Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya samu nasara akan dan uwan shi,amma fa kowanne a cikin su ya daku, banda jini ba abinda ke fita a jikin su su dikan.

Cikin hargowa wajen ya dauki sunan, Oga da No 1, cike da mummunan tashin hankali No 1 ya fara kada kai, ya na ja da baya, kamar wani tsumma haka wani gabjeje a wajen ya wurga shi tsakiyar fili, No 1 ji ya yi kamar zai fitsari a wando tsabar tsoro, kowa ya san Lawwali a wajen, ba shi da na biyu a qarfi, ba shi da Mahadi a qarfi a wajen, to akan me za su hada su? Indai ba so suke a kashe shi ba.

Wani irin fushi ne ya bayyana a saman fuskar Lawwali na irin quncin da ke cikin ran shi, cikin qanqanin lokaci ya kawar da fushin ya fara nuna kawai a bar wasan, kar ya cutar da No 1, dariyar yaqe No 1 ya fara, tare da fadin,

"Oga ya ce a bar wasa haka nan, sai wani lokaci"

A gaggauce Lawwali ya kalli matashin da ya yi wa rad'a, ai kuwa matashin ya yi tsagal ya ce,

"Bamu jiya ba mu dai, mu na so mu ga hwadan manya, zai fi dadin kallo,"

"Muna so, mu ma mu na so, mu na son ganin fadan manya!!!!"

Shi ne abinda mutanen wajen ke ta ihu su na maimaita wa, har suka jawo hankalin mutanen da ke rufe a wajen, ta window da duk wata kafa da za su samu damar kallon me ke faruwa suke leqe, ai kuwa cikin daga hannu d'aya wajen ya yi tsit.

Lawwali ne ya isa gaban No 1 ya ce,

"Kar ka damu aboki na, kawai ka dage, wataqila ka samu nasara akai na, ka ga ba ni da wani qarhi Mubaraka ita ta qarhi na ka sani, gashi ban gane ta ba, za ka iya nasara akai na cikin sauqi"

Wata iriyar zufar saman hanci da saman lebe No 1 ke yi, gashi ya na jin wani ruwa na gangarar masa ta qafafun shi, be gama tantance shin fitsari yake a tsaye ba ko kuma zufa ce, ya ji ana karanta sharadin damben,kafin ya ja baya an harba bindiga, zare ido ya yi, ya na kallon Lawwali, wanda fuskar shi ta sauya, daga fara'a zuwa tsantsar bacin rai, hankalin shi ne ya sake tashi.

Kwasa ya yi a guje zai gudu, Lawwali ya cafke shi, wani irin naushi ya kai ma No 1 sai da ya juya, tare da kifewa a qasa, qoqarin buga hannun shi yake a tashi wasan dan ya san ba zai debi komai a jikin Lawwali ba, Lawwali ya bi hannayen ya taushe, ya hana shi buga su.

Dambe ya yi dambe, No 1 ya daku iya duka, duk wani haushin shi da Lawwali ke ji, sai da kaso mai tsoka ya ragu, sai da ya zamana hatta da tsayuwa No 1 ya kasa, baya iya d'aga yatsan shi ko d'aya, ballantana ya buga qasa, idanun shi sun kada sun yi jawur kamar ya yi taruwar jini a cikin su.

Lawwali da kan shi ya d'aga hannayen shi biyu, ya miqe daga saman No 1, ya tabbata dukan da ya masa sai ya sanya shi jinya ta aqalla sati daya,ya ga ta fita yawon cin amana.

Umarni ya bawa No 4 da ya yi jinyar No 1, cikin azama, No 4 da shi ma yake a jikkace, ya fara qoqarin daga No 1, wata qara ya saki mai qarfin gaske, da sauri no 4 ya sake shi, ko da ya duba sai ya ga ashe No 1 ya samu karaya ne, har hannun ya kumbure, da damar matasan wajen sun ji dad'in dukan da aka yi wa No 1 dama ya addabe su, ya ishe su, tunda Lawwali ya koma kwana da zama a cikin gari No 1 ke musu mulkin kama karya, yanzu gashi an yi musu maganin shi.

Lawwali bai kwana a wajen ba, gida ya tafi, ko da ya isa wanka ya fara yi, sannan ya ci abinci ya zauna a kujera, ya na kallon hotunan Mubaraka, da video da ya dauke ta.

Ya na kalla ya na murmushi, tare da jin dad'in sanin inda take, da kuma halin da take ciki,kulawa ta musamman No 4 yake basu,da taimakon Lawwalin.

Duba time ya yi, ya ga sha d'aya saura, bai wani dogon tunani ba kawai ya danna number'n ta, ta yi ringing sau biyu kamar jira take ya kira, ta dauka,

"Hello"

"Assalamualaikum"

Maida ido sama ya yi, kafin ya amsa sallamar da,

"Wa'alaikumussalam, ran ki shi dade baki kwana ba?"

"Ban yi kwana ba, kai mi ka kai da ba ka yi kwana ba har yanzu? Gobe akwai aiki fa, in muka tashi har wata unguwa za mu tai, last 3days an shiga an yi musu barna, ba kadan ba, mutan garin har wasun su sun yi hijira, qalilan ne ke zaune a garin, saboda basu da wajen zuwa"

Sarai ya san ko ina ne, duk da ba su suka yi aikin ba, amma dai abokan aiki, ai ba sa buya.

"Allah shi kai mu,"

"Ameen, me ya sa ka kire ni yanzu? Akwai wani abu ne?"

Shiru ya ɗan yi na wasu seconds kafin ya ce,

"Babu komi, kawai dai na yi kewar ki ne"

Kwanciyar ta ta gyara, tare da sake manna wayar a kunnen ta, ta na jin yanda Muryar shi ta cikakkun mazaje ke dukan dodon kunnen ta,

"Mun fa hadu d'azu"

"Ehh sanin haka ne ma ya sa na ji duk na yi kewar murmushin ki mai tsadar nan, yau baki yi min shi ba sai sau biyu kacal, gaskiya ban qoshi ba, a qara min,"

Wata iriyar siririyar dariya ta dinga yi, har zuciyar shi bai jin komai game da dariyar ta a yau d'in ,soyayyar da ya fara mata kafin ya san me mahaifin ta ya masa, yanzu ta fara sauya salo, ta koma soyayyar daukan fansa.

"Kaiiii ran ki shi dad'e gaskiya sai da sahe, wagga dariya zata hana min kwana"

"Me ya sa za ta hana ma kwana?"

"Saboda in na kwanta zan dinga tunanin ta, kuma zan ji ina son saurarar wata makamanciyar ta daga gare ki, gashi na sani har abada ba aure a tsakanin mu"

Da sauri ta gimtse fuska, tare da mamakin dalilin da zai sa ya ce ba aure a tsakanin su

"Mi ka ka nuhi? An haramta aure a tsakani na da kai ne ko mi?"

"Ba a haramta ba a musulunci, amma iyayen ki sun haramta shi, sanin kan ki na ba mai barin ki auren driver ko? Ban taba baqin cikin rashin ilimin boko ba da na arabiyya sai yanzu, da ina da ilimi da iyayen ki sun bani ke,......ina son ki sultana"

Tsigar jikin ta ce ta tsaya ta mimmiqe, ji ta yi bugun zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri.

"Da gaske ka na so na?"

"Kwarai da gaske, ina son ki Sultana"

Rintse idon ta tayi, tare da cizon leben ta na qasa,cikin lallausan murmushi ta ce,

"Dan Allah maimaita in ji"

"Inda son ki sultana"

"Ka same ni kuwa, ba abinda zai hana ka aure na,"

"Akwai shi,"

"Me ne ne shi?"

"Iyayen ki, iyayen ki musamman Hajiya bata bari ki auri jahili, kuma driver,"

"Auwal ka dena kiran kan ka da wannan mummunan suna, in baka fad'a cewar baka je makaranta ba, babu wanda zai ce baka je ba, and na ji labarin har saukar qur'ani ka yi, kuma ka fara Makarantar boko itama, to ka ga kenan kai ba jahili bane,"

"Hummm ba zaki gane ba, bari na bar ki ki yi kwana, amma fa ki sani iyayen ki ba za su bar ki aure na ba, ni dai abu guda nis-sani, ke kadai ni ke so, ke kadai nit-taba burin mallaka a matsayin matar da zan aura, bayan ke ban taba son kowa ba, .....Ina son ki Sultana"

Idanun ta a rufe hawaye na kwaranya a idon ta, ya gama zuba kalaman shi masu zafi da kuma dad'i a gare ta, ya kashe wayar shi ya barta cikin yanayin da ta kasa fassarawa.

Shin da gaske yake iyayen ta ba za su bari ya aure ta ba? Me ye dalili? A duniya mutum na iya auren duk wanda yake so, se wanda musulunci ya hana, misali mace ta auri mace, ko namiji ya auri namiji, ko mutum ya auri wata dabba ko wata halitta, ko musulmi ya auri kafuri,ko muharramai su auri junan su, amma Indai akwai so da qauna kowanne namiji zai iya auren macen da yake so, haka ma mace za ta iya auren namijin da take so, to me ya sa ita zata zama daban a cikin mutane? Saboda kawai shi din driver ne?

Da wannan tunanin bacci mai cike da rudanin tunani ya dauke ta.

*************************

Duk abinda aka sanyawa rana, wannan ranar zata zagayo, ko ayi abun, ko kuma a fasa shi .

Yau ce ranar zabe, gwamna da iyalin shi tun asuba suka shirya suka je wajen yin zaɓe, sun dangwala nasu sun koma government house, yau har da sultana aka tafi, ta na can ne kawai, amma hankalin ta baya tare da ita, rashin ganin Auwal na damun ta, tun randa suka yi waya, yau kwana hudu, ta ji shi shiru, shin ko dai ya rabu da ita ne saboda tunanin Hajiya ba zata yarda ba, daddy ma ba zai amince ba? Amma ai bai ce zai rabu da ita ba.

Wannan tunanin sun ma ƙwaƙwalwar ta yawa, har ya fara sanya ta zance a fili, cikin rashin fahimtar me ta fada Sultan ya ce,

"Mi kin ka ce? Wa ye zai bar ki?"

Da sauri ta hau yaqe ta na barin wajen, tare da sanar da shi ,

"Ba kowa, ba komai, kar ka damu, ina zuwa"

Tafiya kawai take a tankamemen gidan da ya cika da mutane kala kala, duk ta gama ratsa su ta wuce wani building, ba abinda ke tashi a hanyar wajen se karar takalmin ta, wayar ta ta tsaya cak ta na latsawa, sama sama ta ke jin muryoyin su,

"......ka tabbata dai ka saka a kawo takardun zaben da aka dangwala ko? Na hwadi maka in banda aikin da Sultana ka yi a gari, sai d'an wanda munka hwara shekarar ga, walle ba mai zabar mu,"

"Ki kwantar da hankalin ki Hajiya, na gama komai, akwai taqadarin yaro na da ka yi min aiki ko wanne iri na, shi da yara nai, ke ko batar da mutum nicce ayi, ba shi koma second d'aya raye indai yaron nan na saka, ke duk wasu abubuwa da ki kaga ina yi da shi ni ka taqama, dan haka zabe kamar na ci na gama ne,"

Wata iriyar dariya suka sanya a tare, suka ci gaba da hira, Gwamna na bawa Hajiya Ikee labarin Lawwali, ba tare da ya sanar da ita sunan shi ba, sai jin dad'i take ta na addu'a Allah ya sa su zarce.

Qoqarin komawa cikin mutane suke, cikin sauri Sultana da ta daskare a wajen ta cire takalmin ta a hannu, ta fad'a wata qofa da ta gani a dan bude ta b'uya, Hajiya Ikee ce da Gwamna Halliru suka fito, cikin farin ciki, sun sha ado na alfarma, sai walqiya suke, da qamshi.

Su na wuce wa sultana ta sanya wani irin kuka mai ban tausayi, mahaifan ta ashe basu da imani? Kuma a haka suke neman su ci gaba da jagorantar al'umma?...........

*Ni Ko nace iya abinda ki ka sani ma kenan 'yannan, ba ki san kalar tsafin da gyatumi ke yi ba*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH

PAGE 33:



Lokuta da dama idan farin ciki, ko baqin ciki ya dami mutum, akwai mutum na farko dake zuwa zuciyar wannan mutumin, walau wanda ya yarda da shi ko da ba 'yan uwantaka ta jini a tsakanin su,ko kuma wanda ke da alhaki akan halin da mutum ya shiga, masoyi shine mutum na farko da ke fara zuwar wa mutum a rai, mace ko namiji, qawa ko saurayi, miji ko mata, ko kuma iyaye.

A baya Sultana ba ta da wanda ya wuce Sultan a wajen ta, saboda shaquwa irin ta yaya da qanwa da ke a tsakanin su, komai nata shi take sanarwa, to amma tunda shi Allah bai sa har yanzu ya gano asalin mummunanan dabi'un mahaifan nasu ba, ba ta so ya sani, kamar yanda suka so ya yi rayuwa haka yake yi, ba ya saba umarnin su, ya kai a ce ya ajiye iyali, amma rayuwar shi abar juyawa ce a hannayen su, gwanda ita sun bata 'yanci, wanda a wajen ta ba 'yanci bane, sun yi amfani da abinda suke kira 'yancin su na biyan buqatar su ta son zuciya da shi.

Lawwali ne babban wanda za ta iya wannan maganar sirrin da shi, (to wai ma makaranta mu dan tattauna wani abu mana, shin daidai ne kawai daga yin saurayi, dan ki na jin kin yarda dashi, dari bisa dari, sai ki ta fada masa sirrin ki? Musamman wannan babban sirrin? 'yan mata da dama su na shirme, da yarinta, kawai yanda ke ki ke jin ki na son namiji, To haka ki ke dauka shima haka yake son ki, kuma yanda kk yarda da shi shima haka ya yarda da ke, wallahi ba haka bane, maza kala kala ne,kashi kashi ne,akwai wanda zai so ki kamar ran shi, amma ba sirri, nashi sirrin ma be riqe ba balle na wani, kuma zai iya rufe ido ya manta da son da yake maki, ya kafta maki uba uban rashin mutunci, daga baya in kun shirya ya baki hakuri, ke kuma ya wuce, anjima ma in wani abu ya taso se kin fada masa. Akwai namijin da zai so ki, kuma zai saurare ki, zai taya ki warware matsalar ki da damuwar ki,zai shiga lamarin ki kamar nashi, kuma ze riqe miki sirrin ki,amma ki sani 'yar uwa irin su basu da yawa a wannan zamanin, wani ma Allah Allah yake yaji maganar ki ya fadawa yan uwan shi da abokan shi, ki na nan tanyare bude a faranti kowa ya san sirrin ki da na 'yan gidan ku, a kiyaye, a dena makahon so)

Wayar shi take ta nema, ana fada mata busy, cikin bacin rai, da sharar hawaye ta bar taron, iyayen nata basu son video ko camera su hau kan ta, ganin yanayin da take ciki, dan haka suka basar sukai ta harkokin su, direct motar ta ta nufa,ta na qoqarin shiga, wani murdadden namiji da baqaqen kaya, da baqin gilashi ya tsaya a gefen ta ya ce,

"Ran ki shi dade, Excellency ya ce kar a bar ki ki hita yanzu,sai an fadi sakamakon zabe gari ya lafa,sannan za ku fita,yanzu ki tai zuwa sashen ku,"

"Saqo ka ke bani ko umarni?"

"Ran ki shi dade, ba umarni bane, dan Allah ki taimake mu ki koma, abincin mu na nan, ke mai tausayi ce, kar ki fita ya zama sanadin barin mu aiki"

Kallon shi tayi, ta gan shi rusheshe, ko a ka aka ce ya maida ta sashen, cikin qiftawar ido ya na iyawa, amma ya gwammaci ya yi amfani da kalamai masu taushi a gare ta, cike da baqin cikin ci gaba da zama a gidan Gwamnatin ta shiga gaba, ya na take mata baya, har bangaren su, ta na shiga ta rufe da qarfi ta saki wani irin kuka, mai matuqar kuna.

"Anya su Daddy za su hadu da rahamar Allah kuwa? Ashe duk abinda Daddy ke aikatawa, Hajiya ta yi kamar bata sani ba ita ka zuga shi aikata wasu munanan aikin? Anya iyayen ga namu su na da imani kuwa? Sun san Allah kuwa?"

Kuka take ta na surutai ita kadai,ga wayar Lawwali ta qi samuwa, se gwadawa take.

Har aka yi azahar ta yi itama, ta kwanta Lawwali bai kira taba, ta fara hasala yanzu kam, amma ba yanda zata yi, gashi ba zata iya fushi da shi ba, saboda kalar son da take masa ma, ba zai bata damar fushi da shi ba.

Wayar ta ta sake laluba, ta shiga wajen rubuta saqo,ta hau rubutu kamar haka.

~Auwal dan Allah ka dauki kira na, zan iya rasa raina in har ban ji Muryar ka ba a yau, kai ne maganin quncin da zuciya ta ke ciki,kai ne farin ciki na,kasancewar ka tare da ni, shi ne cikar farin ciki na, pls ka kira ni, in ka ga saqo na, Ina son ka Auwal, and I really need u now, pls~

Abinci aka shigar mata da shi, ko daga kai ta kalla ma bata yi ba, ballantana su sanya ran za ta ci, duk magiya da roqo da mai aikin ta dinga yi, qarshe itama magiya da roqo, tare da kuka ta sanya wa matar, dole ta hakura ta barta.

Ita kadai ta san ya zuciyar ta take a yanzu, wani irin qunci da ciwo take mata, wace iriyar rayuwa take ciki? Ai da wannan azziqin gwanda talaucin da ba ze raba ka da imanin ka ba, akwai abubuwa da dama da suke zamewa bawa musiba, to ta tabbata wannan azziqin musiba ne a gare su, sai dai za ta yi ta addu'a Allah ya kare su daga fadawa halaka, duniya da lahira.

Abu kamar wasa, Lawwali bai kira Sultana ba, dik da cewa ya ga kiran ta, ya ga saqon ta, aiki ne ya mishi yawa, ga wajen da suke ba network sosai, yau kuwa tun cikin dare suka fita, suna ta kai takardun da aka riga aka dangwala wa yatsan zabe, mazabu kala kala.

A gajiye yake matuqa, ko ya kira ta be san me zai ce ba, ya san dole ta fuskanci gajiyar a Muryar shi, ba shi da abin kare kan shi, dan haka ya qi kiran ta, ya ci gaba da harkokin shi.

Wani sashe na zuciyar shi ya na jin ba dad'i , da bai kira ba, tunda ya san kalar yanda take son shi, ko Muryar shi taji ta na jin dadi a ran ta, kawar da tunanin ya yi, a fili ya furta,

"Gwanda ta ji zafin rashin kiran nawa ma ai, hakan ma wani punishment ne"

Kafin duhun dare ya shiga Sultana ta ji jiki,zazzaɓi mai mugun zafi ne ya kama ta, ba abinda take banda rawar sanyi, Hajiya Ikee ta shiga bangaren nasu ta tarar da Sultana kwance ta lullubu, sai rawar sanyi take, cikin tsananin damuwa ta isa gaban ta, ta na taba goshin ta, dan ture hannun ta sultana tayi, sanan ta juya baya, Hajiya Ikee, waya ta fara yi, akan a kira likita yanzun nan, cikin rawar murya sultana ta ce,

"Ko ya zo ba abinda zai iya min, ...ba na so ya zo,... ki barshi kawai, .....ki je ku ji sakamakon zaben da kuka riga kuka san ku ne ma zaku yi nasara"

Cikin washe baki, da rashin gane mai Sultana ta ce, ta miqe,

"Bari in tai, nahi son a hwadi komai a gabana gashi can ana ta hwadi, har yanzu akwai mazabun da ba su kai sakamakon su ba, da alama za mu samu nasara, mun godewa Allah, bari na tai, in likitan ya zaka sai mu taho a baki magani ke jiya? Allah shi yi miki albarka,"

A hankali ta amsa da

"Ameen"

Shin addu'ar irin su Hajiya ma na cin mutum ne? Ni Ko na ce uwa dai uwa ce, komai lalacewar ta, in ta yi addu'a inshaa Allah, Allah zai amsa, zunubin ta daban, addu'ar ta daban, da ace mummunan kalami zata yi ga dan ta zai same shi,kamar yanda Lamishi bata da burin da ya wuce ta zagi yaran ta, ta musu baki.

Likita ya zo da misalin tara na dare, ya bata magunguna, tare da bata shawarwarin rage tunani,domin jinin ta ya hau kadan, murmushi kawai ta yi masa ta yi godiya, Hajiya Ikee ta raka shi, ta koma wajen ta, dan dai ta san zabe kamar sun ci shi sun gama, amma me ke damun gudan jinin ta har jinin ta ya hau?

Cike da damuwa ta koma dakin, hawaye ta gani daga idon sultana ya na gangarewa a saman pillow duk da cewa idanun nata na rufe ne.

Zama ta yi a gefen kan ta, tare da sanya hannu ta jaye gashin ta da ke gefen fuskar ta, ta shafa kan nata cikin kulawa da soyayya, irin ta uwa, cike da tausaya wa ta ce,

"Sulty Baby mi ka damun ki? Hawan jini? Mi ya maki zahi, da uwar ki da uban ki, ga dan uwan ki masu son ki? In akwai abinda ki ka so duniyar ga ki hwadi min ki na samun shi ko menene shi kuwa"

A wahalce Sultana ta daga ido ta kalli mahaifiyar ta, wadda take bata tsoro, tsoron gaske ma kuwa, dan bata san wanne ne halayen ta boyayyu ba kuma bayan wanda ta ji ta sani, cikin qunar rai ta ce,

"Kar ki damu,Wataqila wannan ciwon shi ne ajali na, wataqila kuma a hankali Allah ya yaye min, amma ku ba za ku iya min abinda nake so ba"

Cikin tsananin damuwa Hajiya Ikee ta sake mannewa a jikin Sultana, ta na jan ta jikin ta, da sigar lallashi, tausayi, soyayya, da tsantsar qauna,

"Habaaa Baby Sulty, wace irin magana ta wagga ki ke yi? Kin San dai ba abinda ki ke nema a duniyar nan ki rasa daga wajen mu, akan su wa muke fadi tashi dan mu tara abin duniya? Duk ba dan ku muke yi ba? Ki sanar da ni abinda ki ke so, yanzun nan zan sa a kawo maki shi"

"Hajiya kar ki damu, na fara lura da kuma sanin abinda za ki iya da wanda ba zaki iya ba, amma wannan kam na san ba zan same shi ba, Dan Allah ki bar wannan maganar ki tai an kusa sanar da sakamakon zabe"

"Rayuwar ki is more important to me, than anything else in the world my dear just tell me what you want and I will get it done for you yanzun ga"

Idanun sultana zafi suke kamar an zuba mata yaji, a hankali ta ware su a fuskar Hajiya Ikee wadda ta nuna tsantsar damuwa da gaskiyar maganar ta, na bawa sultana duk abinda take so.

"Auwal....Auwal shi ne abinda zuciya ta ka so, Auwal na ke so ku aura min, indai har da gaske ki ke za ki yi min duk abinda nake so, shi ne rayuwa ta, in ku ka hana ni auren shi Hajiya zan mutu"

Miqewa tsaye Hajiya Ikee ta yi tana kallon Sultana da wani irin kallon kan ki daya kuwa?

"Wane Auwal ki ke nufi? Lawwali driver? Ki na da hankali kuwa? Na haifi yarinya kamar ki, kyakkyawa, mai ilimin arabiyya da boko sannan ta b'ige da auren jahilin driver? Ki na hauka ne?"

"Hajiya ba fa jahili bane masanin qur'ani ne sosai, masanin qur'ani kuwa ai ba mai kira nai Jahili"

"Sai ni, ni zan kire shi jahili tunda banga alamar shi na aiki da shi ba, qur'ani ya hana neman ilimin boko ne? Namiji har namiji ace driving shikai? Ba da ni ba, kar ki bata min rai, ki nemi komai a waje na, amma banda wanga, yau ga zancen banza zancen yohi, to bari ki ji, kar ma ki kuskura ki wa mahaifin ku maganar ga, dan rai nai sai yahi nawa ɓaci, ba abinda ya tsana sama da talauci ga rayuwa tai, ba zai so ya miqa ki gidan wahala ba, na hwada maki tanadin da nake a kan ki, shi na ki ke debo min wahala? Sam ba zai yu ba,"

Ta na ta Masifa ta bar dakin, a qasan ran ta bata so suka rabu ta haka da diyar ta ta ba, musamman yanzu da bata da lafiya.

Sultana kuwa ko kukan ta kasa, tabbas sai yanzu ta fahimci me Auwal ke nufi,abinda babba ya hango dama an ce yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba, ya riga ya fahimci ba za a bashi ita ba, ita kuma ta zaci son da iyayen ta ke mata zai taimake ta a bata wanda take so.

Ta na nan kwance ido biyu ta ji ana taken Nigeria, ana iface iface, a cikin gidan, rintse idanun ta tayi cikin qunar zuciya ta ce,

"Ban san sanda tallakan Nigeria zai bude ido nai ba, ban san sanda tallakan Nigeria zai fara addu'ar samun shugabanni wanda suka cancanta managarta ba, ba wanda suka so ba, ban san sanda tallakan Nigeria zai gyara tsakani nai da Allah ba, har Allah ya ji tausayin shi ya raba shi da shugabanni kamar su Daddy, ya Allah ka

Please Login or Register in order to submit comment