Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma school ɗin da kansa, driver ya juya su kuma suka shige gidan malam ba wasa na mamakin rashin nauyin Afrah duk da yarinya ce amma ko kaɗan kaman an ɗaga papper.
Da sallama suka shiga palourn sweetie da ta riga su taba faɗin "Hajja ki fito ba kin takurawa Aunty masoyiya taje school ba bayan ta ce miki tayi latti ga shi sun dake ta sun sa ta daina mosti" sai kawai ta fashe da kuka tana gana maganan.
Afreen da fitowanta kenan daga ɗaki tana waya da mummy tana faɗin "habibty har yanzu fa 12 ya kusa ana neman azahar bai zo ba, nikam zan taho da kai na kawai".
Ganin sweetie na kuka sai tawa mummy sallama ta kashe wayan tana tambayan sweetie lafiya? Bata ida rufe baki ba malam ba wasa ya shigo da Afrah a hannunsa, ai wajansa tayi da sauri tana tambayan me ya samu Afrah?
Malam ba wasa ajiyeta yayi akan 3seater bai ce uffan ba ya mai da kallonsa kan sweetie ya ce "qiramun Hajja".
Hajja da ke fitowa a ɗaki ta ce "ganinan me aka kawo mun ɗan nan, ke kuma sakalatun kukan me kike wa ya dawo dake daga makarantar?" Qarisa shigowa palourn Hajja ta yi bata ma lura da Afrah da aka kwantar ba balle Innai da ke raɓe-raɓe ba wanda yasan da ita a palourn sai malam ba wasa dan ko sweetie ta manta akan sun taho da wata ƙawar Afrah.
Malam ba wasa gaishe da Hajja yayi yana faɗin "ayi haquri Hajja wallahi ba'a san da tana da wata laluran ba shiyasa aka dake ta".
Hajja da sai yanzu ta kula da Afrah ai miqewa tayi sai ganinta aka yi gaban Afrah tana faɗin "Ni Fatu na shiga uku wai dukan lattin aka miki da gaske, yau na ga ta kaina na ɗauka wasa kike ba kiyi latti ba, dan Allah takwara ta tashi kinji" Hajja ta faɗa har da guntun ƙwallanta.
Malam ba wasa dai ya rasa yanda zai yi dan shi kunyan Hajja ma yaji an daka mata jikarta, Hajja kuwa masifa ta dinga yi kaman zata ari baki, har su sweerie suka fito a ɗaki suma, ita sweedy har da ƙwallanta, sweerie kuwa faɗi take, "ai wallahi da a Canada muke da tuni yanzu ankai malamin da ya bugi Afrahty children's right association an bi mata haqqinta, mastalana da mutanen Nigeria kenan ba abinda suka iya sai dukan yara, mu ko yaro laifi yayi baka isa ka hukuntasa mugun duka har ya suma ba tuni ma'aikata suka zo suka tafi da kai ko kai ne mamansa ko babansa ba ruwansu, shiyasa AL'ADAN su ke burge ni ba kaman Nigeria ba sun san yanda ake bi da yara su dinga jin magana ba tare da duka ba."
Shi dai malam ba wasa rasa yanda zai yi yayi, cikin qarfin hali ya ce, "Hajja ko akwai abinda ake mata in haka ta faru?"
Hajja ta ce, "ɗan nan ba wani abu face a kaita asibiti tayi jinyan kusan mako guda, kai Allah mun tuba Allah ka yaye mana masifan da ƴan adam ke jawomana."
Jin abinda Hajja ta faɗa sai ya ciro wayansa ya qira Jay suka yi magana ya faɗa masa suna hanya kar su kai ta asibiti zai taho da duk abinda ya kamata, bayan sun yi sallama kenan ya faɗawa Hajja sai ta ce, "yanzu kai ma da nake yabon haka halinka yake? Biyewa jabiru za kayi kamun ya iso yarinya numfashi ya qarisa guduwa ko, to ban isa ba asibiti zamu kai ta".
Sai da ƙyar malam ba wasa ya lallaɓa Hajja suka zauna jiran zuwan su jay shima bai koma school ɗin ba ya zauna, zuwa yanzu malam ba-wasa ya manta da Innai kuma ga shi tana staye a rakuɓe duk abinda ake yi bata zauna ba dan ganin yanayin gidan nasu sai storo ya kamata ga shi tanajin masifan da Hajja ke yi duk da ta saba da ba Baabaa Mero amma sai taji storon kakan Afrah, malam ba wasa shiru ya zauna idonsa na kan TV sai su sweetie da suka zagaye Afrah suna mata fifita sun cire mata hijab ma zuwa yanzu.
Malam ba wasa juyawa yayi da niyan kallon direction na Afrah, ai sai idanunsa carab akan qirjinta da yake sun cire mata hijabi kuma Afrah dama tana da breast kawai ba manya har can bane ƴan dai-dai ne, saurin kawar da kai malam ba-wasa yayi yana maida idanuwansa kan TV.
Hajja dai sai azalzala mita take yi kaman ta jawo Jay.

DMD da ke driving ne ya ɗan kalli gefen da Jay ke zaune ya ce, "what's wrong with Afrah?"
Jay dafe kai yayi ya ce, "dude ai Afrah bansan ko wacce irin yarinya Habibty ta haifa ba, yarinya sai storon bulala ga rashin ji, ace ana taɓaki da bulala kaman ansa wuqa anyanka ki shikkenan kawai sai ki sandare, ai ina jiyawa me auren Afrah wataqila ma ko sharholiya zai yi sai ta sume masa".
DMD jin maganan Jay ya koma shirme sai ya ja guntun staki, "mtsww! Ɗan iska qanwar bayanka ma sai kayi maganan banza a kanta" yana gama faɗa ya qara gudun mota dan su isa da wuri.
Suna shigowa Ashaka suka staya Jay ya sayi wasu abubuwa a pharmacy sannan suka wuce gidan Hajja, sai da yayi parking mai kyau sannan suka fito da sallama suka tura qofan palourn suka shige, Jay da ke gaba yana kallon hanya direct kujeran da Afrah ta ke kwance a kai ya wuce yana cewa, "Autan habibty Allah yaye miki ragwanta da storo".
DMD da ya fidda waya yana dannawa shi ma ya shigo palourn ba tare da ya ɗaga kansa ba yana tafiya sai ji kawai yayi ya buga karo da mutum, rai ɓace ya ɗago zai ga wacece a cikin yaran sai yaga wata kyakkyawan yarinya amma baƙuwa, ƙwafa yayi har zai wuce ya dawo yana kallonta jikinta na rawa ya ce "ke ƴar qauyen ina ce da ba za ki matsawa mutane a hanya ba, idiottttt!"
Duk da a hankali DMD yayi maganan amma maganan ne ya janyo hankalin duka yan palourn dan kallon shi da wa kuma ga shi ya staya a gabanta ya tare ta, malam ba wasa da sweetie sai yanzu suka tuna da Innai, ai da sauri malam ba-wasa ya ce, "afuwan DMD baƙuwace ƙawar Afrah ce."
Jay jin ance ƙawar Afrah da sauri ya leqa dan yaganta amma kuma DMD ya tare ta basa kallonta duka, sweetie ce taje tayi hugging nasa tana basa haquri sannan ya masta, Hajja dai ƙwafa tayi ganin yanawa yarinya qarama magana kuma ba dama a masa faɗa ya ɓata rai.
Innai hawaye take yi jikinta na rawa ga shi kuma ta gaji da tsayuwa dama qafanta da maciji ya sareta ciwo yake mata, Hajja tausayi yarinyar ta bata sai ta mata alama da taxo tana faɗin "qyale mugu wanda bai san qanne ba, zo abunki kyakkyawa kaman jikokina".
Maganan Hajja duk dariya ya basu wai kyakkyawa kaman jikokinta, Jay kam ai kuwa yana ɗaura ido akan Innai ya tabbatar ba ko kokonta ita Afrah ke nufi sai ya ji yarinyar ta burgesa, Afreen haka kawai taji kyawun Innai ya bata haushi sai ta banka mata harara tana faɗin "dukanki aka yi kike kuka da wa ya kawoki?
Hajja sheqeqe ta sheqawa Afreen kallon rashin mutunci ta ce, "tabbas ba ki da mutunci yarinyar nan, kinaga ta rako ƙawarta ba lafiya kina qara mata masifa bayan wanda shugaban masu baqin hali ya mata to wallahi ki fita harkana ko na saɓa miki, zo nan abinki ƙawar fatuna" cewar Hajja tana miqawa Innai hannu kaman wata ƴar goye.
Ita dai Innai duk storonsu ya bi ya cika ta, dan storon Hajjanma take yi jin irin masifanta kaman ya fi na Baabaa Mero, Sweedy dai duk bata ce komai ba tana zaune gefen Afrah, ita a duniya sai abu ya shafe ta take sanya baki halinta sak na DMD, sai dai itama Innai ta burgeta, sweerie kuwa ganin Innai kusan sa'arta ai taji itama ta samu ƙawa, kusa da ita ta masta ta kama hannunta tana faɗin "habibtynmu kibar kuka Afrahty za ta warke" ta ja hannunta har wajan Hajja sannan ta zaunar da ita gefen Hajja, ruwa taje ta kawo mata amma ta kasa sha har yanzu jikinta rawa yake tana hawaye, haushi da tsoron wanda ya mata faɗa ya cika ta ji take kaman ta tashi ta gudu, ganin yanayin Innai sai malam ba-wasa yaji ba daɗi DMD bai kyauta ba, Jay da ke qoqarin yiwa Afrah allura ne ya juyo suka haɗa ido da malam ba-wasa ya kyafta masa ido ɗaya suka yi magana da ido, sai duk suka danne dariyansu dan su kaɗai suka san me suka faɗa.
DMD guntun tsaki ya ja shi kaɗansa, Hajja kallonsa tayi tana faɗin "Allah ya yayemaka cutan da ke damunka, dan ko staka ma cuta ce staki garesa balle ɗan adam ɗan mutum".
DMD ɗaga Afrah yayi ya kai ta ɗakinta ya mata allura ya sanya mata ruwa, sai lokacin ta fara sauqe ajiyan zuciya a jere a jere kaman wacce tayi gudu ko ta sha kuka, sai da ya gama komai sannan ya rage mata qarfin ac ya ja qofan ya fita, ganin har azahar yayi sai su Jay suka fice dukansu uku suka tafi masallacin anguwan bayan sun yi alwala, Afreen harara ta wurgawa Innai da batasan tanayi ba ta wuce ɗaki ta banko ƙofa, sweedy dai zama tayi bata tashi ba dan tana fashin sallah, sweerie ce ta ja hannun Innai suka shiga ɗakinsu ta nuna mata toilet akan tayi alwala amma sai Innai ta kasa sai da sweerie ta gwada mata yanda ake amfani da komai sannan tayi alwalan ta tayar da sallahn azahar nata a zaune dan zuwa lokacin stayuwan da tayi har qafafuwanta sun fara kumbura bayan ciwo da suke mata, tana idarwa tayi addu'a sai ta zuba tagumi a wajan idanuwanta na kan Afrah, tuno stawan da DMD da ta raɗawa suna da mugu ya mata shi ya sanyata qara yin hawaye tana tunanin gida da Baabaanta, ko Baabaa Mero tsakanin su mitan da take mata amma ba'a mata stawa irin haka, sai kawai ta fashe da kuka, sweetie da ta shigo ɗakin zuwa tayi tana cewa, "ƙawar Aunty masoyiya me aka miki? Kiyi haquri da Darling nasan laifinsa ne yana tafiya yana danna waya amma ya miki faɗa kiyi haquri muma haka muke fama, amma inkuka saba za ki daina jin haushinsa dan yana da daɗin zama, yanzu kizo inji Hajja" ta faɗa tana kamo hannun Innai da ta miqe da qyar sakamakon qafafuwanta da suke mata mugun ciwo, da qyar take takawa har suka iso palourn kanta a qasa dan ita ko fiskan sa bata gani ba Lokacin da ya mata stawan, har wajan Hajja sweetie taja hannunta ta zauna tana ciccije baki ji take a gaban baabaanta take ta saki kuka dan ciwon da qafafuwan ke mata.
Daga malam ba wasa har Jay duk sun kula da yanayin tafiyanta, amma Hajja sai ta riga su magana ta ce, "ƙawar fatu na menene sunanki?"
A hankali Innai ta ce, "Innai".
Daga Jay har malam ba-wasa zaro ido suka yi jin wai sunanta Innai, DMD a zahirance hankalinsa na kan wayan amma jin ta ce Innai sai ya yastina fiska a ransa yana faɗin "village girl".
Hajja murmushi tayi ta ce, "suna mai daɗi, amma asalin sunanki fa?".
Nanma a yanayinta na sanyi ta furta "Maryama".
"Ah Masha Allah! Shiyasa fatu ta ishemu da zancenki ashe sunan uwatta gareki, yayi kyau! Ke Munawwara je ki kawo mata abinci ta ci".
Sweerie dinning ta wuce ta ɗibo mata rice and stew da yaji namomin zabbi dan abinda Hajja takeso kenan, kawowa Innai tayi Hajja ta karɓa ta ce, "Maryam sauqa qasa ki ci abinci ya shiga cikinki ko, kibar damuwan nan haka anjima kaɗan za kiga ta farfaɗo storo ne da ƙawar ta ki".
Innai da yunwa ke cinta amma girgiza kai tayi a hankali ta ce, "na qoshi kaka".
Hajja jin Innai ta qirata kaka sai ta ɓata fiska ta ce, "a lallai zamu ɓata inkika qara cemun kaka, yaushe nayi stufan da za'a qirani kaka, qirani Hajja yanda kowa ke cewa kamun mu ɓata, ke kuma Munawwara kai mata abincin ɗakinku ta ci acan naga kaman kunyanmu yake ji fulakon su na fulanin za tayi".
Sweerie abincin ta ɗauka ta kai mata ɗakinsu, Hajja ta ce, "tashi kije ki ci".
Innai a hankali ta miqe dan burinta tabar palourn kuma gidama take son tafiya duk da tafiso sai Afrah ta farka, a hankali take takawa qafan nata na rawa kaman za ta faɗi, Jay ne ya kasa haquri ya ce "Qanwata qafafuwan ciwo suke miki ne?" Bai ida haɗa leɓensa na qasa da na sama ba qafafuwan Innai suka kasa ɗaukan ta tayi ƙasa za ta faɗi, amma kamun ta qarisa Jay da malam ba wasa har rige-rigen tarota suke yi, aka ci sa'a ta faɗa jikkn Jay wanda ya ji kaman ta tabbata a jikinsa a haka, dukda zubinta na mutan qauye ne kuma gata Fulani wanda ba'a rabasu da qarnin nonon shanu, amma qamshi take yi, ɗaga ta yayi itama yayi hanyan ɗakin su Afrah da ita Hajja na mata sannu tana sawa Jay albarka, Malam ba-wasa dai fiskansa ba yabo ba fallasa shi kuma gogan naku duk da kansa na qasa amma tsaki ya ja yana furta "idiottttt".
Hajja haɓa kawai ta kama tana ganin ikon Allah wajan DMD sai ta ce, "kai Mufaddalu dama ba ka da tausayi ba ka da imani? Kaji kunya Wallahi mai halin kafuran da kawai".
Bai ko kalli Hajja ba ya miqe ya fice a palourn, ita kuwa Afreen kaman za tayi kuka haka ta tura baki tana hararan Hajja wai ta mata baqin-ciki tana ganin fiskan masoyinta, Hajja da ta kalli kallon da Afreen ke mata taɓe baki tayi ta dankwaleta ta ce, "tashi maza ki bisa, ai shi qanin ubanki ne dole dan na masa faɗa ki hararen, kuma yanzunnan ba anjima ba ki haɗo naki ya naki kibarmin gida ja'ira kawai".
Afreen tashuwa tayi tana qunquni ta shige ɗakinsu, sweedy dai in matacce na magana to tayi, duk abinda ake wanda za ta iya gani ta gani wanda ba zata iya gani ba idonta na kan wayanta.
Jay a gefen Afrah itama ya kwantar da ita, yana qarewa fuskanta kallo ji yake wani abu na fisgansa game da ita amma sai ya share ya ce "me ya samu qafanki Qanwata?
Ai Innai kaman me jiran ƙiris sai ta fara kuka har da sheshsheqa, sai rararshin dole ya kama Jay da qyar ta stagaita kukan ta faɗa masa tunda maciji ya sareta qafan ke ciwo ga shi ta tsaya sosai, ruwa ya bata ta sha sannan ya ce ta lallaɓa ta sauqo ta ci abinci zai kawo mata magani ya fice a ɗakin ita kuma ta sauqo, bai wuce cokali huɗu ta ci ba ta sha ruwa ta zuba taguminta.
Hira ya samu Hajja da malam ba-wasa suna yi, nan ya faɗa musu damuwanta ya ce zai je sayo wani allura ya mata, Hajja ta basa amsa da "a dawo lafiya" malam ba-wasa ya miqe suka fice tare.
Qiran DMD ne ya shigo wayan sweedy dan dama sun sayo MTN line da Afreen, ɗauka tayi tana sallama, jin abinda ya faɗa sai ta ce, "to Darling". ya kashe wayan a ɗaya ɓangaren ita kuma ta miqe ta fice a palourn ta nufi sashin yayyunsu mazan, da sallama ta shiga ta samesa zaune yana danna wayansa as usual.
Gaishesa tayi ya amsa sannan ya ce "ku qara haquri da addu'a Allah dawo da Ammi lafiya, gobe zan wuce Jigawa akwai abinda kuke buqata?"
"Bakomai Darling, Allah dawo da kai lafiya Allah ya bada sa'a Allah ya bayyana Ammi lafiya, amma please ka tafi da sweetie dan wallahi ko yau ita ta taimaka wajan yin lattin Afrah wai sam sai ta bita ita kuma ba yanda ta iya suka tafi ga shi taja andaketa".
"Okay kice ta shirya anjuma zamu koma Gombe tare sai mu wuce gobe, ran Saturday zamu dawo".
Sweedy na hamdala za'a rage mata aiki ta amsa sannan ta tashi ta fice ta barsa yana wayansa, da sallama ta shiga palourn ta iske sweetie na kan kasa fitina sai ta ce, "inji Darling ki shirya za ku tafi anguwa", sweetie mayyar yawo har da stallen murna ta shige ɗaki wai tun yanzu za ta shirya, Hajja da harara ta bita tana faɗin "ko shan-shani ya ganki ya sara miki da son yawo, gashi kinja an zane baiwar Allah, itama dai ta ja wa kanta da kini-bibin stiya".
Jay motan DMD suka shiga, suna tafiya suna hira da malam ba-wasa.
"Freind yarinyar nan ta haɗu iya haɗuwa ashe gaskiyan Afrah kawai fedding bottle ne mastalan" cewar Jay yana driving.
Dariya Malam ba-wasa yake yi har da na mugunta ya ce, "shegen kaya ashe qarewa ɗalibata kallo kake yi banda labari, kuma dan kai shahararren ɗan iska ne wato har da suna kasawa 'yan biyun mata wai feeding bottle hhhh! To headquartern kuma me ka sa masa?"
Jay murmushi yayi ya ce, "wannan kuma ka jira sai na bi hanyar garin za'a sanya masa suna, iya yawan haukatani da za'a yi iya cancantan sunan da za'a sa masa".
Dariya suka dinga yi har suka je pharmacyn suka sayo alluran suka dawo, Jay ya mata sannan har la'asar tayi, ganin haka Malam ba-wasa ya buqaci ta fito su tafi kar azo ɗaukanta bata nan, Innai kaman za tayi kuka haka ta fito tana ɗan ɗingishi dan zuwa lokacin qafan ya mata dama-dama, tanason tafiya gida amma haushi take har zata tafi Afrah bata tashi a bacci ba gashi ko da ta farka bata yi magana ba ta cigaba da bacci.
Jay ya sa Afreen ta fito su tafi, sweetie ma ta fito a shirye za ta bisu duk ɗaukanta anguwa ne kaman yanda sweedy ta faɗa mata, Hajja har compound na gidan ta rako Innai tana mata godiya sannan ta koma ciki, DMD da ke zaune mazaunin driver kallo ɗaya ya musu ya kau da kai, Jay taɓe baki yayi yana faɗin "Afreen, sweetie da habibtyn Afrah ku shiga baya, freind mu yi squatting a gaba before ku sauqa".
Da wani mugun sauri DMD ya juyo yana wa Jay kallon bakasan me kake faɗa ba, "Mtsww! Ka faɗi abinda zai yiwu dan ba ɗuruwamin a mota za'a yi kaman cow's ba, you better know's the fuck you're saying, in kuma ba za ku tafi ba nayi gaba".
Innai storo da haushi da kuma stanan sa ne suka qara samun gurbi a zuciyarta ji take kaman ta shaqesa kowa ya huta, maimaita abinda ya faɗa take a zuciyanta "Fuck you're saying", qwafa ta yi a hankali tana jin kaman ta fice ta nemi abun hawa ta wuce makarantar.
Jay shima haushin DMD ya ji dan yasan maganan nasa da Innai yake yi, shi dai DMD taɓe baki yayi sai kuma a hankali kaman bai son magana ya ce, "You're waisting my time".
Malam ba wasa ne wannan karon yayi magana, "freind ku ɗauki Maryam ku ajiyeta a school ni zan biyo bayanku banason azo ɗaukanta a samu bata nan kar mu ja mata faɗa kaga ƙawarta ta biyo".
Jay guntun tsaki ya ja, kamun ya ce da Afreen da sweetie su shiga motan, Innai ya duba ya ce, "habibtyn Afrah get in".
Innai lumshe idonta tayi ta tattaro duk iya jarumtar ta da kafiyanta da taurin kanta ta kawo gaban goshi ta buɗe idon sannan cikin sanyin murya ta ce, "hamma bb(big bro) ku tafi kawai ni zan hau mashine".
DMD jin abinda ta faɗa da sunan da ta qira Jay sai ya ja staki, shi kuwa Jay sunan daɗi ya masa har sanda ya murmusa sannan ya ce "a'a Qanwata, sai dai ku tafi da freind kar ki ɓata ba kisan hanya ba" ya faɗa yana nuni da Malam ba-wasa dan ta gane, wani ɗan iskan horn da DMD ya danna sai da hantan cikin Innai suka kaɗa idanuwanta suka kawo ƙwalla a take, malam ba-wasa cikin hanzari ya riqe hannunta suka yi gaba yana mai jin haushin abinda DMD ya musu, shi kuwa Jay rai a ɓace ya shiga motan DMD ya ja su, sunzo dai-dai su Innai ya ce, "Qanwata sai mun sake haɗuwa, kai kuma malami banson shishshigility" ya faɗa yana kallon Malam ba-wasa wanda ya fahimci me yake nufi na ya saki hannun Innai, sai kawai ya sake suka fice, motan su Jay na tafiya cikin ikon Allah su ma suka samu abin hawa, suna isa makaranta suka tarar har ɗalibai sun waste, Innai kaman za tayi kuka haka tayi rau-rau da ido, Allah ya taimaketa ta hango Rabe a can gefen wata bishiya, har wajan Rabe malam ba-wasa ya rakata ta hau ta masa sallama ya amsa yana murmushi ya ce, "Allah kai ku lafiya Maryam, kema Allah baki lafiya".
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yastunta ta amsa, Rabe ya ja mashine suka kama hanyan gida.

Jay tunda suka baro gidan Hajja ya ke aikin cin rai ya ɓata fiska ya qi ya cewa DMD komai, shi ma DMD ganin haka ya taɓe baki tare da ɗaga kafaɗa alaman ko a jikinsa ya cigaba da driving da mugun gudu, sweetie dai bacci ne ya ɗauketa ita kuwa Afreen aikin satan kallon DMD take yi har suka isa Gombe, Jay cikin dakewan murya ya ce "malam a asibiti za ka ajiyeni".
Bai ce masa uffan ba ya ja su har cikin asibitin, sai da Jay ya sauqa sannan yayi reverse suka kamo hanyan gida tare da sweetie da Afreen.
Jay yana shiga ya samu har lokacin patient ɗin bai farka ba, sai ya wuce office nasa y taɓa ayyuka zuwa magrib ya kama hanyan gida.
DMD suna isa yayi parking ya sauqa, Afreen da ke baya yake jira ta fito ya kulle mota amma ya ji tana qoqarin tayar da sweetie, guntun tsaki ya ja yana faɗin "excuse me", mastawa Afreen ta yi shi kuma ya ɗauki sweetie a kafaɗansa ya kulle motan suka yi cikin gida, ba su tarar da kowa a palourn ba sai ya wuce ɗakinsa da sweetie in ta farka ta koma wajan mummy da kanta kamun gobe su tafi.

Har bakin ƙofan gidan Baabaa Mero Rabe ya ajiyeta kaman kullum ya mata sallama sai gobe ya ja mashine ya tafi, gidan ta shige bakinta ɗauke da sallama amma shiru Baabaa Mero bata amsa ba, hanyar banɗaki ta bi da ido nan taga zanin Baabaa Mero a rataye alaman wasta ruwa take yi, ɗakin ta wuce ta cire uniform nata ta ɗau madaran shanu da ta gani mai ɗimi ta shanye tass sannan ta sanya kayan islamiyya ta fito ta tafi dan dama tayi sallah a gidan Hajja.
Baabaa Mero iyayen jimawa a banɗaki ta fito ta leqa sama ƙasa ba taga Innai ba sai uniform nata kawai, taɓe baki ta yi ta ɗauko kayan makarantan ta wanke mata ta ɗaura alwala ta shige ɗaki tana faɗin "ko kin dage da zuwa bokoko a wuta da islamiyyan wa billahillzi sai na miki aure ba ruwana kije can gidan ɗan iskan sa zai aureki ba nunu ku fama ni ya ishe, kayan makarantan ma sai ni zan wanke miki ".

Innai sai da Magrib aka tashe su, bata dawo gidan Baabaa Mero ba ta wuce gidansu tare da Hassu, suna tafiya suna hira Hassu ta ce "Adda Innai kinga nono na suna kumbura sai zafi suke mun bansan wani ciwo ne ya sameni a qirji ba, zan je na nunawa Baabaa ko Inna a shafamun magani".


Please Login or Register in order to submit comment