Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rabon da kuyi cacar baki ko cece kuce da ita?" Ta jefa mata tambayoyin da dukka bata bata amsar ko daya ba,bata jira amsar tata ba saita sake dorawa
"Ke abinda yake damunki indai ranki yabaci baki iya danne fushinki ba,baki iya cinye bacin rai ba,wanda hakan illane a wajen mace,bama mace ba,duk mutumin da bazai iya fin qarfin zuciyarsa ba to ba shakka bai cika mutum bq,kumq za'a yita tunzuraka saboda halinka a bayyane yake,kije kiyi tunani" da haka tabarta da wadan nan maganganun da suka sanyaya mata jiki,tana kade qurar dakin nata tana tunosu.


Daidai lokacin da rufaida ke zaune a tsakar gida tana famam gyaran uban kayan miya da hajiya zatayi tuwon sallar gobe,tattasai kwano biyu wanda tace duk sauta farke shi tacire 'ya'yan,attaruhu rabin kwano,tumatir kwano daya,sai albasa qaramin kwando da uwar kabewa qwallo guda,iya gajiya ta gaji tubus,tunda tatashi take abu daya,kai tunda tazo gidanma bata taba sanya duwawunta ta huta na minti talatin ba,ita kanta tasan ayyukan qiriqrarsu kawai hajiyan keyi wasu,ga suyar kaji data dora suna tafasa wanda za'ayi miyar dasi,kuma ta fahimci ragunan layyar hajiyan guda ukune,wanda duk yaranta dama duk sallah kowa saiya mata rago guda.


Ta rintse ido kana taja tsaki sanda radadin tattasan yake ratsa faratan hannunta,wanda hajiyan tasa duka ta yankesu amaimakon tarasu da takeyi ada
"Wai hajiya duka wadan nan kayan miyar miya za'ayi dasu?,idan ba duka zakiyi amfani dasu ba mana abar sauran daga baya a gyara tunda dare yayi" tana daga kan tabarma tana shan furarta me sanyi tace
"A'ah baki isa ba,ni ma'abociyar jama'ace,saboda haka miya nake a wadace ban saba rowa irin taku na,a gyaremin su tsaf yanzu ana miqawa ladi komai yawansu zata niqemin su" fuska tahade tasoma guna guni qasa qasa,donta soma gajiya da gashin qumar da hajiyar ke mata,har wani qashi tayi,ga baqi datayi
"Toda da bana nan waye yakemiki wannan uwar bautar?"
"Ubankine,idan kin gaji ki aje saina kirashi shi yazo ya qarasa" tafadatana janyo wayarta,tilas tabata haquri taci gaba da aikin,saboda tasani kadan daga aikin hajiyan ta rattabo masa waya,kamar tayar da wuqar tazame awajen ta kwanta haka takeji,amma bata isa ba,aikin da tunda taje gidan jibril da za'a hada dukka ayyukanta ranakun girkinta haryau batayi kamarsa ba yau gashi rana daya duka akanta,tanajin alamun shigowat saqonnin watsapp a wayarta sake qarqashin filon hajiyan amma bata da damar dauka,rabonta da wayar tun bayan sallar asuba,gashi tabar mata data a kunne,tsoroma take kada 'yar data din da take tattalawa ta qare,don bata da kudin saka wata yanzu,hajiya kuwa tasan koda mutuwa take yawo qwandala ba zata bata ba,kamar yadda ta hana abbanta da mamanta bata ko silai.


*_ALBISHIR A GAREKU MA'ABOTA KARATUN LITATTATAFANMU,GAFA DAMA TASAMU,JERIN GWANON LITTAFAN ZAFAFA BIYAR NA FARKO DANA BIYU WADANDA SUKA CIKA GUDA GOMA KENAN CIF 10,SUNZO A KAMMALE,MA'ANA DACUMENTS KAN NAIRA 1,000,JERIN LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*


*WUTSIYAR RAQUMI,GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDUL*

*K'AUNARMU & BURI DAYA NA MAMUHGHEE*

*IGIYAR ZATO & KAIMIN HALACCI NA MISS XOXO*

*DAURIN GORO & SAUYIN QADDARA NA RANO*

*ALQAWARIN ALLAH & DAURIN BOYE NA HUGUMA*


GAME BUQATARSU DUKA GOMAN ZASU TURA KATIN MTN TA WANNAN NUMBER
09032345899
SAISU TURA SHAIDAR BIYA TANAN
09032345899


MASU TURAWA TA BANKI KUMA ZASU TURA TA WANNAN ACCNT DIN

0225878823
HAFSAT KABIR UMAR
GT BANK
SAIKI TURA SHAIDAR BIYANKI GA WANNAN NUMBER
08030811300[10/3, 3:03 PM] Hadiza Tanko: 👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA TAKWAS*


*_ALBISHIR A GAREKU MA'ABOTA KARATUN LITATTATAFANMU,GAFA DAMA TASAMU,JERIN GWANON LITTAFAN ZAFAFA BIYAR NA FARKO DANA BIYU WADANDA SUKA CIKA GUDA GOMA KENAN CIF 10,SUNZO A KAMMALE,MA'ANA DACUMENTS KAN NAIRA 1,000,JERIN LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*


*WUTSIYAR RAQUMI,GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDUL*

*K'AUNARMU & BURI DAYA NA MAMUHGHEE*

*IGIYAR ZATO & NA MISS XOXO*

*DAURIN GORO & NA RANO*

*ALQAWARIN ALLAH & DAURIN BOYE NA HUGUMA*


GAME BUQATARSU DUKA GOMAN ZASU TURA KATIN MTN TA WANNAN NUMBER
09032345899
SAISU TURA SHAIDAR BIYA TANAN
09032345899


MASU TURAWA TA BANKI KUMA ZASU TURA TA WANNAN ACCNT DIN

0225878823
HAFSAT KABIR UMAR
GT BANK
SAIKI TURA SHAIDAR BIYANKI GA WANNAN NUMBER
08030811300


*_AFWAN BISA DOGON JIRA FIYE DANA BAYA_*🙏đŸŊ🙏đŸŊ




Rungume da yaronta ta shiga dakin bbn amir din da sallama,fuskarshi wadace da murmushi yadago ya amsa yana dubanta,itama ta maida masa kafin yamiqa hannu ya amshi yaron,gefansa tasamu tazauna tana masa sannu da zuwa ya amsa yana tambayarta ya suka wuni
"Lafiya qalau" ta amsa mishi.


Ya bude baki xaiyi magana tsulum rufaida tashigo tana rarraba idanu,dauke fuska mmn amir tayi kamar bata ganta ba,fuskarta a dinke taci gaba da dubansu,tana daga tsaye take duban bbn amir din,shima ita yake duba ganin yadda tayi musu tsaye aka kamar wata bodyguard
"Dan bamu guri xamuyi magana" tafada cikin salon dakewa shima fuskarshi a dinke
"Kamar yaya nabaku waje?,ka manta yau ranar girkina ce?" Wani banzan kallo ya watsa mata
"Don ranar girkinne kuma shine me?,sai akace bazanyi magana da kowa ba sai da izininki keme girki?,ki bani waje nace" takaici haushi da baqinciki suka cikata,ita zai yarfa gaban mmn amir din,ita zai ciwa fuska?,saita ja tsaki ciki ciki ta juya zatabar falon tana maganganu
"Duk dai wanda ya zalunci wani Allah bazai qyale ba,koma meye mutum kuma yayi lokacine akwai ranar qin dillanci,ranar da hajar me gari ta bata" ba wanda ya kulata acikinsu,bbn amir nema yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya danne bacin ranshi suka soma maganar da ta sanya yakirata wanda yashafi abun yanka ne ne na suna
"Naso raguna biyu na yanka mishi kamar yadda aka saba,amma wannan karon saidai haquri abubuwan" murmushi tayi
"Haba saikace yau aka fara?,duk wanda yasanmu yasanka ai yasan uzurine,wanda ba wanda yawuceshi,babu komai,albarka kawai muke nema"
"Hakane,Allah yashige mana gaba"
"Amin summa amin" ta amsa mishi
"Sai zancan taron suna,shima inajin halima wannan karon saidai ayimin afuwa" kaita girgiza
"Dama aiba dole bane shi,bare anyi basau daya ba basau biyu ba basau uku ba har hudu,kuma ni yarjewarka kawai nake nema,na gama komai" shuru yayi yana dubanta,ba shakka ba qaramin baiwar mace Allah yayi mishi ba wanda shi kansa baisan da hakan bai yanzu yake sake gani,Allah yasoshi da rahama ya kuma taimakeshi da bai barshi ya rabu da halima ba,ba shakka daya tafka babban kuskure kuma babbar hasara,don yayi imani,ya kumayi yaqinin tsakanin maryam ko rufaida bashi da guarantee akansu kan zasu iya kwatanta hakan,har gwara maryam din da yake yana ganin sauya sauye da dama tattare da ita.


"Allah yayi miki albarka halima,ubangiji ya albarkaci rayuwarki" cikin jin dadin addu'o'insa take amsawa da amin,har cikin ranta takejin dadin yadda haquri juriya da kawaici suka jawo mata babban matsayi a wajen mijinta,duk da haqurin dakau dakai ba qaramin aiki bane,amma hakanan tayi yaqi da kanta da zuciyarta taga tabi komai bisa tsari da kuma dacewa.


****** ****** *******



Ranar sunan tun safe gidan yasoma cika da jama'a,kasancewar mmn amir din 'yar dangice tako ina,suna da yawan family,duk da ba masu kudi bane amma dukkaninsu suna da rufin asiri dai dai gwargwado.


Mmn ummi ce tashigo dakin dauke da qaramin botiki da aka zuba hanji,tunda aka soma zurga zurgar da ita ake komai,tayi qoqari qwarai ta kwatanta abinda mmn amir din tasha yi mata,wanda ita bata taba gwada yi mata ba sai wannan karon,takuma ga jin dadi sosai kan fuskokinsu daga ita har bbn amir din,wanda daga qarshe harsai daya yaba mata,yakuma dauki wasu kudi duk da basu da yawa ya bata yace tasha maganin ciwon jiki.


Zata iya cewa wannan shine karon farko da irin hakan tataba faruwa tsakaninta da mijinta,taji dadi ita kanta,abun ya faranta mata,saita dinga qissima halinta nada dana yanzu,sam babu hadi,babu kuma riba ko misqala zarratin,face qarawa kai qunci takaici da baqinciki,saboda tana lura da rufaida tunda aka soma sabgogin babu abinda take sai qunci da qananun maganganu,hakanan ta lura dasabani da suketa samu da bbn amir din,sannan tunda aka soma saboda baqin hali take kulle adaki,jiyane ma kawai data amshi girki akaga wulqawarta a tsakar gidan,haka kawai ta takura rayuwarta,ta sanyawa kanta mugun kishi da baqin hali,wanda bai kai mutum ko ina face kogin takura qunci da rashin sakewa.


Mmn amir tamiqawa botikin tana cewa
"Ungo riqe mumun gama namu,wanka nakeson naje nayi kafin gidan yasoma cika" murmushi mmn amir tayi
"To aike zaki ajiye wajenki,ni nan ina naga wajen ajiya?,kuma ma zaku diba naku keda yara da babansu"
"Ok to shikenan,hanifa riqemin ummi yanzu nayi wanka nadawo" tafada tana kunce yarinyar daje bayanta tamiqa hanifa dake zaune,wadda taci kwalliya cikin shadda iri daya da sauran 'yan uwanta duka su shidan da babansu,wadda mmn amir dince ta dinka musu dukansu,yayanta ne yakawo mata ita da kudi a matsayin barka saita bar musu.


Mmn ummin na fitowa daga dakin hajiya mahaifiyar bbn amir dasu jidda sukayi sallama gidan,hakan yasa mmn ummi dawowa har suka shiga dakin maijegon,suka gaisa sannan tafita tahada dan abinda aka gama na abincin sunan ta aiko musu dashi sannan tasake wucewa daki donta shirya.


Dai dai lokacin rufaida na daki,sanye da wata tsohuwar doguwar riga ta material,wadda tun a gidansu take amfanarta,sarai taji shigowarsu,sai taja tsaki tana gyara daurin dankwalinta takoma tayi kwanciyarta cikin ranta tana ayyana
"Aikin banza aikin wofi,munafukan banza da wofi,anzo a takura mutane a sanya musu idanu,baza'a bar mutum ma da baqin talaucin dake damunsu ba,saikace wata tsiyar dan nasu ya aje a gidan" da wannan tunane tunanen tayi kwanciyarta taja wayarta tahau charting.


Hira suke sosai abinsu da mmn amir din hajiyar dasu jiddan,hajiyan nata mata godiya kan qoqarin da take
"Aiya gayamin komai,halima saidai Allah yayi miki albarka,ba qaramin dace bane gamo da matar rufin asiri,a zamanin nan samun macen da zaka shiga talauci tarufa maka asiri aiba qaramin dace bane" murmushi mmn amir tayi cikin surukuta tace
"Hajiya an riga da an zama daya koda babu zuri'a a tsakani bare akwai,ba abinda abbansu baiyi mana ba sanda yake dashi,kinga ko koda yanzun bai mana ba aiba abun damuwa bane,Allah dai ya warware yaci gaba da rufa mana asiri"
"Amin 'yar nan,amin" hajiyan tafada cikin matuqar jin dadi,da sake ganin qimar haliman,su kansu su jiddan kallonta suke suna jin dadi cikin ransu na yadda take zaune da dan uwansu.


Cikin hirarsu taji kamar suna batun za'a yiwa jidda kishiya,itadai tana saurarensu,amma bata furta komai ba tunda basu sanyata cikin maganarsu ba,ta fahimci jiddan ta rame sosai,kunnuwanta najin dukka abinda suke fada,sai abun ya bata mamaki yakuma so bata dariya yadda suka wani haqiqance kan kishiyar da za'a yiwa jiddan kowa da abinda yake cewa,saita tuna lokacin da za'a auro mata mmn ummi da rufaidan,yadda su jiddan suka zaqalqale,suka shiga suka fita,sukayi uwa sukayi makarbiya,jira ake a sannan aga gazawarta ko kasawarta,rashin haquri ko juriyarta,sai Allah yasa duka ba'a gani ba,wato su mata a sanda yaruwarsu zata shiga gidan mai mata murna suke,a sanda dan uwansu zai qaro aure murna suke,amma asanda za'a qarawa 'yaruwarsu abokiyar xama sunfi kowa shiga tashin hankali da zaqewa,to wai shin ita wadda zasu kaiwa qanwarsu ba mutum ba?,koshi dan uwansun matarsa da zaiwa abokiyar zama suke murna itadin ba mutum bace?,koba mace bace ita?,tambayoyin data dinga yiwa kanta kenan.


Sai data shiga daki sauya kaya saiga jidda tabita
"Kiyi haquri anty halima kinga nabiyoki ko?,wlh magana naketa so muyi dake"
"Babu damuwa inajinki" sai data zauna gefan gadon sannan tace
"Bakiji muna magana ba daxu,wai abban madina ne yakeson yayimin kishiya ina zaman zamana mmn amir?" Taqarashe maganar hawaye nason sakko mata,kamar dariya zata subucewa mmn amir data tuna baya amma saita danne tayi murmushi kawai sanda take zuge zif din rigarta tace
"Shine kika tada hankalinki haka kika rame kika qanjame kamar qwarangwal?" Tana qoqarin maida qwallarta tace
"Haba mmn amir,abunfa da ciwo fa"kaita gyada
"qwarai kuwa,ni zan gaya miki haka,dukka haka mukaji amma muka danne,yanzu ba gashi kamar ba'ayi ba?....." Kafin ta qarasa aka leqo kiranta,hakan yasa ta dubi jiddan
"Matakin farko kiyi qoqarin cire damuwa a ranki,don tunda yadauki damara babu abinda ya isa ya hanashi fasawa,ki samawarwa kanki nutsuwa da salama ta hanyar addu'a,saikiga komai yazo miki da sauqi,zan samu lokaci muxauna dake"
"To mmn amir na gode" tafada tana maida hawayenta.


"Wai matar gidannan unguwa tafita ne ranar suna?" Hajiyan jibril ta tambaya bayan ta idar da sallar azahar bata wulgin rufaida ba
"Wacce hajiya?" Mmn amir ta tambaya don bata tsammaci rufaidan bata shigo ba
"Amaryarku"
"Ohoo,tana nan mana hajiya....ke hanifa jeki kira antynku,kice tazo zasu gaisa da hajiya"sosai hajiyan taqule amma batace komai ba,don tuni ta fuskanci iyashegen da rufaida ke tatawa,qanwar jidda ce ta tabe baki
"Wai kamar hajiya sai an aika mata tazo ta gaisheta?"
"Uhmmm,Allah yakyauta dai kawai,amma dukka wanda ka goyadin daga baya sai kaga ba 'yan goyon bane" yayarsu jidda ta fada,itadai jiddan babu bakin magana,don ta kanta kawai take yanzun.


"Anty wai kizo inji umma ku gaisa da hajiyan abbanmu" tashi tayi tazauna sosai tadubi hanifa kana ta watsa mata daquwa
"Hajijiya ba hajiya ba,tafi ki bani waje!" Ta daka mata tsawa,dasauri yarinyar tafice takoma dakinsu
"Umma,cewa tayi hajijiya ba hajiya ba,waina taf..."
"Ya isa,banson shirme" mmn amir tayi saurin kwabarta,saidai tuni autarsu bbn amir din taji,don haka tamiqe ba tare data saurari kowa ba ta nufi dakin rufaidan.


"Me kika kira hajiya dashi?" Ta tambayi rufaidan tana tsaye akanta,saita miqe tazauna tana kallonta
"Zuwa kikayi ki dakeni na gaya miki ko kuwa?"
"Idan dukanma ya kama aisai adakekin qaramar mara kunya" miqewa tayi tana dubanta sama da qasa kana ta kwashe da dariya
"Ke baki isheni yi ba,jeki turo manyanki,bazan zauna baqincikin dan uwanku da naku ya halakani ba wallahi,gaisuwa ce bazanje na gayar da ita ba sai me?,bajin dadin danta nima nake ba saboda haka ba wanda zai sake jin dadina nima wallahi"
"Au haka kikace!.....mara..." Muryar hajiya data daka mata tsawa ya tsaidata niyyar wanke rufaidan da tayi
"Fito mata a daki kixo wuce mu tafi" haka hajiyan ta tasa ta gaba,wanda daga haka ma tattarawa tayi sukabar gidan sunan gaba daya,zuciyarta cike fal da mamakin sauyawar rufaidan,yarinyar da kusan kullum kafin suyi aure saita kirata taji yata kwana yata tashi,hakanan kusan duk qarshen wata saita mata hasafi,biyayya kamar ta ahri jibril,har take ganin duk kirki da kyautar halima rufaidan ta shafeta,ashe baka sanin haqiqanin halayyar mutum saika zauna dashi.


Basusan ya akayi labari yakai kunnen bbn amir ba,a daren daya dawo ya tada ballin babu matar data isa ta wulqanta masa uwa ta zauna lpy,lallai sai rufaida tabar mishi gidanshi,mmn amir ita tashiga tafita tagayawa hajiyan me ake ciki,takira jibril din taja masa kunne kan karya kuskura yace tatafi gida,abun yamasa ciwo,dole ya haqura yabi umarnin hajiyan ba bisa son ranshi ba,amma rufaidan tasake ganin sauyi sosai tattare dashi.


Abun itama ya baqanta mata,ace kamar ita mmn amirce zata zama jagaba wajen zamanta a gidan,lallai saita tashi tsaye ba shakka,don ita bazata zauna zaman kwaikwayon kishiya ba kamar yadda tafuskanci mmn ummi tanayi ba.


****** ******* ********


Cikin tsari tsafta gamida sanin abinda takeyi taci gaba da jegonta da rainon yaronta dayaci sunan mahaifinta,wanda cikin wasu satittika tayi bul bul tayi kyau ita da yaronta gwanin sha'awa.


Tun suna da kwana ashirin bbn amir yasoma murda kambunsa kan lallai shifa tunda yanzu tasauka ta amshi girkinta,murmushi tayi taba dubanshi cikin salon tsokana
"Haba abban amir,aina tsammaci saimunyi arba'in biyu sannan zamu koma turaka" hularshi yadauka yadora saman kanshi bayan yamiqe sannan yabata amsa
"A'ah,arba'in dubu zakuyi ba biyu ba" yana qarasa fada yafice yabarta da qyalqyaltar dariyar yadda yayi kicin kicin yana fadin gaskiyarsa,wanda dariyar tata ta fada kunnen rufaida datazo wucewa,girkinta ne,kuma sarai taga ficewar bbn amir daga dakin,gakan yasanyata qulewa.


Tunda ta fuskanci da gaske yake saita koma girki da zarar tayi arba'in saita sake qara qaimi wajen gyaran kanta cikin hikima da sirri,yadda babu wadda zata gane cikin abokan zamanta,dama tunda ta haihun ba hakanan tazauna ba,bata wasa da ruwan zafi da fruits,madarar ruwa,kunun aya,kwadon zagale me qwai,kwakwa da dabino hakanan turarukan tsuguno bayan jini yadauke,dasu kanunfari da sauransu.


Saura sati ta amshi girki sauran gyararrkinta yasoma bayyana,duk da batayi gaban idanunsu saboda gujewa motsuwar kishinsu,da kuma iya taku,amma duk da haka saida rufaida ta sanya idanu tagane komai,saboda hadin qwai da madara da wata dilka da ruwan dumi da mmn amir din kewa jikinta yasanya fatarta ruwan chaculet ta qara sheqi da sulbi.


Take hankalin rufaidan yatashi matuqa,lokacin da taketa tunanin zuwanshi gashi zai iso,nan tashiga itama hade haden magungunan mata da duk kudin data tara wanda tayi niyyar zuwa gidan mardiyya takaita wajen malaminta ne,sai taga bari ta soma kashe wannan wutar gaban nata kafin taga kamun ludayin lamarin.


Mmn amir din ta lura da duk abinda take,amma saitayi murmushi kawai tayi kamar bata gani din ba,saboda abun nata babu wani sirri ko kamun kai a ciki,duk masu tallar magungunan mata turo mata su ake daga sabbin qawayen maqwabtan da tayi,da sunyi sallama dama zasuce wajen rufaida aka turosu,haka zaga danqara ba ruwanta da duba komai nashi,herbal ne kona bature ne,yadace tayi amfani dashi ko baidace ba,indai wata ta bata lbarin ta taba amfani dashi ya mata aiki shikenan anzo wajen ita a wajenta.


Haka ranar girkinta xataita zubda kwalaye babu kyan gani,saidai mmn amir tayita biyan almajirai suna zubda sharar gidan akai akai saboda gudun idanun yaransu kada suga wani hoton banzan dabe dace ba jikin kwalin.


Randa zatakai abba(jaririn)allurarshi ta arba'in,tabiya gidan yayanta,matarshi nabude gumaman kayan bacci masu kyau,takuwa taki sa'a ta zabar mata azababbu,wasu ma sababbine fil,ta amsa tasake zabar wasu kana tawuce gida.


Kafin ranar da zata amshi girki sai data tabbatar ta tsara komai nata,hatta kayan sawar abba da zasu dinga tafiya turaka dasu ta zabesu ta kammalesu,yaranta kuma ta gama tsara musu yadda zasuyiwa kansu wasu abubuwan,hakanan ta fannin girki hadin spices da maggi tayo kala kala,ta sassauya wasu coolers nata da sauransu.


Hatta mmn ummi wannan karon ta ankara,ta fuskanci wani abu,duk da tana qoqarin gyarawa da kwaikwayo amma sai data danji kishi,don bata taba tunanin tayi haka ba ita bayan ta haihu zata koma turaka,amma saita danne itama tadauki damarar sake gyarawa.


Ana ya gobe zata koma turakar taje aka yarfa mata qananun kizo da jan lalle,wanda wuni sukayi sur ranar a waje,don haka a gajiye ta dawo ranar,mmn ummi tadauki abba tana masa rawa
"Yau kunsha wunin waje abba,irin wannan shiri abba da kuke sai muja baya ko?" Murmushi kawai mmn amir din tayi tabar mata abban a hannunta tawuce daki,ta sani kishine wanda yana nan cikin zuciyar kowacce mace,kuma yana iya motsa miki aduk sanda yaso,so dole tayi mata uzuri,don mmn ummi na iya bakin qoqarinta wajen ganin ta caccanza abubuwa marasa kyau zuwa masu kyau,shi yasa ma bata damu ba.


Abban yana hannunta har tayi wanka tasauya kaya,saita dauki wani yankan salatif data siyo musu agidan data gani ya mata kyau
"Ko zaku saka keda ummina,acan gidan nagani yamin kyau" tafada tana amsar abban gamida miqa mata salatif din,fuskarta a sake ta amsa
"Kai amma kuwa yayi kyau,to muma madan sabunta,an gode" murmushi tayi tana riqe da hannun ummi data sake wayo sosai tana gudunta ko ina suka fice zuwa dakinta.


*Har yanzu makarantar nan taku ta koyon ilimin computer wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI) naci gaba da saida foam dinta ga dalibai a matakin farko,da kuma masu neman certificate na DIPLOMA,babu shakka sai an gwada akansan na qwarai 😊😊,makarantar ta bambanta da sauran makarantun koyar da komfuta da kuka sani,idan a birnin kano da kewayenta kake/kike,k'wararrun malamai ba 'yan kuci ku bamu ba,zan iya cewa kinyi sake indai kika bari wannan babbar damar ta subuce miki/maka,maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number*

08033990209
[10/3, 3:03 PM] Hadiza Tanko: 👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA SHA TARA*

*_NEW UPDATE_*




Ana ya gobe zata koma turakar taje aka yarfa mata qananun kizo da jan lalle,wanda wuni sukayi sur ranar a waje,don haka a gajiye ta dawo ranar,mmn ummi tadauki abba tana masa rawa
"Yau kunsha wunin waje abba,irin wannan shiri abba da kuke sai muja baya ko?" Murmushi kawai mmn amir din tayi tabar mata abban a hannunta tawuce daki,ta sani kishine wanda yana nan cikin zuciyar kowacce mace,kuma yana iya motsa miki aduk sanda yaso,so dole tayi mata uzuri,don mmn ummi na iya bakin qoqarinta wajen ganin ta caccanza abubuwa marasa kyau zuwa masu kyau,shi yasa ma bata damu ba.


Abban yana hannunta har tayi wanka tasauya kaya,saita dauki wani yankan salatif data siyo musu agidan data gani ya mata kyau
"Ko zaku saka keda ummina,acan gidan nagani yamin kyau" tafada tana amsar abban gamida miqa mata salatif din,fuskarta a sake ta amsa
"Kai amma kuwa yayi kyau,to muma madan sabunta,an gode" murmushi tayi tana riqe da hannun ummi data sake wayo sosai tana gudunta ko ina suka fice zuwa dakinta.


*Har yanzu makarantar nan taku ta koyon ilimin computer wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI) naci gaba da saida foam dinta ga dalibai a matakin farko,da kuma masu neman certificate na DIPLOMA,babu shakka sai an gwada akansan na qwarai 😊😊,makarantar ta bambanta da sauran makarantun koyar da komfuta da kuka sani,idan a birnin kano da kewayenta kake/kike,k'wararrun malamai ba 'yan kuci ku bamu ba,zan iya cewa kinyi sake indai kika bari wannan babbar damar ta subuce miki/maka,maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number*

08033990209



Tun a safiyar ranar gidan yasamu gagarumin sauyi,shi kansa da ace yana magana tozai tabbatar da cewa lalle yau akwai sauyin dake shirin faruwa,don tunda ta idar da sallar asuba bata zauna ba tasoma qalqale waje waje na gidan wanda tajima tana jin haushinsa saboda yadda akayi sakaci ya lalace.


Girkin rufaida ne ranar kuma ranar zai fita daga dakinta yadawo dakin mmn amir din,don haka hatta shirin makaranta na yara ita tayi musu bata tsaya jiran tashin rufaida ba,wanda dama yawanci yaran duk ranar girkin nata sai sun makara a makaranta,koda basu makara din ba basa samun wani kulawa yadda ya kamata haka suke haquri.


Bakwai da rabi yaran sun gama shirinsu tsaf,daidai lokacin da me adaidaitan dake kaisu yaiso,hanifa tadubi mmn nasu
"Umma...abba bai tashi yabamu kudin break ba,naje na tasoshi?" Sam ko kadan ba al'adarra bace,hasalima bata yadda ko barin yaranta na shiga dakinsa ko dakin daya daga cikin matanshi idan acan yakwana da niyyar tashinsa ko zuwa karbo wani abun,hanasu take harsai sanda yafito,idan kuma ita tana dashi ta sallamesu kawai,wannan karon ma hakan ce ta faru
"A'ah,haba hanifa,lunch box dinku duka da abinci,har lemo fa na saka muku,me kuma zakuyi da kudi?" Langabe kai tayi
"Umma don Allah ko biyar ce"
"Uwar wayo,a baki takeso ta saka fa umma" cewar ahmad yana dubanta,harara ta galla masa
"Ina ruwanka?" Tafada tana tura baki
"Shikenan ya isa,amir" ta qwala mishi kira daga dakinsu sai gashi ya iso
"Ina kudin dana baka ajiya shekaran jiya?" Haka take musu lokaci zuwa lokaci takan dauki kudi da zummar batasan ma nawa bane ta basu ajiya don gwada amanar 'yaran nata,bata taba kuma ganin ba dai dai ba
"Suna can qasan kayana"
"Debomin" ya amsa mata yana komawa dakin nasu,ba jimawa yafito dasu yamiqa mata,tasa hannu tana amsa gami da cewa
"Nawa ne kudin?"
"Dari hudu da hamsin da biyar" haka kudin suke cas tasani,tana sane tasake tambayarshi,saita warware ta baiwa manyan naira goma,qananun biyar biyar dukansi,sai usman da ba'a sashi makaranta ba dake tsaye yana zaro ido suna masa gwalon shi badan makaranta bane ai,zai sanya kuka shima tabashi biyar din ,saiya shiga murna.


Sai data tabbatar sun shiga adaidaitan sannan tadawo tsakar gidan,daidai lokacin da mmn ummi ke sanya silifa dinta dake qofar daki,takalli tsakar gidan tana kama baki
"Tabdi,sannu da aiki mmn yara,yanzu duka yaushe kikai wannan aikin ina can ina bacci?" Yar qaramar dariya mmn amir tayi sannan tace
"Ai gwara ku huta,kunsha aiki da yawa,wata kusan hudu ko biyar aiba wasa ba"
"Gaskiya kin aikatu sannu" tasake fada tana duban yadda marbles din gidan yayi wani haske na daban.


Gaisawa sukayi sannan kowacce tawuce inda zata,mmn amir dakinta takoma donta gama duk abinda zatayi a tsakar gidan,ta sake kintsashi duk da amir da ahmad kansu wuce makaranta bayan sallar asuba suke share mata shi tas,sun kuma iya saboda ta horesu bata qyalesu ba wai don suna maza,idan suka mata shara sai ayita mamaki,zaki tsammaci macace tayi,a sannan abba yana bacci,saboda haka bayan tagama tasirja ragowar ruwan zafin data yiwa yan makaranta wanka tasanya a bandakin falonta tashiga tayi.


Tsaf tashirya bayan tafito cikin atamfa riga da zani,ta bulale jikinta qamshin turarukanta data yiwa tanadi saboda wannan lokacin,koda bata jego bata wasa da turare bare tanayi,qaryarka kadauki yaronta kaji yana qarni tsami ko hamami iyakar sanin da zakayi mata,ganin akwai wutar nepa saita jona burner

Please Login or Register in order to submit comment