Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Suka Fara ja baya sai Kuma suka Fara Saida Kadarori wannan ya siyar da gida wannan Fili,waccan gidan Mai a hada Kadarori ma suka Fara karewa,Sabo da kudi ko nawa ka Tara matukar basa Karuwa sai dai ka Zara to watarana za a shafa aji Babu komai. Gashi da takardunsu na Degree Amma duk sunce sunfi karfin aikin Gomnati Karami,Wanda ma Daddy ya nemowa wasu sun daina zuwa kudin yayi musu kadan.
Mami kuwa zuwa wannan tsawon lokacin Humaira ta yashe Mata Rabin dukiya ciki harda gadon Abdallah Dana Afrah,Daga Nan Humaira tace zata tafi Germany Hutawa zata dawo Nan gaba,ta cika rigarta da iska ta gudu ita da kawarta.
Saida ta Dade da tafiya sannan Mami taga Babu Rabin dukiya aka Fara bincike duk ta siyar da manyan kadarorin ta gudu,gashi Iyaye su Basu San ma an saki Humaira ba,lokacin da zata je Germany kawai dai tayi musu sallama tace Mami ce tace taje ta huta,Ashe Humaira tana Spain ba Germany suka tafi ba.

Mami tayi Kuka tana tsinewa Humaira Amma Babu damar ganin Humaira,ba a San a Ina suke ba,Ganin Haka yasa Mami tace aure zatayi ita wani me kudin zata samu ta aura Kar talauci ya risketa,gwara idan ta auri Hamshakin me kudi ragowar dukiyarsu zasu tsira kafin su Samu business da zasu yi ko Kuma kafin lokacin Abdallanta ya dawo.

Mami gata Kyakyawa da Yar kuruciyarta shuwa Arab Dan danan zawara suke Fitowa manyan masu kudi, katsam ta samu Alhaji Shehu Hamshakin Dan kasuwa ya Tara kudi ta aure abinta sai ji akayi an daurawa Mami aure a can garinsu, ya dauketa zuwa Abuja ita dasu Afrah suna can cikin daula.
Mami gani takeyi kamar ita ke tsarawa kanta rayuwa,Abdallan ma ba wani damuwa tayi dashi ba yanzu ta fiye son Kai,kanta kawai take so,Alhaji Shehu matansa biyu suna Kano da yaransa goma,Mami itace Amarya yar gaban goshi balarabiya Tana Abuja da yaranta,Alhaji Shehu katon me kiba ne Baki sai Muni Amma akwai Naira.
Su Rahmatu da sauran Mata dukiya ta Fara karewa an fara rage barna da kudi an fara tattali Don Kar ta Kare yanzu suke neman ya zasuyi su kafa kansu.

Kwanci tashi su Abdallah sun kwashe lokaci me Dan tsawo a kauyen Nan,Sunyi Masifar Shakuwa da Khadija Wanda Sam basa rabuwa sai in Khadija zata tafi wurin kwananta wato daji Bata iya kwana a cikin gidan wasu, kamar Kullum da safe yake zuwa ya nemota tazo tayi wanka,brush sannan suci abinci su fice yawonsu,tayi wankanta daure da Daura kirjinta tana dakinsu tana kokarin zata sa Riga Abdallah ya shigo dakin sabo da dama idan zata shirya waje yake fita ya Bata wuri,Ya gaji da jira Taki Gama shiryawa ya shigo ya isketa daure da zaninta a kugunta Kirjinta ba komai tana kokarin sa rigar, Kirjinta ya kalla da sauri sai yaji sun birgeshi,gasu wasu jajaye manya dasu a tsaye abin ya birgeshi Kam duk da be san Mene ba,Khadija Bata ma San ya shigo ba sai data juyo ta ganshi Yana Kare Mata kallo,da sauri ta tsuguna kasa tare da jawo zaninta ta daura a saman kirji sannan tasa rigarta t-shirt Fara ba ko bra,Skert tasa dan kanti me kyau cikin kayanta,Abdallah Yana gefe sai faman kallonta yakeyi Yana so ace yasan Mene ne a kirjin Khadija Haka,har ta Gama Suka karya duk motsin da tayi idonsa na kanta,Ficewa sukayi daga gidan suna yawo har cikin Daji wurin Zaman Khadija,Abdallah har dare yayi yau Bai tafi gida ba Yana tare da Khadija a Dajin Nan kusa da Yan shaye shaye.

Tsinkene a hannun Khadija tana Wasa dashi ya kalleta suka hada Ido ya basar tare da Sosa gemunsa da sajensa daya taru da yawan gaske,Zo muje saman katon dutsen cen mu gani Mene a kansa? Khadija ta mike tana murna zasu hau katon dutse,Sai da Suka hau har karshensa sannan Suka gangara ta baya ba motsin ko tsuntsu ga duhu.

Abdallah ya rike kafadun Khadija Yana me kafeta da idanunsa masu matukar kyau Wanda suke rudata,Abdallah yace na tambayeki? Khadija ta daga Kai Wai ae yace wannan mene a kirjinki Ni bani dasu,Khadija tace Nima ban sani ba Haka na ganshi Nima ko na baka daya kana so? Ae yace Nima ki manna minshi a kirjina,Hawaye ne suka Fara sintiri a fuskar Khadija, Abdallah ya rude Yana tambayarta lfy? Khadija tace Wai Ni wacece ne? Ya akayi bani da iyaye? Bamu da gida? Abdallah yace Nima ban sani ba,Jin kukanta yaki karewa sai ya rungumeta a jikinsa,Yaji Dukiyar fulaninta a jikinsa wani laushi Wanda hakan yasa Tsigar jikinsa ta tashi,jikinsa ya fara rawa,itama Khadija Haka sai taji ita Bata son barin jikinsa ta Kara kankameshi.

Juyawa tayi tare da daura bayanta a Kirjinsa ya zagayo da Hannayensa saman Albarkatun Kirjinta,Wata ajiyar zuciya ta saki shima Kuma Haka,Yana so ya taba Yana Jin tsoro sai yayi kamar gyara hannayensa yakeyi ta yanda zasu Dan gogosu sai ya zame,Khadija tana ji ita kadai tasan me takeji na Dadi a jikinta,Bama taso ya zame hannun nasa tafi so ya dinga gogar Mata su.
a hankali tace ai idan naje wanka taba su nakeyi Laushine dasu,Abdallah take so tayiwa wayo, shi kuma tsoro yakeji sai yace uhmm ba ruwana,Khadija ta kalleshi tace basa yin komai fa ka daina tsoro,Abdallah yaki yarda shi sai yace ba ruwana,Khadija ganin abinda yakeyi yasa ta Fisgo Hannunsa ba shiri ta daura saman Albarkatun kirjinta,Abdallah ya kwala ihu ya matsa gefe,Khadija ta biyoshi Yana matsawa ta rikoshi Kam Wai sai ya taba,shi Kuma yaki tsoro suke bashi,Kokawa suka farayi tukuru har suka Fadi kasa,Yan shaye shaye Jin ihun Abdallah tunaninsu Wani abinne ya samesu sai suka hauro saman dutsen da gudu suka Iske irin Kokawar da sukeyi kamar yan Dambe,suna ta dariya Khadija ita Dole sai ya taba,Tsaki Yan shaye shayen suka ja,Daya ciki yace wlh ban yarda da Yan birnin Nan ba,wannan yarinyar maybe satota yayi gashi sai iskanci sukeyi a garin Nan,Ogansu yace to Ina ruwanka Dalla mu Ware,Har Suka tafi su Abdallah Basu sani ba,Har Khadija ta samu Nasara yace zai taba sannan ta kyaleshi.

Ta tsaya tare da turo masa kirjinta tace to Gashi,Abdallah ya kalleta sai ya fashe da kuka shi bazai taba ba,Hawaye sai tsiyayo Masa sukeyi,Khadija tace to na daina kulaka Kuma sai na bar garin Nan,Tunda yaji tace ta daina kulashi sai ya rumtse idonsa Kam ya Kai hannu ya cafki daya da karfin masifa Ba Shiri Khadija ta kwalla Kara iya karfinta, shi Kuma yaki saki yace sai ya Ciro daya ya manna a Kirjinsa shima ya huta ganin nata shima Ya samu nasa,Sai da ta saki kuka sannan ya kyaleta.

Ta mike Wai tayi fushi garin zata Bari ta mike cikin Dajin shima ya bita a dinga tafiya har suka bar yankin suka Shiga wani yankin daban Kuma,ko gajiya basayi cikin uban duhun Nan suke ta faman tafiya har suka samu suka huta sannan Khadija ta tuna da kayansu Amma batayi hankalin su koma su dakko ba,Abdallah Bai tuna ba shima,can kasan bishiya suka kwanta tare,Khadija ta kwanta a jikinsa Bai manta da Dukiyar fulaninta ba Yana Jin tayi bacci ya lallaba a hankali tare da tura hannunsa a rigarta a hankali Wai Kar ta kamashi, sai da hannunsa ya Kai kansu ya shafo yaji wani shegen laushi sai ya lallaba ya zare hannunsa a fili ya furta ba ruwana Allah ya Baku hakuri,Khadija ta farka Jin Yana magana da sauri ya rufe idonsa Kam tare da yin baccin karya kunyarta yake ji,Khadija tayi tunanin bacci yakeyi sai ta dauki hannunsa ta Dora a saman dukiyar Fulaninta a Haka suka tsaya shi Wai kunya yakeji yayi mukus a Haka idonsa a kulle Wai bacci yakeyi.
Jikinsa ne ya tona Masa asiri da ya fara rawa Kar Kar Kar kamar mazari, sai kace Khadija ta samu wani Table ko bench Haka ta dafe shi da Hannayenta Wai jikinsa ya daina rawa tunaninta kamar kujera ko wani Abu marar Rai ne Ana girgizashi,Yana ta rawa karrrrrr ita Kuma ta dafeshi iya karfinta Wai ya tsaya ya daina rawa.

Sai tayi sauri ta cire hannunsa dake kirjinta sai ko ya tsaya cak jikin ya daina rawa,sai ta sake Dora hannun nasa Aiko jikinsa yaci gaba da karkarwa shike Nan ta samu abin Wasa sai ta Dora hannunsa a kirjinta sai ya fara karkarwa karrr sai ta cire sai ya tsaya cak sai dariya takeyi tana Haka shi Kuma kamar wani engine ba hutu,har sai data gaji sannan ta daina ya samu lfy ,ya wani matse idonsa tare da baccin Dole,itama tayi baccinta sai da Rana ta fito kwal sannan Suka farka tare da tsintar kansu cikin wani sabon dajin ba gida gaba ba gida baya.










AsmaBaffa
[12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: 🏵TUBABBIYA🏵









36-40








Official








By
AsmaBaffa






Yakasai,Mom Haneef,Serky Baby,Mrs Muktar Lambata,Zainab Dinawa,Ummihauwa,Raliya Nura lawal,Ummu Hamdana,Fauzat, Maryam Adnan and Maman Sauban.
Page nakune Fans Allah saka da Alkhairi.


MAMAN MASHKUR Ina godiya da Jinjina.








Khadija ta kalli gabas ta kalli yamma ta kalli gabas sannan ta kalli Abdallah,marartace ta Fara murda Mata,Abdallah yace a Ina zamu samu ruwa to? Sam bai kula da yatsina fuska da takeyi ba na ciwon Mara, Shuru tayi Masa sai yace sauri mu Kara gaba,Suna tafiya Khadija ta dafe mararta tare da durkushewa a kasa,da sauri shima ya tsuguna a gabanta Yana tambayarta me ya faru,Mararta take nuna Masa tana Hawaye,Hannunsa yasa a marar Tata Yana shafawa a hankali,Har ta danyi sauki sannan ya rike Hannunta suka ci gaba da tayi,Abu taji kamar ruwa Yana bin cinyoyinta,tana dubawa taga jini ne, tunani ta Lula ta kasa gane jinin Mene,sai ta fashe da uban kuka harda ihu,tsoro ne shima ya kamashi ganin jini na bin kafafunta sai Kuma can yayi Murmushi yace period kike Yi? Khadija tace Dama kasan sunansa? Abdallah yace yanzu na tuna shi,Zama yayi tare da Yi Mata bayanin jinin Haila da hukuncinsa harda wanka du,Khadija ta sani Amma yanzu Bata tuna ba sabo da Abdallah ya fita tunani a yanzu halin da suke ciki.

Jin ba matsala bace sai ta daina kukan,suna tafiya suka hango katon Kogi da ruwa garai garai ba kowa a yankin,Khadija tace muje can ga ruwa na wanke jikina,bishiya Abdallah ya samu tare da ballo musu itacen aswaki Suka Fara goge bakinsu dashi suna tafiya suna Yi har suka Isa wajen ruwan, Kallon Khadija yayi tare da cewa juya bayanki zanyi wanka,Ba musu ta juya Masa baya ya tube kayansa duka ya shiga gefe kadan tare da yin wankansa ba sabulu,Yana gamawa ya saka dogon wandonsa da Singlet sannan yace na Gama juyo,Alwala yayi sannan yace sai kiyi kema,tace to Dame zan shirya kaina na toshe jinin? Abdallah yace ga rigata t-shirt tunda Bata da girma sai ki Sa Haka,pant fa? Yace sai dai tight Dina tunda Dan karamine zai shigeki,

Murmushi Khadija ta saki sannan shima ya juya Mata baya ta Dan shiga gefe kadan ta cire kayanta dama skert da rigace a jikinta ta English wear ,Saida ta Fara wanke kayanta da pant din tas a ruwan sannan ta matsa wani wajen baya kadan ta wanke jikinta fes ta dauki tight din Abdallah Dan mitsili tare da linka Yar rigarta tasa ta shirya tsaf tayi kunzugunta dake tana da Hips sai ta cika Wandon daf,Rigarsa tasa sabo da tafi Tata tsayi har Rabin cinya ta kawo Mata,Fitowa tayi ta shanya kayan data wanke jikin wata bishiya,Abdallah ya kalleta ba karamin kyau tayi Masa ba,sai ta birgeshi rigar tasa ta amshi jikinta.
Suna zaune kowa yayi Shuru suka hango bishiyar Guava tayi manya manya da cashew gasu Nan sun nuna,Zuwa sukayi Suka tsinko da yawa sai da Suka cika cikinsu dam sannan kayanta sun bushe sai kawai tasa skert din pant din Kuma da rigarta ta rikesu a hannu sannan Suka bar wajen.

Mami zaune take saman Makekiyar Kujera ta nutse tana kada kafa duniya na Kai Mata,Alhj Shehu ne ya shigo tare da Zama kusa da Mami ya kalleta sannan yace Hajiyata ya akayi ne? Murmushi Mami ta saki domin ta yarda da Alhj Shehunta yanda yake nuna Mata kauna ba a cewa komai,Su Afra sai Abinda suke so shi yake musu sosai yake rikesu.

Baba har yanzu Bai hakura ba,Kuma baiyyi fushi ba neman Abdallah da Khadija yake ko Ina a fadin Nigeria,Ita Kuma Mami tana can duniya ta samu ta daina neman Dan nata ma gaba daya,Mama ma Addua sukeyi sosai akan Allah ya Bayyana Abdallah da Khadija,Hafsatu Kam ba ruwanta ganin Baba Yana Business Kuma Allah ya dafa Masa yanzu Yana samun kudi suna Jin dadi sai take ganin kamar abinda tayiwa Abdallah shine ya jawo Baba yake samun kudi,tunaninta da Abdallah Yana Nan da Baba bazai samu kudi ba,Bata yi tunanin duk abinda Allah ya tsaga zaka samu duk duniya Babu me hanawa,Haka idan baza ka samu ba idan duk duniya naso ka samu baza ka samu ba wannan a rubuce yake.

Ciwon marar Khadija ne ya dawo sosai,Kasa tafiya tayi,Abdallah ya tsuguna a kasa tare da cewa hau na goyaki,Da Sauri ta Dane bayansa har murna takeyi,tana bayansa ya mike tsaye yaci gaba da tafiya da ita Basu San ma Ina Suka nufa ba, suna tafiya har dare ya farayi ba gida gaba ba gida baya,Wasu gungun Yan Daba ne Suka yanko kwana kicif Suka ci Karo dasu Khadija tana bayan Abdallah tana baccinta,
Yan daban ne Suka kece da dariya tare da furta aiki ya Kare basai mun wahala ba yau,ranka ya Dade a sanarwa Oga Shehu ga dai dai shi an samu,Abdallah kallonsu yakeyi kawai har suka ce Kai sauke wannan yarinyar a bayanka,Bacci takeyi Dan Allah karku tasheta baiwar Allah cewar Abdallah,Surutu ne ya farkar da Khadija ta tsorata da ganin mugayen mutane Haka dauke da muggan makamai ba shiri ta sakko kasa daga saman bayan Abdallah,Ogan su ne yace Kai muje Mana, Abdallah zaiyi musu Khadija ta girgiza Masa Kai Suka bisu,Yan daban Suka tasa su a gaba tare da tafiya dasu salin alin.

Khadija tana rike da Hannun Abdallah Gam ta kalleshi suka hada Ido tare da sakarwa Juna Murmushi Mai kayatarwa domin yamma tayi lis yanayin garin yayi Dadi sosai suna Jin dadi,Yan Daban Nan suna satar Kallonsu yanda suke wani nishadi kamar ba kamasu akayi ba,ba ruwansu Basu San me duniya ke ciki ba, sai da sukayi tafiya me tsananin nisa Amma ko a jikin su Abdallah basa gajiya,sai can Suka hangi wani Dan karamin gida me kyau a cikin Dajin,gidan suka Karasa su Yan Daban sun gaji sosai da kyar suka iya karasawa sannan Suka kwaso lemuka da Ruwa suka Sha abinsu,Khadija tace muma a bamu musha,Ogansu ya gasa Mata Harara sannan yace Kai ya sunanku? Abdallah yace Sunana Khadija,Ni Kuma Abdallah cewar Khadija, Sigari Ogan ya kunna Yana bulbula hayaki yace Kai Baba wannan Yan rainin hankali ne Amma zanyi maganinsu Tiger dakko engine Nan kowa ka zana Masa Tatoo na sunansa daya fada Dan ubansu.

Wanda aka kira da Tiger ya dakko Machine din Tattoo Nan take ya Kama Hannanu Abdallah Damtsensa ba Imani ya kafa engine ya Zanawa Abdallah Sunan Khadija a Damtsensa,Haka ya samu itama Khadija a Damtsensa ya Mata round da suna Abdallah da Capital letter ko wannensu,Abdallah baiyi ko gezau ba,Khadija ce ma tayi Kuka sabo da zafi,suna zaune gaban Yan Daban Nan Suka ji Karar Mota,Wata dariya sukayi tare da furta gafa Oga nan yazo zamu Sha Kudi,Oga Shehu ne yazo tare da escort dinsa suna take Masa baya,Yana shigowa ya kalli Abdallah da Khadija farin ciki ya kamashi irin Wanda yake bukata,Kudade masu yawa ya bawa yaran nasa suna ihu suna Masa kirari,Khadija ce ta matsa kusa da Abdallah tare da rada Masa ya kamata na canja kunzugu na Kar ya Bata Ni, ok Ki Bari a samu wuri cewar Abdallah ya furta Yana Murmushi.
Kai ta jinjina gaba Daya Oga Shehu sai kallonsu yakeyi kamar maye ganin Basu damu ba harkar su sukeyi,da wasu ne da tuni sun Fara kuka Amma su ba ruwansu.

Yaransa yasa Suka shakawa Su Khadija Wata Powder tuni suka zube kamar gawa suna bacci Nan take suka zuba su a mota sannan Suka ja motar suka Kara gaba,Tafiya sukeyi dasu Basu tsaya ba sai da Suka shiga cikin garin Maiduguri sannan suka nufi wani katafaren gida na Alfarma Katon gate aka wangale musu motar ta danna ciki tafiya akeyi a cikin gidan kamar zasu je wata uwa duniya sai da akayi tafiya me nisa sannan motar ta tsaya,wasu yaran Oga Shehu ne Suka zo tare da fitar da Abdallah da Khadija daga motar Suka shigar dasu ciki,takalman mutane ne iri iri gasu Nan da kayan sawar Yara,Manya,Yanmata da tsofaffi gasu Nan Harda na Almajirai da talakawa,wasu takalmin ma da Leda aka daure,Ba kowa cikin wani katon Palo sai Dattijo a rakube jikin bango,ciki aka shigar da Khadija tare da Abdallah dake kwasar bacci.

Ruwa da Abinci yaran Oga Shehu suka kawo suka yi tafiyarsu,sai Dare misalin 11pm Suka farka daga baccin da Sukeyi,Mamaki ya kamasu ganinsu cikin gida me kyau Haka,Dattijon Nan dake karatun Qurani Suka gani Yana zaune gefe daya,Abdallah yace Dan Allah inane Toilet? Dattijon ya kallesu sannan ya nuna musu,Abdallah ya shiga Toilet yasha gyara sai kyalli yakeyi ta Bature,Harda yin wanka da sabulu me kamshi ga sababbin brush Nan da Toothpaste ya dauki sabo yayi ya shirya tsab yayi fresh sannan ya fito,Khadija ma ta shiga Haka tayi wanka da brush sannan ta shiga kwalawa Abdallah Kira tana Toilet,Dattijon Mamaki ya lubbeshi Jin Ana kiran Namiji da Khadija,Jikin Toilet din ya tsaya yace Mene? Tace ka bani daya rigar nayi amfani da ita,Yar karamar rigar ya Bata ta linka tayi kunzugunta da ita,Wanda ta cire tasa a bakar Leda Sannan tasa a dustbin ta shirya ta fito,Abinci Suka ci suka koshi sai Lokacin Dattijon ya musu magana.

Sannuku Yara,Abdallah yace yawwa,Dan Allah Tsoho me akeyi a wannan gidan? Dattijon ya kallesu Hawaye ya zubo Masa sannan yace Nasan Baku sani ba,Wanda yasa aka kawoku Nan Mashirki ne, kudin tsafi yakeyi,Akwai bokayensa da Suke sashi duk sati sai yayi Luwadi da Zina sannan ya samu biyan bukata,Duk takalman da kuke gani na mutanen da ya kawo ne Mata da maza idan yayi amfani dasu sai ya Sa a kaisu wani state din a watsar dasu,Abdallah Da Khadija Suka ce Sam su Basu gane me tsohon yake nufi ba,Dattijon yayi kokarin Fahimtar dasu Amma Basu gane ba,karshe yace idan an shigar daku wurin Oga to karku ci kome zai Baku kawai iya abinda Zan iya Gargadinku dashi kenan,Daga Ina kuke? Abdallah yace mu dai bamu sani ba,bamu sam mu su waye ba,Duk tambayar da Dattijon yayi musu Basu sani ba,anan ya gano ba kalau suke ba kansu akwai motsi.

Khadija tace Daga zuwa Shan Lemo shike Nan aka kawo mu Daji,Yanzu Tsoho Wai Mene Zina? Dattijo ya jinjina Kai yace Tunda Baku gane ba shike Nan abar Zancen kawai muyi Addua Allah ya fitar damu daga gidan Nan lfy,Kai Namiji Ga surori da Zan baka mu dinga karantawa Muna Addua,kema Haka mu dage mu fita lfy,Khadija ita tafi son rayuwa a daji cikin kunci take a gidan Nan sai tace ai Dole mu dage mu bar gidan Nan ba Dadi gwara Muna daji.

Allah sarki Yar bishiyar Madaci na,har na tuno da Dan Micijin Nan green Yana saman bishiya kullum Ni kuwa Ina kasa muyi baccinmu ba ruwanmu,Khadija ka tuna Wannan abin da muke ci wannan bishiyar me Zaki? Abdallah yace oh Kanya ko? da sauri tace ae har na tuno Dan katon dutsenmu da muke baccinmu Allah ya tsinewa mutumin Nan da ya kawo mu wannan Dan Iskan gidan muna rayuwar mu me dadin gaske,Dattijo Baki bude yake kallonsu irin alatun dake wannan gida Amma ace gwara Daji dashi gaskiya ba kalau suke ba gasu a Haka kamar masu Hankali.

Abincinsu Suka jawo Suka cinye tas tare da wanko hannunsu sannan Abdallah ya dinga jera Sallah tun Ana sa ran aidarwa har aka gaji yaki idarwa kawai zirarata yake tayi ba ko zaman Tahiya,Dattijon Yana ta kallo abin ya daure Masa Kai. Dattijon yayi yayi Khadija ta karbi Addua na karatun Qurani Taki,Sai Abdallah ne ya karba ya Kama Yi ba ji ba gani yaki dainawa, kwana daya ba a waiwayi su Abdallah ba sai da Suka kwashe kwana Uku a gidan Nan sai dai a kawo musu Abinci sannan Oga Shehu ya turo yaransa Kan a Kai Masa Dattijon,Abdallah da Khadija.

Ba duka ba zagi Suka tafi dasu zuwa wani katafaren part dinsa Suka samu Oga Shehu ya daura kafa daya Kan a saman lumtsumemiyar kujerarsa Yana karanta Jarida,Tunda ya kalli Khadija Yaji hankalinsa ya tashi ba abinda yake bukata sai ita,Abdallah dai adduar da Dattijon ya Basu yake ta karantawa a zuciyarsa,Oga Shehu ne ya mike ya Kalli Abdallah yace Ku kawo min na Fara gamawa da wannan,Abdallah Bai San me ba yabi bayansa tare da yaransa,bedroom suka shige yaran Suka ja kofa Suka koma,daga Oga Shehu sai Abdallah,Oga Shehu yayi wani surkullensa sannan ya shafi Hannun Abdallah yanda zai kasa magana sai abinda yace shi Abdallah zaiyi,Oga Shehu tunaninsa tsafinsa yaci yace Kai cire kayanka gaba daya komai,Tsirara zakayi,Abdallah yaki,yayi yayi Abdallah yaki ko motsi,a fusace Oga Shehu ya taso da niyyar cirewa Abdallah kayansa Baki daya,Nan Abdallah ya Kai Masa wani mugun duka abinka da Me Aljanu sai ga Oga Shehu ya tashi sama ya Fado kasa Damm....ji kake karas ya karye gida biyu a kafarsa,Oga Shehu ya saki Kara me firgitarwa Wanda gaba Daya yaransa sai da Suka taho da gudu,Abdallah ya fito da sauri Yana zuwa inda su Khadija suke kansa ya Sara ya Fadi a wajen,Dattijon ya shiga tofa Masa adduoi su Kuma Yaran Oga sun ruga dakinsa,Oga kawai ihu yakeyi Yana rokonsu akan su fitar Masa dasu Abdallah Baki daya,Da Gudu mutum biyu suka fito lokacin Abdallah hankalinsa ya dawo jikinsa Yana tashi Family dinsu ya tuna,Danginsa,iyayensa,rasuwar Daddy,Da Kuma farko abinda ya sameshi zai fita office tun daga Nan kamar me makuwa Haka ya dinga tuna rayuwar da sukayi da Khadija tun Hawansu mota har zuwa Kauyen Maiduguri da komai da sukayi cikin rashin hankali sai da ya tuna kaf,to me ya sameshi da har ya kasa gane waye shi da abinda sukeyi da Khadija a daji duk Bai gane ba sai yanzu.

Bai Gama tunanin ba Mutanen Shehu suka zo tare da yin waje dasu Abdallah Suka jefa su a mota suka jasu can bayan gari gefen titi suka watsar dasu sannan Suka figi mota suka yi gaba,Oga Shehu Kuma sun kaishi asibiti tuni.

Dattijon Nan sai kallon Abdallah yakeyi kamar wani Abu na damun Abdallah Amma Bai ce komai ba yace to Alhmdllh Allah ya fitar damu yanzu Ina zaku je? Abdallah yace Kaduna na tuna family da komai,Dattijon yace Alhmdllh to Ni a garin Kafancan nake suna na Malam Saleh muje Tasha sai ku shiga mota Nima na shiga tawa,Abdallah Ya kalli jikinsa mamaki ya kamashi kamar Mahaukaci ga uwar Suma,ga gemu Haka,Khadijansa ya kalla ya tuna itafa Bata samu lfy ba,tana Nan a rashin kwakwalwarta, Aljihunsa ya duba sai yaga Yana da 5k a ciki da Atm card dinsa guda Daya,Kudin ya cire ya tare Taxi Suka shiga yace a kaishi Bank,Sai da aka Fara Kaishi ya cire kudade masu Dan kauri

Please Login or Register in order to submit comment