Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mamakin Mami Abdallah yake kawai Amma Bai ce komai ba Dan kar tace yaki zabinta,Mami tana washe Baki tace Bari Afrah ta kawo maka abincinka Allah ya maka Albarka Abdallah,Ameen ya Furta ransa a bace domin Mami Bata taba sawa yaranta albarka sai dai zage zage Amma yau Dan kawai tana son ya auri Yar me kudi shine harda sa Masa Albarka Allah ya shiryi Mami cewar Abdallah.

Tv ya kunna Yana kallon News sai ko ga taronsu da Khadija ta halatta Ana nunawa,Khadija tayi shegen kyau ya furta a ransa,Yana Kare Mata kallo kamar wata Balarabiya Haka ta fito,a ransa yace Ashe ta iya gyara kanta yarinyar Nan,ganin an nuna jawabinta a matsayin matar da Abdallah zai aura ta mike Kuma ta kawo shawarwari Bai San sanda ya Kama yake hakora ba Yana Murmushi tana gamawa har da tafa Mata kamar Wanda a gabansu take, tana ta rubutu a Dan paper yasan Shi zata bawa,a fili ya furta Dole nayi Miki kyauta.
Kyale tv yayi sannan ya kunna gidan radio ma ya fara saurarar nasu labaran sai gashi kuwa anyi da Jinjinawa Khadija da akayi a matsayinta na Yar yarinya ta kawo shawarwari masu kyau.
Abinda Abdallah Bai sani ba Mami dasu Afrah suna Kallon News Suma sai gashi sunga Khadija ta bayyana kanta a matsayin matar da Abdallah zai aura,kafin kace me Yan gidan ma duk sun samu labari,sannan sun gani har frnds na Abdallah da abokan Business nasu,Daddy da sauran masu ruwa da tsaki.

Ran Mami ya baci matuka,Hafsatu matar Baba sabo da faccalanci sai gata ta suro katuwar jarkar Man gyda Wanda ya Kare a kitchen ta fito tsakar gida fili kamar zararriya da ludayi guda biyu na juya Miya ta Fara kida dam...daram... dam...Dam...dam..kaf...kaf...dum...Dum...ita Kuma kishiyar Mami Amaryar ta fito tana guda Ayyiriri mijin tubabbiya, anan aka Kare,Ina me kudin yau? Yaran kishiyoyi Dana Hafsatu Matan Suka fito suna habaici har da masu dakko farantai manya na silver da cokula suna kida ba ji ba gani,Mami tayi tagumi a daki,Afrah Suka yi mukus a daki,Abdallah ta samansa window ya leko yaga duk abinda sukeyi,yasan Mami yanzu zata zo sai ya sakko yabi ta baya ya figi mota tare da barin gidan Baki daya.

Khadija Koda ta gane me suke nufi suna kida ita kanta jikinta rawa ya fara tana tsoron Mami,ga Daddy baya gari,ba Mama da Baba da sauran Yan uwanta,Khadija ta sama ta hango Mami ta fito a fusace tare da fadawa part din Abdallah,ganin baya ciki tasan ya Gudu sai ta nufi part din su Khadija tare da Securies guda biyu tace ku samu kuci uban yarinyar Nan,kuyi Mata mugun duka,Khadija taga Mami ta Mika musu keys da yawa tace idan kofa Bata bude ba ku balla min kofofin Baki daya.

Kowa a gidan tsoron Mami
Yake ji don Haka masu kida nayi yaran gidan Sunyi mukus,Khadija da Gudu ta sakko tare da fita itama ta kofar baya data bi ta kitchen,a hankali ta lallaba dare ma yayi Amma Haka Daga ita sai short Wando pink da T-shirt Fara bako dankwali ta fito a hankali har ta bi ta dayan gate din na karshe Wanda baza a ganta ba,me gadi na bangaren suna ganinta Basu san me ya faru ba Suka bude Mata kofa ta fice da Gudu tana dariya ko tsayawa batayi ba Titin layin tabi tana tafiya a hankali har tayi nisa da gidan,Hadaddiyar motace ta tsaya a gabanta kadan Baya ya dawo me motar tare da sauke Glass na saitin Khadija,Tana kallo sai taga Ashe Abdallah ne,da sauri ta balle murfin motar ta shige gaba,ya figi motar Suka bar unguwar Baki daya.

Mami kuwa suna murda Handle Suka ji kofofi a bude,ta shiga Palo tana zunduma ashar iri iri Amma Suka ji shuru,ko Ina Suka duba shuru ranta ya Kara baci Dole ta hakura ta koma part dinta tana saka irin yanda zata ci uban Khadija da Abdallah kawai.

Kida ya saki a motar Khadija harda ihu yessoooo tana Daga hannu sama tana rawa a motar a zaune,Dariya ma take bawa Abdallah ba dama taji kida sai rawa,wani mall tsaya tare da shiga ya siyo Mata katon Hijab har kasa me Hannu Arsh color tare dasu Ice cream da kayan ciye ciye masu Dadi na Yan gayu,Hijab din ta karba tare da cewa tnx,Bai ko kalleta ba ya daura Mata ledar kayan tande tande a cinyarta,Hijab din tasa ya Mata Masifar kyau,ba jira ta bude Ice cream dinta ta shiga shatare da kilishi me Dadin gaske,Da kyar take magana sabo da Dadi,Yago kilishin Naman tayi tare da bashi a Baki gashi tunda Driving kakeyi,ba musu ya bude bakin ta saka Masa Yana ci,Ice cream din ma a Haka take bashi Yana tuki ko Ina zai kaisu oho,Hannunta ne ya goce icecream din ya Bata Masa gefen lips kadan,Yatsanta me laushi tasa a saman lips dinsa masu matukar kyau da laushi,Wani shock Suka ji Baki dayansu.

Goge Masa tayi tana tambaya Ina zamuje ne haka? Bai kulata ba sai da Suka je wani Hadadden waje da ake zuwa hutawa da dare cinema ce iri iri,a Nan yayi parking Suka fito ya biya musu Cinema wani Comedy American Film Suka shiga tana rike da ledarsu ta kayan ci, Popcorn ya sake siya musu cikin katon bowl me kyau.
Zama sukayi an fara haska film din.

A zahiri tunani yake yanda zai bullowa Mami da matsalarta,Khadija kuwa tama manta da wata Mami Kallonta takeyi hankali kwance tana ciye ciyenta kallonta yayi lokacin itama ta juyo Ido suka hada da sauri ta janye idonta a kansa domin kwar jini yake Mata ga kamshinsa me rikita ta tare da kashe Mata duk wata laka ta jikinta.

Hannu yasa da niyyar eban poprcorn din itama tasa zata eba hannunsu ya Hadu,wani zirrrr shock Suka ji gaba dayansu sanadin daya jawo Khadija ta rude tare da janye hannunta da sauri ko a jikinsa Abdallah ya ci abinsa suna Haka har Film ya Kare ya duba agogonsa 11pm dare yayi,Muje gida na gaji Abdallah ya furta Yana duba agogonsa dake daure a tsintsiyar hannunsa me kyau da tsada.

Khadija tsoro ya kamata Mami tana jiranta kamar zatayi Kuka idonta cike da kwalla take kallonsa,Kallonta yayi taso bashi dariya Amma Bai ce komai ba ya shiga mota tare da jansu suka Fara tafiya,Hawaye ke diga saman Hijab din Khadija dis dis sai sheshekarta yaji kawai,Ba tare da ya kalleta ba yace ya kike so na Miki? Ina Zan kaiki? Khadija tana kuka tace Ni..Ni...dai..zata..duka Ni...ga Mama Basu nan..ok Dan na taimakeki shine Zaki ajiye min kuka Ina laifi ma Dana daukeki,da nasan Haka Zaki min bazan daukeki a mota ta ba,nasan Yanzu Mami tayi bacci ki bi ta daya gate din ki shiga part naku kina sani magana kaina ciwo yakeyi ga zazzabi nake ji Amma kin dameni da kukan banza.

Khadija Hawayenta ta goge tayi Shuru tana ajiyar zuciya har suka Karasa gida ta daya gate do Suka Shiga,Mami tuni tayi bacci, lafiya Kowannensu ya shiga part dinsa.

Tunda Abdallah ya koma Zazzabi me zafi ya rufeshi sosai Haka ya kwana nannade a bargo Yana rawar sanyi,jikinsa zafi zau,Mami kuwa ko da safe Bata saurari part dinsa ba tana fushi dashi,Haka Bata koma part din Khadija ba tace laifin Abdallah ne daya kulata har ya turata wurin manyan mutane Haka mutane masu daraja ai zaizo ya sameta.

Sunday ne ba aiki Yana ta zazzabi har karfinsa ya kare Babu me taimaka Masa,ga ba abinci,Khadija Kuma tana son zuwa ta gyara Masa part dinsa tana tsoron Mami Don Kar tayi laifi sai ta wuce wurin Mami zuciyarta cike da tsoro.

Tana Shiga Mami ta gasa Mata Harara har kasa ta durkusa tare da gaishe da Mami sannan ta Bata hakuri akan abinda tayi.
Mikewa Mami tayi tace Dan Uwarki Ni saarkice da zanje har part dinku ki kasa bude min,Mami.....kafin tace komai Mami tal kwasheta da Mari tare da rufeta da duka,Afrah ta Miko waya doguwa Mami ta Zane Khadija da ita iya karfinta har yatsa ta fasa Mata jini na zuba,Karshe tace wlh wlh kinji na rantse Dana yafi karfinki aiki na saki Dan matsayinki kenan a gidan nan shegiya Arniya idan Kika Kara shiga safgar Dana saina kashe ki.
Key da ta jefo Mata a fuska tashi kije ki gyara Masa part dinsa Kuma kina gamawa ki dawo Nan ki gyara min nawa Dan Ubanki.

Tana kuka ta dauki Key din ta fito ta wuce part din Abdallah tana gyare gyarenta har ta Gama ko Ina saura dakinsa ta shiga,tunaninta bacci yakeyi ta wuce Toilet tana ta uban Kuka yasan Maminsa ce ma tayi mata wani abin Kuma ta sata aiki,Sai da ta Gama da toilet sannan ta fito taji Yana ta uban Nishi Yana rawar sanyi Kar..Kar..Kar, da Sauri ta koma ta sawa kofar key Wai Don Kar Mami ta shigo ta kamata tana kula Mata danta.
Bed din ta koma tare da yaye blanket din Baki daya da sauri ta rumtse idonta domin daga shi Sai Short wondo surarsa me Jan hankali ta bayyana,Jikinsa ta taba zafi kamar wuta,E-wooooo ta furta da karfi,ur Body is too Hot Yaron Daddy,baki da Magani a Baki ki Sha? Wayarsa ya nuna Mata ta jawo da sauri,,da kyar yace Kira Doctor Hussa
ain,Yasa tomprint nasa Haka ta jawo yatsansa tasa a wayar sannan ta bude ta lalubo Dr Hussain.

Yana dagawa yace Shegen gari ya akayi? Khadija cikin gwarancinta tace lafiya Babu Abdallah ayi sauri a zo a dubashi shi mutuwa ta kusa zuwa Masa sosai ya kusa mutuwa Doctor ta Karasa tana fashewa da kuka,tace Doctor har kudin break yake bani kudin da yawa dubu dubu wooo idan ya mutu wa zai bani.

Dariya ta Kama Hussain dama babban abokin Abdallah ne,Hussain yace ok gani nan zuwa ya datse Kiran tare da kwaso kayan aiki ya taho da sauri,Minti kadan ya Parker motarsa tare da wucewa part din Abdallah,Khadija ya iske ta zuba tagumi tana Hawaye me Bata kudin Break zai rasu.

Hussain Yana dubashi yasan bazai wuce jinin Abdallah da yake Hawa ba ko ya ransa ya baci ko hayaniya sai jininsa ya hau kadan,Magani ya zube yace Jininsa ne ya hau kadan,dama Yana yin Haka Bai son bacin Rai ko Hayaniya,Khadija ta kwalla Kara Hawan jini Doctor Innalillahi lahhhhh na shiga Uku na Gama lalashewa Khadija ta Furta tana tafa hannu,Dr Hussain ya dinga dariya dama yasan Khadija tun bikin Baba,karki Damu Khadija Yana Shan magani zai warke Dan iskan yaron Nan baya Jin magana da kike ganin sa ki daina tausayinsa.

Khadija tace lala ban Dan yiska bane baya yiskanci ko hannun mace Bata rikewa fa Doctor,to ebo min ruwa ba me sanyi can ba a Bowl na goge Masa jikinsa,Khadija ta ebo a toilet tare towel Karami,Duk abinda Sukeyi Abdallah na jinsu,Jeki kitchen dinsa ki dafa Masa abinci Bari na tasheshi yayi wanka ok.

Da sauri Khadija ta shiga kitchen ta Masa lafiyayyen faten Irish potato yasha Kifi ta hada Masa fruit salad tana shigowa da tire ta iske Abdallah har yayi wanka da Sallah Yana zaune gefen bed sanye da farar jallabiya suna Hira da Doctor,Ashe Dr Khadija na fita ya Masa allurar da yake Masa nan take jinin ke sauka Zazzabin ya gudu,Bai son Khadija taga tsaraicin Abokinsa sabo da shi ya taimaka Masa yayi wanka.

Tana shigowa Dr Hussain yace na tafi wurin Aiki Ni,Khadija farin ciki ya cika Mata zuciya da sauri ta ajiye tire a gabansa tare da Dora hannunta a saman goshinsa taji ba zafi tace Alhmdllhi mungodewa wooo ya Baki lfy Allah ya karo lfy da yawa da yawa fa.
Abincin ta bude kamshin Dadi ya daki hancinsa plate din ta dauka tasa spoon tace ka huta Sir Bari na baka,Kallo kawai yake binta dashi har ta ebo ta Kai Bakinsa a hankali ya bude ta Sa masa ya cinye,sai bashi takeyi da sauri Yana cinyewa tana cewa idan ta zuba Masa a baki ehem,oya Cinye...idan ya cinye tayi Murmushi yace yawwa....sannu...Oya...ehem...kawai ta maidashi wani Dan yaro Karami sai kawai yaji dadin hakan ji yake kamar ya fashe Mata da kukan Shagwaba yanda take ta ji dashi Haka ya koma kamar Dan yaye,tas ya cinye Abinci yasha hadin fruits dinsa tasa tissue tare da goge Masa Baki ta bashi ruwa ya Sha sannan ta Mika Masa Magunguna yasha ya koma kasan carpet ta gyara bed din sannan ya kwanta samansa,ta gyara Masa room din neat sannan tace Allah ya baka lfy Bro ta juya zata tafi ta tsinci muryarsa yace Thanks alot ki kawo min Abinci da dare pls,Da sauri tace to Zan kawo ta fita abinta tana murna ta manta ma da raunin da Mami ta ji Mata,sai da taje ta gyara part din Mami sannan ta koma sashensu.







Godiya masu Sharhi kunfi kowa birgeni.







AsmaBaffa
[12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: 🏵TUBABBIYA🏵








11-15








Official








By
AsmaBaffa






ga page naku Yan albarka!

MAMAN FATIMA YOBE,LITTLE ANGEL,HAJJORA MUHAMMAD,SAFNA,MAMAN FAROUQ,MAMAN MUHAMMAD.










Wanka Khadija tayi tare da gasa jikinta da ruwan zafi sannan ta dauki wayar da Baba ya siya Mata me kyau Infinix Haka Merry ma da Mami ya siya musu masu tsada kowannensu,Mama ta Kira taji ko sun taho,Mama tace sai Gobe zasu dawo gaba daya dangin Baba masu mutunci da karamci sun hanasu tahowa yau,hakan baiwa Khadija Dadi ba ta Matsu su dawo gidan ya isheta ita daya.

Bayan ta dawo Daga Islamiyya kitchen ta shiga tana nazarin me zata dafa Masa pounded yam da egusi soup ta hada Masa Tasha naman kaji sai lemo da farfesun beef meat ta Masa Hadi da carrot da sauransu abin Sha'awa.
Wanka ta shirya cikin Riga da da Zani Amma bata iya daurin Zanin ba Sam ta dageshi sosai Kuma ta daura saman rigar ta yafa mayafi a kanta abinka da Fara tare da kyau sai tayi kyau sosai a hakan.
Tana tsoro da sanda ta shiga part din ba tare da kowa ya ganta ba,tana shiga tasa key Dan kar Mami ta kamata, Yana main Palo ta sameshi saman 3seater Yana kwance da Alama bai warke sosai ba yanayinsa,Sallama tayi Masa tare da ajiye abincin a gabansa tana Sannu ya jiki? Da sauki ya Furta,kasha magani ta furta tana dafa saman goshinsa da hannunta har yanzu jikinka da zafi.
Kallo yake binta dashi yanda take damuwa da damuwarsa.

Abincin ta zuba Masa a plate ta koma gefe ta zauna,da kansa yaci sosai sannan ta dakko Masa Magungunansa a bedroom ta ballo tana bashi da ruwa Yana Sha ya Gama ta kwashe Kwanukan tare da Masa sai da safe ta tafi abinta.

Mami kwana biyu Bata ga danta Abdallah tun tana fushi dashi har ta hakura ta tafi part dinsa domin gano lafiyarsa,ai kuwa taga ya rame Bai samu ya warke ba sosai,a gigice ta Karasa gabansa tana tambayarsa lfy? Yace bani da lfy Mami ki yafe min na Bata Miki...kafin ya rufe Baki tace na yafe maka Abdallah na,Allah baka lfy ai ban sani ba,a part dinsa ta yini tana kula da danta sai data ga ya warware sannan ta dawo bangarenta.
Shi kuwa Abdallah murna ta kamashi Maminsa Bata fushi dashi.

Washe gari da Yamma lis Khadija ta dawo Daga Islamiyya kenan motar su Mama tayi parking a gidan sun dawo lfy,Abdallah Yana jikin motarsa Yana kokarin shiga zai fita Yaji ihun Khadija Wanda Saida ta tsorata har masu Gadi,Jakar makarantar ta jefar ta dinga tsalle da ihu tare da fadawa jikin Mama da Merry,Baba Yana kallonsu cike da Jin Dadi,Khadija har kasa ta duka tare da Gaida Baba tana musu sannu da zuwa,tsaki Abdallah yaja sannan ya karaso gaban Baba da Mama ya gaidasu a mutunce tare da musu sannu da zuwa suka amsa suna Masa Godiya tare da tambayarsa kowa lfy.
Ido suka hada da Khadija Abdallah ya harareta yanda take wani murna duk ta cikawa mutane kunne da surutu,ciki suka rankaya shi Kuma Abdallah ya shiga motarsa ya bar gidan.

Bayan sati Uku Daddy ya dawo tare da Matarsa sai sintiri akeyi zuwa gaidashi,Daddy ba abinda yake damunsa irin Rashin hadin Kai na iyalansa,Ga almubazzaranci ganin suna da wadata sai ayi ta barna da abinci ba tattali wata sai tasa a dafa Mata Abinci sai tace ta fasa ci,baza su bawa almajirai ko wasu ba sai su juye a shara,kayan Abinci duk yawansa kwana kadan kowacce zata ce Babu a part dinsu har Hafsatu matar Baba,Haka magani da zuwa asibiti ko Ciwon Kai Suka ji sai Doctor ya dubasu an Tarawa Daddy bills a Hospital kudi me yawan gaske ko tunanin rayuwa basa Yi,idan ba ransa ya zasuyi kenan,gashi duk cikinsu Babu me Jin Maganar wani,Kaninsa Ma Baba Basu daukeshi komai ba,gani sukeyi bashi da wani Amfani a garesu sabo da shi ba wani bane.

Sai yanzu yake ganin illar aure auren da yayi Yana saki,wasu Matan ma da ya aura duk sun tafi da yaransu yanzu Kuma Yana mutuwa zasu zo dasu za a raba gado rigima ya Bari ba karama ba,Bai yi Saar auren Mata na gari ba,Basu San rayuwa ba ko kadan kawai Jin Dadi da Hutu Suka sani shi yasa Basu da hankali gaba daya,Abdallah ne daban duk da shima Bai San ta duniya ba Amma yafi su hankali.

Daddy yaji Dadin auren da Abdallah zaiyi Amma da yayi bincike abin ba kyau,Humaira ba matar aure bace musamman Abdallah,ga Mami ta dage akan kwadayin dukiyar wasu sabo da Rashin wadatar zuci duk kudin mijinsu da yaransu na wasu take hange,Daddy yasan Hana auren Matsala zai haifar ga Abdallah domin Mami zata iya tsine Masa,Babu irin Nasiha da fadan da Daddy baiwa Mami ba akan a hakura da auren Abdallah a nemi wata,Mami har da kuka za a rabata da danta za a Hana danta ya Mata biyayya,Daddy yace Allah ya Sanya Alkhairi Zan Masa auren Amma ko bana Raye sai kinyi kuka da idonki ta Dalilin wannan auren.

Matansa kaf da maza Da Mata yaransa ya Tara wuri daya har da Baba da iyalansa Daddy ya musu Nasiha sosai akan rayuwa da Kuma irin abubuwan da suke Tafkawa Marasa kyau,Ya kallesu yace kun ganni Kuna rainani Kuna ganin kamar bani da amfani a gareku wlh babban katanga ce duk ranar Dana Fadi na Mutu kuka rasani Babu Ni zaku Sha mamaki,rayuwa ba tabbas,Allah ya gani nayi kokarin sauke hakkokina a kanku Amma bakwa ganewa,yanda kuke wulakanta Abinci da sauransu,gaku kune gulma da munafunci ku sai abinda iyayenku Mata suka ce to gaku gasu Nan,duk ranar Dana mutu zakuyi nadamar halayenku, Ina Baku Shawara ku kaunaci junanku,ku hada kanku,Sannan ku dinga aiki da hankali da tunani,ga Dan Uwana Uwa daya uba daya Kuna ganin bashi da amfani na tabbata sai yayi muku ranar da Babu Wanda zai muku ita sai shi.

Ku daina ganin ko na mutu ba wani Abu sabo da na Tara muku dukiya to ko nawa Mutum ya Bari kuka gada zasu Kare cikin kankanin lokacin matukar bakuyi amfani dasu ta hanyar data Dace ba,maza da matanku ku yarana nayi nayi ku fito da Wanda zaku aura kunki gaku da yawa kun Isa aure Amma kun Gaza,bazan muku Dole ba iyayenku Mata zasu aurar daku tunda su kuke so ni ubanku ban Isa ba.

Sosai Daddy yake ta fada da Nasiha sannan yace sauran yarana da suke kasar Nan iyayensu daban ku shirya duk zasu dawo Gidana da Zama Suma, karshe ya rufe taro da Addua,Baba Yana zaune sai kuka yakeyi sosai Sabo da kalaman Yousuf Dan uwansa Sun rudashi tare da bashi tsoro,Shima Abdallah tsoro ya kamashi Daddy na Zancen mutuwa Hawaye yakeyi,Su Khadija suna gefe da Mama Sunyi Shuru,sauran Yaran kuwa Danna waya suke kawai wasu ma Headphone Suka saka,bayan ya sallami taro daga shi sai Baba Dan Uwansa,Wasu takardu ya Mika Masa yace karbi takardun gidajene guda biyu daya Kaduna daya a Kano idan gidan nan ya dameka sun koreka ka koma gidajenka ne na Mallaka maka kyauta halak malak,Sannan ka kula da Business naka sosai Dana doraka a Kai,shi yasa ban hadaka a dukiya ta ba,na baka kasonka daban babu Wanda ya Isa yace kudin magada ne.

Baba ya sake fashewa da kuka yace Yaya nifa ban gane maka ba wannan zuwan,Meke faruwa da Kai Haka? Murmushi Daddy yayi yace ka daina damuwa abinda ya Dace nayi ne kawai tun tuni banyi ba shi yasa nakeyinsa yanzu.
Da kyar ya kwantarwa Baba Hankali,Check na millayan talatin ya mikawa Baba yace naka ne.
Wasu takardu na gidaje guda biyu ya mikawa Baba yace wannan a Abuja wannan a Kaduna Nan gaba ka bawa Abdallah nasa ne halak malak,ba yanzu zaka bashi ba sai Nan gaba,Sai kudi shima ka ajiyewa Abdallah a accnt naka Nan gaba ka bashi,wannan sirri daga Ni sai Kai sai Allah,karka fadawa kowa.

Ban bawa Abdallah wannan Dan nafi sonsa ko don wani abuba na bashine Dan biyayyar da yake min yake maka Dan Uwana,sannan sabo da kyawawan halayensa,na kudurce a Raina duk Wanda yayi Haka Zan Masa wannan kyauta sai gashi Abdallah kadai ya min biyayya.

Baba dai Kuka yake kawai kamar mace har ya karbi takardun da Kuma wasiyyar Daddy a rubuce Dan kar ma ace karya ne watarana shi yasa Daddy yayi rubutu da komai ya bayar, Abdallah da Baba sun rasa sukuni gaba daya gani sukeyi Daddy mutuwa zaiyi kawai,kullum Basu da walwala har aka saka ranar bikin Abdallah da Humaira,biki ya rage saura wata daya Amma Ango ramewa yakeyi kawai sabo da Maganar Daddy shi gani yake Daddy mutuwa zaiyi shi yasa yayi azumin kaffara na rantsuwar da yayi kan bazai auri Humaira ba yanzu ya hakura zai aureta Daddy ya daura Masa aure da kansa Kar ya mutu,Yana so Daddy yaga aurensa.
Khadija kuwa sai kunci takeyi tana zabgewa Kan Abdallah zai auri wacce Baya so tana Taya frnd dinta bakin cikin auren Dole da za ayi Masa,kullum sai tayi masifa tanawa Mama mita Har Baba ta fada Masa karfa ayiwa Abdallah auren Dole,Baba yace taje ta fadawa Daddy da kanta.

Yau da Sassafe Khadija tayi Shirin zuwa wurin Daddy ta fada Masa Kar ayiwa Abbdallanta auren Dole gashi Nan Yana ramewa,Tunda ta shiga sanye da Hijab take sabo da Baba yayi musu fada da nasihar saka Kaya masu bayyana tsaraici ga mazan da ba muharramansu ba Kuma sun dauka duk da watarana suna Dan kin sawa Amma suna gwadawa,Sallama take kwalawa Amma Shuru har sama dakin Daddy Babu kowa,cikin toilet taji kakarin Amai Daddy nayi,baya ta koma Daddy ya fito da waya a kunnensa Yana kiran Doctor a wahalce yace Doctor yanzu fa Ina tunanin zuciyata ta gama lalacewa domin Ko kaki nayi jini ke fita,Baki Khadija ta dafe sabo da a boye take bayan labile tana Jin Daddy na magana saura kadan kwanakinsa a duniya,Doctor Yana kwantar Masa da Hankali Bayan sun gama waya yasha maganinsa sannan ya kwanta saman Bed,a hankali Khadija ta fito yanda bazai kula ba zaiyi tunanin Yanzu ta shigo dakin nasa,Sallama tayi ya amsa Mata da Fara'a yarinyar ta kwantawa Daddy sosai,a gabansa ta zauna a kasa shi Kuma ya zauna saman Bed ta gaidashi,yace Khadija lafiya dai na ganki Haka da Sassafe? Khadija ta dukar da Kai kasa sannan tace Daddy Dan

Please Login or Register in order to submit comment