Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kice mun Fatu ni ina nasan wani masokiya, tana can ɗaƙin su".

"Shikkenan Hajja na barki ke ɗaya na tafi wajan Fatu" ta faɗa tana dariya ta shige hanyan ɗakunan.

Hajja danqwalo ta bita da shi tace "tijararriya sakalalliya zaki dawo ki same ni ai ba dai sunana kika qira gastau-gastau kamar ba sunan uwar ubanki ba".


Jay har sun iso qofan gidan Hajja sai ya waiga bai ga motan DMD a bayansa ba, cikin sauri ya ciro waya yayi dialing layin sa.
"Hello dude ya banganka ba ina ka tsaya?

"Mtsww! Ni ba zani gidan Hajja ba ku same ni a inda nace maka zan je".

"Dude please ka zo wallahi kuwa za mu bika can ɗin ka ji" Jay magiya ya dinga wa DMD har dai cikin ɓacin rai ya kashe wayan ya juyo motansa hanyan gidan Hajja.

Farooq na dariya yace "gaskiya DMD ko mace ta basa hanya a rigima da jan rai".

"Ai wallahi freind ba iya jan rai ba har da na aji kaman ance masa nima ba al'qalamin ne da ni ba kaman shi".

"Amma ai zai zo ko?

"Tunda ka ji ya kashe waya to zai zo amma xansha surutu kam dan kasan halin sa da ya dinga yawaita magana ya gwammace yayi abinda bai yi niya ba".

Murmushi Farooq yayi dai-dai suna qarisa shiga palourn bakinsu da sallama.
Ganin ba kowa a palourn sai suka zauna kawai suna kallo, Jay yace "gwanda da Hajja bata waje dan da taga shigowana bata gansa ba ta farawa mutane aiken surutun ta".

Bai ida rufe baki ba ta fito sanye da hijabin ta hannunta da carbi tana cewa "munafiki wato ma uwar ubanka ce mai surutu kai amma yaran nan kun renani uwayenku duk basu muku tarbiya ba" nan ta fara masifan kuwa tana tambayan bata ga Muhammadu ba?

Farooq ya gaisheta ta amsa tana tambayan sa ayyuka da gidansu ya amsa lafiya.

Ta buɗe baki zata qara tambayan sa sai sallaman sa da ta jiyo yasa tayi shiru ta hau washe baki.


𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚'𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 - 250 𝟏𝐆𝐁 - 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 500
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎......




Abiy yana shigewa gidan yayi mummunan gani dan kuwa Amaryan sa ya gani da mayafi da qaton akwati tana kuka ta taho zata fita ko kallon sa ba tayi ba (dama tana jin qaran motan Abiy ta haɗa kaya ta hau kukan kirsa).

Kallonta yake cike da mamaki yama kasa cewa komai har ta fice a palourn, da qyar ya iya ɗaga qafansa a inda yake staye yayi waje ganin har ta shiga mota tana qoqarin tayarwa, da sauri ya qarisa jikin motan yana mata magana "sweetheart me ya faru? Me aka maki? Ke da wa? Ina kuma za kije baki gayamun ba gashi kina kuka?

Aunty Amarya ko kallon Abiy taqi yi sai aikin kukan da take yi ta qara volume ta kau da kai (kana gani kasan kukan munafurci ne).

Abiy sai aikin rarrashin yake da tambayan ba'a si dan ba qaramin tashin hankali ya shiga ba, babu maimuna itama wannan tana qoqarin tafiya ina zai sanya kansa da yawan buqatan sa? Ai dagewa yayi yana rarrashi Aunty Amarya wacce da abun ya mata yanda take so ganin har da cewa zai saya mata mota sai ta buɗe murfin motan ta fito nan ma bata ko kallesa ba kuma bata ɗau kayanta ba ta shige cikin gida har ɓangaren ta direct ɗakinta ta shige tana kan kukan ta.

Abiy ajiyan zuciya yayi ganin dai ta koma cikin wanda yasan yanzu lallashin zai zo masa da sauqi tunda ta fasa tafiyan, shima bin bayanta yayi yana ƴar waqan soyayya.
"Rabi'atul adawiyya masoyiya ta Amarya ta ƴar aljanna mai haquri ga kawaici ga hankali(Abiy ya faɗa sosai😂).
Har cikin ɗakin ya bita, yana shiga ya cire babban rigar sa ya masta kusa da ita ya jawo ta jikin sa yana bubbuga bayanta yana qoqarin laluɓo bakinta ta fiske cikin kukan kirsa tace "Ni a gidan nan ba'a ɗauke ni a bakin komai ba iya amfanina kenan a biya buqata da ni duk sanda aka so amma wai ace dan ban haihu ba baza'a girmama ni ba aban matsayin uwa ko da zanji sanyi a raina, kowa ya tashi bai da mareniyar wayo sai ni har ɗan ciki na ya mare ni" duk maganan da take cikin kuka.

Abiy da yake mamakin wa zai mare ta sai yace "sweetheart ke da wa?

Hararansa tayi tana kuka tace "Ni da wa kuma ina banda yaronka wai ace har yaronka yayi girman da zai mari matar ubansa ina a matsayin uwar sa dan ni ba mazaunin yadikko nake zaune da su ba yaro na kowa ne".

Abiy da mamaki da ɓacin rai suka cika sa yace "wai har kina nufin MUFADDAL ya mare ki? Yaushe duk rashin kunyan nasa ya kai haka akan me zai mare ki?

Cikin taqaici Aunty Amarya tace "wato baka yarda ya mareni ba? Zanwa yaronka sharri ko? Hmmn! Ba komai dama nasan iya mastayina kai ma baka qaunata kawai amafanina gare ka biyan buqatan ka tunda har kana tunanin duk irin qaunar da nake wa yaran nan zan musu sharri, wai kana tambaya akan me ya mare ni ko? Hmmn! To akan gaskiya kawai dan ita gaskiya ɗaci gare ta, yarinyar nan sweerie na samu ta kunna waqa tana aikin tiqan rawa sai na kashe nace bai kamata ba tana ɗiya mace ga can mama mai aiki a kitchen taje ta tayata wani abun yafi wannan rawa dan ita mace ce kuma aurar su za muyi, kar a dawo mana da su basu iya komai ba, amma yarinyar nan tan tashuwa buɗan bakinta ba zata yi ɗin ba ina ruwa ai ni ba uwarta ba balle na sanya ta aiki. Na fito na dawo ɗaki bance mata komai ba sai can fitowa na na samu an juyemun gaba ɗaya ferfesun da na shiga kitchen na maka da kaina ina mamaki sai ga yarinyar nan ta fito tana faɗamun ita tayi na ɗau mataki, cikin ɓacin rai na fara mata faɗa nace nima mahaifiyar su ne bai kamata ba, ban ida rufe baki ba MUFADDAL ya wanke mun fiska da mari wai na daina haɗa kaina da Ammin su dan ita ba sa'a ta bace" Aunty Amarya na gama magana ta fashe da kuka mai qarfi wanda in kaji ka ɗauka ko uwatta ce ta sheqa.

Abiy cikin tsananin fushi ya miqe zai fice amma aunty amarya ta riqo sa tana kuka tace "nikam kayi haquri na yafe musu Allah shirya mana su dan kaga sun riga sun fita bai kamata ka fita cikin fushi ba banso komai ya samarmun kai mijina kayi haquri kaima ka yafe musu".

Kallonta yayi ransa a ɓace yace "Rabi'a har zaki ce na yafe musu kin yafe musu to wallahi ba za'a yi haka da ni ba na auro mata yara su hanata sukuni dan suna taya uwarsu kishi to zan ɗau mataki dole da shi MUFADDAL ɗin da ita MUNAWWARA su san nine na haife su ba su suka haife ni ba renin yaron nan ya fara wuce gona da iri"

Aunty Amarya murmushi tayi ganin Abba baya ganin ta amma sai ta lanqwasa murya tace "komai suka yi kai ne ka ja dan ya kamata tun farko ka nuna musu ni ma uwarsu ce amma baka yi hakan ba dan haka haquri gare ni ya zama dole tunda yaran mijinane kuma ina sonsa matuqa dan haka dole gare ni na qaunace su suma"

Abiy na huci ya dage zai bi DMD amma Aunty Amarya ta hana sa nan dai ya bata haquri kan zai ɗauki mataki da ta nuna bata so ta haqura sai yayi fushi ya tafi ɗakinsa wanda ganin haka tayi hamdala a rai tasan komin yaya sai ya ɗau mataki dan shirin nata ya tafi yanda take so.
Wata ƴar iskan dogon riga ta sanya shara-shara ta tamke nononta da ya fara kwanciya a bresia tayi hanyan ɗakin Abiy, tana shiga ta same sa da waya a hannu yana aukin qira ana gaya masa "not reachable" alaman ba network, qwafa yake kan jerawa dan har yanzu cikin ɓacin rai yake, jin qamshin Amaryan sa ya sanya shi juyawa duk da kuwa fushin da yake yi da ita, wanda kallo ɗaya ya mata ya kau da kai.

Aunty Amarya ganin haka sanda ta girgiza da fushin Abiy tasan shi koma menene tayi wannan shiga da wannan qamshi zai haqura dan haka ta qarisa ta zauna kan cinyan sa tana qara basa haquri tana shafa sa.

Abiy da Allah yayo sa da qarfin sha'awa duk da kuwa manyantan sa amma garau yake dan haka lokaci guda ya biyewa Amaryan sa suka lula duniyan ma'aurata.


DMD qarisa shigowa palourn yayi da sallama a bakin sa qasa-qasa dan ko ka kasa kunne ba jiyowa za kayi ba sai dai in ka kalli laɓɓansa waɗanda ke mostawa a hankali kaman mai rigima da su, fiskan sa a haɗe kana gani kasan a cike yake qiris yake jira ya juye akan mutun, ba tare da ya kalli ko su Jay ba balle Hajja ya samu waje ya zauna ya fidda wayan sa ya sa Bluetooth.

Hajja kallon sa tayi ta kalli su Farooq ta kuma kallon sa, cike da masifa tace "Muhammadu uwaka maimuna"

Ɗago idanuwan sa yayi da har sun sanja kala, rai a ɓace ya wastawa Hajja wani mugun kallo, kallon karki sake qiran Uwata.

Hajja qwafa tayi ganin irin kallon da yake mata ta ce "an faɗa uwarka maimuna tashi ka cinye ni ɗanye ɗan gidan marassa ji yaro sai aukin zuciya kaman na fir'auna uwarka ta fi uwar wa? Dama wa ya kawo ka gida na tunda kasan rashin kunya ka ɗibo ka taho da shi ba kirki ba?

Cikin fushi ya miqe ya juya zai fice dan yasan muddin ya buɗe baki to abun ba zai yi daɗi ba dan kasancewarta kakarsa bai dame sa ba, kawai tayi kaɗan ya tamka mata shi yasa ya miqe ya fice.
Yana fitowa ya wuce ɗayan sashin da yake nasu yara maza yana ji kaman ya kamo Jay ya shaqe sa dan shi ya jawo masa shigowa gidan.

DMD na barin palourn Afreen ta shigo, jin hayaniyan Hajja ta san tabbas DMD ya shigo nan ta baza maganenta (idanuwanta) amma baya palourn, idonta har da qwalla ta haɗa fiska tace "ke dai Hajja wallahi kin cika masifa da surutu an samu ya zo shine kika kora sa da halinki, big bro Ina yake?

Jay da shima ya cika da surutun Hajjan hararan Afreen yayi dan shima yaji haushi yace "igiyar ajiyan sa da kika ban ya ɓata idiot kauce mun a gani"

Murguɗa baki tayi ta fice, tana fita kuwa ta ga motan sa wanda ke nuni da yana cikin gida bai tafi ba dan haka cikin sassarfa ta tuni sashin yayyunta mazan.

Hajja ma da ta cika da baqin halin jikan nata da ke damunta ga ta masa faɗa kuma bata jin daɗi duk da kuwa irin kallon renin da ya mata amma sonsa da take yi yasa take jin haushin faɗan da ta masa dan haka miqewa tayi itama ta fice dan tasan ba zai wuce yana sashin su ba.

Afrah da sweetie ne suka fito daga ɗaki inda suka baro sweerie a ciki.
Sweetie na ganin Jay ta yi wajan sa da gudu tana cewa "oyoyo big bro"

Afrah kuwa ganin wanda ke zaune gefen big bro ai sai ta storita ta waro ido a ranta tace "Malam ba wasa!"....



FAN'S KU RIQE GODIYAR KU, UWAR BATOORL SHARHI KAWAI TAKE BUQATA.


INA KUKE MASU SANA'A, SANA'A MAGANIN TAQAICIN RAYUWA. SAUQI YAZO MUKU HAR INDA KUKE DOMIN WANNAN BA IRIN NA SAURAN BANE
Ga mai buqata a tallata masa hajar sa ko kuwa dai sana'ar sa to yai maza ya garzayo ga uwar batoorl mai tallata haja a rahusa mai sauqi domin kuwa har da alakoro ina yi.
Talla a littafin kuɗi farashi daban
Talla a littafin kyauta farashi daban dan banbanci da kyauta kaɗan ne

KU TUNTUƁE NI A WANNAN LAYIN NAWA
09161720046
WHATSAPP
TELEGRAM
Ko Gmail nawa
yarmalam96@gmail.com

Akan rahusa mai sauqin gaske, sai kunzooooooo🤝


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
𝙅𝘼𝙃𝙄𝙇𝘾𝙄 𝙆𝙊 𝘼𝙇'𝘼𝘿𝘼𝙃?🥺



𝘽𝙮

Harira Salihu Isah
(Uwar batooler)


اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله


LAFAZI WRITER'S ASSOCIATION shugaba adali da ɗauka cin member's ƴan uwana wannan littafi tukuici ne garemu 2 YEAR'S ANNIVERSARY


JAHILCI KO AL'ADAH? FAN'S CLUB 🤝💙one lurv masu daraja habibties, Uwar batoorl na matuqar qamnar ku da sharhinku da soyayyan ku ga wannan littafi.
Dama waɗanda basa group ɗin amma suna sharhi to tabbas Uwar batoorl na soyayyan ku.


*Wannan page ɗin naki ne NAFEESAH*


FAN'S GA NAKU
𝗜𝗡𝗔𝗬𝗜𝗡𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗦𝗢𝗬𝗔𝗬𝗬𝗔𝗡 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗝𝗜 𝗗𝗔 𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗤𝗔𝗠𝗡𝗔𝗥𝗞𝗨
𝗜𝗡𝗔 𝗠𝗨𝗞U 𝗙𝗔𝗧𝗔𝗡 𝗔𝗟𝗞𝗔𝗜𝗥𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗜𝗡𝗗𝗔 𝗞𝗨𝗞𝗘 𝗔 𝗙𝗔'𝗗𝗜𝗡 𝗗𝗨𝗡𝗜𝗬𝗔𝗥 𝗡𝗔𝗡.
𝘂𝘄𝗮𝗿 𝗯𝗮𝘁𝗼𝗼𝗿𝗹 𝘁𝗮𝗸𝘂 𝗺𝗮𝗶 𝘀𝗼𝗻 𝗳𝗮𝗿𝗶𝗻 𝗰𝗜𝗸𝗶𝗻𝗸𝘂.


💋💋 امى بتولة💋




𝗙𝗿𝗲𝗲 𝗯𝗼𝗼𝗸 🅿️ 29_30


Afrah qasa tayi da kanta ta qarisa cikin palourn wanda shima Farooq idon sa ke kanta yana danne dariyan sa dan yasan bata san me ya kawo sa gidan ba.
Qarisowa palourn tayi ta durqusa ta gaishe shi sannan tayi wa big bro sannu da dawowa.
Jay yace "yauwa qawar qwailar budurwata".
Afrah tura baki tayi tare da yin qasa da kanta duk a tunaninta ba wanda yasan abinda ta faɗa bata san Jay kam ya jima da juyewa malam ba-wasa.


Afreen tura qofan palourn nasu tayi ta shiga da sallama, ganinsa yana zaune yana danna waya sai taji sanyi a ranta ta qarisa ciki zuciyanta na dukan uku-uku dan kuwa tasan halin sa sarai.
Tun shigowanta yaji mostinta har qarosowan da tayi palourn da kuma idanuwan da ta zuba masa duk yana sane amma sai ya basar.
"Darling kayi haquri da halin Hajja" ba tare da yace komai ba ya lumshe idon sa gami da jinginar da kansa a jikin kujeran da yake zaune, yana sauqe ajiyan zuciya.
Haquri taci gaba da bashi tare da masa sannu da zuwa amma ko kallonta bai yi ba balle ya tanka mata, har sai da ta yi addu'an Allah bayyana Ammi kamun cikin sanyi ya buɗe bakin sa yace "Ameen ya Hayyu ya Qayyum" iyaka abinda ya faɗa kenan ya kuma rufe bakinsa gum kai kace baya magana.

Hajja da sallama ta shigo, inda ta hange sa zaune ta nufa tana faɗin "Malam Muhammad Mufaddal, yaro mai sunan larabawa, babban mutum a daina fushi da Amarya mana".
Tun shigowan stohuwar yaji ransa na qara ɓaci, duk surutun ta kuwa bai ko haɗa shi da qasa ba, sai ma earpiece nasa da ya maida kunne.
Zama tayi gefensa tace "haba Angon Hajja mijin Hajiya fushi kake da Amaryan ka?
Duk surutun Hajja ko kallonta bai yi ba bare kuwa ya kai ga mata magana dan DMD sosai yake da zuciya ga rashin son surutu, amma kuma bashi da riqo.

Hajja rarràshi tayi kaman wacce ke rarràshin yaron goye amma ko kulata yaqi yi sai da qyar kamun ya buɗe baki yace "Hajja komai za kuce ku daina sako Ammi ba ruwanta ba abinda ta sani".
Hajja jin ta samu ya kulata ai cikin kwantar da murya ta ce "ai ni tsakanina da Maimuna baiwar Allah sai addu'a da fatan alkairi barin ma dai da ta haifamun ku, karka damu an daina Angon Hajja, amma kai ma ka dubi girman Allah da Manzon sa ka rage wannan halin naka".
Sai lokacin yayi ajiyan zuciya yace "kuma kiwa yaronki ma magana komai za suyi shi da matarsa su daina sako Ammi kowa ya staya iya mastayinsa ya zauna iya mazaunin sa".

"Ai karka damu tsaff na ɗauki mataki na gama dan na sani Rabi'atu cikakkiyar munafuka ce ga kirsa, ai ita abin nata ma yayi yawa yo gaki ba kyau ba ga kuma munafurci, kuma fa damuwan ta duka dan bata haihu bane, ai ni nagode wa Allah da ban haɗa jini da ita ba, kaikam kayi haquri ko Allah ya bayyana maimuna".

"Ameen" ya faɗa a taqaice yana miqewa zai fice a sashin, da Hajja da Afreen duka miqewa suka yi suka bi bayansa.
Motansa ya shiga ya zauna ya mata key kamun ya juyo a daqile yace wa Afreen "ki gayawa Jay na tafi".

Hajja salati tayi kawai ta tafa hannu dan ita tama rasa irin zuciyan wannan jikan nata ko na uban wa ya ɗauko oho, ubansa Mustapha nada zuciya amma ba irin wannan baqar cin rai ɗin ba "to Allah ya shirya" ta faɗa tana shigewa sashin ta.
Afreen kaman za tayi kuka haka tabi bayan Hajja bayan taga fitan motan sa, sosai take mugun sonsa amma ko kallo bata ishe sa ba, ta rasa ta ina ma zata fara ɓullo wa ta nuna tana sonsa kuma gashi ba wanda yake saurara balle ta sama da maganan "Allah dawo dake lafiya Ammi nasan kece kawai zaki mallaka min masoyin raina" cewar ta tana shigewa palourn.

Jay na jin dirin motan DMD nan suka fito shi da Farooq, kusan karo da Afreen suka yi nan ta faɗa musu abinda yace, tana gama magana ta qarisa ta ciki dan lallashin kanta, su kuma suka shige nasu motan.
Jay yaje ya ajiye Farooq sannan shima ya kamo hanyan komawa cikin Gombe.




𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!! 𝐓𝐀𝐋𝐋𝐀!!

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄
𝐲𝐨𝐮𝐫 𝐬𝐚𝐭𝐢𝐬𝐟𝐚𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐢𝐬 𝐨𝐮𝐫 𝐜𝐨𝐧𝐜𝐞𝐫𝐧.

𝐊𝐮𝐳𝐨 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐭𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐪𝐢 𝐦𝐚𝐢 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐡𝐢𝐝𝐢𝐦𝐨𝐦𝐢𝐧 𝐤𝐮 𝐚 𝐨𝐧𝐥𝐢𝐧𝐞 𝐤𝐨 𝐤𝐮𝐰𝐚 𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞-𝐤𝐚𝐥𝐥𝐚𝐜𝐞 𝐚 𝐘𝐎𝐔𝐓𝐔𝐁𝐄 𝐛𝐚 𝐭𝐚𝐫𝐞 𝐝𝐚 𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐢/𝐝𝐚𝐭𝐚𝐧𝐤𝐚 𝐲𝐚𝐲𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐳𝐮𝐪𝐞𝐰𝐚 𝐛𝐚. 𝐈𝐧𝐚 𝐦𝐚'𝐚𝐛𝐨𝐭𝐚 𝐚𝐦𝐟𝐚𝐧𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐚𝐟𝐚𝐫 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐓𝐈𝐊𝐓𝐎𝐊 𝐦𝐚𝐬𝐮 𝐤𝐮𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐚𝐮𝐫𝐢𝐧 𝐪𝐚𝐫𝐞𝐰𝐚𝐧 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐭𝐨 𝐟𝐚 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐛𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐤𝐨 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐞 𝐛𝐚𝐧𝐞 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐧 𝐠𝐰𝐚𝐝𝐚 𝐚𝐤𝐚𝐧𝐬𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐪𝐰𝐚𝐫𝐚𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐢𝐧𝐠𝐚𝐧𝐜𝐢 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐪𝐚𝐫𝐠𝐨 𝐠𝐚 𝐃𝐀𝐓𝐀𝐧 𝐤𝐚 𝐭𝐨 𝐤𝐪 𝐳𝐢𝐲𝐚𝐫𝐜𝐢

𝐎𝐔𝐌 𝐀𝐋'𝐀𝐌𝐄𝐄𝐍 𝐃𝐀𝐓𝐀 𝐒𝐄𝐑𝐕𝐈𝐂𝐄

𝐌𝐓𝐍 𝐀𝐈𝐑𝐓𝐄𝐋

𝟏𝐆𝐁 - 250 𝟏𝐆𝐁 - 2𝟓𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 500
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 750

𝐆𝐋𝐎 𝟗𝐌𝐎𝐁𝐈𝐋𝐄

𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎 𝟏𝐆𝐁 - 25𝟎
𝟐𝐆𝐁 - 50𝟎 𝟐𝐆𝐁 - 5𝟎𝟎
𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎 𝟑𝐆𝐁 - 75𝟎

𝐌𝐮𝐧𝐚 𝐚𝐫𝐚𝐡𝐚 𝐦𝐮𝐧𝐚 𝐡𝐚𝐧𝐚 bashi😊 𝐬𝐚𝐲𝐚𝐧 𝐧𝐚 𝐠𝐚𝐫𝐢 𝐦𝐚𝐢𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐝𝐢 𝐠𝐢𝐝𝐚(𝐢𝐧𝐣𝐢 𝐡𝐚𝐮𝐬𝐚𝐰𝐚)
𝐙𝐚𝐤𝐮 𝐢𝐲𝐚 𝐭𝐮𝐧𝐭𝐮𝐛𝐚𝐧 𝐦𝐮 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐥𝐚𝐲𝐢 𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚 𝐤𝐨 𝐭𝐚𝐛𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐬𝐡𝐚𝐢𝐝𝐚𝐧 𝐛𝐢𝐲𝐚
𝟎𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐂𝐀𝐋𝐋/𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏

𝐀𝐜𝐜𝐨𝐮𝐧𝐭 𝐧𝐮𝐦𝐛𝐞𝐫
𝟕𝟎𝟐𝟓𝟐𝟑𝟐𝟎𝟐𝟗
𝐀𝐈𝐒𝐇𝐀 𝐀𝐋𝐈𝐘𝐔
𝐎𝐏𝐀𝐘 𝐁𝐀𝐍𝐊.

𝐒𝐀𝐈 𝐊𝐔𝐍𝐙𝐎𝐎𝐎......



⭐⭐
Anci hutun qarshen mako an suɗe amma har yanzu qafan Innai bai warke ba har da ɗingishi take yi, baabaa da idanuwanta ke kan Innai da tayi hanyan banɗaki girgiza kai tayi tace "Allah Ubangiji ya yaye wa ɗan mutum jarababben raki da son jiki irin naki takwara, dan kekam abun sun taru sun miki yawa, kece qan-jiki kuma kece raki to wai ma ta ina ciwo zai sake ki in ya kama ki? Ai ranar da za ki haihu akwai kwasan ƴan kallo, Allah dai ya kawo miki da sauqi ya yaye miki, amma tabbas duk shawaragin mijin da ya aureki takwara sai dai a bisa da kondunan haƙuri cikin akori-kura, yarinya gaba-ɗaya kaman wacce nono bai isheta ba, uhmñ ni Allah na tuba ai ma nonon ba isanki yayi ba babu laifinki Allah shiryi uwaki Indo".
Har Innai ta fito banɗaki baabaa na kan mita, kallonta baabaa tayi tace "wai yau har rana ta fito gasto-gasto kina ta yan-yana qafa halan baza ki bokokon ba?

Innai zama tayi gefen baabaa tana faɗin "washh! Qafata, baabaa sai jibi za muje makarantan yau da gobe babu".

"Uwar masu sakalci yanzu wannan ɗan tafiyan shine har da wani washh, na washo miki kan baabaarki Indo, 'yar shawaragin buhun uba".

Duk tsawon kwanakin nan da duk abunda ya samu Innai har taji sauqi Inna ko sau ɗaya bata taɓa gwada ce mata sannu ko ya jiki ba, tun Baffai na fushi har ya gaji ya sauqo yana bin ta da addu'an Allah kyauta dan ya tabbatar lamarin Inna sai a hankali, tun yarinya na stumman goyo har ta girma ta zama budurwa amma babu soyayya da kulawan mahaifiya, sai dai ya qudure a ransa tabbas zai ɗauki mataki kuma itama Baabaa Mero tana nata shirin daban, don abun ya kai su bango zuba mata ido da suke yi shi ne laifin su.


A ɓangaren DMD kuwa zuwa yanzu ko magana baya yi da Abiy akan abinda Aunty Amarya ta faɗa wa Abiy, wanda saura kaɗan Abiy ya stine masa Daddy ne ya taka masa burki, sai Hajja da tace ya dai bincika dan zai yiwu sharrin Rabi'atu ne ko kuwa gaskiyanta fitsaran shi yaron ne.
DMD dai duk zuba musu idanuwa yayi yana kallon su dan shi damuwansa Ammin sa, in ta dawo duk zai koma kan maganan ya ɗau mataki dan ya fahimci matar Abiy na buqatan qarin hankali.

Su sweerie sun gama fahimtan Amminsu ɓacewa tayi kawai Abiy lallaɓasu yayi.
sweetie kuwa kukan yau daban na gobe daban kullum dai ita Ammin ta, gashi Darling tunda ya kawo su bai dawo ba har dai yau da ya kama Monday.

Hajja zaune da jikokin nata a palour, sweetie ke kukan darun da ta saba "Ammiiii naaah! Wayyo Ammiii naaaah! Whmmmmm!.... Ammiiii...." Kuka take da gasken-gaske dan har muryanta ya dishe.
Sweerie tashuwa tayi taje gefen sweetie ta zauna, idanuwan ta cike da qwalla tace " Muheebbah please kibar kukan nan haka za kisa Ammi yin shaquwa kiyi haquri kinji zata dawo" ta faɗa tana qoqarin jawo ta jikin ta, amma sweetie sai ta zille tana kan kuka tana qiran sunan Ammin ta.
Sweerie ganin haka sai itama ta fara hawayen, Afrah dake kallon su itama kukan ta kama dan sosai take son sweetie bata son ganin ta cikin damuwa balle kuma sweerie abokiyar ta, Hajja da ta cika tayi fam kaman ta fashe cikin jin haushin kukan nasu tace "Wai nikam ance muku uwar taku mutuwa tayi ne? Kun maida mun gida gidan makoki to bazai saɓu

Please Login or Register in order to submit comment