Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuba a idon Sultana,tare da jin qauna da soyayyar mubaraka na ratsa ta, tabbas wannan dalilin na cikin dalilan da ya sa Lawwali ke son ta, ta na da hankali da hangen nesa.

Lawwali bai ce komai ba ya bar su a tsaye a wajen,ya tafi dakin shi ya dauki wayar shi da ya manta, ya shiga cikin daji sosai, dan so yake ya yi nesa da su, ya na so ya kad'ita.

*Ohhhh Oga akwai son kai, dake Mubaraka ce ya yi shiru, amma da zai kai wa yar mutane duka😏*
πŸ’…πŸ» *A GARIN MU* πŸ’…πŸ»


BY HAERMEEBRAERH


PAGE 55:



Mubaraka da Sultana kuwa d'aki suka koma, bayan Mubaraka ta taimakawa Sultana ta zauna a bakin gado, Sultanan ta kalli Mubaraka ta ce,

"Mubaraka me yasa kin ka yi wa yayan ki qarya, bayan a kullum shi na yabon ki akan rashin yin qarya? Me ki ke tunani in ya gano baki da hannu a abinda ni na aikata ba ke ba? Gashi yanzu kin rusa muku tafiyar da ki ka jima da burin ki na son ya amince ku yi,"

"Babu komi aunty na,nasan ba zai iya kwana shi na hushi da ni ba, zai sakko ne, ni kuma ba zan iya jure ganin ki cikin halin baqin ciki ba, zai fahimce ki, bashi lokaci ya yi tunani, haka yake, ya na da saurin hushi, amma da ya fahimci gaskiya ya na saurin sauka"

"Allah ya sa ya sauka da wuri, ba zan iya jure fushin shi ba, amma me ya sa kuka dawo?"

"Waya tai yam-mance, shi na mun ka dawo dauka, ya shiga dakin yaga waccan locker a bude, shi ne na ga hankali nai ya tashi,ya na neman ki"

Murmushi Sultana ta yi, ta kalli Mubaraka ta ce,

"Na gode"

Su na nan zaune kamar marayu ya dawo, a rayuwar Lawwali ya tsani rashin cika alqawari da cin amana.

Ya san ya yi wa Mubaraka alqawarin kai ta gida,ga kuma Sultana ta ci amanar shi, dan haka dole ya dau mataki,

"Ki taho mu tai,...ke kuma na janye zuwan ku gida a gobe, har sai na gano gaskiya game da abinda kin ka yi min"

Murmushi mai quna ta yi, akwai zafi, wanda ka ke so, ka yarda da shi ya zama shi bai yarda da kai ba.

"Babu komi, Allah ya sa ka gane irin son da nake maka, ba zan yi komai dan na cuta maka ba"

Kallon cikin idanun ta ya yi, nan da nan na shi suka fara sanyi, da hanzarin shi ya bar dakin,tare da fadin

"ki taho mu tai"

motar shi ya shige, ya na zaune ya na jiran Mubaraka, qasan zuciyar shi na ayyano masa fuskar Sultana,mai cike da ban tausayi, da tsantsar soyayyar shi, ba ya so ya yarda da cewar amanar shi ta ke son ci, amma ya kasa dauke hankalin shi daga abinda ta yi din, anya ba da gaske saboda Daddyn su ta qona ba?

Mubaraka ma bata b'ata lokaci ba ta bishi , ta na shiga ya bar wajen da gudu, ta waya ya bada umarnin a shiga wajen Sultana a duba ta, a ga me ya sa ta ciwon ciki.

Sun isa gidan Dan Talo da misalin sha daya na rana, har a wannan lokacin mazaje masu zaman banza na zaune, a jikin katangar gidan,a jingine da gini, su na shan hantsi, ana ta zuba qarya,domin abun na su ya wuce hankali .

Hango mota mai kyau suka yi ta na tunkarar su, nan da nan kuwa a cikin su aka samu wani maqaryacin ya ce ai ya taba ganin me motar har sun ma gaisa rannan, wasu sun yarda wasu sun qaryata, tunda sun san junan su.

Dan Talo dai sai gwale ido ya ke, ya ga mamallakin motar, domin dukkan alamu sun nuna gidan shi motar ke tunkara, nan da nan kuwa ya miqe ya kade rigar shi da ta fara nannadewa saboda yawan zama da ake akai.

Mota na qarasa tsayawa a gidan shi ya karkata kai ya na kallon motar har sai da su Mubaraka suka fito, ba qaramin jin dad'in hakan ya yi ba, nan da nan kuwa ya yi gyaran murya, da qaramar dariya ya ce,

"Dama k'yale ku ai niyyi, ku qarqare qaryar ku, tun subahin munkayi waya da su suna tahe, Mubaraka ta dawo daga qasar waje, sanda na fadi maku ta tai qasar waje karatu mi kun ka kira ni? Zubairu ko? Tauuu yanzu wa ka qarya ni da ku? Nan nan gaba gare ku, gwauna ya aiko a basuwa hoton yarinyar ga za shi yi mata miji, kun ka qaryata ni, tauu ga dai shi ta dawo ko?"

Wani fad'i ya dinga yi, ya na qobarewa, shi a dole mai gaskiya, kuma yaran shi sun dangwalo azziqi.

Ya na daga cikin sharadin Lawwali kar Mubaraka ta kula kowa a waje, in ya ce kowa ya na nufin kowa, sai sun shiga gida.

Dan Talo na ta washe baki, ya na musu barka da zuwa, Mubaraka ta yi wuf ta fad'a gidan, Lawwali kuwa yanda ya daure fuska kawai ya isar wa da Dan Talo babban saqo, su na shiga ciki suka ji hayaniya kamar za a d'aga gidan, qarasa tsayawa suka yi a qofar shiga gidan, Lawwali ya nade hannun rigar shi, ya zuba hannayen shi a qirjin shi ya na kallon su, 'Yabbuga ta fi kowa zaqalqalewa, Lamishi kuwa ta yi kalar tausayi,yau ko masifar ma ta kasa.

"....An fadi d'in barayin banza barayin wofi, talauci ku kad'ai ke fama da shi? Daga zuwa bukin suna sai a nemi atamfa a rasa? To waye ya dauke ta in ba ku ba? Tunda ku na amince ku zauna qofar mai jego kar dangin mijin ta su shiga suyi sata, to walle biyan ta za ku yi, dan ba bar maku za mu yi ba"

" 'Yabbuga ni ta ce fa Lamishi, aminiyar ki, ni ki ka wa d'iban albarkar ga? Akan atamfar da ko dubu biyat bata kai ba? Ke mance har kyautar Suhwa (super) sai da na miki? Ranar bikin yaron nan ba abinda baki sata kin kai gidan ki kin boye ba, ko aza ki kai bamu sani ba? A gidan nan kin sha zuwa ki ci abinci ki qoshi ki tai, wa ya taba cewa ki biya?"

"Ki na barin yi min gori ki biya ni atamfa ko sai na maki d'iban albarka yanzun ga?"

Haushi ya gama cika Dan Talo, dan kuwa su na b'ata masa lokaci, ya matsu a gama gaggaisawa, in Lawwali zai tafi a bashi dan wani abu, kutsawa zai cikin gidan Lawwali ya dakatar da shi.

Jikin katangar gidan nasu da ba ta wani cika tsayi ba Lawwali ya jingina,ya ci gaba da kallon haukan da suke.

Mubaraka ta rasa me zata yi ta jawo ra'ayin su, ta na tsaka da tunani, ta tuna me ya kamata ta yi, magana ta fara qoqarin yi wa Lawwali, kawai sai ta hau tari, ta dinga tari ba qaqqautawa, nan da nan kuwa hankalin Lawwali ya tashi, ga hayaniya ta masa yawa, ya na ma tambayar Mubarakan me ya same ta ba ta ji, da ya juya ya daka musu wata gigitacciyar tsawa, gaba dayan su suka juya a matuqar firgice, su ka kalle su, shi kuwa da ya ji an yi shiru, kama Mubaraka ya yi ya na tambayar ta lafiya take tari?

"Yah Auwal zan....sha...ruwa, tari na ya sarqe ni,"

Da sauri ya fita mota, dan dakko mata ruwa,hankalin 'Yabbuga in ya fi cikin garin Zamfara to ya tashi, rasa inda zata saka kan ta tayi, Lamishi kuwa me zatai banda dariya tace,

"Shi kenan ma, tsaya ki karbi kuddin atamfar ki da ki ka mana sharrin sata,"

"Habaa Lamishi, ke ba ki san wasa ba halan, wasa ta ni kai miki, bari ma ki ga na tai gida, Dan Jummaa bai ko hita aiki ba"

Ta sa kai zata bar gidan kenan taga Lawwali na dawowa, da ihu da kururuwa ta koma ciki, ta ja turmi, ta haye katangar gidan, ta dira a maqota, duk kurjewar da ta yi bai dame ta ba, maqota kuwa na ganin mace ta dira cikin gidan su,suka d'iba da mugun gudu, kowa na takan shi,basu san me ya diro da ita ba, ko ta kan su bata bi ba, ta arce sai gidan ta.

Lamishi da Mai Buruji na ta sheqa dariya.

Mubaraka ta shiga suka hau dariyar a tare, ko da Lawwali ya shiga ya gan su tare sai ya juya ya yi d'akin shi.

Duk dakin ya yi matuqar yin datti da qura, duddubawa ya yi duk an dauke masa abubuwa masu mahimmanci, har kayan sawa da takalmi.

Ya na nan tsaye ya na tunanin rayuwa, ya dinga jiyo dariyar su Mubaraka, da mahaifan nashi,can kuma ya ji Mubaraka na bada hakuri, da sauri ya bar dakin ya fita.

"Menene ke faruwa?"

Cikin qoqarin maida kwallar ta ta ce,

"Babu komi"

A tsawace ya ce,

"Menene na ce? Waya tab'a ta?"

Lamishi ce ta ce,

"Yo gani nayi ta dawo daga tahiya ba ko tsaraba, hannu na dukan cinya, kuma dai nasan bata kasa sanin irin halin talaucin da muke ciki, abinci ma gagarar mu shi kai, dan rashin tausayi irin naku, kun bi duniya kun....."

Kallon da Lawwali ke mata ne ya sa maganar ta maqalewa a wuyan ta, Dan Talo kuwa ji yake kamar ya buga mata mari sai kumatun ta sun fi na Hameeda tashi (lols) duk za ta bata masa shirin qorafin da yake tafe da shi a lissafe, yanzu in ran shi ya Ι“aci ya fita a hasale wazai bashi sisi?

"Wai ku yaushe ne za ku yi hankali?....shin dan Allah na tambaye ku, ku ne iyayen mu kuwa? Kun san ma'anar haihuwa kuwa? Kun san wane ne d'a ko d'iya kuwa? Ina su Jameelu? Ko kun san ina da labarin irin barnar da su Jameelu suke yi yanzu na sace-sacen kayan mutanen unguwa? Iyaye kala kala ne a duniya tabbas, akwai iyaye nagari, masu kula da d'iyan su, ta bangaren ,ciyarwa,tarbiyya,tuwahi,ilimi, da duk abinda ya kamata, Sannan akwai iyayen banza, irin ku, baku kula da tarbiyyan d'iyan ku, ballantana abinda za su ci, ba ku san ku basu ilimi ba, balle sutura, da ku da iyayen da ke kai d'iyan su almajiranci,ba su san cin yaran su ba, balle shan su, ba su san a wanne hali suke kwana ba,da ruwa da sanyi da zahi, ciwo da halin qunci, duk basu san ya d'iya suke ba, baku da bambanci,duk d'aya kuke, a zato na tunda kun ka ga baku gammu ba na tsahon wannan lokacin, za ku neme mu, za ku damu, ku na nan ba ma cikin ran ku ma, burin ku, mu je mu kewayo, mu kawo maku kuddi ko? Kuddi kuka so ko? Yunwa kuka ji ko? Ina zuwa"

A haukace ya nufi garken awakin Dan Talo, ya bude su, sun kai guda tara, ai kuwa suka fita a guje, Dan Talo na ihu, Lamishi na Ihu,dan akwai uku nata a ciki.

Har qofar gida ya raka awakin ya kalli abokan Dan Talo ya ce,

"Duk wanda ya kama shi tafi da su gidan shi, na bashi,"

Ai kuwa kamar qananan yara haka dattijan nan suka kwasa a guje su na bin tumakin nan, Dan Talo kuwa sai fadi ya ke ya na kumawa

"Walle ban bayar ba, ku bar min bisashe na"

Komawa Lawwali ya yi ya ce,

" kun gane ta nan, ta san darajar ku, ta na son ku, ta na qaunar ku, shi ne dalilin da yasa ta dage sai mun taho ta gan ku, kun san me nake aikatawa, amma ko a jikin ku, ita kad'ai ce ta damu da yi min nasiha, da addu'a dan na bar abinda ni ke, ku fa?....kun san me, ba zan taba yahe muku ba har abada, sai Allah ya tsai da mu a gaban shi, ya ji dalilin da yasa ku ka haife mu, ku ke walaqanta mu, ku ka barmu a lalace haka, sai Allah ya saka muna, ba iyaye na taqama da tsinuwa ba, komi ta yi maki, mai kyau, ko kure ki tsine mata, ki hada ta da mummunan kalami, ke san me ya same ta a dalilin kalaman ki?...."

Da sauri Mubaraka ta zube a gaban shi, ta na kuka,ta na bashi hakuri akan kar ya tona mata asiri, dan kuwa tonon asiri ne wannan, tun da ta san iyayen ba wani son ta suke ba.

"Bari na sanar da ita fatan da take maki kullum na kiyi gantali, baki yi gantali ba,gantalin ne yasame ki, inda ki ke, ko ke san cewa an yi mata fyade? Ki na da labari ko baki da shi?"

Mubaraka ce ta rushe da wani irin kuka mai matuqar ban tausayi, shi kan shi bai san hawaye na zubar masa a idanun shi ba, zuwa jikin rigar shi, tsabar qarfin fitar su.

Bai san ya zai fahimtar da su, ya yake jin baqin ciki a cikin zuciyar shi ba, duk wani irin bayani da zai yi ba zai bayyana yanda ya tsane su ba, Dan Talo da ya shigo ya ji kalaman Lawwali sai da ya zauna dabar a qasa, Lamishi da Mai Buruji Kuka, Mubaraka kuka, dariya Lawwali ya yi ya share hawayen shi ya ce,

"Lallai ku na da abun mamaki, menene kuma na kuka? Fyaden da an ka yi ma diyar ku? Ko kasancewar d'an da kun ka haihwa na kisan mutane da hannayen shi? Ko kuwa salwantar da rayuka da dukiya, da mahallin mutane da gudan jinin ku ke yi, shi ke sa ku kuka?

Barakana tashi mu tai, mun ji, mun amince, ku ba iyayen mu bane, mun yarda ba ku son mu, ba ku damu da mu ba, za mu rayu ko ba ku, mun kuma godewa Allah da ya nuna mana gaskiya, dan haka ku zauna ku ci gaba da rayuwar da kuke kamar ta dabbobi, yau ko dabba ta haihi d'a ta na so nai, ta na kare shi daga miyagun da za su cutar da shi, ta na bashi abinci, amma ku...ku ban san mi zan kira ku da shi ba"

"Yah Auwal ya isa haka, kar ka je ka jawo Allah ya yi hushi da kai, Iyaye na da girma da daraja, dole ne mu kyautatawa musu, ko muna so ko bama so, ko da basu zamo nagartattu ba, ko da kuwa kahirrai ne, ka yi hankuri mu tafi, kar ka hwadi kalmar da zata sanya Allah shi yi hushi da kai, duk yanda suke iyayen mu ne, dole mu yi musu biyayya"

Kallon Dan Talo ya yi, ya ga yanda ya ke ta kuka, shi abun ma dariya yake bashi, to kukan me suke?

Kudi ya kwaso a aljihun shi ya wurga masa, Mubaraka ta yi saurin kama hannun shi, ta na hana shi wulaqanta iyayen shi,domin ta ji wa'azi sosai akan girman iyaye,durqusawa ta yi ta na kwashewa ta na zubawa Baban nasu a jikin shi, a ladabce, wajen su Lamishi ya je ya wurga masu kudi suma, sanan ya kalli Mai Buruji ya ga yanda take kuka sosai.

"Ki dena kuka yanzu, kuka na tahe zuwa nan gaba, ba dai kin biye mata ba, dan kar ta dake ki, yanda kuke yi a baya, ki sha kashin banza, shi ne ki ke qin yi wa diyan ki tarbiyya ko? Ta saki nata sun bi duniya, kema kin saki naki ko? Da kyau, kuka na nan tahe, ki bar taya ta kuka, naki na tahe,"

Kama hannun Mubaraka ya yi, suka bar gidan, cikin tsananin fushi, basu zame ko ina ba sai gidan da ake ajiyar No 1........................


*Jama'ar kwarai gobe ranar Arfa..dan Allah kar ku manta a ajiye duk wasu ABUBUWAN da ba su da mahimmanci kamar yanda alhazai suke can Makka suke kwasar lada mu ma mu kwashi namu a gida, a yawaita karanta LA'ILAHA'ILLAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHULMULKU WALAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADEER.*

*Happy sallah in advance love you mutanen kwarai*



πŸ’…πŸ» *A GARIN MU* πŸ’…πŸ»

BY HAERMEEBRAERH



*Assalamualaikum barkan ku da sallah 'yan uwa musulmi...Allah ya maimaita mana mai yawa mai albarka...Allah ya karbi ibadun mu...ina nan ina jiran barka da sallah naπŸ˜ƒβ€οΈ*

PAGE 56:

Mubaraka dai na zaune a mota, har wannan lokacin ba ta daina sharar hawaye ba, hawayen da ke zubo mata daga can qasan zuciyar ta ya ke tahowa, rayuwar da suke ciki bata da suna, balle fassara, ina ma ina ma su na da iyaye na gari? Lallai da ba wanda zai fi su jin dad'in rayuwa ,amma inaaa, rayuwa na ta gara su, duk inda ta kad'a can take kai su, su kuwa bin ta suke a koda yaushe.

Hanyar da ya ke shiga sabon waje ne a wajen Mubaraka , Ita dai nata ido, bata ce komai ba, har suka tsaya a wani madaidaicin gida.

Fita ya yi, ya zagaya ya bude mata qofar, sannan ya kama hannayen ta biyu, ya tsaida ita a gaban shi, fuskar ta ya d'aga ya na kallon cikin kwayar idanun ta, hawaye ya gani kwance su na rige rigen fitowa, wani abu me zafi da rad'ad'i ya ji a zuciyar shi ya na dukan shi , cikin kad'a kan shi ya ce,

"Ya isa haka nan, daga yau in shaa Allahu ba ki koma yin kuka Barakana, indai su ba za su so mu kamar kowanne iyaye ba, na maki alqawalin zan so ki kamar yanda iyaye nagari ke son d'iyan su, zan so ki kamar yanda yaya nagari yake son qaunar shi, Barakana duk abinda ki ke so na zamo miki ni Lawwali na maki alqawalin zama shi, abu guda ni ka so wajen ki, shi na ki dena kuka, ban san ya zan fahimtar da ke kukan ki ke yi min ga zucciya ba,"

Kwantar da kan ta ta yi a qirjin shi, ta qanqame shi, ta na jin dikkan soyayyar da ya lissafa na shigar ta, tabbas Lawwali babbar katanga ce a rayuwar ta, bata fatan abinda zai raba ta da shi duk duniya, za ta yi ko mene ne da bai sabawa Allah ba dan ganin ta tabbata tare da shi cikin farin ciki.

Kama hannun ta ya yi, suka shiga ciki, yaran oga na ganin shi suka hau fara'a, domin tun kan ya zo ya sanar da kowa shirin shi, ya kuma yi wa kowannen su alkhairi, No 1 aka kira ya fito, gaba daya Mubaraka bata gane shi ba, dan kuwa ya zama gurgu, ya daku matuqa, ya azabtu, duk jikin shi ya nuna alamar wahala da gajiya da azabtuwa.

Godiya ya yi wa Lawwali da ya kauda kai daga ganin shi, ba dan alqawarin da ya yi na dena kisa ba, tabbas da No 1 ba zai bar wajen nan da rai ba, amma ko gurgantakar da ya samu a qafar shi ta hagu ta ishe shi tuna abinda ya aikata har qarshen rayuwar shi.

Kallon da ya kure Mubaraka da shi ne ya sa ta gane ko wane ne, ai kuwa da sauri ta labe a bayan Lawwali, Lawwali kuwa a harzuqe ya kai masa shaqa,

"Shin kallon mi ka kai mata? Ba ka tahiya sai na sauya ra'ayi na na sa harsashin bindiga na hwashe ma kai?"

Da sauri Mubaraka ta riqe hannun shi, amma har a wannan lokacin bata fito sosai inda No 1 zai gan ta ba, ta na labe a bayan Lawwali, hakan ke baqanta ran Lawwalin, No 1 kuwa zubewa ya yi a guiwowin shi duka biyun, ya duqar da kan shi,sai da mubaraka ta saki qara ta yi baya ta sake qanqame Lawwali.

Hakuri No 1 ya fara bata, cikin wata iriyar murya mai son yin kuka, Lawwali ne ya janyo Mubaraka gaban No 1 ya ce,

"Sanya ijiyar (idon) ki cikin na shi, ki gan shi a qasqance a qasa a gaban ki,ba shi iya miki komai wallah, in har baki dena jin tsoro nai ba zan kashe shi yanzun nan, dan ba zan bar abinda ki ke tsoro ya ci gaba da yawo a doron qasa ba"

A hankali ta fara jin tsoron No 1 na barin jikin ta, ko dan kar a kashe shi, dole ta ware, sai da Lawwali ya ga Mubaraka ta daina kyarmar da take sannan ya sa aka tusa qeyar No 1 ko na mota ba wanda ya bashi, ya na ji ya na gani aka rufe gidan,aka bawa Lawwali key, suka shige motocin su suka bar shi a wajen.

Su Lawwali basu tsaya a ko ina ba sai asibiti.

"Yah Auwal waye ba lafiya?"

"Mu tai ki na ganin ko waye"

Asibiti ne na hamsaqai, riqaqqun masu abun hannu, Mubaraka sai kalle kalle take, sai da Lawwali ya samo dakin da za su, ya ja hannun ta suka tafi, 'yan sanda ne guda biyu a bakin qofar dakin, su na tsaron wajen, Lawwali bayani ya musu da cewa shi surukin mara lafiyar ne, sannan suka barshi ya shiga.

Hajiya Ikee na ganin shi ta tafi da sauri cikin kuka ta tsugunna a gaban shi,

"Dan Allah Lawwali ka yi hankuri, ka yahe muna, ka tausaya wa halin da Daddyn Sultan ke ciki, ba shi iya magana, qafar shi ta shanye, hannun shi guda ba shi motsi, gashi har yanzu damuwa bata bar shi ba, rashin ganin yaran shi na damun rayuwar shi,duk daren duniya da ihu, da kururuwa muke kwana, kamar ya na ganin wani abu, gashi ba shi magana balle mu gane me ya ke gani, "

Dariya Lawwali ya yi sannan ya ce,

"Me zai gani ko banda aljannun da ya ke wa tsafi? Bai basu jinin bil'adama ba kwana biyu, ba dole su biyo sahu ba? In ba ku je aka rushe dakin da ya gina ya na tsahi cikin shi ba,kuma baku yi wa aljannu sadaka ba walle yana cikin tashin hankali, kad'an ya fara gani"

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, yanzu ya za mu yi?"

"Ina nissani? Na so gobe yaran ku su zo ganin ku, Sultan ya dawo gare ku, amma 'yar ku ta lalata shirin, ta ci amana ta, ta qone duk wata shaida da zan hannintawa hukuma, dan mu karbi hukuncin mu daidai da abinda muka aikata, amma ta qone su, dan haka ba za su dawo yanzu ba,"

Kuka Hajiya Ikee ta fashe da shi ta ce,

"Yau na shiga uku ni Ikileema, ina zan sa rayuwa ta? Yanzu Lawwali ba wata alfarma da zaka yi muna mu gan su?ka duba halin da Daddyn Sultan ke ciki"

Dariya Lawwali ya yi, sanda ya kalli yanda Excellency ke dalalar da yawu, ya kasa magana sai hawaye.

"Ke walle wanga aljannu ka damun shi ba kewar d'iya nai ba, in ku na neman maganin aljannu ku nema, sai an jima"(ke wannan aljanu ke damun shi ba kewar yaran shi ba, in zaku nemi maganin aljanu ku nema se an jima)

Mubaraka ce ta ce,

"Hajiya ki gafarce ni, ni qarama ce, amma ina mai baku shawara, da ku nemo mallammai na kwarai,wanda sunka san Allah, su yi addu'a aljannun su tafi, amma in kuka yi musu yanka, za su dawo su ce wani abu suke so, ko rayuwar wani a cikin ku, Allah shi kiyaye"

Ai Hajiya ikee na jin rayuwar wani a cikin su, ta tsure, kallon Gwamna Halliru ta yi, ta ce,

"Mu na zaman zaman mu da rufin asirin mu ka doko muna siyasa, gashi nan, mu na ganin ibtila'in rayuwa, ba mulkin, ba dukiyar, ba d'iyan mu, ga wani tashin hankalin yanda za mu rabu da aljanun da ka jajibo muna"

Lawwali kam dariya kawai yake kamar wani wawa, cikin surutai da sambatu suka bar Hajiya Ikee, Gwamna Halliru kuwa na kwaranyar da hawaye ta gefen ido.

Sai da suka tsaya Lawwali ya yi siyayya ta kayan kwalama, da duk wani abu da ya san Mubaraka na so, har zai fita daga wajen shopping din bai sai wa Sultana komai ba, sai ya ji ya kasa tafiya, komawa ciki ya yi, ya daukar mata best chocolate din ta, da candy din da ta fi so, sannan ya ga wani turare mai kyau na mata, daukar mata ya yi, ya na murmushi.

Sai da ya biya kudin komai, sanan ya koma mota, Mubaraka na nan zaune, ta na ta tunanin yanda za ta sanya Lawwali ya bar Su sultana Su je su ga iyayen su, Hajiya Ikee ta matuqar bata tausayi.

Ajiye mata ledojin ya yi a cinyar ta, ya koma mazaunin driver ya zauna.

"Barakana ga naki nan, wancan na Sultyna ne, ki bata amma kar ki ce ni ne na bayar a bata,"

"Yah Auwal kenan, ana soooo ana

Please Login or Register in order to submit comment