Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

se na ci wannan"

Hansatu da yara kuwa na can sun saka barin kaza a gaba, su na ci, su na hamdala ga Ubangijin da ya azurta su da kaza ba tare da sun roqa ba.

Dan sauran lemon Isah ya fito ya miqawa Ahmad ya ce,

"Gashi nan, ba yawa ne da shi ba,...ke kuma in kin gama ki zo ina neman ki"

"To mun gode Allah shi qara budi, Allah shi ruhwa maka asiri duniya da lahira, mun gode,"

"Ameen, ina abinci na? Ko dan kun ci kaza se aka ce miki ba zan ci abinci ba?"

Da sauri ta miqe ta na bashi hakuri, abincin dama da ya rage taliya ce da manja, da dan yaji, har ta na murna in be ci ba da dare ta bawa yaran, tunda komai ya qare, ya siyar.

Ta na bashi kuwa ya zauna a tabarmar da suka tashi, ya cinye tass, ya kora da ruwa.

Daki ya kira ta, da yammar, ana gab da magariba, Hansatu na ta bashi hakuri akan ya bari a mayi sallah haka Isah ya qi, sai da komai ya yi daidai a tsakanin su sannan ya sa ta hura wuta ta ษ—ora masa ruwan wanka, dan a cewar shi yin wanka da ruwan sanyi da magariba mura ze saka shi.

Da kyar iccen ya kama, ta samu ta ษ—ora ruwan ya yi,ta kai masa, itama tayi, ta yi sallah.

Shi kuwa ya na gamawa waje ya yi, ganin shi kuma se sanda Allah ya yi musamman ma da yake jin aljihun shi da nauyi.

Hansatu na shara, ta ji sallamar Yabbuga, watso sharar dakin ta qarasa yi, ledar da Isah yaci kaza ta baje a qasa, ido Yabbuga ta zare waje, tare da sake baki, ta na salati.

"Keeeee waggaa, yanzu kaza kun ka ci shi na ko a qunshe fuffuke a kai min, tau wanda ya ci shi dai, shi dai zai mace, walle a dena rauwwa, yanzu ba daban Allah ya sa na ga kin kunna wuta ba, na zo diban rushi, da ban ko sanin kun ci kaza"

Hansatu mamaki ne ma ya gama qamar da ita a wajen, yanda Yabbuga ta dage ta na magana cikin fad'a ne ya fi bata mamaki, kuma gashi tabbas yawu ya cika mata baki, murmushi ta yi, ta ce,

"Allah shi baki hankuri, dake ba a gidan anka soya ba, balle na ce qamshi ya dame ki, nima yanda kiggane ta haka niggane ta, ya taho mana da ita, amma ki yi hankuri, in ya sake kawowa ina kawo maku"

"Tun da kwadayayya ni ke ko? Yo ce miki niyyi bamu da azziqin cin kaza? Yau na ji zancen yohi"

Yabbuga na diban garwashi ta na Masifa ba a sammata kaza ba.

Hansatu kuwa abun ma ya dena bata mamaki, dariya ta dinga yi, ita da yaran.

***********************

A bangaren Lawwali kuwa............

*Sai gobeeeeee*๐Ÿ˜…
๐Ÿ’…๐Ÿป *A GARIN MU* ๐Ÿ’…๐Ÿป


BY HAERMEEBRAERH


PAGE 27:




Sati biyu ya wuce ba Lawwali ba bayanin shi, ba Sultana kadai ba, hatta da Gwamna Halliru ya fara shiga tashin hankali akan lamarin Lawwali.

Duk wata barna da ta'asa da Lawwali ke aikatawa ta na komawa kunnen Gwamna Halliru, ga zabe ya gabato sauran kwana goma sha uku, lamarin ya tabarbare fiye da tunanin Gwamna, domin kuwa a yanzu Lawwali ko cikin gari bai cika shiga ba, sai jefi jefi dan ya ji halin da ake ciki game da neman qanwar shi da ya sa a yi.

Lawwali ya koma kamar mahauci, akan neman Mubaraka, ya yi kuka har ba iyaka, ya zama kamar wanda ya rasa iyayen shi da dangin shi a dare daya.

Duk wata motar da ta yi tsautsayin bi ta kusa da dajin su, to sunan su matattu, ko kuma ya sa a kame su, ayi ta azabtar wa, ko ya sa a yi ta amsar kudi wajen dangin su, madadin batan Mubraka ya risinar da shi,sai ya sake ruruta masa wutar rashin imani a zuciyar shi.

Sultana kuwa duk ta fige ta rame saboda rashin Lawwali, ko ta je Foundation din ma watarana da kuka take komawa gida, rashin ganin shi a idanun ta ba karamin azabtar da zuciyar ta yake ba.

Duk ta dora laifin akan Hajiya, domin a tunanin ta maganar da Hajiya ta yi ne ya sanya shi yin fushi ya tafi.

Ta gwada No shi ya fi sau shurin masaqi amma ta qi shiga, kullum sanar da ita ake a kashe wayar take, ta yi kuka ta godewa Allah, ta yi sallah ta yi addu'a akan Allah ya dawo mata da shi in da alkhairi, in babu Allah ya sa mata hakuri da dangana, hakan da ta yi ne ya sa ta ษ—an samu sauqi kadan a ran ta, har ta ci gaba da aikin alkhairin da ta sa wa ran ta.

Shiru shirun ta, da rashin shiga mutane da take ya bawa Gwamna damar yada abubuwan da take na alkhairi a gidajen talabijin da rediyo, da duk wata kafar sadarwa, mutane kuwa na ta yabawa, wasu na qara neman taimako a wajen ta, ita kuwa hakan na mata dadi, ganin aikin da take ya na ta bunqasa.

In ta na aikin ta na samun nutsuwa da kwanciyar hankali,da ta dawo gida komai sai ya kwance mata ,ba abinda take gani a idon ta in ba Lawwali ba, tsayuwar shi a jikin mota, da murmushin shi mai sauti, yanayin yanda yake kafe ta da ido, ya na kallon ta, sai ta ji kamar a wannan lokacin ya ke kallon nata, har lumshe ido take, watarana ta yi murmushi in ta tuna, watarana ta fashe da kuka.

An shiga sati na Uku Lawwali be bayyana ba, sai wata safiyar Lahadi, ya shiga gari, direct wajen aski ya nufa,a ka yi masa aski me kyau, aka masa gyaran qafafu da hannuwa, sannan ya sayi turaruka, da kayan abinci ya nufi gidan shi,ko da ya shiga gidan duk ya yi qura, kallon ko ina ya yi, cikin sanyin jiki ya ajiye ledojin hannun shi ya kalli ko ina, wasu irin zaratan hawaye ne masu zafi suka dinga zubar masa.

Mubaraka ce ke masha shara, in ta biyo shi, ta yi wanka ya maida ta gida, ko gyaran da akai wa gidan na qarshe ita ta masa, har ta dinga mishi fadan ta ajiye wani flower vase a tsakiyar table, ta koma ta gan shi a qasa, ya kama kunnen shi ya na bata hakuri, ta na ta tura baki ta na shagwaba, ta ce ta hakura kar ya sake, ta mayar ta gyara komai, ta yi wanka ya maida ta gida, ya na gama tunawa ya sanya wani irin kuka mai ban tausayi, sannan ya ce,

"Barakana ina kin ka tai na? Wanne hali ki ke ciki? Kin ci abinci? Kin yi wanka kuwa? A wanne irin waje ki ke kwana? Barakana, ki yafe wa yayan ki, na kasa kare ki, na kasa nemo ki, baraka na ki dawo gare Ni, ke ce sanyin idaniya ta, na rabu da Sultana duk da son da nake mata, na kasa cire ta a zuciya ta, dan Allah ki dawo ki taya Ni neman soyayyar ta, ba zan iya ba Ni dai,ke Ni ka jira ki sa Sultana ta so ni, Barakaaaa"

Kuka ya dunqule a waje guda ya na yi, kamar qaramin yaro, ya na son dika qannen shi, amma mubaraka ta daban ce, ita kadai ce ke son shi, ita ke kula da shi, ita kadai ta damu da rayuwar shi, tun ya na da burin ya dawo na gari, har ya kangare, ba wanda ya damu da wace iriyar rayuwa yake ciki, kudi kawai iyayen shi suka sanya a gaba, yau kuwa zai kai musu kudin da zai haukata su, amma sai suma sun bayyana masa Barakan shi, ko ya sawa kudin fetur a gaban su ya qona, hakan sai ya fi masu ciwo sama da yanda yake ji a ran shi.

A haukace ya debi kudin da ya koma da su, masu dimbin yawa a jaka, ya zari makullin motar shi, da wayar shi da ya bari a gidan, bai je ko ina da ita ba, motar shi duk ta yi qura.

Ya na shiga ya fitar da ita, ya koma ya kulle gidan, ya na qoqarin fita daga layin, motoci guda biyu da ke kai Sultana Foundation a yanzu su ka shiga unguwar suma,kamar an ce ta daga kai, Lawwali ta gani fuskar shi ba walwala, idanun shi jawur kamar ba shi ba, ya na tsula gudu,gashi duk ya yi duhu,

"Auwal? Dama Auwal na nan? Shi ne ya daina zuwa? Driver bi motar Auwal duk inda ya yi,"

"Tau Ran ki shi dade"

Dayar motar masu tsaron lafiyar ta na ganin an juya suma suka bi su, ta waya ta sanar da su me ke faruwa, kwantar da hankalin su suka yi suka bi su a baya.

Saboda damuwar da Lawwali ke ciki, be ma kula ana bin shi ba, har sai da ya shiga unguwar su, ya tsaya a qofar gidan su, sannan ya kula da motocin Sultana.

Wani irin yanayi ne mara fassaruwa ya shige shi, kewa ne, tsantsar soyayya ce, da kuma neman taimakon ta, duk sun had'u sun game masa waje daya.

Ita kuwa bata san sanda hawaye ke gudu a fuskar ta ba, ga alama nan, Lawwali na shaye shaye, amma bata duban wannan, domin dama dan Adam tara yake, be cika goma ba, ita dai a kowanne hali yake ta na son shi, ita kadai ta san ya take ji.

A hankali suke takawa zuwa ga junan su, Sultana ji ta yi kamar ta kwantar da kan ta a faffadan qirjin shi, ko abinda take ji zai ragu, Lawwali ji ya ke kamar ya isa ya rungume ta, ta shafa kan shi da siraran yatsun ta, tare da fada masa cewar 'Komai zai wuce, zai yi daidai' a cikin kunnen shi.

Sun jima su na kallon juna kafin Sultana ta yi qarfin halin cewa,

"Why? Me yasa? Me ya sa za ka tafi a lokacin da zuciya ta, ta amince, ta yarda, ta kuma gamsu da ta kamu da matsanancin ciwon son ka? Me ya sa ka tafi, a lokacin da nake tsananin buqatar ka, ka kuwa san ya nake ji a nan dina? (Ta sanya hannu, ta nuna saitin zuciyar ta, cikin kuka,) ba zaka gane ba, saboda baka san me ne ne soyayya ba ga dukkan alamu,"

Cikin sauri ya dakatar da ita, dan kalaman ta na sake harzuqa zuciyar shi, ta na hango masa mugunta kala kala.

Cikin cije lebunan shi a cikin bakin shi ya shafa kan shi, da hannu daya, sannan ya ce,

"Sultana, ba ke dai ka jin duk abinda kin ka lissahwa ba, ni ma ina ji dika, wataqila har da dori ma, amma sultana ba ke d'aya zuciya ta ke so ba, qauna ta ita ce rayuwa ta, ban da komai banda kowa sama da ita,ita kad'ai ce gata na a duk qasar ga, ba mai so na tsakani da Allah, sama da ita, a yanzu haka ji na nake kamar duk duniya sun juyan baya, ni kadai ne, ban da kowa banda komai,"

"Wait a minute,me ya samu Mubaraka?"

A cikin tashin hankali Sultana ta masa wannan tambayar, a cikin qasa da minti bakwai ya bayyana mata me ya faru dangane da batan ta,da kuma irin neman da yake mata, bai samu ba.

Cikin kuka Sultana ta juya ta rufe bakin ta, ta jima a haka ta na kuka, Lawwali ma ji ya ke kamar ya yi kukan, sai daga baya ta juya gare shi, ta na share hawayen ta, motar ta ta fara budewa zata shiga,sannan ta ce,

"Mu je gida Daddy na nan yau, mu sanar da shi,a sanya neman ta, duk inda ta shiga, i love her, she is a gud gurl, I can't let anything happen to her, she is like a sister to me, mu je gida Auwal, maza shiga mota mu je,"

Kallon gidan su ya yi, cikin takaici, ya na jiyo muryoyin mata ana ta zabga hira, ya ji haushi da be shiga ya tarwatsa su ba, qanwar shi ta bata amma suke hira haka ana dariya har waje ana ji, ya so ya shiga ya gan su, da duk sai ya musu rashin mutunci d'aya bayan d'ayan su, amma ba komai next time.

Kwafa ya yi, ya shige motar shi, ya bi ta su Sultana.

*************************

Gwamna Halliru na ganawa da su No 1 da 4, su na tattaunawa akan yanda Lawwali ya haukace.

Sultana ta je za ta shiga parlour wasu masu tsaron wajen ne suka dakatar da ita, tare da sanar da ita cewar Gwamna ya ce kar a bawa Kowa damar shiga, sai da izinin shi, d'aya daga cikin su ta kalla tace,

"Ka je ka sanar da shi ni ce, na ke son magana da shi, ya na da mahimmanci na gan shi yanzu"

Har security din zai tafi, Lawwali ya qarasa shiga wajen, su na hada ido, security ya ja baya, tare da fadin,

"Ran ka ya dade Oga, Barka da zuwa"

"Gwauna hwa? "

"Shi na ciki Oga"

Mamaki ne danqare a cikin Sultana, an hana ta shiga amma an budewa Lawwali ya shige,me kenan? Lawwali ya fi ta matsayi a gidan Uban ta kenan?

Ko da suka shiga shiru wajen ya dauka, ba No 4 da ake tausa ba, ana nuna masa ba abinda Lawwali zai yi, as long as bai gane ina qanwar shi take ba, har Gwamnan kan shi sai da hankalin shi ya tashi ainun.

Cikin rawar murya, No 4 ya ce,

"O....ogaa, kai ne da rana haka?"

Lawwali ko kallon No 4 be ba, ya samu kujera ya zauna, tare da harde qafa,No 1 ne ya je ya tsaya a daf da shi,hakan kamar girmamawa ne a gare shi, No1 na ta hararar No 4 tare da yi masa nunin ya nutsu, Sultana kuwa mamakin abinda take gani ya fi qarfin ta, waje ta samu ta tsaya, ta na kallon yanda mahaifin ta ya yi lakwas a gaban Lawwali, bai magana ba akan zaman da Lawwali ya yi a gaban shi .

"Oga har yanzu fa shiru,yanzu haka mun kawo maganar ne wajen Excelency saboda a bamu taimako"

"Mu ma abinda ya kawo mu kenan,na yi iya qoqari na na kasa, ina neman taimako a hukumance, a bido min qauna ta, in ba haka ba,....."

Shiru ya yi, ya taune leben bakin shi na qasa, tare da dukan tafin qafar shi da ya dora a saman dayar qafar tashi.

"Ah ah Sultana, mik-kawo ki nan?"

"Tare muke,"

"Ban gane tare kuke ba, qaqa an kai kuke tare?"

"Dad Mubaraka ce ba a gani ba, kusan sati Uku yanzu, shi ne na rako shi neman taimako wajen ka, amma yanzu na kula is like, ni anka rako, ko wani zai iya min bayani akan abubuwan da nake gani a yanzu?"

Da sauri gwamna ya zari wayar shi, ya kira Head quarter na yan sanda, ya fara bada report din batan Mubaraka, Sultana tuni ta manta da tambayar da take yi, ita da Lawwali sun bawa Gwamna hankulan su.

Wayar aka bawa Lawwali ya yi kwatancen ta,da bayanin ranar da suka nemeta suka rasa, tare da alqawarin ze tura hotunan ta.

Godiya ya miqe sosai ya na wa gwamna, Sultana ma haka.

Gwamna na son bin su ya ji dalilin da ya sa suke a tare, kuma ya na son magana da su No 1, dan haka sai da ya bari su Lawwali sun fita, sannan ya qara jaddada musu su yi taka tsantsan ta yanda asirin su ba zai tonu ba, domin in Lawwali ya san sun sace qanwar shi, har shi kan shi ba zai tsira ba, ballantana su.

Wannan kalamai sun sake birkita No 4, da kyar yake hadiyar yawu, zufa sai karyo masa take, a sati ukun nan, duk 'yar qibar ma da ya yi, saboda kudin da suke samu, duk ta zabge, ya fita hayyacin shi, ba wani kwanciyar hankali a tattare da shi.

Su Sultana kuwa a jikin motar shi, suka tsaya, su na magana, hira ce mai dadi,ta yaushe gamo suke yi, kusan kaso saba'in na hirar dukkan su akan Mubaraka su ke yi, Sultana na son mubaraka, ba wai dan ta na qanwar Lawwali ba,ah ah, yarinyar abar so ce ga duk mai hankali.

Shi kuwa a wajen shi Mubaraka ita ce rayuwar shi, a ganin shi ma ba zai taba samun kan Sultana ba in bata nan.

Bayan sun yi sallama za su tafi ne Sultana ta ce,

"Haka ake sallama da masoyi? "

Kallon yanda ta maida kai gefe ta yi, sai ta masa kyau, murmushi ya yi, kadan, wanda rabon shi da murmushi na gaskiya, ba na mugunta ba, tun kafin batan Mubarakan.

"Ya ya kamata masoyi ya yi sallama ?"

Dan rufe fuskar ta tayi da hannun ta kadan ta ce,

"Kamata ya yi ka ce, Sultana na tafi, zan dawo anjima, ina son ki"

Bude baki Lawwali ya yi, ya na dariya mai sassanyan sauti, ya ce,

"Kaiii ka kaiii ka kaiii, Baraka na ta ce man ke ustaziya ta wallah, ashe ke iya soyayya haka?"

Mayafin ta ta ja sosai ta rufe fuska sannan ta ce,

"To ai soyayya kowa na yi"

"Ok, to sultana Ina son ki,"

Wani irin dad'i ne ya ziyarce ta, musamman da ta kalle shi ta ga babu wasa a kalaman shi, iyakar gaskiyar shi yake fada, ta ji sautin Muryar shi, ba alamar gatse ko wasa, amayar da ta ta zuciyar ta ce,

"Auwal ina son ka, In na ce ina son ka, ba ina nufin ina son ka fiye da yanda kk so na bane, ina nufin ina son ka a kowanne hali, ina son ka ko da wani sabani ya haษ—a mu, ina son ka ko da ka na cikin damuwar da ta sa ka nesanta da ni, ina son ka sama da nisan nan da ke tsakanin mu,ina son ka sama da yanda na ke jin zafin rashin ka a rai na, ina son ka sama da dukkan wani abu da zai qoqarin shiga tsakanin mu, ina nufin nafi son ka Auwal"

Ya Salam, Lawwali ya gama narkewa,kalaman sultana sun wanke masa wani kaso na baqin cikin da ke ran shi,dama haka take fata, shi ne dalilin da ya sanya ta cire kunya ta furta abinda ke ran ta, sai bayan ta gama kashe masa gabban jikin shi, ta juya da gudu gudu ta shige gida,dan kuwa kunyar shi ba zata bar ta ta tsaya jin me zai ce ba again.

Lawwali ya jima a wajen, kafin ya shiga motar shi, ya tada ya bar gidan.

Su No 1 kuwa ya na fita suma suka bar gidan, dan zuwa sauyawa su Mubaraka maboya kamar yanda Gwamna ya bada shawara, da kuma wajen zama.

Lawwali har ya isa gida bai dena murmushi ba, ya jima ya na dirzar dattin jikin shi,kafin ya samu abinci ya ci rabon shi da abinci sosai kamar na ranar ba zai iya fadin ga lokacin ba.

Ya na kammalawa ya kwanta, dan hutawa.

**********************

Vissa ta samu, na tafiyar Isah Saudiya, ana sauran kwana biyu tafiyar Isa, Hajiya ta sa Isan ya kai mata su Hansatu su gaisa, Hansatu ta sha mamakin jin duk abinda ke faruwa a bakin mahaifiyar ta, ace duk wadannan abubuwan na faruwa bata sani ba? Haka ta dinga yaqe ta na yabawa Isah ,tare da yanka qarya kala kala, dan ta kare shi, yaran ta na ta mamakin qaryar da take ta shinfidawa.

Ba daban ta basu tarbiyya mai kyau ba, tabbas da sun tona mata asiri, dan kuwa ba su so ta rufa masa asiri ba.

Isah kuwa sai murmushi yake ya na fadin,

"In ban muku ba wa zan wa?"

Yayan Hansatu ya qara masa dubu hamsin ya qara a kan jarin shi, sai godiya suke ta zabgawa.

Da yamma Hajiya ta sa mota ta maida su gida.

Tafiyar Isah Makka daiiii sauran kwana biyu, wace zata yi rakiya?????๐Ÿ˜‚

๐Ÿ’…๐Ÿป *A GARIN MU* ๐Ÿ’…๐Ÿป



BY HAERMEEBRAERH


PAGE 28:

Kafin tafiyar Isah ya yi qoqarin ajiye musu buhun shinkafa, ya aje musu galan din man gyada da manja, galan daya daya, ya sai masu maggi, wake,barkono, da gishiri, ya sai musu taliya, su omo da sabulun wanka da wanki, rabon Hansatu da ta ga irin wannan kayan a hade waje daya, tun sanda suka yi aure, sai yau, kuka take ta yi, saboda rabuwa da masoyin ta.

Hajiya ta mata alqawarin zuwa da ita da yaran da Hajiyan kan ta,ta bata hakuri tare da lallashin ta akan ta bar shi ya tafi domin kasuwancin shi.

Yaran Isah kuwa murna suke da tafiyar tashi, har abun ya kasa boyuwa, garin murnar su da surutun da suke ne ya ja hankalin Yabbuga, da ta kasa kunne a cikin gidan, tun sanda ta ga ana shigar da kayan abinci.

Dan Jummaa ne ya wurge ta da dan qaramin dutse, ya ce,

"Ke hwasa zuwa gidan Kareema? Ina ta magana ke yi shiru"

"Bar tahiyar nan, zuwa gobe zan tai, wai shin dole na sai ka kaini? Mu na tahe saman mashin kamar 'yan bangar siyasa, ka yi tahiyar ka na yi tawwa"

"In baki hau bayan nawa ba, ai ke hau na wani qato, tau ki sani, walle baki zuwa ko ina in ba ni na zan kai ki ba, zancen banza zancen yohi"

Cikin fushi y fice ya bar gidan, Ita kuwa ko a jikin ta, kunnen ta na gidan Isah, so take ta ji kalmar da zata gama da wadda ta qunsa ta haษ—a su bata ma'ana amma ta kasa.

Tsaki ta ja, ta zari mayafin ta, ta shuri takalman ta ta fice daga gidan ,ko jan qofa bata yi ba.

Ko sallama bata yi ba, haka ta afka gidan, karaf kuwa kunnen ta ya ji maganar Ahmad, ya na fadin, in baban su ya tafi Saudiya gobe a gado zai kwana.

Wani irin salati ta zabga, tare da tafa hannaye, Hansatu ce ta fito daga daki da gudu, ido ya mata jawur da alama kuka take.

"Lahiya? Mi ya hwaru halan? ",

"Yanzu ke Hansatu ina ganin ki shiru shiru ashe munahika ta? Ashe ke dauke ni maqiyyiyar ki da baki hwadi min mijin ki zai tahiya Makka, yau Allah ya sa ina da kunnuwan jin dumi, na jiyo daga wajen diyan ki, se qaqa?",

Cikin fushin da Hansatu bata san ta na da kalar shi ba ta kalli 'yabbuga ta ce,

"To sai qaqa kuwa? Ko ki na hana mai tahiyar na? Yo Ni na ji ikon Allah, komi na se na hwada miki? Tunda muke a matsayin ki na makwacciya ta ke taba zuwa ki tambayen shin na ci abinci Ni da diya na? Ko ke taba zuwa ki tambayen wane na abba lahiya cikin d'iya na ko niya? Haka d'ai ki dora min jidali? Don Allah dai ki barni na ji da abinda ka damu na"

Daga 'Yabbuga har yaran sai da mamakin Hansatu ya aure su, budar bakin Amina kuwa sai cewa ta yi,

"Kaiiii Umma ke burgeni wallah, dama haka nan zaki zanka yi wa Baba"

Wani kallo Hansatu ta mata, wanda ya sanya ta hadiye dariyar ta, suka shige ciki dukan su,

"In kin qare jin Isah zai tahiya Makka, sai a tai shiyya a baza"

Habaaa nan da nan kuwa 'Yabbuga ta hau bala'i ta na fadin yarinya qanwar bayan ta na kiran ta da munahika, a haka dai ta zare ta bar gidan, cike da borin kunya

Hansatu kuwa ta gama hada wa Isah kayan shi kafff a jaka, sabbin dinkunan da yayi, da takalma da duk wani abu da zai buqata su na akwati.

Shi kuwa ya gama hada goron shi da duk wani abu da zai buqata, ya daure ya aje, gobe kawai ya ke jira ta yi.

Daren ranar Isah ya mori jikin Hansatu kamar ba zai barta ba, Ita kuwa ta ci kuka kamar ba zata bar idanun ta su huta ba, zuciyar ta na matuqar zafi da quna, a duk sanda ta tuna gobe zai tafi, duk ta bi ta qular da Isah, amma ya danne, waya ya dauko aljihun rigar shi, yar qarama, me kyaun fasali, ya miqa mata.

Da a da ne ya bata da tayi murna, amma yau ji take kamar ya na bata takardar saki, ji take kamar ta na bankwana da shi na har abada ne, rabon Isah ya lallabata haka tun ta na amarya.

Ran Isah fa ya gama ษ“aci yanzu, ya na bata waya ta na gani ta qi amsa ta na kuka, tsawa ya daka mata, sai da zanin da take ta share hawayen idanun ta ya kusan subucewa,

"Keeee ! Ki na barin kukan iskancin nan ko baki bari? Ban son shashancin banza da wofi za

Please Login or Register in order to submit comment