You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
Allah an tafi asibiti a gani ya mutu ko da ransa,ai Mami itama sai ta sume aka shiga Kwara Mata ruwa likitoci kawai aka kawo gidan suna aikin soke mataye da mazaje da Allurai da karin ruwa,sabo da ga masu Aljanu ga masu Suma ga masu zazzabi kowa Babu lafiyayye a gidan Dr Hussain Yana kan Abdallah a asibiti.
Mami ma an Mata Allurar bacci,Yan zaman makoki Kuma har Humaira fadan halin Daddy suke na gari yayi musu kaza kaza etc Khadijan ma da tabi Abdallah sai Allurai akayimata na bacci aka shimfideta gefe domin ta Hana kowa sakewa Kar mijinta ya mutu.
Abdallah ko ya farfado idan ya tuna sai ya sake Suma Haka aka kwana daya biyu sannan ya Fara samun lfy da taimakon frnds da Khadija da suke ta Masa Nasiha har akayi sadakar uku Dr Hussain ya Hana Abdallah sallama sabo da yasan Yana zuwa gidan zai sake dawowa gidan Jiya,Khadija ke sintiri taje gida tayi girki taje gidan makoki ta dawo asibiti ta kula da Abdallah ita da Dr Hussain.
Yau kwana Uku Yau Humaira tazo dubiyar mijinta, Khadija lokacin taje gida sai da ta Fara zuwa wurin taaziya sannan ta wuce gida tare da gyara part din Abdallah da Kuma part dinta sannan ta shirya lafiyayyun abincinta iri iri na Yan gayu,Wanka tayi ta shirya Cikin Lace Brown and Golden batayi kwalliya ba sabo da kukan Rashin Daddy da sukayi Babu nutsuwa,Mayafi ta yafa sai tayi Masifar kyau ta fito a wata Hajiya malam,Da Sauri ta shiga Room din da Abdallah yake dauke da Sallama a bakinta,Humaira tana gefensa sai Danna waya take tana murmushi, Khadija tana shiga suka hada Ido da Abdallah ganin Yana hawaye yasa Khadija ta Karasa da sauri kusa dashi tasan Daddy ya tuna, Hannunsa ta rike tare da tsugunawa a gabansa Sabo da Humaira ta tare inda zata zauna,Kayi Hakuri Lokacinsa ne Addua ita zamuna Yi Masa Ok? Kai ya gyada mata kawai Amma ya kasa hakuri,sai da Khadija tasa yayi Sallar Laasar da Addua sosai sannan ya samu Yar nutsuwa ya koma saman bed ya kwanta,Abincin ta zuba a plate sai kamshi ke tashi,Sai gani sukayi Humaira ta mike tana tsaki ta fice abinta.
Khadija tace Alhmdllh dama duk kin tare wuri Ni gaba ta kaini ta zauna a gefen Abdallah tare da cewa to Dan zauna kaci abincin,Kai ya girgiza Mata shi ya koshi,Fuska ta Bata haba ranka ya Dade naje gida Nasha wahala kace baka ci pls ka Dan ci Dan Allah haba me kyau,Daddy Inshallah Yana Aljanna firdausi Yana can Yana Jin dadinsa Kai kana Masa bakin ciki kana kuka,Fadin hakan data yi sai Yaji kamar Daddy Yana Aljanna Yana Nan Yana kuka sai ko yaji sanyi,Khadija taci gaba da Masa kalamai masu Dadi da Wasa sai ya Ware ya zauna saman bed din,Khadija ta ebo abincin tana murna ta Kai Bakinsa ya karba Yana ci,sai da ya koshi dam ta kyaleshi tace saura wanka ko na maka,kallonta yayi da sauri sai tayi Murmushi tare da boye Fuskarta ta Furta Wasa nake maka,dariya ma ta bashi Amma baiyi ba ya shiga wanka ya fito ta dakko Masa lotion dinsa ya shafa ta Mika Masa kayansa Wanda ta dakko Marasa nauyi ya shirya kamar bame jinya ba,Har Bayan sunyi Sallar Isha sai ga Mami da Yan uwanta.
Tunda suka zo suke hararar Khadija suna fadar bakaken kalamai tana jinsu ita dai har suka Gama duba shi suka tafi gida,gefensa ta koma ta zauna har ta fara gyangyadi,gefensa ya matsa Mata yace kwanta,Hijab mayafinta zata cire yace idan wani ya shigo fa? Da kansa ya gyara Mata Mayafin ta kwanta a gefensa,Wani shock suke ji kawai duk tunanin Abdallah na mutuwar Daddy sanda yaji jikin Khadija na gogan nasa wata nutsuwa ce ta shigeshi da farin ciki,tunaninsa ya tsaya cak ya nutsu Sunyi Shuru zuciyoyinsu ke bugawa kawai,Juyowa Khadija tayi suna facing juna, da sauri ya dauke kansa,a hankali tace sleep sleep tana shafa Kirjinsa,gaba daya ta hargitsa Masa tunani Baya son ya Mata wani Abu sai ta Kara girma Amma ji yake Anya zai iya kuwa? tunawa yayi ai ba soyayya suke ba,ba Kuma sonta yake ba sai ya canja tunani,Yana ji tayi bacci abinta a nutse,Dr Hussain ne ya shigo yace Kace shegen a gadon asibitin ma Amarci kakeyi,Gobe Zan sallameku ku huta,Murmushi kawai Abdallah yayi,Dr yazo Wai zai sa Masa Drip ya juya tare da Rungume Khadijan sa a jikinsa Wai baza a sa Masa ba,Dariya Dr yayi kawai ya fita abinsa a Haka suka Sha baccinsu harda makara yau.
Washe gari da wuri aka sallamesu suka wuce Family House Ana ta makoki,Abdallah mutuwa ta dawo Masa sabuwa kuka ya dinga yi Haka duk ya bawa Yan gidan kuka Suma again,Baba ne me lallabashi Yana Masa Nasiha,Yana part din Mami duk yaji kewar Khadija ya Saba kullum suna tare,duk sai yaji ya damu gashi Mami baza ta Bari tazo wajensa ba.
Khadija kuwa tana part din Mama tana baccinta,Abincinta yake son ci gashi baida number dinta,Merry Ce ta shigo tare da kawowa Mami kayanta data sata wanki,Mami na kusa ba dama yace a turo Masa Khadija,Mikewa yayi yace Ina zuwa Mami,a compound ya tsaya Merry tana Fitowa yace Ina Sis naki? Tana dakinta ba kowa ma a part dinmu kaje kawai Mama sun tafi Dubiya makwafta,Part din nasu ya shiga ya gaji da Tsafta kamshi na daban ne,Nutsuwa ce ta shigeshi Har Bedroom dinta ya shiga ta fito a wanka daure take da guntun farin towel ta daure gashinta da wani farin Towel din,Cinyoyin Nan gasu Nan santala santala farare tas dasu hips kamar me.
Kasa dauke idonsa yayi akanta sai data karaso gabansa tace Sannu da zuwa Bro ya jikin? Zauna ga bed Harara ya zuba Mata sannan yace kinzo kina ta bacci banci komai ba fa? Da Shagwaba ya furta sai yayi kyau ya birgeta,Tana shafa lotion ta duka tana shafawa a kafafu tana cewa ai dazu nayi Abinci naka Yana Nan,Shi kuwa hankalinsa Yana kasan mazaunanta data duka Suka fito ta Baya kadan,Sabo da yafi gani da kyau sai ya kwanta a bed din,Yana lekawa Baya gani sosai,tana gamawa ta mike tsaye tana gyara towel din,tace bacci zakayi Kuma? A'a kawai ya iya cewa hankalinsa ya tashi.
Hijab tasa zata sa bra da pant yace oh har wani Hijab Zaki sa Ni ga Dan iska ko? Baki bude tace kayi hakuri badan Kai nasa ba,to cire ki shirya a Haka Dan munafunci,Hijab din ta cire sannan ta dakko Bra dinta da pant ya gansu manya a ransa Yana ayyana girmansu yace Wai ke bakya period ne? Khadija kunya ta kamata tace ae ban taba yi ba wlh har 17yrs ko asibiti za'a kaini?
Sai wasan Haihuwa Kika iya keda wannan Abun take ko wa cewar Abdallah,haba ai Mama tace mun girma ba Wasa yanzu na daina Yi dama Abu ke sani Dole na girma yanzu Matar aure ce ni ta furta tana murmushi,Baki ya tabe tasa hijab ta kawo Masa abinci me Dadi,a hankali ya furta kin San ban warke ba Taya zanci Abinci da kaina? Dama Ita ta Saba ko bawa kannenta a Baki ma, kusa dashi ta matsa Yana zaune gefen bed, ke cire hijab dinnan Yana takura min,Kai da ba ajiki naka yake ba ta Ina zai dameka?Shuru yayi Mata tasan Bai son musu sai ta cire sai Dan guntun Towel dinta a ransa yace wannan Hurul ein din duniya ce Dan dai kawai tayi karama da yawa ne inyi soyayya da wannan ko na batawa kaina lokaci tare da zubar da girma na,kawai ta dinga bauta min shike nan.
Humaira tana can gida tana fushi tare da jiran Abdallah ya dawo,kawai sun barta a gida ko bukatarta baifi sau uku ya taba biya Mata ba,tana huci ta Kira Kawarta Zuly ta fashe Mata da kuka,Zuly tace lfy? Humaira tace Allah ya Isa kun cuceni kun zugani nayi aure gashi ku Kuna ta shanawa Ni kuwa Ina kunshe a gida bana Jin Dadi da Mijina ko kadan Ina bukatar Namiji wlh idan na gaji wurin samarina Zan koma.
Zuly ta sheke da dariya tace Albishirinki dama tazo na samo Mana shegun malamai sai abinda kika ce da Abdallah shi zaiyi wannan Khadija sai ya saketa,gobe zanzo gidan da wuri Hajiya ta,Humaira tace Allah kawata na gode sai kinzo.
Hafsatu zaune take cikin danginta suna zugata,Yayarta tace Kika sake Haka za a raba gado Baku samu komai ba Tunda kin tsaya Wasa tun Daddy Yana da Rai Baki yago Mana komai ba to wlh ki mike tsaye sai fa kin tashi tsaye kin fisgi rabonki idan ba Haka ba gidan Nan kina gani zai Fi karfinku, Hafsatu tace ai nayi Shiri Yar uwa,wannan Dan Iskan Abdallah shine matsalata sai Naga bayansa shine kawai zamu samu lfy,Kwarai kuwa ki tabbata kin dauki mataki cewar Kanwar Hafsatu,Dariya da shewa sukayi Baki dayansu.
Humaira Washe gari Zuly tazo tace Gobe za ayi sadakar Bakwai Mijin naki da Yar Iskar suna can gidan ko? Baki Humaira ta tabe sannan tace suna can maybe sai jibi zasu dawo,wlh Zuly Naga kamar Yana son yarinyar Nan,Zuly ta Ciro wani magani a jaka tace gashi Inji Malam Rai banza,Au sunansa Rai Banza? Kwarai kuwa cewar Zuly ki sawa Khadija a kasan pillow dinta Dan kadan Zaki Barbada data kwanta akai to da kafarta zata bar gidan Nan,Kuma ba family House zata je ba sannan ko Yan uwanta baza ta tuna ba kawai baza ma tasan ita wace bace Haka zata dinga garari a duniya ita ba mahaukaciya ba lfy Ras ba, galantoyi ta farashi yanzu har karshen rayuwarta.
Sannan ko wasu sun riketa baza ta taba Zama ba sannan baza ta Bari ayi Mata magani ba.
Farin ciki ya cika Humaira tace saura na Ogan ya kamata na mallakeshi fa,Zuly tace shi din banza ki fara korar kishiyar nasa me sauki ne,sai Uwarsa Yar iska har ita Zan Kora ta koma danginta can yanda baza ta dameni ba.
Tafawa sukayi suna dariya sai yamma Zuly ta shige motarta ta wuce.
Mami zaune take tare da Afrah,Mami tace Kai Na Matsu ayi Bakwai a raba gadon nan muga kasonmu sai yanzu nake Dana sanin haifar Yara kadan,da nasan hakane ai Haihuwa zanyi da yawa shike Nan da gado me yawa zamu samu mu da talauci har abada,Afrah tace wlh kuwa ai Ni na Matsu a raba na sake siyo dankareriyar mota,Haka suke ta hirarsu ta gado ko Bakwai ba ayi ba.
Rahmatu, Haule da Bilkisu sun hade kansu su Matan su uku da yaransu Suma suna so zasu hada Kai da lauyoyi sabo da kaso me tsoka ya Fado kan yaransu,Haka yaran ma sauran Wanda Daddy ya Haifa dake wasu garin da iyayensu Duk sun zo sai an raba gado zasu tafi,kullum cikin fada da rikici suke,da gulmace gulmace,Abdallah Yana sane da duk abinda ke faruwa shi da Baba basa ko cewa kala,Haka samarin ma kowa ya Dora burinsa akan gadon da zasu samu,Wanda ya mutu shi ya mutu.
AsmaBaffa
[12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: 🏵 TUBABBIYA🏵
26-30
Official
By
AsmaBaffa
KHADIJA MUKTHAR, HAFSAH,HAFSY and HAJIYA ABOU.
Page nakune.
Washe gari anyi sadakar Bakwai yayin da kowa ya watse sai iya Yan gidan,Abdallah,Usman,Sagir tare da Baba sune ke hada Kan dukiyar marayu kaf Ana tattara komai sabo da tarin dukiyar Daddy sai dai Alkali da kansa ya raba tafi karfin rabon Yan fake fake,ga Yara jimgim a kanta, Hafsatu matar Baba ta fada wajen malamanta ganinta Abdallah ne akan komai na dukiyar Bata San Shirme take ba,sabo da gulmar da Yan gidan keyi akan gado yasa Baba yace a fitarwa kowa hakkinsa da wuri a huta tunda Allah yasa Daddy ba a binsa bashi,su Rahmatu da Suka hade kansu sunga abin ya wuce tunaninsu baza su Samu damar cutar ba,sai sukayi fada ko wacce tace daga ita sai yaranta,Mama dasu Khadija sai kallon ikon Allah suke suna mamaki gaba daya ba wadatar zuci,son duniya ya rufewa iyalan Daddy ido.
Humaira taga Shuru har yanzu su Khadija Basu dawo ba suna family house har an kwashe 2wks Abdallah Bai ce ta koma ba itama Khadija Bata nemi ta koma ba sabo da ko ganinsa Bata yi kullum suna fita Kan harkar Gado.
Yau da safe Khadija ta shiga bangaren Mami zata gaida ta,Ko amsawa Mami Bata yi ba sai ma cewa tayi ke Dan Uwarki tashi ki barmin part bana son gaisuwar ko Dole ne shegu Tubabbun banza agololi wlh sai kun barmana gida tunda bana ubanku bane,Ai za a raba gado wlh sai dai Uwarki su San iinda zasu koma gida na magada ne Wanda ya Baku damar Zama a gidan ya mutu sai muga inda zaku zauna,Afrah ta amshe da shegu matsafa munfi karfinku wlh abinda kuka yiwa Abdallah yake kulaki mu Baku Isa ba.
Khadija ta zaro Ido tare da furta Allah baka hakuri ta mike ta bar musu part din kamar zatayi kuka,a Hanya taci Karo da Abdallah ranta a bace ta wuce Bata ko kalleshi ba,da sauri ya riko Hannunta tare da jawota gabansa,Kanta a kasa Taki ko kallonsa yatsansa yasa tare da dago habarta ta kalleshi idonta cike taf da hawaye lfy? Ya furta dama kadan take jira sai ta fashe da kuka tare da fadawa jikinsa,Tsigar jikinsa ce ta tashi yarrrrrr da kyar yace me akayi Miki? Mami ce? Kai ta daga Masa tana shesheka tace zagina Yana Yi Wai na miki asiri kana so na,yaushe kace kana Sona Dan Allah? Abdallah ya danyi Murmushi kadan yace bance ba Kam,Khadija tace to ka fada Mata pls baka Sona,Harara ya Mata kadan ya goge Mata hawayen sannan yace jeki shirya Driver ya maidaki gida Kinga kin huta da Mami ko? Murmushi tayi tace to yaushe Kai zaka dawo? Anjima da dare,Ok tace da murna ta wuce da gudu.
Khadija tana shiryawa tayiwa su Mama sallama sai gida,Humaira tana ganinta tace Alhmdllh,Saida ta Bari Khadija ta Gama gyara part dinta neat ta Shiga wanka sannan ta lallaba tare da Barbada maganinta kasan pilonta ta fito tana murna.
Khadija ta shirya abinci taci ta koshi tana jiran taga dawowar Abdallah Amma Shuru,a Palo bacci ya kwasheta har gari ya waye ko bedroom Bata shiga ba,Hakan baiwa Humaira Dadi ba Amma Haka ta Kuma lallabawa bayan Khadija ta gyara bed ta barbada Mata again lokacin tana kitchen.
Hafsatu ta karbo itama nata Maganin Na Bokanta,Suma sauran matayen sun zage wurin neman Mafita,Mami muguntarta kawai take hadawa akan Baba Dole ya kwashe iyalansa ya bar musu gidansu na gado.
Yau da safe aka Tara kowa Alkali ya raba gado Babu zalunci,yanda yayi rabo kowa ya gamsu tare da shedu Yan uwan Daddy da lauyoyi tare da Yan Uwan matayensu,an fitar da komai duk hadamar mutum Dole ya hakura da yanda aka raba sabo da ba zalunci,Mami ce kadai take Jan tsaki ita Wai an cuceta tana habaici,Baba dama ya Gama shirinsa zai bar musu gidansu ya koma nasa Wanda Daddy ya bashi na Kaduna kusa da Family House nasu Unguwa Daya suke,Mami da sauran Mata suka dinga bakin ciki cewar ai Baba zalunci yayi a cikin gadonsu ya sata,Mama taji dadin barin gidan zasu huta da Jarabar gidan,Hafsatu kuwa tafi so a zauna ayi ta kwasar bala'i,,Abdallah kuka yayi sosai da wasu samarin ganin Mutuwa me tonon silili Baba ya bar gidansu da iyalansa,Baba motocinsa biyu masu kyau Abdallah ya Kara Masa guda dalleliyar gaske ba tare da kowa ya sani ba.
Kowa Dukiyarsa an damka Masa Yara da Mata Kuma an bawa yayyensu manya wasu Kuma iyayensu sun karba,Mami kaf ta tattara na Abdallah Dana sauran yaranta ta karba Wai ita zata ajiye musu,Kowa yayi mamaki duk girman Abdallah Wanda ko dukiyar Daddy ma shike juyata kaf Amma Wai zata ajiye Masa,Wanda Daddy ya bawa Baba a bawa Abdallah kawai Baba boyesu yayi Bai bawa Abdallah ba Yana tunanin sai Nan gaba idan sun samu nutsuwa.
Bayan komai ya lafa Yara duk wasu sun Fara baragaza da kudadensu,Hafsatu takanas ta tafi gidan Abdallah Wai ziyara tajewa Humaira,Humaira tayi Mata wulakanci ta shige daki,dama Hafsatu abinda take so kenan ta samu ta lallaba sama part din Abdallah ta saci rigarsa jallabiya da takalminsa ta fito ta gudu gida, Ranar Kuma Abdallah ya dawo gidan shima,Khadija har an kwashe kwana biyar da dawowarta tuni ta kwanta Kan maganin da Humaira ta barbada Mata,Ganin Bata bar gidan ba Humaira ta Fara takaici tana zagin malamin ita kadai,Abdallah Yana wanka a part dinsa Allah Allah yake ya Gama yazo yaci abincin khadijansa me Dadi bai sani ba Khadija yau tun Sassafe data yi wanka ta shirya cikin Arabian Gown tayi kyau ta hada kayanta a katuwar Akwati tana Jin kamar Ana hura Mata wuta a gidan a gigice ta salale da akwatinta ta bar gidan gaba daya,Kuma Bata iya tuna kowa nata in Banda Abdallah sunansa kadai take iya tunawa kawai ta manta kowa da komai,ta manta wacece ita har sunanta Bata sani ba.
Bayan Abdallah ya Gama wanka kamar sabon Ango ya fito Yana Murna ya nufi part din Khadija duban duniya Bata Nan,ba inda Bai dubaba na gidan Bata Nan,a gigice ya duba part dinsa ya fada dakin Humaira ta juyo a tsorace yace Ina Khadija,Humaira tace Ina ruwana Zan boye ta ne ko Ni na Aurota,tsaki yaja ya fita wurin masu Gadi Suka ce ai Hajiya karama ta Dade da barin gida tun safe,Mota ya shiga kawai Yana kallon hanya ya tafi Family house,gidan Baba,har gidan frnds ko Ina ya duba ba Khadija ba labarinta,Mami ma cewa tayi ta tafi karuwancinta,gida ya dawo idonsa jajir Yana hawaye ya wuce dakin Humaira dake waya da Zuly suna sheka dariyar murna harda Ihu,Yana shiga shi Yana zargin Humaira domin Khadijansa Bata nisa da gida ba tare da ya sani ba,Wuyan Humaira ya shaka Yana Ina Khadija,Wlh duk inda take ki fito min da ita kafin na kasheki,Humaira tana Kakarin mutuwa tace wlh ban San inda take ba,ban sani ba,Waya ya Fisgo ya fara Tafkawa Humaira Yana tsula Mata,kuka da ihu takeyi Amma taki fadan gaskiya,Mari Saida ya Mata yafi goma,Fuskarta tuni ta kumbura sumtum, Amma Humaira Taki fadan gaskiya dukanta yakeyi yasan wlh da Sa hannunta har sai da ya farfasa Mata ko Ina na jikinta masu gadi da Yan aiki suka shugo agaji yace wlh duk Wanda ya tako dakin Nan na koreshi daga aiki ba shiri suka juya Suka tafiyarsu dama Humaira ta Addabesu Bata da mutunci,Ganin baza ta fada Masa ba kawai sai ya dakko takarda da biro yace me kika yiwa Khadija ya furta da kakkausar murya,Humaira tace ban sani ba ya rubuta Mata na Sakeki saki daya ya cilla Mata takarda yace kafin 5mnt ki tattara ki barmin gidana,fuuu ya fita a mota ya fara neman Khadija lungu da sako,Mama da Baba ma sun bazama,Haka su Dr Hussain Amma ba a ganta ba,tuni Har an bada Sanarwa gidan radio da tv da gaggawa Amma ba labarin Khadija.
Humaira kuwa Mami ta Kira a waya tana zunduma kuka ,sai ga Mami da Afrah a gidan taga harda takardar saki,ran Mami ya baci tace Alhmdllh tunda saki daya ya Miki Baki saku ba wlh,zaizo ya sameni tashi muje asibiti ki koma gabana da Zama wlh Dole sai ya zauna dake muje,Humaira tana murna ta lallaba Suka tafi asibiti akayi treating nata Suka dawo Family House Ana gulma labari ya watsu tuni a ko ina.
Hafsatu sai Murna take taga Mama dasu Merry na kuka sun rasa inda zasu saka kansu,Su Madam Ngozi duk an tambayesu Basu ga Khadija ba,Abu kamar Wasa har an kwashe 3days Abdallah Yayi kukan fili Dana zuci,kamar zai mutu da bakin ciki,Addua yake ba dare ba Rana,Haka su Mama da Baba ma basa bacci.
Mami ta nemeshi Amma yasan akan Humaira ne sai yaki zuwa,Hafsatu tana dawowa daga kauyensu ta samu da dare ta wuce can Bayan gari gidan Tururuwa ta Haka wani Rami ta binne layoyi sannan ta saki wata farar kaza akan gidan tururuwar tayi fuffuka ta fada daji da gudu sai da ta Gama ta dawo gida tace daga gidan Kawarta take.
Kwana Uku tsakani Abdallah ma ya fito kenan zai tafi Office tare da neman Khadija sai yaji kansa ya Sara tunaninsa ya kauce kawai sai ya ajiye key din motar a kasa ya taka zuwa bedroom ya Hado kayansa a akwati shima ya fice a kafa ya fita daga gidan,me gadi sunyi tunanin lfy wani Abu zai dubo domin baiyi zaton Abdallah ba lfy yake ba ganin kullum a firgice yake tun bacewar Matarsa.
Tunda Abdallah ya fita baibi hanyar titi ba sai dai yayi ta bin lungu da sako Yana garari har ya tsinki kansa a Tasha masu saka mutum a mota suka Fara murna passenger ya samu Suka karbi akwatinsa suna Alhaji Maiduguri zaka je? Drop kake so? Abdallah Yayi Shuru sukace Maiduguri zakaje ko Lagos? Abdallah yace Maiduguri ai kuwa suka ce Drop kake so kawai yace a'a, sai suka sashi a wata katuwar Bus a gidan gaba,Can anjima kafin mota ta tashi sai ga Khadija da Gudu ta shigo tashar da akwatinta futu futu da ita tana zuwa suka tambayeta Maiduguri Hajiya? Tace ae itama aka sa Kayansu a Boot suka sata a gidan gaba ita da Abdallanta,Babu Wanda ya gane Dan Uwansa kamar Baki,Khadija ta muskuta sosai tare da ture Abdallah da mazaunanta tace Malam ka matsa ka tare wuri tana hararsa,Abdallah tsaki yaja ya matsa kadan duk ya faffake wajen ya Saba da harkar manya,kallonsa Khadija tayi tace Kai Bawan Allah kana Kama da wani,Bai kalleta ba yace wa? Khadija tace Wanine na manta sunansa Ni dai,kaima Maiduguri zaka je? Abdallah yace Haka sukace masu motar,Khadija tayi dariya tace Allah irin nawa sunce Wai Maiduguri Zani Ni kuwa nace ae to Wai mece Maiduguri ne? Abdallah irin shegen Nan yace Bank ne fa wajen cire kudi,Khadija tace Kai baka sani bama Ashe wajen Saida lemo ne,muje musha lemonmu a can,Wanda suke motar Ana Jin hirarsu kowa Yana mamaki to su basuyi Kama da Mahaukata ba Kuma,suna ji akace a kawo kudin mota,Sai Abdallah ya zaro dubu goma ya Basu sai sukayi tunanin su biyu ya biyawa har Khadija dama Bata da sisi,Suka dauki kudin mutum biyu suka bashi ragowar kudinsa.
Karba yayi tare da maidawa Aljihunsa, mota ta tashi suka Fara tafiya,ko minti biyar Ba ayi ba Abdallah yaja tsaki yace kai me mota Wai ba a zo bane har yanzu? Kowa ya bude baki a motar,Khadija tace aikin banza tun dazu sai tafiya akeyi ko kwana aka ce muku zamuyi a Hanya? Shuru akayi Ana mamakin Anya kuwa masu hankali ne conductor yace yaa ke Hajiya ko ba Borno state zaku bane,Khadija tace Muna shiga uku Muna lalashewa anshe maki Maiduguri kace ae to mu wlh ba Borno state zamuje ba Maiduguri zamuje wurin Shan Lemo,dariya aka kwashe da ita,Abdallah yace Kai...,sai Conductor yace yawwa me hankali fada Mana Kai ai Maiduguri kukace zakuje ko? Abdallah yace yes Bank ba zamu cire kudi,Salati aka saki a motar Driver yace Dalla ku kyalesu Yan rainin hankali suna Bata Mana lokaci gasu lafiya dasu Amma sai wani Raina mana hankali sukeyi, Khadija tace hey Ina zamu ga hankali naka har mu Raina maka shi,aikin banza kanayi, Kuma ka daina zagi namu.
Tafiya akaci gaba da Yi har Khadija tayi bacci Abdallah Yayi bacci shima,Basu sani ba suna farkawa ba gida