Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke zuciyar ta shi ne a zuciyar shi,

"To dubiya kacce ka taho, amma ba ka yi min ya jiki ba"

"Ban ga alamar ciwo a tattare da ke ba, sai ma alamun cikakkiyar lahiya, amma, ya jikin ki? Ina hwatan da sauqi ko?"

"Na ji dama, ciwon da ke jiki na ba a zahiri yake ba, a badini ne, domin kuwa zuciya ta na quna matuqa akan abinda zai iya koma ya faru da mutanen can, da kuma abinda ka hwaruwa a garin nan, da ma Nigeria baki daya"

"Hummmm"

Shi ne kawai abinda Lawwali ya iya cewa, nan da nan ya tuna addu'ar da ta musu, cikin sauri kar a zurfafa magana ta sake yanko wata addu'ar ta cimmusu baki daya ya ce,

"Ran ki shi dade, ina fatan ban yi karambani ba, na je zan siyo ma mara lahiya kayan dibiya, na rasa mi zan kawowa, na kwaso wadannan"

"Na gode sosai, amma da baka wahal da kan ka ba"

"Babu komi, indai ke ji dad'in kyauta ta, farin ciki na zai qaru"

"Lallai ka yi farin ciki domin kuwa na ji dadin kyautar ka"

Yar dariya suka yi a tare, Lawwali ya shagala da kallon ta suka ji an rangada salati, da sauri sultana ta miqe ta na zare ido, cikin in ina ta hau yi wa Hajiya Ikee Barka da zuwa, wani mugun kallo take bin Lawwali da shi, daga sama har qasa, babban abinda zai ba mai karatu mamaki shi ne, Lawwali dai ba a talauce ya je ba, kayan jikin shi kawai sun tasamma dubu dari,ga tsarabar daya kawo ma Sultana ya kashe 50k, wayar hannun shi abar kallo ce, ga motar shi can a waje, ko wani dan attajirin sai haka, amma Hajiya Ikee ke masa maqasqancin kallo,

"Ran ki shi dade Barka da War haka,"

Cikin tsawa ta ce

"Dakata min diyan tallaka! Me ya kawo ka har parlourn manyan baqi? Ke Sultana wacce wanga diyan tallakan ya shigo min har nan?"

Cikin kame kame da tura baki Sultana ta ce,

"Hajiya ke san hwa mai tsaron lahiya ta shike, Daddy ne yacce duk inda ni aje qawahu na shi sa na shi, tau yau na ce masa ban zuwa ko ina ban da lahiya, shi ne yazo diba ni, in baki yarda ba ki tambayi daddy shi ne yacce duk inda niyyi shi ma shi yi"

"Akan wanne dalili za a hada ki da wanga gola golan qato? Tau ban yarda ba, ke da gani nai ke san shi na shan wani abu, kuma...."

Cikin jin kunyar kalaman Hajiya Ikee Sultana ta katse ta, dan cin fuska ba shi da dad'i ,tsabar kunyar Lawwali Sultana ta kasa kallon shi.

Lawwali kuwa kawai ayyana irin azabar da zai ganawa Hajiya Ikee yake a duk ranar da tsautsayi ya had'a su, a fuskar shi kuwa murmushi ne bayyane, wanda ba me gane ma'anar shi in ba yaran shi ba, da ace a daji ne yake wannan murmushin to fa tabbas sai ya kai harbi, kad'a kai ya yi, ya ajiye ma Sultana tsarabar ta a gaban ta da kyau da kyau,ya kalle ta ya ga yanda take jin kunyar hada ido da shi, qoqari ya yi suka kalli juna, kashe mata ido daya ya yi, ta kuwa sanya murmushi, tare da rufe fuska, Hajiya Ikee salati ta saki, ta na tafa hannaye, Lawwali kuwa wucewa ya yi tare da fadin,

"Na bar ku Lahiya, Ran ki shi dade "

Ya na fita Hajiya Ikee ta ja Sultana, ta na masifa, tare da fadin, dole a sauya mata driver, bari Daddyn ta ya dawo, kuka kawai Sultana take, ta na bada hakuri, amma haka Hajiya Ikee ta murje idon ta, ta ce sai an sauya mata Lawwali.

************************

Da asuba Mai unguwa ya fita Masallaci, an yi sallah, aka hadu da mutanen unguwa aka sauke qur'ani, aka roqi Allah, akan Allah ya kawo qarshen wannan tashin hankulan da ake ta yi, sannan aka roqi Allah akan ya bayyana Isyaka, Mai Unguwa fadi yake, ya na kumawa,

"Ya Allah ko gawar shi ne Allah ka gwadi mana, mu san ya mutu ne, ya Allah ka bayyana muna da shi lahiya"

Bayan kammala addu'a kowa na tafiya gida ne, wasu da basu samu zuwa har gida jajanta masa ba, suka jajanta masa a nan.

Sai da gari ya dan fara wayewa ya yi sallama da mutane ya dau hanyar gida, a hanya ya gamu da wani daga cikin yaran shi ya na ta gudu, ya na haki, tare da murna, ya na hango baban nasu yaci burki a gaban shi, ya ce,

"Baba ! Baba !! an ga Isyaka, ga shi can gida, kwance jikin Baabaa"

"Alhamdu lilLAAH, Hamdan katheeran, Allah na gode maka,"

'Dan dandamalin wani gida ya hau a gefen hanyar, ya yi sujjadar godiya ga Allah, sannan suka kama hanya, suka nufi gida.

Ko da suka je, ga Isyaka nan, ya yi fururu, kayan shi duqun duqun, jikin shi alamar ya ci duka ya gaji.

Ya na ganin Mahaifin nasu kawai sai ya fashe da kuka, a da kuwa ko kukan ma ya kasa.

Mai Unguwa ma kukan ya fara yi, ya na sake godewa Allah tare da fadin,

"Ba abinda ya fi qarfin Allah, duk abinda Allah ya yi daidai ne, Allah mun gode maka, Allah ka qarawa Annabi daraja da wasila da fadhila, Allah mun gode maka, d'an baba, ya aka yi?"

Ya na cikin kukan ya saki murmushi, hawaye na zuba.

Kishiyar Baabaar Isyaka ce ta zo, ta ce,

"Tau ga ruwan wanka can na sauke taso ki je ki wanke shi ya ji dad'in jiki shi"

Godiya Baabaar Isyaka ta mata, ta kinkime shi ko nauyin shi bata ji,su ka nufi bayi, riga ta fara cire masa, ta fara qoqarin cire masa wando, ihu ya sanya, ya na fizge fizge, kamar mai jinnu, tare da fadin

"Ba na sooo, kar ka taba ni, ba na sooo wayyooo Allah na da zahi, zahi nika ji wallah, wayyoooo a taimaka min...."

Kuka sosai Baabaar shi ke yi, ta fita da gudu, zata kira taimako, ta tadda Mai unguwa da kishiyar ta da wasu daga yaran gidan a bakin qofar bayin, da kyar a ka samu ta nutsu, ta yi bayani, dakko shi akai waje, aka cire wandon, juya bayan shi Mai unguwa ya yi, wani wari ya ji ya na fita daga bayan yaron nashi, su na daga shi aka duba sosai, an fafake ma yaro baya, jini da wani ruwa mai danqo danqo ke zuba, ga wari, ihu da kururwar mata da yaran gidan ne ya cika ko ina na gidan, Mai unguwa kuwa suman tsaye ya yi, hawaye na bin kuncin shi, zuciyar shi ta yi mugun qunci, ta yi baqiqqirin,

"Wa ya yi maka wannan mummunan al'amari Isyaka? Wa ye ya bata maka rayuwa Isyaka? Wa ye ya zalunce mu? Ya aikata abinda Allah da Manzon shi ya yi hani da shi, ya tsine wa masu yi, da wanda aka musu, Allah ya na fushi da masu wannan mummunar dabi'ar da ko dabbobi ba sa aikata wannan alfashar,wa ye ya ci amanar mu? Waye shi ? Waye ya ci amanar mu?"

Babban dan Mai unguwa ne ya kama Isyaka daga hannun mahaifin nasu, ya aje saman tabarma, sannan ya ja hannun baban nasu suka koma gefe, ya zaunar da shi saman kujerar shi ta tsakar gida, ya na jin ya zauna, ya dafe goshin shi, ya fashe da wani irin kuka, mai ciwo.

Gaba daya gidan ya rikice, da sassafiyar har maqota sun ji koke koken sun shigo, kafin ka ce kwabo, labari ya baza unguwa.

Wasu da ke a social media kuwa har sun fara yadawa, tare da ɗaukan hoton Isyaka ba da izinin iyayen shi ba, ba da sanin shi ba.

Gani suka yi kukan ba zai kai su ba, uwar gidan Mai unguwa ce ta dauke shi, ta na kuka ya na kuka, ta wanke shi tass, ya suma ya kai sau uku kan a gama, saboda ciwon da ke jikin shi.

Ranar ahalin Mai unguwa ba mai maganar karyawar safe ma balle na rana, kowa hankalin shi a tashe yake, bayan sun gama shirya yaron, Liman ya yi sallama da Mai Unguwa.

Ko da ya je, suka gaisa ya jajanta abinda matan shi suka je suka bashi labari, sai ya bada shawara akai yaro asibiti, sannan a kai ma yan sanda rahoto.

Haka kuwa akayi ,a police station an yi ma Isyaka tambayar duniya bai san su waye suka dauke shi ba, bai ma san sanda aka dauke shi ba,sannan aka maida shi, (sharrin asiri,wasu masu aikata hakan su na sihiri,domin in b asihiri ba ba yanda za a yi wasu abubuwan su faru, se kuma son zuciya da rashin tsoron Allah, Allah ya ma na tsari da mugun ji mugun gani, mugun aiki)

Ba yanda suka iya, daga qarshe dai aka ce za a yi bincike, wanda zai wahala ayi din,cases irin wannan sun fi dari a wajen yan sandan,ba kan shi farau ba,an dad'e ana yi ba a bi ma mutane haqqin su, domin wasu masu bin haqqin ma suke kwace haqqin, asibitin aka wuce da shi, nan ma sai da aka sha fama kafin a samu bashi gado.

**********************

Lawwali na fita daga gidan su Sultana unguwar iyayen shi ya nufa, domin yanda ran shi ke tafasa da kalaman Hajiya Ikee, in bai dora sanyin idaniyar shi a idon shi ba ba zai ji salama ba, bai san me zai iya aikatawa ba.

Ko da ya isa gida kuwa, ya yi sallama Mai buruji da Kameelu ne suka amsa shi, Kameelu ya tafi da sauri ya na ma yayan nasu sannu da zuwa, ya ga ba walwala a tattare dashi, nan take ya ce,

"Yah Lawwali Mubaraka kuwa bata nan, tun da ta tafi makarantar boko bata dawo ba, wataqila ta wuce islamiyya daga can"

Idanun shi ne suka kada suka yi jawur, cikin d'aga murya yace,

"Miii ! Mi ka ce? Ina ta tai? Yanzu hwa mangariba ake kira, ina ta tsaya?"

Lamishi ce ta fito daga dakin ta, ta tsartar da yawu, ta na saka takalmi ta na daura zani ta ce,

"Ina ko ta tafi banda gantali, na ce kar ta tai makarantar wahalar ga amma sai da tassa qafa ta hita, in ma sace ta ank....."

Wani duka Lawwali ya kai wa randar da ke tsakiyar gidan, sai da ta tarwatse, ruwan cikin ta ya baje a wajen, ba Mai Buruji ba da ta riga ta fara tsorata da yanayin da ya shigo da shi ba, hatta ita 'yar taurin wato Lamishi sai da ta shiga taitayin ta, kameelu kuwa a guje ya bar gidan, cikin hargowa ya kalli Lamishi yace,

"Ina raga maki ne saboda Baraka na, duk wani abu ya same ta, sai na yi ajalin ki"

Yanayin yanda ya yi maganar ya kad'awa Lamishi hanji, a rayuwar ta kafff yau ce rana ta farko da ta ji tsoron d'an nata, ashe kyale ta yake saboda Mubaraka na hana shi, Dan Talo da ya so shiga gidan dan ganin motar Lawwali ne, ya ji ana tashin hankalin nan, ya koma cikin sanda ba tare da kowa ya ga shigar shi ba, balle fitar shi.

Dakin shi ya shige ya dinga wurgi da duk wani abu da hannun shi ya kai wajen, tunawa ya yi da ya sai mata waya, kiran wayar ya fara, amma ta na ringing ba a daga ba, wata qara ya saki, sannan ya daki qofar dakin da qafar shi, sai da ta balle tai qasa.

Mai Buruji ta gama shiga tashin hankali ,mayafin ta a hannu ta fice a gidan cikin sanda, ta afka gidan Yabbuga.

Lawwali ne ya sake kiran No Mubaraka aka ce, a kashe take, ihu ya saka, tare da zabura ya fita ya bar dakin , a guje ya ja motar shi ya bar gidan...........

*Mubaraka Allah ya sa ba gidan qawaye ki ka fara bi ba, tunda an fara sa manyan kaya, Lols*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 25:

Ko da ta farfaɗo,kwance ta gan ta a wani gado madaidaici, wanda da alama sabo ne dan katifar shi ma ko leda ba a cire ba, haka aka saka ta, mirror da komai na dakin sabo ne, hatta da fentin dakin, sabo ne, kamar irin dakin sabuwar amaryar nan.

Gefen ta ta kalla, a yayin da ta ji kafar ta ta yi nauyi, Murjanatu ce a hannun ta na hagu, ta danne mata qafa da jikin ta, dayan hannun ta na dama kuwa Saliha ce.

Tunanin baya ta fara yi.

Ta kammala duk wani aikin ta na ranar, ta shirya dan tafiya makarantar boko, Lamishi ta hana ta, ta ce ba inda zata ta zauna ta jire gida, ta yi magiya, ta yi roqo amma inaaa, fafur Lamishi ta ce ta zauna ta jire gida, in ba yawon tazubar zata ba, karatu dai an jima ba aje ba mi za ta gane yanzu?

Bayan sun tafi, Mubaraka na zaune gidan shiru, kawai sai dabara ta fado mata, ta kuwa sake shirin makaranta, ta dura hijab da niqab din islamiyya, ta dauki kudi cikin wanda Yah Auwal din ta ya bata, shago ta je, ta sai kwado, aka bata mai kyau, me kwari.

Ta na zuwa ta samu ko ina ta rufe, ta sa kwado ta garqame qidan, ta kai wa Yabbuga ajiyar key, ta ce ta yi makaranta .

Da azahar an tashi boko, ta tsaya a makarantar har lokacin islamiyya ya yi, dan ta san bata isa zuwa gidan gwamna ba, Lamishi na can, Auwal na can za su yi rikici a gaban mutane.

Saliha da Murjanatu yaran mutum guda ne, jinin su ya hadu da Mubaraka, kasancewar ta mai qoqari, su kuma su na son mutum me qoqari da kamun kai, (Sai hali ya zo daya ake abota), dan haka suke qawance, boko da islamiyya, su na zaune da iyayen su anan unguwar Tudun Faila.

Sun roqi Mubraka da su tafi gidan su, in za su islamiyya sai su tafi tare .

Haka kuwa aka yi, da misalin qarfe uku, na rana, sun ci abinci sun yi wanka, sun shirya cikin kayan makarantar su, sun sanya niqabin su.

Tafe suke su na hira, suka ji an taka wani wawan birki, a gaban su, kafin su gama tunanin me ya faru, an dauke su cak kamar wasu leda an watsa a mota Bus, ihun su ya qare ne a lokacin da No 4 ya zira hannun shi cikin niqabin su ya shaqa masu wani abu, suka hau bacci.

Tun daga nan suke bacci ba su san a inda suke ba, sai a wannan lokacin da ta farka .

Tashin su Saliha ta yi, ta na qoqarin yin kuka, su na farkawa suka hau ihu, No 4 ne ya bude qofar ya shiga hannun shi dauke da wata qatuwar bindiga ya na muzurai, tare da fadin.

"Ko ku mana shiru ko na tarwatsa kan yarinya,"

Kamar an yi ruwa an dauke, haka suka yi shiru, sun qanqame junan su, su na rawar jiki, No 1 ne ya shiga, fuskar shi a rufe, idanun shi ne kawai a waje, hatta da hannun shi da qafa duk a rufe suke, cikin kakkausar murya ya ce,

"Ke ! Zo nan"

Cikin rashin fahimta Saliha ta miqe ta je, wani mummunan duka ya kai mata sai da ta juya, ta kidime,

"Da ke nake? Ke kuma inna sake kiran ki ba ki zo ba, za ki ga yanda zan lahantar da ke,"

Cikin rawar jiki, Mubaraka ta miqe,dan kuwa ya nuna ta da yatsa, ta san da ita yake tabbas, amma gudun kar ya dake ta ta tsaya daga nesa.

"Ba zaki zo ba kenan?"

Da sauri ta isa gaban shi, ko ina na jikin ta rawa yake, tsabar tsoro,hijabin ta ya cire ya yi wurgi da shi,sannan ya tuge dankwalin ta, gashin ta irin na hausawa mai cika ya kalla, cikar shi da tashon shi sun burge shi,hannu ya kai zai taba, ta yi baya da sauri tare da fadin,

"A'uzu billahi,meye haka ka ke yi, ko baka san haram bane ka taba ni"

Wata iriyar dariya ya kwashe da ita, sannan ya nuna ta da hannun shi manuni, ya ce,

"Ke, ke ce ke fad'in an tabi haramun? Qaunar Lawwali ka batun haramun?"

Hannun shi ya sa gaba daya ya fizgeta ta fada jikin shi da qarfi, qara ta saka, ya kuwa wanke ta da mari se da bakin ta ya fashe, jini ya dinga diga, kuka ta fashe da shi ta na kiran sunan Allah, akan ya kawo masu agaji, Lawwali ne ya fado mata a rai, nan da nan ta kalli bawan Allahn da ya mare ta, kallo ta bishi da shi daga sama har qasa, tabbas shi ne, abokin Yah Auwal, wanda ta ji ya na kira da No 1, cikin rawar murya, ta furta,

"No 1?"

Da sauri No 4 ya fita daga dakin hankalin shi a tashe, zufa na tsattsafowa daga kowacce kafa ta jikin shi,cikin tashin hankali ya kira wayar No 1, shi kuwa ya na ciki ya na ganawa Mubaraka azaba, bai so ta gane shi ba, ya na ganin kiran No 4 ya sake ta ta fad'a cikin su Murjanatu,nan da nan kuwa suka rungume ta, su na lallashi.

Ya na fita No 4 ya ce,

"Dama ka san da qaunar Oga a cikin su? Garin ya ankai muka dakko da qaunar Oga? Ba cewa ka yi wata qaunar abokin ka za mu dauka ba? walle ba ruwa na in oga Lawwali ya gano kai ka ɗauke ta, kar ka kira suna na, ina da iyali, ina da mahaifiya da tai yi min saura, ban shirya mutuwa ba ni da dangi na"

Wata tsawa No 1 ya sake ma No 4,

"Wai kai me ye haka? Kana wani tsoron shi kamar ba namiji ba? Yanda ya ke jin shi shege ne mu ma muna jin kan mu, kuma ka na ganin da mun tsaya diba wadda nika batu ka na ganin ba za a kama mu ba? Dallah be a man, yanzu ka tai zuwa samo musu abinci mu kulle gida mu koma daji, kahin a kula bamu nan"

No 4 dai bai gama daukan wannan maganganun ba, a mugun tsorace yake, gani yake kamar zai ga Lawwali a gaban shi, cikin rawar jiki ya tafi ya samo masu binci, da ruwa, da duk wani abu da ya kamata su yi amfani da shi, dayan dakin dake can lungun gidan suka maida su, dakin na dauke da bayi, da babban gado, su na wurga su suka rufe gidan, sannan suka tsorata su da fadin akwai masu gadi, in suka ji kwakkwaran motsin su, sun bada umarnin a shiga a harbe su.

Ko da suka fita daga gidan, ina dubawa sai na ga wajen sabuwar unguwa ce,ba gidaje sosai, Bus suka shige suka dauki hanyar da zata sada su da maboyar su.

***********************

Lawwali ya firgice ya haukace wajen neman Mubaraka, tsakanin makarantar su ta boko da islamiyya da unguwar su ya yi zuwa ba iyaka, daga baya gida gidan yan makarantar su ya dinga bi ya na tambayar sanda suka gan ta na qarshe, jikin Lamishi kan ta sai da ya fara sanyi, Dan Talo kuwa ya na can yawon bin abokai, bai san me ke faruwa ba, sai wajejen sha daya da ya dawo ya ji Muryar Lawwali cikin maye ya na ta ashar tare da alwashin in ba a gan ta ba a gobe sai ya yi ajalin Lamishi, mugun bakin ta ne da tsanar da take wa Mubaraka ya ja ta bar gida.

Lamishi fa yanzu tsoron d'an nata ya gama shiga kowacce kafa ta jikin ta, basu taba ganin shi cikin matsanancin hali irin wannan ba, ya farfasa musu abubuwan amfani, ya jiwa kan shi rauni kala kala, ga shi ya kasa kokawa, banda huci ba abinda ya ke fitar wa kamar wani damisa.

Dan Talo qin shiga gidan ya yi, ya labe a waje, (uban banza kenan) jira yake ya samu Lawwali ya shiga dakin shi ya afka gidan, in ya so a nutse ya tambaya ya ji ina Mubarakar ta tafi.

Da misalin sha daya da rabi na dare Lawwali ya gama yanke shawara, makullin motar shi ya dauka,ya ja qofar shi zai fice, Dan Talo na maqale ya ji motsi, kwanar gidan ya sha a guje, Mai Buruji da Yabbuga na tafe su na tattauna tashin hankalin yau da Lawwali ke ta yi a unguwar, Yabbuga na fadin, da an sha kwana za ta koma, bata fatan had'uwa da shi ya na lafiya ma balle yanzu da yake a fusace.

A guje suka ga Dan Talo, su ma diba suka yi a guje Yabbuga ta yarda yar kwabirar wayar ta rakani kashi, sai ihu take ta na kiran Dan Jumma tare da zagin shi ta na fadin ya na sane ya qi raka su.

Dan Talo ya riga su fad'awa gidan su Yabbuga, dafe da qirji suka same shi ya na maida numfashi, Dan Jumma ne ya fito a tsorace ya na tambayar waye.

"Mi na na kun ka shigon gida haka a guje kamar wad'anda aka biyo? Yaqi akai halan?"

"Yaqi ake amma a gida na, wannan shegiyar yarinyar ce ta tafi yawo, bata dawo ba, ta ja muna bala'i, hatta da gambun gidan nan bai tsira ba, sai da Yaron nan ya ɗebe shi yau, komi ya hwashe ya lalata, na jiyo ya na fadawa Lamishi gobe in ba a ga Mubaraka ba sai ya yi jalin ta, ban ko wallah shiga shi gama da ni"

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, anya Dan Talo kun yi addu'a kuwa? Yaro awa diyan shedannu? Bashi jin maganar kowa sai dai a ji tashi?"

"Ke Yabbuga shige ciki, kai kuma, dan Allah ka kama matar ka ku tafi gida, kuma da ka ke fad'in Mubaraka ta tahi yawo, ka hini sanin halin ta, iya sani na da ita ba za ai mata shaidar yawo ba, yarinya ce me hankali ,ko tunanin wani abun ne ya same ta baku yi, ku kam Allah ya yi muku sauqi, (gyara tsayuwar shi Ɗan jumma ya yi, ya na kada hannu, ya ce) zan ruhe gida"

Cikin sanyin jiki Mai buruji ta bi Dan Talo da jiki ya wa sanyi, sai yanzu maganar batan Mubarakan ya fara shigar shi, tabbas ita ba me yawo bace, kawai dai yawan fad'a da Lamishi ke yi ne ya sa shi ma yake fada.

Su na shan kwana suka tsaya cak, sai da suka tabbatar motar Lawwali bata nan, suka qarasa.

Su na shiga suka ga Lamishi na hada kayan ta, cikin tashin hankali, Dan Talo na tsaye a bakin qofar shiga dakin ya ce,

"Ke kuma mi na na ki ka yi haka? Ina zaki da wanga tsohon dare?"

"Gidan iyaye na zan tafi, tunda d'an da na haifa da ciki na ya ce sai ya yi ajali na akan qaunar shi, diyar da ni na haihe ta da ciki na, wanga wanne irin bala'i na? Ka dai san yadda Yaron nan shike ko?"

"Tau in kin tai can an ce maki barin ki zai? Kin ga kin ja musu musiba, gwanda ki zauna, gobe mu tai bid'ar ta gaba dayan mu, ki yi tunani dai"

Shiru ta yi, ta na nazari,to ina Mubaraka ta tai? Ita din ba me yawo ba ce, (sai yanzu ta san ba me yawo bace, duk sunayen da take kiran ta da su).

***********************

A hargitse ya shiga dajin, kowa ya san Oga ba lafiya a daren,dan haka kowa ya nutsu, No 1 da sauran yaran shi na kusa ne suka bi shi a baya, dakin da suke ajiye mutanen da suka sato, 'yan uwan su sun kasa biyan kudin fansa ya shiga ,firfito da su ya sa aka dinga yi, sai da ya fidda wajen mutum biyar sannan ya jera su a filin wajen, idanun shi kadai abin tsoro ne, bindigar da aka cika da harsashi ya karba ya dinga kai musu harbi, sai da ya harbe su tass, sannan ya koma dakin shi da ke wajen, ma'ajiyar giyar shi ya je ya bude,ya jima kwarai rabon shi da shan giya ,dakko kwalba ɗaya ya yi, ya kafa kai, bai aje ba sai da ya sha ta kusan rabi, wata iriyar razananniyar qara ya saki, ya buga kwalbar a qasa, wannan qarar ta firgita No 4 ba kadan ba, hankalin shi ya yi bala'in tashi, tsoro ya hana shi tunanin mafita.

In ya ce ze sanar da gaskiya,ya san bai tsira ba, in ya bari har Lawwali ya gano da kan

Please Login or Register in order to submit comment