Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[9/18, 6:22 AM] UmmDiDi👩‍👧: *Da sunan Allah mai rahama maijin qai*





©️®️ *SAFIYYA HUGUMA*


👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
_Ba shiga birni ba_

Mallakar

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*


*_Taqaitaccen labarine wanda ke dauke da kukan kurciya da kuma tsumagiyar kan hanya_*❗


*zaku iya sauraren litattafaina tsofaffi dama sabbabin da zan soma dorawa a dandalin youtube,a tashata ta SAUTIN HIKIMA*

*littafin ALKAWARIN ALLAH yanzu haka yana can nasoma dorashi gamai sha'awar saurare*





Dai dai lokacin qarfe biyu saura na rana ne,tana zaune cikin madaidaicin falon nata wanda ya wadatu da tsafta,gefe guda kayan yaranta ne data debosu daga kan igiya bayan sun bushe tana ninkesu daya bayan daya tana tarawa a gefanta,gefe daya na zuciyarta cunkushe suke da tunani kala daban daban da taketa qoqarin kauda su.

Idanunta tadaga sanda taji an yaye labulen,maman ummi ce ke shigowa hannunta dauke da qaramar yarinyarta da take goyo,idanu mmn amir(mamallakiyar dakin) tabita dasu tana karantarta,lokaci guda duka ta zabge ta rame tayi firgai firgai,haka taci gaba da kallonta harta samu kan daya daga cikin kujerun tazauna sannan ta aje ummi,wadda tana ajeta ta rarrafa tayi wajen mmn amir,yarinyar na qarasowa ta dauketa tana juyata gami dayi mata wasa yarinyar tasoma dariya
"Yanzu maman amir kina ganin zamanmu a haka yayi dai dai kenan?,munaji muna gani haka baban amir zai sake kawo mana wata cikinmu?,muna zamanmu muda yaranmu cikin kwanciyar hankali zai debo mana matsala?" Ta qarashe maganar wanda kana jin sautin muryarta kasan cewa ba qaramin tashin hankalo bane cikin zuciyarta,daga kai mmn amir tayi daga wasan da takewa ummi ta dubi mmn ummin,ba shakka kishi abune mai ciwo dacin zukata,kuma ita kanta zuciyarta kullu yaumin ba cikin dadi take ba duk da cewa ba wannan ne farau a kanta ba,amma ita kishiya kullum sabuwace a wajen mutum,saidai wannan ba komai bane idan aka kwatanta da sanda xa'a auro mata mmn ummin,banda Allah yasanya ta hadu da iyaye nagari,takuma yi yaqi da zuciyarta da wataqila yanzun hakan ba wannan zancan ake ba,cikin kwantar da murya tace
"To yazamuyi mmn ummi?,baban amir dai bamu muka haifeshi ba bare muce zamu hanashi abinda yayi niyya" kai take kadawa da sauri
"Zamu iya hanashi mmn amir indai zamu hada kai mu duka biyun muyi masa bore kamar yadda nakeyi yanzun,yanxunma abinda yasa haqata ta kasa cimma gaci saboda ni kadai naketa qoqarina kinqi kisa min hannu" qaramin murmushi ya subuce daga fuskar mmn amir tana duban mmn ummin,ta tuna wasu shekaru baya da suka shude,lallai wanzami baison jarfa
"Mmn ummi,abinda nakeso ki gane shine,dukkanmu qarqashin bbn amir muke nida ke gaba daya,duk wani abu da zamuyi don mu tashi hankali komu hanashi aure bamu da riba don Allah ne ya halasta masa,bugu da qari da haka nayi a baya da wala'alla nima bana bigiren da nake kai a yanzu,abinda dai na gayamikin shi zanci gaba da gaya miki,kiyita haquri ki kauda kai,komai yayi farko yana da qarshe,kuma babu wani abu dawwamamme sai ikon Allah,watarana sai labari,hakanan me haquri shike da riba" miqewa mmn ummi tayi cikin fushi da rashin gamsuwa,baki tadan tabe
"Munaji muna gani mmn amir wlh zamu zama 'yan kallo idan bamuyi da gaske ba,ke kuwa kinsan yadda yarinyarnan ta mallake baban amir?,hala bai taba waya da ita a gabanki bane saini daya raina?" Murmushi ta sake saki
"Ba rainakin da yayi,face ke da kokaqi tsayawa ki fahinci komai..."
"Mmn amir" mmn ummi tayi saurin dakatar da ita
"Wallahi wallahi yarinyar ban labarinta kaf yazomin kunnena,duk cika da batsewar unguwarsu babu tantiriyar yarinya mara kunya irinta,inata boye miki ina miki hannunka mai sanda amma na fuskanci baki gane ba,yana daya daga cikin abinda yasa hankalina yasake tashi kenan,bin malamai take kamar tashin hankali,ki fuskanta mmn amir muyiwa kanmu gata tun batazo ta fiddamu daga cikin yaranmu ba" tsai tayi tana duban yadda mmn ummi ta sake firgicewa,sai data gama sannan tace
"Zauna don Allah mmn ummi muyi magana ta qarshe dake" kaman bazata zauna ba,amma dole tazauna din don neman hadin kai da mafita take,sai data tattara dukka hankalinta akanta sannan tace
"Kin yarda da Allah mmn ummi?" Kaita gyada tana dubanta
"Indai haka ne to ki yarda da cewa babu wata halitta data isa ta cutar dake saoda yardar mahaliccinki,sannan matuqar zuciyarki a wanke take ba wani abu mummuna da xai sameki saidai idan qaddararki ce,duka wannan abun da kikewa baban amir bashi bane zai sanya ya fasa aurensa ba,saima qara nisanta kanki dashi da kike,idan kyautatawa na saka namiji ya qara aure da baban amir bai auroki ba,amma da lokaci yayi hakanan na haqura,na shanye duk abinda yabiyo baya na kama kaina na haqura,wannan abun da kike ba mafita bane,tashin hankali bazai qara miki komai ba sai wani tashin hankalin,ki nutsu don Allah ki sawa ranki haquri da salama" shuru mmn ummin tayi,wanda kafin takai ga cewa wani abu anyi sallama a tsakar gidan nasu,dukansu suka amsa suka zubawa qofa idanu don ganin wanda zai shigo.

Ba jimawa baquwar tayi sallama a qfar dakin mman amir din sannan ta daga labulen tashigo,cikin fara'a maman amir din tayi mata maraba duk da cewa baquwar mmn ummi ce,amma yanayin da mmn ummin ke ciki yasa ta kasa sakin fuska ko tarbarta,gaisawa sukayi sosai cikin mutunci sannan tadubi mmn ummi
"Lafiya kike kuwa maryam?" Baquwar tafada tana duban mmn ummi,shuru mmn amir tayi tana ci gaba da ninke kayanta ba tare data saka musu baki ba,ajiyar zuciya mmn ummi tasaki ba tare data bata amsa ba,saita waiwaya taba duban mmn amir
"Mmn amir lafiya kuwa?" Sai a sannan ta dubi baquwar,tasan cewa qawace sosai ga mmn ummi kuma makusanciyarta,don haka tasan da cewa tasan komai
"Kiwa maryam fada wala'alla keta yarda da zancanki,kan maganar qarin auren bbn amir,gaba daya ta daga hankalinta tafita hayyacinta,ba abinda ban gaya mata ba taqi ji,wai ai tasan halin yarinyar anxo an gaya mata"
"Eh fa,da wannan don wannan,yarinya fa kusan halinta a bayyane yake koni nayi bincike,mara kunyace ta qarshe,sannan ko a gidansu uwarta itake juya ubanta,sai abinda tace,bata ganin kowa da gashi" sosai gaban mmn amir ya fadi,amma saita ambaci sunan Allah ta kuna kauda tsoronta,donta tabbatar idan har hakan ya bayyana to kamar ta baiwa kanta dasu qofa ne
"Idan harka riqe Allah zai isar maka,yakuma tare maka abinda yafi qarfinka"
"Hakane,amma dole ku tashi tsaye,kuyi duk yadda zakuyi wallahi,don nikam ina jiye muku"
"Abinda naketason ta fahimta kenan amma taqi ta gane" mmn ummi tasamu bakin magana a wannan gabar
"Ahto dai" baquwar mai suna rashida tamiqe tana daukan ummi sannan tace
"Bari mu qarasa ciki"
"Toh" kawai mmn amir ta fada,jikinta a sanyaye saidai tana qoqarin qwararawa kanta gwiwa,mmn ummin tabi bayanta suka fice.


**************


Cikin nishadi da walwala ta kashe wayar,fuskarta washe fes tana jin wani farinciki na gewayata,ji take kaman ta mallako baban amir ta gama
"Gaskiya kina sha'aninki rufaida,kinacin duniyarki da tsinke,kin samu mutumin nan fa a hannu yadda ya kamata" dariya rufaida ta sheqe daita
"Wata abu takazar ubanma saina shiga gidan,kinsan Allah?,gaba daya tausayin matansa nakeji" wata muguwar dariya zahra'u tasaki
"Wallahi harkinsa na hango randa zan shiga gidan auwal,ni kaina matarsa tausaya mata nake" kai kawai rufaida ke kadawa cikin nishadi da gadara,tana hango yadda zata maidasu
"Na rantse da Allah duk saisun raina kansu,sainasa a karan kansu sunji cewa su gidadawane basu iya komai ba,sai baqinciki yakusa hallakasu saboda ganin zallar madarar soyayyar da xa'a dinga zubarwa a gidan,zasu gane kurensu,zasuyi danasanin hada kishi dani"
"Allah yakai damo ga harawa" zahra'u ta fada cikin qyaqyata dariya,sai a sannan fatima dake zaune gefe tayi magana
"Wallahi wallahi zahrau da rufaida kuji tsoron Allah gaba dayanku,haka kawai bayin Allah nazaune da mazajensu da yaransu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali zaku je musu da mugun tanadi da baqin qulli na tarwatsa zaman lafiyarsu?,waishinma ce muku akayi matan nasu gazawa sukayi da yasa zasu aureku?"
"Gazawa sukayi mana!.....idan banda tsabar gazawa ta yaya zaki bari mijinki yaga wata harya aura,wallahi dani yasoma aura ko mace daya bazan bari yaqaro ba bare biyu,da basu gaza ba da basu nemu ba" cewar rufaida tana tafa hannuwa gami da jefawa fatima harara
"Kinga qyale wannan,batasan dawar garinba da Allah,ai babu cinyewa da nuna isarki,ki nunawa mace kurenta,ki kuma nuna mata cewa keba sa'arta bace,wutsuyar raqumi tayi nesa da qasa irin ki shiga ki taddata kiyo waje da ita"
"Shine qarshen magana" rufaida tafada tana tattare katin bikinta daya kawo mata dazun tanason tasoma rabo sati mai zuwa,kallonsu kawai fatima take tana kada kai,lallai wanda yayi nisa baya jin kira,ta tabbatar su rufaida sunyi nisa cikin kuskure
"Tashi don Allah tawan mu wuce,igbo road nakeso mu soma zuwa zan kwaso qananun kaya na tarwatsa zuciyar kishiya ya halakata saboda tsabar kishi,kin gansu nan dubu ashirince cif yakawominsu inje in siya" shewa suka saka bayan sun tafa
"Muje muje muje,mu zabi qarshen magana,amm fatima,don Allah idan kin gama ki gayamin saina sameki a gida" rufaida ta fada tana yada mayafinta cikin sauri,har suka fice fatiman bata iya sake cewa komai ba face binsu da kallo da takeyi.
[9/18, 6:22 AM] UmmDiDi👩‍👧: 👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA* 👁️‍🗨️👁️‍🗨️
_Ba shiga birni ba_


©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*


*BABI NA BIYU*



Bakwai da rabi na dare bayan sun gama sallar isha'i,tana tsakiyar yaran suna aikin gida da aka basu a islamiyya,yaranta ne guda hudu,amir,ahmad,hanifa da rabi'a,sai yaran mmn ummi guda biyu mubarak da usman,wanda da can baya sai da aka kai ruwa rana kan donme mmn ummin zata dinga yiwa yaran aikin makaranta?,ko cewa akayi itadin bata iyaba ko bata da karatun,saida suka kai ruwa rana ita da baban amir kafin ta sauko ta haqura.

Tana daga gefe tana kallonsu,hannunta daya saman cikinta wanda yafara nauyi,kadan kadan tunaninta na tafiya kan zuwan hafsat shekaran jiya gidan,wanda hakan yasake sawa mmn ummin takumsa sauyawa,har ita kanta tasake sauya mata,dan hadin kan da rabarta da take tasake janyewa,wanda ita ko kadan bai mata dadi ba,tasani cewa dole sai sun wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu sannan koma wacece xata shigo daga baya itama tayi koyi dasu.

Sallamar baban amir ita ta katse mata tunaninta,suka hada idanu sanda yaran ke rige rigen isa gareshi su rungumeshi gami dayi masa sannu da zuwa,ya qaraso dakin yanaji da sannu da zuwan yaran,tayi qoqarin qaqaro murmushi saman fuskarta tana masa sannu da zuwa,amsa mata yayi yana nazartarta,yanajin tausayi tausayinta yana kamashi,haliman taci sunanta qwarai shi kansa yasan da hakan,komai Allah shike tsarawa dan adam shi,auren maryam na cikin qaddararsa,haka rufaida da yakejin sonta cikin jikinsa,hakanan yana jin cewa tayi dai dai dashi ta kuma dace da ra'ayinsa,banda hakan babu abinda halima mmn amir tarasa,wanda daa a baya baisan da hakan ba,kafin ya auri maryam ganin gazawar haliman yake,gani yake kaman nata iya komai ba,akwai abubuwa da yawa da bata iya masashi wanda yake hasashen samunsa gurin wata macen,ashe Allah ya tsara masa auren maryam ne don ya fidda qima da darajat haliman a idanunsa,sai bayan ya auri maryma ne ya tabbatar haliman ba kayan banza bace,wannan dalili yasa yake matuqar ganin qimarta da qoqarin kyutata mata,gefe guda kuma yanajin kunya da nauyin abubuwan daya ringa aikata mata lokacin da idanunsa suka rufe yana neman auren maryam,wanda yayi imanin cikin kawaici da yakana ta halima haryau wani abun bata gayawa maryam shidin ya mata ba lokacin neman aurenta,sai gashi ayanxu yana samun sassauci da sauqi daga wajen haliman fiye da maryam,wadda ta bazawa idanunta kwalli,takuma shafawa fuskarta toka ta fitittike kamar basu taba wani abu soyayya ba kan auren da zai qara
"Sannu da zuww" haliman ta katse masa tunaninsa,ajiyar zuciya yasaki a boye
"Yauwa halima,kece da sannu,ya nauyin jikin?" Ya qarasa fada yana bude ledar daya shigo da tsarabar da yayiwa yaran nashi yasoma raba musu,murmushi kawai tasaki
"Alhmdlh" ta fada kawai a taqaice,sai daya gama rabawa yaran duka tana zaune tana kallonsu sannan yacewa amir
"Jeka kiramin antynku,banji motsinta ba" aje kayan hannunsa yaron yayi yafita kiran kamar yadda ya umarceshi.

Minti biyu amir din yadawo
"Abba,tace ba zata iya tasowa ba batajin dadi"
"Kace magana zanyi dasu,tazo injini" dakatar dasu mmn amir tayi
"A'ah,tunda bazata iya tasowa ba ka taddata can mana,yaukam batajin dadi sosai don tun daxun data gama aikima tana daki kwance" jim bban amir yayi,don yana tantamar hakan,don lokacin dayashigo tsakar gidan yana ganin sanda tashige dakinta abunta,ba tare data kula da sallamar da yakeyi ba,amma yasan mmn amir din taui hakane saboda akaucewa idanun yaran,saboda haka yace
"Shikenan,in zaki iya tasowa ki sameni a dakin nata" yafada yana miqewa yadauki manyan ledojin yafice.

Sai data basu wasu mintuna sannan ta yunqura tamiqe tabi bayanshi
"Ai dama ko bakayi hakan ba nasani ba wani sona ko damuwa kayi dani ba,ta yaya ranar girkina zaka wani shige dakinta kuma ka aika wai naxo.....to wallahi bbn amir ni bazan dauki wannan ba,tun yanxu wallahi tallahi donma kasani" duk abinda take fada cikin kunnenta suka fada,amma sai tayi kaman batajiba tayi sallama tashiga,sallamar tata tasa bbn amir din bai maida mata amsa ba,saita samu waje tazauna tana yiwa mmn ummin sannu da jiki,zama yayi yasoma bude ledojin yafito dakayan ciki,yayin da take tsaye har yanzu taqi zama
"Gashinan,kayan fadar kishiyane,kowacce saita dauki leda daya" jiki a sanyaye mmn amir ta sa hannu tadauki leda daya tana cewa
"An gode,Allah ya amfana" tana daga tsaye tanajin kaman zata fashe da kuka,wani mugun kishi yana ratsata,wato dai da gaske yake bazai fasa din ba kenan,kai ta gyada cikin fada da bala'i tace
"Tabdijan,duk wani rashin adalcinka muraran yafito wallahi jibril,ka narkawa amarya kaya akwati akwati kalar wanda takeso,mu kuma shine zaka dubemu da wadan nan 'yan tsirarun kayan da basu wuce kala goma goma ba?" Ta fada tana nunasu cikin rainuwa,kai ya daga ya kalleta
"Ke kin manta kala nawa akayimiki?,shine yanzu yazama laifi don an yiwa wata?"
"Au hakama zakace?,wato bban amir gidan nan bau shegiya banza kamarni,to idan haka ne ita mmn amir daka yi mata kai daya da nawa,nan da wata uku kazo kasake mata na haihuwa taci tudu biyu kenan ni tudu daya?" Bacin ran baban amir yaqi boyuwa,cikin fada da hargagi yace
"Ke malama kin fara isata fa kin soma kaini bango,uwatace ke da dai abinda kika tsaramin zanyi?,don kinga ina daga miki qafa ina qyaleki?,to na rantse da Allah ki shiga hankalinki,banason hauka da iskanci kinji ko?" Da sauri mmn amir ta dakatar dashi
"Don Allah kayi a hankali yara zasu iya jiyowa,indai kaya ne ni saina qara mata a nawan tunda ni xakamin na haihuwa idan Allah yakaimu da rai da lafiya"
"Bata isaba wallahi saidai idan kada ta saka" ya fada yanajin nauyi da kunya da tuna sanda ya hana mmn amir din ko tsinke sanda zai auro maryam din da sunan kayan fadan kishiya,a sannan yace mata bashi da kudi,bayan ba haka bane ita kanta tasani amma ta qyaleshi bata sale daga maganar ba,sai kayan fitar sunan ahmad ta saka
"Lallai samu yafi iyawa" mmn amir din ta fada a ranta itama tana tuna lokaci irin haka da za'a kawo mata maryam din a matsayin kishiya,tunda harya riga daya rabtse gaka ta tattara kayan nata tafito tabar musu dakin,don ta tabbatar yau din Allah ne kadai yasan wainar da za'a toya tsakaninsu,tayi imani cewa da maryam ce uta a wancan lokacin da tuni tajima da barin gidan,cin kashin da yayi mata lokacin aurenta dashi a yanzu ko rabinsa baiyi ba,tayi imani Allah baya barci,kuma duk abinda kayi sai an maka mafiyinsa,gashi tun ba'aje ko ina ba tana dandana irin abinda ta dandana itama,ashe nata salama ne tunda ta iya haquri da mallakar kanta.

_WASHEGARI_


K'arfe shida na sassafiyar ranar maman amir na kwance saman gadonta,tun bayan data idar da sallar asuba bata koma ba,idanunta biyu sai azkar da takeyi wanda idan tagama saita sake dauko wani.

Daga bakin uwar dakin nata taji sallamar ahmad,kamar yadda ta koyar musu shigo mata daki sai sun tsaya sunyi sallama tabasu izini,kai ta daga ta amsa masa sallamar sannan yashigo,ya gidata duk da qananun shekarunsa ta amsa
"Umma,mama batayi mana wankan ba,kuma lokacin makaranta yana qurewa" shuru tadanyi,al'adarsu shine duk wadda keda girki ita zatawa qananun wanka sannan tashirya musu abinci naci dana tafiya makaranta,tunda taga haka tasancewa lallai jiyan anyi bacin raine ita da baban amir
"Shikenan,bari na taso nayi muku,duba min kettle din idan da akwai ruwa kazo ka gayamin".

Dai dai lokacin da yake duba kettle din abban nasu yashigo
"me kake anan?ina shirin makarantar taku?"
"Umma ce tace na duba ko akwai ruwa a ciki
" ba'ayi ma wankan ba kenan?"kai kawai yaron ya daga,sosai yaji ranshi yabaci,wato shi zata nunama iyakarshi kenan?,a fusace ya qarasa qofar dakin nata ya yaye labulen yashiga.

Tana zaune gefan gadonta tana baiwa ummi nono,idanun nan a kumbure hakama fuskarta,gaba daya jin duniyar take ta juya mata baya,batajin dadin komai,kamar tafita tabar mishi gidan haka takeji,jiya kwana tayi kuka,har sanda mmn amir tafito ta daura alwalarta ta ka'ida takoma daki duk tana jinta.

"Wadan nan yaran?,wa kika barwasu?,waye zai musu wanka?"wani kallo ta dago ta watsa masa
" oho,kaje ka kira wancan tantiriyar da zaka auro tayi musu,tunda mu bamu isar maka ba,kaga gwara mu zame hannuwanmu ita tazo tayi abinda mu muka kasa ko bamu dashi"yana sane yasaki murmushi
"Me kike ci na baka na zuba?,tana nan zuwa kuma zatayin,amma a yanzun dole ki tashi kiyi kafin nata lokacin" sosai maganar tashi tasake bata mata rai ta kuma dugunzumata,wato babu abinda zai fasa kenan gameda abinda ya niyyata,har yana ma mayar mata da magana,nan fa sa'insa ta kaure tsakaninsu,kowanne ranshi yabaci yasoma maidawa dan uwanshi da magana.

Dai dai lokacin da mmn amir tafito tsakar gidan don hada kan yaran tayi musu wanka taji tashin muryoyinsu,gefe daya amir na tsaye fuskarsa cikin damuwa shida ahmad,kada yaran tayi dakinta sannan ta fada dakin mmn ummin
"Haba haba baban amir,bai kamata bafa,kuna abu kaman yara?,duk kunsa hankalin yara yayi kanku?,kiyi shuru mmn ummi mana haba"
"Kinga ba abinda yashafeki,ki qyaleni dashi wallahi,duk wani take takensa na gama ganeshi,tunda ke baki iya qwatarwa kanki 'yanci ki barni nina qwaci 'yancina"
"Don Allah kiyi shuru mmn ummi,haba mana"
"Qyaleta halima,barta tayi,dani take zancan na rantse da girman Allah,tunda aka tada zancan nan kin hana kowa hutawa?,saikace ke daya ce macw cikin gidan nan?,to kiyi duk haukar da zakiyi ki gama,aurene dai babu fashi sai nayishi"
"Ka fada duk abinda kakeso mana jibril,ai namiji kake,batulu,namiji ai dama hankaka ne,gabanka fari bayanka baqi,ka manta lokacin daka dinga daukarmin qawuran bayanni babu wata?,kamanta sanda kake neman aurena ido rufe kanason nashigo gidanka na haska maka shi na zamemaka fitila saboda gidan ya maka duhu acewarka a sannan?,shine zakayimin butulci a yanzu?"duk ya tuna,ya tuna komai,nauyi da kunyar mmn amir suka dabaibayeshi,gashi da alama mmn ummin tonon silili takeson masa,da sake tada husuma,tanasone ya rasa kwanciyar hankali da biyayyar da yake samu wajen haliman kenan?
"kinga maryam,tunda ke baki da mutunci,bakisan darajar mijinki ba to xama babu dole,ki tattara ya naki ya naki ki tafi,don bazan zauna kina haddasamin bala'i da masifa ba tun yanzu"
"Ashasha,haba baban amir haba?,wannan ma aiba zance bane" inji mmn amir duk ranta a jagule,baiko sauraretaba yafice abinsa,don tabarmar kunya yakeso ya nade dama da hauka kada ya baro wani zance daya shafi tsakaninsa da mmn amir din.

Kuka sosai mmn ummin take,ta nemi gefan kujera taxauna tana ci gaba da kukanta,amir ta qwalawa kira tace yayiwa 'yan uwan nasa wanka,ya saka musu unifoarm tan nan fitowa,sannan ta sake maida hankalinta ga mmn ummi
"Kinga irinta ko?,kinga irin abinda nake gaya miki,akan wata can a waje da batama kai ga shigowa ba har yanzu zaki girgide aurenki,ki fita kibar yaranki wanda baki da yaqini ko tabbacin yadda rayuwarsu zata kasance,yanzu wa gari ya waya?" Itadai batace komai ba sai kuka da take faman sheqa,mamaki duk ya cikata tana tuna soyayyar da suka zuba ita da baban amir,ko a mafarki bata taba tsammatar irin haka zata faru ba,shuru ya ratsa dakin kafin mmn amir tamiqe tana cewa
"Ba inda zaki,ina zuwa" ta juya tafice daga dakin da niyyar baiwa baban amir baki,saidai koda taje dakin nashi bainan,ahmad ya gaya mata yafita,saboda haka ta sauya akalar tata zuwa dakin girki ta dorawa yaran ruwan tea,tanayi tana tunani cikin ranta.

******************

"Haba don Allah dear,nifa banason ka dinga bata ranka a banza a wofi,yanzu kamar kai ace kana teburin me shayi wannan ai zubarmin da mutunci kawai kayi" jim tayi ma wasu mintina sannan tace
"Aini wallahi banga wani abu da xakayimin da har zai kaimu ga haka bama,nidai don Allah ka koma gida koka qaraso nan gidam anty luba na hada maka break,tunda su duka basu damu dakai ba nina damu dakai" sake shuru tayi kafin daga bisani tace
"Toh shikenan,i love you" daga haka ta aje wayar tana murmushi
"Uhmmm,rufaida kenan,ke naga ko a jikinki ma,da aketa jiye miki shiga tsakiyar mata biyu" dariya tasaki kafin ta tabe baki
"Mata biyu ko muna mata,nifa wallahi anty ko a jikina,wadan nan niban daukesu a bakin komai ba,kada madai uwar gidan nan tashi taji labari,wadda ko isasheshen ilim boko bata da,yadda kikasan matar ladar noma,gwara gwara ma ta biyun itace kawai nakega tafi fada a wajensa fiye data farkon,haba anty,me zanji,kamata?,nida nake da karatu har matakin degree dame zasu tsoratani?,wancan mai kwalin diploma din ko dayar da banda kwalin

Please Login or Register in order to submit comment