Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin dakin ta, zan shiga in dauke ta, domin babu abinda ba zan iya ba akan cikar buri na, kamar yanda kai ma ba abinda baka yi dan cikar burin ka"

"Lawwali d'iya ta ka ke son a yi wa irin wanga aure? Sati guda kamar d'iyar tallaka?"

Da sauri Hajiya Ikee ta ce,

"Kar ka ja mana magana, ka bari kawai a yi nan da sati guda din, kaga Lawwali, ka turo magabatan ka kawai a sa rana a yi komi a gama lahiya"

Murmushi mai kyau Lawwali ya saki, ya dauke qafar shi da ya dora a saman kujerar su, ya duqa gaban Hajiya, Ita kuwa ta yi baya da azama, dan ba ta so ma ya rab'e ta ko kusa, rabon da a dake ta ba zata iya tunawa ba, amma gata da girman ta, ta sha shaqa .

"Yauwa suruka ta, da kyau,bari na tai gida na sanar da iyaye na, gobe za su zo, a gobe nake so a saka rana, duk wanda ya lalata min shiri, zan lalata masa rayuwa, wanan alqawari na ne"

D'aga kai kawai Hajiya take, Gwamna kuwa kallon Lawwali kawai yake, ba komai, zai aurawa Lawwali Sultana, amma zai nuna wa Lawwali mulki gaba yake da dabanci................

*Hummmm kun amince Mulki gaba yake da dabanci?*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH

PAGE 41:


Zaune ya ke a kujerar da ke kallon ta a cikin office din na ta, su na fuskantar juna, hannun ta ya kama guda daya ya riqe a na shi, ya na kallon yanda gyararran farcen ta yake sheqi, cikin sassanyar murya ya ce,

"Ran ki shi dade, ki na ganin za ki iya zama da ni a duk inda na ajiye ki? Domin ba zan taba karbar gida ko wata alfarma da iyayen ki za su bani ba, ke sani Hajiyan ku da kyar ta yarda da auren mu, dan kawai ina diyan tallaka, ina so na yi komai da kuddi na, ina so ki goya min baya akan wannan, za ki iya?"

Tunda ya fara magana take kallon shi, ta gano gaskiyar maganar shi, ta kuma fahimce shi, ta na alfahari da kasancewar shi mijin da za ta aura, ya san yanda zai ya tsaya a matsayin shi a koda yaushe, baya manta tushen shi, sai dai ta na tsoron rayuwar wahala, amma indai da Auwal din ta ne ba komai, ba abinda ba zata iya yi domin shi ba, sai dai in abun sab'on Allah ne, dan haka ta na ji a jikin ta, za ta iya taya shi cika duk wani burin shi, indai su na tare komai zai zo da sauqi da yardar Allah.

Cikin murmushin da ke nuna gaskiyar maganar da take son furtawa, ta d'aga kai, tare da janye hannun ta daga nashi ta ce,

"Na amince, na amince Zan zauna da kai a duk inda ka ajiye ni, duk inda ka sa qafa nan zan aje tawa, ni kai nake so,ba kudin ka ba,zan amfani da tushen ka ne, ba na iyaye na ba, kai nawa ne, ni taka ce"

Godiya ya mata, suka ci gaba da hirar su sama sama, ta na tsara takardun da za a ware tallafi zuwa ga mabuqata.

Bayan ya maida ita gida, suka ga motoci masu numfashi an Parker su a harabar gidan, Sultana na gani ta gane su waye a ciki, juya ido sama ta yi, ta amshe jakar ta a hannun Lawwali da ke mata sai da safe, sallama suka yi ta shiga gida, ta samu Hajiya Ikee a parlour su na hira da qawayen ta sai zuba musu qarya take, akan shaharar Lawwali a kasuwancin qasashen waje, duk da haka bata tsira ba, sai da suka dinga yada mata da baqar magana, akan 'yar ta bata samu auren shugaban qasa ba.

Gaida su Sultana ta yi ta haye sama, ta na matuqar takaicin rayuwar qaryar da mahaifiyar ta ke gudanarwa.

A can parlour kuwa su Hajiya da qawayen ta sun gama tsare tsaren yanda bikin zai kasance, a cikin qawayen ta akwai wadan da sun taba aurar da yara mata, sun yi alqawarin kawo masu gyaran jiki na musamman har gida.

Wani party da duk abinda Hajiya Ikee ta ke da buri ya faru a bikin nan, sun kammala tsara yanda zai kasance, a bangare guda kuma Lawwali ya gama hurewa sultana kunne kar ta yarda a yi wadannan abubuwan, kuma ta yarda da hakan, bata bayyana ma Hajiya abinda suka tsara ba ita da Lawwali sai bayan tafiyar qawayen Hajiya ne Sultana ta sanya riga da skirt na bature, ta daure gashin ta a bayan ta, ta sanya takalmin ta ta sauka qasa, zama ta yi kusa da Hajiya,dauke da wayar ta a hannu, ta na dannawa ta na wa Hajiya bayanin da ya zama kamar dukan tsiya take wa Hajiyan.

"To kin ji yanda mukai da Auwal, Hajiya in ba gyaran jikin ba ni dai dan Allah ki bar zancen wasu party har kala hudu, ayi guda daya ma ya isa, ni dayan ma da za a bi nawa da ba za a yi ba, amma saboda kema ki fita kunyar qawayen ki za mu yi, yanzu yaushe Juwairah din za ta zo, na ji ana zancen gyaran jikin ta, irin na sudanis ya na da kyau" (ta na a garin Bauchi ga mai neman kwararriyar mai gyaran jiki irin na sudanis ku min magana)

"Na ji duk bayanan ki, kenan ki na nuhin shi Lawwalin ne yacce ba a yin komi?"

"Eh Hajiya, ko na kira shi ku yi magana, dan..."

"Ahhhhh ni ba na neman tashin hankali da ki ka ganni nan, magana ta qare, ai auren ku ne, in ma cewa kun kai a daura a kai ki haka nan ku kun ka sani, ni na hau sama, in Sultan ya zo ki kire min shi, ba mu da lokacin fita waje dan siyayyar kayan aure, in ma mun ce order za a yi, yanzu yaushe mun ka gama zabe zaben abubuwan da duk muke da burin saye? Ni dai wanga aure naku Allah dai shi hisshe ni kunyar abukkai na"

"Ai Hajiya ki kwantar da hankali ki, domin kuwa ya na da inda zai aje ni, ya ce ko cibi (tsokali) ba shi so a siye, ni kad'ai ya ke so a bashi, kin san hwa gidan da yake a nan shiyyar yake, kuma gida ne mai kyawu daidai misali, dama ni kin san rayuwar qarya bata gaba na"

"Hummmmm in ji me ciyon haqurra, ba ke ji komi daga baki na ba, ballantana ki hwadi mai, na hau sama, Allah dai shi gwadi mana ranar bikin"

"Ameen Hajiya ta"

Sama ta haye ta na ta maganganu qasa qasa, ita kadai ta san me take ji a zuciyar ta, na baqin cikin auren Lawwali amma ba halin bayyanawa, da ace wani na sauraron abinda mutum ke quqqullawa a zuciya, lallai da Hajiya Ikee ta shiga bala'i.

Ko da Sultan ya dawo, ya ji dadi matuqa da ya ga qanwar shi cikin farin ciki, fatan alkhairi ya mata sosai sannan ya je kiran da Hajiya ke masa.

*************************

Lawwali ne ke ta Video call da Mubaraka, sai tsokanar ta yake wai ta girma, ya ga ta na fari, ko bleaching take ne?

"Haba Yah Auwal, mi zai sani bleaching, baqi na mai kyawu na wallah, tau ko ba shi da kyawu ma yanda Allah ya yi ni haka nan zan zauna, sab'a halittar Allah haramun na, ina dai gyara jiki na da abubuwan da muke da su na gida shi na yas-sa ka ga na yi haske, Aunty Fateema ke yi min gyaran jiki, in ta yi,"

"Ohhhh Mubaraka, wanga bayanin kare kai, anya ba bleaching din ki ke ba? Tau ba wannan ba, ke san kuwa maganar aure na ta tashi ni da mutuniyar ki?"

Hamdala ta dinga yi, tare da babbaka dariyar farin ciki,

"Yah Auwal yaushe ne bikin? Kuma yushe za mu taho"

Dan jimmm ya yi, kafin ya gyara zaman shi ya ci serious dan ba ya so ta masa daru,

"Ke gane ko, saboda abubuwan da suka hwaru a baya, shi ne nicce ko za ku zauna ba sai kun...."

Cikin kukan shagwaba ta katse shi,

"Ni dai gaskiya sai na zo, bikin ku ne fa"

"Baraka na ki saurare ni da kyau, zan so a ce ki na nan, rashin ki zai zama kamar bani da dangi ne a wajen, amma ba zan iya sanya rayuwar ki cikin hatsari ba, hatsarin da nake ciki a yanzu ya hi Wanda kin ka sani,ki bani goyon baya, na miki alqawari hatta da hita ta daga gida, sai an miki video kin gani, kwanciyar hankalin ki da zaman ki lahiya ya hiye min komi ga rayuwa ta, dan Allah kar ki min taurin kai"

Cikin hawaye da sanyin murya ta ce,

"Yaushe ne bikin?"

"Asabar din ga me zuwa, yau saura kwana biyu,ki yi hakuri, i am very sorry, in ji ku turawa"

Cikin kama kunnuwan shi duka biyun ya ke bata hakuri, ran ta ya ɓaci , wai a ce sauran kwana biyu bikin shi, sai yau yake fada mata, amma ba komai, za ta girmama maganar shi, wataqila hakan da ya yi shi ne daidai, fatan alkhairi ta dinga musu, ta na murnar yaqe, qasan ran ta kuwa ta na jin ba dad'i , za ai auren Yah Auwal din ta guda ba ita.

Shi kuwa wasa da dariya ya dinga mata dan dauke hankalin ta, ya samu nasara kuwa dan ba su bar video call din ba sai da ya tabbata ta saki ran ta.

Kwantawa ya yi ya na kallon sama, tunanin iyayen shi yake yi, a rayuwa shi dai ba shi da sa'a, wai ace ya na da iyaye a cikin garin Zamfara, amma kamar ba shi da kowa, ba wanda ya ke da kusanci da shi, da zuciyar shi, balle ya ji damuwar shi, ba wanda ya damu da rayuwar shi,tunawa ya yi da sanda ya kai musu maganar auren, kafin ya fita daga gidan ya na dakin shi, ya ji mata na ta shiga ana fita, ana yi wa Lamishi Barka, d'an ta zai auri diyar gwamna, wa ya je ya baza a unguwar sai Allah masani.

Gaba daya basu damu da wai bari a bincika a ga mene ne dalilin yin auren ba, farin cikin su kawai dan su zai auri yar gwamna, ba komai, Allah dai ya kai mu biki lafiya.

Tunani ya dinga yi, na me ya rage a bikin wanda yake haqqin shi ne bai ba? Domin hatta da lefe da ya yi wa Sultana maganar shi, cewa ta yi ba sai ya yi ba, Hajiya Ikee kuwa ta ce bata san zance ba, ba a ɗauke masa lefe ba, sai ya yi, duk abinda ake buqata, dan haka kudin kawai ya tura ta account din Hajiya Ikee, ya ce su sai duk abinda ya kamata, ganin mahaukatan kudin sun rudar da Hajiya Ikee, amma bata yi mamaki ba, duba da wa ya tsaya masa a garin, ba qananan kudi yake samu ba a wajen Gwamna, Hajiya ta dau alqawarin ita zata kula da lefe, to amma ya rasa dalilin da ya sa yake neman dalilin da zai kai shi gidan su Sultana, ya na so ya sanya ta a idanun shi, zuciyar shi na azalzalar shi ta na tunzira shi akan ya je ya gan ta, daya bangaren na zuciyar shi na kwabar shi, bai biye wa daya daga cikin su ba, ko da ya fita ya dauki hanya, bai tsaya a ko ina ba sai gidan su.

Ko gaishe su bai ba, ya tsaya a tsaye ya ciro kudi masu uban yawa daga aljifan jikin shi, ya ajiye wa Lamishi, ya ce gashi nan su samu inda za a musu ɗinkin gaggawa in sun sai tufafin da suke so su sa a bikin, ba ya so su je masa wajen biki a hargitse.

Godiya suka dinga yi kamar za su kwanta, makullin mota ya bawa Jameelu, ya ce ya dakko wasu manyan ledoji a bayan motar, a guje ya fita ya na tsalle, ledoji ne manya masu nauyi Jameelu ya shiga da su, Dan Talo na ta bata rai ba a bashi komai ba.

Lawwali murmushin takaici ya yi, dan duk ya fahimci komai, tura leda daya gaban Dan Talo ya yi, ya ce,

"Sai ka bar bata fuska, ka sanya ranar daurin aure, kuma ka yi wanka dan Allah, kaya duk kyawun su in ba wanka ba sa kyau, Jameelu ga naku nan,ga wannan ku tai ku sai takalma da hulla, bana so ku taho wajen nan kamar almajirrai,"

"Tau Yaya mun gode"

"Kaiii wanga yaro Allah shi qaro bud'i" in ji Dan Talo.

"Addu'ar ku kenan,bud'i dai bud'i dai, to Allah shi bud'a din, ba bu ruwan ku da ta ina bud'in zai taho"

Fatali ya yi da dan karamin kwanon man gyadan da Mai Buruji ta soya, ya bar gidan, cikin takaicin iyayen nashi.

Ko da ya koma unguwar da yake zama, har zai wuce gidan shi, kawai ya tsaya, ya kira Sultana, ta na dauka ya ce,

"Ki shirya ki hito, zamu daukan hoto, ina jiran ki, nan da awa guda"

"Daukan hoto kuma? Na ko aza bai dame ka ba irin wannan abubuwan"

"Za mu yi ne dan Hajiya, ke san wadda taka son ayi komai a bayyane, hoton zai faranta ran ta"

Ta ji dadin yanda ya duba lamarin Hajiyar ta, da gaskiyar shi, hoton zai faranta ranta matuqa.

A gaggauce ta shiga wanka,ta fara shirya wa, dan bata so ta bar shi ya zauna jiran ta.

Shima gida ya wuce, ya samu ya watsa ruwa, ya yi shirin shi tsaf cikin farar shadda mai golden din aiki, ya na daga cikin dinkunan da suka siyo ready made shi da Sultana, a qalla sun siya kaya masu kyau da tsada kusan kala goma goma, a gogon shi na gold ya daura, kuma kalar aikin kayan shi (maza ku sani haramun ne namiji ya sanya agogo gold ko zoben gold sai azurfa).

Takalmin shi ma kalar aikin rigar shi, sai hula fara mai ratsin golden, Masha Allah, ko shi kan shi sai da ya jima gaban madubi ya na kallon kan shi, a fili ya bayyana cewa,

"Lawwali kenan, dan gidan Lamishi da Dan Talo, Yayan Mubaraka, Angon Sultana"
(Aunty Asma'u😆)

Murmushi ya yi, ya dauki turarukan shi ya dinga fesawa a hankali, ta yanda qamshin su ba zai hau kai ba, ya na gamawa ya taje gemun shi da ke qarawa fuskar shi kyau da kwarjini, (Team Gemu🥰)

Sai da ya rufe gidan sannan ya shige motar shi da ya bari a waje.

Ya na zuwa qofar gidan su Sultana Kiran ta na shiga wayar shi, dauka ya yi, ya ce ta fito ya na waje.

Ya na nan zaune a mota ya ga securies guda uku sun bude mata qofar, kamar hadin baki ta fito sanye da doguwar riga golden color, ta na ta walkiya a cikin duhun daren, Lawwali sakin baki ya yi ya na kallon Sultana, anyaa ita ce kuwa?

Sultana ta ji dad'in yanda Lawwali ya shagala da kallon ta, sai yanzu ta ke godewa Hajiya da ta dage sai an kawo wadda zata shirya ta, dan kuwa in ita zata shirya ba zata fito a matsayin amarya ba, dunkunan da a ka kashe makudan kudi aka yi su, a banza za a sanya su ba su yi kyawun da ake so ba.

Da sauri ya fita ya bude mata qofa, ta shiga, ta na murmushi qasa qasa.

Bayan ya zauna kafin ya tada motar,suka kalli juna, a tare suka furta,

"Ka/kin yi kyau"

Dariya suka yi, sannan Lawwali ya tada mota, sai hadadden gidan Hoton da ke cikin garin na Gusau, tun da suka shiga wajen mutane ke kallon su, domin kusan duk amaren da angwayen da suka je wajen dan d'aukan hoto Lawwali da Sultana sun fi su yin shiga mai kyau, da tsari, da burgewa.

Sai da aka gama wa mutum uku, sannan aka zo kan su, a lokacin qarfe goma na dare ta gota.

Style kala kala aka dinga nuna musu su kuwa su na kyafewa ana daukan su hoto, style din da suka ga ya sabawa shari'a in ance su yi, sai Sultana ko Lawwali d'aya daga cikin su yaqi.

A haka dai aka gama daukan su hotunan, wasu matasa ne suka gane Sultana, habaa manaa nan da nan waje ya cika da surutai kala kala, wasu na yabon ta, su na ta so a dauke su hoto da ita, wasu kuma na tsangwamar ta saboda mahaifin ta.

Lawwali bai tsaya biye wa shiririta ba, ya ja ta suka tafi gida.

Hajiya ta rude ta rikice da ta ga hotuna, ga su an tura musu ga waya, ga wasu sun taho da su a envelope,kallon Lawwali ta dinga yi daga sama har qasa, ko ba shi da arziki ya na da kyauwun huce takaici.

A cikin daren ta dinga dora hotunan a social media, qawayen ta kawai take jira su ga wannan hotunan, ta ga reaction din su akan mijin Sultanan ta.

Sultana ma ta dora hotunan a social media, musamman Instagram ,ganin yanda suka rude da kallon hotuna kamar basu da lokacin shi ne ya sanya Lawwali yin sallama da Sultan ya tafi gida.

Kayan shi ya cire ya tafi daji, domin ya na da mahimmin abu da ya ke so ya gudanar a can.................

*Biki bidiri buredeee*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 42:


Tokare take jikin gini, kamar wadda aka jingine, ta na ta dariyar yaqe, hannun ta dauke da kwano, shinkafa ce a ciki, ta sha ganyen zogale da quli, tumatur da albasa, da soyayyan mai, abincin da Lamishi ke matuqar so kenan.

"Ko ni mutan gidan ga ba su amsa sallama ne? Sai buga sallama nake tun garka shiru ka ke ji"

Lamishi ce ta fito, sanye da kayan da ta ke gwada wa, in da kudin ka yanzu za ka samu abinda ka ke nema, har sun samu ɗinkin da suka kai, guda bibbiyu, manyan leshi guda biyu atampa manya biyu, kowa d'aid'ai, sun siyo takalma da jakunkuna, sarqoqi da abun hannu, sai sabbin mayafai .

Lamishi ce ta yatsina baki ta ce,

"To wa ya ji ki mu na can mu na harikar azziqi"

"Ai fa, na ga harikar azziqi, mutumi na zai yi aure shi na ko a fad'i min, duk abin da ya faru a baya ai ke san sabanin harshe da haqori ne, to Allah shi sanya alkhairi, ni zan koma, ga gwaben shinkahwa na kawo miki, na san ki na so"

Wangale baki Lamishi ta yi, ta amshe kwano, ta gauraya gaban ta ta afa a baki, dad'in abun ne ya soki kunnen ta sai da ta sosa.

'Yabbuga na ganin haka ta saki jiki ta na zuba, ta ce wannan ta ce wancan, nan dai Lamishi ta manta da komai, suka hau hira akai ta bawa 'Yabbuga labarin abun azziqin da ke ta gudana a gidan.

"To ni dai ba wannan ba, ke dai ga bikin ga da ya taho a qurarren lokaci, ko tuwahi sabo ban dunka ba, dama ya kai wata guda ne, da na sa Dan Jumma ya sai min Holan ko Suhwa, nima na daura ana bikin Babban d'a"

Dariya suka sanya sukai shewa, tare da tafawa,

"Kar ki damu, ina nan da wata da Hajiya Ikeelima tabban, ke san su irin wannan ba shi gaban su, sai su sa sutura su ɗebe su basuwa kyauta, anjima in sun gane ta ba su ganewa "

'Yabbuga guda ta kama hanci ta zabga, ji take kamar ta jawo goben a d'aura auren,

"Ohhhh Allah na gode maka, ashe da rabon zan daura suhwa a duniyar ga,Allah ya kaimu wannan rana da rai da lahiya"

"Ameeen, ki na da takalme da jikka?"

"Ina da su, amma tun wanda na ci bikin Kareema ne wallah"

"Kayya, ki ce baki da su kawai"

"Sai goben ki taho akwai wanda zan baki, na Mubaraka ne, Sultana tabbata su,"

Wani tsallan bad'ake 'Yabbuga ta buga ta yi baya, ta ce,

"Yo ance miki kwana na na yaqare da zan saka kayan Mubaraka? Banni na tai bukin ga lahiya mu dawo lahiya, ke san halin Lawwali akan abun Mubaraka, walle ba ze ji nauyin yagan rigar mutunci ba gaban kowa, banni na tai da tsohhin nawwa, ai guntun gatarin ka ya hi sari ka bani"

Dariya Mai Buruji ta ke ta yi, bayan ta dasa kujera a gefen Lamishi ta zauna.

"To bid'i wuri ki zauna in ke qare tsallen, matsoraciya, jiya kuwa yattaho, na san yau ma shi na nan tahe"

Rarraba ido 'Yabbuga ta fara, tuna ranar da ya dawo cikin bacin rai ta yi, ta na baccin wahala, takalmin ta ta shura ta ce,

"Too mutanen ga na yi gida, zan bawa bisashe(awaki/tumaki) ruwan yami, rabon su da ruwa tun jiya"

"Ke dai hwadi gaskiya, dan an ce Lawwali na tahe, shi na ki ka son gudu"

"Ko ni ba haka nan na ba, ai ko Allah sanya alheri ina tsayawa na yi mai, zan dai je ne na ba bisashe ruwa"

"To ya yi, jira na doko miki kayan da za ki saka goben"

Lamishi ce ta shiga ciki, ta dakko atamfar ta bawa 'Yabbuga, kaya ne kamar sababbi fess da su, Godiya ta yi ta yi, ta tafi.

Su kuwa suka ci gaba da shirin kayan zuwa biki, har lalle suka tsara za su daura a daren.

***************************

A gidan gwamna kuwa, ko ina ka wurga ido mutane ne, na birni da na kauye, Sultana ta yi mamakin ganin yawan mutane, ko dan ba a taba aurar da kowa a gidan bane, tunda sukai kudi, mahaifin su ya zama Gwamna dangi suka dena shiga jikin su, saboda tsabar wulaqanci da tozarcin da Hajiya Ikee ke musu, in ka ga ta kula wani a dangi, to fa ya na da maiqo,bata bar dangin ta ba, balle dangin miji, kowa ma tabawa take.

Sai gashi mutane sun yi hakuri da halayyar da ta musu a baya, sun zazzo bikin, domin zumuncin Allah ba dan halin ta ba.

Amarya ta sha gyaran jiki da gyaran gashi, duk inda Sultana ta wuce qamshi ke bin ta,a cikin yan uwan su, har da masu taba jikin ta, dan kawai su ji ya yake, tsabar kyaun da ta musu a ido.

Sultan kuwa na can na hada ma Sultana babban surprise din da ya san in ta gani sai ta yi murna sosai da sosai.

Washe gari kuwa da safe tun safiya ake qawata hall din da za a yi bikin na su, duk wanda ya ga yanda aka qawata wajen zai tabbatar da bikin na manya ne ba na qananan mutane ba.

Amarya da ango kuwa kyawun da suka yi ba mai faduwa ba ne.

Lawwali ba shi da abokan da suka wuce abokan shi na cikin daji, sabbin matasan da suka horar suka bari tsaro da gadin dajin nasu, su No 2, No 3 da no 5 su ne manyan abokan ango.

Da yamma kuwa Mota biyu Lawwali ya aika unguwar su, dan ya san sai su Lamishi sun yi gayya, ai kuwa motocin nan sai da aka cika su taf da mutane.

Su Aunty Asma'u, Khadeeja Katuru, Halima (Maman yayana),Khadeeja Jabo, Eeshaa, Maman Jasrah,Aunty Rumma,Ameena Saudia, Su uwar gida Sarautar mata Iyar Ilham, Ashwal, Mom Sawwama, Maman Husnah,Maman Muhseenah,Mum Basheer, kai da dukkan mutanen group din A GARIN MU, sai da suka samu mota guda ta kwashe su zuwa event center din nan.

Amarya Sultana kuwa a zaton ta tunda bata da qawaye Lawwali ne kawai zai je su tafi, sai ta ga an kawo motoci da yawa, da damar su gilashin su baqi ne, har wadda akai wa decoration wato ta amarya da ango, a tunanin ta sauran motocin da ke take musu baya securites ne a cikin su, haka ta shiga motar cike da son ganin irin kwalliyar da angon ta ya yi.

Lawwali ma Allah Allah yake ta qarasa shiga motar ya qarewa kwalliyar da ya hango ta baqin gilashin motar kallo.

Ana budewa qamshin su ya qauraya da na juna, kasa lumshe idanun su suka yi, saboda yanda suke kallon juna.

Kowannen su na godiya ga Allah, da ya haɗa shi da abokin rayuwa kyakkyawa kamar dan uwan shi.

Hawayen farin ciki ne suka fara sauka daga idanun Sultana, tissue lawwali ya miqa hannu gaban mota ya zaro, ya fara goge mata hawayen ta, duk abinnan da suke, masu video da hotuna na ta dauka.

Mai hoto guda daya aka samu ya zauna a gaban motar, da ya ga sun yi abinda ya burge shi sai kuji kyasss kyarasss ya dauki

Please Login or Register in order to submit comment