Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta na taba shi, shi ya na guduwa, shi ne yanzu zai nuna mata ya iya taba jikin mutum yi ne kawai ba ya yi,daukan tarkacen ta tayi, ta shige gida cike da nishadi, Allah Allah take su hadu da Sultan ta bashi labari, ta na sanya qafar ta, a cikin gidan, ta ji an ce,

"Kee Sulatana, zo nan!"

Cikin tsananin firgita da tsoro ta taka zuwa babban parlour'n na su...........

*A yi hakuri da wanga sai zuwa anjima ko gobe inshaa Allahu zan ci gaba, thank u mutanen Ogaaa😂*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 38:


Mubaraka na matuqar jin dadin zama da su Taheer da iyalan shi,domin duk wani abu da take so, ko suka kula ta na da buqata da wuri za su yi mata shi.

Da kyar Fateema ta yarda ta ke taya ta girki,shi ma dan Mubaraka ta dage ne, kuma cikin ikon Allah, sai ya zamana su na samun qaruwa da juna, abinda dayan su bai iya ba, sai daya ya koya ma daya.

Yaran su kuwa kamar qannen ta haka ta dauke su, ita ke musu wanka, ta shirya su, su je islamiyya su dawo tare.

Ranar Monday mai zuwa za ta fara zuwa Makarantar boko, a tunanin Lawwali makarantar Army Day ne kawai za ta samar wa Mubaraka tsaro, dan haka can ya saka ta, ya sa Taheer ya nemar mata driver da zai dinga kai ta, saboda shi bashi da lokacin kai ta, ya fara zuwa kasuwa, ya na saida shaddodi.

Ranar farko da Mubaraka ta fara zuwa, ta samu masu son qawance da ita kala kala, musamman dan ganin a irin motar da aka kawo ta, amma dake tin kafin Lawwali ya bata gargadin yin qawaye barkatai, ita ba me son tarkacen qawaye bace.

Dan haka gaisuwa ke hada ta da kowa, ta raba ta da kowa lafiya.

Tun ranar da aka kai ta makaranta wasu sojoji wanda suka addabi d'alibai mata, suke kula da zuwan ta, da tafiyar ta.

Yanayin kamun kan ta, ya ja ra'ayin su, su na son sai sun lalata mata rayuwa, (wannan duniya yanda ta lalace Allah ne kawai zai gyara mana ita, in ka yi shigar banza, maza na kallon ka, su na dakon ka, in ka yi ta kirkin ma, wasu so suke su yaga maka rigar mutunci)

Lokuta da dama ta kan gan su, in ta je shago siyan wani abun, shagon na dan nesa da asalin cikin makaranta.

Watarana ta zo makaranta sai ta kula an sace pen din ta, gashi an basu assignment ta na son ta yi, in ta isa gida, dan haka tsayawa ta yi a shagon dan siyan pen.

Ta na tsaye ta na jiran a sallami wasu,sannan a bata abinda take buqata, kurtun sojan nan ne dai da ya sa mata ido shi da abokan shi ya zo shiga wajen, duk warin hayaqin sigari da wiwi ke tashi a jikin shi, ga hanya can da za ta ishe shi ya shiga shagon amma sai da ya rabi jikin Mubaraka har ya na gogar qirjin ta.

Tura shi baya tayi ta ce,

" Allah ya saka min azzalumi "

Kurawa sunan dake jikin rigar shi ido ta yi, ta kasa gane sunan nashi Saboda sunan arna ne da shi, kuma da yare aka rubuta,duk qoqarin ta na ta karanta sunan ta kasa.

Zuwa ya yi ya daddafe ko ina na jikin qofar, ya sanya ta a tsakiya kenan, da kyar take shaqar numfashi, hannun shi ya sa ya shaqe mata wuya, duk wajen ana tsoron shi, dan ya saba zuwa, in ya ga mata masu kyau, ya yi ta bibiyar su.

"Hey, what are you doing, pls let me go, stop touching me, I will tell my brother if I go home"

(Kai me ka ke yi ? Dan Allah barni na tafi, bari tab'a ni,se na fad'a wa yayana idan na ne gida )

Kuka ta fashe da shi, duk jikin ta na rawa ko ta ina, da kyar mutanen wajen suka bashi hakuri ya rabu da ita ta fita daga wajan a guje, motar ta ta nufa ta ga drivern da Taheer ya daukar mata baya ciki, ashe abokan sojan nan ne suka kira shi, suka tsare shi, sun tabbatar dole zata je inda motar take, daga nan za su kamata su tafi da ita, sai sun gama abinda suka so da ita su dawo da ita.

Haka kawai jikin ta ya bata ta gudu, tunda bata hango driver a motar ba, dan acaba ta gani, irin masu fitar da mutum wajen gate dinnan, ta haye, ta ce ya Kaita gida ko nawa ne zata bashi.

Ai kuwa ya na jin haka ya ce ta hau, ta haye ta rufe fuskar ta dan kar a gane ta, gudu suke zubawa, har suka kai gate, sun fita kenan, ta hango qaramar motar da sojojin uku suke ciki, dira qasa tayi daga machine din, ta buya a gefen wasu ciyayi da ke bakin kwata, duk abinda ta ke su na ganin ta, gani ta yi sun tunkaro ta, bayan sun rufe motar su, cikin Barack ta shiga da mugun gudu, duk ta daddauje jikin ta, ya na mata zafi,sojojin da ke bakin gate ta dinga roqa kar su bari su tafi da ita, ta na ta rusar kuka, bata fatan sake riskar abinda ya faru da ita a baya.

Su na ganin haka suka koma, domin ana ta complain akan su, kar akai rahoton su.

Cikin sa'a kuwa ta tarar da wani babban soja na qoqarin shiga motar shi, gefen shi wani karamin soja ke bude masa mota, wajen shi Mubaraka ta kwasa a guje, ta masa bayanin komai, akai akai ta fadi sunan shi ta kasa, sai ta rubuta a qasa, Sojan na gani, ya gane wa take nufi, duk da bata rubuta daidai ba.

A nan take ya bada umarni a je a nemo driver din ta, a cikin daji aka same shi an daure shi, ya sha duka ,har gida sojan ya raka ta shima a tashi motar.

Godiya ta dinga mishi, ya ce aikin shi ne, ba sai ta yi godiya ba, bayan ya koma Barack ya sa aka nemo wadannan sojojin, aka musu hukunci daidai da abinda suka aikata, su kuwa cikin zuciyar su sun qudirta duk inda suka hadu da Mubaraka sai sun dau fansar abinda aka musu.

Mubaraka kuwa Taheer na dawowa daga sabon wajen sana'ar da Oga Lawwali ya bude masa a kasuwa, wato shagon saida shaddodi na mata da maza, ta sanar da shi komai, ya kuma yi mata alqawarin daga ranar ta bar zuwa makarantar barikin sojoji, tunda ba diyar soja take ba.

Da kan shi ya sauya mata makarantar private da ba ta da nisa da su, a kai ta a maida ta hankali kwance.

Ya gargade ta da kar ta sake Lawwali ya ji wannan maganar, in ya ce me ya sa aka sauya mata makaranta su ce ba a karatu a can shi ya sa.

Dariya ta yi, ta daga kai, ko dama da ta ce za ta gayawa yayan ta shi take nufi ba Lawwali ba.

************************

Tun saukar shi a jirgi ya ke gwada layin No 1 bai dauka ba, Gashi dai ta na ta ringing amma ba a daga ba, lambar No 4 kuwa ma sam ba ta tafiya, damuwa ce qarara a fuskar shi, tsoron shi kar dai yaran sun hade masa kai da Ogan su?

Da sanyin safiyar masu tsaron lafiyar shi ne tsaye a bakin motocin da suka zo da su dan daukan shi, bude masa motar da zai shiga aka yi ya shige ya zauna, sake gwada No yake amma gashi ta na ringing ba a dauka.

Cikin zuciyar shi ya ke tunani,

'Na manta yanzu safiya ne, wataqila ko tashi ba su yi ba'

Maida wayar shi ya yi, ya ajiye, har suka isa gida bai dena jin yanayin da yake ji ba, na rashin dadi a zuciyar shi.

Hajiya Ikee da ta san da dawowar mijin ta, ta sha gayu, har ta gaji, ta bawa masu aiki umarnin hada abin karin kumallo masu rai da motsi, na musamman.

Kwararru kuma hadaddun masu girkin tuni suka fara bade gidan da qamshi, Sultana na zaune a saman sallaya, bayan idar da Sallah da azkar, ta fara karan ta qur'ani, ta na jin qamshi na tashi kala kala, ta tabbatar Daddyn su na tafe, murmushi ta yi, tare da qara qaimi wajen karatun ta, dan ta na so ta haɗa da addu'ar samun nasara daga wajen Allah.

Da misalin shida da hamsin da bakwai 6:57am Gwamna Halliru ne a zaune bakin katafaren gadon su, ya zubawa Hajiya Ikee ido, ta na ta rattaba masa bayanai, akan abubuwan da ke ta faruwa a bayan shi,(rashin iya tarbar miji, daga dawowar shi, ba a bashi ko da abin da zai sha ba, balle a bari ya huce gajiya an fara bashi munanan labarai)

Gwamna Halliru shiru ya yi ya na sauraron ta,

".....shi ya sa na fada maka, ka kori Yaron nan, ka qi, gani ka ke in ba shi Sultana ba zata iya takawa ko da gate bane ba tare da an halaka ta ba"

"Kwarai da gaske, baki da masaniyar waye shi, har yanzu cikin jahilcin sanin waye shi kk, shi ya sa ki ke wannan surutan,"

Miqewa ya yi ya shiga wanka, ko da ya fito be ga Hajiya Ikee ba, bai wani damu ba, dama ita ba mace bace mai taya mijin ta shirya wa, sai da ya gama shiri tsaf, ya ga wayar shi na ringing, dauka ya yi, ya na tsaki,

"Ko mi zata hwadi, da ba zata iya dawowa daki ba"

Amsawa ya yi, ya kara ta a kunnen shi,

"Ka sakko parlour 'n baqi yanzun nan"

Shi ne kawai abinda ta fadi, cikin rawar murya, aka kashe wayar.

Cikin sauri ya dauki wayoyin shi ya fita, sai da ya wuce parlour biyu kafin ya isa inda take neman shi, ya na bude qofar ya yi turus ya qame,

"Barka da dawowa Excellency ,Bismillah shigo, kai da gidan ka?"

Wani yawu Gwamna Halliru ya hadiya makwat, Allah yake ta roqo ya sa ba wannan bace ranar da tun farko No 1 ya guje musu.

Lawwali ne zaune ya harde kafar shi daya bisan daya, hannun shi daya riqe da bindiga, ya aje wayoyin shi da na No 1 a gefen shi, sai jujjuya bindigar yake, Hajiya Ikee na gurfane kamar me neman gafara,

"Hajiya wai mi na na hakan ga ki ka yi? Na ce miki ki hau kujera, yanzu in Sultana tag-gane ki duqe gaba na ai sai ta hwasa aure na, tunda kin ka shigo ni ke baki baki ki hau kujera, ko sai na taimaka Maki ne"

Gyara bindigar shi ya yi, ya bata rai, da sauri ta miqe ta zauna a kujerar dake daf da wadda gwamna Halliru ya zauna, jikin ta sai rawa yake, a duniya Hajiya Ikee na tsoron mutuwa .

"Lawwali mi na na ka ka yi haka? A gida na za ka fiddo bindiga, ga iyali na? Me ke damun ka?"

"Ni ka ke tambaya me ke damu na? Ashe baka bawa matar ka labari na ba? Ashe baka hwadi mata ko ni wane ne ba? Take ta min wasan yara"

Hajiya Ikee ce ta matsa kusa da Gwamna Halliru, ta na magana kamar me rad'a, kunnuwan Lawwali kuwa a bude suke tsaf dan sauraron ta,

"Ka danna kiran Yaron nan na ka shi taho, shi kawo mana dauki, wajen wanga qaramin dan iskan"

A hanzarce Gwamna ya kalle ta, ya maida kan shi wajen Lawwali, Lawwali ma cikin sauri ya dauke kan shi, kamar be ji me suke fada ba, cikin rad'a Gwamna ya ce ma Hajiya Ikee.

"Lawwali shi na yaro na da ni ka hwada maki,"

Wata 'yar siririyar qara Hajiya Ikee ta saki, ta damqe bakin ta da dika hannayen ta biyu, ta na zaro idanu, domin duk wani labarin ta'addanci da rashin azziqin lawwali ba wanda ba ya riskar ta, wani irin tsoro ne ya sake damqar ta da qarfin gaske,

"Hajiya ni kin ka aikawa 'yan iska su kashe ko? Ni kin ka hana kwana, kin ka b'aci uwa ta da qauna ta gaba garen, Hajiya ke ko san irin laihukkan da kin ka aikata min?"

Da sauri Hajiya ta kada kai, alamar ah ah.

Gwamna Halliru dai ya yi shiru, domin ko ya kirawo jami'an tsaro a kama Lawwali kamar ya yi ihu ne ya yi kirari ya dabawa kan shi wuqa a bainar nasi, in securities ne na gidan kusan rabin su Yaran Lawwali ne, shi ya horar da su, ga dai su nan yanzu sai yanda Oga yace.

Lawwali Wayar shi ya dauka, ya shiga videos ya kunna video Na farko da ya fara yi wa No 1 azaba, ya kunna ya miqa wa Gwamna,

"Ka bi ka ishan da waya tun hwarar sahiya, shi na nit-taho da kai na dan kawo maka wayar da mai wayar dan ka gan shi, gashi ku gani tare, dan Hajiya ta fi gane shin wane ne Lawwali, ya yake maida mutane in an ka ci amana tai"

Sanda Hajiya ta ga yanda ya ke zubawa No 1 ruwan batir a baya, fatar na qonewa kuka Hajiya Ikee ta fashe da shi,kan ta ta hango ana mata wanan izaya, ya zata yi?

Duk wata wahala No 1 ya sha ya gode Allah,kuma Gwamna da Hajiyar sun gani.

"Ina yarinyar take?"

Cikin matsancin fushi Lawwali ya miqe ya daki glass table din dake center din su, da bakin bindiga ya tarwatse a wajen, qara mai qarfi Hajiya Ikee ta sanya, ta qanqame Gwamna,

"Gwamna Halliru ina mai tabbatar maka da cewa ka tafka babban kure da ka ɗauke min qauna, ka san a wane hali wancan qaramin dan iskan ya jefa ta? Ka san me ya mata! Ko akwai sa hannun ka a lalata ma qauna ta rayuwa? Akwai sa hannun ka ne!"

Cikin matsanancin tsawa yake maganar shi,wanda ta sanya Hajiya Ikee gama rushewa da matsanancin kuka, wannan shi ake kira da madaki kusa maceci nesan, da ta san wannan shi ne yaron da ake bata labari da bata so ma yi masa iskanci ba, labarin ta'adi da ta'asar shi ba wanda bata ji, ido da ido ne basu taba haduwa ba, da kuma sunan shi, ta san dai kowa Oga yake ce masa amma bata san shi ne Lawwali ba.

Sultana da ke shiryawa ce ta ji qarar fashewar abu da qarfi, dan guntun tsaki ta ja, sannan tace,

"Masu girkin nan basu rabo da hwashe kwanna, (kwanuka) aiki suke kamar su na aikin hwashe dutsi"

Mai ta hau shafawa ta na tunanin kayan da za ta sanya dan burge masoyin ta, sannan ta na tunanin shin ta masa magana akan abinda ya mata ne jiya? Ko ta bari? Dan gaskiya ita bata son irin soyayyar nan ta zamani a yi ta kiss da sauran irin romace din nan.

A can parlour kuwa Lawwali ya titsiye Gwamna akan sai ya sanar da shi dalilin da ya sa ya sace masa qaunar shi,

"Lawwali baka san me ya hwaru ba, ranar da kun ka kawo mani yaro nan...wani almajiri, har niyyi wani aiki, to qaunar ka ta na gidan nan, ta gane ni, shi na dalilin da ya sa nic-ce a ɗauke ta, kuma ban ce a mata komai mara kyau ba, hasali ma har gida da kuddin da za a zanka sai mata abubuwan more rayuwa sai da na aika wa yaran ka, ban dauke ta da nuhin a cutar da ita ba"

"Me ya sa ba ka hwadi min abinda ke hwaruwa ba? Qauna ta ba mai Surutu bace,ta san aikin duk da nake maka, bana boye mata komi, bata hwasa yi min addu'a ita ko, akan Allah ya shirye ni, ko ta sani ba matsala bane, dan kuwa ba ta hwadi ma kowa, ta san komai, kahin ta gan ka,dan haka yanzu dai ka san ba a yi min ban rama ba ko?"

"Kai wa Allah Lawwali maganar ga ta wuce,"

"Ta wuce? Ashe ma ni ba dan halak bane, shin da na hwadi ma an lalata rayuwar qauna ta ka tambaya ka ji ya take? Saboda bata dame ka ba, kamar yanda lalacewar rayuwa ta bata dame ka ba,to ka sani, abubuwa daya zuwa biyu za ka min dole, in ba ka min ba,.....in baka min ba....ka ga wanan? Sai ya shiga duniya"

Hotuna ne da video da aka dauke su a tare, suna aikata mugayen ayyuka, wanda Gwamna ya yi matuqar mamakin yaushe aka dauka, a take anan, ya qara sallama wa lamarin Lawwali, abun nashi babba ne.

"Yan zu mi ka ka so? Kuddi, kadarori? Ko muqami a gwamnati, dan Allah kar ka tona muna asiri,"

"Kar in tona maka asiri dai, dan kuwa tunda kagga an doka hotuna da video din ga da niyya ka san ina da plans, ba haka nan nike zaune ba, and ko da an kama ni ka sani bani da asarar komi,"

"Lawwali ka sanar da shi abinda ka ka bida, ko mi ne ne zai maka ka ruhwa muna asiri"

"Ba kullum ikirarin in Gwauna yaddawo zai sa yaron shi ya kashe ka, sai na ga bayan ka...tau yanzu ta qare, ni ba na buqatar komi wajen ku a yanzu, amma ban muku alqawarin ba zan nemi wani abu ba a gaba, a yanzu buqatar diyar ku nake baku umarnin ku karba, in ba haka ba....."

Miqe wa ya yi, ya na bin su da wani irin mummunan kallon da ya sanya Hajiya Ikee matse hannun Gwamna tare da toshe bakin ta da hannu daya dan kare kukan da ke son ya fito.

Bai ce komai ba bayan kallon daya baza musu ya bi ta hanyar da baqi ke shiga parlour'n ya bar wajen, kafin ya isa bakin motar Sultana ya maida bindigar shi bayan wando, ya mayar da wayoyin shi wandon shi, wayar No 1 kuma a gaban aljihun shi.

Hajiya Ikee kuwa ya na fita ta hau yi wa Gwamna masifa,

"Ashe annubar da ka dakko muna kenan? Yanzu ya zamu yi? Ya zame mana qadangaren bakin tulu, duk ta inda munka yi ba mafita, ka san me yake nufi da biyawa diyar mu buqatar ta? A aura wa Sultana shi fa, ni kuwa ba zan taba bari wannan al'amarin ya hwaru ba, ko zan rasa raina kuwa"..........

*Oga ko zaka dawo ne? Dan bana jin Hajiya ta ji Warning dinnan*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGGE 39:

Tinda ta duba ko ina bata ga iyayen nata ba, kawai se ta karya a gaggauce ta fita, da qudirin in ta dawo za su tattauna akan maganar Auwal din ta.

Tsaye ta gan shi, ya na yarfe hannun shi, jini ta ga ya na zuba, cike da tashin hankali ta kira sunan shi, su na hada ido ya sakar mata murmushin da ke sake nannade zuciyar ta cikin son shi, kashe mata ido daya ya yi, sanan ya ce,

"Ran ki shi dade kin gama mu tai?"

"Me ya sami hannun ka? Ka na zubar da jini! Mu je ciki na sa maka magani,"

Bai mata musu ba, ta kama hannun shi zuwa main parlour din su, su na shiga ta tarar da Sultan na bude qofar dakin shi,ya na fito wa, da alama bai jima da tashi daga bacci ba, shi ma da jinin da ke zuba a hannun Auwal ya yi arba, da hanzari ya qarasa isa gaban su,

"Subhanallah me ya faru haka?"

Hajiya Ikee da Gwamna ne ke tafe, kowannen su zuciya ba dadi, ganin me ke faruwa ne ya sanya su zuwa wajen suma,Hajiya ta tuna ya akai ya samu wannan raunin, sanda ya fasa masu table din su mai kyau da tsada ne ya samu ciwon, kauda kai ta yi ta bata rai, dan ba ta so ma ta kalli jinin da ke diga a saman tsadadden carpet din ta.

"Sultana tai ki dakko fist aid box,yi sauri"

"To Yah Sultan"

Duk ta kidime ta rude, a wajen Lawwali wannan is just a scratch ,amma su a wajen su babban ciwo ne, sai da Sultan ya gama gyara ma Lawwali ciwon sannan Sultana ta kalle shi, cikin kulawa ta ce,

"Gaskiya yau, ba inda zaka, ka zubar da jini da yawa, ka zauna, a samu wasu guards din su kai ni"

"Ba za a yi haka ba Ran ki shi dade, ba damuwa ai an saka min magani, zan iya kai ki"

"Ni dai gaskiya ahhh ahhh, Daddy ka ce wani abu manaa"

Gwamna Halliru ba abinda ya ke da ya wuce kallon ikon Allah ,yaushe Lawwali ya ci shi da yaqi haka?'yar shi har bata iya boye soyayyar shi a gaban su, murmushin gefen baki Lawwali ya yi, ya kafe Gwamna da idanun shi da ke dauke da kallo irin na tsokana.

"Daddyyyy ka mishi magana pls, ya ji ciwo a hannun shi fa"

"Amm...uhmmm..Lawwali ina ga ka d'ai zauna, zan samu masu kai ta kawai"

"Ran ka shi dade Sultana ba uwar daki na bace kadai ta nada matsayi mai girman da ba zan iya barin wani abu ya same ta ba, kasan yanzu yanda duniya talalace, kana kauda ido sai ka nemi naka ka rasa,"

Cikin wani irin salo da kwarewa ya yi maganar, Hajiya Ikee da Gwamna sun gane karatun, karr kuma tarr a zuqatan su.

"Sultana kar ki damu, kuje kawai, wa ya fada maki, dan wanga ciwo na damun mazaje? Ai zaman gida se mata"

Har sun kama hanya za su fita Sultana ta koma ciki,cike da dan jin nauyi ta tsaya gaban Daddyn su, tare da kama hannun shi ta ce,

"Daddy, tunda Allah ya dawo da kai lafiya, ga ka ga Hajiya, Yah Sultan da Auwal din kan shi, ka jima ka na min magana akan rashin kula maza da nake, ka na cewa a haka zan yi aure watarana? Tau Daddy yau ina so na sanar da ku cewa na zabi Auwal ya zama abokin rayuwa ta, dan Allah Daddy kar ka ce ah ah, shi nake so, shi nake fatan ya zama abokin rayuwa ta, ba zan iya rayuwa da kowa a matsayin miji ba bayan shi,dan Allah Daddy"

Hajiya Ikee ce ta bude baki za ta yi magana, suka hada ido da Lawwali da ya sunkuyar da kan shi, amma idanun shi na d'age ya na kallon kowa,kallon da ya mata ya yi matuqar shiga kowace kafa ta jikin ta, nan take ta tuna maganar da Gwamna Halliru ya mata a can parlour'n baqi.

'Ke hwaa baki da hankali, sai ki dinga abu babu lisahi,halan baki ga mi ya nuna mana ba, ido da ido kin gan ni sanda na ke duba makaman da za a kai musu daji,tare da ni da su muna hira cikin nishadi, ido da ido kin ganni ina yanka jarirrai har guda ukku (jarirai) kin ga yanda ya ke kisan mutane kamar ya samu kiyashi,amma kin fi so wai har sai asirin mu ya tonu sannan ki nutsu, d'iyar da ki ke taqama taki ce, za ki aurawa shugaban qasa ta san me muke aikatawa sai ta tsane mu,Za ki iya jure tsanar da 'ya' yanmu za su yi mana? In ki na iyawa ni ban iyawa, Sultana ruhi na ce, ba zan taba bari wani abu ya same ta ba, dan su nake duk wanga abu da kika gani, dan na wadata su da dukiya da jin dadin duniya nake abubuwan ga, dan haka in ki ka kuskura ki ka kawo abinda Yaron nan zai bata min suna a duniya, sai na halaka ki da hannu na wallah'

Ihun murnar Sultana ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula, Sultana ce ta saki daddyn ta,ta tafi da gudu kamar wata qaramar yarinya, ta fada jikin Hajiya Ikee, ta ce,

"Hajiya Daddy ya amince, zai aura min Auwal, Hajiya ba ki ce komai ba, kin amince da zabi na?"

Wani abu ne mai daci da maqaqi ya tokare wuyan Hajiya Ikee, har wani d'aci-d'aci take ji a wuyan ta, idanun ta sun qanqance, saboda baqin cikin da ke cin zuciyar ta, amma ba halin bayyanawa, cikin Muryar da kamar shaqe mata wuya akai, ta ce,

"Na amince, Allah ya sanya albarka"

Rungume ta Sultana ta yi, ta na farin ciki sosai, ranta fari tass, kamar madarar shanu, Sultan ma sai wangale baki yake, ya na taya qanwar shi murna.

Dan gyara tsayuwar shi ya yi, ya wani turo qirji gaba, shi a dole ga babban yaya, gyaran murya ya yi, sannan ya ce

"Ban gane ana ta neman izini ba , ba wanda ya nemi nawa?"

Lawwali ne ya duqa cikin wasa,

Please Login or Register in order to submit comment