Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo mana qarshen wannan rayuwa mara aminci da muke ciki, ya Allah ka sa qasar mu Nigeria da duniya baki daya ta zama waje mai aminci ga bayin ka,"

"Ameeen Sulty Baby, ya jikin naki? Hajiya ta je ta na ta hwada, ban san akan mi take magana ba dai, amma na ji ta na akwai tanadin da ta yi akan ki, ko kin san akan mi taka magana?"

Murmushin da be kai ko ina ba ta yi wa Sultan da Ke bin ta da kallo, sannan ta ce,

"Ka manta mun je gidan dan takarar shugaban qasa? To tun daga can ta fara ciniki na, ka shirya kaima za a yi naka kwanan nan, da ta samu wadda ta hito gidan kuddi za a saishe ka, Yah Sultan ina da wanda nika so, ta ce kar ma na bude baki na sanar da Daddy, sun gama maganar wanda za su bawa ni"

Hawaye ne suka fara tsartuwa daga idanun ta, ran Sultan ya ɓaci matuqa, zai d'auki komai akan shi, amma ba zai taba jure ganin Sultana cikin mummunan hali haka ba, nawa take har da za a ce hawan jini ya kama ta?

Cikin fushi ya bar d'akin, ta na ta kiran shi bai juya ba.

Ya na fita wayar ta na daukan ringing, da kyar ta janyo ta, ta na ganin sunan Auwal, hannun ta ya d'au rawa, bakin ta na rawa saboda kukan da ya taso mata, ta na dauka kuwa ta fashe da kuka, Lawwali na jin kukan ta, ya ji wani abu mai qarfi ya daki zuciyar shi, ba ya son jin haka saboda ita, ba ya son jin damuwa da damuwar ta, amma ya kasa jurewa sai da ya tausasa murya ya ce,

"Ran ki shi dade ki yi min afuwa,na shiga matuqar busy ne, inda na tai ba network ,shi yasa ban dauka ba,amma ki yi hankuri, gani na dawo gida,dan Allah ki dena kukan"

Cikin shagwaba ta ce,

"In ka sake tafiya inda ba Network zan yi fushi da kai mai tsanani, ba zan sake kula ka ba"

Siririyar dariya ya yi, Sannan ya ce,

"A min ahuwa, in ki ka dena kula ni, ashe qarshen rayuwa ta ne ya zo, ba ke ba Mubaraka, lallai da zan zama kamar gunki, domin zan zam ba rayuwa a tare da ni"

Itan ma dariya ta saka, wadda ba zata iya tuna sanda ta yi dariya ba a ranar gaba daya.

"Na maka alqawarin sai ka mallake ni a matsayin matar ka, kuma sai mubaraka ta dawo gare mu lahiya"

Kalaman ta na qarshe ba karamin faranta ran shi suka yi ba,har ya ji sabon lamari game da ita...............

*Tambaya ta anan shi ne, Sultana da ke yi wa Lawwali alqawari, ta manta maganganun Hajiya ne?*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH



PAGE 34:


"Dakata min Sultan, kai har ka isa ka taho ka yi min titsiye? To bari ka ji, kai kan ka, ina nan na tanadar maka wadda za ka aura, lokaci nika jira, ta na kammala digirin ta ta dawo qasar ga za a daura muku aure, diya ce ga minister'n tsaro, kuma babbar diyar shi, na duba wayar ka tass na ga duk matan da ka ke mu'amala da su, duk ba ya wuce gaisuwa, Ita dai nigga ku na hira jefi jefi, tunda Allah ya sa hankalin ku ya gamu waje guda, Daddyn ku ya ma iyayen ta magana, kuma sun yi na'am, ka shirya, ana gama auren Sultana naka za a yi"

Baki Sultan ya sake kawai ya na mamaki, ya na namiji amma ana so a masa auren dole, to ba ma wannan ba, in an masa auren dole ya hakura tunda dama baida budurwar da ta kwanta masa ga rai, to ita sultana da ke son Lawwali fa?

"Hajiya na amince ku aura min duk wadda kuka so, amma fa ba zan amince ku aura wa sultana mutunin da bata qauna ba"

"To Uban mu, mun jiya, in an tashi auren sai ka hana,...dalla fita ka ban waje, yau so kuke sai kun batan duk wani farin ciki da nake ciki na ga alama"

Daddy ne ya shiga dakin bakin nan kamar gonar audiga, cikin, farin ciki ya ce ma Sultan,

"Ku shirya kai da qaunar ka gobe akwai party, around 1am, kwana za a yi ana murnar samun nasara, diyoyin gwamnoni ne suka partyn a Abuja, na san za ku buqaci kudi sosai, dan kusan kowa a wajen ya na taqama da uba nai, ga wannan, ku dauki duk nawa ya muku"

Wani dan kati ya miqa masa,wanda yake a matsayin makullin ma'ajiyar kudin Gwamnan, kallo kawai Sultan ya bisu da shi,ya kasa cewa komai, da kyar ya bude baki ya ce,

"Yaushe ku ka zama haka? Yaushe kuka dena damuwa da abinda muke so sai wanda kuke so? Yaushe za ku saki duniya, ku kama qiyama?"

Daddy bai fahimci ina Sultan ya dosa ba, ita da ta san akan me yake magana, tuni ta miqe, ta na son kawar da zancen Sultan ya sa kai ya bar dakin.

"Kwantar da hankalin ka ka jiya diyan ga in ka ce kabi nasu to fa ruwa ma sai an tauna musu an hadiye musu tsabar gata"

"Amma mi an kai mai ? Ban taba ganin Sultan ya yi hushi haka ba,mi kin kai mai? Ki hwadi min gaskiya ko inna bincika na gano kin masa wani abu ran ki zai ɓaci, ban hada d'iya na da kowa ba"

"Ni kuma ni na haihe su , har da ka ke hwadi min baka hada d'iyan ka da kowa ba, maganar wannan yaron driver ne taqi qarewa gidan ga, ya zo ya na wani hwadin magana yanda ya ga dama, to shi kan shi na sanar masa magana diyar Minister , shi na yake hushi "

Shiru ya yi bai ce komai ba, ya fita ya bar dakin, bai tsaya a ko ina ba sai dakin Sultana, ta na bathroom, ta na alwala, sai da ta gama ta fito taga wayar ta a hannun shi, ya na duddubawa, har ta isa gaban shi bai aje wayar ba sai da ya gama abinda yake.

"Sultana da dukkan alamu ki na son Lawwali, amma Sultana ki sani, ke baki san waye Lawwali ba, ni na san waye shi, ina mai baki shawara da ki hakura da shi, tun da wuri, tun lokaci bai qure miki ba"

"Daddy kenan, indai Hajiya ta ji ta gani, ta ke zaune da kai, banga dalilin da zai sa ni na kasa auren driver na ba"

Cikin rashin fahimta ya ce,

"Me ki ke nufi? Sultana yaushe kin ka hwara magana irin wannan? Me ki ke nufi da abinda kin ka hwadi yanzu?"

"Never mind Daddy, ina so nayi sallah, pls"

"Sultana ina son sanin damuwar ki, talk to ur Daddy Sulty Baby, ki sanar da ni mi ki ka so"

Cikin kuka ta ce,

"Daddy ka tambayi Hajiya, ta san komai, dan Allah ka barni na gana da Ubangiji na, shi ne kaɗai zai min maganin damuwa ta, Hajiya ta tabbatar min da ba zan samu me nake so wajen ku ba, yanzu ka tabbatar min da na hakura da farin ciki na, saboda bai muku ba, bai yi daidai da abinda kuke so ba, ni Auwal nike so, ba wani shugaban qasa ba,"

Daddyn su ne ya ja ta jikin shi ya na lallashi, a zuciyar shi kuwa ya na mamakin sanda ya yi sake Lawwali ya yi nasarar dasa soyayyar shi a zuciyar sultana haka, sai yanzu yake tunawa da alamomin da Hajiya ke sanar da shi, lallai ya yi sake, Lawwali na shirin yi masa babbar illa, indai har ta nan ya biyo.

"Ya isa kukan haka nan, zan yi tunani akan maganar, ki daina kuka"

Da sauri ta kalle shi, ta na son tabbtar da gaskiyar maganar shi, dan yanzu gaba daya ta cire yarda a tsakanin su, gani take komai nasu qarya ne.

Sai da ya ga ta daina kukan ya bar dakin, wajen Hajiya Ikee ya koma, ta na zaune ta zabga uban tagumi ta na tunanin yanda za ta raba tsakanin Lawwali da sultana.

"Ki na da gaskiya ashe da kin ka ce na kori yaron nan daga gidan nan naqi ji, ashe ya min babbar illa ina zaune ba tare da na sani ba?"

Kamar an sosa mata inda ke mata qaiqayi haka ta miqe, kallon lokaci ta yi, ta ga ya tafi sosai, ta gaji tilis, kuma maganar nan na buqatar dogon nazari, ko kadan ba ta son batawa Sultana, amma dole ne ta raba tsakanin su da Lawwali.

"Wannan magana ta riga ta wuce, yanzu mafita za ka nemo mana, dan kuwa ba zan taba yarda diyar ciki na ta auri driver ba, yau ko min muqamin da za ka damqa masa a gwamnati walle ba ya hanawa a kire shi da driver, ba zan zama abin dariya cikin abukkai ba,dole ka dau mataki"

"Ba zaki gane ba, yanzu raba tsakanin sultana da Lawwali babbar musiba ce wallah, duk yanda zan miki bayanin yaron nan ba zaki gane ba, ni na san wane ne Lawwali,"

"Driver din? Me ye ba zan gane ba? Yau muke tare, ka kore shi kawai, shi bar gidan"

Bai ce mata komai ba ya fada bathroom.

Mita ta dunga yi tare da fadin ya sa yaron shi din nan da ke masa aiki, a sace Lawwalin ya bar doron qasa baki daya, Indai ze zame musu fitina akan dukkan tsarin su.

*************************

Sai guje guje suke abin su a katafaren tsakar gidan kakannin nasu, cike da nishad'i da jin dadi, ita kan ta Hajiyar Hansatu rabon ta da fitowa farfajiyar gidan haka ta manta, Hansatu na ta tuna yarintar ta, zaune suke a saman kujeru na qarfe masu matuqar kyau, gaban su table ne an aje fruits da abin sha, su na ta hira a tsakanin su, wanda ya san Hansatu sati Uku da suka wuce ya gan ta yanzu ba zai gane ta ba, ta ciko ta murmure, ga wani haske da ta yi, in ta saka riga da skirt sai ta cike su famm, ban taba zaton hansatu na da shape haka ba sai yanzu.

Hajiya ce ta kalle ta ta ce,

"Gaskiya ya kamata a sauya maki waya, yanzu da yar wayar nan ta zamani ake hira da miji, sai ku yi chatting din ku kamar ku na tare, haka naga Yayan ki na yi da waccan maras kunyar da ta qi dawowa, amma fa soyayya a waya kamar Juliet,"

"Hajiya wai mi an kai mata ne haka?"

"Wannan fa baki gane alqiblar ta, dan yanzu ko an ce mi yayi mata bata hwadi, ta na can qasar waje, da alama can taka so su koma da zama, tunda can ta yi rayuwar ta, ni kuwa ba me d'auke min yaro shi tai wata uwa duniya"

"Ohhh amma ko bata kyauta ba gaskiya, ai mace hankuri aka santa da shi a gidan miji, ba irin wanga hali ba"

"Haka ne, ita kam sam bata san wannan ba, komi so takai ayi yanda taka so, ba ko shi yiwa,"

"Allah to ya shirya ta, ya sa ta dawo su ci gaba da zaman su lahiya,"

"Ameen dai"

Su na tsaka da hira Hajiya ta dauki waya, ta kira Yayan Hansatu, tace ya aiko mata da waya mai kyau, kafin Hansatu ta wuce, amsawa ya yi, da toh, sanan suka yi sallama.

Hansatu bata koma gida ba kuwa sai da dalleliyar waya mai kyau, ba ta wani murna da wayar kawai dai ta nuna ta na murna ne, domin kuwa wanda ake mata kwadayin su yi hirar da shi, tunda ya tafi sai dai taji labari wajen Hajiya sun yi waya, amma baya kiran ta, balle ta samu No shi, kuma ita ba zata iya tambayar hajiyar ta No isah ba.

Ko a mota ajiye kwalin wayar kawai ta yi a cinyar ta ta na tunani, ga dai shi ya tafi, kuma ya fadawa Hajiya kasuwancin goro yayi albarka, amma ko sisi bai masu aike ba, bata san ranar dawowar shi ba.

A qofar gidan su motar ta tsaya, fitowa suka yi ita da yaran, kowa ya gan su ya ga jikokin masu azziqi, hatta da takalmin su yanzu mai tsada suke sakawa.

Ko kallon majalisar su 'yabbuga bata yi ba, ballantana ta ga yanda suka sanya mata ido su na gulmar ta.

Sallama ta yi da driver suka shige gida.

Can majalisar su Lamishi kuwa banda gulmar su ba abinda suka ke.

"Hummmm wagga ai ni zan baki labarin Hansatu ta sauya, bari dai, ai za su koma yar gidan jiya ne, ta na zuwa roqon abu zan mata kaca-kaca, yanzu ta koyi walaqanci,ko kallo bamu ishe ta ba,dan ta hwara daura suhwa, da holan, walle ta na barin shi"

"Ohhh ke kuwa me ya sa kin ka ce haka? Ai ba kin mata hwatan komawa gidan jiya ba, indai ta sha wahala yanda kun ka ce"

'Yabbuga ce ta kalli Asshibi a sheqe ta ce,

"Na hwadi, na ce na hwadi baki ganin wani kallon walaqanci da takai wa mutane?"

"Ai kuwa ko kallon wajen ga ma bata yi ba"

"Tauuu PA din Hansatu, ko zuwa zaki ki hwadi mata mi nicce?"

Lamishi da ta zabga tagumi ta na tunanin shin duniya ina Mubaraka ta shiga ne, ta ce,

"Dan Allah ku bar yi mana hayaniyar ga, wadda ku ka yi domin ita bata san ku na yi ba, ni abinda ya ishe ni ya dameni"

"In baki so ki ji mi muka hwadi tai garkar ki, nan garka ta ta wallah"
(in bakya so ki ji me muke cewa je ki gidan ki, nan gida na ne)

Ran Lamishi ya baci, nan da nan kuwa magana ta girmama, aka hau fada, sai ga tone tonen asiri ana ta yi, akan gulmammakin da akai ta kitsawa anan ne matar Yahai taji maganar da daga ita sai 'Yabbuga suka yi ta, ya akai Lamishi da baquwar da bata fi watanni hudu da su ba ta sani?

Ai kuwa sai fad'a ya koma kan 'Yabbuga da Matar Yahai, nan fa suma suka hau nasu maganganun, abu fa ya qi ci ya qi cinyewa, har da dambe.

Asshibi naso ta raba amma abu ya fi qarfin ta, cikin sa'a kuwa Matar Yahai ta samu d'aga 'yabbuga ta maka da qasa, ta haye cikin ta, ta dinga kirba,sai da ta farfashewa 'Yabbuga baki sannan Asshibi da Mai buruji suka samu d'aga ta a jikin 'Yabbuga, Lamishi ta ji dadin hakan, dan kuwa ko ba komai an koya ma 'Yabbuga hankali, ta na miqewa ta hau kade jikin ta ta na fadin,

"Baki daki banza ba, zaki gani, har gida se hukuma ta kama min ke, bari dan Jummaa ya dawo"

"Baku da wanan azziqin da alfamar a Nigeria,"

"Haka kin ka ce ko?"

"Na hwadi,"

Haka nan suka yi ta sa'in sa har aka kirayi magariba suka tafi gidajen su, Asshibi kuwa gidan su Lamishi ta nufa suka yi ta gulmar sauran.

**************************

"Excellency gamu asibiti da shi, ba shi da halin magana shi yassa"

"Mi ya same shi halan?"

"Allah shi taimake ka wasa ta an ka yi, shi na ya samu rauni"

"Allah ya bashi lahiya, ka na ji na ba, wannan ajiyar ina so a qara bata tsaro, gaf nake nai amfani da ita, ba na so Ogan ku ya san me ke faruwa, ka gane?"

"Na gane Excellency,"

"Tau ya yi, ka gaishe shi in ya hwalka"

"Zai ji ranka shi dade "

Bayan sun gama wayar ne, ya sanar da No 1 duk yadda suka yi da gwamna, cikin jin jiki ya ke d'aga kai, alamar ya ji.

Cikin ran shi kuwa ya na tunanin kalar azabar da zai ganawa Mubaraka, duk abinda ya tunano sai ya ga ya yi kadan, qarshe saboda tsananin ciwon kan da yake ji, dole sai hakura ya yi da tunanin zuwa wani lokacin.

*Hummm anya ka daku kuwa No 1???*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻



BY HAERMEEBRAERH




PAGE 35:




Satin su Sultana biyu kafin Gwamna ya bata izin fita daga gidan gwamnati, a wannan satikan kuwa duk ta rame, ta yi zuru-zuru rashin ganin Lawwali da bata yi ya fitar da ita daga hayyacin ta, ita kan ta, ta na mamakin kalar soyayyar da take masa, anya wannan soyayyar ba zata zama ajalin ta ba kuwa?

Masu tsaron lafiyar ta ta dinga kallo daya bayan daya, sanda ta fito tafiya,dukkan su kamar sabbi ne, bata taba ganin wasun su ba.

Juyawa ta yi, ta kalli Hajiya Ikee da ta ke zuba mata murmushi, ta kalli Sultan wanda ke kallon ta da tsantsar kulawa da tausaya wa, ta ce,

"Ina driver na?"

Hade fuska Hajiya Ikee ta yi, sannan ta bude baki zata yi magana, al'ajabi ya sanya ta hadiye maganar ta.

Lawwali ne cikin uniform din shi, wanda da gani ka san sabbi ne, sai dai wadannan ba fari bane, ash color ne, da ratsin baqi a jikin riga da wandon kayan, duk yanda zan fasalta maku kalar kyaun da ya yi ba zai yu ba, sai ido ya gan shi kawai.

Hawaye ne kawai ke tsartuwa daga idon Sultana, a lokaci daya kuma ta na dariyar farin ciki, da murnar ganin jarumin maza Auwal din ta.

Ita kan ta Hajiya Ikee kasa magana ta yi tsabar kwarjinin da ya yi mata, Sultan kuwa zuwa ya yi ya daki kafadar Lawwali, tare da matsa ta, ya na zuba murmushi,

"Me na fada maka game da sa min qauna kuka?"

Lawwali dan duqawa ya yi, sannan ya ce,

"A min ahuwa ran ka shi dade, an min iyaka da shigowa gidan nan ,yau ma Umarni uwar daki na tabban, ta ce na taho na maishe ta gida, in ban taho ba zata taka daga nan zuwa can gidan da qafa, shi yasa na dawo bakin aiki na, ina fatan za a karbi uziri na"

Cikin share hawaye Sultana ta ce,

"Mu je"

"Ku tai ina? Sulty baby yaushe ki ka hwara kafiya da taurin kai, akan wannan qasqantaccen drivern ne ki ka hwara rashin kunya ko? Mu na hwadi ki na hwadi?....kaiii malam ji nan, bar ganin ka na da qirar majiya qarhi, qarhin mulki ba qarya ne ba, zan iya sanyawa a batar da kai, da kai da kaff dangin ku, ba Lamishi ba ce uwar ka? Ko ba ita ta ba? To zan ci mata mutunci gaban ka, in sa a dauren ku har igiya ta yi saura,in ga uban da ya tsaya maka kafff garin Zamfara, ka rabu da diya ta, tun kana gane hanyar komawa gida,ka karya asirin da ka mata kafin na haukata ka, ka na ji na? Ke kuma wuce mota ta mu tai"

Hannu ta sanya ta fizgi Sultana da tun da ta fara zagi da ci wa Lawwali mutunci take kuka ta na bata hakuri, Lawwali kuwa tsaye yake ya na murmushi, babu mai iya karantar yanayin da yake ciki a fuskar shi.

A cikin zuciyar shi kuwa, kawai tunanin yanda zai yagalgala naman Hajiya Ikee a dajin su yake, manyan mata masu ji da kan su ma sun nuna su na son Lawwali yaran manya da attajirai sun qaunace shi, a duk sanda Gwamna ya dauke shi suka fita babban taron manya, ya na wahala ya bar wajen bai samu wadan da suka maqale masa ba, to ita sultana daban ce da ba zata ta so shi ba? Tunda jini na tsargawa a jijiyoyin jiki da tsokar ta.

Hajiya Ikee ce ta danna Sultana a motar ta, ta zagaya zata zauna, kafin ta zauna Sultana ta fita da gudu ta nufi Lawwali,

"Sultan kar ka bari ta tabi wannan dan talakawan, ta janyo mana tsiya a zuri'a, kar ka kuskura ka bari ta tabe shi zan saba maka"

Yanayin Sultan ya nuna ba ya son riqe sultana, Amma dole ya riqe ta, dan bai saba sab'a Umarnin iyayen nasu ba, rungume ta ya yi, ita kuma ta na tirjewa ta na kuka, tare da miqawa Lawwali hannun ta, shi dai ya na nan tsaye bai motsa ba, bai kuma b'ata rai ba, hasali ma murmushin nan ne a fuskar shi, Hajiya Ikee na kewaya wa ta daga hannu zata wanke Sultana da mari taji an mata wani irin riqon da sai da ta ji fatar hannun ta na tabo qashin ta.

Sultana kuwa ta rintse idanun ta, ta qanqame Sultan, ma'aikatan wajen da dama sun riga sun san Lawwali, tini suka sha jinin jikin su, dan kuwa bacin ran da yake ta boyewa sai da ya bayyana a saman fuskar shi, wanda basu san shi ba kuma a ma'aikatan gidan sun zabura za su kai masa hari, akan me zai riqe hannun matar gwamna haka?

Shugaban masu kula da securities ne ya dakatar da su cike da tsoro, kar su ja musu bala'i, Lawwali ya huce akan su.

Yan kanzagi da 'yan maula da 'yan siyasan da ke giggilmawa ma sun tsaya ganin ikon Allah, a hankali murmushin fuskar Lawwali ya dawo, sannan ya saki hannun Hajiya Ikee, wadda ta ji kamar jijiyoyin wajen sun tsaya da aiki, wani yammmm, zummmm hannun ke mata, a hankali Lawwali ya furta .

"Ran ki shi dad'e,shiga Mota na kai ki gida,daga nan ina da wajen zuwa"

Da sauri kuwa Sultana ta bar wajen, har ta na haɗawa da gudu gudu, ta shige motar ta, ta zauna a gaba.

Shima shigewa ya yi, ya zauna, ya ja motar, Sultan ma take musu baya ya yi, cikin tsananin fushi da jin nauyin mutanen da suka zuba mata ido, Hajiya Ikee ta fada motar ta ta zauna, jan ta akai motocin da ke take ma nata baya suka bi su.

Lallai idan Gwamna ya dawo daga tafiyar da ya yi, za a yi ta ta qare, maganar Lawwali ta zo qarshe a shafin rayuwar su.

************************

A ranar da No 1 ya ji sauqi a ranar ya shirya dan zuwa maboyar da aka ajiye su Mubaraka, duk abinda yake No 4 na kai wa Oga bayani ta message, Oga ya gama shirya duk yanda za a yi, jiran zuwan No 1 kawai yake.

Agogon shi ne last abinda ya daura, sannan ya kalli No 4 ya ce,

"Mu tai, ka kai ni, da ina iya tuqa motar ma da kai na zan je, ba ni buqatar rakiya, amma ba zan iya ba saboda yanayin da nake jin kaina a ciki"

"Kar ka damu, zan iya kai ka duk inda ka ke buqata, kai dan uwa na ne"

"Na gode, mu tai ko"

"To Oga"

Sun fita daga dajin No 4 ya koma wajen No 1 dan zuwa maboyar su Mubaraka.
No 1 na gaba a mota, No 4 ya aikawa Lawwali saqon gasu nan sun bar gidan.

Shi kuwa waya ya yi ma sabbin yaran da ya horar, guda bakwai, su ma suka tabbatar masa da a shirye suke.

Cikin duhun magariba suke tafe, kafin su isa har an yi sallah, wanda su ba ta gaban su, sunan musulmai ne kawai da su, amma duk wani abu da Musulmin kirki yake su ba sa yi.

A qofar gidan su ka kashe motar, su ka fita, No 1 ne a gaba, ya na dingisa qafa, ya sanya key ya bude qofar, ya na fito.

Kafin ya kunna fitilar ya ji fito a bayan shi,cikin sauri da faduwar gaba ya lalibi makunnin fitilar dan kunnawa, hasken ta bai gama haskaka ko ina ba wani daga matasan ya sa bindiga ya harbe kwan fitilar, qara da ihun 'yan matan ne ya cika gidan,tun da suke a gidan basu taba jin an yi dambe ba ma, ballantana harbin bindiga, yau tasu ta qare.

No 1 kuwa asalin matsoraci ne dama shi, makircin shi da iya hada tuggun yaqi ne ya sanya aka bashi muqamin da yake da, amma ba jarumta ba, hankalin shi in ya yi dubu ya tashi, wani irin duka aka sakar mishi a qirjin shi, da bakin bindiga, sai da ya fara jin jiri, daya daga matasan ne ya wuce su, ya bude dakin , ya fidda yan matan, sannan ya kai su mota, tayar da motar ya yi, ya shiga gari da su,sai kuka suke, su na bashi hakuri, sun fara bashi haushi, ta madubi ya ga yarinya daya ko a jikin ta, kallon waje kawai take, ta na lumshe idanu, ita bata damu ba kenan ko sace ta za ai?

"Kaiii dalla kun cika min kunne, Oga ne ya aiko mu, wace ce Mubaraka cikin ku?"

Da sauri suka nuna ta, cikin ran shi ya ce,

'Dole ki taurin rai yarinya,'

Sai da suka shiga garin sosai,ya tsaida mota ya wurgawa su Murjanatu kudi, ya ce su bace masa da gani, in sun je gida kome aka tambaye su, su ce basu sani ba,

Please Login or Register in order to submit comment