Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga Uku na Mutu na Gama wayyoooo....hattana tsuntsun gidan Saida ya farka kowa hankali tashe ya fito aguje Abdallah Bai tsaya wani bin Hanya ba Kamar wani Sunnil Shetti Haka ya tsallake flowers masu tsayin gaske, Khadija Bata daina ihu ba,Makwafta duk suka farka a bacci Ana ta buga gida a bude aji ko lafiya me ya faru Mata da maza.

Khadija ihunta take tana burbuwa da uban kukan gaske,Ana zuwa Baba yace me ya faru kunama ce ko miciji? Abdallah ya mikar da Abarsa tsaye Yana duduba jikinta ko lafiya? Khadija ta Kara tsandara ihu harda tsalle tana yarfe Hannu,Mama tace Zan mareki wlh idan baza kiyi magana ba duk kin Tara Mana jama'a, Mami ta matso tana Mene ne Yata? Khadija sai lokacin tace Baba Wai Abdallah ne zaiyi aure zai dawo da Humaira Kuma cutar Kanjamauce da ita tana da Hiv yace shi ba ruwansa Haka zai auro ta Ni wlh yaji zanyi.

Baba da Abdallah Babu Wanda ya gane nufinta Baba yace Khadija Aljanunki ne Suka tashi yaushe Humairan Ta dawo? Tsaki kowa yaja dake wajen suna Amma kin cucemu Muna baccinmu,Mami tace mune da laifi ke Baki San Wasa ba Khadija tsokanarki fa akayi,Abu ta sheke da dariya tace Yanzu ke daga fadar magana sai ki yarda har da Kara karyarki Wai cutar Hiv to mu bamu ga wata Humaira ba,Sai lokacin Abdallah yace a'a wlh laifinku ne ya zaku dinga hada min wuta nida Khadija Dan Allah,jiba yanda baiwar Allah ta koma Rana daya duk ta rame ta fita a hayyacinta,Ni dai Dan Allah ya Isa Haka wasan Nan ku kyale min abata Haka Ina sonta zatayi hankali,Abu tace Kai muke taimakawa wannan Bata San zuru ba, Abdallah Rai bace yace Ni dai ku kyaleta ki daina Hadani da wata Humaira,Khadija Jin Wasa ne sai taji kunya Amma duk da Haka tace Allah Baba kayi musu fada,Masu Gadi ne suka leka waje tare da Sallamar makwafta nasu ganin kwaf sukace Yar matsalace komai ya Zama normal.

Abdallah Kuma ganin kowa ya tafi makwancinsa sai ya tsuguna Khadija ta Dane Bayansa suka wuce bangarensu,har sukaje room tana shesheka, dama yayo musu take away na kaji, tayi Shuru kamar yau aka kawo ta gidan miji, da kansa yayi Mata wanka da ruwa me zafi,ya shiryata sai binsa takeyi da kallo har ya Gama ya bude Mata abincin Nan ma ya Bata a Baki sai da taci ta sannan sukayi brush yace to kwanta sarkin Kishi, mukus tayi Bata ce komai taji kunya da irin ihun data dinga yi, sun kwanta Yana bukatarta Amma Bai nemi hakan ba, da kanta Kuma ta juyo ta Fara kissing dinsa tana shashafa shi Bai kulata ba, tace to muyi Mana,dariya ta bashi ya kanne da kyar tare da cewa me zamu yi? a'a ke da bakya Abu Dan Allah sai dan gudun kishiya, Haka zaka ma? Ai dai sonka ne yasa nake kishinka Kuma Ni badan kishiya nayi ba Amma tunda kace Haka na daina kulaka ma ta matsa gefe,da sauri yace Wasa nakeyi Ya jawota jikinsa ya shiga Tsokanarta suna dariya daga Nan wasan nasu ya canja salo da fasali ya koma na love.

Da Alama Abdallah Yana Jin dadin harkar Nan yanda yake wata farfadiya abin sai Wanda ya gani, Khadija yau Dadin shagalin Nan nasu taji domin ba irin Kalar kukan daba tayi ba itama Harda sambatu, sai da komai ya lafa Suka samu nutsuwa Tare da tsarkake jikinsu,Khadija ta zauna gefen bed tayi shuru tana tunani ita kadai tana wani Murmushi tana Jin Dadi ita daya Har Abdallah ya Gama fesa turaruka Yana kallonta ta Mudubi abinda take tayi kamar me aljanu.
Saida ya Gama ya zauna gefenta yace my Khad Me kike tunani ne? Ido ta rufe da tafukan Hannunta a hankali tana dariya kasa kasa tace Nidai a bawa Jaruma Hakuri Ashe tana da daraja haka,Dariya Abdallah ya shigayi Dan Khadija Shirmenta yawa ne dashi, Yace Yanzu kin fasa yankata? Keda Kika dinga zaginta,Kara boye fuska tayi tana dariya tace Dama Ana barinta a gida da sai ka dinga tafiyarka Office kana bar min ita a gida Ina ajiye maka ita, Abdallah ya dinga dariya kamar me.

Yanzu Khad Beauty idan na bar Miki ita wa zaiyi aikin to? Jikinsa ta fada tare da boye Fuskarta a Kirjinsa tace to ai kawai boye ta Zan na Yi Ina kula da lafiyarta, Ni yaushe zamu tafi gidanmu? Mami ta warke gashi Jibi zata koma part dinta a Family House, Farin ciki ya Kama Abdallah yace da gaske kin yarda? Kai ta daga Masa tana Murmushi,Yace Hmm banyi zaton Zaki Amince yanzu ba,nifa ban son Zama a Nan ki zaba Abuja ko Lagos? Khadija ta wani Kara lafewa ajikinsa Sannan tace duk inda kake so farin cikinka Baby shine nawa.
Abuja nafi so,Ok Allah ya kaimu,Ameen Abdallah ya amsa sannan suka kwanta suna Hira har Bacci ya kwashesu.

Washe gari da safe Haka Suka sake goge juna Shuru Babu Wanda yaji motsinsu,Khadija Abinci kawai tasa me aiki ta kawo musu kawai love suke Sha kamar zasu cinye juna sabo da suna Jin dadin junansu matuka.

Usman yazo wurin Abinsa suna ta zuba hirar soyayya,so yake Abdallah ya fito su tafi inda Baba ya aikesu sun ajiye Alkawari da Abdallah 9am zasu Fita Amma ba Abdallah ba labarinsa,wayarsa ko an Kira ba a dagawa, Abu ta koma Kiran Khadija itama ba a dagawa har 12pm Shuru,sai da Kiran yayi yawa sannan Khadija ta dauki wayar Abdallah tace Hlo Ya Usman Ina kwana, ya aiki? Bacci yakeyi Bai Jin Dadi sosai, dake Usman Dan duniya ne sai yace Kinga Khadija karki min wani karya Dan Allah malama ki bawa mayen yaron Nan waya,Abdallah Wanda Khadija ke Masa tausa ya karbi wayar sai lokacin ya tuna da Aiken Baba,Tsaki yaja yace Kai Usman nifa Ba gwauro bane irinka shike Nan Mutum bazai huta ba? Zagi Usman ya kunduma Masa Mayen mace Harijin banza ka dai tuna Aiken Baba wlh na baka 30mnt ka fito mu wuce.

Wayar Abdallah ya kashe ya kalli Khad dinsa da Tsantsan so da kauna Yana wani narke Mata yace Beautyna zamuje Unguwa Baba ya aikemu zamu aika wasu Doc England Dan Allah idan kinje ciki ki dawo da wuri Nan kafin na dawo nafi so Ina dawowa na ganki ok? Kai ta daga Masa tana Murmushi tace Zanyi missing naka Sweetheart, me too Baby zo ki tayani wanka na shirya na fita Kar mayen can ya dameni,Yanzu mukayi wanka fa ko wani zaka sake? Kina min wannan tausa me Dadi ai Dole nayi wanka, dariya sukayi gaba daya tare da tayashi ya shirya sannan ya fito yaci uban wanka kamar wani Ango ta rakashi ya tafi.

Itama sai data gyara part din Kal ko Ina Yana sheki sannan ta shirya taje wurin su Mami daga Nan suka Hadu dasu Abu suka dinga Hira Khadija harda Basu Shawara Abu wlh kuyi Addua ayi ayi muku aure Kunga Niimar data ke cikinsa sai Wanda ya gani,Yara Kuna Shan wahala Allah sarki an barku a baya,Abu tace munafuka kawai kice Majalisi ya Kama da wuta,Merry ta sheke da dariya tace Kamar ba ita ke guduwa ba,Husna karama tace hmm daga tayi muku waazi,Khadija tace ke tashi ki bar Nan fitsararriya manya na magana kina saka Baki kina kallon bakinmu, Husna ta girgiza Kai Allah Baku hakuri Amma girman Nan Nima nayi shi ss2 fa na shiga ko Aure akayi min daram Zan zauna, Khadija ta kalli kanwar tasu tace naga Alama to fita ki koma Dakinki ai dama Mama tana kitchen kije ki koyi girki.
Husna ficewa tayi tana kwafar haushi.

Yinin Yau Khadija da Abdallah text kawai na kalaman luv suke ta aikawa juna,har dare Basu dawo ba, sai 9am yace gasu Nan dawowa, sai data ji saura 1hr ya dawo taci uban wanka tare da Sa kaya na Jan hankali, tana wajen Mami ya dawo ta fada mishi a waya tana Taya Mami shirya Kaya,shi yasa ya wuce tare da yin wanka yayi Shirin bacci sannan ya kirata a waya,dama sanye take da Hijab sai da ta sake gyara jikinta da Fuskarta sannan tayi musu sallama ta tafi,tun kafin ta Karasa ciki ganin Abdallah tsabar Jarabar Khadija taji tayi wet ta cika makil.

Yana tsaye Yana kokarin Jona wayarsa a a charge sanye da short Khadija ta Fada jikinsa tare da Masa wata zazzafar rungumar Daya manta ko jona wayar baiyi ba ya dauketa cak kamar jariya suna sakarwa Juna Zazzazfan Murmushi me dauke da aburansan kauna Yana shiga zuciyoyinsu kamar Ana harboshi.

Au na manta abincinka Bari na koma na dakko,An hutar dake yauma akwai take away sai kin ture.
Love ma sai yau akayishi Ashe jiya ba komai bane akan na yau Sabo da yau Kuma sabon style sukayi a nutse yake binta itama haka, ya gano Khadijan tasa jarabarbiya ce dai dai dashi take ba karamar jaruma bace ta gaske shi yasa baya iya hakura da ita,baya iya salala Mata Kuma bazai taba iyawa ba shi Kam.

Washe gari Mami ta koma Family House tare dasu Afrah Su Rahmatu da yaran gida sai Murna sukeyi,Abdallah yaje Mami tace Abdallah kudin gadonka? Mami karki damu na Dade da yafe muku komai ba damuwa,Murmushi Mami tayi tace har yanzu akwai kudade masu Dan yawa mun Gama yanke Shawara da Afrah kawai ka rike ka hada su,Fafur Abdallah yace Mami Ni Ina da kudi ki rike duk abinda kike so kuyi dasu ba matsala,Dole Mami ta hakura ta kyale tana sawa Abdallah Albarka.

Bayan sati Abu ta koma kauyensu yayin da aka Kai kudin auren Usman tare da Sa Rana daya dasu Firdausi da su Omar,Khadija sai Murna takeyi Abu zata shigo family itama,Bayan wani lokaci Abdallah ya Gama tsara gidansa na gasken gaske a katafariyar GRA ta manyan masu kudi a Kaduna Sabo da Mami tace Bata yarda ya bar dangi ya koma wata state ba,Dole ya hakura,Mama daf take da Haihuwa itama.

Abdallah Haka ya biya musu aikin Hajji shi da Khadija suka je tare da zuwa kasar Russia Hutawa daga Nan suka dawo Nigeria,steal suna gidan Baba Allah ya sauki Mama lafiya ta haifo danta Namiji katon gaske Kyakyawa sai Murna sukeyi,ranar Suna yaro yaci Sunan Daddy Yousuf ana ce Masa Prince lokacin ne Mami taje Dubai ta hadowa Khadija lefe akwati Tara Kaya na alfarma masu tsadar gaske Wai akan ba ayi Mata lefe ba tayi Mata sabo da kyautatawa,Murna su Khadija dasu Mama, Ranar Saturday Abdallah da Khadija suka tare a katafaren sabon gidansu na Alfarma,gidane part uku sama da kasa ya Hadu karshe Babu abinda Babu na more rayuwa,Bayan sun tare da Sati hudu Abdallah ya Sa Khadija a private University me kyan gaske tana zuwa.

Ana zaune lfy kowa lfy cikin nishadi ranar Friday sai ga Mariya da Yaranta biyu Salman da Sakina sunzo Family House Neman Mami,Basu samu matsala ba suka Samu ganinta tana palonta Suka gaisa a mutunce Babu Wanda yasan wani ,Mariya tace Sunana Mariya Uwar gidan Alhj Shehu,Mami tace ok Sannu,Mariya taci gaba Alhaji dai Allah yayi Masa rasuwa,sannan ya bar wasiyya akan Azo a nemi gafararki ki yafe Masa,Mami tace Allahu Akbar Allah ya ji kansa na yafe Masa Allah ya yafe Mana Baki daya.
Sai yamma lis suka bar gidan bayan sunyi musu sallama,Mami tayi jimamin Mutuwar Alhj Shehu har Abdallah yazo ya isketa a haka.

Mami lafiya kike kuwa? Abdallah ya tambaya,Mami tace Alhaji Shehu ne Wanda na aura ya rasu, Abdallah ya tabe baki tare da cewa Allah yaji kansa Wai Mami Baki da pics dinsa? Wayarta ta jawo ta kamo Hoton Alhaji Sheshu ta nunawa Abdallah,lokacin Mamaki ya Kamashi yace Mami ai na sanshi Nan ya kwashe labari lokacin da Oga Shehu yasa aka kamasu da abinda yake Shirin aikatawa garesu,Mami tace wato shine yace Hatsari yayi Allah ya kyauta ya Kara kiyayewa,Ameen Abdallah ya furta daga Nan suka Fara Shirin Bikin su Abu dasu Firdausi.








AsmaBaffa.
[12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: 🏵 TUBABBIYA🏵








91-95







Official








By
AsmaBaffa








DIYAR KATIBI page dinki ne.

Ina gaisuwa fans Wanda suke ta nemana da bibiyar ko lafiya nake, Nayi zazzabi ne Amma na warke Insha'Allah very soon ma zamu Fara sabon Novel.










Yau Saturday Abdallah ya fita sai 5pm ya dawo sabo da Shirin biki da suke tayi, yau ba Schl Hajiya me Majalisi Ana gida taci uban Wanka Kamar zata je Dinner Haka tayi mugun kyau tana Kamshi ta fito main Palo ta hakimce tare da kunna tv,Wani Yar kiba da kyau take karawa tayi wani irin haske tana Shining, Zamanta kenan taji Dirin motar Abdallah,Murna da farin ciki ta Fara yi, kafin ma ya shigo har ta mike tsaye Kamar wani sarki ne zai shigo, Yana zumudin ganin sarauniyarsa ya shigo da Sallama dauke a Bakinsa yasan tana Palo Tasha uban kyau tun kafin ya karaso yake Jin kamshinta, a nutse ta Karasa gabansa kamar wata sarauniya ledar Hannunsa ta karba tare da rungumeshi a jikinta suna shakar Kamshin juna a hankali ya Fara kissing dinta suna tsotsar bakin juna Kamar me,Sai da Suka dauki dogon lokaci sannan ya kyaleta,tace Sannu da zuwa My King,Kasha gajiya masu biki sun Hana min miji sakewa,Murmushi yayi tare da furta dauki abinki naki ne, sai lokacin ta bude Ledar tana Murna kamar yanda ya Saba kayan ciye ciye ne iri iri masu tsada da Dadi harda Ice cream manya roba hudu,ya rigada ya Saba shi Baya shigowa gida Haka Babu abin Lashe Lashe Haka yake ya Saba.

Tana murna tace wow Thank you so much my Husband,Allah ya Kara budi da arziki na halak masu Albarka,gaskiya nayi sa'ar miji sai abinda nake so Allah Kara maka lafiya da Nisan kwana, tare dake My Khad, Godiyan yayi yawa Haka muje ki tayani wanka na gaji yau bacci nake ji, Wani Dukul Khadija taji a ranta ita Sha'awar mijinta takeyi yau,gashi taci abubuwa masu Kara lafiya da sha'awa sai da ta Gama Shiryawa yau amma da Alama ya gaji yau.

Sabo da gudun Kar ya Kara tayar Mata da Hankali tace kayi wankan Bari na kawo maka Abinci sama ba sai mun sauka Dining ba Tunda ka gaji,Alright My Khad, sai da ta Bari ya Gama shirinsa cikin Jallabiya Fara,lokacin Magrib har tayi Sallah kawai yayi itama Khadija tayi a dakinta sannan ta shigo dauke da tire, kallo ya bita dashi har ta sake wanka tayi wani uban shiri daban na musamman cikin kana Nan Kaya na daban kusan ace tsirara ma ma take,Bai taba sani dasu ba Dan Babu a lefe,da yawa tana sa Kaya masu Uban kyau da daukan hankali Amma ya rasa Ina take siyosu tunda ko a kasar waje da Suka je yasan iya Wanda ta siya duk yawansu, kallonta yakeyi tayi Masa kyau,yace Khad Wai Ina kike samo wasu kayan ne? Murmushi tayi tace Wasu a Online nake yin order,kudin Kuma fa? Ya tambaya,idan ka bani Mana kace ko Zan siyi Abu dasu nake siya accnt nake sawa nayi order ta abinda nake so,Murmushi yayi tare da Furta 'yar gayu kinyi kyau kin iya zaben Kaya sosai Allah dai ya miki Albarka matata, Ameen ta amsa.

Kallonsa tayi Yana cin abincin Yana Santi tana dariya kwantar da kanta zuwa kirjinta tayi a gadon bayansa, a hankali tace My King ya amsa Na'am ya akayi ne Khad Dina duk yau na ganki wani iri me kike so ne? Khadija ta Kara narke Masa cike da Shagwaba tace I need you Amma naji kace yau ka gaji bacci zakayi,farin ciki ya Kama Abdallah da halin Khadijansa ba boye boye da wani gulma shi yasa yake jin dadin rayuwa da ita,shi Kam ya tsani zaman karya da boye boye,komai baza a Fadi gaskiya ba,baza a nunawa miji gaskiya ba,ka rasa gane Kan mace tana ta pretending komai ba gaskiya,sai dai Namiji shi kadai shine marar aji,shine zalamamme,shine marar kunya etc.

Kuma Dan na gaji a jikina sai aka ce Miki bazan iya wannan ba,ai gajiya daban wannan harka daban ai sai dai na huce gajiyata ma,tunaninki bazan more ba? Ki daina wannan tunanin kullum banyi da yawa ba nayi sau daya sau biyu,ba a so ne kawai yayi yawa ko yayi kadan normal Normal kawai.
I love you My King Khadija ta furta love you too Beb ya Furta Yana Mikewa ya Shiga Toilet ya wanke hannunsa da brush ya fito ya jasu Jam'i sukayi sallar Isha tare da adduoi sannan ya kashe kayan wuta tare da kulle ko Ina ya dawo suka kwanta.
Nan fa Khadija ta Raina kanta sai da Abdallah ya biya Mata bukatarta yanda takeso sannan Suka sararawa juna.


Bikin su Abu yazo Ana Shan Shagali sosai anyi Dinner sai da aka kawo Abu gidan Usman Hadadden gaske sannan akayi Dinner, su Firdausi da ango Sulaiman, Omar da amaryarsa Hanna, sai Halima da Ango Bashir gaba Daya anyi nasu an Kai amare lfy,Abu ce sai da aka kawota sannan akayi shiri tare da yin tasu ita da Usman Wanda Ana gamawa Abdallah ya dauki Ango da Amarya ya maidasu gida ya wuce gida abinsa.

Usman gidane na Alfarma me kyan gaske da motocinsa biyu Dalla Dalla dasu,Abdallah shi yayiwa Abu kayan daki komai da komai ganin iyayenta Basu da karfi ya dauke musu nauyi tare da zubawa Abu Kaya na Alfarma.
Khadija Kuma ta dauko Nauyin gyaran Amarya Abu ba karamin kyau tayi ba,shi kanshi Usman Bai San yayi Dace ba sai daya ga Abu daf da biki gaba Daya sai ya sukurkuce.

Usman dama shi yasan Mata kafin Allah ya shiryeshi ya tuba,Allah yasa yanzu Kai ya waye kafin aure sai anyi test Kuma Alhmdllh Amarya da Ango lfy suke ba wata matsala.
Abu sai kuka takeyi Yan uwanta duk sun watse ba Wanda ta sani sai mijinta, da kyar Usman ya lallasheta,Bayan sunyi Sallah da kyar ta yarda taci Kazar Daya Bata a Baki suka koshi da fresh milk,Shirin bacci sukayi,Rigar baccin da Khadija ta ba Abu tasa yau tayi fitsara da yawa Abu kunya ta kamata zata cire ta canja wata cikin na lefe Usman yace ki bar min ita Ina so kinyi kyau,kin ganki kuwa gaskiya nayi Dace Allah na gode maka.

Abu kawai ta fashe da kuka,Usman yace Lfy? Me ya faru pls ki daina kukan nan,kamar bama son juna,Abu tace to ai Kaine kace kayi Da ce,Usman yayi dariya to me kike so nace banyi Dace ba ko me? Abu tace to me ka Dace dashi, Murmushi yayi kawai tare da cewa ba komai sai da Suka Gama komai sannan Suka kwanta,Abu dai tana tsoro tsoro Amma tunda ya Fara Wasa da sassan jikinta Yana Murzata son ransa,taji dadin gaske sai ko tayi luf tana maida Masa martani,sai da Suka ka Kai karshe sannan Usman ya Nemi Majalisi tare da baje hajarsa a ciki,Abu ta bashi mamaki da batayi kuka ko kadan ba,kawai dai yanda takeyi ya nuna tana Shan azaba kwarai,shi kanshi yasha wahalar shigarta sabo da Yarinya ce kuma Real Virgin.

Wani sambatu da sauti yake fitarwa iri iri gasu nan Yana yabon Abu,Ya Dade Yana aiki har Abu ta Fara gajiya zata Fara kuka.
Sai da yazo gasata sannan tayi Dan kuka kadan,sai da Suka Gama komai sannan Suka kwanta Yana zuba farin ciki da Murmushi ya rungumeta jikinsa tsam bacci ya kwashesu.

Dai dai wannan lokacin Khadija tana jikin Abdallah suna kwance ta duba agogo taga karfe 1 na dare tace Uhmm Allah sarki Abu Ana can Ana kuka yanzu,yau Abu zata Gane kurenta wurin Usman, sarkin sa ido Ina ruwanki? Cewar Abdalla, Dariyar mugunta Khadija tayi Abu yau Majalisi yaga ta kansa,kowa ance Miki irinki ne shagwababbe? Cewar Abdallah,Khadija tace hmm Ni ko Gobe idan Zan wuce schl Zan biya ta gidan Abu saboda nasan sai an Kai Mata dauki Ya Usman mayen Mata ne tun tuni, kije kiyi Mata me? Baza kije ba Schl Driver zai ajiyeki,Pls Honey kaga fa magani Zan Kai Mata Wanda zata warke da wuri ba Wai sa Ido zanje ba,Alright na yarda idan maganin warkewa ne kije Amma kawai ki kwashi kafa ki tafi gidansu da Sassafe.

Washe Gari 9am Khadija Driver ya tafi Kaita schl tasa ya Fara kaita gidan Abu,Abu tana kitchen ma tana soye soyenta taji Khadija tana sallama,Fitowa tayi tare da bude Mata kofa,Khadija mamaki ya kamata tabi Abu da kallo Tana Abu Wai Dan Allah lfy kike? Babu abinda yayi Miki,jiba irin wankan da Kika dauka da safe Haka, Dariya Abu tayi wlh tunda na ganki nasan sa Ido ya kawoki to Lfy nake ko kuka banyi ba don Ni jarumar mace ce,ba irinki bace daga an tabaku sai kuka,Karya ne Abu ban yarda ba kawai daga Miki kafa yayi jiya,Abu tace wlh yayi sosai ma kawai na daure ne, Sam bazan yarda ba cewar Khadija na wuce schl gobe Zan dawo da safe sai na kureki Abu ki gaida Ya Usman tayi waje abinta.

Washe garin da safe Khadija zata je schl Haka ta sake tsayawa gidan Usman ta Iske Ango da Amaryarsa a kitchen suna girki tare,Khadija ta sake ganin Abu ras da ita sai da taji kunyar Usman Amma duk da Haka ita Bata yarda ba sai cewa tayi Maybe sai Abu ta cika 3 days a gidan Zai Fara Shan Amarci.

Daga gidan Abu tana schl sun Gama text kenan Dama tana Jin Dan Zazzabi da tashin zuciya sama sama,suna Fitowa tare da frnds ta shiga sheka Amai ba ji ba gani,Allah yasa Driver yazo daukanta,a waya ya Kira Abdallah tare da sanar Masa,Lokacin Abdallah yana Office hankalinsa ya tashi kamar zai tashi sama ya tuka mota ko Driver Bai jira ba,kafin yaje ma tasha Paracetamol ta Danji sauki sai gashi hankali tashe,Aiko yaji ance ai Tasha magani ya dinga masifa akan me zata Sha magani idan ciki ne da ita fa?sai ya zube,Daya cikin kawayen Ramlat tace ai paracetamol kawai Tasha ba wani magani bane,koma Mene Bai kamata ba cewar Abdallah ya furta tare da Sallamar Driver ya koma da motar gida,shi Kuma ya dauki Khadija Kamar wata jaririya tare da sata cikin mota ya tuka abarsa Yana Mata Sannu ,tuni Bacci ya kwashe ta a motar.

Koda Suka Isa gida Sai da ta Kara sheka wani Aman Yana kula da Abarsa duk ya tashi hankalinsa Kuma ta Hana aje Hospital Wai ita kalau take,Sai da tayi wanka ta kwanta sannan tace Dan Allah Baby Ina za a samo min Naman ganda shi kawai nake bukata,shi Zan iya ci,ai sai dai naje Wurin Mami itace kadai zata iya Nemo Mana, Abdallah da sauri ya sake tuka mota sai gidan Mami Family House bazai iya musu waya ba, zasu Bata Masa time Khad dinsa ta gaji da cewar sa, Mami suna tare dasu Rahmatu a palo suna hira sai ga Abdallah ya shigo hankali tashe kamar zai Fadi Mutuwa,Suna gaisawa yace Mami akwai Naman Kai a Gidan Nan? Khadija ce Bata da lfy take son ci Baki ganta ba Mami duk ta rame ya furta kamar zaiyi kuka,Mami ta kalleshi sai tayi dariya itama Rahmatu dariyar tayi.

Sai Abdallah yaji haushinsu ya za ace mutum Bai da lfy su tsaya dariya,Mami ko har yanzu bakwa kaunar Khadijan tawa ne Wai? Ban gane

Please Login or Register in order to submit comment