Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hoto.

A hankali motocin ke tafiya, har suka isa wajen event din, wani irin kidan waqar Hamisu breaker aka saki da ya yi wa amare, Lawwali ne ya fara fita, ya zagaya, ya budewa Sultana mota, ta fita, hannun ta na cikin nashi, kan ta a qasa, ta fara takawa, duqawa ya yi kadan ya mata rad'a a kunne, daga kai ta yi, a lokaci daya ta fashe da wani irin kukan farin ciki, hannun ta ta sanya bakin ta ta na zubar da hawayen farin ciki, ba kowa ta gani ba illa qawayen ta da suka yi karatu da ga na nan gida Nigeria har turawa na can qasar waje, sai tsirarun abokan Sultana da Sultan din kan shi, sun yi ankon baby pink din wani tsadadden material, larabawa da hausawan mu na nan sun yi rolling kan su da mayafai masu adon duwatsu.

Turawan cikin su kuwa an musu dinki daidai da yanayin su, an gyara gashin nan sai sheqi yake, an ci dogayen takalma masu tsini.

Yau kwanan su biyu a Nigeria, Sultan ne ya gayyace su, tare da tsara komai da ya kamata, duk da cewa a qurarran lokaci ne ya samu nasarar tsara abubuwan yanda ya kamata, a hotel din City king hotel Gusau, ya musu masauki.

Nan da nan kuwa suka dinga zuwa daya bayan daya suna gaisawa da Sultana, ana rungume rungume ,da sumbace sumbace irin na gaisuwar mutanen qasashen turawa.

Sai da suka gama tsaf ta taka zuwa gaban Sultan,ta rungume shi da kyau, ta na kuka tare da yi masa godiya.

Share mata hawaye ya dinga yi, ya na girgiza mata kai, shiru ta yi, ta na murmushi, basu shiga main wajen taron ba, sai da suka je wani daki a hotel din da ake taron, aka gyara mata kwalliyar ta, sannan qawaye suka fara shiga aka sanya amarya da ango a tsakiya, ana tafe Hamisu breaker na waqe su.

Ranar su 'Yabbuga an yi ciniki, dan duk kudin da iska tai gangancin kawo shi wajen zaman su, to fa b'atan dabo yake, ba a sake ganin shi .

Biki ya yi biki, Hajiya Ikee da qawayen ta, sun samu abinda suke so, an ci, an sha, an raqashe, an watsa kudi,su Asshibi, sai kallon turawa ake ana musu hoto, Mai Buruji da Lamishi kuwa sai fad'i ake wa mutanen unguwa ana tinqahon bikin d'an su ake.

Lawwali kuwa can qasan ran shi kewar Mubarakan shi yake, ana hidimar bikin shi amma bata nan, da gwamna bai mishi abinda ya masa ba da tuni, auren nan, da zuciya daya za a yi shi, ba wata boyayyar manufa, da tuni masoyiyar shi, kuma qanwar shi abar qaunar shi na wajen, in ma ya kyale gwamna bai rama abinda ya masa ba a rayuwa ai bai cika dan halak ba.........

*Wai ni dan Allah ba za a hakura da wannan daukan fansa bane??*

๐Ÿ’…๐Ÿป *A GARIN MU* ๐Ÿ’…๐Ÿป


BY HAERMEEBRAERH

PAGE 43:



An tashi taro lafiya, babu wani wanda ya tafi da qorafin bai samu abun biki ba, ko bai ci ya qoshi ba.

Bangaren su Lamishi kuwa ta so su gaisa da Hajiya Ikee da qawayen ta, ko dan ta qara kankaro wa kan ta aji da mutunci, wajen mutanen unguwar su, amma haka Hajiya Ikee ta dauke kai, ta na yatsina ta ce musu ta na zuwa, ko da ta tafi sallama tai ta yi da qawayen ta da suke komawa gidajen su, ta na gama sallamar su, ta tafi ta ta motar, aka ja ta sai gida.

Haka su Lamishi suka gaji da jira suma aka kwashe su sai gida, Sultana ranar a hotel din da qawayen ta suke ta kwana, duk da Lawwali ya so ya maida ta gida,amma ta nuna masa rashin dacewar hakan, tunda dan ita suka zo.

Ai kuwa kwana suka yi su na hira, suka ci suka sha, suka yi games kala kala, irin na al'adun wasu qasashen.

Basu suka kwanta bacci ba sai bayan sun yi sallar asuba, su na idarwa kuwa suka hau baccin gajiya.

Sha daya na rana suka tashi, suka hau wanka, da shirin tafiya gidan Gwamna, yau za a Daura auren Sultana da Lawwali, masu gyaran jiki da kwalliya sun hallara, nan da nan amarya da qawayen ta suka sha gayu, ankon purple din yadi suka sanya, amarya ta saka nata kalar golden da milk, qamshi sai tashi yake ko ta ina, in ka kalli wannan sai ka ga kamar tafi kowa kyau a wajen, da ka kalli 'yar uwar ta sai ka ga ta doke ta farkon kyau , kowacce na ji da kyau, aji, ilimi, da gayu.

Manyan motocin da suka je daukan su abun kallo ne, cike da nutsuwa ake tuqa su har zuwa gidan Gwamna halliru, tin daga farkon layin unguwar har qarshen shi motoci ne, na alfarma, matan manya ne danqam a cikin gidan, wasu daga wasu garuruwan suka zo, wasu a cikin garin suke.

Amarya na shiga gidan hankali ya koma kan ta da qawayen ta, Sultana ta gode ma Sultan a ran ta ya fi sau a qirga, ba dan shi ba da sai dai ta yi ta yawo ba qawaye, da kuwa abun bai yi armashi ba.

Bayan an yi sallar azahar ne aka daura auren Auwal da Sultana a Central mosque, da ke cikin garin na Gusau, a kan sadaki Naira dubu dari biyar, lokacin da Dan Talo ya ga Uban kudin da Lawwali ya damqa masa a hannun shi ya ce na sadaki ne, ji ya yi kamar ya suma dan takaici, a cewar shi wannan qarawa mai qarfi qarfi ne ai.

Haka dai ba dan ya so ba ya bada sadakin nan.

Kowa ka gani cikin farin ciki yake, Lawwali kuwa ba a magana, bakin shi ya qi rufuwa, sai doka murmushi yake, daga qasan zuciyar shi, ya na jin wani irin dadi mara misaltusa, kwanciyar hankali da nutsuwa ta baibaye shi.

Bangaren gwamna Halliru kuwa, zuciyar shi baqiqqirin haka yake jin ta, amma haka yake ta murmushi da dariyar dole, ga mutanen da suka halarci daurin auren.

Lawwali ne ya ja abokan shi gefe ya ce musu,

"To an daura auren hwa, daga yanzu zuwa kowane lokaci wasan zai fara"

"To Oga, muna maka fatan alkhairi"

"Godiya ni ke, da irin jajircewar ku, da tsaya min bisa gaskiya da amana, sai na taho"

Sallama suka mishi, suka koma inda suka fi wayo, masu iyalin cikin su, sai da suka leqa iyalin su, da iyayen su, sannan suka tafi daji.

*************************

Gidan Alhaji Dan Talo mutane ne danqam,Lawwali ya saki bakin aljihu, sai wadaqa ake da abinci da abun sha, Hajiya aunty 'Yabbuga su ne akan abinci, sai abinda tace a zuba, a gefe kuwa Kareema 'yar ta ta zo itama, sai ta debi kaji, da drinks ta boye a zani, ta wurga mata, ita kuma Kareema ta dauke ta kai gida, in ta juye ta koma, haka suka dinga yi, sai da 'Yabbuga ta tara naman kaza me yawa da snarks da drinks .

Kusan duk wanda ya zo daga kan 'yan uwan Lamishi da Mai Buruji, da Dan Talo sai da suka yi ta tambayar Mubaraka, Lamishi ba ta da amsar bayarwa, dan haka sai ta shashantar da maganar, Mai Buruji ce ta qirqiri karya ta ce Yayan ta ya kai ta karatu qasar waje,shi ya sa ba a gan ta ba.

Ba qaramin dad'in wannan qaryar Lamishi ta ji ba, sai ta ji ta qara son kishiyar ta ta, Dan kuwa Mai Buruji abokiyar zama ce ta gari.

Lawwali ya sanar da su, ba sai sun je daukan amarya ba, shi da kan shi zai dau amaryar shi, su yi bikin su kawai anan.

****************************

Kamar yanda al'adar amare take, yin kuka a duk sanda za a kai yarinya dakin mijin ta, Sultana ma, ba a barta a baya ba, daga ita har Gwamna Halliru kuka suke, Hajiya Ikee kuwa idon ta kyamas ba alamar hawaye, sai dariya take musu, Gwamna Halliru na matuqar ji da Sultana, gashi ya zama dole a gare shi ya hannun ta ta zuwa ga Lawwali, Lawwali da kanshi ya je daukan amarya, ko aboki daya bai raka shi ba, Hajiya Ikee ta tanadi wanda za su raka amarya dakin ta, ba su da wani yawa.

Da kyar Sultan ya samu ya banbare Sultana daga jikin Gwamna Halliru, ya na kuka, itama ta na kuka, haka Sultan ya damqa ta a hannun Lawwali, wanda ya ke jin zuciyar shi ta karye matuqa.

Anya zai iya bada auren Mubaraka kuwa? Wani iri yake ji a zuciyar shi na rauni, wanda ya sanya shi zubar hawaye, bashi da abinda yake so sama da mubaraka a rayuwar shi, nisan da ta mishi ba qaramin qona zuciyar shi yake ba, kallon gwamna Halliru yayi, cikin tsananin takaici da tsana ba dan shi ba, da tini da Mubaraka a wajen.

Da sauri ya ja Sultana suka shige motar da ya zo da ita.

Hajiya Ikee sai da ta ga Sultana a mota ta tabbata tafiya zata yi, sannan ta ji hawaye na gangare mata, daga musu hannu mutane suka dinga yi, mota biyar ne suka dafe musu baya, dan raka amarya dakin mijin ta.

Gidan da Lawwali ke da zama suka nufa, gidan ya sha gyara, an qawata shi sosai da sosai .

Lawwali qin bude motar ya yi, ya ce ma driver ya sanar da su, su shiga su ga gida, in sun gama su tafi, da kan shi zai shigar da amaryar shi.

Dariya mutane suka dinga yi, su na ganin he is very romantic, qawayen ta dik sun mata sallama, kuma sun shiga sun ga waje, sun yaba, mota suka koma aka maida su hotel din da suka sauka, washegari kowa zata koma garin su da qasar su.

Sai da wajen ya rage daga Sultana sai Lawwali, Sannan ya fita, ya bude mata qofa, ta na zira qafafun ta waje, ya sunkuya ya dauke ta, driver ya buษ—e musu gate ya na dariya, wayar Lawwali na hannun shi ya na musu video.

Har saman gado ya ajiye ta, sannan ya amshi wayar shi, ya je ya rufe gida,ya koma dakin amarya, wadda ke ta kukan rabuwa da gida.

Lallashin ta ya dinga yi, ya na bata hakuri, da kyar ya samu ta yi shiru, gani ta yi ya cire kayan shi ya sanya na bacci, ya haye gado ya dau laptop din shi, da kallo ta bi shi, dama haka ake yi? Ina dan abinda ake kawo wa amarya? Ba zai je su yi Sallah ba dan godewa Allah? Ba zai mata addu'a ba da ake wa amare? Me ke damun shi?

Muryar Mubaraka ce ta karade dakin, cikin zumudin son gani da jin Muryar ta yake magana,

"Barakana an gama komai , an daura auren, an kuma kawo min amarya ta, ohh ni na manta, ni na dakko abata ta da kai na,"

Murna wajen Mubaraka ba a magana, se dariya take, ta na sanya albarka,

"Yah Auwal ina Aunty Sultana? Yaushe za ka turon pictures videos na yau,na ga na jiya, sun yi matuqar kyau,ba kadan ba gaskiya"

Da hannu ya yafici Sultana, wadda ita ma ta ji dadin ganin Mubaraka, gaisawa suka yi Mubaraka, ta musu fatan alkhairi, sultana ce ta ce.

"Wai Ni ina ki ka tafi ne akai bukin ba ke?"

Cikin shagwaba Mubaraka ta ce,

"Ina nan a Kan....."

Kit Lawwali ya kashe kiran, ran shi a dan bace, ya dauke laptop din ya sauka daga gadon.

Mamaki ya gama kashe Sultana a zaune, me kenan?

"Me ya faru? Bamu yi sallama ba ka kashe muna? Ban gama jin mi tace ba, ko dake da dukkan alamu Kano take son cewa"

Wata iriyar firgitacciyar tsawa Lawwali ya bugawa Sultana,

"Inji uban waye yace a Kano take? Ko kin ji sanda tace a Kano take? Kar na sake jin maganar inda Mubaraka take a wajen ki, ko da da nj ne, ballantana da wani"

Wasu irin hawaye ne masu quna, suke zuba a idon Sultana, mamakin shi ya hana ta rufe bakin ta, bin shi kawai ta dinga yi da kallo.

Bayan ya aje laptop din kwanciyar shi ya yi, ya juya bayan shi, ya na kallon gini .

Jiki ba kwari haka Sultana ta miqe, ta rage kayan jikin ta, ta shiga bathroom, ta yi alwala, ta zo ta tada Sallah ,dan a yanda ta kula ran shi ya dagule ba ta jin zai yarda su yi nafilar ma a tare.

Ta na idarwa ta miqe ta kashe fitila, ta kwanta cikin tsananin tsoro.

Lawwalin duk ya sauya mata a dare daya, dama maza haka suke lokaci qanqani za su sauya, to amma me ta masa da zai bata ran shi haka?

A hankali ta zira hannun ta jikin shi, cikin murya mai sanyi ta ce,

"Ka yi hankuri, ba zan sake maka, maganar inda Mubaraka take ba, balle in wa wasu."

Hannun ta ya riqe sosai a na shi, sannan ya ce,

"Dan Allah kar ki sanar wa da kowa, inna ce kowa ina nuhin kowa,"

"Inshaa Allahu"

Sultana dai na ta jira ta ji ango ya yi wani motsi ta ji shiru, har bacci mai dad'in gaske ya yi awon gaba da ita.........

*Ikon Allah, wannan wanne irin ango be????*
๐Ÿ’…๐Ÿป *A GARIN MU* ๐Ÿ’…๐Ÿป

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 44:

Abu kamar wasa, Lawwali ya qi sam wata alaqa ta auratayya ta had'a shi da Sultana, ba dan ta san dad'i ko wahalar abun ba, amma dai ta san kowanne miji da mata suna kasancewa a inuwa guda, bayan aure.

Duk wata kulawa da soyayya Lawwali na bawa Sultana, amma banda ta auratayya.

Yau sati Daya cif cif kenan da auren su, sultana na zaune gaban Laptop din ta, dan yanzu duk wani abu da ya danganci qungiyar ta, ta social network ta ke gudanar da shi, ta na transfer din kudi, da bada umarnin bude store a debi kaya duk ta internet ba tare da ta je ba.

Lawwali ne ya shiga gidan, cike da gajiya, da dukkan alamu ya yi wani aikin ne fitar shi, dan kuwa har da ciwo ya ji a hannun shi, da sauri Sultana ta isa gaban shi, ta kama hannun, ruwan dumi ta samo a yar qaramar roba, ta sanya detol ta wanke masa hannun, duk Surutu da sannu da zuwan da take masa bai amsa ba, sannan bai nuna mata yanda yake jin zafin taba ciwon da take ba, kalmar da taji ta fito daga bakin shi, shi ne ya bata mamaki, dan bata ga dalilin sake yi mata tambayar ba.

"Kin ce kin amince za ki zauna da ni a ko ina ko?"

Cikin mamaki ta amsa masa, tare da qarewa fuskar shi kallo.

"Kin amince kin ji kin gani, ki na so na a kowanne hali nake a dukkan yanayin da nake ko?"

D'aga masa kai ta yi, alamar Eh, dan ita da kan ta ta rubuta masa hakan a wani message da ta taษ“a yi masa.

"Kin yi alqawari ba zaki sauya alqawarin ki ba komai wuya komai rintsi? Kuma ko da ke san asalin gaskiyar wane ne Lawwali?"

"Dan Allah ka na bani tsoro, ka sanar da ni me ke hwaruwa, na ji na amince a kowanne yanayi, a kowanne hali, kuma ko kai wane ne zan zauna da kai,zan ci gaba da son ka,na maka alqawari, Sultana ba ta alqawari ta karya ka san da haka"

Hannun ta ya kama, ya zaunar da ita a saman cinyar shi, sannan ya ce,

"Ki shirya, akwai inda nake so na kai ki, ni ma na maki alqawalin duk abinda zan hwada maki ba zan hwadi qarya ba,na miki alqawalin ba zan riqe ki ki zauna da ni akan dole ba, daga lokacin da kin ka ce baki yin aure na, a lokacin zan sauw....."

Hawaye ne ke gudu a saman fuskar Sultana sosai, dan ta tabbata duk abinda za ta ji anan gaba ba mai dad'i bane, dan haka ba zata bari kalmar sauwakewa ko rabuwa ta hau saman labban shi ba, ta yarda da shi,ta san ba zai mata qarya ba.

"Ki shirya kayan ki a akwati, duk abinda ki ka son anhwani da shi naku na mata, ko akwati nawa zaki hada ki hada,daga nan zuwa dare, ko qarhe nawa zaki kai, kar ki damu,zan kai ki wani waje, nan gidan ba nawa ba ne, sultana ina so ki bar qungiyar ki hannun ma'aikatan ki, saboda tahiya ce za mu yi mai nisa"

Tsoro ya fara shigar ta ainun, amma abu daya ta sani,shi ne, ta yarda da shi, ta amince ba zai cutar da ita ba, cikin sanyin jiki ta tashi zata sauka daga jikin shi, ya kama hannun ta ta koma, fuskar ta ya qurawa ido, ya ga yanda take cikin damuwa da tsoro, a hankali ya ke share mata hawayen ta, ya na shafa bayan ta, irin yanda ake lallashin yaro in ana so ya bar kuka.

Bai barta ba, sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa, sannan ya daga ta, ya raka ta har dakin,shi ma had'a kayan shi ya fara, ganin haka sai ita ma ta fara hada nata,su na yi su na hira sama sama.

Laptop din ta da wasu abubuwan ta hade waje guda,Lawwali ya kalle ta ya ce,

"Ki ajiye su a gefe, ga wasu can a can dakin na sawo maki, ki yi anhwani da su,ki maida komai naki cikin su, wadannan ki goge komai ki bar su nan"

Kallon shi ta yi kamar zata masa tambaya sai ta fasa, ta yi duk yanda ya ce.

Basu suka kammala duk abinda suke ba sai qarfe takwas da rabi na dare.

Suna gamawa Lawwali ya yi waya, sai ga qofar parlour ta bude, wasu zaratan matasa Sultana ta gani na shiga, sai da ta gudu bayan Lawwali ta buya, saboda tsoron da suka bata, janta ya yi jikin shi ya rungume ya na buga bayan ta, da alamar lallashi.

Sai da aka kwashe kayan nan tasss aka zuba a bus guda biyu, sannan Lawwali ya kama hannun Sultana da ke sanye da doguwar rigar ta, da mayafin kayan.

Su na fita ta ga motoci Bus uku, qarama guda daya.

Cikin qaramar suka shiga ita da Lawwali, da kan shi ya ke jan motar, sauran kuma yaran shi ne a ciki.

Sun wuce qofar gidan Gwamna Halliru sai ta ji kamar a tsaya ta ga mutanen gidan su, amma ba hali, ta na ji ta na gani suka wuce gidan iyayen ta, suka dauki babban titi.

Tun ta na gane unguwanni, da qauyukan da suke wuce wa, har ta dena gane wa,tsoro da tashin hankali sun fara shigar ta, ba dan itan ta na son abun duniya ba, ah ah tsoron irin qauye da rayuwar qauye da zata fara take, bayan bata taษ“a yi ba.

Gani ta yi sun shiga daji ba gida gaba, ba gida baya, waje ne daji sosai , ta bude baki za ta yi magana, Lawwali ya dora yatsan shi a labban shi, shiru ta yi, ta na tsiyayar da hawaye.

Ina ne nan?
Me suke yi anan?
Wajen wa suka zo?
Shin a irin wannan dajin za su ci gaba da rayuwa?

Wadannan su ne tambayoyin da Sultana ke ta yi wa zuciyar ta,amsar ta bata samu ba sai da suka share awanni biyu da mintuna su na keta dajin, sannan ta hango wasu fitulu masu kama da na solar, dan kuwa a dajin nan zai wahala a samu wutar lantarki.

Kade kade ta dinga ji ya na tashi, da ganguna, ana waqoqi irin na kai amarya a qauye dinnan, bata san sanda murmushi ya kubuce mata ba, a ran ta ta ayyana cewar,

'Ashe ma qauyan su ya kawo ni, duk na bi na damu,'

Sun tsaya a harabar wajen da ake ta kade kaden da raye raye, nan da nan murnar ta ta koma ciki, sakamakon ganin matasa mata da maza dauke da makamai, da bindigogi.

Cikin ta ne ya bada wata iriyar qara, sai da ta damqe shi ta ษ—an duqa.

Lawwali ne ya d'aga hannayen shi sama ya na rawa,wajen kuwa aka dauki ihuuu, ana ci gaba da kid'a da waqa.

Sai da ya yi rawa sosai ya gaji, sannan ya kama hannun Sultana da ke tsaye a tsorace ya yi alamar a yi shiru, ko tari ba wanda ya sake yi a wajen kuwa, hakan ba qaramin sake firgita Sultana ya yi ba, ta kalle shi, ta ga ba alamar wasa a fuskar shi, sai dai wani kwarjini, da izza da ta gani kwance a fuskar shi.

"Ga amarya ta na kawo cikin mu, ina fatan za ku girmama ta, a mata duk wani abu da take so, kamar yanda za a yi min, sannan ina fatan za ku kiyaye dokoki na, dan mu zauna lahiya, ba cutaaaa???"

"Ba cutarwa, ba cin amana, ba karya alqawali"

"Da kyau, a ci gaba da shan shagali"

Kafin ya gama rufe bakin shi an dauki kade kade da raye raye, masu shaye shaye na yi, masu zinace zinace na jan abokan su suna barin wajen, kamilallun mutanen da aka kamo aka ajiye wanda suke da burin komawa gidajen su watarana na gefe, su na kallon masu rawa, a ranar zuqatan su sun taya Oga farin cikin kawo matar shi, domin ko ba komai, sun san ba ruwan shi da neman matan wajen, su na girmama yanayin yanda yake gudanar da wajen, ba yunwa, ba qishirwa, in baka so a kusance ka, ba mai maka dole wadan da aka wa dole ma a baya, yanzu sun wattsake, sun maida wajen kamar gida.

Babban abun takacin shi ne, ba ibada a wajen, duk da ba a hana mai so ya yi ba, amma fiye da rabin wajen basu damu da bautar Allah ba, basu damu da kiyaye duk wasu dokokin Allah ba, shaye shaye da zinace zinace sun yawaita.

(Ta yaya za a rabo ka da ga gidan iyayen ka, ko cikin iyalan ka a kai ka wata rayuwa mara 'yanci sannan ka dinga ganin an kyauta maka? Yau ko a wahale ka ke a rayuwa sace mutum ba abu ne mai kyau ba, Allah na sane da yanda ya aje dikkan bayin shi, dan haka sace mutane ko ta wacce fuska ce me kyau ko mara kyau ba daidai bane, Ya Ubangiji Allah, masu satar mutanen nan bayin ka ne suma da ka ke so, ka halicce su ka sanya su daga cikin halittu mad'aukaka, Allah ka basu ikon gane d'aukakar da ka yi musu su sauya rayuwar da suke kai zuwa wadda ka ke so Ameen)

************

Kayan su Lawwali an gama jere su a dakin su, akwatuna ne sun kai takwas, dakin babba ne, an qayata shi da kayan more rayuwa, sak dakin amarya, Lawwali duk ya ษ—ebe giya da duk wani kayan maye dake dakin, an maye gurbin wajen da lemuka manya irin masu tsadar nan,Sultana ta gaji da yin shiru, gaban shi ta tsaya, ta na hawaye, ta ce,

"Dan Allah ka warware min wannan qullin da ke cikin kai na da zuciya ta, kar ya matse ni na rasa raina "

"Ba zaki rasa ran ki ba Ran ki shi dade...auuu Sultana, taho nan ki zauna,abinda zan nuna maki, ba zaki iya kallon shi a tsaye ba"

Kwace hannun ta tayi, ta had'e su a qirjin ta, ta na jiran ya nuna mata duk ma me yake son nuna mata, ta gaji da yin shiru,

Murmushi ya yi, ya kwalawa No 5 Kira, ya shiga a guje, ya miqawa Lawwali wata baqar Laptop qirar Lenovo .

Ajiye ta ya yi, a saman wani dan table, ya kunna, ya shiga wani file, ya kunna wani video, nan da nan kuwa ya fara playing , abubuwan da Sultana ta fara gani, sun sanya mata jin jiri.

Jikin ta na rawa ta samu waje ta zube a qasa, ragwab a gaban laptop din, hannun ta ta sanya a bakin ta, ta na kuka, ta na jin wani irin sanyi na shigar ta,

Duk wasu kashe kashe da qone qonen garuruwan bayin Allah da akai, yau ta ga su waye ke yi, da kuma mutanen da ke sanya su yi din, duk wani tsafi, da fyaden yara qanana maza da mata, ta ga masu aikatawa, da masu kai musu yaran a aikata din, duk wani sabo da aka aikata da littafin Allah, ta ga wanda ya aikata dan kawai mulki, da son duniya.

Sultana kam qarshe numfashin ta ne ya dauke,ta zube a wajen.

Lawwali ya san za ayi haka, dan haka a shirye yake, yar locker da ke wajen, da yake ajiye ruwan gorar shi ya bude ya dauko, ya watsa mata, sannan ya dauke ta cakkk ya ajiye a saman gado,ya fita, dan ya bata waje, ta yi

Please Login or Register in order to submit comment