Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da dariya, ya ce,

"Ran Babban yaya shi dade, a mana ahuwa, ina neman izinin auren Sultana a hannun ka"

Cikin dake wa, Sultan ya dafa kan Lawwali, ya ce,

"Na baka izinin auren qauna ta, Allah ya muku albarka,"

Dariya sosai Sultana take, Lawwali na taya ta, Sultan ma cikin dariya ya dafa kafadar Lawwali ya ce,

"Congratulations man,Allah ya sa ayi da mu"

"Thanks bro, ameen, bari mu tai, lokaci na tahiya"

"Yau ba za mu zauna mu yi murnar wannan rana ba?"

Cikin shagwaba Sultana ta fadi hakan, ta na dan noqe kafada, ba qaramin kyau ta wa Lawwali ba, iyayen ta kuwa a zuciyar su sai suka gan ta, kamar yar qaramar yarinyar su, da suke matuqar lele, da qauna a zuqatan su.

Sultan ne ya kama kumatun ta, cikin sigar wasa ya ce,

"Ohhh Baby Sulty za ta zama babbaaa, ki tafi NGO din ki, ki gode Allah ma ki na da abun yi, unlike me, sai dai a dahwa a bani na ci, na kwanta, da jikin qiba gare ni, da na fi wata mata da aka kira da Hameedan Hamma (Lols)"

Dariya sosai Sultana ta yi, amma abu daya na d'an damun zuciyar ta, kallon kallon da ke tsakanin iyayen ta da Lawwali, da kuma rashin fara'ar su, da walwalar su, a wajen ta wannan babban abun farin ciki ne, da sauri ta kawar da tunanin komai, da ta tuna dalilin da ya sa iyayen ta ba su cikin farin ciki sosai,Lawwali talaka ne, kuma driver, sun amince ne kawai saboda farin cikin ta, babu komai, hakan ma sun taimaki rayuwar ta ai, ta na godiya.

Sallama suka ma iyayen na su suka tafi, ko da ya je bude mata mota da sauri ta bude, ta ce ta gode, ya kula da hannun shi, ba dan ya ce ba komai ba ma, yau ba inda za su.

Zuciyar su fari tasss suka isa, Lawwali kan shi jin amincewar su Hajiya Ikee ya ke a matsayin wata babbar nasara da ya taba samu a rayuwar shi,duk da dai har yanzu auren Sultana ya na nan a matsayin auren daukar fansa a zuciyar shi, (zan so ganin anyaa Oga zai cika wannan alqawari da ya daukar wa kan shi? Sultana ce fa).

************************

Kwanan su Hansatu uku ba wuta, saboda NEPA sun yanke musu wuta, sakamakon rashin biyan kudin da ba su yi ba, wayar ta babu caji, sai dai ta kai gidan 'Yabbuga, daga kaiwa jiya, yau an kai 'Yabbuga ta fara masifar za a dame ta da saka cire din caji, ba aikin ta ba kenan, kar su dame ta.

Dan haka Hansatu da kan ta, ta saka Hijabi ta kai wayar ta gidan Asshibi, dan sun dan saba yanzu, su na dan ziyarar junan su.

Ta tarar da Mijin Asshibi zai fita, suka gaisa, ta tambaye shi ko Asshibi na nan ta kawo caji ne, ya tabbatar mata da cewar ta na ciki, ya fice abin shi.

Ya na shiga Mota ya danna kiran Isah, bayan sun gaisa, ya tambaye shi ya Makkan, Isah ya kalli kayan abincin da ke gaban shi, ya shafa tumbin shi da ya fara ajiye wa ya ce,

"Laminu Makka ta yi, ka ci ka sha ka kwanta ka yi bacci, ba me tashin ka,in kuwa ka na da suruka kamar tawa ko ba ka sana'a zaka warwasa Alhaji"

"Shegen kaya, ka na can ka na tatsar surukar ka a nan"

"Bari kawai Laminu, shekaran jiya ni ce mata an kwace sauran goro da ni tai da shi, ta tausaya min sosai, ta aikon da dubu dari biyu,"

"Dan iska, shi ne ba ka turo min ko yar hamsin ba ce nima na dan more kuddin surukar taka"

Hansatu ce ta je zata wuce, ya yi shiru ya dena magana, sai da ta fita ya ce,

"A gaskiya Isah in ka dawo ka ga Hansatun ka ba zaka gane ta ba, ka ga yanda ta yi qiba, ta yi mulmul da ita, wagga ba da ban taka ta ba ai sai na kai mata ziyara"

Da sauri Isah ya zauna daidai, ya ce,

"Kar ka kuskura, kar ka soma taba min mata, ko da ka ga ina abinda na ke so, dan na san na kama ta a hannu ne, har yanzu a hannu take, ina son mata ta, kar ka kuskura....akwai wata harqalla da ya kamata fa mu hada Alhaji, za ta kawo wuta sosai, ya kamata a hada ta yau yau din nan, kafin ta zo karbar wayar ta anjima"

"Kwantas, ni ba abinda zan da matar aure, ga 'yan mata nan, masu taken zawarawan gida? Ka biya kudin shawarma yanzu ka samu yadda ka ka so, wace harqalla ka ke magana akai?"

"Shegen sama Asshibi na gida ana cin amanar ta a waje, sai ka koma gida ka zam kamar bawan ta, ita ko gani takai kamar duk duniya ta hi kowa Sa'ar miji"

"Iya taku kenan"

"Wani abu sai ka zo Makka,takarun nan na nan Alhaji, bari kawai, sai ka zo kawai, yanzu mu yi magana akan wannan babbar harqallar da za mu hada,"

Nan Isah ya sanar wa da Laminu duk irin abinda yake son su yi, cikin dariyar kwararrun 'yan duniya Laminu ya ce,

"Shegen sama, ka na son ka hini iya tsiya hwa"

"Babu komai, kai ne dai uban gida na"

Sallama suka yi Laminu ya duba wayar shi, ya ga Isah ya tura masa da No da zai kira, nan da nan kuwa ya danna kiran yaran shi biyu, ya basu umarnin da ya dace da abinda suke qullawa,barin gidan ya yi ya tsaya nesa da unguwar su sosai, sannan ya cire sim din shi da yake amfani da shi,ya sanya wani ya danna kiran No da aka tura masa, cikin maqale murya ya ke magana, ya na gamawa ya cire sim din ya karya shi ya yar, sannan ya tada motar shi ya bar wajen.

************************

"Yaya ba fa zaki hushi ba akan abinda ya faru ki ce baki koma zuwa aiki, ke ma ke san aikin da mukai ba wani aiki bane, alfarma ce dai aka mana ba komi ba, walaqanci kuwa ba kalar wanda bamu gani ba a baya"

"Wani ya taba kiran mu da barayi? Cewa fa tay-yi in mun tai su na rasa abubuwa, ana musu sata, Allah na tuba duk a halaye na marasa kyau bana sata bana maita, yo akan cin mi, za a ce na yi sata?"

Dan Talo ne ya ajiye butar hannun shi, ya zauna a bakin qofar dakin su Jameelu, ya wage baki ya na hamma.

"Ke dai san in baki tai ba yawan abinci na raguwa ko? Tunda in an tashi kason ragowar abinci ba a kasawa da na ki, tunda baki tai ba, ko wanda aka dafa wa masu aiki ba a sawa da kason ki, ko dai baqin ciki ki ke mana"

Wani mummunan kallo Lamishi ta watsawa Dan Talo, cikin bacin rai ta ce,

"Ban zuwa din, lalataccen yohi kawai, baka da aiki sai son banza, baka b'arkata komi a gidan ka sai dai mata su maka, kaii Arrrr, tur da miji irin ka, ni na rasa ma mi na sa na aure ka, ba fusss, ba ka da lissahin da ya wuce wanne abinci muka kawo, da ya akai ya qare kamar kai ka nemo, baka nemo ba amma ka iya bin diddigi, kai....."

Mai buruji ta san in aka bar Lamishi sai tai awa uku tana zage Dan Talo, gashi lokaci na ta tafiya, dan haka ta katse ta ta ce,

"Yaya ki wa Allah, ki rabu da wanga mai matacciyar zuciya, ga hijabin ki na doko miki, mu tai ki dena ganin shi ko ran ki ya yi hwari, ni kai na mamaki ni kai, wai hankalina na ina sanda ya je garkar mu neman aure na, har na amince na auri miji kamar shi"

Dan Talo ne ya miqe tsaye ya na dariya ,ko haushin zagin da suke masa baya ji, ya kade rigar shi ya ce,

"Haka dai kun ka ganni kun ka ce ku na so"

*************************

Driver take ta jira ya dawo daga inda duk ya tafi ya kaita asibitin amma shiru, ta tambayi mai gadi ya ce be jima da fita ba, bai san inda ya tafi ba, gani ta yi lokaci na tafiya, bata san takamaimai me ya faru ba, har aka kira ta, cikin sauri ta dauki hijabin ta saka jakar ta dauka ta fita harabar gidan.

Makullin mota ta fitar daga jakar ta, tare da bude daya daga cikin motocin gidan, zama ta yi ta kunna, tare da danna horn da qarfi, cikin tashin hankali da damuwa ta bar gidan.

A hanyar ta ta barin unguwar tasu ta ga wani yaro a saman titi ya na ta tsala kuka, cikin sanya birki mai qarfi ta tsaya gaban yaron, fita tayi ta duqa zata tambaye shi daga ina yake dan da ganin shi ba a irin gidajen unguwar yake ba.

Wani abu ta ji an fesa mata ta shaqa, kan ta ya mata nauyi, kafin jiri ya qarasa diban ta ta kai qasa an tare ta, da kyar suka ciccibe ta suka danna a motar su, suka sanya wata takarda a motar ta daidai mazaunin driver, suka ja tasu motar a guje su ka bar waje . ......

*Allah ka shiryi kilimapas*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻



BY HAERMEEBRAERH


PAGE 40:


Inda suka saba ajiye mutane nan suka kai ta, suka yi wa Laminu waya, ya isa, ya na zuwa ya leqa ta bulin da ya saba leqen wanda ya sa akamo, agogon hannun ta da sarqar wuyan ta ya sa su cire su kai masa.

Ko da suka ciro ya jujjuya su a hannun shi, ya girgiza kai, a kiyasi in aka siyar za su kai million daya da dan motsi haka, murnushi ya yi, ya ce,

"Aikin ku na kyau, yanzu ku taho mu tai, a saishe da wanga, sai na baku kuddin sallama a ciki, dan wannan kayan da kuka gani, mai hatsari ne, ba zan so ku zauna kusa ba, asiri ya tonu, a yi kame da ku"

Godiya suka yi ta yi, dan ba wani wayo ne da su ba, ya samu irin majiya qarfin qauyawan nan ne kawai su na masa aikin da ya so, ya sallame su da kudi qalilan su tafi su na murna abin su.

Ya kira Isah ya sanar da shi duk abinda ke faruwa, Isah ya sanar da shi duk wata hanya daya kamata ya bi,dan ba ya so ma abun ya dad'e, gudun tonuwar asirin su.

*************************

Asshibi ce ta yi lullubi ta tafi gidan Hansatu, ta na zaune ta na tsintar gumi, (shinkafa yar gida kenan) ta ji sallamar Asshibi.

"Ahh ah maraba, Bismillah shigo"

"Ba zama zan yi ba, na dora sanwa, wayar ki ce ke ta kuka, na ce bari na kawo maki, wataqila kiran na da mahimmanci, ko mutanen Saudiya na sun ka kira, na taho shigowa na ga waccan wahalalliyar matar garka, ita da abokiyar fadan ta, har sun shirya kenan?"

"To ina na sanin musu, ni da ke cikin gida, Allah ya sa sun shirya din ne, ai hwada ba dadi"

Dan guntun tsaki Asshibi ta yi, ta ce,

"Ke ai ba ki son rikici, gashi nan an sake kira ki doka"

Da sauri kuwa Hansatu ta amsa, zuciyar ta na tsananin fata da begen Allah ya sa mijin ta ne, wata iriyar murya ta ji, na mata magana,

"Ke ta Hansatu ko?"

"Eh ni ta, da wa naka magana?"

"Ba ki da buqatar sanin wanda ka batu, ki sanar da yayan ki, mun dauke Hajiyar ku, mu na da buqatar kuddi kafin mu sake ta, in kun kawo yau, ba tare da kun sanar da jami'an tsaro ko wata hukuma ba, yau din ga muna sako maku ita, amma in kun tsaya bin diddigi da kwakkwafin mu, tau ku na ganin gawar ta kuwa,ko da an kama mu mun dai kashe ta"

Hawaye sun jima da wanke fuskar Hansatu ba abinda take kira sai Innalillahi wa inna ilaihirraji'un.

"Bawon Allah, ka yi wa Allah kar ku cutar min da ita, zan sanar da yayana ko nawa kuke so indai muna da shi za a baku, dan Allah kar ku cutar mana da ita,"

"Zan sake kiran ki"

Kuka take sosai ta na neman hijabin ta, da dan kudin ta da zai kai ta gidan su.

Asshibi na tambayar ta me ya faru, ta na kuka ta na sanar da ita komai,

"Dan Allah ki min alfarma diyan ga su zauna wajen ki, har na tai na dawo"

"Ba ya da komi, Allah shi bayyana ta cikin aminci, wadannan mutane masu aikata wadannan laihukka Allah shi tona musu asiri azzalumai, su ko satar ma ba basu iya ba, su rasa wadda za su dauka sai boyar Allah, irin Hajiya mace mai sauqin hali, da halin kirki, anya masu satar ga basu san ku ba kuwa?"

"Hummm Asshibi kenan, su ina ruwan su da halin ta, in ba na kuddi ba? Tunda ko sun san ta na da halin kuddi ai shi ne dalilin dauke ta, bari na tai,ku yi ta taya mu da addu'a dan Allah"

"To Ummaa sai kin dawo, Allah ya bayyana Hajiya lafiya" in ji Ameena, da ta fi sauran 'yan uwan ta wayo, dan haka ta fahimci me ke faruwa.

"Ameeen"

Kafin ta kai bakin titi yayan ta ya kira ya sanar da ita, an kira shi an fada masa an sace Hajiya, sun fadi cewar a basu milliyan ashirin, sun yi ciniki za a basu million goma, yanzu hada kudin yake ze kai, ta zauna a gida ba sai ta fito ba, kar a yi biyu.

(Mutane na kuskuren qin sanar da jami'an tsaro irin wadannan abubuwan, ko dake jami'an tsaron suma tsoro suke ji, Allah dai ya bamu tsaro da kan shi a wannan qasa da duniya baki daya)

Hankalin ta bai kwanta ba, amma bayanda za ta yi, dole ta koma kamar yanda ya Umar ta, ashe ma sun kira Yayan nata shi ne suka kira ta kamar ba su sanar da shi ba, Allah ya saka musu, ya bayyanar da Hajiya lafiya shi ne addu'ar da ta dinga yi, har ta koma gida, ta na zuwa kuwa ta tarar da su Asshibi na qoqarin rufe gidan, za su tafi, labarta mata komai ta yi, ta mata godiya, akan ba sai yaran sun bi ta bama tun da ta dawo.

Ko da suka shiga gidan alwala ta yi ita da yaran ta, suka yi nafila, raka'a biyu, sannan suka yi ta addu'a, ba qaqqautawa, akan Allah ya kare Hajiya ya bayyana ta da gaggawa cikin aminci .

Har goma da rabi na dare basu sake kira ba, ga kudi an hada su kawai ake jira, ranar haka gidaje biyun suka kwana cikin tashin hankali , Yayan Hansatu kuwa damuwa ta masa yawa, shi kadai ne a gidan ba mai lallashin shi, ran shi ya ɓaci, kuwa da rashin matar shi a kusa, cikin fushi ya dau waya ya dinga kiran ta, a so samun shi ya sake ta ya huta, tunda bai ga amfanin ta ba.

Cikin rashin sa'a bata daga wayar ba, haka ya hakura, ya dinga sintiri, daga daki zuwa parlour, zuwa dakin Hajiya, qarshe a dakin Hajiya ya kwanta, bacci mai dadi ya dauke shi.

Da misalin qarfe biyu na dare, wayar shi ta hau qara, ya na dubawa ya ga No masu garkuwa da mutanen ne, hannu na rawa ya dauka.

"Ina ta kiran ku ba ta shiga, na hada kuddin tun dazu gasu"

"Tauu ka hito ka kawo su daidai inda kun ka samu motar Hajiyan zan karba, in ka yi gangancin zuwa da jami'an tsaro ina mai tabbatar maka, na bada umarnin in na qara minti uku ban koma ba su kashe ta"

Jiki na rawa ya dauki jakar da kudin suke waya na kunnen shi ya fita daga gidan a qafa,

"Ba zan zo da kowa ba, gani nan zuwa, da qafa, ita ko Hajiya yau she za ta dawowa?"

"Kai dai ka kawo kuddi, ai ni na maka alqawarin zata dawo lahiya ko?"

"Tau gani zuwa"

Tafe yake ya na nishi, saboda ba laifi ya na da dan jiki, gashi bai saba da motsa jiki ba, duk inda za shi sai a mota,sai waige yake ko zai ga wanda yake waya da shi .

Har ya isa wajen da aka ce ya aje kudin ya tafi bai ga kowa ba, ya na ajiye wa kuwa ya juya dan komawa gida.

Bai sake waigawa ba sai da ya yi nisa sosai, duk da wajen da dan duhu, bai hana shi ganin wani mutum ya dauki jakar ba ya tafi, a can nesa da wajen mota ce kunne ta na jiran mutumin, ya na zuwa ya shiga suka bar wajen, wani irin kukan takaici ne ya zo wa Yayan Hansatu, ina aka kai musu Hajiyan su, a wanne hali take?

Dama Hajiya ita ce ke tada shi sallar asuba, to yanzu bata nan, baccin shi yake ta sha, musamman dama bai samu kwantawa da wuri ba.

Buga qofar shiga gidan ya ji ana yi da qarfi kamar za a balle qofar, a gigice ya tashi cikin magagin bacci, ya nufi qofar ya na fadin

"Wane na?"

"Alhaji Hajiya ta taddawo,bude qohwa"

Ai ya na jin Muryar mai gadi kuma ya ji an ce Hajiya ce ta dawo, da sauri ya bude qofar, shi ya kamo ta suka shiga ciki, kwana ɗaya ta yi ba a gida ba, amma duk ta fada, bakin nan ya bushe, su ko dan ruwa ba su san su bawa mutum ba, (ashe gwanda su Oga Lawwali ma).

Ruwa mai dumi Hajiya ta haɗa ta fara yin wanka, kafin masu aikin gidan su zo da safe ta samarwa kan ta abinda za ta ci, dan kuwa wata baqar yunwa take ji, da misalin bakwai na safe, ta kira Hansatu ta sanar da ita, Allah ya dawo da ita gida lafiya.

Murna da godiya ga Allah Hansatu ta yi ta yi, ta ce za ta je duba Hajiyan,Hajiya ta ce ah ah ta bari ba yanzu ba, domin ta kula ko ma wa ke kidnapping din nan idon shi na kan su ne, saboda an ga su na da azziqi, hira suka sha sosai, Hajiya na bata labarin yanayin yanda aka dauke ta, da wajen da aka aje ta, Hansatu ta tausaya ma mahaifiyar ta, sannan ta mata fatan Allah ya kiyaye gaba, Allah kuma ya ninka musu arzikin su da suka rasa.

Bayan sun kashe wayar take sanar da Asshibi, Asshibi ta taya ta murna sosai, sannan kuma ta mata fatan alkhairi, yara ma sai murna suke kakar su ta dawo lafiya.

A ranar Isah da abokin sheqe ayar shi suka raba kudin su daidai, kowa na ta farin ciki da murna.

Ya tafi yawon bude ido a cikin garin Makka Hajiya ta kira shi, kamar ba zai dauka ba, ya daga cikin bata rai, ya yi sallama, bayan ta amsa sun gaisa ne ta ke tambayar shi, ya taji Muryar shi qasa qasa?

"Ban da lafiya ne, yanzu ma asibiti zani, zazzaɓi ya kama ni, ina so na ga likita"

"Subhanallahi, Allah shi baka lahiya, ni ma jiya ina zaune an ka kire ni an ka ce Hansatu ba lahiya ta na asibiti, na hita ni d'ai dan na duba jikin ta,ina hita a mota an ka samu wasu marassa imanin sun ka sace ni, sai da an ka biya million goma da subahi sun ka maido ni gida"

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, ya Salam, subhanallahi, Hajiya ke da kan ki aka sace, ince dai ba abinda ya samu lafiyar ki? Dan ta kudi ai mai sauqi ne, Indai lafiya bata tabu ba,"

Yanda ya rude sai ya sanya Hajiya ganin rashin kyautawar ta, da ta sanar da shi, musamman labarin tunda ya ce ba shi da lafiya, ya na ma asibiti.

"Kar ka daga hankalin ka dan Allah, ina nan lafiya qlou, ai Hansatu nacewa zata zo duba ni, nace dan Allah ta zauna, masu satar nan, da dukkan alamu sun san ko mu su waye"

"Tabbas kuwa Hajiya, ya kamata kuma a tsananta bincike,abun ya yi yawa haka nan"

"Inshaa Allahu, bincike kam za a yi shi, yanzu haka magana na ga hukuma"

Wani yawu Isah ya hadiya mai qulle wuya, sai ga tari, ba qaqqautawa, sannu Hajiya tai ta masa tare da yin sallama da shi, ta kira Yayan Hansatu ta na ta masa fada akan ya dawo da matar shi .

***************************

Soyayya tsakanin Sultana da Lawwali ta bunqasa, ta girmama, ta yanda Sultana ba ta iya kwana ɗaya bata gan shi ba, shi kuma ya na sane watarana zai fashi ya qi zuwa, da kan ta take sanya driver ya aje ta gidan Lawwali ta duba shi, kafin ta wuce.

Lawwali yanzu ba shi da burin da ya wuce na ya ga ya mallaki Sultana a matsayin matar shi,duk da ya rasa dalilin jin hakan, amma abu daya ya sani, zai aure ta ne dan daukan fansa, Itan ma bata da burin da ya wuce na ta auri Auwal,babban burin ta kenan yanzu a duniya, ta ga ta zama mata a wajen Auwal din ta.

Lawwali ne ke kulle gidan shi, ya shiga motar shi, sai gidan Gwamna Halliru, dan ya na sane da cewar bai je ko ina ba, ya na da masu leqen asiri a gidan Gwamnan ba tare da kowa ya sani ba, duk wani bayanai da ya ke da buqatar sani ana sanar da shi, kafin ma ya tambaya.

Har cikin gidan ya shigar da motar shi, a dadai wannan lokacin Sultana na NGO, sun rabu da shi akan ba shi da lafiya, ba zai samu damar zuwa ba.

Har parlour ya shiga ba tare da ya sanar da kowa zuwan shi ba, da Sultan suka fara haduwa ya shirya tsaf zai fita wajen abokin shi, bayan sun gaisa ne ya ke sanar da shi ya zo wajen su Hajiya ne, Sultan ne ya sanar da su zuwan Lawwali, sannan suka sake gaisa wa ya tafi, Lawwali na zaune harde da qafa daya kan daya kamar ya na a gidan shi, Hajiya Ikee da Gwamna Halliru suka fito a tare.

Cikin daure fuska tamau Lawwali ya miqe tsaye, ya na wasa da glass din shi, sannan ya ce,

"Ba na son jira ka hi kowa sanin haka Excellency ,me yasa ka ke bari na yin jira?"

"Lawwali har yanzu ina da tantama akan baka d'iya...."

A zafafe Lawwali ya juya ya kalli Gwamna ya ce,

"Tantama? Tantama hwa kacce, ka na da wani zabi ne da ya wuce ka aura min ita, ko ku na so ko ba ku so,na ga alama kun zaci ba zan aikata abinda na hwadi ba ko? Ka san ni, ka san wane ne ni, ka san mi zan iya da wanda ba zan iya ba, kar ka bari raina shi fi haka ɓaci, abin ba zai mana kyawu ba"

Cikin hura hanci Hajiya Ikee ta ce,

"Yaro yaro ne bai san wuta ba sai ya taka, in ka na da abinda ka ke ganin za ka yi, ka je ka yi, diya ta bata auren dan iska irin ka, lalatacce d'ebabbe"

Abu kamar sihiri, kafin ta rufe labban ta Lawwali ne a gaban ta, ya sa hannun shi guda daya ya shaqe mata wuya, ya sanya bakin bindigar shi cikin bakin ta, jijiyoyin kan shi, da hannayen shi sun fito rudu rudu, idanun nan kamar an watsa masa barkono, leban shi na qasa ya ciza sai da jini ya fito,Gwamna ne ya isa gaban shi ya fara qoqarin kwace Hajiya Ikee da ke fitar da numfashi a wahalce, idanun ta na ta tsiyayar da hawaye, sai miqawa gwamna hannu take, wata tsawa Lawwali ya daka mata, akan ta dena wannan motsi da kukan da take, diffff ta hadiye kukan nata, ido ya fito ya mata gulu gulu.

"Me ki ka ce, yaro bai san wuta ba sai ya taka? Waye yaro? Na ce waye yaro? A duniya akwai lalatattu d'ebabbu Sama da ku ne? Har ni zaki kalla ki wa zagin d'iban albarka, ke ba dan ina da burika masu yawa ba kin isa na bar ki ki kai gobe, (subhaballah kamar ran a hannun shi yake)"

Ba damar magana bindiga na baki, ga wuya ya sha shaqa,

Da qarfi ya wurga ta qasa ta fad'i, a gigice take neman iskar shaqa, tsabar azabar da take ciki, dishi dishi take gani, Gwamna ne ya duqa gaban ta, ya na taimaka mata wajen daidaita numfashin ta.

"Ku na ji na ko? Nan da sati guda nika so a yi auren mu da Sultana, in hakan bata faru ba, ku sani, har

Please Login or Register in order to submit comment