Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takeso irinta sauya.


Sai la'asar sakaliya suka gama komai tun safe,bayan sunci abinci suka soma shirin komawa,suna tsakar falon salima ta miqo mata kudi
"Ga kudin tsohon fridge dinki" murmushi tasaki tana irgawa
"Amma sun sayeshi da daraja,ban zaci zaikai haka ba"
"Ai mutumin yace duk yadda akai asalin mai firinjin tana da tsafta,shi yasa baiyi komai ba,don babu abinda ke saurin nakasta firinji bayan rashin kunnashi sai qazanta"
"Gaskiya ne" ta fada taba raba kudin biyu
"Wannan kikaiwa innarmu kice tasaka albarka" sannan tasake fidda wasu ta baiwa yaran saboda aikin da sukasha,sauran tasake miqa mata bayan takuma cire wasu
"Acika kudin firinjin dake wajen auwalu,freezer tana nan wajensa,yace idan aka cika sai adauko,don Allah gobe ko jibi a nemo masu kawomin,a hadamin da labulayena" dai dai lokacin da mmn ummi tashigo,taji komai kan kunnenta
"Mmn amir flask din shayinki zaki aramin in qarasa kwashe ruwan zafi" ta fada tana basarwa kamar batajimusu zance ba
"Miqo mata gashican khadija" mmn amir din tafada tana nunawa khadijan inda ta aje.


Koda ta karba tafita sai zancan ya tsaya mata arai itama,anya kuwa bbn amir bai zage ya baita wani abu ba?,wannan uwar hidima haka?,aiko sanda aka aurota bataga tayi wannan hidimar ba,komai sabo,kayan furniture harda kujeru,ga labulaye da freezer ana maganarsu?,take ranta yabaci,zargin bbn amir wanda baisan ma me ake cikin gidan na don bainan sanda suka shigo kuma bata gaya mishi ba yacika zuciyarta,a haka aquntace tagama aikin nata,takoma daki tazauna taba qwafa zuciyarta cike da zargi.
[10/3, 3:02 PM] Hadiza Tanko: 👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA SHA BIYAR*



*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*


*ALKAWARIN ALLAH*

*DAURIN BOYE*

*KUNDIN KADDARATA*

*MUTUNCIN MACE*

*DANGANTAKAR ZUCI*

_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_






Dukka wadan nan abubuwan mmn amir batasan dasu ba,saboda tana cikin dakinta suna qarasa gyara kayansu amir a drower dinsu,bata ma sake ganin fuskar kowaccensu ba bare tasan da sauyin fuskarsu ba.


Baishigo ba kuwa dan halas sai bayan sallar isha'i,yaran sunajin sallamarsa gaba daya suka runtumo suna masa oyoyo,kowa ya maqalqaleshi,shima yayi mamakin ganin nasu,saboda baisan da dawowar tasu ba,hanifa ce cikin zumudi tasoma cewa
"Abba....zo kaga dakinmu yazama sabo,mama ta canza mana kayan daki" idanu yafiddo duk daya tsammaci quruciyarta ce kawai
"Kai haba hanifata,muje nagani" dai dai lokacin da rufaida tayi burum ta yaye labulenta tafito tana kallonshi
"Duk dakunan nan zaka wuce kasoma shiga nasu?" Waiwayowa yayi yana dubanta cikin mamaki,wannan bashine karon farko ba,sunsan tsarinsa,dakinta shine dakin da yake soma shiga duk sanda yadawo gidan,yayin da wadda keda girki kuma itace qarshe,daga ban zai wanka yaci abinci da sauran abubuwa
"Eh,ina nan shigowa bari nafito tukunna" daga haka yayi gaba zuwa dakin mmn amir.


Wani sabon bacin ran ne yasake taso mata,wato namiji dai munafuki ne,shi yabada kudin shi yasa yana shigowa gidan yasoma shiga dakin kenan don yaga irin kayan,banda haka ta yaya zai wuce dakunansu yashige nata?,haka tasaki labulen takoma kan kujera taxauna tana dakon shigowarsa,ta rantse yau sai tayi masa tas,saita wanke ciki dabai.


Yatsanta ta ciza tanajin zuciyarta na suya,waita yaya ma?,me yasanya yake nuna rawar qafa akan wannan tsohuwar matar tasa mai haihuwa hudu zatayi tabiyar?,bata taba tunanin xataga kwatankwacin haka daga gareshi ba,amma koma meye wallahi sai inda qarfinta yaqare.


Sanda yashiga mmn amir din na qasa a zaune,ta dora qafafunta da suka kumbura saman abu mai tudu donta samu kumburin yasabe,fuskarta a sake da fara'a ta amsa sallamarsa tana masa sannu da zuwa
"Iyyeee,shi yasa hanifata tace nazo nagani,ashe mamanta amarya tazama" yafada yana bin dakin da kallo gamida leqawa,dariya tasaki
"Da gaske dai halimatu kin zama hajjaju,eh lallai kudi basa magana" yafada cikin dalon tsokana,wannan karonma dariya yasake bata sosai
"Kai bbn amir,wani yaji wannan zancan saiya dauka da gaske kake,kawai kudin 'yar sana'ata ne dana adashin dana shiga sai yanzu na dauka na hada duka da kudin tsaffin kayana,sai yaya mansur dayamin dan ciko"
"Ma sha Allah,ma sha Allah,Allah ya sanya alkhairi,yasa rai aka yiwa"
"Amin" ta amsa cikin jin dadi.


Biyewa surutun su amir da suka dan jima basa tare yayi,sunata bashi labarin gidan inna,har yadanja lokaci ba tare daya sani ba,saida mmn amir ta ankara sannan ta fiddashi cikin dabara,amma duk da haka saida hanifa da usman suka bishi.


Da sallama itama yashigar mata kamar yadda yasaba,tana zaune ta gama cika ta gama batsewa,daqyar ta amsa idanunta kamar xai fado akanshi,ganin yaran tare dashi yasake tunzurata,cikin tsawa ta zazzare musu idanu kana tace
"Me kukazoyi?!,ku fice maza kubani waje,da wasu idanunki guru guru kamar anyi barin qwai" tuni yaran suka tsorata,sai suka wuce sumi sumi suka fice daga dakin,yayin da bbn amir yabisu da kallp har suke fice kana yamaida kallonshi kanta,yafuskanci fushi a fuskarta,hakan yasanya ya mata uzuri saboda baisan meya bata mata rai ba.


Fuskar hanifa akwabe ta shiga tana duban mamanta
"Mama" tafada kamar zata saka kuka,daga kai tayi tadubeta
"Meye haka?,ke kuma dawa?"
"Anty amaryace,muna shiga ta shine tayi mana tsawa tace mufito mata daga daki,wai da idanunmu kamar....."
"Shshahsh...." Maman amir ta dakatar da ita ta hanyar saka yatsanta akan lebanta
"Ya isa,basai kin gayamin ba,antynku batajin dadi ne,kuma idan kuka zauna surutu zakuyita sanyata da fitinarku"
"Wallahi umma bazamu mata fitina ba,aikinsan bama barna"
"Ya isa hanifa,samu waje kizauna,dauki jakankunan makarantarku ki goge muku ki baiwa yaya amir yakai muku daki" da haka takashe bakinta.


A nutse yasamu hannun kujera yazauna yana dubanta,sai huci take kamar wata macijiya
"Mun yini lpy" yafada yana duban tvn daketa aiki
"Wallahi kabani mamaki matuqa jibril,kuma sai yanzu nasake yarda da zancan hausawa dasukace namiji hankaka ne,niji tabarmar qashi,namiji qanin ajali" cikin mamaki yafidda ido yana dubanta
"Rufaida,lafiyarki qalau kuwa?,kinsan me kike fada?"
"Lafiya lau nake,ras nake,nakuma san me nake fada,kaine dai nake tunanin ba cikin hayyacinka kake ba,ka gama kallamemu da maganganun kana cikin rashi saboda kayanku da duka bace a jirgi,sai gashi ka kwashe kudi ka yiwa matarso kayan daki,ka canza mata komai da komai,mu muna zaune mun shanya baki dayake mata muka rako duniya"


Cike da tsantsar mamakin maganganun rufaidan yake kallonta,kana yanuna kanshi da yatsa
"Rufaida ni kike gayawa wadan nan maganganun?" Ya sake jaddadawa,ko daya batajin xata raga masa yau,saboda duk wani abu da take hange tattare dashi ashe HANGEN DALA NE ba shiga birni ba
"Kai nake fadawa,saboda kaima ka yaudareni,duk abubuwan dana gani a waje kafin na aureka ashe ba haka bane,idan kuma kana musu zan lasafta maka,na farko a waje koda bakazo zance ba inacewa ina da buqatar kudi kaza zaka turomin,na biyu kati baya yankewa a wayata,na uku duk inda kake nakiraka nace kazo inason ganinka ko zaka kaini waje kaza da gudunka kake zuwa,amma ko shekaran jiya da zanje gida sai keke napep nahau,sannan gaba daya a baya ka bani lokacinka,amma ayanzu ganinka saina kwana biyu,shima idan kana dakina saika kama ka kwasomin shirgin yara kuzo kucikamin waje,sannan wannan duka bai maika ba,so kake ka daidaita matsayina da matanka,harma kana neman wata daga cikinsu ta dara matsayina,wallahi nayi madamar aurenka,saboda ka gamamin romon baka gaba daya,ka nunamin cewa idan nashigo gidanka zan samu fiye da yadda nasameka a waje,amma me nasamu banda zallar baqinciki,da bautar girki da nakewa matanka,ka gayamin".


Sosai ranshi yakai qololuwar baci,idanunsa harsun sauya kala yadubeta
"Zan miki gargadi na qarshe,kin fada basau daya ba basau biyu ba,kada bakinki ya qara kiran yarana da tarkace ko shara,domin kuwa bani da kamarsu,ku dukkanku zan iya rabuwa daku amma su har abada bazan sauyasu da wasu ba,matana dakike magana akansu sanda zan aureki na gayamiki na daina sansu shi yasa na aureki?,ko baki fada ba amsar itace a'ah,na aureki saboda inasonki kamar yadda nake sonsu,ba wulaqantattu bane a wajena,suna da qima a idanuna kamar yadda kike daita,sauran dukkan abinda kika lissafa kuwa idan baki sani ba ko kin manta bari na tuna miki,aure ibada nae,gidan aure filin bautar Allah ne,saboda haka dukkan wani aiki da mace zatayi ba'a banza zai tashi ba,tana da rubutuccen lada wajen Allah,kisan me zaki dinga fadamin,ni mijinki ne ba yaronki ba,sa'annan koda ni nayiwa halimatau kayan daki ban fadi ba,abinda kikaci a waje halimatu bataci rabinsa ba,koda tacin ma tare kika ganmu daga ke har maryam,kinsan fadi tashin da mukayi tare har muka kawo wannan bigiren?,kinsan haqurin datayi da abubuwan data shanye,to ki kiyaye wannan tun lokaci bai qure miki ba"daga haka yamiqe yana shirin ficewa daga dakin,sai itama tamiqe cikin fushi,cikin maganganunsa kaf yabon mmn amir da yayi yafi komai qona ranta
"Idan ban kiyaye ba saime?,me zai faru?,iyaka dai kace zaka sakeni,to wallahi donka sakeni ma ni gaba takaini,ban tsinci komai a aurenka ba,abokan aurena kowacce tamin fintikau,gaskiyace dai bazan fasa fada maka ba ko zaka haqa rami ka bunne ni,idan ma ba'a hayyacinka kake ba gwara ka dawo dai dai" kallo daya yayi mata kawai yasanya kanshi yafice daga dakin ba tare daya sake saurararta ba,saboda yana tsoron kada zuciya da shaidan su debeshi.


Bacin ran daya fita dashi yasanya bai shiga dakin mmn ummi ba,saiya tura usman ya gaya mata yadawo,tana zaune saman kujera saita girgiza kai
"Bazaidai fasa yimin rashin adalci ba wato kenan,tome zan masa daya dawo din?" Daga haka ta shareshi taci gaba da sabgarta,don takaicinsa take ji,tana ganin ya baiwa mmn amir wani abu a boye,sannan kuma yashiga dakin kowa amma banda nata saboda wulaqanci,harya gama wankanshi yashirya yazauna kawai yanajin dacin abinda rufaidan tayi masa babu mmn ummi babu dalilinta.


Tun hankalinsa baikai wajen dadewarta bata shigo ba har yakai din,saiya miqe yafita zuwa dakin nata.


Azaune yasameta dirshan abunta,yadanne fushinsa yayi sallama ta amsa a dage
"Usman bai gaya miki na dawo bane?" A yatsine tace
"Ya gayamin" kai tsaye,saiya jinjina kanshi,don itama ua shinshino wani abu
"Toki kawomin abinci tunda saina fada" yasaki labulen yajuya,sai idanunshi yasauka kan dakin mmn amir,suna ciki abunsu ita da yaran,yana iya jin muryarsu sama sama kamar tana hada musu kayayyakin makarantarsu ne waje daya,tana nunawa amir tare da masa bayanin idan sun tashi su shirya kawai kada wanda ya tasheta da sassafe,sai yaji ranshi ya quntata,babu qarya yasan yayi kewarta,kukawarta da iya mu'amala,sauqin kai da sanyin hali,take ya zargi kansa da me yasa ya barta ta aje girki?,ya hadiye wani yawu na takaici,harya doshi dakin nata saiya sauya akala,saboda sam bai kamata taga fushinsa ba,bayan batasan hawa ba sannan batasan sauka ba.



A qalla saida sake kwashe wasu mintuna goman sannan tashigo dauke da abincin,baice nata komai ba,saidai tuni har abincin yafita daga kanshi ba tare data sani ba,zuba masa tayi ta tura masa sannan takoma kan daya daga cikin kujerun tazauna tana hade gabas da yamma.


Jan plate din yayi yasoma tsakura,minti goma tsakani sannan tace
"Amm....ina da magana" dubanta yayi kana yace
"Bismillah"
"Dama cewa nayi na hada 'yan kudadena na yiwa yaran nan dinkin sallah,to yanzu abinda yarage takalmansu da kudin dinkin,sai huluna,naira dubu goma ne nakeso kabani" tsaida cin abincin yayi cak sannan yakalleta cikin ido
"Maryam mantawa kikayi da yanayin da muke ciki?,wanda tuni ai nayi muku bayani ko?,sannan bayaga haka dukkansu da qaramar sallah dinki kala biyar biyar nayi musu,takalmi biyu hula biyu,shaddodinsu wankin inji nakai aka musu basu isa su sake sawa ba?".


Bacin ranta yafito qarara a kan fuskarta
"Baka da kudi amma kayi wannan hidimar a gidan nan?" Cikin alamun tambaya yake dubanta,da yake ita ta gane saita dora
"Dama kowa yasan nice borar gidan nan,tun kafin na tambayeka dama nayi imanin bazaka bani ba,amma Allah yana gani idanma an zalunceni,shikenan kowanne juji da bola akaina,idan na rantse bazanyi kaffara ba cewa kana da hannu kan uban canjin da akayi yau a gidan nan a dakin uwargidanka,saboda rashin tsoron Allah yanzu sai kazo kawani ce wai baka da kudi,inataga kudin wannam aikin ita kadai?,shikenan koma meye Allah yana gani,kuma yarana ni bazasu saka tsaffin kaya ba bare su fito amusu dariya ba,Allah zai horemin" daga haka tamiqe fuuuu kamar zatayi fatali da abinda ke gabanta ta wuce.


Kasa cewa komai tayi sai binta da yayi da kallo baki sake,kiran sunan Allah yadinga yi,mamaki dukka yakamshi,wato kowaccensu abinda mmn amir din tayi ya tsone musu idanu suke ganin shi ya mata?,amma abun da mamaki,shekararsu nawa da maryam?,tunda ya aureta irin wannan situation din bai taba faruwa ba a gidan tsahon shekarun,kullum cikin wadata suke,amma yanzu da tsanani yazo shine zata rufe idanunta kamar bai taba mata alkhairi ba,lallai manzan Allah S A W yayi gaskiya da yace daya daga cikin dalilan daya sanya mata sukafi yawa a wuta shine *SUNA KAFIRCEWA MAZAJENSU* ma'ana:- rainuwa,da kuma idan irin wannan yanayin ya ratsa mace ta rufe idonta kamar baka taba yi mata alkhairi ba arayuwarta.


Ita kuma rufaida dame ya rageta?,dukkan wani naqasu da gazawarta yayi haquri dasu kan hakan,yadauka cewa saboda tana matsayin budurwa ne batasan kan abubuwa ba,ya rufe idanunsa yana mata uzuri amma ita sam bata gani na,sai qoqarin dabbaqa da kururuta laifukansa take ba tare da tana hangen nata ba.


Ya aureta cikin wadata hakanan yakawo ta cikin wadatar ubagiji bakin gwargwado,ashe itama bata zama matar rufin asiri ba?.


Yana tsaka da wannan tunanin yadinga jiyo kukan hanifa,da kamar bazai fito ba saboda yanayin da jiki da zuciyarsa ke ciki,amma jin batayi shuru ba yasanyashi miqewa yafito zuwa dakin mmn amir.


Shigarsa dakin kawai ko a idanu da yanayi saiyaji ya banbamta da kowanne sashe na gidan,badon sabbin kaya dake ciki ba,a'ah,dabi'ar zuciya ce da binbini da nacin bigiren datake yawaita samu nutsuwa.


Tana zaune hanifan na zaune gefanta tana tsala kukan,yayi sallama tadago tana dubanshi ta amsa a nutse,kallo daya tayiwa idanunshi ta karanci akwai damuwa tattare dashi,yasamu hannun kujera yazauna yana miqawa hanifa hannun gami da cewa
"Meya sameta?,waya daketa" tsaki mmn amirdin taja tana zuge jakar ahmad data gama shirya masa litattafai
"Tsamigaye ne da inna tabasu nace taraba ta baiwa su mubarak,a'ah shine fa ita bazata basu ba nata ne ita kadai"
"To kuma shine kika daketa kenan" yadanyi maganar cikin kaushi kaushi wanda ke nuna zafin dake zuciyarsa,dan sak tayi tana dan karantar yanayinsa,ta fuakanci an fusatashi ne daga wani waje,bawai iya dukan hanifa ne kadai yasashi wannan furucin da kaushi ba,saita sassauta muryarta gamida sakeyin laushi tace
"Kayi haquri,Allah yahuci zuciyarka,amma 'ya'ya amanar Allahne a hannunmu,itace tun yana danye ake tanqwarashi,idan ya bushe shikenan,tun daga wadan nan shekarun kake iya gyarawa yaro halayya da bata kamata ba zuwa wadda ta kamata,yan uwanta ne,raba abu tare dasu zai sanya yaro yatashi da zuciyar kyauta,da raba duk abinda yasamu tare dana kusa dashi,amma baza'a sake ba in sha Allahu" ta qarashe maganar idanunta a qasa.



Wata wawuyar ajiyar zuciya yasaki wadda ke nuna lallai ba shakka yana cikin damuwa
"Hanifa bata da rowa,abinda kikayi kuma ba laifi bane,amma dai dukanne banso"
"Baza'a sake ba in sha Allah" tasake fada a tausashe,tare da qoqarin hakaito meya bata masa rai,bayan da wasa da dariya suka rabu yanzun babu jimawa,wala'alla ko duka zancan kayansunne da suka bata?.
"Kije fridge din dakina ki dauko muku qananun lemo kowa dai dai" da murna suka miqe suka fice,harya miqe zai bisu yatsinci muryarta
"Ka yawaita karanta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita sahla,ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis,dukkan tsanani yana tare da sauqi,hakanan babu abinda ke iya sauya qaddara sai addu'a" wani sanyi ne yasaukar masa daga kalamanta,harsai daya fidda ajiyar zuciya,yakuma kasa daurewa sai daya dubeta yace
"Madalla da mace tagari,wadda annabi yace idan ka kalleta saita faranta maka,Allah yasaka miki da mafificin alkhairi"
"Na gode da wannan yabo dana samu daga wajenka".


Cikin farinciki yafice daga dakin,wanda bai tsammaci samunsa a dan tsukukun ba,koda yakoma dakin bai bari bakinsa ya subuce daga addu'o'in ba,kafin wani lokaci duk wani qunci da yakeji sai yaji babu shi,harya kwanta mmn ummi bata dawo dakin ba,shima hakan bai wani dameshi ba,saboda yasan qarshenta idan tadawo din kwana zasuyi tana mita tana qorafi ta hanashi bacci a banza,saiya sakaya qofarsa yayi kwanciyarsa.


******************



Washegari sai qarfe goma sha daya na safe yayi shirin fita yafito,bayan mmn ummi ta aika masa da break dinsa ba tare data koda leqashi ba bare ta gaidashi,shima a ranar babu wanda yaleqa cikinsu banda mmn amir,saboda yanajin ya kamata ya nunawa kowaccensu fushinsa.


Koda zai fita ma usman yabaiwa kudin cefane yakai mata,yayi hanyar fita saiya lura qofar dakin rufaida a kulle yake,cikin mamaki ya qarasa qofar dakin,ya jijjiga kulle kam take,mamaki yasake kamashi,shidai a iya saninsa yasan cewa bata tambayeshi zata wani waje ba,saiya juya zuwa dakin mmn amir ya tambayeta kota mata magana sanda zata fita.


Tana bacci ya tasheta,tuni yaran duka sun jima a makaranta,tace mishi batasanma bata nan ba,saiya zaro wayarshi yasoma kiran layukanta.


Har ta qaraci ringing ta katse bata daga ba,haka yayita maimaitawa kusan sau biyar amma babu amsa.


Cikin damuwa mmn amir ta debeshi
"To Allah dai yasa ba wani abunne yafaru ba ko a gidansu?" Ranshi adan bace yace
"Ko wani abunne yafarun bana cikin gidanne da bazata iya gayamin ba?,saita sanya qafa tafice?" Shuru mmn amir din itadai tayi batace komai ba,saiya soma kiran layin mahaifinta.


Da sauri mmn amir tace
"Don Allah karkace kana cigiyarta,ku gaisa kawai idan wani abunne zai gaya maka" baice uffan ba harya daga,suka gaisa lafiya lafiya,sukayi sallama ba tare dayace komai ba,tabbacin bataje ba,kuma komai lafiya yake a gidan,saiya sauke wayar daga kunnensa yana maidawa aljihun shaddarsa gamida furzar da iska daga bakinsa,kana yajuya yasoma tafiya yana cewa
"Saina dawo"
"Allah yatsare hanya" ta fada a sanyaye tana addu'ar Allah ya taqaita koma meye,sabida tasani babu abunda bbn amir din yafi tsana irin leqe da fita bada saninsa ba.


Dai dai lokacin da rufaidan ke cikin dan sahu,tana gab da qarasawa gidan mariya qawarta da suka hadu gidan lallen biki wanda sukayi waya kwanaki,daren jiya tayanke shawarar zuwanta gidan,don wala'alla tasake samun haske da dabarun raba jibril da matanshi tazama ita kadaice a zuciyarsa,donta fuskanci itakam tasamu yadda takeso ba kamar ita ba,don haka babu jinkiri takirata.


Koda tashaida mata zatazo ta amsa mata tace dama itama jiran zuwan nata take,ta tura nata adress,hakan ya yiwa rufaidan dadi,ta qiyasta wala'alla an samu sabbin hanyoyin mallaka ne.


Sanda tasauka qofar gidan ta biya dan sahun sai data tsaya ta qarewa gidan kallo,ba laifi yatsaru,ta tura gate din gidan tashige,saita tsaya a farfajiyar tana kwatsa sallama,saboda part biyune da gidan,batasan wanne ne sashen mariya ba.


Jin shuru yasanyata daukar waya tasoma neman lambar mariyan zata kirata tace mata tazo,dai dai lokacin da wata mace tabude daya daga cikin sasssan gidan tafito tana amsa sallamar da akeyi.


Kallo rufaida tasoma qare mata tun daga nesan,bata da tsaho za'a iya kiranta gajeriya amma bacan ba,kalar fatarta ruwan tarwada mai kyau da qyalli,tana da madaidaitan idanu da dogon hanci.


Tun daga nesa kana iya jiyo qamshin dake tashi a jikinta,sanye take da atamfa riga da skert da suka kamata ba wani can ba,amma sun fitar da sigarta gaba daya,tana da mazaunai da albarkatun qirji wanda hakan yasanya dinkin jikin nata yazauna mata das,tayi kwalliyarta mai kyau wadda tasake qawatata ta qara mata kyau matuqa.


"Baiwar Allah wa kike nema?" Sai data dan yatsina fuska sannan tace
"Mariya amaryar gidan nan" fuska ta washe sosai cikin fara'a tamkar tasan rufaidan sannan tace
"Ayyah,sannu da zuwa,gashi kuma tafita wallahi,amma ba damuwa muje falo saina kira miki ita,inajin ba nisa tayi sosai ba" kamar ba zata bita ba,sai kuma tabita din,don tanason kallon qwaqwaf,tana gaba tana binta a baya,tana qare mata kallo,hatta tafiyarta awani nutse take,da haka har suka qarasa sashen matar,wanda suka tadda yalwataccen falo wanda keta zabga qamshin turaren wuta da airfreshner,ko ina neat kamar bacci zai daukeka saboda dadin qamshi da sanyin ac madaidaici dake tashi
"Ga guri zauna,bari na dauko wayata" matar tafada cikin fara'ar dai tanayin ciki.


Ba'a dauki wasu mintuna ba tadawo dauke da tray da wayar a hannunta,kayan breakfast ne komai da komai akai,kama daga tea mai zafi da qamshi,lallausan biredi,gefe kuma farfesun naman kan rago ne ta aje gabata,dukkansu acikin kwano suke kuma ba'a rufe ba
"Bismillah,ga abinci ki karya kafin ta dawo,duk dadai nakirata amma bata daga wayar tawa ba,amma ke ki gwada kiran nata wala'alla ta daga" dukka tayi maganar ne cikin fara'a.


Da mamaki rufaida ke kallonta tanason tantance ita din wacece?,amma saita kauda duka wannan tunanin saboda qamshin girkin dake dukan hancinta yasanya yunwarta tasowa gamida kwadayin abincin,daga qamshin kawai tasan zaiyi dandano,duk yadda taso mazewa taqici abun yaci tura,saboda haka tajawo kayan tahau kaiwa baka.


Ta kuwa kama naman dakyau,don dama tunda aka shiga wannan yanayin bbn amir bai kawo nama gidan ba,kafin ta gama matar ta aje mata juice mai sanyi,duk da haka tanaci matar na janta da hira cikin fara'a da sakin jiki tamkar ta santa.


Bata kira rufaida ba saidatayi nak sannan takirata
"Kiyi haquri,nadan fitane,amma nan da rabin awa zan dawo,dole ce ta fiddani amma gani nan" haka tace da ita,duk sai haushi yakama rufaidan,tasan zatazo amma shine zata wani fita?,da haka matar taci gaba dajan rufaidan da hira,tun tana tsumewa harta sake ganin kirkin matar ya isa,sai nan nan take da ita kamar wata 'yar uwarta.


A qalla saida rufaida ta rufa awa daya harda rabi sannan tadawo,a fusace tatur qofar falon matar gagaga,
"Yauwq,tun dazu taketa zaman jiranki,yanzu nake shirin sake kiranki tadan jima wallahi" cewar matar cikin murmushi,kallon banza mariya tayi mata sannan ta jefeta da harara sannan tace
"Munafuka algunguma,Allah ya fiki,qawata taso mutafi" lafazin saiya daurewa rufaida kai,du kirkin matar ta amsar mata baquwa irin haka amma takirata da wannan sunan,kodai bazata mata godiya ba bai kyautu ta jefeta da baqar magana ba haka,amma batace uffan ba sai tarin tambayoyi fal zuciyarta tamiqe tana saba jakarta,qarasowa tayi ta tattara sauran abinda rufaidan bata cinye ba tamiqa mata tana cewa
"Ki tafi da wannan din tunda yanzu tadawo,kyaci kafin a gama girikin rana ko?" Da sauri mariya ta figi hannun rufaida
"Da Allah taho qawata,makircinki yakusa zuwa qarshe wallahi"tafada tana nunata da yatsa.


"Wai meye haka mariya,bakiga karamcin datayimin ba?,ko bakwa shiri?" Rufaida ta tambayi mariya tana dubanta sanda mariyar ke qoqarin bude qofar bangarenta.


Wata muguwar qwafa kawai mariyan taja,idan tufaida ta lura dakyau qwalla ce tacika mata ido
"Muje ciki dai qawata tukunna zakiji komai" ta fada tana tura qofar sashen nata tasaka kai rufaida tabita a baya cikin xaquwa taji me mariyan keson gaya mata?.
[10/3, 3:02 PM] Hadiza Tanko: 👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸ *HANGEN DALA*👁ī¸â€đŸ—¨ī¸đŸ‘ī¸â€đŸ—¨ī¸
_Ba shiga birni ba_


Šī¸ÂŽī¸ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA SHA SHIDA*



*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*


*ALKAWARIN ALLAH*

*DAURIN BOYE*

*KUNDIN KADDARATA*

*MUTUNCIN MACE*

*DANGANTAKAR ZUCI*

_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_





"Wannan matar da kike gani rufaida ta bani mamaki,ashe dukka *HANGEN DALA* nayi ban shiga birnin ba sai yanzu?" Ta fada cikin sigar tambaya kamar tanason samun amsa daga rufaida.


Sai a sannna rufaida dakebin hargitsatsen falon mariyan da kallo tamaida idonta kanta tana cewa
"Kamar yaya?,yimin cikakken bayani"
"Hmmmm" tace tana gyara zamanta sosai
"Wannan matar bansan yazan fasalta miki ita ba,makira ce algunguma annamimiya,wannan matar rufaida ta rabani dakowa nawa ciki harda mijina,da shegen kisisinarta,kinga abinda tayi miki?,to kadanne akan abinda takewa dangina ko mamata idan tazo,rufaida,tabi ta karbe kowa ta kalallame kowa da kirkinta na munafunci da rashin tsoron Allah,kowa baya gani ganin laifinta,yanzu dana zagi hadiza gwara na fallawa kaina mari koda wajen 'yan gidanmu ne,idan sukazo fa wajenta sukafi zama,wai zasu zabi abinda ransu keso ta girka musu,sannan falonta yafi nawa dadin zama,bata musu fada bata hantararsu,ke mamarmu rannan cewa tayi naje wajenta nakoyi yadda ake karrama baqi kijimin wani abun baqinciki" ta qarashe zancan da alamun abun ba qaramin qona nata rai yayi ba,sai rufaida ta gyara zama tanajin ikon Allah
"Miji kuwa wallahi rufaida idan hadiza tace wannan farin mayafin nawa baqinr wuluk to zancanta haka yake koda yafi nono fari,hadiza bata laifi a wajensa,koda baya ban tayimin abu qiri qiri ba donta cusa min haushi tayi idan yadawo na gaya masa saiya hau fada,wai tunda suke da hadiza bata taba kawo mishi qarata ba,saini da kullum bani da aiki saikai masa qararta,kuma koya kirata ya tambayi algungumar wallahi koni namata abu saita saki wanu munafukin murmushi tace aiya wuce,tasan bada gangan nayi mata ba,rashin sanine kuma zan gyara,rufaida,takai takawo hadiza dai ita kejan ragamar gida da dukkan abinda yashafi dangin auwal,na zama kamar wata 'yar kallo sai abinda ta kasq zan dauka,idan kuma nayi qorafi ko gaban waye sai suce waina fiya kishi,ba'a taba jin hadiza ta nuna kishi ko tayi qorafi akaina ba,bata zancena,na raaa me take masa take dauke hankalinsa haka,kuma wallahi bata boka ko malam,ko kusa ko alama,tako ina rufaida

Please Login or Register in order to submit comment