Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

talaka,Dana ya auri Yar Malam Shehu ai naji kunya,burina duniya tasan da zamana,so nake duniya tasan Dana ya auri Yar manya.

Mami Haka take ta kuri Babu ko sa Allah a ciki,duk abinda zaka dinga kuri ka Dora ranka Kai ba ruwanka da Allah to kuwa Allah zai iya kunyataka a idon duniya,Haka Kuma zai iya kyaleka ya baka abinda kake so ba ruwan Allah.

Garin Zamfara kauyen Nahuce Liman fa ya dukufa ya dage Dole sai yaga bayan su Khadija,tsafe tsafensa yake tayi akanta yarinya karama sabo da rashin Imani.
Khadija kuwa ta dage sai Kwangilarta take nemowa da yaranta suna aiki sosai,Haka Allah yake ko yaya kayi Abu idan yaso ya dafa ma sai asha mamaki,Khadija da kudin take ci dasu tufatarwa da kudin makaranta wa kannenta,Mama Sai mamaki takeyi kamar Wasa ga Khadija kuwa ta Zama 'yar Kwangilar harkar Noma, tayi katon asusu Ana Tara wasu kudin,ga samari yanda suke tururuwar sonta sabo da tsananin kyawun Khadija,indai kyau ne to a shafa Fatiha kawai a kanta,ga kyan sura da diri,skin dinta wata sumul sumul kasancewar babarsu Yar north Sundance farare ne kwal,Haka Babansu farin bafulatani ne,Khadija round face ne da ita,da hancinta madaidaici baiyi tsini da yawa ba,Idanunta Dara Dara,ga gashi har baya kusan tsakiya,hakoranta kanana kyawawa,ga dimple,girarta me yawa baka,Gata da uban Hips cinyoyi manya,gata da Da tsayi Amma ba can ba,kowa yaga Khadija yasan ta cika mace ta gaban kwatance,Haka su Merry ma kannanta kamar su sukayi kansu kyawawane sosai gwanin Sha'awa.

Khadija sabo da zaman kudu rawa wajenta kamar mazari Kuma na Yan kudu takeyi ayi ta girgiza mazaunai,a wani duka kasa tare da rike gefen Riga Babu kunya ko a gaban uban waye Haka suke rawa har Maryam Merry,A kauyen Khadija tana da kawa Abu,Abu yau tazo gidan ba Islamiyya ta samu Khadija da Merry har Ihsan tare da Ahmad sun kunna gidan radio an Sa wakar Wizkid suna ta tikar rawar suna ihu eh...eh...eh...sun cika gidan,yanda Khadija ke rawar zanku kamar kanwar Zlatan,Mama tana aikinta dake itama kudu ta ratsata sai cewa tayi Abu Bismillah ga rawa fa kiyi kema,kunya ta Kama Abu tace ban iya ba,Khairat ta wani duka tana eh....eh...chineke God ah...ah...we dey chill woooo let's dance Abu,Common eh...ehh Merry ma ta jawo hannun Abu Wai sai tayi rawa.
Mama tana kallonsu tana dariya harda gyarawa Ahmad rawar tana kalli yanda Khadija keyi maza ka koya kaima,Abu ta bude Baki Jin yanda Mama tace kunya ta rufe ta.








AsmaBaffa.
[12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: 🏵TUBABBIYA🏵








2








Official






By
AsmaBaffa





Auta, Asycool And Jannat page naku ne.







Khadija tana rawarta sai da Magrib tayi sukayi Sallah tare da cin Abinci suna ta Wasa tare da Abu Wai wasan Yar baby sukeyi Khadija ta Haihu Abu ce babarta suna ta abinsu,Khadija tace yawwa Abu Zaki koya min Hausa Ina so na iya sosai,Abu Kuma Yar Sokoto ce daga can suka dawo Zamfara gaba daya Hausar tasu data Zamfara ba irin ta kano da Kaduna bace,sabo da Hausar da banbanci idan sunji ta Kano da Kaduna sai suce Yan iska ne batsa sukeyi,su ma Yan Kano ko kd idan sunji tasu sai suce batsa ce,Dan Haka Khadija tace muje gindin bishiyar can,Abu tayi sauri tace ke Yar iska ce wallahi irin Yan Kano ce ke ba Haka ake cewa ba,Khadija tace ya ake cewa? Abu tace Gutsun bishiya ake cewa shine ba iskanci ba hhhh,Haka Abu duk tabi ta canjawa Khadija Hausarta ita Kuma Khadija ta rike ta gyara Dan Haka gaba daya hausarta idan Dan kd ko dan Kano yaji shima iskanci zai ce,Abu tace Khadija dare yayi Zan tafi gida Kinga mazan garin Nan fyade sukewa Mata,Khadija tace me fyade? Abu Kiri Kiri tace Ci ake cewa,wallah Wagga samari cin kaca zasu Miki sunka kamaki,Khadija tace oh raping da Hausa Abu da sauri tace Ci ake cewa shine ba iskanci ba,Khadija tace kamar Abinci? Gaskiya yayi dai dai chop chop,Abu tayi dariya tace Nima Zaki koya min Wagga turanci na lailayoshi ga mutanan wagga garin.

Khadija ce Tasha wanka cikin rigarta da kadan ta wuce gwiwa doguwar rigar atamfa red Dan siririn gyale red ta daura a kanta dama su Basu Saba lullubi ba sai in zasu Islamiyya suke saka hijab Mama ce kawai ke yafa gyale,ta fito tana tafiyarta da sauri kamar yaren kudu ba wani yanga ko Jan aji kawai tafiya normal kamar maza ba saurarawa, kaurinta kitika kitika a waje sumul sumul,sai kallonta akeyi a garin Haka ta biya gidan su Abu wacce itama ta shirya cikin Riga da Zanin Atamfa ta yafa gyalenta Wai kasuwa zasu tafi can cikin city din Zamfara,Tasha suka je tare da shigewa mota,Khadija tana ta wakokinta da yaren Igbo,Har suka je suka yi siyayyarsu suna dawowa kauyen sai suka ga wata fyaleliyar mota a gefen Gona da wani Dattijo Kyakyawa dashi me kamala,Khadija tace hey...Abu wait for me ga Alaji can me kudi zanje ko Zan samu Kwangilar aikina,Abu tace to Khadija,da Gudu ta Karasa wajen Mutumin tace Alaji aiki za a ayi maki na gona Ina da Yara sunfi Twenty zamuyi ka biya mu,Alhaji ya kalleta yace Ke Amma ba yar arewa bace? Khadija uwar surutu nanfa ta Fara bashi labarinsu kamar Haka:

Cike da gwarancinta hausar da kyar take fita Tace Alaji mu Yan Asalin Zamfara ne Cikin kauyen Nan na Fulani a Karamar Hukumar Nahuce, Adam Shehu shine Babanmu shi kadai Iyayensa Suka Haifa,ya girma Yana aikin noma sosai har aikin ya bunkasa yake Kai Kayan masarufi state daban daban,ganin yafi samun kasuwanci a kudu Anambra state ya koma can da Zama Baki daya sai dai yazo Nan ya siyi kayan ya koma can,ya Dan Jima sai Allah ya hadashi da Iyayen Mamanmu Yan Asalin Sudan ne sakamakon yakin da akayi duk aka kashe Yan Uwan Mama tare da sauran dangi da yawa,da kyar Babanta ya samu Suka gudo Nigeria ya sauka a Anambra state.

Babanmu ya tausaya musu ya dinga taimaka musu Nan Suka ga mutumin kirki ne suka bashi auren Mama Saudat,Bata ko Haihu ba Allah ya yiwa Mahaifinta Rasuwa sakamakon Ciwon Koda,Sabo da bakin ciki Babar Saudat Mama kenan ta hadu da Hawan jini itama Bata Dade ba Allah ya Mata Rasuwa,Mama Bata da kowa sai Babanmu Adam Shehu,Danginta Kuma na Sudan da suka rage sun Manta da ita ma,itama Haka kasancewar dama ba dangi na jini bane shi yasa ba a zumunci.

Bayan Saudat ta Haifeni Nice Khadija Babba Wanda yanzu shekarata 16 sai Kanwata Maryam 14yrs,Ihsan 12yrs sai auta Ahmad 9yrs, duk da Babanmu ba Mai kudi bane amma mun taso cikin gata ga karatun boko Dana Arabic,ko a Anambra state a unguwar talakawa muke gaskiya sai dai ba rashin ci da Sha bare rashin sutura,makaranta me kyau muke zuwa, Muna Yara lokacin Ina Jss1 Babanmu Adam ya Allah ya Masa rasuwa a hanyar zuwa zamfara motarsu tayi Accident,Munsha bakin ciki Wanda sai da Mama ta kwanta a Hospital na 2wks,bayan komai ya lafa Sai Mama Ta Fara Sana'a sosai dama a gidan haya muke zaune a can,a Haka har naje ss2 Maryam Ana ce mata Merry tana jss3 Ihsan jss1 Ahmad Yana Primary 5 Mama Kudi suka Kare duk an siyar da gonakin gadonmu dake Zamfara,zaman Kudu ya fara gagararmu, me gidan Haya ma ya Kore mu, Dole Mama ta tattaro mu muka dawo kauye,cikin Dangin Adam Suka ce ga gidan Adam ne daya Gina kafin Ya koma Anambra sabo da Haka Muka gyarashi muke Zama a ciki,gidane na kasa rubabbe.
Wannan aikin Dana nema a wajenka Alaji dashi Muka dogara,Ina da Yara zasuyi maka aiki me kyau.
Jinjina kai Alhaji yayi gaskiya yaji tausayinsu, yace to karatun Addini fa kunyi? Khadija ta daga Masa Kai yace munyi Dan kadan dai dai gwargwado Wanda zamu bautawa Allah Amma bada yawa ba,sabo da halin da muka shiga shi yasa,To Maman Taki Bata yi aure ba ita?

Khadija tace nice na hanata gaskiya Ina kishin Dad namu,baka ga Mama ba Kyakyawa kamar ba ita ta haife mu ba,gata da masoya Niko nace baza tayi aure ba,Alaji yace to muje Naga gidan naku idan nazo aikin sai na kiraki,sannan ban yarda dake ba sai na tambayi Mamanki,Khadija ta jawo Abu suka tafi tana ta zubawa Alhaji surutu yana dariya Dan Hausarta da kyar takeyinta.

Har gidansu suka zo ta shiga tare da Kiran Mama,Mama ta yafa gyalenta tare da Fitowa,Ai Alhaji Bai Zaci Haka matar take da shegen kyau ba,gata wayayya,Nan ya rude gaba daya,bayan sun gaisa yace Sunana Alhaji Tahir Amma anfi sanina da Alhaji Karami,ya tambayeta akan labarin Khadija, tace gaskiya ta fada Yace to sai Gobe zai dawo ya kirata suyi Masa aiki.

Murna wajen Khadija ba a magana har mota ta taka Alhaji ta dawo gida abinta,
Tunda Alhaji ya koma masaukinsa Hotel yake tunanin Saudat Mama,Allah ya Sa Masa sonta sosai,washe gari da wuri ya dawo kauyen har gida yaje Saudat ta fito Suka gaisa sannan Khadija ta bishi bayan ta gaidashi suka tafi gona tare,Alhaji Tahir yace Khadija Ina so muyi wata magana.

Khadija tace to Ina jinka Alaji,Yace idan nace Zan auri Mama Zaki yarda? Khadija kawai ta kalleshi sai ya Mata kwarjini ta kasa cewa a'a duk kishin Ubanta da takeyi sai ta samu kanta da yin shuru,Alhaji Karami yace Karki damu Khadija idan na auri Mamanki Zan tafi daku Gidana Zan kula daku kamar Yayan cikina,Khadija tace kana da aure? Yace ae matata daya Hajiya Hafsatu da yarana guda hudu,Nafisa 19yrs itace Babba,sai Hindu15yrs,Mubaraq 13yrs da Salis 10yrs, gidanmu estate gudane Kinga nida yayana ne Uwar mu daya ubanmu daya,shima a gidan yake da matansa da yaransa kowa da part dinsa,wlh Zan rikeku da Amana,ko me kuke so Zan muku.
Khadija tace to a wanne state kake? Kaduna state,Hmm to Allah ya taimaka na yarda sai ka tambayi Mama idan ta yarda,Ai murna wurin Alhaji Karami ba a cewa komai,da yamma wajen Mama ya koma,Bai Sha wahala ba ta Amince sabo da dama tana son auren Kuma gashi ta samu mutumin kirki asirinsu zai rufu gashi uwa uba Khadija ta yarda,Su Merry ma sun Amince Dan sunji me kudi ne zasu koma birni

Mama ta kalli Alhaji tace baka bani labarinka? Alhaji ya fara da mu Asalin Yan Adamawa ne,Fulanin Adamawa daga Ni sai Yayana Yousuf Balarabe Iyayen mu suka Haifa,tun Muna Yara Allah yayiwa iyayenmu Rasuwa sai dangi,munyi karatun Addini da na zamani,Yayana Shi Allah ya azurta,ya fara da kana Nan sana'a Munsha wahalar rayuwa har Allah ya budawa Yousuf ya auri Matarsa ta farko Rahmatu da yaranta Usman,Sarah,Ikhram,Nura,Omar,Zahra,Na'im da Naima Auta, sai Matarsa ta biyu Hajiya Zainabu yaranta biyu Aliyu da Nana Khadija,Matarsa ta uku Binta yaranta Sagir da Saleem sai ta Hudu Hajiya Aisha Kwara ce Wanda suke kamar Larabawa Haka suke tana da yaranta Abdallah 30yrs,Afrah 19yrs sai Islam auta 14yrs,sai Kuma Matan daya aura ya saki su Hudu ne Kuma duk suna da Yara wata biyu wata uku suna Nan a hannunsa sun girma,daga samari sai yan Mata a gidan,gidane Family House Amma ba takura kowa part dinsa daban,ko Ni part Dina daban ne da yarana kema Kuma part dinki za a Baki daban ke da yaranki,Sai dai kuyi hakuri gidan da zaku sai kun shirya domin Babu Wanda ke shiri da dan uwansa,kullum cikin tsegumi da Jan fada ake,Yayana Yousuf me kudin gaske ne,mun gaji sarauta a Adamawa,sannan Dan kasuwa ne,Dan siyasa ya rike mukamai da dama.

Shi yake min komai nawa da Sauran dangi,Mutumin kirki ne matsalarsa kawai aure aure domin ya auri Mata sama da goma Sha uku,Yaransa Kuma kaf Babu me Hankalin Abdallah sai dai gaskiya sai kunyi taka Tsantsan domin shi kanshi Abdallah watarana sai a hankali Bai son magana da hayaniya,ga Kunci,baya Dariya,ga iyayi sannan Bai son raini,Yana da gadara tare da shegen Iyayi,Uwarsu itace tafi kowa iya shege a gidan Nan,Bata son talaka,Haka sauran Matan da yaran ma,bazan boye muku ba har matata itama gaba suke a gidan da faccalolinta,faccalanci suke sosai,dukkansu Matan da yaran basa kauna wani ya fisu,gasu da masifa,Bai sai na fada muku komai ba kuyi a hankali kawai ku iya Zama dasu,Abdallah dai ba ruwansa duk baya shiga wannan harkar mutumin kirki ne,Haka mazan ma su basa fada Basu damu ba,Matan ne kawai ke haddasa fitina basa son zaman Lfy.

Mama ta nisa tace ba komai muma ai mun iya fadan sai muje da Shirin mu,ke Khadija ki dauki cuttlas din Nan guda biyu mu tafi dasu ko zata baci ayi sare sare, Alhaji ya bude Baki Yana Basu hakuri.
Bayan sati daya Alhaji Karami Dan uwansa kawai da Matarsa ya sanarwa zaiyi aure,Hafsatu ta haukace gaba daya yayin da Matan Daddy Yousuf su Mami suke ta murna dama Hafsatu ta ishesu ita tafi karfin kishiya,Nan fa maza da Mata aka dinga murna sabo da Hafsatu faccalarsu Bata da mutunci ko kadan,Mamin Abdallah Masu kida ta dauka,tuni gida suka Fara shirye shirye Banda Hafsatu da yaranta dake kuka kullum.

Hafsatu yanzu gaba takeyi sosai da mijinta Alhaji Karami,Amma yace wlh ko mutuwa zata Yi Babu fashi dama ta addabeshi Bata da kyan Hali ko kadan.

Sati biyu tsakani Ya Gama komai na biki,Mama lefe na gani na fada ya hada Mata akwati guda Tara shake da Kaya iri iri,sai makudan kudade na shagalin biki,Haka su Khadija Akwati guda biyu biyu ya musu na kayan da zasu sa idan sun koma gidansa,Murna sukeyi sosai,tuni har ya Gama nema musu schl masu kyau a Kaduna.
Ranar Daurin Aure Dangin Adam ne suka yiwa Mama walicci,Alhaji Karami Kuma da danginsa da Kuma yayansa Yousuf tare da yaransu maza suka zo Daurin aure,dake na manya ne Babu wasu mutane da yawa aka daura Auren Mama da Alhaji Karami a Kan sadaki dubu Dari cash.

Khadija dasu Merry kawai bakin ciki sukeji kamar su kashe kansu,sabo da Haka ko kwalliya basuyi ba,kayan su na gwanjo suka Sa,Madam Ngozi tare da wasu Mata su biyu kawayen Mama Suka shirya dasu za a Kai Amarya,Driver tare da Daddy sukayi motoci biyu Dasu za a Kai Amarya,Kayansu kawai suka Sa a mota Khadija harda kuka zasu rabu da Abu Kawarta.

Mama taci wanka cikin wani lace me tsada na lefe ba karamin kyau tayi ba,Khadija kuwa da Kyar Mama ta lallashesu suka yi wanka Amma Fafur suka ki San kayan Alhaji Karami suka shirya cikin wasu tsangalalllun rigunan gwanjo dogaye da kadan suka haura gwiwa, ba ko yafa gyale Suka daura siririn gyale a kansu sabo da farare ne masu kyau sai sukayi kyau a hakan.
Madam Ngozi kuwa taci uban gogoro tasa rigar farin lace da Zanin atamfa ta daura tare da tsangaleshi Haka suka shiga motocin daukan Amarya suka bar kauyen Baki daya zuwa KD.


Mami Ina so next Month zanje Usa,Baka Isa ba Abdallah wlh kaji na rantse ka Gama Masters ba inda zaka tafi Daddy ya Gama shiryama aikinka sannan ga kasuwancinka kanayi,Office dinka ya Gama maka komai sabo da Haka aiki kawai zaka Fara Nan gaba ayi aurenka,Yasan tunda ta rantse ba Kuma canji kawai sai yayi Mata shuru ya mike tare da tafiya part din Daddy.

4:30pm kida kawai ke tashi a gidan na Dj sai rawa ake cashewa Ana ci Ana Sha suna farin ciki anyiwa Hafsatu kishiya karya ta Kare,Tunda motocin Amarya suka tsaya kowa ya gyara Ido zaiga Amarya ga kida na zamani ya cika ko Ina,Lokacin Khadija sun Gama rudewa da ganin gida Haka hadadde Wanda Basu taba ganin irinsa ba ko a mafarki,Mama Da Madam Ngozi suna gaba sauran suna baya Khadija da Merry tare da Ahmad mamaki sukeyi,suna kalle kalle Dai dai lokacin Abdallah ya fito zaije part din Daddynsu, Baki bude ake kallon su Mama domin zaton kowa arna ne basa Sallah musamman Ngozi Tare dasu Khadija.
Khadija tuni farin ciki ya cikata a Nan gidan zasu zauna,sai ta daina bacin Rai sai Murna,Jin kida yasa jikinta ya fara rawa Bata San data duka kasa ba tare da rike gefen rigarta ta Fara rawa tana jijjiga Hips Haka Merry ma, Itama Madam Ngozi ta Fara rawa suna tafiya da rawa,Bakin kowa yaki rufuwa,Abdallah daya gansu Saida ya tsaya Kallon ikon Allah don Bai Zaci ita ce Amaryar Kanin Babansu bace,dama ance da yaranta zasu tare,Rashin kunya ta gaske ya gani musamman Khadija da tafi kowa ga tsangalalliya r shiga,itama Mama baza kace Amarya bace,sai Dan Karan kyau kowa sai da ya yaba.

Alhaji Karami gidan ya shigo ya Iske Khadija da Yan uwanta suna cashewa,Farin ciki ya kamashi sun saki ransu,Khadija tana ganinsa ko kunyar ba Bata ji ba,Abdallah Yana gefe Baki a bude Yana Kallon ikon Allah,Khadija da sauri ta bi bayan Alhaji Karami ta wuce da gudu Suka jera tare dashi suna Hira,tace Alaji wannan gidan Yana da chau Amma ku akwai kudi ne gaskiya,Gashi kowa ya waye a gidan Yan gayu ne,Sam Khadija Bata kula da Abdallah ba Wanda ke Jan tsaki an kwaso musu arna.

Part din Hafsatu uwar gida Wanda yake cike da danginta aka wuce da Mama da yaranta,Hafsatu ganin kyawu irin na Mama gabanta ya Fadi,Bata Zaci Haka ba musamman da akace Mata tubabbu ne,kishi da bakin ciki ya taso mata,ta mike tsaye gayyar tsiya ki tafi part dinku shegu Tubabbun Arna,Nan kawaye da Dangi suka kwashe da dariya,Mama Cikin Hausarta da Bata fita tace wallayi mu dai ba Tanbabbu ne ba,Dariya suka kwashe da ita gaba daya,uban Mene to cewar Hafsatu,ganin Haka yasa Yar Uwar su Daddy taja su Mama zuwa hadadden part dinsu sama da kasa ne,Mama tana sama yaranta a kasa,yasha kayan Alatu Babu abinda Babu a ciki.

Abinci iri iri aka kawo musu,Khadija kuwa tana Wurin Alhaji Karami ta makale Masa,Tare suka Isa part din Daddy Baban su Abdallah Wanda shima Abdallah Yana can,Da Sallama suka shiga,Abdallah ta gani cikin rantsatsun kana Nan Kaya yasha uban kyau tunda take Bata taba ganin me kyansa ba,ga kwarjini da haiba,Fuskar Nan murtuk ba Rahma,Har kasa Khadija ta duka tare da gaisar da Daddy,ya Amsa da sakin fuska tare da cewa Ashe kun iso?

Cikin Hausarta wacce da kyar takeyinta tace Yes Dad Munzo Kai najiya Dadi wallayi wannan gida me Chau ne, da Ina ta fushi Amma Ina zuwa na daina fushi Kai... Alhmdllh Daddy Munsha rawa yau yaran gidan Nan Yan gayu ne,Hausarta ce ta bawa Daddy dariya yace to Haka ake so ga yayanki Abdallah sunansa,Khadija ta kalleshi ko kallonta baiyi ba,tace Samari sannu fa wooo gaskiya kana da Chau,Daddy wannan yafi kowa Chau sose,Ina kwananmu? Abdallah a ransa sai zagin Khadija yake kawai ta cika Masa kunne da hayaniya,Sabo da Alhaji Karami ya Dan saki fuska yace lfy,Baki Khadija ta tabe tace wannan ba fara'a fa Daddy kullum yaronka Yana fushi aka, Kai ka Zama kana smile Yana da chau, Mikewa tayi Abdallah yabi kafafunta da kallo ya dauke Kai.

Bayan sun fito Khadija part dinsu aka rakata ta tana cin Abinci ta jawo hannun Merry suka fito inda masu Dj ke cashewa Matan gida Ana ta shagali,Khadija ta kutsa ciki Ana kallonta wuri ya cika maza da Matan gidan Ana kallon ikon Allah,Lokacin Mami taje ta jawo Abdallah Wai Dole sai yayi liki yanda Hafsatu zata Fi Jin haushi,ala Dole ya biyota Yana kunci,Khadija ta karbi speaker ta Fara magana.

Assalamualaikum wooo.. Alhmdllh muna godewa Allah fa daya kawo mu wannan gida me Albarka, I'm so so Happy ganin Mamana a gida iri wannan,we Hope zaku karbe mu, Yan Matan suka Fara tabe Baki suna kus kus Usman da yake saurayi Dan 34yrs yace yess oooo.

Khadija ta washe Dan bakinta tace thank you Bro,so Yanzu Dole mu nuna farin ciki da muka zo wannan Family,Haj Ramatu matar Daddy ta farko tace Aiko Dole watarana ku bar Mana gida,Khadija tace baza mu fita ba wooo Muna nan.
Merry Ce ta karbe speaker tace we must Dance today Coz we are in Good Mood, Dj play the music abeg.

Dj ya saki Sautin wakokin Nja zo kuga Khadija da Merry ka rantse gidan gasar rawa suke,sai da suka birge uban kowa da rawarsu,fili aka Basu gaba daya Ana Shan kallo ba a San sanda aka rufesu da liki ba,rawa suke me a zabar kyau a nutse,sai da suka kayatar da kowa,Ko uban Iyayi Abdallah kasa daina Kalla yayi ya zuba musu Ido,Khadija ta jawo Usman Ciki,ta Figo hannun Sagir da Omar tare da wasu Yan Matan tace Dole suyi Suma,suka danyi kadan Ana ta dariya da liki,Abdallah dai ya kasa motsi,Khadija tazo wajensa tace Dan gidan Daddy kayi liki Mana oya spray the Money for me,Ko kulata baiyi ba,Khadija ta faki idonsa ta fisge kudin ta koma filin ta Fara liki tana Wasa da kudin Yan dari dubu dubu, Abdallah Kuma ya juya ya koma ciki part dinsa.










AsmaBaffa
[12/31/2019, 3:00 PM] AsmaBaffa: 🏵TUBABBIYA🏵







3








Official







By
AsmaBaffa






ZAINAB GARBA BUTALAWA page dinkine jinjina gareki da tarin Godiya wajen Kokarin yin Document na dukkan Novels Dina.

Fans ku tafawa Zainab Garba Butalawa domin itace ke muku Document na dukkan novels Dina,sabo da Haka masu Sharhi ku kwashe Mata da tafi.😄


Sai wurin 9pm sannan suka Gama shagalin taronsu, Hafsatu matar Alhaji Karami Haushi Wai itama an Mata kishiya karyarta ta Kare,Khadija kuma wurin Mama suka koma,Khadija ta zabi lafiyayyen bedroom dinta,Haka Merry ma da Ihsan dakinsu daya da Ahmad kowanne dakinsu daban lafiyayyen gaske yasha kayan more rayuwa,Madam Ngozi da sauran Dangin Su Khadija da suka rako Amarya Nan suka kwana washe gari Dangin su Daddy suka sauki baki da Kyakyawan Kari na Alfarma, yayin da Hafsatu ke cika tana batsewa tare da habaici akan Dangin Su Daddy Dangin Miji kenan Wanda dama Suma murna sukeyi da aka yiwa Hafsatu kishiya sabo da Bata da mutunci ko kadan.
Misalin 9am Su Madam Ngozi suka yi shiri Driver ya maida su Zamfara kauyensu.Daga Mama Sai yaranta hudu su suka rage.

Duk yawan Yan aikin gidan Nan Hafsatu ta Hana ko wanne shiga part din su Mama bare suyi musu gyara da girki etc,Ganin Haka yasa Khadija da Merry tare da Ahmad har Ihsan suka zage suka gyara part dinsu sabo da dama tsaftar masifa ce dasu har tayi yawa ma,ga iya girki,kamshin dake fita a part dinsu na daban ne,Haka girkin da Khadija keyi a kitchen ya turare gaba daya estate din da kamshin Dadi,sai gulma akeyi ai yare Dama sun iya girki, Upstairs Khadija ta hau tana shanya Kayansu data wanke a Washing machine daga ita sai 3qutr da Yar bingilar Riga,surarta me matukar kyau ta bayyana,wakokinta takeyi na yaren Igbo, dai dai lokacin Abdallah ya fito shima ta samansa corido Yana Shan juice tare da shakar fresh air, kasancewar Girman Kudu ne Su Khadija basa magana a hankali Waka take rerawa da karfin Wanda Ya bawa Abdallah damar Jin wakar ta,juyowa tayi suka hada Ido,da sauri ta washe bakinta tare da kwallawa da karfi tace Hi.....Harara ya watsa mata,jikinta ne yayi sanyi sai ta share Amma ta kasa hakura ta sake kallonsa tace Ina kwananka? Yatsunsa ya wara tare da antayo Mata Dakuwa Ambola ya wani turo lips dinsa masu kyau da sheki,Khadija ta nuna kanta Wai da ita yake,Yaja tsaki Yana harararta tare da komawa bedroom dinsa,tana Gama

Please Login or Register in order to submit comment