Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nazari akan abinda ta gani,ya san yanzu in ya yi magana ma ba zata fahimce shi ba, har sai ta dawo dadai .

Lawwali na can na casun shi, da mutanen shi, kamar ba abinda ke damun shi, nan kuwa qarfin hali ne, ba ya so ya gina rayuwar auren su akan qarya, tsakanin shi da Sultana ya na so su fahimci juna, su gina zaman su akan gaskiya da gaskiya, in ya yi nasara ta karษ“e shi, ta aminta da shi,zai fi kowa farin ciki, da hakan zai amfani, wajen musguna wa Gwamna Halliru.

In ta qi karbar shi ya na da sauran shaidun da zai nuna mata, ya tabbatar da cewa za ta yarda da shi, za kuma ta zauna da shi.

Bai koma dakin ba sai sha biyu da rabi na dare,dauke yake da abinci, wanda gasasshiyar kaza ce, da madara, sai ruwan sha.

Ajiye wa ya yi, ya zauna a bakin gadon ,a zaton shi ta yi bacci ne, ya ja bargo ya rufe ta da shi, zai tashi, ya ji Muryar ta da ta sha kuka ta gaji, ta ce,

"Me ya sa ka biye musu, ku ke aikata barna a bayan qasa? Mai ya sa ka zama daga bayin Allah wadan da yake fushi da su, ya tsine musu? Ko ka san hukuncin wanda ya kashe rai kuwa a wajen Allah? Me ka ke nema a duniya da ya kai ka aikata munanan zunubai haka? Kaico na ni Sultana na yi asara a duniya, ban yi dacen masoyi da iyaye ba, kaico na, kaico na"

Yanayin yanda take kuka, sai da ya kawo wa Lawwali kwalla a idon shi, cikin qunar rai ya ce,

"Ba da so na bane, ba laihi na ne ba, laihin shugaban nina ne, sun qi su bani taimako a lokacin da na je musu ina cikin mawuyacin hali, na je su tallafe ni su agaje ni a lokacin da nake tsananin buqatar hakan,amma suka maida ni dan ta'adda,mai sace yaran mutane ya kai musu, ba na mantawa ina da qarancin shekarun da ba za su wuce shekara sha biyar ba, lokacin mahaifi na ya na ganiyar zaman banzan shi, caca da shan sigari su kadai ya sanya a gaba, ga iyayena mata basu da aiki sai dambe da tashin hankali a shiyya ( unguwa).

Duk inda zaman lafiya bai samu ba, talauci ya fi wahal da wadannan mutanen.

Sai mu kwana mu wuni ba mu ci abinci ba, a lokacin mahaifiya ta na dauke da cikin Mubaraka, na matsu matuqa na samu qani ko qauna, wanda zan dinga gani na ji dadi ga rayuwa ta, wanda zan dinga hwadi wa abin da ka damuwa ta, tunda iyaye na basu damu da rayuwa ta ba tun asalin tashi na, sai na kwana na wuni ban ci ba, ban sha ba, ba mai tambaya ta ya na wuni, ko ya na kwana, sai nai ciwo na warke ba wanda ya sani,sai an ga na rame a ce 'Baka da lahiya ne halan?'

Na sha wahalar rayuwa matuqa a baya, saboda wahala dole na bar makaranta, na fara bin abokan banza bayan na sauke qur'ani, na ajiye boko, ina Jss 2, na fara bin wani babban dan daba a nan shiyyar mu, muna bin qananan 'yan siyasa, su na saka mu nemo musu yara qanana, tun ban san mi ake da yaran ba, har na sani, sai da ya zamana na hwara dokan yaran shiyyar mu ina kaiwa, sai dai a nemi yaro a rasa, kuma da ni za ai ta bid'a a shiga nan a shiga can, in yi shiru .

Mahaifi na kuwa tun da yaga na dena kwana da yunwa, ina sauya kayan sawa ta, sai ya fara ja na a jiki, inna tafi na samo dan wani abu, sai na samma sa, ana haka Lamishi ta haihu, ta samu diya, an ka sa mata Mubaraka, tun da na dawo daga yawo na, na dora ido na kan Mubaraka na ji qaunar ta ta shiga zuciya ta, na sha ji a wajen Lamishi in mai jego na samun abinci me kyawu diya na samun ruwan nono mai yawa mai kyau, daga nan na hwara siyo abinci ina kawo wa dan ta ci qauna ta ta samu ruwan Nono mai kyau, kar ta zauna da yunwa kamar yanda na yi rayuwa da yunwa.

A hankali a hankali na hwara zama gagararre, kuma mutane suka hwara sanin mi nake ina samun kuddi, ni dinnan da kin ka gane ni, na yi gidan yari, sai da ya zamana in an kama ni, 'yan siyasa da kan su, suke hiddo ni, saboda ba qaramin nasara suke samu ba in suna tare da ni.

Gwauna da ya gabata shi ne ya tsunduma ni a babbar harkar da nake ciki yanzu, shi ne ya dauki su Lamishi aikin wanke wanke a gidan, mahaifin ki kuma shi ne wanda ya hwara koya min kisan mutane, har sai da ya zamto in ban kashe mutum ba a rana ina jin kamar ban tabuka komi ba a ranar, sai da ya zama ni ke jagorantar kisan gari guda,na qone shi ni da yara na, duk bakowa ne ya maishe ni haka ba face mahaifin ki.

Mahaifin ki ya aikata min laifin da ba zan iya yahe masa ba, ya sa an sace qauna ta, an yi lalata da ita da qananan shekarunta, duk wani buri nawa da nata an rusa mana shi.

Shi yasa na yi alqawarin yanda ya cutar da qauna ta, da nafi so a rayuwa ta, ni ma sai na cutar da abinda ya fi so a rayuwar shi, na so kwarai na cutar da ke, kamar yanda ya yi ma qauna ta, amma ki sani a baya na yi zina, daga baya da na girma sosai na fara jin kyankyamin ta,se na dena, dan haka ni yanzu a duk abinda ni ke bana zina, na biyu soyayyar da nake miki ta hana ni cutar da ke ta kowace hanya, dan haka da na yunqura zan yi lalata da ke sai na kasa, Sultana ke da Mubaraka ku na da matuqar mahimmanci ga rayuwa ta, ba zan bari a cutar da ku ba, balle ni na cutar da ku da kai na.

Kamar yanda na yi miki alqawari, duk sanda ki ka ji ba ki so na, ki fadi min zan sauwaqe maki aure na, ki koma ga iyayen ki, amma fa ki sani, ba zan kyale mahaifin ki ba, sai na dau fansar abinda an ka yi wa qauna ta ta wani wajen,zaman ki anan zai banna mai rayuwa (bata masa rai) sama da yanda kike tunani, domin na zauna da shi, kamar yanda mubaraka take a waje na, haka ki ke a wajen shi"

Sultana ta ma rasa me zata ji a wannan labarin da Lawwali ya gama bata, abu daya kawai ta sani shi ne ta na son shi, alqawarin da ta masa ya na nan ba za ta sab'a ba, ta sani mahaifin ta ya fi bada mahimmiyar gudun mawa wajen lalacewar Lawwali, duk da ba shi ne ya fara b'ata shi ba,
In ba a taimaki matashin da ke da basira ba to kuwa zai illata qasa shima, kamar yanda Lawwali yake yi a yanzu.

Miqewa ya yi tsaye, ya ce,

"Wannan shi na dalilin da yasa ban kusance ki ba, ina jiran na samu yardar ki da amincewar ki, saboda ban aure ki dan sha'awa ba, na aure ki ne dan ina son ki, kuma ina so in dauki fansar abinda Gwauna ya yi wa Mubaraka na"

Shirun da ya ji, ya tabbatar masa da cewar Sultana bata yarda da shi ba, dan haka takawa ya fara yi, zai bar dakin, har ya kama hannun qofar ya ji Muryar ta da ta gaji da kuka ta ce,

"Ina zaka je ka bar amaryar ka ta na jin yunwa?"

Ta na nan kwance cikin bargon da ya rufe ta, ta ke maganar, cikin farin ciki ya juya ya na qare mata kallo, komawa ya yi ya zauna a gefen ta, ya janye mayafin da ya rufe mata gefen fuskar ta, ya shafa kuncin ta sannu a hankali .

'Daga ta ya yi kamar ya na daukan k'wai, a saman cinyar shi ya zaunar da ita,ya bata abincin, ta ci ta qoshi.

Sannan shi ma ya ci, qarfe daya da rabi na dare ya yi, a tare suka shiga dan bandakin da aka yi musu na musamman, duk da cewa na qasa ne, amma dai ba a hade yake da wanda kowa ke shiga ba.

Gani ya yi ta na alwala bayan ta wanke bakin ta, fita zai yi abin shi ta ce,

"Ba zaka yi alwala ba? Na ga baka yi sallah ba fa"

Kamar ya fada mata shi ya manta rabon da ya dora goshin shi a qasa ma, kawai ya tsaya, ya na kallon ta, bata sake masa magana ba, ta idar ta fita, ya jima a tsaye kamar ba ze yi ba, ya dau butar ya yi alwala, ya bi bayan ta.

Babu abin sallah a wajen, a saman carpet din wajen ta tsaya, ta ce

"Bismillah ka ja mu, muyi sallar isha'i, dare na yi, kar lokacin ta ya fita"

Shafa kan shi ya yi, ya zauna a bakin gado, ya ce,

"In ma na yi sallah yanzu ba zata karbu ba sultana basshi kawai ke ki yi sallar ki, na tabbata Allah zai karb'i taki, saboda baki zamo daga mutane iri na ba"

Gyara zama ya yi a saman gadon ya kwanta.

Mamaki ne danqare a cikin zuciyar Sultana me yake nufi da hakan???.......

*Hummmm hummmm*

๐Ÿ’…๐Ÿป *A GARIN MU* ๐Ÿ’…๐Ÿป

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 45:

A daren ranar haka Sultana ta na ji ta na gani, mijin da ya ke nata ya kwanta bai sallah ba, ba ta samu bacci ba sai da ta yi sallolin ta, sanan ta roqi Allah da ya shiryar mata da shi, a da in ta ga bai sallah ba sai ta yi tunanin ko ya yi a waje kafin ya je wajen ta, ko kuma zai yi in ya koma gida, amma tabbatar mata da ya yi, ya jima baya sallah abun ya daki zuciyar ta, mummunan duka kuwa.

A qasan carpet din ta kwanta, har bacci ya dauke ta.

Cikin dare ya tashi zai zaga, ya gan ta a qasa, bai tashe ta ba sai da ya zaga can wajen yaran shi, ya ga kowa na lafiya, masu gadi na aikin su, masu bacci na baccin su, sannan ya koma daki, a inda ya barta nan ya same ta, tashin ta ya yi, cikin magagin bacci ya taimaka mata ta kwanta a gado, suka ci gaba da baccin su.

Da asuba Sultana bata tashi ta ga Lawwali ba, sannan ta yi mamakin ganin ta a gado, dan dai ba zata iya tuna sanda ta hau da kan ta ba.

Lawwali bai shiga dakin ba har takwas na safiya ya gota, sultana ta yi wanka, ta gyara gadon da suka kwanta, ta dauke ledar da suka ci nama ta leqa waje ta wurgar, ta na hango yanda mutanen wajen ke ta mu'amalar su, kamar ba abinda ya dame su, ba alamar tsoron wani abu, ko fargaba a tattare da su, daga nan inda take, ta ke hango yanda suke bin layi su Barirah su na zuba musu abinci, wasu kuma na zaune a dandaryar qasa, sun kama kai, da alama a wajen suka kwana, sun shawu sun yi tatil, sun kuma tashi da ciwon kai.

Daga nesan ta hango Lawwali da wasu zaratan mazaje a wani fili, ya na koyar da su fad'a, kura ma jikin shi da babu riga ido ta yi, daga baya ta sauke ajiyar zuciya, ta juya za ta koma ciki, d'an dakatawa tayi, a daidai lokacin da ta kula ba ita kadai bace ke kallon surar jikin Lawwalin, wasu 'yan mata ne zaune riqe da plates da cups na abinci da suka karba,sun Qura wa jikin mijin nata ido, kamar su jawo shi gare su .

Sultana tunda take bata taษ“a jin wani abu mai zafi da ciwo a qirjin ta mai kama da wannan ba, da sauri ta fada dakin ta, ta dauki mayafin rigar ta, ta zira takalmin ta, ta tafi inda Lawwalin yake,tafiya take cikin sauri, ta na kartar qasa da takalmin ta, saboda yashin da ke wajen, bata saba da tafiya cikin yashi haka ba, har qoqarin faduwa take amma haka ta isa gaban Lawwali, duk idon mutanen da ke wajen ya koma kan su.

Cikin tura baki ta ce mishi.

"Ina ta neman ka tun dazu ban gan ka ba, ashe ka na nan ka na bude musu qirjin ka su nata kalla ko?"

Dan had'e girar shi ya yi, cikin rashin fahimta, su wa ya budewa qirjin shi? Juyawa ya yi, ya ga yanda wasu matan ke kallon shi, to indai wanan ne ai ba yau aka fara ba, shi be ma dauki wannan wani abu ba, kallon yanda take ta tura baki, ta na babbata fuska yake, a hankali murmushi ya fara maye gurbin hade fuskar da ya yi.

Hannayen shi biyu ya sanya ya daga ta sama, ita kuma wata iriyar kunya ce ta kama ta, sai da ta yi da ta sanin zuwa wajen shi, da ta sani ma aikawa ta yi aka kira mata shi, yanzu wannan abun kunyar da ya ke qoqarin ja mata fa?

Dariya wajen ya dauka, dan ganin yanda take ta dukan qirjin shi, ta na wutsil wutsil da qafa, Ita dai ya sauke ta qasa ya saka rigar shi, shi ne burin ta,

"Ran ki shi dade, nan wajen da ki ka gan su, duka qanne na ne, ba wadda nika so, ko ta ke so na, su na d'ai so na a matsayi na na shugaban su, kuma yaya a wajen su, ki kwantar da hankalin ki, jikin ga naki na ke dai,"

A hankali suke magana, wanda ba lallai ne na gefen su ma ya ji me suke fad'a ba, iya burgewa kawai sun gama burge mutanen wajen.

Kwantar da kan ta tayi a kafadar shi, ya sassauta riqon da ya mata, su na dariya, baki ta dan tura, ta daga kai ta kalle shi ta ce,

"Ni dai ba na so ka na zama ba riga,ko vest ne ka na sawa pls"

"Ok"

Ajiye ta ya yi, ya dau rigar shi, ya rataya a wuya, ya ja ta, zasu koma ciki, matasan da ya ke horar wa sun zaci tafiya za su yi, suka ji ya ce,

"A ci gaba sai 10am, a tashi"

Ba bata lokaci kuwa suka ci gaba, shi kuma ya shige dakin su da matar shi, mai kishi.

Matan wajen wasu sun ji haushin yanda ta dauke musu shi, wasu kuwa ta burge su, yanayin yanda take shagwaba da jan ra'ayin ogan nasu ya basu sha'awa, basu tab'a ganin shi a irin wannan yanayin ba.

Su na shiga ya jingina da bakin qofar ya wurgar da rigar shi, ya tokare qofar wajen da hannun shi daya, dayan kuma ya sa shi a qugun shi ya na kallon ta.

"To Sultyn Lawwali, ga Lawwali gaban ki, ki kalla har sai ke ce ya isa haka nan"

Rufe fuskar ta tayi, ta ce,

"Ni fa ba haka na ke so ba"

Takawa yayi gaban ta, ya zauna daf da ita, ya na kallon fuskar ta da ta rufe, ya zare hannun ta ya dora a qirjin shi, ya ce,

"Haka ki ke so to?"

Da sauri ta janye ta miqe tsaye, cikin shagwaba ta sa kukan da ba ko hawaye ta ce,

"Ni fa yunwa nake jiii"

Da sauri ya nutsu, sai a sannan ya tuna ba fa a kawo musu abinci ba, su Bareerah ya sa su dafa abincin da zata iya ci, kuma har yanzu shiru.

Ran shi b'ace ya sanya rigar shi ya tafi wajen su, su na tsaka da gyara cups din da suka dora musu a farantin ya isa.

"Mi da ba ku kawo abincin ba tun dazu?"

Cikin ladabi da kuma ban hakuri, suka masa bayani, ba ta iya irin abincin da ya ce a yi ba, sai da suka nemo wadda zata koya mata, sakin fuskar shi ya yi, ya musu godiya, ya karba da kan shi, zai kai, a tsorace Bareerah ta riqe farantin, ta na bashi hakuri ko da ta yi wani laifin bata sani ba,

"Yaseerah da Barirah tsakani na da ku sai godiya, na dai hi so na kai mata da kai na ne, amma ba ku yi min lehin komi ba, na gode, ku tai ku ci abincin ku"

Godiya suka yi, ya tafi, hira suke a tsakanin su, Barirah ta ce,

"Walle na hankura, da gani nike kamar Oga na so na, tunda ba shi yi min hwada, kuma komi nicce ya na yi, ko ya bari, ban dai iya shiga tsakanin shi da matar shi, yanda ya ka son ta haka, kallo ma ba zan ishe shi ba"

"Ai na fada maki tun hwarko, da ya na son ki da ko so guda ne, da ya maki maganar, kin dai ga yadda kowa ke da budurwa wajen ga, a manyan nan, sai wanda suke da mata ne kadai basu da budurwa, ai da ya na da ra'ayi da ya yi magana"

"Kaiii mu je mu ci abinci yunwa ni ka ji wallah"

A can dakin su Lawwali kuwa sun ci sun qoshi, sai suka tsaya hira abun su, ranar dai ba wanda ya sake ganin Oga sai azahar.

Ya na ganin za ta yi sallah ya bar dakin, takaici duk ya dami Sultana, wato ba ma ya so ta masa maganar sallah ko? Ba komai za su hadu ne, shi ma abinda ta kula ya na kwadayi tsakanin safiya da azahar dinnan ba zai samu ba.

***************************

Da yamma motar gidan su Hansatu ta tsaya a qofar gidan su Isah, driver ne ya yi ta doka sallama, kamar an mintsini 'Yabbuga ko an kira ta haka ta bar majalisar su data cika da su Lamishi, ana hirar bikin Lawwali, da takura wa Lamishi ta kai su gidan Lawwalin su ga gida, yau ma Mai Buruji ce ta yanka qarya tace sun tafi qasar waje, fadawa gidan Hansatu 'Yabbuga ta yi kamar an aike ta, ta na ta kwala wa Hansatu kira,

"Ke hito, motar gidan ku ta taho, ana ta bidar ki,kin qule a qurya,"

Hansatu ce ta miqe daga kwancen da take, cikin duhu, share hawayen ta tayi sosai, yanda ba za a gane ba, ta daura dankwalin ta, ta gyara doguwar rigar ta, da Hajiyan ta ta dinka mata, ta fita.

"Wane na ka bid'a ta?" (Wa ke nema na)

"Nace maki motar gidan ku ce ta taho, ana ta miki sallama ba ki jiya ba"

"mu je, gani nan zuwa"

Hijabin ta ta sanya, ta bi bayan 'Yabbuga da ta qi tafiya, sai ta ga kwal uwar daka.

Bayan sun gaisa da driver ne ya ce Hajiya na gaishe ta, ta kuma bada saqo a kawo mata, ga takarda, ga kuddi, ya zaro ya miqa mata.

Fita ya yi ya dinga shiga da kayan da ya zo da su, sai daya gama tass, ya ce

"Ta ce ki na ganin bayanin komi cikin takardar, abinda baki gane ba ki mata waya"

"Tauu ya yi Malam Jafaru, ka gaishe ta, na gode"

Sallama ya mata ya tafi, 'Yabbuga kuwa majalisar da bata koma ba kenan, Hansatu kuwa kayan da bata bude ba kenan, dan bata san mene da mene ba, kar ta bude gaban ta ya zamana bai kamata ta gani ba.

Har sai da suka ji Machine din Dan Jumma sannan ta fita a gidan ta na b'ata rai.

Ta na fita kuwa ta sa su Ameena suka shigar da kayan parlour suka rufe qofa, cikin ladabi Ameena ta tattare kan qannen ta suka bar wajen, ta ji dad'in hakan sosai, albarka ta sanya musu, sannan ta bubbude kayan, har da akwati qarami.

Kaya ne na sanyawa kala biyar, sai rigunan bacci, da undies ,takalma biyu, da turaruka kala kala, har da musk.

Sai dabino mai kyau mai yawan gaske, sai kayan qamshi, da bagaruwar mataa danya, ganyen magarya, da lalle .

Kaiiii makaranta abubuwa ne masu tarin yawa Hajiya ta aiko mata, har da kayan abinci da nama soyayye.

Hansatu ta na dubawa ta na godiya ga Allah, tare da sanya wa mahaifiyar ta albarka, da yi mata fatan samun cikawa da kalmar shahada.

Takardar ta bude ta karanta kamar haka.

~Hafsat ina fatan ki na lahiya da jikoki na? Na san dai mijin ki ya sanar da ke shi na nan dawowa qarshen wanga sati, to ga kayayyaki nan,ki yi amfani da su yadda na nuna maki rannan da ki ka taho, sannan wannan bagaruwar da ganyen magaryar, ki na diban bagaruwar kadan da ganyen magaryar ki tafasa ki zauna ciki, amma a yanzu ki dauki bagaruwar danyar ki matse ruwan ta ki liqe a wannan haqorin da ya bule-

Ta na gama karantawa ta dinga dariya,dan ta gane haqorin da Hajiyan ta ke nufi,Hajiya akwai hikima, ta tuna sanda take mata complain din ta na jin gaban ta kamar ya bude, shi ne Hajiyan ta yi wannan dabarar,dariya ta dinga yi, sanda ta tuna, wani lokaci kafin auren ta, an yi auren qanwar Hajiyan, sai suka je gidan, suka shiga har dakin amaryar suka ga gadon amaryar duk ya ษ“aci, ta na ganin Hajiya na kallon wajen, sai ta cire dankwalin ta ta rufe wajen, ta na ta jin kunya.

Bayan sun koma gida sai Hajiya ta haษ—a dankwalaye ta bawa Hansatu, ta ce ta kai ma auntyn ta ta ce mata, in ji Hajiyan wai ta yi amfani da dankwalin nan ta rufe saman gadon nata saboda qura, amma da zata cire ta wanke qurar da ya fi.

Sai bayan ta yi aure a washe garin daren ta na farko ta fahimci me Hajiya ke nufi da hakan.

Ta na tsaka da dariya ta koma kukan baqin ciki, Wannan wace iriyar rayuwa take ciki? Wai ace mijin ka bai damu da kai ba, yau kusan watan shi daya da tafiya, ba kira ba saqo, sai dai ta ji maganar shi a bakin mahaifiyar ta, ba komai, za ta bashi mamaki.

Tattare kayan ta yi, ta ware duk wanda ya kamata ta ware, sannan ta kira su Ameena ta deba musu soyayyan naman suka ci, cikin nishadi.

**************************

"Ni fa Sultan ban san me ke faruwa ba, yau kwana biyu kenan, ina kai qawaye na gidan su Sultana Amma ina ganin gidan a ruhe ,shin lahiya? Ko ba kuyin waya ne kaima? Dan ni dai na kira layin ta ba shi shiga"

"Ni ma dai layin nata bai shiga Hajiya, amma na san duk inda take ta na tare da mijin ta, kar ki damu"

Ai sai a wannan lokacin ne hankalin ta ya shiga jikin ta, a zabure ta miqe, ta hau kiran layin Gwamna Halliru, ta kira ya fi sau hudu ana sanar da ita ya na meeting,daga qarshe masifa ta balbale mai amsa wayar ta ce ya kai ma gwamna wayar shi, ba ruwan ta da wani meeting ita.

Yanayin yanda ta daga hankalin ta ya bawa Sultan Mamaki.

Mene ne abun damuwa dan an ce mace na tare da mijin ta ba kwarto ba????......

*Gane min hanya Sultan, wai makaho ya so gulma*


๐Ÿ’…๐Ÿป *A GARIN MU* ๐Ÿ’…๐Ÿป


BY HAERMEEBRAERH



PAGE 46:


Fitowar gwamna Halliru daga meeting ba wuya, Hajiya Ikee ta sake kiran wayar, da sauri aka miqa masa ya karba, bayan ya amsa ne ya kara a kunnen shi,jin Muryar Hajiya cikin tashin hankali ne ya sanya shi matsawa daga cikin mutane, ya fara tambayar ta dalilin tashin hankalin ta, Sultan ta kalla wanda ya dauki remote ya na sauya tashoshi hankali kwance, ta ษ—an matsa daga inda yake, ta fara magana.

"Sultana fa da wannan shegen yaron ba su gidan su,ni ina jin tsoro musamman tunda ka ga basu fada muna inda su ka tafi ba, Kuma gashi ba a samun ta ga waya"

"Kwarai da gaske yau nake so na tambaye ki ko ku na waya, ban samu dama ba, tunda ban kwana gidan ba, amma abin ya na dauren kai ace ba ta kiran kowa, bari zan bincika in ji, ki kwantar da hankalin ki, kin dai san ba yarinya bace ke, tunani kadan zai sa miki ciwo"

"Wai kai in ba ka fadan baqar magana ba baka jin dadi ko? To ai na san ba yarinya ni ke ba, ba se ka maimaitan ga kunne na ba"

A hasale ta kashe wayar ta koma ta zauna,

Please Login or Register in order to submit comment