Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta Yi, cikin murmushi mai sauti,take bin Mubaraka da kallo, sai ta ji yarinyar ta shiga ran ta,

"Masha Allah, Mubaraka ko? Ashe ke din hafiza ce,masha Allah Muryar ki na da dadin karatu, izun ki nawa?"

"Na sauke Aunty sultana ,Amma ba a Mana bikin sauka ba, na gode da yaba min,"

Har ran ta ta ji dadin yabawar da Sultana ta Mata, ta so samun wannan yabon wajen iyayen ta, amma ina, ba su san mahimmancin karatun qur'ani ba su, balle su yaba.

A haka ta gama gyara dakin suna karatu ita da Sultana, cikin nishadi, sai Sultana ta ji kamar ta jima da sanin Mubaraka, yarinyar ta shiga ranta cikin lokaci qanqani, sai take jin ta kamar a mkaranta take, da ta gama aikin ta ma, hira suka dan yi, anan Sultana ta ke jin wasu labaran da bata ji dad'in su ba, game da rayuwar Mubaraka, ta na son karatu, iyayen ba su damu ba, a nan ne ta ji kwadayin son shiga cikin gari,ta na son ta je ta ga yanda mutane suke rayuwa a cikin unguwanni, da kewaye, amma ta san zai wahala ta samu hakan.

Daga baya Mubaraka Neman izinin zuwa wankin ta yi, sai da ta sake zuwa wajen Mai Buruji ta nuna mata wajen, dan yanayin kyaun gidan na ruda ta, ta manta hanyar zuwa wajen da ake wankin, har tunanin yanda za ta koma wajen Sultana ma take.

Yawo take a gidan Dan ganin ya gidan ya ke,ta na tafe ta na qarewa qayataccen gidan kallo, ta na jinjina lamari irin na masu kud'i, cikin murmushi ta ayyana a ran ta

'Dole gida ya had'u ya tsaru, gidan gwamna guda'

Tunanin ta ya tsaya cak a daidai sanda ta shiga wata farfajiya, a hankali take jiyo kukan qaramin yaro, ta na tafe, har ta kai saitin inda kukan ke fitowa, ta na saurarawa sai ta ji ya na fad'in,

" Dan Allah ku kyale ni da zafi, wayyoo na Shiga uku"

Wani gini ta gani, an dan kebance shi daga jikin ginin babban gidan, dan haka can ta nufa, rasa ta inda za ta leqa ta Yi, saboda ya nayin gidan ba qaramin gini aka Masa ba ta yanda zata samu damar leqawa ta ga me ke faruwa.

Wankin da ta je shanyawa ta maida hankali wajen shanyawa , ta shanya biyu ta samu gefe ta zauna zaman jira riqe da bokoti, da kuma sabuwar wayar ta da earpiece da Lawwali ya siya mata, ta tabbata koma su wane za su fito, to kuwa zata jira,hannun ta ta sanya qasan rigar ta ta zaro wayar ta da earpiece din ta, ta danna a kunnen ta ta rage qirar'ar da ta kunna sosai, hankalin ta tashe, ta rasa me akewa yaron da ta ji ya na ihu, ji take kamar ta fada dakin ko da za a kashe ta sai dai a kashe ta, amma ta na so ta ga agajin me yaro qarami yake nema a wannan babban gidan, da alama gidan nan na dauke da wani sirri...

Bata gama tunanin ba ta ji ana son bude qofar qara volume din wayar ta tayi, ta ci gaba da shanya, ba tare da ta nuna alamar ta San komai ba, da gefen Ido Kuma cikin dabara ta ke kallon wajen, qaramin yaro almajiri aka fitar qafafun shi a ware yake takawa, dik inda ya wuce jini ke diga, Yayan ta Lawwali ta gani da wani amintaccen yaron shi riqe da yaron, kukan da take riqewa ne ya ke qoqarin tona asirin ta.

Su na wucewa Excellency ya fito, ya na qarasa gyara rigar shi ,tare da yarfe zufa,wata takarda ce a hannun shi ya na tafe ya na nannade wa, ya zagaya bayan ginin wajen, ya bude wani Dan Rami a wajen suck away ya wulla takardar da in ba qarya Mubaraka zatai ba rubutun larabci ne a jiki, domin ma'abociyar karatun irin takardun ce ita a kullum, dan haka ta san me idon ta ya hango.

Wata iriyar zufa ta ji ta karyo Mata, shin meye wannan?

'ya Allah ka Sa ba abinda nake zargi bane' shi ne abinda ta ayyana a ran ta.

Cikin tashin hankali ta shanya rigar Sultana ta bacci ta qarshe.

Ta durqusa ta dau bokiti za ta tafi ta ji an ce

"Keee"

Ta so ta nuna ta ji Amma sai ta Dake, ta fara rera karatun qur'ani ta na bin na wayarta.

Kula da abinda ke kunnen ta ne ya Sanya Excellency jinkirtawa,ya daina motsi, ya na son tabbatar da shin ta gan shi ko bata gan shi ba, har ta dau bokin ta za ta tafi zuciyar ta ta hau ayyana mata ta juya, kwakwalwar ta Kuma ta bata shawarar ta ci gaba da tafiya, shawarar kwakwalwarta ta dauka ta ci gaba da tafiya, kamar bata ga komai ba, kuma bata ji komai ba.

Bata tsaya ba kuwa se da ta kai qaramar qofar da zata sada ta da cikin babban gidan, hannun ta mai rawar tsoron da ya mamaye zuciyar ta ta sanya ta bude qofar, tai wuf ta shige.

Ta na Isa dakin da washing machine din ya ke ta ajiye bokitin ta dinga kuka, kamar zuciyar ta ta Fado bakin ta.

Ta na tsaka da kuka ta ji dawowar su Lawwali, lallabawa ta Yi ta bi su a hankali, a daidai wani lungu ta tsaya, ta ji suna magana qasa qasa ba ta ji me ake fadi ba dai, Amma tabbas har da Gwauna, ta najin motsin komawar su ta gudu ta koma ciki itama, mayafin ta ta Sanya, ta fita gate, su Lawwali na fita Suka gan ta, ta na tafiya a qasa, tsaida abun hawan ya sa aka Yi.

Sannan ya ce ta Shiga

Gani ya Yi ta na kuka, cikin damuwa ya ce,

"Barakana ya akai? Kukan me ki ke?"

Kafe shi ta Yi da jajayen idanun ta, kamar ta amsa shi ta fasa.

"Kai na ke ciwo"

"Subhanallahi....Kai mu wuce chemist"

Can kuwa Suka je, a ka hado Mata magani kala kala, ya sai Mata yagot da lemun roba ya sai Mata gasasshen nama, ya ce su tafi.

Har gida Suka Kai ta, ya kama hannun ta suka shige, yaran shi na mota su na jiran shi,

Lawwali na shiga ya Bata Rai,

"Uban wa ya aike ta aiki gidan can ? Na ce waye ya aike ta aiki can gidan yau?"

"Uban ka na, ishasshe,nicce uban ka na, Dan uban ka ba ka Yi min hwadin banza, (baka yi min fad'in banza) ni uban ka zan CI ni kwana lahiya"

"Ni ba fad'a nake nema ba Lamishi, kin San yarinyar Nan Bata Saba da aikin wahala ba, wacce a aike ta aiki can gidan?ta je makaranta ta dawo ta je aiki? Habaa"

"To na tashi masassara ta damen, Shina nicce ta tai ta taya ni, yo wankin sultana nawa ne? Diyar da kamar yanzu ta Sanya ta cire haka tuwahin ta suke, Kai ka daure ma yarinyar ga gin**take Mana iskanci wallah"

Mubaraka ce ta ja hannun Lawwali Suka je dakin ta, ta ce

"Yah ni fa qarya na Yi Amma ba ciwon Kai nake ba"

Cikin mamaki ya kalle ta, Mubaraka da qarya?

"Ke ko me ya faru haka?"

"Yah Auwal ka fadan gaskiyar abinda kuka wa almajirin nan, na ji kukan shi, ya dawo ya na zubar da jini ta qafar shi, shin..... Innalillahi....wayyooo Allah na....Yah Auwal ka rantse min da Allah Kai baka.....wayyooo Allah na"

Jikin Mubaraka ne ya hau rawa ta ma kasa kukan.

"Ba bu ni Mubaraka ba na aikata luwadi, na Yi maki alqawari ba bu ni, yaro kawai muka samo saboda umarnin me gida ne"

Kukan da take riqewa ne ya kwace Mata, ta dinga Yi kamar zata shide,tausayin yaron ne ya Mata yawa, hango girman Gwauna ta Yi, ta hango yaron, wani kukan ta fara tare da tari Mai qarfi, ta na shessheqa,ruwa ya bude ya fara bata, ta Yi wurgi da ruwan, cikin kuka ta ce,

"Yah Auwal ka bar aiki da shi, zai Kai ka wuta, yah Auwal ko ba abinci za mu rayu ba zamu iya second daya cikin wutar Allah ba, yah Auwal ka min alqawarin baka taba aikata wanan abun da kowa ba, ba kuma za ka bari a yi da Kai ba,"

"Na maki alqawari na tsani luwadi,qazanta ne, ban taba ba, ba a taba Yi min ba, Dan Allah ki dena kuka, zuciya ta zafi take in Ina jin kukan ki, yanzu Lamishi sai ta zo,"

Muryar ta kuwa Suka jiyo,

"Shegiya 'yar bid'ar a Yi, wato kuka ki ke masa shi Kuma uban mu ya zo ya Dake mu ko? To ki suma,na hada ku dika na ci uban ku"

Ta kasa daina kuka, to me ya Yi da takarda Mai rubutun Arabic?

Tashin hankali ne ya sake shigar ta, ta kama hannun Lawwali da qarfi ta ce,

"Yah Auwal ka bar aiki gidan Nan, bana so, in ka ci gaba zan mutu"

Wani Mari ya sakar Mata, cikin tsananin bacin rai,sai da ta ga gilmawar walqiya, nan take nadamar saurin fushin shi ta shige shi, amma ai laifin ta ne, dan ta san ya na son ta shi ya sa take maganar mutuwa,da sauri ya rungume ta, ya na lallashin ta,

"Yi hakuri baraka na, Kar ki qara furta mutuwa akan ki, ba Zaki mutu ba, inshaa Allahu zan bar aikin Amma sai da dabara Inna Bari yanzu ku na cikin matsala, kinji?"

"Ka Yi alqawari?"

"Na Yi alqawari Barakana "

Share Mata hawaye ya Yi, sannan ya ce,

"Kinga yanzu dole ki Sha maganin da muka siyo Dan yanzu kan ya fara ciwo da gaske."

Nama ya miqa Mata gaban ta da komai, ya ce ta ci, ta Sha maganin sannan ya tafi, kasa ci tai ta koma aikin kuka.

Shi kuwa har suka tafi maboyar su bai daina jiyo kukan qanwar tashi da ya ke so sama da kowa da komai a duniya ba.

Dakin shi ya shige ,ya kwanta, kamar ko da yaushe, ba ya shiga shirgin yaran da aka sa su kamawa, indai ba 'yan siyasa ba, kusan a ce ma duk wanda suka kama ba su san shi ba, No 1 zuwa No 5 kawai suka sani.

Sai juya kalman ta yake a ran shi,

'Za mu iya jure rashin abinci, ba za mu iya jure wutar Allah ba'

**********************

Da misalin takwas na safiyar asabar, Isa ne ke zaune a majalisar su ta masu zaman banza, labarai ake ta bayarwa da suka ja ra'ayin shi matuqa, shiruuu ya yi, ya na sauraron su, bai tanka ba, matashin da ake kira da Idi ne ya ce,

"Yau Malam Isa ya shiga tunanin uwar gida, ko dai gida za ka koma ne, kar ka yi laifi"

"Habaa Allah ya kiyaye, ai mata bayin mu ne, sai yanda muka yi da su, da sassafen nan me zan mata a gida inna koma? Zaman gida ai sai matan"

Miqewa Idi ya yi zai tafi, Isa ma tashi ya yi, ya bi bayan shi, sun yi tafiya mai nisa Isa ya ce,

"Ka na ta sauri Ni fa biyo ka na yi game da maganar da kai a majalisa, da gaske ka ke sana'ar saida goro a Makka indai an samu ta shiga akwai riba ?

"Kwarai da gaske, kai baka taba ji ba?"

"To a ina zan ji? Ni ba wasu yan uwa masu maiqo nake da ba"

"To da gaske ne, yanda ka ji din nan, haka abun yake"

"To na gode, zan neme ka inshaa Allahu"

Dariya Idi ya yi, ya kalli Isa sama da qasa, sannan ya tafi ya na dariyar ina Isa zai samu kudin siyan goro ya kai Makka, balle ya samu na kujerar tafiya makkan ?

Isa gari ya shiga, ya dinga yawo, domin neman qarin bayani akan sana'ar saida goro, abun ya kidimar da shi ,yanda ya ji ana samun kuɗi, ai kuwa ya qudiri aniyar fara saida goro, shi ma ya fita layin su Dan Talo , wato masu mutuwar zuciyaaaa......


A GARIN MU








WRITTEN BY HAERMEEBRAEH






PAGE 10:





Tissue ce a qasa jiqaqqu an wurgar a tsakiyar parlour'n, ba abinda ke tashi sai sautin kukan Sultana ,jikin ta sai rawa ya ke, idanun ta da fuskar ta sun yi jajawur, abinka da farar fata, kallon wayar ta sake yi a karo na ba adadi, ta na kallon wani video ne a YouTube, mata ne da yara tare da mazaje na wani qauye da ke a cikin garin Zamfara aka yi wa barna, an karkashe mata da qananan yara, mazajen su an masu yankan rago,gidaje na ci da wuta, wasu daga cikin iyayen na ta rusa kuka, an dauke masu 'yan matan yaran su, wata mata ta na kuka ta na fadin,

'A gabana yakkashe ta, yabbi ta ya taushe-a gabana ya kashe ta, ta bi ta ya taushe... Fyade) , mahaifin ta ya tai wajen, kar a ci ma diyatai mutunci, sun ka yanka shi, ina gwaunati take? Shin ba mu da masu taimakon mu ne? Ana kashe mu, da diyoyin mu, ana halaka dukiyoyin mu, yanzu ki duba gidajen can da an ka bankawa wuta, ina na zamu koma? Wa zai karbe mu? A dangi wa muka ajiye da zai amshe mu da lalurorin mu? Kowa ya na fama da kai nai a wanga yanayi na matsin rayuwa'

Kuka ne ya ci qarfin matar da ke magana, da dukkan alamu ita kan ta 'yar jaridar kuka take, Sultana kuwa kamar ta sume saboda tausayi,Lamishi na tattare tissue da Sultana ta ke zubarwa ta na hawaye.

"Uwar daki na ki yi hankuri, masu aikata wadan ga muggayen laihukka(laifuka) ba mutane na ba, domin shi mutum ba shi kisan dan uwa nai, kuma su ba dabbobi na ba, domin ko zaki bauna da barewa suna cin abinci kusa da shi bai tabe su ba, saboda a qoshe yake, duk kin ka ga dabba ta kashi 'yar uwar ta, to yunwa taka ji, wadan ga mutane ba aljanu na ba, domin aljani ma sai an masa wani abu yake daukan fansa, ko kuma wasu daga azzalumai suna aiki da su, suna sanya su aikata mugunta, wadan ga mutane Allah dai yassan su, kuma shi zai muna maganin su, uwar daki na kukan ya isa haka nan, zaki zazzaɓi"

Cikin tsananin kuka Sultana ta ce,

"Baba Lamishi Ina za su tafi? Wandancan gidajen su ne gidajen su, an qone su, an yanka wasun su, kuma an sace matan su, ya zuqatan su suke a yanzu? Baba Lamishi what if su ma aka tunzura su, tunda ba mai taimakon su, suka fara irin abinda aka musu? Shin laifin waye ? Waye silar samar da ta'addanci a qasar nan ne? Ya Allah ka kawowa bayin ka agaji a cikin wannan musibar rayuwar da suke fuskanta,"

Kukan ta ne ya qaru da ta ga wata mata ta fita da gudu, ana tare tare, ashe a gaban ta aka yanka mijin ta da matashin yaron ta, aka tafi da yan matan yaran ta uku.

"Ke Lamishi,amshe wayar nan ki kashe, sanan ki tashi ki tafi,"in ji cewar Hajiya Ikee da ke isowa cikin parlour'n cikin b'acin rai.

"To Hajiya, Allah ya huci zuciyar ki, ran ki shi dade,"

Wayar ta karba cikin ladabi, ta kashe, sannan ta ajiye a gefen Sultana, ta qarasa tattare tissue din zata fita, Sultana ta miqe dan komawa dakin ta, wani jiri ne ya ɗebe ta, ta kuwa tafi luuu za ta fadi, Hajiya Ikee da Lamishi suka tare ta, Hajiya sakin ta tayi, Lamishi ta kai ta har dakin ta, ta taya ta ta kwanta, ta rufe ta, soyayyar Sultana na huda duk wata gaba ta jikin Lamishi, domin tausayin ta ga talakawa, da da hali ita aka damqawa shugabancin ba mahaifin ta ba.

Ko da Lamishi ta koma parlour kafin ta Isa ta ji Hajiya na bayanin dalilin zubar tissue Mai datti a qasa,

"Sultana ce fa, daga ganin abinda ya faru a wannan qauyen da ake ta haskawa a gidajen talabijin da kafafen sada zumunta shi na duk ta daga hankalin ta, yanzu haka ta na daki kwance"

"Wai me ya sa ba ki jin magana, shin ban hana ki barin ta kallon irin wadannan shiraruwa ba? yanzu da ta ji sauqi zata yi ta tambaya ta kamar ni na kashe su"

Da qarfi ya ke tafiya cikin bacin rai, wanda bai boyu wa, cikin zuciyar Lamishi kuwa cewa ta yi,

'Dan buta uba mai suhhwar tumakin Dan Talo, wanga mutuni mara tausayi Allah ka yi muna magani nai,'(Dan buta uba mai siffar tumakin Dan Talo, wannan mutumi mara tausayi Allah ya mana maganin shi)

Lamishi bata fita daga qofar dakin Sultana ba, sai da ta ji qarar rufe qofar shi ,Hajiya ta bi shi ta na ta bashi hakuri, ya na ci gaba da zazzaga masifa, kwashe komai ta yi ta je ta zubar, jikin ta duk a sake.

Har suka gama aikin su bata sake walwala ba, lokaci zuwa lokaci ta na leqawa dakin Sultana ta ga ya take, kukan dai shi take yi, kamar a lokacin ta ke ganin abinda ya faru.

Lokacin da Lamishi ta yi shigar qarshe dakin Sultana ta gan ta zaune ta na tunani mai zurfi.

"Uwar daki na lafiya? Ko na kawo maki abinci ne ki dan taba kadan? Saboda ke ne kawai ban tahi gida ba,"

"Lamishi, Ni kam na tambaye ki mana,"

Da sauri Lamishi ta zauna a gefen Sultana ta Bata dikkan hankalin ta,

"Dan Allah gidan ku ya yake?.. Amm... Ina nufin akwai sirri? Wani zai iya zama ba tare da an sani ba?"

"Tab gidan mu yanda ki ka san bakin kassuwa haka yake ,kowa shiga yake, maza na qofar gida, mata na ciki, dan dai a ci abincin da muke tahiya da shi, da an gama ne dai baki koma ganin wasu sai wanshegari"

"Ok, ba komai jeki kawai,....kuma ba ki san ko ina ba da mutum zai iya zuwa na sirri haka?"

"Gaskiya ban sani ba..... uwar daki na, in hasashe na ya Yi daidai, ke ce ke son fita daga gidan ga ko?"

Shiru Sultana ta yi, ta juyar da kan ta, hawaye na tsiyaya a idanun ta, jin ta take kamar a gidan kurkuku

"In haka kike tunani ran ki shi dade ki bari, domin zaman ki anan shi ne ruhin asirin ki da kariyar ki, kinga duniyar da ke a wajen gidan nan? Duniya ce ta azzalumai, duniya ce ta daukan rai ,duniya ce ta shan jini, da kwace muhalli, duniya ce azzaluma,duniya ce cike da miyagu masu raba Mata da maza da mutuncin su, zaman ki a inda iyayen ki sun ka killace ki shi kad'ai ne kwanciyar hankalin ki da kariya a gare ki"

Cikin kuka Sultana ta ce,

"Su kuma bayin Allah da ake kashewa fa? Haka za su ci gaba da rayuwa?"

Tashi ta yi da gudu ta fita daga dakin,

Lamishi kuwa komawa ta yi wajen Mai Buruji, ta ce su tafi kawai, dan bata ga alamar Sultana za ta ci wani abu ba.

Dakin mahaifan ta ta nufa ta dinga buga qofar da qarfi, Hajiya Ikee ce ta fito ita da Sultan ,Sultan na ganin yanayin Sultana ya san ba lafiya, cikin hanzari ya nufe ta, tare da qoqarin kama ta ta kwace ta yi gefe,

"Ina daddy? "

"Yanzun Nan ya fita, za su fita government house me ne ne sulty na?"

Da gudu ta fita, ba ko takalmi a qafar ta,

Gwamna ya shiga motar da zata kai shi gidan gwamnati kenan, bayan shi da gaban shi kuwa motoci ne masu bashi kariya, duk sun yi shirin tafiya, ganin Sultana ta fito a birkice cikin kuka, da hargowar kiran sunan shi ne ya sa ya dakatar da su, ya fita,

"Sulty baby me ke faruwa? Ina za ki haka?"

"Daddy, Ina zaka je? Za ka je wajen mutanen can ne da aka qonawa garin su? Daddy pls help them, they really need ur help, daddy su ma fa mutane ne, Kuma a qarqashin kulawar ka suke, me ya sa haka take faruwa da su ne?"

Dan kallon gefe da gefen shi ya yi, ya ga kan mutanen da ke wajen a dan duqe, wasu kuma sun qura musu ido, dan jin amsar da zai bayar, dan kama kafadun ta ya yi, ya goge mata hawayen idan ta, wanda ba su daina zuba ba duk da gogewar da yake ta yi,

"Sulty baby, yanzu haka can zani,ki koma ciki, guards ku tsananta tsaro, kar a bar kowa ya shiga ko ya fita,"

Ya kalli idanun Sultana a lokacin da yake fadin hakan, saboda ba yau ta saba satar jiki ta fice ba,sai dai ya ji labarin ta kai taimako wajen Wanda ibtila'i ya fadawa.

".....ina nufin kar a bar kowa ya fita, a tsananta tsaro"

Ture hannun shi ta yi daga kafadun ta, cikin hawaye ta ce,

"Me ya sa ba za a ba wa mutanen can tsaro ba kamar yanda ake ba wa wannan gidan? Shin masu gadin mu a gidannan nawa ne? Yawan su bai isa ya kare wani qaramin garin ba? Me ya sa ba za a kai taimako wajen da ya dace ba?.."

"Keep quiet sultana and go inside kafin na saba maki,"

Mota ya bude cikin fushi ya shige, nan da nan kuwa aka kunna jiniya, motocin da ke bashi kariya na biye da ta shi.

Qoqarin durqusawa take a wajen ta na kuka, Sultan ya tallabe ta, sai wutsil wutsil take tana son kwacewa, motar su Lawwali ce ta shiga gidan , Lawwali ne a gaba gefen mai zaman banza, yau ce rana ta farko da ya fara dora idanun shi a kan Sultana, yau ce rana ta farko da ya taba jin wani abu mai nauyin gaske, wanda bai taba jin kalar shi ba a gaba daya rayuwar shi ya soki zuciyar shi, wani irin yanayi ne mai dad'i cike da shauki, da wani dandano wanda bai san yanda zai fassara shi ba, har motar ta tsaya,yaran shi suka fara fitar da wasu buhuna da aka nannade aka ma wani irin dauri, wanda komai kwakkwafin ka ba ka Isa gane me ye a cikin daurin ba, Lawwali na zaune a mota, har Sultan ya yi nasarar dauke Sultana wajen Lawwali bai ma sani ba, ganin ta kawai yake a cikin kwayar idon shi, kamar a mafarki ta na zuwa gaban shi,shi kuwa sai zabga murmushi yake.

"Oga an gama,"

A dan daburce ya kalli No 1,

"Tau tau, ya Yi, shiga mu tahi, kun aje dai inda Excellency yacce ko?"

"Eh oga,"

"Tau ya yi, muje"

Kallon inda ya ga Sultana a duqe ana fama da ita ya sake yi, ya dan saki murmushi,

'shege Excellency, dole ya dinga kaffa kaffa da zuwan mu, ashe ya aje kadara mai tsada a gidan shi,'

Cikin zuciyar shi ya ke wannan tunani, har suka fita daga gidan suka dauki hanyar dajin su bai magana ba, No 1 na Masa magana gaba daya hankalin shi ya tafi wajen tunanin sultana.

*********************

"Ki na nufin har yanzu ba su dawo ba? Kuma ki ke zaune a gida ki ke kukan banza ba ki tafi Nemo su ba? In wani abu ya samu yara na Hansatu sai na maki abinda ya fi qarfin mutuwa azaba, ..ba Zaki tashi ki tafi makarantar tasu ba?"

A tsawace ya Yi maganar, cikin rashin kwarin jiki, da ciwon da qirjin ta ke Mata ta miqe ta nabin bango, duhu ya fara, ko yar touch light dinnan ba ta da shi, ga shi ba wuta a unguwar, cikin duhun da ya fara Shiga, ta nemi takalmin ta, ta dauki mayafin ta, ta fita.

Ko Bai Mata fada ba, ta na da niyyar in ta idar da sallah ta fita Neman su, amma me ya sa ba zai Taya ta ba, zai aika ta? Ko su tafi tare, yaran ai Shima na shi ne, zuciyar ta ce ta sanar da ita cewar,

'Hansatu yau ne kike tare da Isa ? Yau ko ke Kika Bata ai ba zai je Nemo ki ba, ballantana yaran da ya tsana, ya ke ganin su na daga cikin silar talaucin ku'

Hawaye ne masu tsananin zafi ke sauka a fuskar ta, a zuciyar ta kuwa wani irin quna ta ke ji, qirjin ta ne ya sake Yi Mata suka, sai da ta damqi saitin zuciyar ta, ta durqusa a tsakiyar hanyar, da mazajen kirki na unguwar na ta fitowa daga masallaci Dan komawa gidajen su.

A hanyar Isa ya same ta,

"Tsayuwar me kike anan?"

Daga Kai ta Yi a wahale ta ce

"Gaba (qirji)na ka Yi min ciyo, Amma yanzu zan tafi"

"Hummmm"

Shi ne kawai abinda ya fadi ya wuce ta ya na kwafa, da

Please Login or Register in order to submit comment