Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji Abiy ya saki Ammi dan haka ta baje, washegari aka koma sabon gida.
Aunty Amarya taji daɗin sabon gida dan komai yayi sai dai baqin ciki take yi duk tulin wannan dukiya bata da ko kakkauran kashi balle ɗa ɗaya mai gada, nan ta fara damuwa ganin koma mene Ammi ce da riba.
Ammi na fita ba ta nufi Indiya ba dan kar ta ɗagawa Dr Mufaddal mahaifinta hankali, sai ta nufi Canada.
Su sweedy kaman daga sama suka ga Ammi, sunji daɗi amma rashin ganin sweetie abun ya dame su, Darling dai ya mastawa Ammi sai da ta faɗa masa komai yanda aka yi nan ya dinga farinciki Abiy ya sake Ammi sun huta, washegari ya shirya ya ɗauko sweetie ko ta kan Abiy bai bi ba.
Ammi taji daɗin ganin autar tata nan tayi murna ta rungumi yaranta suna rayuwa hankali kwance, bata kai wata guda da dawowa ba kawai suka ga Abiy wai ya zo su koma da Ammi da yaransa, ita dai Ammi ko sauraransa ba ta yi ba amma yaran kam abu da uba da 'ya'ya sai Allah sunji daɗin ganin mahaifinsu, har Abiy ya tafi Ammi taqi kula shi.
Nan fa Abiy ya mai da Canada wajan sintirin sa duk bayan kwana biyu sai yazo kuma sai yayi kwana 2 ya koma, amma duk da haka Ammi ko kulasa ba ta yi duk da duk ranar da ya tafi sai ta ci kukanta a ɓoye, Allah ya gani tana qaunar mijinta kuma tasan shi ma yana sonta, a gefen Darling duk abunnan da ke faruwa yana gani kawai yaqi shiga harkan Abiy ne dan gudun ɓacin rana, kuma bai wa Ammi magana ba tunda yasan sun riga sun rabu to iya ƙoƙarin sa zai yi kar ma a mayar da auren.

Ko da mummy taji labarin nan ba ƙaramin mamaki tayi ba duk da tasan kaɗan kenan daga sharrin Aunty Amarya, kuma dama su kanuri zama da su a kishiya sai in Allah ya staga dan wasunsu basa zama banza, Daddy ma yayi bala'in shi sannan ya ce da Ammi kar ta yadda ta kula Abiy ta barsa ya gama haukansa tunda da girmansa yake biyewa munafurcin mace.
Hajja dai labari bai kai kunnenta ba, a lokacin kuma jay ya fara aikin asibitin sa, Afreen da suka samu huta ta dage sai ta je Canada dan haka ba wanda aya hanata tayi tafiyanta tunda kowa yasan soyayyan dake tsakanin Ammi da Afreen da yake Afreen takwarar Ammi ce.
Abiy fa tun yana ɗaukan abu wasa har ya zama gaske, Ammi taqi ba shi dama ya mata bayani balle yayi yunqurin bata umarni ta yarda ta bi, ɓangaren Aunty Amarya ba abinda ya dameta tana farantawa Abiy tana rayuwanta qalau, dan babbar damuwarta dama Ammi da yaranta ne kuma ga shi cikin ruwan sanyi sun tafi sun bar mata gidan.

Abiy Darling ya sama akan yawa Ammi magana ta sauraresa duk abun bai kai haka ba, amma ko kallon kirki Darling bai yiwa Abiy ba domin duk sanda ya ɗaga ido ya kalli Abiy ba abinda ke faɗo masa sai marin da ya yiwa Amminsa da kuma wulaqanci wai a sunan soyayya.

Wasa-gaske Ammi watanta 2 a Canada kuma Abiy bai bar sintiri ba, sannan ita kuma bata kulashi ba, ganin abun yaqi ci kuma yaqi cinye wa sai Abiy ya niqa garinsa ya kama hanyar India domin yasan in ba tanan ya biyo ba ba zata sauraresa ba.
Abinda Abiy bai sani ba kuwa ashe Aunty Amarya ta gama shafawa mutanen Maiduguri kan cewa ya saki Ammi, suna can suna ta farinciki har da ita ba wanda yasan sintirin da Abiy yake na ganin Ammi ta dawo gare sa.


INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله


LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member's ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR'S ANNIVERSARY

FAN'S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.


💋💋 امى بتولة💋

Wannan page naku ne masu daraja

Surayyatou (habibtyna)

Ummin karima

Amina khamil

Deejer nata'ala

Maman abdusamad (kakata jidda)

Ƙawata Salima(Maman unborn)

Ummu muhammad

𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 43_44


Abiy na sauqa a India ya nufi gidan Dr Mufaddal, cikin Sa'a kuwa ya same sa a gida dan dawowansa daga ganin likita kenan.
Bayan Dr Mufaddal ya ma Abiy iso sun zauna sun gaisa sai ya numfasa yana magana ganin yanayin Abiy da ke nuni da akwai mastala, da hausansa da ba sosai ya nuna ba ya ce "Mustapha ince dai Maimoon ba wani laifin ta maka ba?
Cin girmamawa Abiy ya ce "Papa ba wani laifi ta mun ba illa iyaka nine mai laifi, Maimoon na iya ƙoƙarinta amma abubuwan sai a hankali, to kwana biyun nan nayi tafiya ina dawowa na tarar gaba-ɗaya yara sun tafi Canada ba tare da izini na ba, abun ya ɓata min rai har ya kai mun samu saɓani da Maimuna har dai na bata takarda to sai ta tafi Canada,to bayan an kwana biyu naje akan tayi haquri mu dawo amma taqi saurara na kuma shi ma yaron yaqi taya ni bata haƙuri, dan Allah a bata haƙuri ta dawo Papa dan na gane laifi na kuma Insha Allah ba za'a kuma ba".
Murmushinsu na manya Dr Mufaddal yayi kawai ya girgiza kai dan mamaki yake har yanzu daga Maimoon har Mustapha kaman akwai yaranta a kansu, duban Abiy yayi ya ce "Asshhha! Asshhha! Amma wannan abu sam bai yi daɗi ba, Mustapha da girmanka sai ka biyewa Maimoon? Kun girma fa zuwa yanzu kuma kun tara yara bai kamata abinda ba kuyi a yaranta ba kuyi shi da girmanku da yaranku wanda na tabbata da Mufaddal yayi aure to da kunyi jika kuma, zan mata faɗa Insha Allah za ta koma amma fatan sakin dai auren bai ƙare ba? Kuma a dinga haquri da iyalai, domin su mata da kake gani 'yan lallami ne da kuma rarràshi, mulki ne da su ba kaɗan ba, mu yi haquri mastayinmu na shugabanni samansu mu zauna lafiya domin ƙwaƙwalwan mace wani lokacin sai a hankali, a dinga haquri Mustapha, yaro kuma ku cigaba da masa addu'a Insha Allah zai gyaru duk yarinta ke damun Mufaddal daga zaran aka ce yau ya ajiye mata to komai zai daina ku dinga haquri".
Abiy cikin jin daɗin maganan Dr Mufaddal da kuma mamaki wanda ya gauraye da jin daɗin ya faɗa duniyar tunanin "saki aure bai ƙare ba kuma?" Cikin mamakin abinda kusan kowa ke ɗaukan barin maimuna gidan ya dinga jujjuyan maganan Dr Mufaddal har sai da ya qira sunan sa kamun ya dawo daga duniyan tunanin yana faɗin "Papa ba wani sakin da ya shiga stakanina da Maimuna, bansani ba ko ta ɗauka a sakin ne amma ni ba haka na rubuta a takardan ba, kuma ina ta qoqarin bata haquri na fahimtar da ita amma taqi saurarana".
Dr Mufaddal jinjina kai yayi kamun ya ce "to Masha Allah! Allah kiyaye na gaba ya ƙara muku haquri, Allah albarkaci zuria'anku, in Allah ya yarda za ta koma karka sa damuwan komai, irin tunanin matan kenan, kaga bata buɗe takarda ta gani ba ta hau dokin fushi, su mata guntun zuciya gare su, Allah muku albarka duka".
Da "Ameen" Abiy ya amsa kamun suka ɗan tattauna daga bisani yawa Dr Mufaddal sallama, ya kamo hanyan Nigeria da nufin bayan kwana biyu zai koma Canada.

Ammi da yaranta zaune a babban palourn gidan nasu, Darling ne ya shigo sanye da suit wanda ke nuni daga office yake, zama yayi a kujeran da Ammi ke zaune mai ɗaukan mutum uku, kansa ya kwantar a qafan Ammi yana lumshe ido, sweedy ganin haka sai ta taso daga inda take zaune ta zo ta cire masa takalman sa sau-ciki tana magana cikin harshen Indianci "Darling sannu da dawowa".
Gyaɗa kai kawai yayi bai ce uffan ba, Ammi ganin haka sai ta murmusa tana cike da mamakin halin wa Darling ya ɗauko dan dai iya saninta wasu halayyan nasa sun ɗarawa na mahaifinsa nesa ba kusa ba.. muryansa ne ya kaste mata zancen zuci da take saqawa.
Da Indianci ya ce "Ammi ya naga kina ramewa ko kewan Abiy ne?
Sanin halin sa sai ta murmusa cikin zolaya ta ce "to dama ta ya ba zanyi kewan mijina ba, kunbi kun kanainaye masa mata, ai na kusa komawa sai kuyi zamanku abinku amma nikam gidan mijina zan koma".
Kwaɓe baki yayi kaman mace ya ce "Ammi cin fiska ba kyau, ai munfi Abiy buƙatan zama tare da ke".
Murmushin ta kuma yi wanda ke nuni da yaro man kaza, tana faɗin "aikam dole ka ce haka tunda kai ka kasa yin matan, to ba da Maimoon ba ni gidan mijina ma zan koma gwanda kasan na yi tun wuri da qannenka tunda kai kaje ka ɗauko su duka, dan haka in na tashi komawa ma daga ni dai jakan kayana zan koma, in zaka nemo mata ta riqe maka qanne in kuma za ka mayar da su ka haɗu da Abiynku ba ruwa na, in kuma ka masta na koma da su to fa sai dai a koma da kai kaima kabar Canada kenan".
Lumshe ido ya kuma yi bai ce uffan ba duk da kasancewar yana da abun faɗan, a haka ma dan yana tare da Amminsa ce domin in ba ita ba ba shi da lokacin dogon zance balle shagwaɓa ko dariya.
"Baban Amminsa" ta qira sa a yanayi na magana mai muhimmanci take so suyi.
Buɗe kyawawan idanuwansa yayi da suka rine zuwa ja, a hankali kaman zai yi kuka ya ce "na'am Ammina".
Kallonsa tayi ganin yanayin fiskansa sai ta girgiza kai kawai ta ce "baban Amminsa me mastalanka da maganan aure? In wani abun na damunka ko in akwai wani mastalan ka faɗamun ni mahaifiyarka ce bayan ni ba ka da wacce ta fini inka cire mahaifinka da matar da za ka aura, me mastalanka da kake qin aure?
Qannensa ya kalla da idanuwan nasa da suka rine, ganin kallon nasa duk sai suka miqe suka haura sama, mai da idonsa yayi ya rufe kamun a hankali ya buɗe baki ya ce "Ammi lafiyana qalau".
"Darling lafiyanka qalau, to ko matan ne ka rasa? Naga dai alhamdulillahi Allah ya horewa yarona kyau, ilimi, kuɗi, nasaba, duk wani abu da mace ke buƙata wajan mijin aure kana da shi dan ko halinka sai wanda bai fahimceka ba ne zai yi ƙorafi akan hakan amma Masha Allah! Kana da haquri, kau da kai, ko kayi fushi kana sauqowa da wuri, rashin magana ma na sani inhar ka samu mace to tabbas a gabanta wannan stohon zance ne dan sai abinda ta buqata za ka faɗa surutu sai ta ce kanari, please son kar na mutu banga jikoki na ba" ta qarisa maganan tana kamo hannun sa.
Jikinsa ne yayi sanyi amma duk da haka shi ya sani ba shi da yanda zai yi, ko kaɗan baya jin buqatan mace ko kaɗan baya ganin mace yaga ta burge sa, shi in mace tayi ƙoƙarin taɓasa ma ji yake kaman ya kashe kansa ko kaɗan mace bata gabansa baison maganan mata, shi kansa yayi gwaji yafi a irga amma lafiyansa qalau result ke nunawa amma ko kaɗan baya jin buqatan mace balle yayi kwaɗayin aure, wahalallen numfashi ya sauqe tare da furzar da iska mai zafi da huci ya miqe ya zauna tare da jingina kansa a jikin kujeran da suke zaune, idanuwansa a lumshe dan ya rasa amsan da zai baiwa Amminsa, qarshe miqewa yayi ba tare da ya ce qala ba ya nufi step's da zai sada shi da ɗakin sa, Ammi kuwa bayansa ta bi da kallo tana murmushi kawai, tana faɗin "Ni Maimoon banda ta cewa sai dai fatan alkairi da binku da addu'a, Allah ya sanya jinkirin na alkairi ne kuma Allah qaddara min ganin jikoki na, Allah shiryamun ku ya muku albarka, qannenka ma Allah basu mazaje na gari da ma duk sauran yara da basu da aure, Allah stare mana ku ya stare mana mutuncinku" murmushin ta kuma yi a zuciyarta tana tuna mutanen Maiduguri da dokan su, qarshe dai itama miqewa tayi ta haura saman tana jinta cikin kewan Abiy sosai.

Yana shigewa haɗaɗɗen part nasa, direct akan kujera ya wa kansa masauqi, kwanciya yayi yana riqe kansa ya rasa me ke damunsa, qira ne ya shigo wayansa, ganin layin Jay sai yaja guntun staki ya kaste qiran dan in ya ɗauka to surutun Jay sai ya sanya shi zazzaɓi ya sani.

Ammi da haurawanta sama kenan wayanta ya ɗau kara, ganin layin Jay sai ta ɗauka tana faɗin "my boy ka qira Ammi bata kusa a mata afuwa ina can ina fama da ɗan uwanka da rashin jinsa".
Murmushi Jay yayi a ɗaya ɓangaren ya ce "Ammi sai haquri da mu, dana Afreen ce sun kusa isowa wai za ta taho Hutu wajanki".
"Ah! My boy shi ne sai yanzu za ka sanar min? Shikkenan kaste waya ba naje driver ya kai sweedy ta ɗauko ta".
Kashe wayan Ammi tayi, ta laluɓo Numbern Sweedy, tana ɗauka ta ce "maza-maza ki shirya driver ya kai ki airport Afreen na hanya" tana gama faɗa ta kaste qiran ta wuce toilet, alwala ta ɗauro ta fito, tana ɗaga wayan ta ga misscall na Papa amma sai ta bari sai tayi sallah ta qirasa.

Sweedy shiryawa tayi cikin riga da wando ta ɗauko top ta ɗaura da hulanta, ta ɗau wayan ta ta fice.
Driver ta samu ta yiwa magana, ya ɗau mota suka nufi airport, suna isa ba jimawa jirgin su Afreen yayi landing, cikin farin ciki suka rungume juna suka shige mota driver ya kawo su gida.
Afreen tun da ta shigo palourn ta Lumshe ido, jin ƙamshin abun qaunanta, sai ta bi step's da zai sadaka da part nasa ta kallo tana jin farinciki mara misaltuwa, Murmushin da take yi har sweedy sai da ta ankare sai kawai ta girgiza kai a zuciyar ta tana faɗin "Allah ya sa Darling ya aure ki dear".
Sama suka haura har ɗakin Ammi, ba qaramin daɗin ganin Afreen Ammi ta ji ba nan ta rungumeta kaman za ta maidata ciki, har ta manta da misscall na Dr Mufaddal.
Da dare duk suna zaune a dinning a sashin su suna cin abinci, Ammice ta ce "wai nikam yau rashin cin abincin ya mosta wa yayanku ne bangansa ba?
"Ammi ai Darling kam ni rasa da ne yake rayuwa a cikin sa nake, ba ya cin abinci fa, gaskiya matar Darling aiki ya ganta sai ta dinga feeding nasa ko ɗura ma" cewar sweedy da ke saving na kanta.
Murmushi Ammi ta yi ta ce "to dai Karki sake ya jiki ba ruwana, yanzu ku kai masa wani abun sashin sa ko".
Sweedy ta maida kallonta kan Afreen ta ce "dear ki kai wa Darling abinci".
Ammi buɗe baki tayi ta ce "Muhseena ashe ba ki da kirki? Yaushe daughter ta huta da zata kai abinci, maza tashi ki kai masa yanzun nan kamun na saɓa miki".
Sweedy tura baki ta yi za tayi magana sai Afreen ta kasteta ta miqe ta fara jera abincin dan tasan mai yake son ci da dare ko da ya je Nigeria, kuma maganan sweedy ya mata daɗi za ta samu ta ga "peace of mind" sunan da ta sanya masa.
Ammi ganin haka sai bata ce uffan ba ta ci gaba da cin abincinta, Afreen haɗa komai ta yi ta ɗauka ta fice a palourn, a hankali take haura step's ɗin har ta isa bakin qofan, knocking tayi shiru ba'a amsa ba, jin shiru sai ta tura qofan ta shiga.
Wani irin lumshe ido tayi wanda tunanin da take yi ya sanya idanuwanta cika da qwallah, a hankali ta furta "Allah ka nunamin ranan da za'a kawo ni wannan sashin a matsayin matar Darling Mufaddal" mostin da ta ji ne ya kaste maganan nata tayi saurin saita nustuwarta.

Tun da ya kaste qiran shi ne bai mosta ba sai da ya ji MuslimApps da ke wayar sa na qiran sallah sannan ya miqe ya haura sama inda ɗakunan sa kenan, alwala yayi ya gabatar da sallahn sa sannan ya cire kayan jikinsa ya shige toilet dan ya watsa ruwa , ko da ya shiga jacuzzi ya sakarwa kansa shower sai da ya kwashe kusan awa 3 kamun ya fito dan bacci ne ma ya fara kamasa a cikin abun wankan jin ruwan ɗumi da ya sanya masa nistuwa.
Yana kwance daga shi sai towel a qugun sa ya ji kaman mosti sai ya nemi short ya sanya ya saka 3quater sannan ya nufo sauqowa palourn nasa na qasa dan duk zatonsa su Sweedy ne shiyasa bai damu da sanya riga ba.
Qarasowa palourn yayi ba tare da ya kalli wacce ke zaune ba, ya zauna a kujera mai ɗaukan mutum guda yana faɗin "empty tea" da harshen Indianci.
Afreen da tun isowansa palourn duk wani laƙa na jikinta ta neme shi ta rasa, faɗi take a zuciyanta "ya subhanallah!! Allah ka mallaka mun wannan haɗaɗɗen bawan naka da ko shi ya stara kansa ba zai kai haka haɗuwa ba.." maganan nata ne ya kaste jin daddaɗan sautin sa na magana da Indianci ita kuma ga shi ba ji take yi ba, ɗan yastine fiska ta yi kamun a hankali ta furta "peace of mind banji ba".
Da mamaki DMD ya juyo yana kallon wacce ya ji muryanta, kallo ɗaya ya mata ya lumshe ido a ransa ya furta "yarinya ƙarama sai iyayi" dan ya ji sunan da ta qira sa da shi.
"Shayi empty" ya maimaita a taqaice.
Haɗa masa tayi ta miqa masa ya karɓa yana kurɓa idanuwansa na kan TV, ita kuma ta mai da shi TVn ta har sai da yayi kaman zai qware sannan ta dawo hayyacinta ta maida ido kan TV itama.
"Yaushe kika zo" kaman daga sama ta ji muryan sa yana tambayanta, sai kuma ta juyo ta kalli kaman ba shi yayi magana ba, murmushi tayi na jin daɗi sannan cikin kwantar da murya ta ce "ɗazu ne, big bro na gaisheka, mummy na gaisheka, Daddy na gaisheka".
Jin yayi shiru bai ce komai ba ta ɗago ta kallesa, ta ga kaman dai ba da shi take maganan ba, kaman za tayi kuka haka ta qara zuba masa idanuwa.
Cikin gajiya da kallon da take masa ya ce "za ki iya tafiya" yana gama magana ya miqe ya haura sama.
Tattare cup's ɗin tayi sannan ta miqe ta fito a sashin tana jin farinciki abinta ta koma sashin su Ammi.

Yana haurawa sama ya shirya sama-sama ya ɗau makullin mota ya sauqo, ganin duk basa palourn ya ciro wayansa ya qira layin Ammi yana faɗin "Ammi na fita sai na dawo".
"A dawo lafiya Darling".
Qitt ya kashe wayan ya fita, driver na ganinsa ya nufi ɗauko mota amma sai ya dakatar da shi, ya shiga wata arniyar mota qirar 2020 ya ja ya fice a gidan.

Washegari da wuri Ammi ta sanya su suka shirya breakfast, sweedy ta tura dan ta qira Darling ya fito yayi breakfast, amma ta dubo baya sashinsa wanda da alama bai ma kwana a gidan ba, mamaki Ammi ta dinga yi akan inda yaje tunda tasan ba halinsa bane yin dare a waje balle kwana a waje, amma sai ta share tana addu'an Allah yasa lafiya.
Bayan sun gama breakfast, masu aiki suka tattare wajan, Ammi da yaranta kuma duk suka koma bacci, sai Afreen kawai da ke dakon shigowan Darling.

Tuqi yake da mugun gudu duk da kasancewar safiya ce amma burinsa ya isa gida akan lokaci dan yasan Ammi nacan ta damu ya kwana a waje bai sanar mata ba.
Dai-dai lokacin da ya iso bakin gate ɗin gidan yayi dai-dai da isowan Dr Mufaddal shima, da mamaki Darling ke kallon sa yana murmushin sa mai stada, dan a rayuwansa bayan Ammi da 'yan uwansa in akwai wanda yake mugun qauna da kuma iya masa dariya to kakansa ne.
Yana gama parking ya fito ya rungumi Dr Mufaddal ɗin yana magana da Indianci "landlord ka zo amsan kuɗin haya ne irin wannan sammakon" ya faɗa yana kan murmushin.
Dr Mufaddal girgiza kai yayi yana sansanyar dariya cikin qaunan takwaran nasa kuma jikansa namiji kawai ya ce "in ba'a biya ba kuma a bar mini gida yanzun nan".
Suna murmushi duka suka nufi shiga cikin palourn, mostin qafan mutum da suka jiyo ana sauqowa daga kan step's ɗin sai duk suka kai kallonsu wajan da tunanin ko Ammi ce, ganin mai sauqowa Darling kau da kai yayi yana faɗin "fitinanniyar yarinya".
Dr Mufaddal na murmushi yayi magana da turanci "ah! Lallai na iya zuwa a dai-dai, ga Amarya ga ango an haɗu sai a ɗaura kawai mu koma India in kuma ɗan-kwali ya ja hula sai ku koma Nigeria" ya faɗa yana darawa, Afreen da ta qariso palourn tana murmushi itama ta ce "stoho mai ran qarfe sannu da zuwa, amma dai ni kamun stufa sabon jini nake so" ta faɗa tana satan kallon Darling da ya kusa shigewa sashinsa dan bai san ma suna yi ba.
Afreen ruwan sha ta kawo wa Dr Mufaddal da kayan kari ta ce "Angona bari na qira maka Amminmu" ta juya ta nufi sama wajan Ammi.
Tana isa shiga palourn sama dai-dai Ammi na fitowa a ɗakinta tana faɗin "daughter hayaniyan me nake ji, ko Darling ya dawo ne?
"Eh Ammi, ya dawo amma tare da stoho mai ran ƙarfe na gansu, yana palourn ƙasa ma na ce masa ne bara na qira ki".
Ammi da sai yanzu ta tuno misscall's na Papanta ai wara ido tayi tana faɗin "Papa dai?
Afreen na murmushi ta ce "shi ɗin dai Amminmu".
Kamun ta ida rufe baki Ammi har ta fice a palourn, da sallama ta shiga palourn qasan tana faɗin "sannu da zuwa Papa".
Dr Mufaddal yana murmushi ya ce "yauwa Maimoon".
Qarisowa tayi ta zauna gefensa tana gaishe sa.

Darling yana haurawa sama, ya wasta ruwa sannan ya sanya kayan shan iska da suka yi matuqar ansan sa, palourn sa na qasa ya dawo sannan ya shige kitchen nasa, sama-sama ya samawa kansa abinda zai sanya a cikinsa sannan ya gyara komai ya fito ya kulle qofan ya nufi wajan su Ammi.
Ammi na kallonsa ta fara murmushi dan kullum gani take yaron nata na qara kyau "baban Amminsa sai yanzu aka shigo?
Dr Mufaddal na murmushi ya ce "ai Maimoon yaronki ya renani nima, halin 'yan adam yake nuna min wai nazo amsan kuɗin haya ne da sassafe, ina laifi nazo naga lafiyansa tunda shi baya tuna kowa".
Darling na Murmusawa ya zauna gefen Ammi ya gaisheta sannan ya fidda wayansa yana dannawa.
Dr Mufaddal girgiza kai yayi kawai a ransa yana faɗin "sarautan da bamu da ita ta mosta"🤣.
Ammi ne ta dubesa ta ce "yau ba

Please Login or Register in order to submit comment