Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duhu ya fara amma hasken ɗakin yana haska su, matar fara ce kyakkyawa in ka ganta ba zaka ce babbar mata bace, kama take da larabawa.
Gaisawa da matar Arɗo da Baffai suka yi sannan Innai ma tace "ina wuni".
Matar fuskanta da murmushi dan yarinyar ta shiga ranta tace "how are'u doing baby? Innai tace "am doing good"...
Bayan sun gama gaisawa cikin harshen turanci da Innai wacce ba wani sosai-sosai ta iya ba, nan matar ta faɗa mata komai dalla- dalla yacce zata gane dan tawa su Arɗo bayani.
Innai ajiyan zuciya tayi tace "Baffai wai ita a cikin Gombe take amma hastarin ya faru da ita ne tana dawowa daga Jigawa state dan acan suke zaune da yaranta, yanzu tana so zata koma Gombe ne saboda yaranta tasan hankalinsu a tashe yake amma in Allah ya yarda zata zo baza'a jima ba" Matar murmushi take dan tasan Innai ta fahimci zancen ta kuma yarinyar ta qara burgeta.

Arɗo duk da ba sosai yake jin hausa ba amma kasancewar Innai tayi wani maganan da fillanci shima ya fahimta nan dai yace ba komai Allah kaimu.
Bayan sun fito Baffai ya yi sallama da Arɗo suka kamo hanyan komawa gida ga dare yayi ga duhu, tafiya suke suna hira na ɗa da Uba.

Ihu Innai ta sanya "Wayyooo! Allah naaaaa, hande kam mi boni! Baffai qaya ya soke ni, Wayyo zafi!" cewar ta tana yarfe hannu dan azaba.
Da sauri Baffai ya laluɓo touchin da ya kunna yana haska qafan nata, wuff kaman walqiya yaga gimawan bindin abu, cikin sauri Baffai ya haska qafan Innai.
Salati yayi ganin abinda yayi tunanin ne ya faru, maciji ne ya cije ta ba qaya ba, tana yarfe hannu har ta fara kuka dan ciwon da take ji.

Abinda ya rataya a wuyan sa kaman ɗan-kwali ya jawo ya kama qafan nata ya ɗaure mata cinyan ta sannan ya ɗaga ta cikin sauri suka qarisa rugan nasu yana mata sannu.
Innai ba abinda take sai hawaye, suna shiga cikin gida Baffai yace "A'ishatu kawo mun tabarma".
Inna ta fito da tabarma ta shumfiɗa masa ya ajiye Innai yace "zo ki mata fifita ba naje na qira Baabaa".
Inna tana tsaye daga gefe har Baffai ya juya zai fice bata mosta ba.
Baffai juyowa yayi ganin ta tsaye bata mosta ba ransa a ɓace yace "A'isha ba dake nake magana ba?"
Inna sunne kai tayi qasa ta juya ta shige ɗakin ta.

Baffai har zai bita ɗaki sai kuma tuna yarinyar sa kar dafi ya haura mata sai ya fice da sauri ya je gidan Baabaa Mero, da sallama ya shiga Baabaa na kallonsa tace "kai mai sunan Malam lafiya na ganka haka ragaja-ragaja kaman an biyo ka? Ina ita takwarar tawa take?"
Baffai yace "Baabaa mun gamu da stautsayi ne ki taimaka mana da gadalin dafin maciji".
cikin sauri Baabaa ta miqe daga zaunen da take ta ɗaura hannu a kai tace "kar ka ce mun takwara ta maciji ya ciza?"
Baffai yace "baabaa ita ce".
Baffai bai ida rufe baki ba Baabaa Mero ta wawuri hijab tayi hanyan waje sai kuma ta juyo ta shige ɗakin ko minti guda bata yi ba ta fito da wani qulli a hannunta tayi waje ko takan Baffai bata bi ba.
Shigowa gidan tayi ba sallama dan ta manta da Sallaman ma, inda ta jiyo nishin Innai tayi ta same ta kan taburman sai zufa take yi numfashi sama-sama kaman zata sume.
Cikin hanzari Baabaa Mero ta riqo qafan da taga an ɗaure ganin babu haske ta ɗaga kai za tayi magana sai taga Baffai a gefenta, qaramin tsaki taja tace "kai Isa ka sanya ni gaba kaman mai neman tubarraqi ba zaka kawo mun haske ba dan tambaɗewa tunda ciwon ba'a jikinka yake ba ko?"
Touchi ya kunna ya haska mata qafan, nan ta murza gadalin ta manna mata a wajan ciwon.
"Miqo mun ruwa a kofi" cewar Baabaa tana duban Baffai, miqewa yayi ya wuce madafin gidan ya ɗu kofi ya ɗiba ruwa ya kawo wa baabaa, jiqa maganin tayi tana tallafo kan Innai sai gani tayi Innai ta sume.

Magaji ne ya shigo gidan da sallama ganin su Baffai sai yayi wajansu "me ya same ta Baffai?" Cewar Magaji ganin Innai a kwance a sume kuma baabaa na sharar qwalla kaman anyi mata mutuwa. Cikin masifa Baabaa tace "Ubanka Musa ne ya same ta dan rashin tausayi ko sannu ba zaka mata ba".
Kallon Baabaa kawai yake yi tana bam-bami tana sawa Innai ruwan maganin da ta jiqa a baki amma yana zubewa ne kawai baya shiga bakin ta.
Ganin haka sai Magaji ya amshi kofin maganin ya riqe kan Innai ya ɗan buɗe bakinta yana stiyaya mata ruwan maganin.
Ruwan maganin na isa maqoshi ta ta buɗe ido tana haɗiyan ruwa, sai da ta shanye tass sannan ta rufe idonta ta koma tayi luff da kanta a cinyan Magaji.

Baabaa ido ta zaro tana salati tace "na shiga arba'in da uku ni Meramu yau me ya samu takwarata tasha maganin kuma ansa mata gadali sannan ba tayi amai ba sai faman lumshe ido take kamar mai shirin mutuwa, don Allah takwara bar wannan lumshe ido kamar wacce ke mashashshara ki buɗe idonki kiyi amai son ranki kinji".
Ba ita Baabaa ba har Baffai da Magaji hankalinsu ya tashi ganin taqi yin amai sai ma lumshe ido da tayi tana bacci da ya ɗauke ta yanzu".

"Wai nikam mai sunan Malam babu mutane a gidannan ne? Ko wata sabon salon baqin halin aka qutto gida shiru kaman ba halittan mutane ga yarinya bagatantan kaman wacce zata mutu amma ace ko ɗan stunstu bai fito dubamu ba kaman wanɗanda muka musu kashi akan gado jarababbu tambaɗaɗɗu marassa imani da tausayi" faɗin Baabaa Mero da ta miqe tayi hanyan ɗakin Inna A'i tana cewa "uwar jaraba mai sharɓa-sharɓan baqin hali kina gani yarinya ba lafiya cizon maciji na faman kashe ta kina zaune a ɗaki da hijab kamar mai takaba, wuce muje kiwa jikata tofin cizon maciji nikam".

Inna dake zaune akan sallaya da carbi a hannun ta sai qasa kawai tayi da kanta tana jin maganganun Baabaa har ta gama bata mosta ba bata ce uffan ba.
Baabaa tace "Indo wai har halin naki ya balaga ya kai haka? Indo rashin storon Allahn ma ya girmama ya wuce misali? Ina magana kina zaune wato ta mutu? Kai subhanallahi tirr da wannan tambaɗewan rayuwa wai AL'ADA, Indo Sallahn ki ma ba karɓuwa zai yi ba dan alhaqin baiwar Allah dake kanki, ni Meramu wannan JAHILCI KO AL'ADAH za'a qira sa? To koma me yake Aradu nayi Allah wadai da shi, Mutum na da iliminsa amma ya cika carbin burbushin tunaninsa tsaɓ da JAHILCI" Baabaa na gama magana ta fice rai a ɓace.

"Kai Magaji ɗauka mun yarinyar nan mu tafi gida na dan in tana gidan nan tun ranar mutuwanta bai yi ba zasu qarisa kashe ta dukansu gaba suke da Allah da ya qaddara zuwan takwara duniya".
Magaji miqewa yayi ya ɗauke ta a kafaɗa suka fice tare da Baffai sai gidan Baabaa Mero.

Suna shiga gidan tasa Magaji ya ajeta akan tabarman da dama take zaune a kai kamun Baffai yazo qiranta, mafifici ta shiga ɗaki ta dauko Baffai ya karɓa yana fifita Innai Magaji kuwa kanta na cinyansa.
Baabaa tagumi kawai ta zuba tana ganin ikon Allah dan duk iya sanin ta ko wani irin maciji ne ya ciji mutum muddin ta basa wannan magani ta manna masa gadalin shikkenan sai ya amar da dafin, dan a wajan mijinta ta gaji duka magungunan.
Miqewa Baabaa tayi ta shiga ɗaki can ta fito da wani qullin magani da qwai da kofi, tana zama ta fasa qwan sannan ta sanya maganin ta kaɗa, Magaji ta miqawa ya karɓa ya buɗe bakin Innai yana sa mata, sai ta kuma buɗe ido tana haɗiya kaɗan-kaɗan, yana gama bata ta wara ido tana ya tsine fiska sai lokacin ta fara jin tashin zuciya, in tayi kaman zata rufe ido sai taji amai na taso mata tana buɗe ido ya kwanta.
Baabaa tace "kai Magaji yanzukam ɗago ta kar ta ɓata maka jiki" sai ya ɗago kanta ya zaunar da ita amma yana riqe da ita. Sai lokacin Baffai ya tuna da maganan tofi nan take ya ɗau kofi da ruwa ya fara addu'a yana tofawa sannan ya sa mata a bakin ta sha, tana gama sha ko kofin bai gama barin bakinta ba sai amai, sosai take amai kaman zata harar da kayan cikin ta, ganin haka sai duk suka yi hamdala suna aikin jera mata sannu.
Sosai tayi amai ta galabaita, tayi luuuu! zata faɗi Magaji yayi saurin taro ta, nan Baabaa ta miqe ta ɗauko roba da ruwa sannan ta sanya Magaji ya gogewa Innai jikinta ta kawo wani riga tace ya sanya mata, kallon Baabaa yayi jin abinda tace na ya sawa Innai riga, duk da dai qanwar sa ce kuma yarinya ce tunda shekarunta sha-huɗu 14 kuma ba komai qirjinta amma baya jin zai iya sa mata rigan dan gudun mastala shi shaiɗan ba'a iya masa.
Ganin ya tsaya da riga a hannu sai ta harare sa ta karɓa zata sa mata shi kuma Magaji kau da idonsa yayi sai da ta gama da mata ya juyo, baabaa ta sanya shi ɗaukan Innai ya kaita ɗaki, ya ɗauke ta ya kaita ɗaki ya kwantar da ita akan gadon ta ya juyo ya fito.

Duk suna zaune zugum-zugum kowa yayi shiru ko wannensu da abinda yake tunawa a ransa yayinda shi kuma Magaji tunani yake wannan yarinya ko kaɗan bata da nauyi kullum ka ɗaga ta kaman ka ɗaga stinke.

Baabaa Mero tace "mai sunan Malam kana ji na?"
Baffai ɗaga kai yayi alaman yana sauraranra, sai ta numfasa tace "mai sunan Malam abun ya isa haka yau shekara ɗai-ɗai shekaru sha-huɗu kenan da haihuwan takwara sannan tun randa aka haifeta har yau ba abinda ya sanja na daga AL'ADAN da uwarta ta ɗaura wa kanta, abun ya isheni yau an qureni na tabbata nan gaba ko ba rai aka kawo takwara indo ba zata kalli gawanta ba balle batun ta mata addu'a ko ta wanke ta dan haka zan ɗau mummunan mataki a kanku duka abun ya ishe ni, ku tashi ku bani waje" ta faɗa tana kallon Baffai da Magaji.

Magaji kallon Baabaa yayi yace "baabaa kiyi haquri amma ni na tabbata Inna na son Innai irin matsanancin soyayyan nan ma, dan Allah kuyi haquri ku mata uzuri".
harara baabaa Mero ta aika masa da shi tace "kai dan ubanka Musa tunda ba kai ake azabtarwa ba dole kace haka, bayan AL'ADA ta kunyan ɗan fari kasan akwai AL'ADAH ta SHA'DI kamun aure ko? To tunda kace haka ka tabbatar sai an maka za'a baka mata jarababben mara tausayi har za kayi magana ni da nasan ba dan an daina sha'di ba sai dai ka mutu ba aure, to ciwon da ake ji a shaɗi na ɗan awanni ko mintuna ka isa ka haɗa shi da irin ciwon da ake ji na rashin kulawa daga mahaifiya? Anbar duk waɗan nan AL'ADUN saboda zamani yayi kowa ya fahimci yawancin AL'ADU ba komai bane face JAHILCI da kuma ɗaukan alhaqin bayin Allah a banza da wofi abu ba aya ba bare hadisi kuma dai ba Mustahabbi ba ko sunna balle a qira sa farilla kaman yacce mutane ke jahiltan kan su suka aza a gaban goshi, ciwon da takwara ke ji ba ko wanne mai laga-lagan zuciya bane zai iya ɗauka ka godewa Allah uwarka Habiba ba ruwanta da wannan JAHILALLEN AL'ADA dan da kai ne na tabbata sai ka shiga duniya dan jaraba".

Baffai kansa a qasa ya kasa cewa komai shi kaɗai yasan me yake kissinawa a ransa, dan sosai yau A'isha ta quresa.
Baabaa masifa take kaman zata ari baki barin dai in ta tuno rashin kunyan da Inna ta mata, cewa su Baffai tayi su tafi dare nayi tunda qarfe ɗaya na dare har ya gota, ficewa suka yi suka tafi gida, Magaji yawa Baffai sai da safe ya wuce ɗakin sa.
Baffai yana shiga ɗakin ya samu Inna a kwance da alama tayi bacci ma, qaramin tsaki yaja ya shumfiɗa sallaya ya kwanta a nan qasa.

Baabaa ɗaki ta shiga, cike da tausayi ta kalli Innai tace "takwara Inshà Allahu damuwanki ya kusa qarewa nasan me zan yi" nan ta kwanta a nata gadon bayan tayi addu'a ta shafawa Innai itama ta shafa nata.


Ina mai matuƙar baku haquri na rashin ji daga gareni jiya Monday sakamakon wani uzuri da ya riqe ni, amma Insha Allahu yau page's 2 zan turo, amma fa ya danganta da sharhinku, dan in kukayi yamun to da yamma ma zakuga update inkuma shirune to sai gobe kuma.


MASU SHARHI UWAR BATOORL TAKU TA GODE🤝 DAN SHARHIN KU SHINE QWARIN GUIWANA
MASU GODIYA BANSON THANKS NAKU KUMIN SHARHI KAWAI SHI NAKE BUQATA
Masu sharhi waɗanda basa group na JAHILCI KO AL'ADAH Uwar batoorl na godiya tana yinku❤️


INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚

𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


Free book
Kyauta bada kudi ba duk wanda akasayarwa to ycn baruwana nide littafina na kyauta nayosa

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله


Wannan shafi gaba ɗayan sa sukutum nasa, sadaukarwa ne gare ki rabin rai na, my peace giver, tattaɓa kunnena, ecleeyhn Kakus mum ɗin ta♥️ ECLEEMAT ABDUL (Ummu khamaluddeen wa Sheikh Mufaddal).
Mum Noor wa batoorl a isarwa antyn Nana saqo.
Jama'a kuyiwa TATTAƁA KUNNE NA addu'a da fatan alkairi.


LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION 🤝 shugaba adali da ɗauka cin member's ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 💃 2 YEAR'S ANNIVERSARY


FAN'S GA NAKU

𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.


💋💋 امى بتولة💋






𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 17_18


𝗖𝗔𝗡𝗔𝗗𝗔⭐⭐

Zaune yake a katafaren office nasa wanda staruwa da haɗuwan office ɗin kai kace a ɗaki ne dan yafi ɗaki ma staruwa da haɗuwa ga ko ina qamshi ke tashi a office ɗin, waya ce qirar cammon 20+ a hannun sa yana magana kaman mai storon buɗe bakin sa.
DMD kenan haɗaɗɗen saurayi kyakkyawa ajin qarshe mai ji da kyau da kuɗi wanda ba zai haura shekara 29 da haihuwa ba, magana yake a wayan cikin harshen turanci yana cewa "look jay am not coming to Gombe again I wan rest serious cuz dis day's the work's are plenty am even tired with the company" ya faɗa yana yastine fiska.
Dariya Jay ya sanya a ɗaya ɓangaren yace "DMD kaji muryanka kuwa da yacce kake magana kaman mace gaskiya babe naka ta shiga uku dan nasan bata isa ta gwada maka rigima ba, shikkenan in baka shigo Gomben ba ni zan shigo Canada ɗin soon ba".
"Ai ni ba'a haifi babe na ba tukunna ina tunani ma ba macen da zata burge ni kamun aje zancen gaba dan haka mata suyi rayuwan su nayi tawa rayuwa ba su yafi daɗi" cewar DMD.
Jay dariya ya kuma yi wanda kana ji kasan na shaqiyanci ne sai ya kwaikwai muryan DMD ya maimaita abinda ya faɗa kamun yace "wannan bashi ne kuma soon zan tuna maka abinda ka faɗa".
Dariyan da Jay yayi ya qular da DMD dan ya stani yawan dariya kaman ba lafiya ba shi abu mai wuya ne kaga murmushin sa ma balle dariyansa, staki yaja cikin fushi yace "Jay kai ba'a dogon magana da kai sai ka ɓata wa mutum rai, so Ammi zata shigo Gombe in zata dawo sai ku taho tare".
Qitt ya kashe wayan ya aje kan table dake gabansa ya busar da iska a bakin sai ya danna wani button akan table ɗin, sai kawai wata ta shigo tana rusunawa tace "Sir" nuni ya mata da first-aid box dake ajiye acan gefe wanda shi kanshi abun kallo ne.
Tana ganin haka tasan me yake nufi sai ta buɗe box ɗin ta ciro magani ta miqo masa tana rusunawa, amsa yayi ya ɓalla ya wasta a bakin sa ba ko ruwa ya haɗiye ya miqa mata saura ta mayar box ɗin sannan ta fita.
Sanda ta fita kamun ya buɗe idon sa yana unbotting na jacket nasa ya cire ya aje ya dannan wani button jikin kujeransa sai yayi kaman resting chair, ya ɗaura qafan sa kan table ɗin ya lumshe ido, wai ɗan maganan da yayi har kansa ya fara masa ciwo.

Jay na kashe waya yayi murmushi yace "gaskiya DMD kana fama da cuta" matar da ta shigo palourn ganin sa yana magana shi ɗaya yana dariya sai tace "kai jabeer lafiyanka kake magana kai kaɗai? Murmushi yayi ya sosa qeyansa yace "habibty lafiya lau kawai DMD ne yaban dariya".
Taɓe baki tayi tace "kai da shi kam ai sai addu'an shiriya, fatan Amminsa na lafiya?
Jay yace "tana lafiya wai ma tana hanyan shigowa Gomben", "to Allah kawo ta lafiya, dan gaskiyar baiwar Allah ya kamata ta leqo gidan mijinta duk da dai dan yaranta take zaune acan ɗin" cewar mummy tana zama a kujera.
Jay yace "ai wallahi Ammi na da qoqari mummy kullum fa tana sintiri a hanyan nan ita ce Gombe ita ce Canada Allah dai ya stare ta".
da "Ameen" mummy ta amsa a taqaice.

Jay(jabeer) kenan matashi mai kyau da aji sannan ga kuɗi shi kuma babban likita ne a babban asibitin cikin garin Gombe FMC Gombe.

Sai da ya huta sosai ganin ba zai iya aikin ba sai ya danna button na ɗazu wannar matashiyar baturiyan ta kuma shigowa ya miqe yayi gaba ya fice a office ɗin, jacket nasa da ya cire da wayoyinsa ta ɗauka tabi bayansa da sauri, ta danna button na lifter ya buɗe sai ya shige ita kuma ta shiga na gefen, floor na qarshe liftern ya tsaya buɗe da kansa ya fito ita kuma baturiyar ta jima da fitowa a nata ta staya gefe, yana fitowa yayi gaba tabi bayansa.
Driver ne ya staya da mota a dai-dai qofan fitowa Companyn sannan ya buɗe wa DMD qofa ya shige sai ya kulle, baturiyan ta miqa masa jacket da wayoyin DMD ya amsa ya aje masa a gefen sa sannan yaja motorn.


𝗤𝘂𝗲𝗯𝗲𝗰 𝗖𝗮𝗻𝗮𝗱𝗮
Gaban wani tangamemen gida dake quebec area a canada baturen drivern yayi horn aka buɗe musu haɗaɗɗen gate ɗin gidan wanda kana gani kasan sai dai a qasar wajen dan gida ne iya gida, baturen na parking ya fito da sauri ya buɗe wa Ogan nasa qofa, DMD fito da haɗaɗɗun qafafuwan sa dake sanye cikin sandal's wanda a qalla kuɗin su zai kai 700k a kuɗin Nigeria, sannan a hankali ya fito gaba ɗaya, ya juya zai shige cikin gidan ganin drivern a bayansa sai ya juyo yayi magana cikin harshen turanci "Christ na hana ka shigowa cikin gida na ina kuma zaka bini?" rusunawa baturen da aka qira da Christ yayi yace cikin turanci shima "Sir kayi haquri dama wayoyinka ne".
Ba tare da ya kuma cewa komai ba ya amshi jacket nasa da wayoyinsa sannan ya miqa masa wani envelope yace ya kaiwa sakatariyar sa liliyan.
Karɓan envelope ɗin Christ yayi shi kuma DMD ya qarisa shigewa gidan da sallama a bakin sa.

Wata yarinya ce wacce ba zata wuce shekara 10 goma ba mai matuqar kama da shi banbancin su kawai ita tana da duhun fata amma ba har can ba dan tafi chocolate color skin kawai dai ba za'a ce mata fara irin hasken sa ba. Da gudu tazo tayi hugging nasa tana cewa "oyoyo Darling sannu da dawo wa" murmushi ya mata ya ɗaga ta sama yayi juyi da ita kamun yace "sweetie kin fara nauyi fa" tura baki yarinyar da ya qira da sweetie tayi ta fara hahharba qafa akan ya ajiye ta tunda ita ce ma ta fara nauyi yarinya da ita, ganin ta tura baki kuma yasan me take nufi dan bata so ace mata tana da jiki ko tana da nauyi, sai ya miqa mata waya yaja kunnen ta ya wuce kan step's yabi hanyan da zai sada shi da sashin sa, duk maganan da suke da turanci suke yi dan kaman kwata-kwata basa jin Hausa.

Ya Ilahi! Inji masu karin zance suka ce wata miyar sai a makwaɓta, tabbas wata duniyar ko a mafarki sai mai rabo ke kallonta dan kuwa haɗewan sashin DMD ba zai faɗu ba dan duk staruwan office nasa in kaga sashin sa kai kace bola ne, duk haɗuwan wannan gida daga waje bai yi rabin kwatan haɗuwan sashin DMD ba, wasu arnun england-chair's ne a palourn kusan set huɗu dan haɗuwa da girman palourn, akwai white, dark-blue, black and light-blue, daga gefe wasu haɗaɗɗun transparence labule ne masu kama da glass-door a dinning area wanda in mutum na zaune a dinning ɗin zai iya hangen komai na palourn amma in kana palourn ba lallai kaga komai na dinning ɗin ba, daga gefe kuma wani corridor ne wanda bai kai wajan gidan ba amma akwai swimming-pool mai ɗauke da shape na heart sannan ruwan cikin sa fari tass har kana iya hango qasan pool ɗin, daga gefe kuma qofa ne wanda zai sada ka da kitchen na palourn sai kuma step's a gefe wanda DMD yabi dan haurawa ɗakin sa, a saman ma wani palourn ne wanda ya haɗu ya gaji da haɗuwa sai dai bai kai na down-stairs girma ba sannan akwai duk wani abun buqata a nan ɗin ma har da kitchen da dinning area.
A bakin ɗaya daga qofofi 6 na glass dake saman ya staya, sai da ya sanya yastan sa a jikin wajan fingerprint wani abu a jikin qofan kaman computer ya haska qwayar idon sa sannan a hankali qofan ya buɗe ya shige ɗakin nasa.
Wata arniyan gado ne a ɗakin wanda yasha shumfuɗi kai kace ba'a kwanciya a kai, gadon nada girma sosai daga jikin bangon kuma plasma ne mai girma a manne wanda kaman a jikin bangon aka qerosa sai wall-drop da ya cinye rabin ɗakin dan girma. Aje wayoyinsa yayi a kan bed side drawer sai ya cire kayan jikinsa ya rage daga shi sai short-nicker, kayan da ya cire ya rataya a hanger dake cikin Sip ɗin sannan ya nufi wani ɓangaren ɗakin, yana tsayawa a wajan sai qofa ya buɗe a wajan wanda inka gani da farko ka ɗauka duka bangon ɗakin ne.
Bayan mintuna ya fito ɗaure da guntun towel wanda iyakacin sa guiwansa sai wani qarami a hannunsa yana share ruwan jikinsa, qirjinsa mai cike da haiba da jarumta cike yake da kwantaccun gashi luf-luf jikinsa a mummurɗe kaman ɗan kokawa(restiling).
Gaban dressing mirror yaje ya staya sama-sama ya shafa mai ya shafawa gashin kansa da

Please Login or Register in order to submit comment