Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na gode Maka,na gode Maka Allah da baka barni na wulaqanta wannan kyauta Mai daraja daka yimin ba,halima.....Allah yayi Miki albarka sau babu adadi" sassanyar murmushi tasaki,wani farinciki itama Yana ratsata,ba shakka farinciki Miji shine farincikin duk wata mace tagari "Amma banjin zan sake gangancin barinki ki dauki hutu Koda 'yan hudu xaki Haifa,na fuskanci wani horo kamar Kika yimin a fakaice"idanunta tajuya kawai Tana dariya,kusan zata iyacewa ya canka.


A lokacin zuciyarta na cike taf da qunci da kuma kishinsa,Bata da wata hanyar da zata baiwa jiki da zuciyarta hutu a sannan Banda ta sallama musu Shi,ta gama karantar next level da rayuwar gidan nasu ta fada a nutse kafin tasan hanyar da zata bi ta magance komai, beside ma Tana da buqatar hutun na haqiqa a halin da take ciki Don tasamu ta rabu da cikin dake jikinta lafiya,alhmdlh koma meye kwalliya ta biya kudin sabulu dari bisa dari. Hirarrakine masu Dadi Suka biyo baya tsakanin ma'auratan,wadanda Suka qara musu wata qaunar juna dakuma fahimtar juna din.


Bayan wani lokaci bbn amir din yakoma yasake kwanciya kafin lokacin fitarshi,bata bari takoma ba saboda tasan akwai shirin yara makaranta da sallamar maigidan da gidan kanshi,don haka gari na qara sha tafita ta kama ayyukanta bayan ta tabbatar da duka yaran sunyi sallah


Bakwai da rabi na safe kusan komai ya kammala,don yaran duka sun shirya kowanne kuma da abincinsa na tafiya makaranta,yau dinma mai adaidaitanne zai kaisu,saboda haka ta sallamesu suka wuce ba tare data bari sun tada bbn nasu ba,sai data gama dasu sannan tadawo ya kama sauran abubuwan da suka rage matan.


Takwas da rabi rufaida tashigo kitchen din inda take wanke wanke tana raba idanu,kusan tun sassafen takula da cewa idanunta biyu,da alamu kuma baqin kishi ya hanata sukuni ne,kallo daya tayi mata ta dauke kai,idanun rufaidan kawai sun isa shaida maka bata samu isashshen bacci ba,kamar zata saki dariya saidai idan tayi hakan tasan cewa kamar ta siyawa kanta raini ne,don haka saita dauke kai taci gaba da abinda take.


Qerere take tambayatta abun kari,bawai don zataci ba,ta tanbaya ne don tace bata gama ba ko babu kodai wani abun makamancin hakan ta tada bala'i cikin gidan wanda zai tada bbn amir din ba tare daya shirya ba,saidai kafin abun takaicin da hannu ta mata nuni da inda natan yake ba tare data dubeta ba,sanda ta isa daki taga yadda ta shirya break fast din sai baqinciki ya kamata
"Wai ita komai sai tayi wanda yafi nawa,duk yadda nake haqilo da qoqari amma saitayi wani abun daya wuce hankali,yanzu don Allah yaushe ka tashi ka sallami yara ka gyara gida kayi wadan nan soye soyen,bayan kitchen din ma dukka kayan abincin nasu yayi low sosai,saboda wannan yanayin na batan kayansu bbn amir din" haka tazauna tana cizon yatsa.


To kusan dukka kwanakin da mmn amir tayi na girkinta babu abunda ta tsinta sai bacin rai da baqinciki,don a yanzun sam mmn ummi ma bata gabanta,mmn amir din tafi tsaye mata a rai,babu ma kamar ranar da bbn amir din yatashi babu ko sisi a hannunsa yasa mmn amir din tabata kudin cefanen abincin gidan gaba daya,ranar ji tayi ina wuta ta sanyata.


Da fari ya tsammaci dokin komawarta dakin miji ne bayan ta gama jego yasa mmn amir yin duk abinda takeyi din,ta tsammaci da an kwana biyu zata watsar da komai,saidai ga mamakinta saitaga babu abinda ta fasa kota janye,saita daura damara itama tasoma bin sahu,da mmn amir din ta ankara sai abun yadinga bata dariya,saidai ko daya bata damu ba,tasan cewa abun alfaharine a wajenta tazama kamar wata makaranta abar koyi wajen kishiyoyinta,saidai da yake abun a jini yake,tun ba'aje ko ina ba ta watsar saboda gajiya da tayi.


Lokacin da tafiya tayi nisa sai taji ba zata iya jurewa ba,kamar dukan yana neman yi mata yawa ne,ga mari ga tsinka jaka,bbn amir din nasake shiga rashi ga kuma mmn amir din data fuskanci itako a jikinta albarkacin sana'a,kusanma ma lokutta da yawa itake bada kudin cefane babu gori wariya ko nuna damuwa,wanda mmn ummi ma tuni ta kama sana'a da taimakon mmn amir din data ranta mata kudi tana juyawa,hakan yasanya ta yanke shawara,yanzun babu wata hanya data rage mata ko wani zabi da take dashi banda takoma gidan mariya qawarta ta rakata gidan malamin da tace mata tasamu,duk da babu wani cikakken kudi da take samu a aljihun bbn amir din,don shima bawani kudi yake shigowa dashi ba,amma kuma ta fannin kayan abincin da takewa dauki dai dai tana tarawa qasan gadonta tasan zuwa yanzu ta tara da yawa,hakanan idan ta saida zasu hada mata kudaden da takeso



*_SHUKA A IDON MAKWARWA_*


A hankali cikin sanda tashigo dakin nata sanye da hijabi wanda ta boyo taliya guda biyu aciki,tun jiya da aka kawo cartoon na taliyar qwaya daya da aka baiwa bbn amir din kyauta idanunta suke kai,don tanaso ta cike taliyar data dinga zara da ɗai da ɗai ta cika cartoon itama idan zata fita anjima kan ta shiga gidan mariya tatsaya a wani shagon tasiyar,tasan idan ta hada da shinkafar data tara wadda a qalla takusa kwano goma da semovita wajen jaka goma shima zata samu kudaden da zasu isa a soma mata aiki kan bbn amir din da sauran matan gidan duka harda yaran ma idan ta kama.


Tun sassafe tatashi da niyyar xata sallami 'yan makaranta ne,anu ya baiwa shi kansa bbn amir din mamaki don yasan yadda ake daga da ita kafin ta shirya yaran amma yau gashi da kanta tayi tashin sammakon,bai tanka ba dai yakoma ya kwanta,tsam ta tsaya tana dunan bbn amir dake bacci gefan gadon nata,tana son ta tabbatar baccin yake ko idonsa biyu.


Sai data tabbatar bacci yake sannan ta lallaba don kada ta tadashi,ta duqa qasan gadon ta jawo jakar datake tara kayan a hankali,ta zauna sosai qasan gadon tasoma irga yawan taliyar,sai data tabbar guda ashirin da biyu ce ashirin da hudu harda wadda zata saka sannan tasaki murmushi,taciro ta cikin hijabinta ta saka kana ta nannade bakin ledar zata tura ta mayar.


Ga mamakinta sai ganin mutum tayi yatashi yazauna gefan gadon,wani irin xabura tayi sannan cikin rudani tasoma qoqarin maida ledar ta qarfin tsiya.


Idanu kawai yazuba mata yana kallon yadda ta hautsine,tabbas yajima yana lura da yadda ake masa dauki dai dai a binci,kuma ba komai yajawo hakan ba da har yayi saurin fahimta face yanzu bashi dashi,kusan abincin kai da kai ake siyowa idan an samu ma,wani lokacinma sai sun irga zaikai musu kwana kaza kafin yaqare,amma abun mamaki sai a rasa na kwana daya,wanda inda sanda yake da wadata ne yake ajewa da yawa ba lallai ya fahimta ba,bai taba zargin kowa ba cikin matansa saidai kuma abun yana bashi mamaki.


Hannu yamiqa yace "miqomin na tayaki irgawa" saita hau kame kame
"Menene?,me zaka irga?" Hannu kawai ya saka ya janyo ledar duk da yadda take qoqarin hanashi,ya zazzage dukka taliyar yana qare musu kallo,ba shakka kayan abincinsa ne,hakanan yaji bai gama aminta ba,saiya miqa hannunsa qasan gadon,sai gashi ya jawo ledar taliya da semo,semovitan da aka dinga nema harda buhunsa da yace su adana saboda idan an tashi siyan shinkafa azuba a ciki tunda buhun mai qwarine.


Idanu ya daga yana dubanta,fuskarsa da zuciyarsa cike fal da mamakinta
"Rufaida?" Yadda yakiratan ya tabbatar mata akwai qura,kuma matuqar ta yadda ta amsa laifinta kota nuna karaya ko nadama to zata kunyata ce a banza a wajensa,donta lura qurar babu ce take bugunsa,zai iya sauketa akanta,gwara ta tsaya da qafafunta daga baya idan suka haura sa sauko,don haka sai tayi kicin kicin ta hade rantsa tsaf kanta tsaye kuma ta amsa kiran sunanta da yayin itama take duban tsakiyar idanunsa.


Cikin sanyin murya dake nuna mamaki yace
"Rufaida diban kayan abincin mijinki?,kinsan ma'anar hakan?,sata fa kenan?" Ya fada cikin yanayin mamaki yana ci gaba da dubanta,zuciyarta ke gaya mata maza zuma ne sai an cisu da wuta,kuma tabbas idan tayi masa lako lako ita zata sha wuya,tabarmar kunya kuma da hauka ake nadeta,bugu da qari bataga illa ko aibu na abunda ta aikata ba,tunda tunsanda ta aureshi meta samu?,meta tsinta?,ba gwara rayuwarsu a waje ba sau dubun dubata,hannu ta daga masa cikin tsiwa dason nade tabarmar kunya
"Karka sake ambatarmin lafazin sata,don ni ba barauniya bace,don na diba kayan abinci naga na mijina ne ai,haka kawai kai baka iya morawa mutum komai ba,kullum gwara jiya da yau,sannan kuma ace mutum bazai yi wadda zata fishsheshi ba?,to wallahi niba barauniya bace,karkasa sake cewa nayi sata ehe" ta qarasa fada tana juya mishi qeya,sosai abun ya daure mishi kai,yasoma gajiya da rashin mutuncin rufaida,rabonshi da wani mu'amalar arziqi ta hadasu tun a waje lokacin da ake honey da darling,bata iya magana ba sam haka take,baga shi ba,baga matansa ba baga 'yan uwanshi ba,har yau qannenshi basu shiga dakinta idan sunzo saboda ta yanko magana ta gaya mutun wannan ba damuwarta bane,yana sane da yadda take qananun maganganu kan halin babun daya shiga tundaga babbar sallar da basu samu layya ba har yau mita da gori take masa kamar shi ya dorawa kanshi,koda yake kuka da mmn ummi gwara ita sau dubu akan rufaidan,don ita takan qyara wani lokaci kodan mmn amir,amma banda rufaida,sannan koda bata so a kaso goma idan tayi masa halinnata zata bashi haquri koda kaso uku ne amma sam wannan banda rufaida,qoqarinsa har kullum a banza yake,kullum gajiyayyene shi a wajenta.


"Ni wallahi nasoma gajiya,na gaji da wannan rayuwar,aure babu wani ci gaba?,haba da Allah,idan banda tsiya da talauci ma meye donka debi abincin gidan mijinka?"
"Ni kike kirawa tsiya da talauci rufaida a gaban idona?,nine matsiyacin?" Yafurta cikin mamaki
"Eh aiba qarya nayi ba,gidan nan kowa yasani mun fada cikin tsiya wallahi" kai ya jinjina ranshi yana wani irin baci,kowa yasani sautari wasu magidantan kan shiga depression idan suka shiga halin rashi ko babu,sukan muzanta su dinga tsargar kansu musamman mutumin daya sana hidimawa iyali yau a tashi bashi da abun basu saidai su su bashi
"Tsiyarma da takai ace matarka ce take cida kai,kishiyarki itake miki cefane?,haba wallahi munci baya" tsawa ya daka mata cikin zafin rai
"Ki iya bakinki" saita tafa hannu
"Wai meye na fada qarya ne a ciki jibril,nida aka cuta fa niya kamata na tuzura haka" ya fuskanci so take ta sanyashi ya aikata wani abun da zai sanyashi dana sani,saiya dauki hularsa ransa na suya
"Ki wuce gidanku,saina nemeki"
"Tafi nono fari,solobiyo karan mata" ta fada da qarfi har zuwa tsakar gida ana jinta,tana tafa hannu da kama qugu.


Wani bacin rai yadinga bijiro mata,tadinga tuna wace ita,kamar ita rufaida da tayi tashen samari kala daban daban,kaf unguwarsu zuwa makarantarsu babu wanda baisanta ba,babu yarinya kamarta,bata mantawa a wata takan dinka sutura kala daban daban,sai wadda ta zaba,don duk saurayin datace mishi ga abinda takeso bai tsallake zancanta zai kawo mata,wani farinjini tazuba wanda har tayi aure ba'ayi kamarta ba,ta kafa tarihi,don rufaida indai matsala ta kudice bata da ita,vare katin waya da kana iya samun sama da dubu biyar credit na wayarta,abincin gidansu sai randa taso takeci,kayan qyale qyale da kwalliya a wajenta 'yammatan unguwarsu suke aro,amma yau ace ita jibril yayiwa haka?,tafi qarfin wulaqanci namiji,kuma don tayi aure ba'ace tazauna adinga mata komai tana jan baki tana shuru kamar batasan 'yancinta ko ciwon kanta ba.


Sam su mmn amir basusan me yake faruwa ba,sunyi tsammanin kawai unguwa taje,saida aka kwana washegari taji suna waya da innarsa
"Duk da abinda tayimin inna bani nace tatafi ba,saboda nasani cewa da zarar nace taje gidan duk gaskiyata za'a ga don ina cikin babune yasa na aikata hakan" sai yayi shuru yana sauraren abinda innar take fada sannan yasake cewa
"Kiyi haquri inna,bazan iya binta ko zuwa bikonta ba,kuma su dinma babu wanda yacemin wani abu" daga qarshe yace
"To shikenan inna saina shigo".


Tun basu da niyyar yi masa magana har sai da suka masa kan rufaidan ganin lokaci na turawa amma yaqi batunta,ita mmn ummi ma cewa tayi uffan bazata ce ba,mmn amir ce tace
"ba wani abu bane mmn ummi,kodon 'yan uwantaka ta musulunci aima tuntubeshi muji,ko meye rufaida tayi mana zamufi fatan gyaruwarta akan rabuwarsu".


Sanda suka masa maganar kuwa dukka saida ransu yabaci,don hakanan yaji yasamu wani inner peace tawani bangaren,damuwarsu ta ragu,babu wadda ke tada masa hankalin cikinsu don bai bata wani abuba sabida dukkaninsu suna sana'arsu,babu mai yada masa habaici saboda anci fara damai,babu mai uzzura masa saboda abinci babu nama,babu me daura masa lalurar da suka san bashi da ita,kowacce tayi haquri da yanayin da ake ciki,saima qoqarin sawwaqa masa da taimaka masa da sukeyi da sana'arsu
"idan kune kuka auromin ita tun farko saiku dawomin da ita,bani nace tatafi ba don haka billahil azim bazan taka qafata gidansu ba".


Ta fannin rufaida kuwa daga yayunta har kakarta suna sane suka mata dif sukaqi cewa komai kan batun dawowarta gida,hakanan sukaqi neman bbn amir din a wannan karon,tunda sun fahimci rufaidan halin tsiya ne kawai yake damunta,kuma iya bakin qoqarinsu sunyi kan ta zauna amma taqi,don haka suka dauke mata wuta suka fita batunta kamar basusan da zamanta a cikin gidan ba.


Da fari itama rufaidan bata damu ba,a nata ganin yadda jibril yake sonta bazai iya barinta ba,bata san cewa halayenta sun wanketa tas daga cikin zuciyarta ba ta sire masa,daga baya ta fahimci akwai lauje cikin nadi,yadda tunda tazo baibi ta tata ba,hakanan agidan babu wani me ce mata komai,sannu sannu sai hankalinta yasoma tashi,saidai tana jin girman kan ta nemi jibril din,idan tayi haka kamar tafado ne ta zubda ajinta,don haka tadinga neman hanyoyin da zata karkato da jibril amma a banza,daga qarshe ta yanke zuwa gidan mariya,ta samu wasu daga cikin kayanta masu kyau ta saida ta hada kudin tayiwa gidan mariya dirar mikiya da wata safiya.


Yanayin data iske mariyan ya bata mamaki qwarai,ta sameta ta kode ta lalace kamar ba ita ba,har tafi baya kyan gani,abun yadaure mata kai,saida suka zauna sosai take cewa da ita
"Matarnan kusan asarar kudina kawai ta sakani yi rufaida,na saida gwalagwalan da maigidan yasissiya mana nida ita,na dauki kadarorine da yawa na saida,har kayan lefena rufaida na taba,amma wallahi matar nan daga ita har yaran ko mummunan zazzabi babu wanda yatabayi,dukka malaman da nake zuwa wajensu cemin suke da gagga gaggan aljanu take aiki shi yasa muka kasa shan kan lamarin,amma naqaro kudi sai a gayyato manyan abokan aiki aljanu,ayimusu yanka suyi aikin,mutum daya tak ne yacemin tana da tashin dare,duk randa yake ba kwananta bane takan raba darenta ne tana sallah,hakanan ni shaida ce kan azumin litinin da alhamis dinta,kuma ni shaida ce kan yawaita jin karatun qur'ani da take"


"Rufaida na saida dukkan wata kadarata dana mallaka,yanzu bani da komai,dan abinda nasamu lokacin amarci sanda ludayina yana kan dawo duka sun salwanta,yanzu haka tafini da komai,shekaran jiya da doller tayi tsada ina gani tabaiwa abbansu yasaida mata gwalgwalanta tasamu ribar dubu daruruwa,daya nemi nawa nima yasaida min sai qarya na masa nakai gida ajiya amma zan amso nabashi....rufaida....gaskiya dukkan wata hanya da zanbi na lura babu riba tattare da ita,kawai na yanke shawarar zan jarraba sanya idanu naga yadda take mu'amalantarsa harta janyeshi haka,nima na gwada ingani ko za'a dace,don na fuskanci HANGEN DALA kawai na dinga yi daga wajen birni,tunda gashi har wankin hula yana neman kaini dare".


Haushine yacika rufaida,takalli mariya
"Karki bani kunya mana,kishiya zaki sallamawa kanki mariya?,kin manta mudin su waye da alwashin da mukasha sa'adda duk muka samu damar shiga kowacce mata?"
"Rufaida,gudun da babu tsira kwanciya tafishi,kuma idan an jarraba hagun taqi ai sai a koma dama,bawai ayita abu kullum jiya iyau ba,saika gwada wani hannun wataqila a dace".


Sam rufaida bata yarda da maganganun mariya ba,don itakam tariga ta sanya niyya,don haka ta kafe kai da fata kan babu gudu babu ja da baya,a haka dai sukayi sallama,daga nan cikin qawayenta ta lalubi gidan wata wai ita nusaiba,nusaiban batayi qasa a gwiwa ba ta hada rufaidan da irin malaman da takeso.


Saidai duk yadda take narka kudadenta a banza wak an mintsini kakkausa,kome kama da bbn amir bata gani ba bareshi,harta kammala idda shuru maqatau wai malam yaci shirwa.


Ta fanninsa shima babu abinda yaji,abinda kawai yadan sauya ma shine yawan fada da suka fuskanci yakoya,ita da mmn ummi suna zaune a wani yammaci suke tattaunawa,sai suka masa uzuri suka dora hakan kan lalurar halin babu dayashiga,don haka suka sake takatsantsan,da kuma sanyashi a addu'arsu ta kullum Allah yaye masa dukkan abinda ke damunsa,cikin qanqanin lokaci sai gashi yadaina.

***************


Cikin watanta na biyar da komawa gida saiga qawarta tun ta 'yammatanci ta kawo mata ziyara,suna zaune su biyun tadubi rufaida
"Ke kinga yadda kika koma?,wallahi ni kina bani mamaki rufaida,waishin me jibril yamiki ne,anya haka yabarki kuwa?,mu gamu da bamuyi auren ba fes damu munata cin duniyarmu da tsinke babu wani baqincikin da namiji dake damunmu,ta yaya zaki zauna da kyanki da quruciyarki da komai namiji yasaki a gaba da tarin bacin rai,maimakon ki miqe ki xama bazawarar zamani kishiga a dama dake,kusan kullum sai isma'il yayimin maganarki,yayi kudi yazama babban yaro,da alama har yau yana muradinki,banda haka bazai dinga tambayarki ba,ke kinga motar da yake hawa kuwa?,ke ba isma'il kawai ba,wallahi Allah duk tsaffin samarinki babu wanda bama haduwa dashi ba tare daya tambayeki ba yace kin gujeshi,to wallahi shawara daya zan baki,idan zaki yage jibril daga zuciyarki ki yageshi ,ki tashi kibi sahu,don babu wanda zai dubeki idan kika gyagije yace kin taba aure,Allah ya doka miki bargon suttura ma baki haihu dashiba bare a dameki".


Kwana tayi tana tunanin maganganun qawartata,mafi rinjaye na zuciyarta ya karkata kan tabi shawarar qawartata,don haka cikin qanqanin lokaci tasoma buga zawarci,nan da nan saiga tsaffi da sabbin samarinta sun soma dawo mata,cikin lokaci qarami kudi yasoma shigo mata,saita soma ganin baiken auren da tayi da jibril,ta dinga jin kamar wani kurkuru taje tadawo,nan tasoma dinka sabbin suturu duk da bata rasa ba,don ba qaramin lefe tasamu daga jibril din ba,tuni ta mance da igiyar dake kanta,ta manta da jibril gaba daya,abu daya take kiyayewa bata kawo kowa gaban gidansu,saboda tasan akwai qura.


Ta fannin jibril kuwa inna data gaji da shurun shi game da rufaida tayi kiranshi,fada ta masa kan lallai lallai yaje yadawo da matarshi,koma meye aime wucewa ne,hakanan babu wanda baya kuskure,kuma ko meye tayi masa ai zamanta a gida zuwa yanzu ta gane kuskurenta.


Shi kansa a yanzun zafin da yake ji game da rufaidan yaragu sosai,don haka baiyi mata gaddama ba ya amsa,kwana biyu tsakani suka shirya shida kawunnan shi da abokinsa suka isa gidansu rufaida.


Kusan kowa yayi murna da zuwan nasu,suka kuma bashi haquri gamida nuna mishi nauyinsa ne yasa suka kasa nemanshi.


Sanda aka kira rufaida sai labari yasha banban,sun zaci zatafi kowa murna amma saita qeqasa qasa tace ita sam ba zata koma ba,sosai hankalinta yatashi ma don bata zaci ma zai waiwayeta ba,sai gashi ba zato ba tsammani ya bata mata plan.


Tana komawa tadauki waya ta nemi qawarta ta zayyana mata komai,cikin bala'i da masifa tace
"Tabdijan,wallahi kada ki soma yarda,ashe jibril dan baqinciki ne ban sani ba?,dan rainin wayo da hankali,sai yanzu da yaga kin soma wuce ajinsa zai wani lallabo yace zai maidaki,wato salon ya jaza miki asara kina ji kina gani,bayan isma'il da murtala duka sun miki alqawarin aure,kuma babu wanda bai ketawa jibril na,me zaki kuma kiyi a gidansa,me zakici dashi?"
"Aikima daina bata bakinki qawata,ni mahaukaciyar inace wai?,ai wallahi ko maza sun qare,ana aure don riba washin me na tsinta a gidan jibrin,banda bacin rai da qunci,da fifita tsofin matansa akaina?,nifa bansan juya miji ba,tun ina waje kafin nayi aure,bansan isa da mulki na mace ba cikin gidan,tsinanniyar uwargidansa ta tare komai,kai matarnan Allah ya zuba mata abu,wallahi qawata a waje kafin muyi aure idan akace min zanyi wata biyu ban fiddata daga cikin gidan nan ba zan qaryata,amma sai naga abun ashe ba haka bane,to koma meye suje su qarata dagasu har jibril din,amma haihata nida aurensa,gwara naje inda koda zanyi qunci zanyi cikin ac a gaban kwanon kaji" dariya tasanya itama tana tayata sannan tace
"Ai kawai ki shirya ki rakani naje har gidan tsohuwarsa nakai mata kashen ɗanta,taja masa kunne,babu ni babu shi ato"
"Kinyi tunani mai kyau kuwa,babu damuwa jibi sai muje" da wannan shawarar sukayi sallama.


Cikin wata matsiyaciyar fitted gowan take baqa wadda tabi jikinsa,ta rataya jan mayafinta akafada,sai takalmi mai tsinin dunduniya data sanya,bayan tafkeken glass data sanya,bakinta dauke da chewing gum tana tauna qas qas,ta fannin qawarta itama kusan kalar shigar datayi kenan,a haka suka kutsa kai zuwa gidansu jibril.


Innarce ita kadai zaune a tsakar gida tana baza barkono data shanya tanason yabushe zata dakawa jidda yajin haihuwa,jin sallamarsu yasa ya daga kai tana amsa musu,fuskarta a sake saidai akwai mamaki kwance qasan fuskarta na yanayin shigar rufaida.


Miqewa tayi tana musu iso zuwa cikin falonta,rufaida ta dakatar da ita
"Kinga inna,ba shiga zamuyi ba,don ba zama ne ya kawomu ba"
"Auto,aiga tabarma" ta fada tana janyo tabarma ta shinfida musu,suna dai tsaye don kusan ita kadai tazauna saman tabarmar tata
"Inna" takira sunanta,a mamakance ta amsa tana dubanta
"Kashen jibril danki na kawo miki,kija masa kunne ki gaya masa cewa nidin yanzu ba sa'arsa bace,kuma ruwa ba sa'an kwando bane,bana aurensa a yanzu bana ra'ayi,karya sake tako qafarsa yazo gidanmu da niyyar neman wani banzan sulhunsa,niba sulhu nakeso ba"
"Haba 'yar nan haba rufaida,sulhu aiduk inda yake alkhairi ne,hakanan da mutuwar auren da rashinsa ai zaman yafi alheri"
"A'ah walllahi..." Ta dakatar da ita
"Ba irin wannan auren dan naki ba da babu ci gaba saici baya,kullum jiya iyau,ban taba jin dadinsa ba,don yadda yadaukoni a waje ba haka yaci gaba da yimin ba,to wallahi inna bari kiji,dana koma gidan jibril gwara akai gawata wallahi na gwammace na mutu" baki innar takama mamaki ya gama kasheta
"Ba za'a kai gawarki ba,abun ai baiyi zafi haka ba"
"To idan baiyi zafi ba ki gaya masa tun muna shaida juna ya rubuta takardata yabani don babu abinda zanyi dashi".


Kasa daure maganganun da yakeji suna fita daga bakin rufaidan yayi,saboda haka yafado gidan kanshi tsaye,kallon kallo aka soma yi,cikin fushi da bacin rai yasoma cewa
"Nima babu abinda zanyi dake,matuqar zaki iya bude baki ki gayawa mahaifiyata wadan nan kalaman,koda kece autar mata na haqura dake har abada,na....." Tsawar da inna ta daka mishi ita ta dakatar dashi
"Banson shirme ko sakarci,banason ka sake cewa komai jibril,wuce kawai" kamar zai shaqeta haka yabita da kallo,yayin da itama shi take kalla din cikin harara kamar idanunta zai fado tana jan hannun qawarta kana ta saki tsaki
"Idan baka qarasa fadin abinda zaka fada din ba baka haifu cikin uwarka ba" tana kaiwa nan ta sanya kai tafice,ba jibril ba hatta ina furucin ya tabata,dukka shuru sukayi bayan fitar tata kowa najin abun cikin jikinsa
"Inna,don girman Allah kibarni...." Kai ta girgiza
"Ban yarda ba jibril,bada amincewata ba" kawai saiya sanya kai yafice daga gidan don bazai iya ci gaba da zama ba,maganar ma dayazo gaya mata na an soma gano inda jirgin kayansu ya nufa duka bacin ran daya tarar ya hadiyeta gaba daya.


Kwana uku abun yana

Please Login or Register in order to submit comment