Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani abu da zai hada ta hulda da su Yabbuga, tunda ta san halin su.

Su na nan su na gulmar ta, ta na gida ta na fama da matsanancin ciwon qirji, ba komai ne ya kawo mata shi ba, illa rashin cin abinci, yaran ta ta kalla guda uku, biyu mata ,daya namiji, suna ta kai loma, hannu baka, hannu kwarya, akan qanzon da ta masu fate da shi.

Lallabawa ta yi ta dan debi loma daya ta kai bakin ta, wani irin zafi da murdawa qirjin nata ya yi, sai da ta durqusa,tare da rintse ido, hawaye ne suka sauka mata, da sauri ta share,dan kar yaran su gani,bata samu nasara ba kuwa, qaramin yaron ta mai shekara hudu ya ga sanda ta ke share hawayen,dakatar da cin abincin ya yi, ya ce,

"Umma sannu, qirjin ki na ka ciyo?"

Cikin murmushin yaqe ta ce,

"Eh shi na ka ciyo Ahmad, amma yayi sauqi, kaga Ni ma har na tashi ? Maza ka ci abincin ka yaron kirkin Ummaa,ku ta tahiya makarantar Allah"

"To Umma"

Amina da Bilkisu ma sannu suka mata, sannan suka dauki dan sauran faten da suka rage, suka aje a gaban ta, suka ce sun qoshi.

"Abincin da ba shi da yawa, ku canye shi maza, kahin ku dawo,inshaa Allahu zan sama mana wani abun, ku canye ku tafi makarantar Allah maza"

Qin ci suka yi, tare da barin kwanon a gaban ta suka tafi da gudu wanke hannu, suna gama wankewa, Amina mai shekara goma,ta shirya Ahmad cikin wasu yagaggun uniform din da sun dage masa, ita kuma hijabi kawai ta saka tamiqawa Bilkisu mai shekaru takwas nata hijabin, su na kammala sakawa suka yi wa umman su sallama suka fita, bakin su dauke da addu'a .

Ta gaban su Mai Buruji yaran suka wuce, sai da suka gaishe su sannan suka tafi,amsawa sukai su na bin su da kallo.

"Dazu fa Baban su har da shi a garkar mu, wajen cin abinci"

"Ai wadda kika san dan shi d'ai muka zuwa aiki,kullum shi na garkar mu, da ya qare cin abinci shi tai yawo"

Yabbuga ce ta karkace zata yanko wata gulmar Isa ya taho zai shige gida,cikin izza da isa da taqama ya ke tafiya , wanda be san shi ba zai rantse wani namijin azziqin ne.

Har su na rige rigen gaida shi ,juyawa ya yi, ya amsa tare da tsokanar su Lamishi .

"Ah ah matan Dan Talo kenan, irin wanga gayu haka awaz-zaku biki? Ko dake masu hidima gidan Gwauna ai dole ku wataya "

Murmushi suka yi, su na irin abun nan na mata in an yabe su, Yabbuga kuwa tsaki ta ja, sannan ta ce,

"Haramun dai, ka tsaya yabon matan wani, ka baro ta gida ba yabo"

"Yabbuga kishi takai da ku wallah, kun San bata iya ganin wani ya yi abu, batai ba"

Dariya suka sanya har da shewa, ya shige gida,ya bar Yabbuga da mita.

Kafin ya qarasa shiga ya daure fuska tamau kamar ba shi ne ya gama hira da matan wasu a waje ba.......

A GARIN MU






WRITTEN BY HAERMEEBRAERH









PAGE 4:


Jin motsin shi ne ya san ya ta miqe wa da kyar, hankalin ta tashe, domin shi din kamar wani dan aiken mutuwa n ne a gare ta, rashin fitar ta tsakar gida zai iya ja mata masifa a wajen mijin nata da take tsananin so da qauna.

Murmushin yaqe ta sanya a labban ta, tare da yi masa sannu da zuwa, bai amsa ba, sai shura buta da ya yi da qafar shi ta hagu, cikin wani irin mummunan yanayi ya juya ya kalle ta, yawu ta hadiya da kyar, cike da tsoro, bakin ta na rawa ta ce,

"Ka yi hankuri, su Amina na sun ka wanke hannu, Na....naaa manta ban zuba ruwa ba"

"Zaki debo min ruwa ko surutun banza za ki tsaya yi min?"

Da sauri ta tafi daukan butar, kafin ta sa hannu ta dauka ya tura mata da qafa, dan baya ta ja saboda kar ta bige ta, sannan ta duqa ta dauki butar, wajen diban ruwan daidai inda yake a tsaye ne, ya diba kawai, amma sai ya wahalar da ita.

Ta na gama zubawa ta duqa ta fara zuba masa, qamshin miya ta ji a hannayen shi a lokacin da ya tara su gaban ta dan ta zuba masa ruwa.

Murmushi mai ciwo ta yi, ta tabbata yau ma ya ci abinci a waje, ba tare da ya damu da ita ko yara sun ci ko basu ci ba.

"Baban Amina, nicce akwai dan kuddi wajen ka na dahwa muna abinci? Yau kwana uku ba mu ci abincin kirki ba, dazu ma qanzo na nissamo gidan Yabbuga niddahwa mun ka ci, kuma da alama yaran nan basu qoshi ba"

Hannayen shi ya sanya a qugun shi ya na kallon ta, irin kallon nan mai kidimar da wanda ake kallo, ta gigice matuqa, dan bata san me zai je ya zo ba, amma koma mene ne, bata da zabi, dole shi ne zai kula da su, shi ne zai yi mata duk wani abu da take buqata ita da yaran su .

"Kin raina Ni ko? Na ce kin raina Ni ko? Kin fara min tambayar titsiye ko? To ina da kudi,kin gan su, ba zan bayar ba"

Hannu ya sanya a aljihun shi ya zaro dari bakwai, ya nuna mata, sannan ya miqa su daidai fuskar ta,

"Ko zaki kwata ne? Tunda na ga kin yi qarfin halin yi min magana yanzu, ban sani ba ko kin yi qarfin duka na ki amshi abu a hannu na ne"

Kada kai take ta yi, tare da fadin,

"Ah ah, ka yi hankuri, ba haka nika nuhi ba"

"Hansatu , Hansatu, Hansatu ki kiyayen, kar ki bari na juyo kan ki ba zaki ji dadi ba"

Duqar da kan ta tayi, tare da share majinar da ke diga daga hancin ta, saboda kukan zuci da take,

Daki ya shige, ran shi a matuqar bace.

Babban abinda ya ban mamaki, haushi, da tausai shi ne, kwano ne ajiye a wata shimfida, abinci ne a ciki, kalar wanda ta bawa yaran ta da rana, duk yunwar da take ji, bata iya ci ba, sai da ta aje masa.

Dan mugunta irin ta Isa dauka ya yi, ya fara ci, sai da ya cinye tass ya sude kwanon ya yi fatali da shi ya bar gidan.

Qarfe biyar da rabi, ta rasa ya zata yi, dan haka mayafi ta dauka, ta yafa a saman kan ta, sannan ta saka takalmin ta silifa da ya sude, ya ke qoqarin bulewa.

Jan qofar gidan ta yi, ta nufi dandalin gulmar su Lamishi, duk wanda ya kalle ta da kyau zai tabbata ta sha kuka, amma ya zatai, ba zata iya boye yanayin da take ciki ba, tunda mai rufa mata asirin ya tone shi kowa ya san halin da suke ciki, (ba mai rufa asiri sai Allah).

Ta na zuwa ta Gaishe su, dikkan su amsa wa sukai, cikin zumudin son jin me ya faru, ba wai dan su taimaka mata ba.

Shiru ta yi, can suka ci gaba da hirar su, amma hankalin su na kan ta, gani ta yi lokaci na tafiya, cikin sanyin murya ta ce,

"Uhmmm... Nicce ko akwai wadda ke da wanki cikin ku? Ku kawo na hwara na kuddi, amma za a hada da kuddin wanki da klin da toka(sabulu) "

Kusan a tare suka hada baki suka ce babu, ji ta yi kamar an daki zuciyar ta, da me za su ci abinci dare?

"Ko wani aiki ba ku da shi? Wanda zan yi ku biya Ni?"

Lamishi ce ta ja ta gefe, ta ce,

"Ina da wankau, amma fa na yau ne kawai zan baki, ba wai kullum zaki zanka(dinga) yi min wanki ba"

Kamar ta durqusa a qasa ta gode mata, haka Hansatu ta hau godiya.

Gidan Dan Talo suka koma , Lamishi ta bata wankin, ta bata kudin omo da sabulu, ta biya ta ladan wanki dari uku, godiya ta dinga yi har da kwallar ta.

Ɗaukan wankin ta yi a ka ta yi shago, ta auni wake, dan ya fi arha, kuma in ta dafa za su jima suna shan ruwa in an ci, ta sai man ja ta sai maggi, ta sai omo da sabulu, sanan ta yi gida.

A hanyar ta ta komawa gida, ta ga dandalin su Lamishi suna nan suna hira, kafin ta qarasa ta ji Lamishi na basu labari taimakon da ta mata, ran ta ya baci, amma ba yanda ta iya, wanda ya ajiye ta shi ya ja mata komai, ta na yin kusa da su sukai shiru, kamar ba su ke magana ba.

Gidan ta ta shige, ta ɗora tukunya ta wanke wake ta jiqa tokar murhu kadan ta zuba dan ya dahu da wuri, itacen ba yawa, fatan ta Allah ya sa ya dahu da wuri, ba dan yaran sun kusan dawowa ba da jiqa waken zata fara, ta rage asarar ice.

Bokiti ta dauka ta je ta roqi Yabbuga akan za ta debi ruwa a rijiyar gidan ta, cikin daure fuska ta ce ta je ta diba, godiya ta yi, ta shiga ta dinga jidar ruwa, qirjin ta na matsanancin ciwo, amma ba yanda za ta yi, dole hakuri za ta yi, ta nemawa yaran ta abin da za su ci.

Ta na fitowa daga gidan Yabbuga ta ji ta na fadin.

"Kuuu ban baku labari ba, kun kuwa san an yi baquwa a shiyyar ga tamu? Humm in kun gane(in kun ganta) ta baqa awab-baqar talle (kamar baqar tukunyar miya) , mijin ta ko kyakkyawa, nicce wanga mi yaggani da ya kwaso mace hakan ga awak-kuddi (kamar kudin shi basu cika ba) nai basu cika ba"

Dariya suka sanya da shewa , suka tafa,

"Yabbuga idon duniya, ta wanne bangare gidan yake gobe in su Lamishi sun taso aiki mu tai ganin gida ?"

"Can bayan gidan su Lamishin ne ai, sai kun ga gidan , wayyooo aljannar duniya kenan, gidan da nika mahwalkin samu Allah yabbatar, babu komi, su ci anan, mu ci a can"

"Ke haba na gane gidan, gidan nan me dan banzan kyau, ashe an tare"

"Shi hwa ni ka batu"

Lamishi na qoqarin magana Yabbuga ta jiyo qarar machine din Dan Jumma, da wata iriyar alkafura ta hantsila ta fada gidan ta, dariya suka fara yi, suna fadin ,

"Shegiyar za ta yi tsiya kenan,duk ka ga Yabbuga ta shiga gida bata son Dan Jumma ya gan ta nan, to akwai tsiya"

"Ina yini Dan Jumma ?"

Cikin daure fuska ya amsa ya shige, bai jira jin me za su fada ba, cikin qunar rai, dan ya san dole Yabbuga ma na wajen, sai dai guduwa ta yi da ta ji shi.

Sallama ya rangada, tare da jingine machine din shi, ya cire yar ledar da ke jikin hannun machine din, ya taka zuwa bakin qofar dakin nasu, kwance take abun ta, ta na jin shi ya na sallama ta qi amsawa.

Murmushi ya Yi, dan kuwa ya san halin kayan shi, ajiye ledar ya yi, ya zauna tare da bude kwanon abincin da ke gaban shi, shinkafar ce dai da miya, kullum abincin kenan, in an sauya kuwa to tuwo ne, in ya kawo taliya ko wani kalar abincin sai ta dafe lokaci daya ta raba wa qawaye ta nuna masu itama ana cin dadi gidan ta, ba wai dan ta samu lada ba.

Budewa ya yi ya fara ci bayan ya yi Bismillah,

"Au ka na gani ina hushi ba za ka kula Ni ba ko? Tauu ya yi, ci abincin ka ka qoshi da kyau, ya yi" ta juya baya ta na zumbura baki, ita a dole fushi take.

Dan Jumma bai kula ta ba, sai da ya ci abincin shi sanan ya tattara hankalin shi zuwa gare ta......

A GARIN MU








WRITTEN BY HAERMEEBRAERH










PAGE 5:





"Ina sauraron ki sarauniyar mata, mi am-matsalar ki yau Kuma?"

"Auuu ni ce matsalar ma ko? Tau ya yi"

"Kin dai san ba haka nika nuhi ba ko? Ina so na San damuwar ki, da har zan sallama ki qi amsa min ki na musulma"

"Suhwa nika so"(super na ke so.. Atampa)

"Me ne ne haka nan? (Me ne ne hakan)"

"Atanhwa suhwa nika so," (atampa super nake so)

"Ai ko aiki ya gane ki wallah, ni da nike qaramin ma'aikacin da rabo na da albashi yau wata biyu, haka d'ai sai ni kama sai maki wata super Dan dai ban da hankali ko? To mi za mu ci in kin Sanya super?"

Kuka Yabbuga ta saka, har da Kiran ta shiga uku, tsiyar auren talaka kenan, bata rai Dan Jumma ya yi sosai ya kalle ta,

"Ni ki ke kira da talaka yau Kuma Yabbuga? Lallai mace akwai ta da mance alkhairi, ke manta sanda nike da walwala, ke mance sanda nike da azziqin da kk Shan gatan da ba bu ya ke a cikin tsarar ki? Ke fa ba qaramar yarinya bace, karki manta bara waccan anka kai Kareema d'aki, yanzu haka ciki gare ta, kin kusa kai wa ga jika, shi na ki ke Wagga baqar tabi'a"

"Ni ke baqar d'abi'a ko kai? Yanzu ace yar super ga ba ka iya sai min? Shin ta Ina ka bi ka shigo gidan ga? Ba ka ga su Lamishi a waje bane?ko ba ka ga irin tuwahin da ke jikin su ba ne? Nan Nan Isa da yaggane su sai da ya tsaya ya yabe su, ni matar ka Kuma maqotan shi kallo ban ishe shi ba"

Wani irin zabura Dan Jumma ya yi, tare da kallon Yabbuga a yanayi na tashin hankali.

"Mi na na ki ka ce, Isa ya gane ku bai yaba tuwahin ki ba ,shi ka banna maki rayuwa hakan ga?(Isa ya gan ku be yaba kayan ki ba shi ke bata maki rai?) Ashe dama Isa ki ka aure ba Dan Jumma ba? To ki tai Isa shi sai maki super Yabbuga na Yi masallaci"

"Walle ba ka Isa ka juyan magana ka tafi ba, ka San ba haka nika nuhi ba, super ko sai ka siye ta gidan ga, kahin ka ga hwari na,"

"Irin wanga halin da ki ke shi Kareema ta koya, daga yin aure mijin ta ya kawo qara ya hi sau bakwai, kwanaki ba koro ta ya yi ba da ya gaji da bani bani da sai min? Da girman ki amma ki na wanga mummunan hali, ba lehin ki na ba, lehi na na, da a baya niyyi zamanin sai maki duk wani abu da aka yayi, maimakon yanzu da Banda shi ki hakura ki San na kyautata maki a baya, shi na kk hango na sama da ke, se ki fada min, da su Lamishin Basu aiki gidan Gwauna Ina na zasu samu kwancen tsohuwar super ma balle sabuwa? Sannan da ki ke gasa da Lamishi, ai Lamishi ta ciri tuta tunda ta iya zama da kishiya, me ya sa baki gasa da ita ta nan ba? Gashi can su na zaune lahiya kamar Yaya da qauna"

"Babbar batasin Nan, ni ka ke kalla ka yi min batun kishiya Dan Jumma? Ashe ka daina so na? Ka San ya akai Suka hwara zaman lahiyar ne ? Ai na dole ne, tunda Mai Buruji ta hwara rashin nasihwa(rashin mutunci) , ta ga bata diban komai jikin Lamishi, shi na aka zauna lahiya, Kuma indai batun suhwa ne Dan Jumma yassa ka min batun kishiya riqe suhwar ka, banni so, amma ka sani kai da ka samu kwaciyar hankali gidan ga sai na huce haushi na"

"Ga leda nan na shigo maki da ita, huce haushin ki saman ta"

Alwala ya fita waje ya yi, ya wuce masallaci, qofar gidan ba kowa dik su Lamishi sun tafi,bayan sun gama jin drama da akai a gidan, ko a gida ma labarin da sukai ta yi kenan.

Hansatu kuwa bayan ta gama dafa wake,ta soya man ba ko albasa, ta zuba ita da yaran, ta aje ma Isa na shi, da ruwan sha, a shimfidar shi da yake zama, a tare Suka ci da yaran ta, suka qoshi, kowa ya Sha ruwa, cikin hamdala, sai annashuwa da murna suke, ga wani Nan ta Dan rage da safe ta zafafa (dumama) musu su ci.

Ta na idar da sallah ta hau wankin Lamishi, bata tashi ba sai da ta gama shi tsaf.

Ta shanya, lokaci ne na iska, bata kwanta ba sai da ta ninke su ninkin guga ta daure ta ajiye, qarfe Sha d'aya saura, hamma ta ke ta dokawa, ta gaji matuqa, ga shi har wannn lokacin qirjin ta bai daina ciwo ba, ya dai rage ne kawai.

Dan kishingid'a ta yi a tsakiyar yaran ta da ke kwance a parlour , Nan da Nan kuwa bacci Mai dadi ya share ta.

Bata sani ba, shin ta jima ta na baccin ko kuwa? Kawai dai taji an take qafar ta ne, har sau biyu, tsabar mugunta, ba zai durqusa ya tashe ta ba, sai dai ya take qafar ta.

Da sauri ta janye qafar tare da miqewa ta na masa sannu da zuwa.

Amsawa ya yi ciki ciki, ya qaqalo murmushin dole, Wanda ya Sanya gaban Hansatu faduwa da qarfi, Dan ta San ma'anar shi, taba wuyan ta tayi, ta ji shi zafi rau, ta San ba komai ya ja ba sai aikin da ta Sha, ga ciwon qirji na damun ta, gashi ta yi aiki cikin iskar da ke kadawa me sanyi.

Kwallar ta ta mayar, ta raka shi waje tare da zuba masa ruwa ya wanke hannu, kamar wani qaramin yaro, abinci ya ci, ya qoshi, tare da zabga wata gyatsa me Dan banzan wari.

Kauda kai Hansatu ta Yi, Isa kuwa ko a jikin shi, ya na tashi ta tattare komai, sannan ta je ta wanke bakin ta da ruwa da dan gishiri, ta bi shi daki, (ita ta iya ta wanke bakin ta, saboda Kar a ji warin shi, Amma shi ya wuni zubur da baki bawanki, sannan ya ci abinci, ko kurkurewa bai ba, ya tafi ya kwanta a haka)

Ga Isa da Dan banzan son yin kiss, ga baki na wari, Kuma Hansatu bata Isa ta nuna hakan ba, duk wani qoqarin ta na Sanya shi ya dinga wanke bakin,abun ya gagari tunanin baya ta fara, ta gwada aje masa hodar wanke baki da suke amfani da shi, ya yi fatali da ita, qarshe sai da yajibge ta, ya ce ta raina shi, shi zata kalla ta ce bakin shi na wari?

Ta gwada Yi masa magana direct, ya jibge ta, Kuma ya mata kiss ta qarfi, ya ce in mutuwa zatai sai dai ta mutu, Amma yanzu ya fara.

Gani ta Yi tunani ba zai kai ta ba, ya na iya fizgar ta da qarfi, da kan ta ta cire kayan ta ta kwanta a saman qaton gadon nasu, Wanda ya yi matuqar bani mamaki, ace kamar Hansatu masu ci da kyar ta na da irin wanna gadon.

Addu'a kawai take a ran ta har ya gama abinda zai ya tashi, fatan ta Allah ya raba ta da daukan wani cikin, ya Kuma bashi ikon dinga wanke bakin shi, tunda ta Yi dik wani qoqari ya qi farawa, Allah ne kawai zai sauya masa ra'ayi ya fara.

Cikin daren Isa na barci,jikin Hansatu ya dau zafi Mai tsanani, ga wani irin sanyi da take ji, bargon ta ta ja ta lullube jikin ta da kyau, Amma dik da haka sanyi take ji, Isa bai ma San tana Yi ba, Kuma in ta tashe shi ta San sauran, tunda naquda ma ya yi fada da ta tashe shi ballantana zazzabi.

Haka ta kwana da mummunan zazzabi, da zafin jikin ta ya dame shi ma sauka ya yi daga gadon, ya sa pillow a qasa ya kwanta, ya na ta surutai qasa qasa.

Hawayen baqin ciki ne suke kwaranya a idanun ta, har aka Kira asuba,ta na Nan kwance, takasa tashi.

Ba ta samu damar tashi ba kuwa sai da safiya ta fara Yi, da kyar ta iya hura wuta ta sa musu ruwan wanka, Amina da Bilkisu ne Suka shiga gidan Yabbuga duka samo ruwa, sai masifa ta ke masu, ta na fadin wata Rana ta ga alamar sai sun qafar mata da rijiya.

Ta na gama wanka ta Yi sallah, Isa ya fita tun tini, ya na can wajen Mai soya masa, ya ce a bashi ta dari biyu abin shi.

Kayan da ta daure jiya, ta kunce ta raba, ta Dora ma yaran ta ce,

"Maza ku kai wa mama Lamishi, ki ce mata Ina godiya,in ta na da ra'ayi ta na iya kawon wani wankin Nan gaba, ku Yi sauri kafin su fita, sun kusan tahiya gidan Gwauna , maza"

Da sauri kuwa Suka je, suka isar da saqon Mahaifiyar su, aiko wanki ya yi wa Lamishi kyau, ta ce zata kawo wani in ya taru,Mai Buruji ma ta ce za ta kai nata.

A hanyar su ta komawa ne Bilkisu ta ce,

"Amina mu je ta wajen Mai masa, na San baba na can,"

"Kin San dik ya kammana muna leqen shi Kashi zai liqa Muna ga banza ko?"

"Dun Allah mu tai, ni ko yawu na hadiya, mu dawo"

Da sauri ta kama hannun yayar ta da ke son guduwa gida, suka nufi rumfar me Masa.

Isa akwai jarabar wanke hannu, an zuba masa ya ja gefe shi kad'ai ya aje masar shi, ya tafi wanke hannu.

Bilkisu kuwa lallabawa ta Yi ta dauke kwanon Masa, ta ja hannun Amina Suka gudu gida.

Su na zuwa suka miqawa Maman su, Suka ce

"Gashi baba na yacce a kawo maki"

Cikin matsanancin jin dadi Hansatu ta amsa, ta sa yara a gaba Suka fara dukan waina da ci, su na ci ta na murmushin jin dadi.

A can rumfar me Masa, wasu matasa da Suka San isan da yaran shi,sun ga sanda Suka dauka, Dan haka dariya kawai Suka dinga Yi.

Isa na zuwa bega Masa ba, ya hau matasa da duka, ya na fadin sai sun biya shi masar shi, da kyar aka raba fadan, Nan suke sanar da Isa su ba su bane, diyoyin shi ne mata Suka dauke.

Wani irin ashar ya Danna, sannan ya Sanya takalmin shi guda da ya fadi wajen dambe ya nufi gida.........

A GARIN MU







WRITTEN BY HAERMEEBRAERH








PAGE 6:





Da qafar shi ya daki qofar gidan, gaba dayan su zabura Suka Yi a tsorace, Hansatu ce ta Dan Yi murmushi da ta ga shi ne, godiya ta ke da niyyar Yi ta ji ya hada yatsun shi biyar da fuskar ta.

A kidime ta kalle shi, domin sanin laifin da ta aikata, Amina da Bilkisu ne suka shiga tsakanin su, ya ja hannun Amina ya kife ta da mari, zai qara mata Bilkisu ta riqe shi ta na kuka,

"Baba ka bar dukan su, ni ta nid-d'akko, ni zaka daka, Kuma ni nicce Kai ka bayar mu zo gida mu ci"

Wurga ta ya yi gefe, ta fadi ta dauje guiwar hannu, kuka ta Sanya Mai qarfi, tuni Hansatu ta durqusa ta na duba hannun nata, cikin sanyin murya da mamakin halin mijin nata ta ce

"Yanzu akan wainar jikka biyu ka fiddawa diyar ka jini? Ka daki matar ka ? Wadda ta sadaukar da millions saboda Kai, anya Isa Kai ne Wanda na fada son shi shekaru Sha uku da Suka wuce kuwa? Anya Isa Kai ne Wanda ka min alqawurran kyautatawa kala kala? Haqqin ka ne fa ciyar da mu, Amma ba ka Yi, da na san ba Kai ka Basu ba dakkowa suka Yi,da bamu cin ta wallah, ka Yi hankuri inshaa Allahu ba mu koma tambayar ka kuddin abinci, ko Kuma mu dau abun ka, tashi Mu je na wanke maki, sannu"

Kalaman ta Basu ratsa fatar shi ba ma, balle tsokar jikin shi, hasalima wata fassarar ya Yi ta daban.

"Auu abun gori Kuma ya koma Hansatu? To da ni da ke wa ya fara furta ya na son wani? Sannan wa ye ya kafe ya guji kowa na shi saboda masoyi? Kar ki dakko maganar baya akan haramun din da ki ka ci ke da yaran ki, duk Wanda ya sake min wannan gangacin zai ga ganganci"

Kamar ta sanar da shi ba su ci haram ba, sai ta kama bakin ta, saboda ta San dukan banza za ta sha, har ya shiga daki ba Wanda ya sake motsawa a cikin su, sai sautin shassheqar kuka kawai ke tashi.

Ya na shiga daki ya laluba ko Ina bai samu ko sisi ba, fitowa ya Yi sannan ya ce,

"Ba kuci banza ba, ki tabbata kin nemo min

Please Login or Register in order to submit comment