri naji abinda ya faru, wato tunda shi Mustapha yanzu ya butulu ɗa namiji hankaka gabansa fari bayansa baqi shi ne har da saki nan Rabi'atu ta qiran tana faɗamun".
Ammi da tayi qasa da kai cewa tayi "Hajja bakomai ba saki bane nice naje Canada".
"A'a 'yar nan karki wani rufa masa asiri ai na sani, shi Mustapha dan staɓar ya zama ciki ba Godiyan Allah balle tuna alheri ya mance yanda ya sha gwagwarmaya ya aureki har zai iya daukan hannu ya baki takarda tunda shi sha-sha-sha ne, to ya taimaki kansa dan da mun haɗu tabbas sai na saɓa masa".
"Bakomai Hajja ya wuce, am nace ba Hajja dama munason zuwa Maiduguri da yaran nan".
Washe baki Hajja tayi ta ce " 'yar albarka Allah miki albarka ai ya kamata kam zuwa Maiduguri dan za suce tunda Allah ya ɗauki Alhaji shikkenan kuma ni da ku bama zuwa, yanzu dai wannan tafiya duka za'a yi sa kowa da kowa".
"To Allah ya kai mu".
Ammi washegari tabar Ashaka su, DMD kuwa sai da yayi kwana biyu kamun ya dawo yabar su sweedy a can, dan sweetie indai gidan Hajja ne to ko babu Ammi za ta zauna.
DMD ya je ya dubo Companyn Jigawa, sannan ya wuce Abuja nan ma ya duba sabon shopping-mall da zai buɗe, komai lafiya sannan ya juyo. a ranar kuma duk suka tattaro da iyalan Daddy da na Abiy suka nufi Maiduguri.
Sosai family suka ji daɗin zuwan su Hajja, nan aka sauqesu a sashi na daban, dan duk da kasancewan basa zuwa amma duk wani dangi yana da masauqi a family house ɗin domin a yanzu yawansu ma ya sa an raba family house ya zama biyu, ɗaya stohon na iyaye da kakanni ɗaya sabon kuma na jikoki da yara, sannan duka gidajen manya ne iya ganin ka wane anguwa guda.
Zuwan su Hajja ya sanya an haɗa qwarya-qwaryar family meeting in da aka buɗe taro da addu'a sannan Alhaji babba da zuwa yanzu shima ya stufa sosai ya fara koyo bayani, sai da yayi ya gama sannan aka buqaci duk wani mai abun faɗa ya faɗa.
'yar uwan Hajja da suka haɗa uba ne ta fara koro bayani akan abinda suka kista da Aunty Amarya na game da auran yaran kan cewa su Jay da DMD su zaɓi mata su sweedy ma anmusu miji.
Tun shigowan sa babban palourn ya samu waje ya zauna wayansa ya ciro yana laste-lastensa bai ko kalli kowa ba balle ya tofa musu qala har sai da ya ji abinda dattijuwan da Hajja za ta girmeta da kaɗan ta faɗa, ɗagowa yayi ya wasta ma matar da baisan wacece ma ita a wajansa ba wani malalacin kallo, har zai buɗe baki sai kuma me ya tuna oho ya maida hankalinsa kan wayansa, Daddy ne yayi magana "in Allah ya yarda Duk zasu zaɓi mata in yaso ba jima sai ayi auren tunda duk yanzu suna da aikin kansu".
Jay idanuwansa ya baza a ɗakin ganin yaran mata basa palourn sai ya taɓe baki yana faɗi a ransa "in yaranku suna da kyau kuma sun nuna to ko huɗu ne ni Jabeer zan aura amma in kwailaye ne to tarihi zai maimaita kansa, mata zan nemo zuqeqiya" vibrating na wayansa ne ya kaste masa zancen-zuci da yake yi, ganin mai qiran sai ya miqe ya fice a palourn yana ɗaukan qiran.
Shi ma miqewa yayi yana maida wayansa aljihu tare da sanya ɗaya hannun a aljihun wandon jeans na jiginsa da yayi matuqar amsar sa, gaskiya DMD kyakkyawan qarshe ne dan yanda qananan kayan suka zauna a jikinsa kai kace ba ɗan Nigeria ba ne, ficewa yayi a palourn duk sai suka bi su da kallo Aunty Amarya da dattijuwan da tayi magana taɓe baki suka yi, Ammi kuma qasa tayi da kanta tana addu'an shiriya ga yaran nasu da maganan da suke ja musu, Abiy dai ko qala bai ce ba dan shi komai aka yi dai-dai ne baya qaunan ya kuma yin wani laifin.
Hajja dai tayi supporting na shawaran, Aunty Amarya ranta fari tass har aka yi addu'a aka waste, wasu na ta zancen DMD ya rena mutane ai gado yayi wajan Mustapha.

Jay yana gama wayan yabi bayan DMD da ya nufi ficewa a sashin babban palourn da ake meeting yana faɗin "dude Angon ƴar Maiduguri jirani mu fara shirye-shirye".
Ko nuna alaman ya ji abinda yake faɗa bai yi ba balle batun ya jirasa, sai da Jay ya haɗa da gudu kamun ya iso sa yana faɗin "Allah nuna min randa zanga ƴar Maiduguri ta sanya ka wanke-wanke wallahi sai na sanya ta ramamin wulaqancin nan da kake mun".
Kallon banza ya bi Jay da shi yana faɗin "ba'a haifi iyayenta ba balle ita, ni banda lokacin mace balle aure amma inaga tabbas zan yi dan waɗannan mutanen su san basu isa su sanya ni auran yaransu ba".
Jay murmushi yayi ya ce "ashe kai ma ka gama yanke shawara? Ai ina gaya maka dude nikam in har suna da qosasssun yara kyawawa to ko huɗu suka ce zan aura amma aradu indai qwailaye ne to sai dai ayi wanda za'a yi inyaso a yafe ni daga family dama can bai damen ba, bare zan nemo na aura zuqeqiya nunanniya dan ni banson harka da qananun mata, dama muna can Gombe me ya haɗa mu da Maiduguri, Ni fa inaganin ta Abiy zan yi India zan koma na zaɓo mata nustaststiya mai kyau wacce ta iya soyayya kaman Ammi, matan Nigerian nan in ba sa'a kayi ba to duk shiru ne".
Taɓe baki yayi yace "ɗauko mota ka kaini airport sai ka dawo musu da motan".
Jay dubansa yayi ya ce "badai yau zaka koma ba dude?
"In na zauna ban koma ba aikin ne zan maka?
"A'a mai da wuqan jirani na ɗauko motan, amma gaskiya ba dan ina buqatan qarewa ƴammatayen kallo ba da na biyo ka mun tafi".
"Mstww! Ai kai maganan mata shi zai kashe ka, za ka ɗauko ne ko na tafi da kaina kuje ku samu motar a airport?
Jay yana dariya ya juya dan yasan kaɗan daga halin DMD sai ya tafi ta motan ya barota a can yayi tafiyansa.
Motan ya ɗauko DMD ya shiga suka nufi airport, har suka isa Jay shi kaɗai ke surutun sa DMD hankalinsa duka na kan waya kai kace dan kallon waya aka halicci idonsa.
Sai da jirginsu ya tashi sannan Jay ya juyo ya dawo gidan, Ammi na ganinsa ta tambayesa Darling sai ya faɗa mata ya koma Gombe, addu'an a sauqa Lafiya da na Allah shirya ta bisa da shi, Jay kuwa baza idanuwa ya dinga yi yana qarewa ƴammatayen gidan kallo, kyau kam iya kyau Allah ya azurta wannan family da shi don kana ganin ko waccen budurwa za ka tabbatar tabbas Kanuriya ce gaba da baya, Jay yayi kallo iya kallo qarshe dai ya gama rawan idonsa ya rasa ta zaɓa.

Ammi da yaranta suna ɗakinsu a zaune, Jay ya shigo yana faɗin "Ammi gaskiya ni na gama dubawa sama da qasa banga wace ta mun ba kawai na yanke shawara zan jira sweetie ta girma", ba iya Ammi ba har sweetie da bata cika shekara goma ba sai da tayi dariya duk da rashin wayonta.
Ammi ta ce "son Allah ya shiryaku, ai gwanda ku dage ku nema kamun a nema muku, ka bari kayi ta huɗu da sweetie lokacin ta girma", tura baki sweetie tayi ta ce "ni Ammi banson ta huɗu ta ɗaya nakeso".
Duk dariya suka sanya, Jay na faɗin "sweedy ku dage ku zaɓi ku darje duk da nasan ba zaku samu kyawawa irinmu ba".
Sweedy na murmushi cikin rashin son yawan magana ta ce "big bro kai ma kasan mijina sai ya fika kyau, amma yanzu dai ba ta wannan ake yi ba".
Hira suka ci-gaba da yi suna dariya, cikin dabara Ammi ke tausarsu tana nusar da su fa'idan bin magana da biyayya ga iyaye, amma sweedy dai ta tuɓure ba wanda ya mata dan abun kaman wanda suke jiran qiris samarin gidan kowa sai faman isar da saqon soyayyansa yake gare su barinma dai Sweedy, domin a duniya sweedy Allah ya hore mata kyau banbancin ta da DMD kaɗan ne dan da ta kaisa shekaru ko ta biyo sa kusa-kusa za'a iya qiransu twin's.




MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA.




INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚



𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله


LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member's ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR'S ANNIVERSARY

FAN'S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.


💋💋 امى بتولة💋

Ayi haƙuri da rashin update jiya sakamakon wayar tawa sai a hankali har yanzu ba ta farfaɗo sosai ba.



𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 47_48


DMD bai nufi Gombe ba direct Abuja ya wuce dan ankammala komai na shopping-mall ɗin, wata arniyar hotel ya kama ta manyan masu kuɗi wanda daga masu mulki da manyan 'yan siyasa sai manyan masu kuɗi ke zuwa hotel ɗin, kwanansa ɗaya washegari ya fito daga mall ɗin wanda ake shirye-shiryen buɗewa gobe ya dawo hotel ɗin, bayan yayi parking ya fito a motan ya kulle, tafiya yake hankalinsa na kan wayansa da aka turo masa saqo daga Canada yana dubawa, ba tare da ya kula ba ya ji ya yasar da key na motan sa, har ya shiga ɗakin da ya kama bai kula da ya yasar da abu ba, ruwa ya wasta sannan ya yi ordern coffee aka kawo masa.
Yana kurɓan coffee nasa yana ayyukan sa a waya sai ya ji knocking.

Wata haɗaɗɗiyar mota ne ta shigo hotel ɗin da mugun gudu, ana gama parking aka buɗe duka qofofin kusan a tare, wasu ƴammataye ne suka fito guda uku sai gefen da yake na driver ne kawai a buɗe ba'a fito ba, ɗayar da ta fito daga gefen zaman driver ne ta ce "reeysah me kike kallo ne ba zaki fito mu tafi ba?
Wacce aka qira da reeysah ce ta jefo qafafuwanta waje, wasu arnun hill's ne a qafanta wanda daga takalmin qafan zaka tabbatar mai qafan ta haɗu, a hankali ta qarisa fitowa, sanye take da riga da wando iri ɗaya wanda ake qira da Up&down wanda a qalla kuɗin kayan zai kai 300k, inda take kallo duk ƴammatan suka bi da kallo, ganin guy ɗin sai duk suka shagala da kallonsa suma, ɗayar ce ta ce "reeysah amma guy ɗin nan ya haɗu fa".
"Hmmn! Zee ba kaɗan ba, ai ni naga mijin aure dama excellency ya fara magana miji kamun ya bar villah" tana gama magana ta taka a hankali ta ɗau abinda ya faɗi a hannun guy ɗin da ta gani sannan ta bi bayansa, sai da ta ga ɗakin da ya shiga sannan ta juyo wajan freind's nata tana faɗin "let's go guy's".
Ɗakin da suka kama suka shiga sai da suka huta sannan ta ɗau key ɗin ta fito bayan tawa qawayen nata sai ta dawo, tana isa qofan tayi knocking.

Tashuwa yayi ya buɗe dan duk a tunaninsa ko waiter ne yazo amsan cup na coffee ɗin, kallo ɗaya ya mata ya ce "lafiya?
Cike da qwarqwasa ta ce "zan iya shigowa?
Ba tare da DMD ya ce komai ba ya juya ya shige ciki sai ta biyo bayansa, zama tayi a ɗaya daga kujerun palourn tana gaishesa cikin harshen turanci, har ta yi ta gama bai ce mata ko qala ba kuma bai kalleta ba, gajiya tayi ta ciro car key nasa ta ce "am dama key na motanka ka yasar shine nace bara na kawo maka".
Hankalinsa da idanuwansa na kan waya ya ce "okay thanks! You can kept it".
Yana gama faɗan haka ya juya ya shige bedroom.
Reeysah kaman za tayi kuka ta ajiye ta tashi ta fice, amma tana ayyana wa a ranta itafa taga mijin aure, ko da ta koma cewa qawayenta tayi ya amshi soyayyanta.
Fareesah(reeysah) kyakkyawan budurwa wacce a qallah za ta kau shekara 26 da haihuwa, yarinya ta uku ga present president na Nigeria, wacce tayi karatu a America bata jima da dawowa ba aka fara mata maganan aure, da farko ta nuna taurin kai tana yawon ajenan-ajenan da qawayenta sakamakon yarinyace da bata ji an sangartata, yayyunta biyu duka sun yi aure sai qannenta maza biyu da suke karatu a outside, yaran manya ministoci da 'yan kasuwa na sonta amma ba maganan aure a gabanta, amma ganin DMD sai taji za tayi auren.
Yana jin qaran fitan ta ya ja guntun tsaki, ya rage hasken wutan ɗakin ya kwanta.
Washegari da sassafe ya shirya ya fice gaba-ɗaya a hotel ɗin, reeysah kuwa sai da rana ta fito gastal-gastal suka tashi da qawayenta, sunje ɗakin DMD suka tarar baya nan, kaman za tayi kuka haka suka tafi tana faɗin sai ta nemo shi dan ita ba ta da miji a duniya bayan shi, ko da kuɗi ko da mulki sai ta aure.
(😂 Jama'a kuwa fareesah fatan nasara).

Bayan sun qara kwana biyu suka tattara suka koma Gombe, bayan sun ajiye Hajja a Ashaka.
Maganan aure da aka yi kuma daga Daddy har Abiy ba wanda ya ce wa yaran komai, dan Hajja jira take su haɗu duka ta ja musu kunne kar su kuma jawo mata wani abun.
Ammi zamanta take hankali kwance bata shiga tsabgan Aunty Amarya dan zuwa yanzu Ammi ta fahimce ta amma tabar hakan a mazaunin kishi ba wai munafurci ko kissa ba.

Sai da aka kammala hidiman komai aka buɗe shopping-mall sannan ya kamo hanyan dawowa Gombe, cike da gajiya ya shigo gidan, ba tare da yayi part na Ammi ba ya nufi ɓangaren da yake nasa, yana shiga qamshi ya doki hancinsa sashin staf-tsaf ko ina a gyare sai qamshi, ganin haka sai ya murmusa yana faɗin "Allah barmana ke Ammi" ya shige ɗakin nan muna a a gyare har toilet, ruwa ya wasta ya ɗauro alwala yayi Sallah sannan ya bi lafiyea gado ya kwanta.

Fareesah tayi iya nemanta amma ba alama ko guda da zata samu daman samun ko da phone number na DMD balle sunansa, masu hotel ba abinda suka sani akansa sannan bata da labarin shopping-mall da ya buɗe, duk da haka dai kan nemansa take yi taqi haqura.

Hutu na qarewa suka tattara suka koma Canada, inda suke rayuwa cikin kwanciyan hankali sai Ammi kawai da aka barta da sintiri yau tana Nigeria gobe tana Canada, domin Abiy zuwa yanzu sai dai ya dinga leqosu lokaci-lokaci yakan shafe wata guda bai je ba, Ammi hakan dai bai dameta ba domin ita tana zuwa tayi sati guda ta koma in tayi sati biyu a Canada ta qara zuwa tayi sati guda ta koma.
Jay yana aiki a FMC Gombe sai Afreen da ke final-year semester a GSU tana karantan computer science, Afrah kuwa tana gaban Hajja tana secondary school.


Fitowa DMD yayi da shirin tafiya office amma sai ganin Ammi yayi ta fito da nata shirin ita ma, gaisheta yayi yana faɗin "Ammi sai ina?
Tana murmushi ta ce "sai gidan mijina, tunda ku kunqi gidan ubanku".
Taɓe baki yayi yana gyara zaman suit nasa ya ce "adawo lafiya a gaishesu, and please Ammi inkin samu lokaci kamun ki dawo ki dubamun Companyn Jigawa".
"Darling yai shekara nawa rabonka da Nigeria? In banyi qarya ba kafi 2 year's ba kaje ba, tun last da muka je tare muka je Maiduguri kaqi ka koma, ina ji dai anfita harkanka akan batun auren tunda dama shi ne damuwarka, ka fita idona inba haka ba zan mugun saɓa maka, maza-maza nan da Friday anabawa su sweerie hutu ka tabbatar kun biyo ni dan wannan karon zamu kwana biyu acan tunda hutun su sweedy da yawa".
"Ammi karki manta da zuwa jigawan please" iya abinda ya faɗa kenan yayi hanyan fita waje.
Girgiza kai kawai Ammi tayi tawa yaran nata bankwana sai sun zo, sweetie har da kukanta za ta bi Ammi ai saura two days a bayar da hutu inyaso sweerie ta karɓo musu hutun, da kuka ta bi Ammi har compound na gidan, kallon da DMD ya mata shi ya sanyata haɗiye kukan, Ammi ta shiga motan da ya shiga suka zauna tare a baya driver yaja su sweedy suna ɗaga mata hannu har motan ya ɓace sannan suka juya suka koma ciki.

"Darling sam-sam bana son irin wannan halin da kakeyi bai kamata ba".
Kaman zai yi kuka ya ce "Ammi nifa bansan dalili ba gaskiya banson Nigeria, amma kiyi haquri zan je wani hutun, wannan karon in aka basu hutu dai zasu taho ko Abiy ya zo ya tafi da su".
"Hmm! Ni Maimoon me zan ce

Please Login or Register in order to submit comment