Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah karka yiwa Abdallah auren Dole,baka gani duk ya rame,baida nutsuwa,ko Abinci Bai fiye ci ba,idan aka Masa Haka zai cutu Daddy,Daddy yayi Murmushi yace Khadija ko dai kina son Abdallan nawa ne? Da sauri ta hangame Baki tace Daddy a'a Frnd Dina ne kawai Yana min kirki shi yasa Kuma har kudin break yake bani,yasa a kaimu schl kamar kowa a gidan Nan,to kaga duk me maka Haka ai Dole ka damu da damuwarsa That's why ma nace Kar ayi Masa,yanzu Daddy ko Murmushi ya daina Yi min,idan na Kai Masa abinci baya ci,part dinmu ma ya daina zuwa,Kuma before Daddy idan kana ganin dariyarsa kullum da yawa da Murmushi,harda Icecream yake siya min,da kaza katoto,yanzu idan Ya Tafi wurin Matarsa shike Nan Kuma baya sonta fa.

Daddy yayi Dariya kawai ta manya yace to zanyi tunani Khadija jeki,Tun daga wannan rana kullum da safe ko dare sai taje wurin Daddy taji ko yayi tunanin sai yace baiyi ba,har aka kwashe wata guda biki saura sati Biyu,Yau Khadija tana shiga part din Abdallah sai ta Iske Yana kuka saman Sallaya tunaninta auren Dole yakewa kuka sai itama ta zauna a gefensa ta fashe da kuka,Suka ruguntsume suna ta kuka,Dan shi dayaji Khadija tana kuka sai ta Kara Masa karfin gwaiwar yin nasa sabo da shi gani yake Daddy mutuwa zaiyi shine damuwarsa bana auren ba,Ita Kuma Khadija tsoronta za a Masa auren Dole ta manta ma taji Daddy nada Ciwon zuciya ta auren dolen Abdallah takeyi.

Tana kukanta tace kayi hakuri kaji idan ka aureta ka saki shegiya saki uku zaka Mata,ranar da aka kawota gidan nan da Sassafe zanje na Mata shegen duka dashi zatayi breakfast,duk kuncin da Abdallah yake ji Saida Khadija ta bashi dariya,a ranta tace Kinga Yana dariya Ashe Lallai Yana so na Duke ta ya tsaneta sosai,a fili tace ka daina kuka sai na ci Ubanta wlh kaji na rantse sai tasan ta aureka tunda munafuka ce tsinanniyar yarinya,Ni Malam liman ma ubansa naci a kauye.

Abdallah sai gashi ya daina hawayen Yana dariya,Mikewa yayi tare da wanko fuskarsa ya wuce wurin Mami,tana ganinsa ta tabe Baki Abdallah ko kashe kanka zakayi Dole sai anyi auren nan kaji na rantse,Murmushi kawai yayi ya gaidata ya fice Bata San meke damunsa ba,Wurin Daddy yaje suka Sha Hira sai ga Khadija tazo tambayar tunanin Daddy Ina ya tsaya,tana gaida Daddy ta zauna kusa da Abdallah tare da furta Daddy kayi tunanin? Daddy zaiyi magana tace Sirrinmu ne fa Daddy karka fada Abdallah yaji,Daddy yace gaskiya ne nayi tunani na yanke hukunci Khadija me kyau kije kiyi Addua kawai.

Khadija tayi dariya tace tnx Dad ta kalli Abdallah tace na ceceka yaron Daddy ka Fara murna kawai ta fice da gudu, Ana ta shirye shiryen biki,Khadija kuwa ta mike kafa sai fada takeyi ku Gama gyaran banzarku baza ayi wannan aurenba.
Tana part din Mami duk sun baje Kaya sun sata aiki,ta kalli Afrah dake ta iyayi Khadija tace ku Gama wannan aure bazai yuwu ba,baza ayi shi ba,kune Baku sani ba,Mami taji a kunnenta tana Fitowa ta rufe Khadija da duka Dan ubanki mugun fata kike Mana shegiya matsafiyar banza Da kyar Khadija ta kwaci kanta tare da guduwa part dinsu.

Duk wani anko da komai Baba yayiwa Su Khadija Suma,Khadija ranta fes nufinta baza ayi biki ba kawai ta dinga gyare gyare ita da Merry kamar Amare Baba ya Basu kudi Suma na gyaran da akeyi,sun Gama shiri Daddy yace baza ayi shagali ko guda ba,za a daura aure kawai suyi Dj a gida a Kai Amarya ba biki,Hakan yayiwa Abdallah Dadi,Amma Mami kamar zatayi ihu sun Gama shirya karyar da zasuyi a bikin Daddy ya rusa sai haushi suke ji bikin farko a gidan an hanasu,kishiyoyin kuwa sai Murna Yan bakin ciki,Hafsatu Sai da ta rangada guda an Hana biki tana murna.

Ana gobe Biki Baba da Mama sun Dade a wurin Daddy suna magana,Su Khadija kuwa an tafi saloon da Lalle,Gida ya cika da Yan uwa da abokan arziki tare da kawayen Yan Matan gidan,abokan Ango Dr Hussain ma suna part din Ango an gayyaci frnds da yawa,Khadija ma ta gayyaci Yan schl frnds nasu mutum hudu duk da cewar Bata tunanin za a daura Auren Nan,Abu Kawarta ta kauye da Madam Ngozi sunzo bikin,Khadija tana lalle Bata san Abu tazo ba.
Sai wurin 6pm Suka dawo Abdallah ya gaji da nemanta ta samo Masa abinci sai yayi ta aikowa ace Basu dawo ba,Kyan da Khadija tayi ya baci lalle ne na kece raini kamar itace Amaryar,gashi yaci gyara,Ganin Abu yasa suka buga tsallen murna,Abu tace kin ganki kuwa Wallah kamar Yar Shugaban kasa, Kin daina wasan kasa ke ko? Khadija tace ai nan birni ne basa Yi Ina so muyi basa Yi,Abu tace ai nazo zanyi sati guda sai muyi wasanmu ko? Khadija tace har katuwar Teddy gareni da ita zamuyi abinmu.
Madam Ngozi tace kunfa girma Amma Kuna wani Wasa yanzu wa yake Haka,Khadija tace wanne girma Ni dai zamuyi Ina so.
Abinci sukaci Khadija taja Abu Garden Suka Fara wasansu Khadija tace Ayyiri yiri Anyi aurena,wasansu suke Basu San Su Sagir kannen Abdallah da abokansa sunzo wurin bama suna Hutawa,Suma su Abdallan da frnds nasa duk sun dawo Nan Ana ta Hira,sai lokacin Suka kula dasu Khadija Jin gudar da Khadija ta rangada kamar an kawo Amaryar gaske,hakan shi yaja hankalinsu suke saurarar wasan yaran.

Khadija tace to anyi min Aure kece Mama ta sai ta fashe da kukan karya Wai an kaita gidan miji tana kuka,Abu tace to kizo ganin gida wurin Mamanki kina da ciki Kato,Khadija ta cire dankwali tayi ciki dashi ta taho wurin Abu tare da cewa Ina kwana Mum,Abu tace oh Baki gaji ba Khadija wannan katon ciki Haka dashi kike yawo da zauna me za a dafa miki? Khadija ta dafe cikinta ta zauna da kyar tace wash a shagwabe Agwalima nake so kawai,Abu tace kash Ina ma da yaro sai ga Ahmad kanin Khadija sukace zo muyi Wasa Ahmad,Shima yazo wurin Suka Fara wasan tare Abu tace karbi Tanimu ga kudi maza siyowa yayarka agwalima,Ahmad ya karbi ganyen bishiya matsayin kudi sannan yaje bayan bishiya ya tsinto wasu Yayan bishiya kana na ya kawo,Khadija tayi zaman masu ciki tana cin karya,bayan wani lokaci Wai sai ta Kama Nakuda ta haifo Teddy dinta,Abu tace gaskiya Yar Nan da kyau take santali Khadija tace Mama ki kawo a Bata Nono Tasha,sai sata a kirjinta tace yawwa ta koshi, Haka suke ta wasansu Abu shegen wayo gareta kamar Yar tsofaffi,samarin suna jinsu ta baya can suna ta dariya musamman Khadija komai sai ta gwada.
Da suka gaji Suka ce Wasa ya watse kowa ya tashi Merry ta fito tace ke Khadija Mama tace tun dazu Yaya Abdallah ke nemanki Zaki Masa aiki.
Khadija ta dafe kirji tace wlh na manta Yana Ina? Gashi can a bayanku shi da mutane,Kunya ta rufe Khadija tasan Dole sunji wasansu da sukayi na Haihuwa,Merry Hannun Abu taja da Ahmad suka yi ciki,Dankwalinta ta yafa saman doguwar rigar Tata,Lalle Kam gashi Nan yayi Masifar kyau da gashin Nan daya sakko ta baya,frnds na Abdallah sai yabawa sukeyi kowa Yana so Khadija ta Zama mallakinsa.

Hausarta ke Basu dariya da Bata iya ba,nesa kadan dasu ta gaishesu tare da cewa Bro Abdallah Mama tace kana nemana? Sai yanzu Kika ga damar zuwa? Na manta ne I'm sorry lalle naje fa kalla nayi kyau ta durkusa a gabansa tare da nuna Masa hannayenta da kafa,Kallo daya yayi Masa tun dazu suna Wasa ya Gama gani dama, Harara ya zuba Mata tayi Shuru tace na tafi? Jeki yace kawai zata sheka da gudu kenan ya Mata mugun kallon da ba shiri ta nutsu ta fasa gudun ta tafi a hankali,tana tafiya frnds Suka Fara Koda kyawunta wasu ma sunce suna kamu,shi dai Abdallah Bai kulasu ba.

Sai da Khadija ta Shiga cikin Yan biki taji Ana cewa lefe akwati ashirin da biyar Mami tasa Abdallah hada,takaici ya Kama Khadija tace Allah yasa wuta ta Kama kayan Amaryar sai da Mami ta duketa.

Washe gari kowa yayi Shirin tafiya Kano a jirgi abinka da manya maza an dau wanka da wasu Matan Dangin Ango za aje a sheda,Wai Wai Ango yau kamar yau aka kyankyasheshi yazo duniya sabo da kyan da yayi abin alajabi ne ma,Khadija da wuri taci kwalliya cikin Shadda dakakkiya da Daddy yayi musu dama tunda taga an kawo kalar da Ango zaisa farar shadda itama tace Baba farar shadda zai siya Mata,Su Kuma su Merry nasu daban,Khadija ita kadai tayi anko da Ango ba karamin kyau tayi ba itama gidan kwalliya taje aka Mata har dauri ka rantse itace Amaryar ganin da gaske fa Daddy sai yayiwa Abdallanta Auren Dole shi yasa ta hakura kawai tayi kwalliya yanda baza a barta a baya ba.

Kuma dama ta rantse Abdallah ne zai Fara ganin kwalliyarta sai da ta Bari sun fito da Frnds nasa zasu tafi Airport Mami su Afrah da sauran Matan gida duk suna compound Ana kallon Ango Ana Masa pics sai ga Khadija Dan tsokana bul ta fito kusa da Ango ta karaso,Da kyar Abdallah ya ganeta sabo da tsananin kyan datayi ga Daurin dankwalin ya Hadu ka rantse Amaryace sukayi anko da Angon ,Dariya tayi Masa tace munyi anko da Ango,Murmushi ya saki ba shiri,Dr Hussain ya shiga kyastasu a pics, Khadija ganin kowa na kallonta da mamaki ta dafa Ango aka daukesu,ta rike hannunsa shock na taratsatsi a jikinsu Dr Hussain kuwa sai dauka yake Yana Basu style,
Daddy da Baba Suka fito Khadija ta jawo su ta hadasu da Ango Dr Yana ta daukansu ba ji ba gani sai Da Baba ya koresu,Khadija tace Ango saura daya gobe fa zaka bar Mana gidan,Hannayenta ya riko biyu suna facing juna Dr ya dauka kyas kyas,Sai ga Mami ta Fado tare da make Khadija Saida ta Fadi a kasa,sannan ta bita da ashariya,ganin Haka yasa angwaye Suka tafi mota Drivers suka jasu,Daddy Yana kallon abinda Mami tayiwa Khadija ta cikin mota,kwafa yaja kawai suka tafi.

Su Afrah duk anbi jirgi an tafi sheda Daurin auren Yayansu,Khadija kuwa part dinsu ta koma Dakinta inda Abu ke zaune tana kwalliya sai ji tayi Khadija ta rushe da uban kuka,Abu ta saki powder ta tarwatse tace nashigesu ke Kuma lfy? Khadija tace Daddy zai Masa auren Dole shike Nan ya daina dariya,Tsaki Abu taja tace banza sai kiyi ai har kullum baza ki hankali ba Khadija,Kinaga yanda yake washe Miki Baki Ana muku hoto kice baya sonta munafuki Yana son Abarsa kina Nan Zaki ji ya dirka Mata ciki ta haihu, gwara ma ki daina batawa kanki lokaci muyi wasanmu Ina ruwanmu mu Dan anyi Masa auren Dole.

Khadija tace anjima rawa za a Sha a gidan Nan,wlh zamu cashe a gidan nan ai Ni ko Dan rawar Nan ma na daina fushi gwara da aka Masa aurensa,Abu tace ahaf aikin banza kin Sa na fasa Hodata Yar dari uku da Hamsim wlh sai na dauki Taki kin biyani,Khadija tace taf sai dai na karbo Miki kudi wurin Abdallah ki siya wata.

Kano can masallaci Yan Daurin aure suka Sheda An daura Auren Abdallah Yousuf da Humaira A.A.Sani Kan Sadaki Naira dubu dari biyu,Ba a Gama murna ba Suka ji an sake bada Sanarwa An daura auren Abdallah Yousuf da Khadija Adam akan Sadaki dubu dari biyu,ko Shi Abdallah daga sama kawai yaji abin Kamar a mafarki,bakin ciki ya kamashi shi ya tsani Mata biyu a duniya tun daga kan abinda ya gani akan Daddy dinsu ya kudurce a ransa ko baya son mace ko wanne Hali gareta matukar ya aureta to ita kadai zai zauna da ita ba kishiya sabo da yaransa,Kar a samu matsala,Shi Kuma Khadija za a bashi yarinya karama me ta iya idan Banda wasan Yara,ko girkin ma kawai dai Dan ta Dan iya ne da Tsafta,Abokansa suka yanyamesa Ana Ashe da biyu dazu suka dinga pics suna soyewa Ashe munafunci ne abin Amma ba a buga Iv da Khadija ba, tuni masu kaunarsa sai Murna ake tayashi Mata biyu lokaci guda,Haka su Daddy ma dasu Baba Ana ta murna tare da Baban Humaira baiji komai ba sai Murna yake ya aurar da Humaira ya Huta da halayenta na banza duk da Yana sonta sune silar lalata Mata tarbiya Amma yaji dadi ya aurar da ita,Humaira da Mamanta tare da dangi tunda Suka ji su biyu aka aura sai suka Fara balai an yaudaresu wlh da hakane baza su bada yarsu ba,an tona musu asiri,An Basu kunya kamar Humaira za a hada da kishiya,Nan fa aka dauka Ana ta cacar Baki su Humaira harda Ihun kuka da zazzabi,Uwarta ma Haka sai kuka tana Mami ta cucemu.

Afrah ta fashe da kuka data tabbatar Khadija agola ake nufi sai ta makowa Mami waya Wanda Basu San ma me akeyi ba,Mami tace Hello Afrah an daura tana murna,Kukan Afrah taji tana Bata labari a Nan take Mami ta sume aka kwasheta sai asibiti,Maman Khadija kuwa dama ta sani da ita akayi Shawara Da Daddy da Baba tare Suka yi Shawara.
Gida tuni ya dauka kafin kace me zance yaje ko ina,Khadija Bata San me akeyi ba suna ta uban Wasa da Abu a bed room,ganin masifa ta barke a gidan Madam Ngozi sai zaga Palo take tana ewooo....Yarinya Karami Khadija aka yiwa aure heeeeeey Hausa people woooo ahhhh...Mama Abinci ta kaiwa su Khadija tace zata kulle su da key Kar su yarda ko motsi suyi fada akeyi a gidan,Khadija Bata San me ba taga har ruwa duk an kawo musu mama tasa Key an kullesu a daki su kadai,duk Basu San me akeyi ba,Yan Daurin aure na dawowa bala'i ya balle a gidan Mata garin habaici Suka Fara kokawa da dukan juna wannan Mata da danginta waccan ma Haka aka fara
da fashe fashe har da masu dauko ludayin Miya,wasu an fasa musu Kai,wasu fuska da hanci etc,Afra ta makure Nana firdausi Yar Hafsatu budurwa suna ta kokawa,maza Sunyi Sunyi a raba fadan yaki,sai da Daddy ya Kira Yan Sanda yace duk su kwashe Masa su sannan aka samu lfy akayi solving case kowa na Jin haushin kowa Daddy yace duk wacce ta Kara magana akan auren Khadija da Abdallah Bai yafe ba,Haka aka ci gaba da biki.

Sai ga Mami ta tashi an dawo da ita daga asibiti tana shugowa ta Fadi a tsakar gidan ta Fara gunjin kuka tana tsinene,Allah ya tsine maka Alhaji Karami Kai ka auro Mana su,shege tsinanne,an aurawa Dana Talauci,za a shafa Mana talauci,wayyo..wayy....yoiiiii ta daura hannu a kanta ihu take Wanda har makwafta suka zo,bacin Rai kamar zai kashe Daddy,Abdallah,Baba,mami ta Gama tona musu asiri an cika gidansu,Mami Bata hakura ba Ta samu Kayan Dj ta farfasasu kamar ta haukace,Daddy yace Kar Wanda ya kulata,har gaji Dan kanta ta Gama,tace In kin Isa Mama ke da yarki ku fito wlh sai na kashe ku,in yaso na Mutu a prison.

Abdallah wurin Daddy ya koma yace Daddy saki Mami Dan Allah,Daddy yace Sam Sam abinda ta shuka a sannu zata girbi abinta Abdallah Nan Ya Masa Nasiha akan rike matansa da adalci.
Securities ne Suka Kori Yan kallo da kowa gida ya koma tsitttt kamar anyi mutuwa,abin arziki ya Zama tsiya,Mami wani tunani Tayi danginta Suka zazzageta akan abinda tayi tare da Bata shawarar banza,Wata da suke ce Mata yashuwa tace ke banza ce ai yanzu ba Haka akeyi ba ai an waye,kawo kunnenki kiji....sai suka kwashe da dariya sannan Mama tayi wanka ta cakare ta biya masu DJ Kayansu ta dakko wasu masu DJ din gida Kuma ganin komai ya lafa aka ci gaba da shagali musamman da kida ya fara tashi a gidan,Daddy da Abdallah kawai Murmushi sukayi Baba yasha tsinuwa wurin Dangin Mami,Amma yaga zasuyi kida yace kai da wata a kasa.

Khadija tana bacci duk Bata San me akeyi ba ita da Abu,kidane ya tashesu sukayi wanka Khadija ta sake shiri cikin lace light blue.
Mama ta budesu tace kuzo kuje ku cashe Kuma,ke Khadija Zaki ji Ana cewa kema matar Abdallah ce karya sukeyi karki kulasu kuyi bikinku kawai.
Khadija tace to dama Ni Ina ruwana iyakaci idan an kawo Amarya naje na mata dukan tsiya Abdallah Zan ramawa.












AsmaBaffa
[12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: 🏵 TUBABBIYA🏵









16-20









Official







By
AsmaBaffa












Wannan page naku ne masu Sharhi.

MAMAN KHALIFA,MAMAN AFFAN,OUM AMATULLAH,HAUWERH ZD,MMN BASMA, HAUWA IBRAHIM YARO,MAMAN SADEEQ,JEEDDAH LUV,MAMAN FATEEMA,SILENT QUEEN,WACY BABY ,MRS A and KHADIJA ALAD.






Lace din light blue ba karamin kyau yayi Mata ba fitted Gown ta fitar da surarta kasa ta baje,Madam Ngozi ta Mata Gogoro me shegen kyau,Abu ma cikin Atamfa Riga da skert sun Mata kyau kamar ba daga kauye ba,Merry da Ihsan sun canja Material me kyau Suma,Khadija sauri take taje wurin kida Bata San bala'in da akayi dazu a kanta ba,Abdallah yasha sabon wanka ya fito da Frnds nasa da yawansu,Khadija duk inda tayi sai taga Ana kallonta Ana nuna ta Ana gulmarta,Ango na zuwa wurin da Mami ta kirasu Wai Yazo suyi musu liki yanzu za a kawo Amarya Humaira gidan, gobe sabon shagali za ayi sannan a Kai Amarya Humaira,Khadija dama tuntuni tasan duk kalar kayan Ango da zaisa shi yasa duk kalar tasa Baba ya dinka Mata,sai dai Bata san yanzu zai sa kalar kayan taba sai suka sake yin anko ita lace shi wani arnen Yardi light blue,kowa daya gansu sai da yayi zargin dama can suna sani sukayi hakan har Mami,Data kalli Khadija sai data ji kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,dannewa tayi kawai da kyar sabo da shawarar danginta.

Abu ganin su Mami na filin rawa tace bamu da kudin liki ki tambayi Mana Abdallah naki Mana,Abdallah Kuma tuna Maganar Daddynsa da Khadija da tace yayi tunani wannan sirrinsu ne sai ya bashi tabbacin Khadijan ce tasa Daddya ya aura Masa ita,sai yaji haushinta yaji tsanarta zata jawo Masa auren Mata biyu,Khadija Allah sarki Bata San komai ba Merry Ce kadai ta sani Amma Mama tace karta fadawa Khadijan.
Khadija ta kutsa ta cikin abokan Ango Suka Bata waje sanin Amaryace da kanta,Kusa da Abdallah ta tsaya da karfi tace pls Bro kudin liki Dan Allah ka bamu muyiwa Mami,Hararar da Bai taba Mata ba ya watsa Mata ba shiri ta ja baya,Dr Hassan Yana kallo sai ya mikawa Khadija Yan 1k bundle guda,tace Sunyi yawa fa Dr niba Amarya ba zanyi liki Haka a banza ka Bari sai bikina Nima yazo,Karaf kunnen Abdallah,Dr ma yayi mamaki da Bata sani ba,sai ya bigi cikinta yace kina Ina duk auren da aka daura Miki yau,Dariya tayi tace nifa Mama a daki ta kulleni da key bacci Nasha da kawata ban San Ma anyi komi ba sai kida naji shine muka fito rawa.

Dr yace Allah sarki to ki bawa kawar Taki Mana gata itama Kyakyawa Haka,Abu harda Jin kunya an yabeta, Abdallah ya tabbatar Khadija Bata sani ba Kam gaskiya tunda har yaga ta iya rabar kusa dasu Mami tana musu yayyafin kudi,Sai harararta sukeyi,Afrah kuwa da kawayenta da Suka shiga Nan ma Khadija ta Fara musu liki sai Afrah ta take Mata kafa da takalmi me tsini sai da tayi Hawaye ba shiri ta fita daga filin,ta Dade a tsugune sannan Dan maita irin ta Khadija ta koma filin Nan tace a samusu Kida ita da Merry da Abu yau farin ciki zasu nunawa Abdallah,Merry kawai kallon Khadija take da tausayawa.

Aka saki Sauti Khadija ta fara rawar bajinta Wanda gaba daya aka koma kallonta domin ta birge kowa ka rantse sai da tayi training,Ana ta ganinta a Amarya marar kunya ita Kuma Bata San komai ba,Duk Wanda zai Mata liki sai Mami ta Hana matasa naso har wasu Matan Amma Mami ta Hana,Abu ta shige ta dinga zuba Yan dubun da Dr Hussain ya sake Bata,Abdallah ya mikawa Merry kudin a boye taje itama wasu Matan da mazan suka rufeta da liki,Ana Haka sai ko akace Ga Amarya Uwar gida Humaira ta iso,zo kuga Murna wurin Mami tare da Danginta,Kowa yasan Amarya ta hadu ga kyau Amma da ka kalli Khadija kasan ta zarta a komai.

Kawayen Amarya da Yan uwanta sai yatsine yatsine suke an tsaya da kida Ana ta nuna musu Khadija ta fito zasu fita daga gidan ita da Abu Wai yawo zasu je ita Bata San tana da aure ba,tuni Humaira da Danginta jikinsu yayi sanyi ganin Khadija ta zarta su nesa ba kusa ba,Khadija Kam a wajen gate suka wuce angwaye suna taku dai dai su a dole Yan Mata suka Shiga Napep Abdallah kamar zai saki ihu sabo da bakin ciki Ana kalle Masa Yar Amaryarsa Tasha kyau, gashi ma ta hau Napep wa yasan duniyar da zasu je Suma su kalli rabonsu,Merry Ce ta fito da sauri tana Ya Abdallah Ina Khadija yace ta shiga Napep tare da balbale Merry da masifa kun San Bata sani ba ai Gashi Nan ta tafi yawo gashinta a waje kaya sun matseta wannan Yar iskar kwalliyar da akayi Mata ai ba dai dai bane,Angwaye Suka kece da dariya Dr Hussain yace munafuki ai kana kallonta ta tafi Kai girman Kai baza ka hanata ba Muna gani muma muka kyale maka Albarka yanzu ka rufe yarinya da masifa Ina ruwan Merry.

Merry ta koma gida ta fadawa Mama,an Kira a waya Amma ta bar wayar a gida,har dare karfe Tara da rabi suna can yawo da Abu Wai suna ganin gari,Abdallah Yana part dinsa shi da Frnds nasa na kusa Dana nesa Amma sam ya kasa nutsuwa sai duba waje yakeyi ko zaiga Khadija ta dawo Shuru,Yana ta tsaki Yana duba agogo,Sai dariya abokai ke Masa Ana tsokanarsa.

Mami ta kirasu suzo gaida Dangin Amarya Kawai ya Hango Khadija wani Dan saurayi matashi ya rakosu har gida,English teacher dinsu ne da Merry tace saurayin Khadija ne,ita Kuma Khadija yawonsu kawai sukaje Suka hadu dashi a Hanya kusa da gida,Shine ya Dan tako musu ya rakosu ya juya gida.

Angwaye Suna shiga Suka gaisa Abdallah ya mike yace ya manta wayarsa Bari ya dawo,Part din su Khadija ya shiga,Mama ya tambaya Ina Khadija? Tace tana daki yanzu nayi Mata fada Kuka takeyi ma,Dakin ya shiga Abu tana dakin Merry, Khadija ita daya ce a dakinta ta kwanta saman bed tana Kuka,Kamshinsa yasa ta mike Zaune zubur tasan Abdallah ne yau Kuma har dakinta, gidan Ubanwa Kika je? A rude Khadija tace bafa...bafa....uhnm...wani waje bane..kawai yawo na Kai Abu,To wanne Dan Iskan ne ya rakoku? English teacher dinmu ne a Hanya muka gansa yace zai rako mu,yanzu Mama ta mareni ta dukani akan na fita,ai Ni ba yaro ne ba nasan Hanya bazani bace ba,Abdallah da masifa ya furta Ok gobe ki Kara fita mu gani pls ya juya a fusace tare da bugo Mata kofa,Khadija Bata gane ba tayi Murmushi tace yace gobe na fita again har da rokona,Aiko tunda Abdallah yace na fita Ba ruwana da fadanki Mama gobe zamu fice da Abu na kaita wani yawon, hh Khadija Bata gane gatse Abdallah ya Mata ba.

Washe gari karfe biyu suna yin Sallah Khadija da Abu suka ci kwalliya Suka saci jiki suka sake ficewa yawo,anzo Kai Amare neman duniya aka nemi Amarya Khadija aka rasa,Daddy zai Mata nasiha Amma ba Khadija ba Abu sun tafi yawo,Abdallah yaji labari tuni an Kai Humaira Sabon katafaren

Please Login or Register in order to submit comment