Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutunci watarana,Dariya sukayi gaba daya ya rungumeta suka kwanta bacci ya kwashesu hankali kwance.
Ko da Asuba da sukayi Sallah Saida ya sake yi sannan suka koma baccinsu.

Usman kwance yake yasha Shirin bacci shima iyayine dashi wajen kakale kakale da harkar kamshi,10pm ya jawo wayarsa tare da Kiran Abu,bangaren Abu tana ganin kiran Usman ta Fara yanga sai da ya Kira sau uku ta kusa tsinkewa sannan ta daga tare da makale Murya ta gyarata tayi wani Zaki sannan a nutse tayi Sallama,ta birge Usman ba Hello sai Sallama shima ya amsa mata, gaishe shi tayi da matukar girmamawa ya amsa Yana Jin fa Abu ta birgeshi yarinya sai nutsuwa Haka, Yan Mata ya Jin Dadi? Murmushi Abu tayi cike da kunya tace Jin Dadi Sai ku ai kune Manyan kasar, bakwa kusa ai ba Jin dadi cewar Usman,Abu a dakin ta mike tayi rawar girgiza da kirjinta ba tare da Usman yasan me takeyi ba a waya Kuma a nutse tace a cikin Yan uwanka Ina iya na gane ka,idan ma Baki sanni ba ai Zaki sanni Nan gaba,Abu tace na sanka ma,yau she Zaki zo wurin kawar Taki? Next week Inshaallah zanzo na ganta,Ashe Muna da babbar bakuwa,Hmmm sosai ma,to ya ake ciki nifa da gaske nakeyi ba Wasa nake Miki ba Shi yasa ma tunda Abdallah ne ya zabo min nasan ba zaban tumun dare bace,Abu tayi Shuru,ya Kika ce? Kunyarka nakeji Zan tura ma text, murmushi Usman yayi yace ok ba damuwa Ina jiran amsa.

Kwanaki kadan Abu da Usman suka Saba da juna soyayya me zafi ta kullu a tsakaninsu,kullum cikin waya da chat suke,Abu ta iya takunta ta Gama Mallake zuciyar Usman lokaci guda Khadija Bata san me akeyi ba.
Hafsatu kuwa tunda ta bar gida take garari tana tsince tsince Ana tausaya mata,tana cikin tafiya motar asibitin Mahaukata tayi parking Suka jefa Hafsatu ciki sai gidan Mahaukata,Dama Gomnati yanzu ta Hana barin Mahaukata suna yawo a gari Ana samun Marasa Imani su cutar dasu,Gata da Katon cikin sihiri kowa yayi zaton cikin gaskiya ne.

Alhaji Shehu tunda Mami ta bar gidan ya dinga Murna Yana Jin Dadi ya rabu da Jaraba, Kano yaje wajen uwar yaransa Amma Yana shiga da yamma ya dinga masifa shi komawa zaiyi Abuja gari duk zafi,ga sauro bazai iya kwana ba,Mariya ta kawo Masa Abinci ya tabe Baki bazan Ci wannan abincin naku ba Baku iya komai ba kauyawa daga tuwo sai shinkafa da wake,ai baka ba da cefanen me dadin ba,tsaki yaja tare da mikewa yace Ni na tafi ya Shiga Mota Driver ya jashi zuwa Airport ko yaransa Bai gani ba ya tafi,Mariya takaici ya isheta ta Fara kuka tace Allah ka saka Mana Allah kana gani Allah ka bi min hakki na,Alhaji Shehu ashe da Amaryar sa yazo Kano Yar gaban goshi tana Hotel tare da kawayenta Karuwai Yan uwanta,a waya ya kirata suka hadu a Airport sai Abuja,Driver ya daukosu sunbi ta saman Wata gadar sama Sukayi Hatsari Suka dunguro kasa daga saman gadar, Amaryar nan take ta mutu tuni tayi Daga daga,Driver ma ya sheka kafin a kaisu asibiti,Alhaji Shehu ne Bai mutu ba Amma yayi daga daga shima a asibiti aka yanke Masa kafafu gaba Daya guda biyun, yaga Ishara shi da kansa ya gane Hakkin Matarsa ne Mariya,Mata mu rage yawan addua marar kyau ga mazajenmu,da an Miki abu kice Allah ka saka min idan Yana cutarki Allah zai iya amsar adduarki Nan take wani mummunan Abu ya sameshi, Kinga ya shafeku gaba Daya ga yaranku, ko ba komai Kuma kun shiga wani hali sai kinfi kowa kuka pls mu dinga danne zuciya Muna Allah ya shirya ya ganar da Mutum gaskiya.

Alhaji Shehu yaji wahala sai lokacin ya Tara yaransa da Matarsa Mariya dama suna wajensa suke jinyarsa suna kuka da bakin ciki,yanzu ma gaba dayansu kuka sukeyi sakamakon Likita ya shigo yace Daji ya shigi jikinsa iya Cinyoyinsa Dan Haka sai an sake datse kafafun,yanka biyu kenan a kafafu har wurin cinya, kuka sukeyi gaba Daya halin da Suka iskeshi ciki abin tausayi,sai Tuba yakeyi ga Allah Yana cewa yaransa su yafe Masa, Dr yana taba kafar azaba tasa Alhaji ya zabura tare da sakin Kara, yace idan na Mutu kuyi min Addua ku rokar min gafara wurin Allah,na aikata aiki Munana ku yafe min,Mariya tana kuka da yaranta sukace su sun yafe.

Ban sani ba ko Allah zai yafe min sabo da ban tuba ba sai da Naga mutuwa daf, nine shirka,Neman maza da Mata,Zalunci na zalunce ku,Mariya tace wlh mun yafe maka gaba dayanmu,Mami Matar Dana aura muka rabu Alhaji Shehu ya goge hawayensa Yana cije lips sabo da wahala Sannan ya Basu Address din Mamin Abdallah yace Dan Allah ko bayan Raina kuje ku nemar min yafiyarta..da sauri Mariya tace Inshallah, Babban Dan Alhaji Shehu Salman wani Kyakyawan gaske chocolate Dan gayun gaske ya rubuta Address din, Alhaji Shehu ya sanar musu inda dukiyar sa take kudi da Kuma Kadarorinsa masu mugun yawan gaske,Babu Wanda yayi zaton Yana da dukiya Haka sai yanzu.

Bayan an sake yankewa Alhaji Shehu kafa tsananin wahala Allah ya karbi abinsa ya rasu,Mariya da yaranta sunsha kuka.
Bayan wani lokaci komai ya lafa dama iya yaran Mariya ne su 9 aka raba gado suka zama Attajirai,dama Allah yasa Mata da mazan Sunyi Degree sai masu HND su Suka ci gaba da juya dukiya suna aikin Alheri sun Zama manyan Attajirai musamman Salman Yanda ya Kara kyau da haske kamar wani Dan Shugaban kasa.

Mami Kwana biyar da Fara maganin adduoi sai gashi ta samu lfy saura kadan,Malamin yace Sihiri ne a jikinta da Allah yasa ta Kara Wata daya a gidan Alhaji Shehu bayan cutar ta kamata da tuni Dodo ya shanye jininta,sai dai tayi ta cuta har ta mutu ba tare da an gane ba,Kuma Dan Allah yasa lokacin daya Kama su Abdallah ya samu matsalar karaya ne lokacin da Abdallah ya bugashi da kasa ya karye yasha jinya,da ace kalau yake da tuni yayi tsafi da Mami,Hauka da bacewar su Abdallah tayi mata amfani da Rana Wanda Basu gano hakan ba sai zuwa gaba sabo da Abdallah Bai San waye wanda Maminsa ta aura ba sai Nan gaba,Haka Mami Bata da labarin mutuwar Alhaji Shehu ta lafiyar jikinta takeyi.

Tun ranar da Khadija taje Suka Sha love da Abdallah Bai sake ganinta ba wasan buya sukeyi ita Wai har yau Bata warke ba Kuma ta warke,ga Mama tana tsumata, ga Abdallanta ba hakuri Yana Nan ya Gama shirya Mata duk ranar data zo Hannu zata Gane kurenta.
Yau Saturday yau Kuma Abu ta dira a Kd kofar gidan Baba Taxi ta sauketa, lokacin Khadija sun tafi Saloon da Lalle Haka kawai,Abu tazo tuni tana jiranta a wurin Mam,dake Abu Bata da bakunta ba ruwanta har sun Saba da mutane Ana ta Hira,tayi wanka ta cakare taci abinci har Sallah tayi kawai Khadija take jira,Khadija Basu dawo ba ita da Afrah da Firdausi har dare,Abdallah Bai sani ba Mami ce tayi shishigi tace taje.

Yana wurin Dr Hussain 9pm Drivernsa yayi parking Bakin gate zai shiga Da motar gida yaga mota daban ta tsaya Khadija ta Fito tana gyara mayafinta zo kuga uban Kyan data tayi kace Amarya ce,Firdausi ta Fito a gaban motar sai Afra itama a baya,Me mota sukayi sallama da Budurwarsa Firdausi ya tafi.

Abdallah Bai Bari an shiga dashi gida a mota ba sabo da Jarabar kishi ya fito a fusace yasha kana Nan Kaya ba karamin azabar kyau yayi ba ita kanta Khadija taji kishin fitarsa a Haka Dole tasan wasu Matan su kalleshi,Su Afrah suna ganinsa ba mutunci Yana aika musu Harara Suka yi cikin gida da sauri Dan tun tuni sun san halin abinsu.

Khadija kuwa ganinsa a Hasale ta tsorata gashi tasan ita me laifi ce tana kin zuwa tayashi kwana tun Yana naci har ya hakura,gashi ta fita Bai sani ba Mami ce ta barta,sannan ya gansu a motar wani.
Skert din lace dinta ta tattare tare da cire takalminta tana ja da baya ta arce da gudu ta fada gidan, Abdallah yanzu Bata fadan yakeyi ba Kar tayi gudu Masu aiki su kalle Masa abubuwa suna kadawa,ai taku biyu yayi ya damko ta, Hakuri ta Fara bashi ganin karyarta ta Kare pls I'm so sorry Husband,haba Dan lelena Kalla fa Lalle naje takanas sabo da Kai nayi shi Dan kaji Dadi, Abdallah shi tuni ma ya manta laifi tayi Masa sabo da ya susuce a kanta sai wani Kyau takeyi,Khadija ce ta kalli ko Ina ba kowa inda suke da Duhu kadan,rungumeshi tayi yanda zata Kara kashe Masa bakin magana,ai ko Abdallah yaji wuta sai ya koma kallon Lalle Yana yabawa tare da kissing Hannayen, a hankali Khadija tace yayi maka kyau? Sosai ma dama garin Nan sun Iya Lalle haka? Sabo da Kano sunfi iyawa Kd watarana sai a hankali sai kurin wayewa da boko🤣 Khadija tace Sun iya sosai Gidan wankan za a gayawa gayu? Ai Kd karshe ne, Abdallah yace bana Bayan masu bacci da glass,Khadija tace aiko yanzu ma Saida Firdausi ta biya ta siyo Littafin Tarihin America zata karanta Wai sai ta dinga bada labari kamar taje can Haka sukeyi a garin kd, a karanta tarihin wasu kasar Mutum ya dinga baka labari kamar yaje,Ga Aron Kaya da mota sai anyi nisa kaga Ashe guy din Bakanike ne, Ni baza ki min wayo ba da surutunki cewar Abdallah kizo mu tafi muyi wanka sai Naga lallan sosai,Suna Shirin tafiya sai ga Abu ta Fito tare da kiran Khadija tace ke Dan Ubanki Nazo fa.

Khadija ta saki Kara kadan tace shine Baki fada min ba? Ya Hanya Iyye Abu wannan girman da kikayi kin Kara gogewa gashi farinki ya Kara Fitowa Mene sirrin? Abu tayi dariya tace Masassakin Budurci ne yazo ya Fara kera Ni yarinya,ke baki kalli kanki ba Khad kalleki fa, sai lokacin ta gaida Abdallah a mutunce yace yaushe kika zo? Abu tace tun safe yarinyar Nan ka Bari take yawo Haka Yaya Abdallah so kake Maza suyi ta tare maka ita.

Murmushi Abdallah Yayi yace Kema kya fada Zainab Tafi karfi na ta Gama mallakeni,Abu tayi dariya tace nazo zan gyara Mata Zama ka Kwantar da hankalinka Abu Wiring tazo Zan hada ma Wiring, Dariya Abdallah Yayi yace to idan kun Gama ki koro min ita Ina jira Naga aikinki ya Fara daga yau.

Bayan Abdallah ya tafi Khadija tace Abu Kinga yanda Kika yi kyau kuwa komai ya karu Kamar ba a kauye kike ba,Abu ta turo dauri gaba tace ance Miki kune kadai kuka san ta duniya? Ki tsaya ki dauki Darasi yarinya,Dariya Khadija tayi tace Ke Abu Nima ba karamar shegiyar kaina bace,Abu itama da kuruciya a kanta tace ke na fiki iya shege Iskancina ya take naki Khadija,ke da Banga komai ba da Kika nannade zuciyar mijinki ai Hajiya Ki Zama Karuwar Me gida,Khadija ta rike Baki tana kallon Abu tace Abu ki rufawa kanki asiri Baki san tsiyar Jaruma ba,Abu tayi shewa tace Yar albarka Ina taga wani tsiya? Ke kawai Da lango raguwar banza,Idan zaki mike ma ki mike,kin ga mazan Nan idan Majalasi baya yiwa Jaruma saukar ban girma to kina gani zasu juya Miki baya tare da Rado miki Kishiya Kuma kin San Matan yanzu a matse suke Majalisi ya Gama bada Balance tun a waje,bare ke da mijinki yake so Hot cab Khadija na hango Miki abokiyar Zama kusa.

Khadija taji tsoro tace Abu da gaske kikeyi? To yanzu ma kawar Merry ta bawa Merry labari taga wani Abdallah a gidan tana so ta jaraba sai ta aureshi,Khadija ta zaro Ido tace ke Abu,to ki tambayi Merry kiji idan karya nakeyi,dazu aka Gama Dramar, Khadija Nan take ta Fita a hayyacinta tace da Merry za a cuceni Kanwata ai wlh sai naci Ubanta,Kawar Merry guda fuuuuuuu Khadija tayi ciki Abu na biye da ita tana dariya,Mama ta Iske a Palo tare da Mami suna Hira sai Ga Khadija Kamar zatayi hauka tana cewa Ina Merry? Mama ta kalleta ke Kuma lfy? Halina dake Khadija shashanci tana bedroom,Da Sauri ta banka kofar Bedroom din tare da shakar wuyan Merry tace ke Merry dake za a cuceni har kawarki ta Isa taga Mijina tace tana sonsa?

Abu da sauri ta yiwa Merry Signa,Merry tace ah to Mene amfaninki sis kullum tare muke kwana dake bawan Allah yayi ta Miki waya kina wulakanta shi ai gwara ya auri ta biyu tun dazu ma ba Kya Nan ya karbi number wayarta sunsha Kuma hira.

Kara Khadija ta saki tare da kyale Merry tace ai zanje wajensa Anjima zanji idan gaskiya ne banza kawai wlh idan gaskene sai na yankaki,Abu tana ta dariya a boye har Khadija taci abinci tayi Sallah sai wanka ta Salla ta hade cikin wata Rigar bacci da ita gwara babu tare da daura katon Hijab a Kai sannan ta fito tana kamshi,Abu tana waya da Darling Usman ta makale Murya tana ranka ya Dade pls karka wahalarmin da skin naka ya lalace Kar kazo da rana kazo da yamma kasan Ina ji da Kai ban son abinda zai taba min lafiyarka.
Khadija tana jinta Bata San Abu da wa take waya ba Tunda Bata da masaniyar sun jone da Usman.

Babu wanda ta kula Ta wuce part din Abdallah da sauri tana so taji gaskiyar lamari,tana zuwa ta iskeshi a bedroom ya Gama Shirin bacci ya kwanta tare da kashe light.
Khadija tayi sallama Bata jira an amsa ba tace ka tashi bacci Bai sameka ba,tashi Babu lafiya,Bawan Allah Bai San me ya faru ba ya tashi zaune,Khadija ta kunna light tace yanzu duk abinda kake so baza ka fada min ba Mene nake dashi a duniya zan hanaka,Hijab din ta cire ta Haura gefensa ta zauna itama tayi Shuru ganin Bai wani rude Yana kallonta ba kamar yanda ya Saba sai ta tabbatar ya samu sabuwar Budurwa kafin kace me sai Kuka ya kwacewa Khadija,Abdallah Bai San meke faruwa ba.

Zaune ya mike Yana kallonta da mamaki a fuskarsa yace me ya faru Kuma Khad? Tana kuka tace ba Kaine ba zakayi aure ba kana ta son wata? Ni din? Wa ya fada Miki? Abu ce da Merry wai kana son Kawar Merry,Sai yanzu ya gano Abu ce ta shirya tsiya ta Koro Masa ita a ransa yace gaskiya Abu tayi.

A fili Kuma ya Kara tamke fuska yace ah to idan wata ta Kika wata ai sai ta soka Ni na gaji Khadija da lallabaki,har sai yaushe zakiyi hankali? Sai na nemeki Zaki zo wajena,Abinci duk ba ruwanki Kinga tunda baza ki iya ba sai a kawo Mai taimaka Miki,Khadija ta sake sakin sabon kuka tace Bana ce maka Ni girman Custard ce ba,saurin fa girma nayi, Abdallah yace to ai yanzu zan auro girman tuwo, Dan Allah kayi min Rai na tuba zan gyara halayena,bazan sake ba, mamaki yakeyi yanda duk ta firgice tace Ina sonka da yawa,tun kafin ka Fara Sona nake Mugun sonka Dan baka sani bane dama boye maka nakeyi Dan naja aji ne Amma fa har Addua nayi Allah yasa ka Soni,Farin ciki ya Kama Abdallah Khadija tana ta tonawa kanta asiri,da shi kadai yake fada Mata sirrinsa.

Ganin ta damu kanta sai ya rungumeta Suka kwanta a hankali ya rada Mata ki daina damuwa indai kin gyara halinki to bake ba kishiya,Khadija tace na gyara wlh, yau Abdallah ya samu Banza yau Jaruma ta dagargaji Majalasi yanda yake so,ita kanta Khadija taji a jikinta Tasha wahala sai daya fanshe kwanakinsa gashi Mama tayi Mata gyaran gaske ya sake Jin canji sai ya susuce, cikin sambatunsa shima ya dinga tonawa kansa asiri irin son da yakewa Khadija, Harda Karyata su Abu,Cikin Sambatu yace su Abu karya sukeyi kawai so suke su hada mu fada basa kaunarmu,Khadija tace duk sai naci Ubansu gobe Allah ya kaimu Ni zasu rainawa Hankali, Abdallah yace Abu ce ta Shimfida Karya Ni na Isa na Miki wata kishiya,duk abinda Nake nema kin hada to me zanyi da wata.Khadija tace Lallai Abu zata Gane kurenta Allah ya kaimu gobe Yar iskar yarinya zata sa zuciyata ta buga,Abdallah Harda lallaba Khadija yace Karya Abu takeyi Ki daina damuwa ba wata sai ke daya.











AsmaBaffa.
[12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: 🏵TUBABBIYA🏵








86-90






Official








By
AsmaBaffa





PAGE NAKU NE:

TUBABBIYA FANS,TASKAR ASMABAFFA, ASMABAFFA FANS CLUB AND ASMABAFFA FANS










Ko da Suka Fara bacci kafin safiya tayi Abdallah jarabarsa ta motsa Murza da yanda yake shafe Khadija shi ya tasheta a bacci Bata wani Hana ba sabo da itama lokacin jikinta ya karbi wuta suka shiga sarrafa juna Yanda take bada hadin Kai Abdallah ba karamin Dadi yake ji ba,sai yaji Ashe da farkon Nan wahala yakeyi yanzu yake amarcinsa Yana more rayuwa Yana Jin dadinsa Sabo da Haka sai ya Kara matowa akan Khad dinsa,wani Masifar Kara sonta yake ji Kamar ya cinye ta.

Washe Gari sai 10am Suka tashi yace sai Sunyi Wanka tare Khadija tana Jin kunyarsa Haka ta bishi Toilet Amma da Suka shiga Sai ta kasa tube kayan idan ya Miko Hannu zai jawota ya cire Mata sai ta matsa baya tana dariya, Da kyar ya samu ya kamata tana Nokewa ya cire Mata kayan da kyar,Shi Kam sai yau ya taba kallonta da Rana tar, sai yaga Ashe a baya cutar kansa yakeyi da baya kallo ga inda abin kallo yake sai ya tsaya Yana ta faman kallonta,Khadija tace Ni ka daina kallona ai wayo ne wannan Kai jiba da Short a jikinka Amma Ni kamin wayo ai Dole kaima ka cire na kalla, Kafada ya makale da sigar Wasa yace dashi zanyi wanka, Khadija tace ban yarda ba Allah Ni ta Fara dire diren kafafu ko Ina a jikinta Yana rawa tare da karkadawa Abdallah ya dawo kamar wani dolo Yana kallon abokan aiki.

Hannu ya Miko ya jawota gabansa ya kunna shower ruwa me zafi zafi kadan ya fara Zubo musu,Khadija tace Allah bazan yarda ba sai ka cire wandonka kaima,Wai tunaninki kunyarki nakeji? Kafin tace komai ya cire sai ta rumtse Ido,yasa hannu Yana kokarin Gwale Mata Ido Wai Dole sai ta gani,dariya sukeyi Baki daya,Dole ta bude Ido Khadija tace An gaisheki Jaruma,Abdallah yace tana amsawa tana gaida babban Dan uwanta Majalisi, sai da Suka Dade suna Wasansu na maaurata sai da Suka kwashe 2hrs a toilet kafin su Gama komai su fito,Sosai Suka shirya.
Abdallah yasa Shadda sea blue Khadija Material tasa me tsadar gaske Riga da skert Tasha kyau matuka suna kamshi Yace muyi sauri yunwa nakeji, Ni kuwa bana jin yunwa yau,bayan kin kwashe min Abincin jikina kaf, dariya tayi to Ni nace ka juye min,Hannunta ya kamo Suka fito tare gwanin Sha'awa.

Suna Fitowa Khadija ta kwace Hannunta sabo da Kar wani idon kunya ya kamasu,Mene Haka? Cewar Abdallah,Kunya zanji Ni Khadija ta bashi amsa,sai kiyi ta kauyancinki ai Kuma wlh karki ga kin kwana jiya wajena yau najiki Shuru idan Baki zo ba zakiga abinda Zan Miki,Dariya Khadija tayi tace ai zanzo to ka Adana muguntarka.

Suna shiga Suka Iske Abu tana yiwa Merry Kitso a Palo,Khadija ta kallesu suna ta Hira Suna dariya Su kadai a palon,sai Muryar Khadija sukaji tace munafukan banza Bari na dawo,dariya sukayi gaba Daya Suka gaida Abdallah ya amsa tare da wucewa Dakin Mama,Bayan sun gaisa ya wuce wurin Mami Khadija ma tana wajen Mami suna Hira,Daga Nan ta wuce Wurin Mama,Mami sai Murna takeyi taga danta yau a nishadi,Khadija kuwa tsuminta ta karba wurin Mama ta Sha,sannan Suka danyi Hira ta fito wurin su Abu lokacin Abdallah ya fito yazo da niyyar yiwa Khadija kiss Khadija Taki yarda sabo da su Merry wai karsu Raina Mata miji, Harararta kadan yayi ya fita abinsa,a waya ta tura Masa zazzafar Message me dauke da kalaman so da kauna shima yayi mata reply.

Abu ta kalleta tace Khadija masoyan asali, Abu ai duk naji karyar da kuka shirya ke da Merry Allah sai nayi muku rashin mutunci Zan fadawa Mama,Abu ta kalleta ba Wasa tace Lallai Khadija Baki da wayo yanzu yarda Kika yi da Abdallah? Ya Gama tsaraki kin yarda to Bari kiji Kinga dai Abu Ni bana Wasa Dama jiya boyeki mukayi Sabo da mun San haukarki karki manta Khadija Abdallah ba kece Matar daya aura ba Ke kadai akwai Humaira,wacce Saki Daya yayi Mata ba uku ba ko yaushe zai iya maidata,Kina da labarin yanda ta kwashi kudi ta Gudu kasar waje? To jiya ta dawo tazo ta bawa Mami Hakuri tare da dawo musu da dukiyarsu tana Rokon Mami tasa Danta ya maidata,jiya sauka ta kenan na iske Ana Zancen,Khadija Bata San sanda tayi cilli da wayarta ba Allah yasa ta fada saman Kujera,zumbur ta mike sai dakin Mami.

Abu tana ta Dariya domin Har Mami aka hada plan din,Khadija tace Mami jiki ashe ya Gama warwarewa sosai Haka sai yanzu na gani,Kai Masha Allah,Mami da ganin Khadija tasan akwai matsala tace Khadija lfy dai ko na ganki Haka wata sukuku? Zama tayi a kasa Mami na gefen Bed,Khadija ta kalli Mami sai taji kunyar Yi Mata magana sai tayi rau Rau kamar zatayi kuka,tace Mamina Wai Humaira ta zo jiya da safe lokacin mun tafi Lalle? Mami tace ohh ai Bata Dade ba tana zuwa ta tafi wajen Abdallah tazo Bata sameshi ba Bayan ta bamu hakuri, Husna kanwar su Khadija dake ss2 yanzu tace Yau zasu Hadu a gidan Dr Hussain Maybe ma Ya Abdallah can ya tafi.

Ga Mami Khadija Ana Jin kunyar Suruka ba damar yin hauka sai tayi Shuru tare da sadda Kai kasa kafin kace me Hawaye Ya wanke Mata fuska,sai da suka ji tausayinta kawai Sunyi ne Dan ta dawo Hayyacinta yanda zata dinga kula da Mijinta sosai sabo da yanda mutane ke dauke Mata hankali daga sun rabu da Abdallah da safe bazai Kara ganinta ba sai taga dama,ga Jarabar son yawo,Mami Kuma baza ta iya hanata ba,ita Khadija har yau zaman Kudu ke taba ta Dole sai ta fita kullum inda take so.

Mama ce ta dawo daga asibiti ita da Firdausi Tsaki Kawai Mama taja tace Allah ya kyauta Miki Khadija tashi Ni ki Shiga kitchen abincin Mijikinki ma Baki San ki Kai Masa ba ko ki tambayeshi Mai zai ci ke ba ruwanki kwanan ma badan Allah kike zuwa ba sai sabo da Kar ayi Miki kishiya.

Mami kamar ta fada mata gaskiya, sosai Khadija ta Bata Tausayi,yinin yau gaba Daya Kuka ta yini tana Yi ba ci ba Sha,Abdallah Yana can Yana tunanin Babynsa Allah Allah yake ya dawo gida yaga Khad dinsa, Koda ya dawo Bai ganta ba ta tafi part din su Firdausi ta kulle kanta a daki tana bakin ciki tace tayi zuciya ta daina kula kowa a gidan har Baba da Mama ba ruwanta dasu,Dare yayi Shuru ba Wanda ya nemeta ga yunwa na cinta ga bakin cikin kishiya, duniya tayi mata zafi ta rasa me zatayi har 3am tsakar dare Abdallah Yana can ya kasa bacci jaruma ta sashi gaba,tunaninsa Khadija ce tayi Masa abinda ta Saba sai taga dama.

Cikin Daren Khadija ta fito tsakar gida tsakiya ta daura Hannu akai ta shiga zunduma ihu tana burbuwa tana wayyo Allah na

Please Login or Register in order to submit comment