Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi nan ma bai tsira ba, ya zai yi??????

*Ina nissani?*

[6/21, 5:15 PM] HAERMEEBRAERH ❀️: πŸ’…πŸ» *A GARIN MU* πŸ’…πŸ»



BY HAERMEEBRAERH



PAGE 27:





Sati biyu ya wuce ba Lawwali ba bayanin shi, ba Sultana kadai ba, hatta da Gwamna Halliru ya fara shiga tashin hankali akan lamarin Lawwali.

Duk wata barna da ta'asa da Lawwali ke aikatawa ta na komawa kunnen Gwamna Halliru, ga zabe ya gabato sauran kwana goma sha uku, lamarin ya tabarbare fiye da tunanin Gwamna, domin kuwa a yanzu Lawwali ko cikin gari bai cika shiga ba, sai jefi jefi dan ya ji halin da ake ciki game da neman qanwar shi da ya sa a yi.

Lawwali ya koma kamar mahauci, akan neman Mubaraka, ya yi kuka har ba iyaka, ya zama kamar wanda ya rasa iyayen shi da dangin shi a dare daya.

Duk wata motar da ta yi tsautsayin bi ta kusa da dajin su, to sunan su matattu, ko kuma ya sa a kame su, ayi ta azabtar wa, ko ya sa a yi ta amsar kudi wajen dangin su, madadin batan Mubraka ya risinar da shi,sai ya sake ruruta masa wutar rashin imani a zuciyar shi.

Sultana kuwa duk ta fige ta rame saboda rashin Lawwali, ko ta je Foundation din ma watarana da kuka take komawa gida, rashin ganin shi a idanun ta ba karamin azabtar da zuciyar ta yake ba.

Duk ta dora laifin akan Hajiya, domin a tunanin ta maganar da Hajiya ta yi ne ya sanya shi yin fushi ya tafi.

Ta gwada No shi ya fi sau shurin masaqi amma ta qi shiga, kullum sanar da ita ake a kashe wayar take, ta yi kuka ta godewa Allah, ta yi sallah ta yi addu'a akan Allah ya dawo mata da shi in da alkhairi, in babu Allah ya sa mata hakuri da dangana, hakan da ta yi ne ya sa ta Ι—an samu sauqi kadan a ran ta, har ta ci gaba da aikin alkhairin da ta sa wa ran ta.

Shiru shirun ta, da rashin shiga mutane da take ya bawa Gwamna damar yada abubuwan da take na alkhairi a gidajen talabijin da rediyo, da duk wata kafar sadarwa, mutane kuwa na ta yabawa, wasu na qara neman taimako a wajen ta, ita kuwa hakan na mata dadi, ganin aikin da take ya na ta bunqasa.

In ta na aikin ta na samun nutsuwa da kwanciyar hankali,da ta dawo gida komai sai ya kwance mata ,ba abinda take gani a idon ta in ba Lawwali ba, tsayuwar shi a jikin mota, da murmushin shi mai sauti, yanayin yanda yake kafe ta da ido, ya na kallon ta, sai ta ji kamar a wannan lokacin ya ke kallon nata, har lumshe ido take, watarana ta yi murmushi in ta tuna, watarana ta fashe da kuka.

An shiga sati na Uku Lawwali be bayyana ba, sai wata safiyar Lahadi, ya shiga gari, direct wajen aski ya nufa,a ka yi masa aski me kyau, aka masa gyaran qafafu da hannuwa, sannan ya sayi turaruka, da kayan abinci ya nufi gidan shi,ko da ya shiga gidan duk ya yi qura, kallon ko ina ya yi, cikin sanyin jiki ya ajiye ledojin hannun shi ya kalli ko ina, wasu irin zaratan hawaye ne masu zafi suka dinga zubar masa.

Mubaraka ce ke masha shara, in ta biyo shi, ta yi wanka ya maida ta gida, ko gyaran da akai wa gidan na qarshe ita ta masa, har ta dinga mishi fadan ta ajiye wani flower vase a tsakiyar table, ta koma ta gan shi a qasa, ya kama kunnen shi ya na bata hakuri, ta na ta tura baki ta na shagwaba, ta ce ta hakura kar ya sake, ta mayar ta gyara komai, ta yi wanka ya maida ta gida, ya na gama tunawa ya sanya wani irin kuka mai ban tausayi, sannan ya ce,

"Barakana ina kin ka tai na? Wanne hali ki ke ciki? Kin ci abinci? Kin yi wanka kuwa? A wanne irin waje ki ke kwana? Barakana, ki yafe wa yayan ki, na kasa kare ki, na kasa nemo ki, baraka na ki dawo gare Ni, ke ce sanyin idaniya ta, na rabu da Sultana duk da son da nake mata, na kasa cire ta a zuciya ta, dan Allah ki dawo ki taya Ni neman soyayyar ta, ba zan iya ba Ni dai,ke Ni ka jira ki sa Sultana ta so ni, Barakaaaa"

Kuka ya dunqule a waje guda ya na yi, kamar qaramin yaro, ya na son dika qannen shi, amma mubaraka ta daban ce, ita kadai ce ke son shi, ita ke kula da shi, ita kadai ta damu da rayuwar shi, tun ya na da burin ya dawo na gari, har ya kangare, ba wanda ya damu da wace iriyar rayuwa yake ciki, kudi kawai iyayen shi suka sanya a gaba, yau kuwa zai kai musu kudin da zai haukata su, amma sai suma sun bayyana masa Barakan shi, ko ya sawa kudin fetur a gaban su ya qona, hakan sai ya fi masu ciwo sama da yanda yake ji a ran shi.

A haukace ya debi kudin da ya koma da su, masu dimbin yawa a jaka, ya zari makullin motar shi, da wayar shi da ya bari a gidan, bai je ko ina da ita ba, motar shi duk ta yi qura.

Ya na shiga ya fitar da ita, ya koma ya kulle gidan, ya na qoqarin fita daga layin, motoci guda biyu da ke kai Sultana Foundation a yanzu su ka shiga unguwar suma,kamar an ce ta daga kai, Lawwali ta gani fuskar shi ba walwala, idanun shi jawur kamar ba shi ba, ya na tsula gudu,gashi duk ya yi duhu,

"Auwal? Dama Auwal na nan? Shi ne ya daina zuwa? Driver bi motar Auwal duk inda ya yi,"

"Tau Ran ki shi dade"

Dayar motar masu tsaron lafiyar ta na ganin an juya suma suka bi su, ta waya ta sanar da su me ke faruwa, kwantar da hankalin su suka yi suka bi su a baya.

Saboda damuwar da Lawwali ke ciki, be ma kula ana bin shi ba, har sai da ya shiga unguwar su, ya tsaya a qofar gidan su, sannan ya kula da motocin Sultana.

Wani irin yanayi ne mara fassaruwa ya shige shi, kewa ne, tsantsar soyayya ce, da kuma neman taimakon ta, duk sun had'u sun game masa waje daya.

Ita kuwa bata san sanda hawaye ke gudu a fuskar ta ba, ga alama nan, Lawwali na shaye shaye, amma bata duban wannan, domin dama dan Adam tara yake, be cika goma ba, ita dai a kowanne hali yake ta na son shi, ita kadai ta san ya take ji.

A hankali suke takawa zuwa ga junan su, Sultana ji ta yi kamar ta kwantar da kan ta a faffadan qirjin shi, ko abinda take ji zai ragu, Lawwali ji ya ke kamar ya isa ya rungume ta, ta shafa kan shi da siraran yatsun ta, tare da fada masa cewar 'Komai zai wuce, zai yi daidai' a cikin kunnen shi.

Sun jima su na kallon juna kafin Sultana ta yi qarfin halin cewa,

"Why? Me yasa? Me ya sa za ka tafi a lokacin da zuciya ta, ta amince, ta yarda, ta kuma gamsu da ta kamu da matsanancin ciwon son ka? Me ya sa ka tafi, a lokacin da nake tsananin buqatar ka, ka kuwa san ya nake ji a nan dina? (Ta sanya hannu, ta nuna saitin zuciyar ta, cikin kuka,) ba zaka gane ba, saboda baka san me ne ne soyayya ba ga dukkan alamu,"

Cikin sauri ya dakatar da ita, dan kalaman ta na sake harzuqa zuciyar shi, ta na hango masa mugunta kala kala.

Cikin cije lebunan shi a cikin bakin shi ya shafa kan shi, da hannu daya, sannan ya ce,

"Sultana, ba ke dai ka jin duk abinda kin ka lissahwa ba, ni ma ina ji dika, wataqila har da dori ma, amma sultana ba ke d'aya zuciya ta ke so ba, qauna ta ita ce rayuwa ta, ban da komai banda kowa sama da ita,ita kad'ai ce gata na a duk qasar ga, ba mai so na tsakani da Allah, sama da ita, a yanzu haka ji na nake kamar duk duniya sun juyan baya, ni kadai ne, ban da kowa banda komai,"

"Wait a minute,me ya samu Mubaraka?"

A cikin tashin hankali Sultana ta masa wannan tambayar, a cikin qasa da minti bakwai ya bayyana mata me ya faru dangane da batan ta,da kuma irin neman da yake mata, bai samu ba.

Cikin kuka Sultana ta juya ta rufe bakin ta, ta jima a haka ta na kuka, Lawwali ma ji ya ke kamar ya yi kukan, sai daga baya ta juya gare shi, ta na share hawayen ta, motar ta ta fara budewa zata shiga,sannan ta ce,

"Mu je gida Daddy na nan yau, mu sanar da shi,a sanya neman ta, duk inda ta shiga, i love her, she is a gud gurl, I can't let anything happen to her, she is like a sister to me, mu je gida Auwal, maza shiga mota mu je,"

Kallon gidan su ya yi, cikin takaici, ya na jiyo muryoyin mata ana ta zabga hira, ya ji haushi da be shiga ya tarwatsa su ba, qanwar shi ta bata amma suke hira haka ana dariya har waje ana ji, ya so ya shiga ya gan su, da duk sai ya musu rashin mutunci d'aya bayan d'ayan su, amma ba komai next time.

Kwafa ya yi, ya shige motar shi, ya bi ta su Sultana.

*************************

Gwamna Halliru na ganawa da su No 1 da 4, su na tattaunawa akan yanda Lawwali ya haukace.

Sultana ta je za ta shiga parlour wasu masu tsaron wajen ne suka dakatar da ita, tare da sanar da ita cewar Gwamna ya ce kar a bawa Kowa damar shiga, sai da izinin shi, d'aya daga cikin su ta kalla tace,

"Ka je ka sanar da shi ni ce, na ke son magana da shi, ya na da mahimmanci na gan shi yanzu"

Har security din zai tafi, Lawwali ya qarasa shiga wajen, su na hada ido, security ya ja baya, tare da fadin,

"Ran ka ya dade Oga, Barka da zuwa"

"Gwauna hwa? "

"Shi na ciki Oga"

Mamaki ne danqare a cikin Sultana, an hana ta shiga amma an budewa Lawwali ya shige,me kenan? Lawwali ya fi ta matsayi a gidan Uban ta kenan?

Ko da suka shiga shiru wajen ya dauka, ba No 4 da ake tausa ba, ana nuna masa ba abinda Lawwali zai yi, as long as bai gane ina qanwar shi take ba, har Gwamnan kan shi sai da hankalin shi ya tashi ainun.

Cikin rawar murya, No 4 ya ce,

"O....ogaa, kai ne da rana haka?"

Lawwali ko kallon No 4 be ba, ya samu kujera ya zauna, tare da harde qafa,No 1 ne ya je ya tsaya a daf da shi,hakan kamar girmamawa ne a gare shi, No1 na ta hararar No 4 tare da yi masa nunin ya nutsu, Sultana kuwa mamakin abinda take gani ya fi qarfin ta, waje ta samu ta tsaya, ta na kallon yanda mahaifin ta ya yi lakwas a gaban Lawwali, bai magana ba akan zaman da Lawwali ya yi a gaban shi .

"Oga har yanzu fa shiru,yanzu haka mun kawo maganar ne wajen Excelency saboda a bamu taimako"

"Mu ma abinda ya kawo mu kenan,na yi iya qoqari na na kasa, ina neman taimako a hukumance, a bido min qauna ta, in ba haka ba,....."

Shiru ya yi, ya taune leben bakin shi na qasa, tare da dukan tafin qafar shi da ya dora a saman dayar qafar tashi.

"Ah ah Sultana, mik-kawo ki nan?"

"Tare muke,"

"Ban gane tare kuke ba, qaqa an kai kuke tare?"

"Dad Mubaraka ce ba a gani ba, kusan sati Uku yanzu, shi ne na rako shi neman taimako wajen ka, amma yanzu na kula is like, ni anka rako, ko wani zai iya min bayani akan abubuwan da nake gani a yanzu?"

Da sauri gwamna ya zari wayar shi, ya kira Head quarter na yan sanda, ya fara bada report din batan Mubaraka, Sultana tuni ta manta da tambayar da take yi, ita da Lawwali sun bawa Gwamna hankulan su.

Wayar aka bawa Lawwali ya yi kwatancen ta,da bayanin ranar da suka nemeta suka rasa, tare da alqawarin ze tura hotunan ta.

Godiya ya miqe sosai ya na wa gwamna, Sultana ma haka.

Gwamna na son bin su ya ji dalilin da ya sa suke a tare, kuma ya na son magana da su No 1, dan haka sai da ya bari su Lawwali sun fita, sannan ya qara jaddada musu su yi taka tsantsan ta yanda asirin su ba zai tonu ba, domin in Lawwali ya san sun sace qanwar shi, har shi kan shi ba zai tsira ba, ballantana su.

Wannan kalamai sun sake birkita No 4, da kyar yake hadiyar yawu, zufa sai karyo masa take, a sati ukun nan, duk 'yar qibar ma da ya yi, saboda kudin da suke samu, duk ta zabge, ya fita hayyacin shi, ba wani kwanciyar hankali a tattare da shi.

Su Sultana kuwa a jikin motar shi, suka tsaya, su na magana, hira ce mai dadi,ta yaushe gamo suke yi, kusan kaso saba'in na hirar dukkan su akan Mubaraka su ke yi, Sultana na son mubaraka, ba wai dan ta na qanwar Lawwali ba,ah ah, yarinyar abar so ce ga duk mai hankali.

Shi kuwa a wajen shi Mubaraka ita ce rayuwar shi, a ganin shi ma ba zai taba samun kan Sultana ba in bata nan.

Bayan sun yi sallama za su tafi ne Sultana ta ce,

"Haka ake sallama da masoyi? "

Kallon yanda ta maida kai gefe ta yi, sai ta masa kyau, murmushi ya yi, kadan, wanda rabon shi da murmushi na gaskiya, ba na mugunta ba, tun kafin batan Mubarakan.

"Ya ya kamata masoyi ya yi sallama ?"

Dan rufe fuskar ta tayi da hannun ta kadan ta ce,

"Kamata ya yi ka ce, Sultana na tafi, zan dawo anjima, ina son ki"

Bude baki Lawwali ya yi, ya na dariya mai sassanyan sauti, ya ce,

"Kaiii ka kaiii ka kaiii, Baraka na ta ce man ke ustaziya ta wallah, ashe ke iya soyayya haka?"

Mayafin ta ta ja sosai ta rufe fuska sannan ta ce,

"To ai soyayya kowa na yi"

"Ok, to sultana Ina son ki,"

Wani irin dad'i ne ya ziyarce ta, musamman da ta kalle shi ta ga babu wasa a kalaman shi, iyakar gaskiyar shi yake fada, ta ji sautin Muryar shi, ba alamar gatse ko wasa, amayar da ta ta zuciyar ta ce,

"Auwal ina son ka, In na ce ina son ka, ba ina nufin ina son ka fiye da yanda kk so na bane, ina nufin ina son ka a kowanne hali, ina son ka ko da wani sabani ya haΙ—a mu, ina son ka ko da ka na cikin damuwar da ta sa ka nesanta da ni, ina son ka sama da nisan nan da ke tsakanin mu,ina son ka sama da yanda na ke jin zafin rashin ka a rai na, ina son ka sama da dukkan wani abu da zai qoqarin shiga tsakanin mu, ina nufin nafi son ka Auwal"

Ya Salam, Lawwali ya gama narkewa,kalaman sultana sun wanke masa wani kaso na baqin cikin da ke ran shi,dama haka take fata, shi ne dalilin da ya sanya ta cire kunya ta furta abinda ke ran ta, sai bayan ta gama kashe masa gabban jikin shi, ta juya da gudu gudu ta shige gida,dan kuwa kunyar shi ba zata bar ta ta tsaya jin me zai ce ba again.

Lawwali ya jima a wajen, kafin ya shiga motar shi, ya tada ya bar gidan.

Su No 1 kuwa ya na fita suma suka bar gidan, dan zuwa sauyawa su Mubaraka maboya kamar yanda Gwamna ya bada shawara, da kuma wajen zama.

Lawwali har ya isa gida bai dena murmushi ba, ya jima ya na dirzar dattin jikin shi,kafin ya samu abinci ya ci rabon shi da abinci sosai kamar na ranar ba zai iya fadin ga lokacin ba.

Ya na kammalawa ya kwanta, dan hutawa.

**********************

Vissa ta samu, na tafiyar Isah Saudiya, ana sauran kwana biyu tafiyar Isa, Hajiya ta sa Isan ya kai mata su Hansatu su gaisa, Hansatu ta sha mamakin jin duk abinda ke faruwa a bakin mahaifiyar ta, ace duk wadannan abubuwan na faruwa bata sani ba? Haka ta dinga yaqe ta na yabawa Isah ,tare da yanka qarya kala kala, dan ta kare shi, yaran ta na ta mamakin qaryar da take ta shinfidawa.

Ba daban ta basu tarbiyya mai kyau ba, tabbas da sun tona mata asiri, dan kuwa ba su so ta rufa masa asiri ba.

Isah kuwa sai murmushi yake ya na fadin,

"In ban muku ba wa zan wa?"

Yayan Hansatu ya qara masa dubu hamsin ya qara a kan jarin shi, sai godiya suke ta zabgawa.

Da yamma Hajiya ta sa mota ta maida su gida.

Tafiyar Isah Makka daiiii sauran kwana biyu, wace zata yi rakiya?????πŸ˜‚
[6/21, 5:15 PM] HAERMEEBRAERH ❀️: πŸ’…πŸ» *A GARIN MU* πŸ’…πŸ»


BY HAERMEEBRAERH


PAGE 26:


Da misalin tara na safe,Isah ne tsaye a qofar katafaren gate din gidan su Hansatu, mai gadi ya hana shi shiga, sai bala'i suke, hargowar su ta ratsa har cikin gida,Hajiya na zaune ta na kallon Sunnah TV ana gabatar da maimaicin wani shiri akan kiwon lafiya, rage volume ta yi, ta saurari rikicin da ake tsakanin Isah da mai gadi, tashi ta yi, ta leqa window , magana ta ke amma ba sa jin ta, gashi Yayah'n Hansatu baya nan,matar shi ma tun jiya ba ta nan, daga an mata fad'a akan rashin iya kalami, ta yi fushi ta tafi gida.

Hijabin ta ta sanya, ta fita, Isah na ganin ta ya saka fuskar tausayi, kiran shi ta yi, mai gadi ya bar shi ya shiga, zai wuce ciki ya yi qasa da murya, ya ce ma mai gadin.

"Tallakan banza da wofi, haka za ka qare a gate Dan walaha kawai,"

Wangale baki ya yi ya qarasa gaban Hajiya tare da zubewa a qasa, cikin sauri ta ja baya sannan ta ce,

"Habaa Isah tashi, tashi mu shiga daga ciki,"

Tashi ya yi, amma ya coge ya qi shiga, cikin raunin murya ya ce,

"Hajiya na zo ne a taimaka mana, ba da ban ba yanda zan ba, nan ne waje na qarshe da zan zo, domin ku din surukai na ne, bai kamata Ku saida akuya ba ta dawo ta na ci muku danga, ina cikin wani hali Hajiya, kasuwanci ya tsaya cak saboda rashin jari, da can ina dan zuwa makka ne na kai goro, ina samu sosai, muna cikin walwala, da wadata, da iyali na, amma yanzu har kunyar shiga gida nake, saboda babu, inna shiga yara na na kukan yunwa na kan ji kamar na kashe kai na dan baqin ciki, babbar damuwar yau mun tashi ba ko silin hatsi, ga Hansatu na fama da zazzabi , shi ne na ce bari na zo ko dubu daya ne na samu na kai ta asibiti"

Hajiya ta shiga matsanancin tashin hankali, 'yar cikin ta ke zaune cikin uqubar rayuwa haka? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un.

Cikin sauri ta shige ciki, tare da bashi umarnin ya bi ta ciki.

A parlour'n su ta bar shi ta shige ciki, kudi masu yawa ta dakko, har bata san adadin su ba, hawaye na zuba a idanun ta, tsabar yanda take jin ran ta na quna, ta tafka babban kuskure, su na da dukiya haka yar ta ke fama da rayuwa ,abu daya ne ya ba zuciyar ta hakuri, da ta tuna kowa a rayuwar shi iya arzikin da Allah ya yanke masa zai ci, to ita ma haka ne.

Isa kuwa kafin ta fita ba inda bai leqa ba a gurguje, ya tabbatar dukiya ta ji a gidan, ko ta ina akwai arziqi.

Komawa ya yi ya zauna ya na jinjina kai, Hajiya kuwa ta goge hawayen ta tas, ta zauna ta miqa masa maqudan kudin hannun ta, sanan ta ce,

"Isah daga yau kar ka qara kiran kan ka da suruki na, kai d'a na ne, ba suruki na ba, duk abinda ka ke so ka same ni kai tsaye,ga wannan, ka na da passport?"

"Eh ina da shi a da, amma yayi espaya yanzu, na jima ban je can Makkan ba, saboda rashin jari"

"To ga wannan, ka je ka yi, sannan ka min magana, sauran kuma ka kai ta asibiti, ka sai maku kayan abinci, in komai ya daidaita passport ya samu za muyi magana, ka na da waya?"

Dan sosa kai ya yi ya ce,

"Ehhh ina dai da sim, Amma ba waya, ta lalace da jimawa, a na ta abinci Hajiya wa ya ke ta waya?"

Wani abu ta ji ya maqale mata a wuya, mai d'aci, murmushin yaqe ta yi, ta miqe ta shiga dakin ta ta dawo, riqe da waya, wayar ta ce, ta cire sim din ta da komai, ta zauna ta yi formating wayar sannan ta miqa masa, waya ce mai matuqar kyau da tsada, ta tasamma dubu d'ari biyar da wani abu.

"Ga wannan, ka yi amfani da ita, last 3weeks Wannan yaron ya siyo min ita, in kaje ka gaishe ta, ita ma zan sai mata wayar dan mu na gaisawa"

"Hajiya ban san da wanne kalami zan maki godiya ba, amma ina fatan Allah ya jiqan Alhaji, Allah ya masa rahama, Allah ya sa kiyi kyakkyawan qarshe na gode na gode "

"Ameeen Isah, ka dena godiya, yi wa kai ne ai"

Haka ya tattare yan kudaden shi ya na godiya ya fita, sai da ya kai gate ya juya ya ga ba me kallon shi, ya fiddo kudin ya na tafiyar fad'i.

A gaban me gadi ya tsaya, ya dinga juya su, ya na masa kallon raini.

"Kai mai gadi, ka shiga hankalin ka, in ba haka ba, se na sa an kore ka, masu gadi uku na fitar a gidan nan tun sanda ina zama a gidannan, ka tambaya ka ji wane ne Isah direba, tsohon dan iska ne ni, kuma surukin gidannan ne, daga yau na sake zuwa ka min iskanci se ka bar gidan nan, tunda ba gadon tsoho a ciki wajen gina shi"

Me gadi baki ya sake ya na kallon ikon Allah, se da Isah ya maida kudi aljihu, ya gyara tsaf sannan ya bar gidan.

Ko daya isa gidan shi, ya tadda Hansatu na ma yara wanka,ta share gidan fess ko ina qalqal, ta yi wankan ta shar da ita, da kayan da aka bata daga gida, ramar da ta yi ne da baqin da ta yi ne kawai ze nuna halin rayuwar da take ciki.

Murmushi ta mi shi, wanda bata gajiya da yi masa a duk sanda ze fita ya koma gida, dauke kai ya yi, kamar kullum.

Ba sallama ya shige, za ta bi shi ta masa sannu da zuwa ya dakatar da ita cikin daure fuska, komawa ta yi ta ci gaba da yi wa Ahmad wanka, ta na yaqe, abun ya mata zafi sosai, amma ba halin magana.

Se da ya boye kudin shi tass sannan ya dauki dubu talatin ya bar gidan, ta na fada masa ga abinci amma bai kula ba.

Direct wajen yin passport ya je, aka ce gobe ya koma, bai ji dadi ba, haka ya tafi, ya na saman machine suka wuce wani mai saida gasasshiyar kaza,yawun shi ne ya yanko, ai kuwa ba bata lokaci ya ce ma me machine ya juya, Isah kamar abun wasa, ya ce a bashi kaza daya, qosasshiya aka yanka masa ita aka bade ta da yaji, sannan ya ce a bashi rabin kaza again , aka yanka aka sa yaji, ya amsa, shagon kusa da wajen ya je, ya sayi drinks, ya samu wani mai machine din ya nufi gida.

Ya na zuwa ya tadda su a tsakar gida Hansatu na musu karatu, miqa mata ledar kaza ya yi, ya wuce daki, Hansatu da yara na ta murna, su na ta zuba godiya.

Ya na shiga dakin ya bude tashi, sai a lokacin na kula da qatuwar kazar nan ya aje wa kan shi, ya basu rabi, kamar abun wasa, Isah ya sa kazar nan a gaba da ci, bai tashi ba se da ya ci ya taune qashi ya kora da lemo me sanyi, sannan ya saki muguwar gyatsa, ya ce,

"Yauwaaa Allah na gode maka,me ake da talauci? Allah ka nuna min buri na ya cika, kullum

Please Login or Register in order to submit comment